Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallah
Tana gamawa ta miqe ta fice Dan ayyukanta data Saba dasuke gabanta.

Kunun abbanta tafara damawa kafin ta soya doya tadafa ruwan Lipton ta juye a qaramin flask ta Kai Palo tadawo ta dauki na abbanta takai masa.

Cikin dauriya tayi aikin gyaran koina ta zauna tana bawa Abban abinci,
Daga fuskarsa Yana iya Jin hucin zafin jikinta dake hurowa
Take jikinsa yayi matuqar sanyi zuciyarsa ta narke da tausayin kansu dagashi har itan
Ya zuba Mata idonuwansa dasuka sauya Yana danne hawayen Dake kokarin gangaro Masa Dan karya qara Mata damuwa akan wannan halin datake cikin.

Tana Gama basa ta gyarasa ta fice zuwa gyaran palon Momy da dakunansu,

Daqyar tagama gyaran ta dauki kasko ta fita tasamo garwashi maqota tadawo ta zuba turaren wutar kadan ta aje palon Saida ya Kama koina har dakunansu kafin ta dauka takaiwa abbanta shima ya samu tadawo da kaskon tsakar gida ta aje.

Kicin taje ta zaunda Kan kujera ta janyo abincinta tafara ci taji Bata iyacin ta dauki Kofi taje ta debo kunun babanta kadan ta zauna acan tasaka kanta Sha Dole sbd Kar ciwon yafi qarfin hakan.

Tana gamawa cikin magunan abbanta ta dudduba tasamo paracetamol Wanda Yaya abdullahi ke ajewa Dan kansa shima ta balla biyu Tasha ta fito Abban na binta da kallo zuciyarsa na sake shiga hali na damuwa.

Shanyar Momy ta kashe tayi ciki dasu ta aje gefen kujera ta zauna qasa Dan tana lumshe fararen idanuwanta dasukai duhu ga jiri datake Dan gani.

Mintuna biyar ta dauka zaune agurin kafin ta miqe ta Kashi kayan ta dauko dutsan guga daga dakin anty Sa'adah tayi palon Abba sbd acan take guga Dan palon Momy tanada center carpetย  bayan tayils din dake qasan batason a Kona Mata carpet shikuma palon abban tayils dinne kawai Dan Haka acan take gugar duk zafi kuwa ahaka take gugar ita zufa Abban zufa.

Qatuwar daddumar baqin Abban ta shimfida tazauna akai tafara gugar.

Har Saida Suka tashi daga barci suka fito gurin Sha daya kafin tagama gugar ta kwaso ta fito suna Palo zaune Momy tagama cin abinci tana waya da umma Jamila hamshaqiyar yayarta Mai abun duniya Kamar yanda take fada.

Anty Sa'adah dake Shan ruwan Lipton har lokacin tafara kalla cikin kulawa tace"

Anty Sa'adah antashi lfy?

Lfy kalau Laylah,
Gama abunda kike wani guri Zaki rakani
Yau umma Jamila nanan zuwa inason binta daga can yafimun kusa da hanyar makaranta sbd exams din zamu fara kinsanni da yawan bacci anan duk exam sainayi latti.

Ahankali ta gyada Kai tana sakewa anty Sa'adahn murmushi tace"

Allah yabaki sa'a Anty Sa'adah.

Satar kallon gefen Momy tayi kafin ta qarasa kadan gefenta cikin nutsuwa da girmamawa tace"

Barka da fitowa Momy.

Hannu kawai momyn ta iya amsa Mata dashi kafin tasaki murmushi ta juya ta shige dakin momyn da kayan gugar
tana shiga ta ajiye Kan gado ta bude Yar qaramar wardrobe din momyn ta jere Mata kayan tas ta cire na Anty Sa'adah ta aje gefe tafara gyaran gadon da momyn ta tashi
tana gamawa ta nufi toilet din dakin shima ta wanke kafin ta dauki kayan Anty Sa'adah din tafito dasu takai Mata nata dakin.

Ganin alamar yau momyn Bata fita yasa ta nufi dakinta takoma ta Dan kwanta Dan kanta Kamar zai tsage ga zazzabi.

Baccin wahalane ya dauketa har batasan yayi nisa ba Saida taji Ana tasata da qarfi
Bude idanuwanta tayi tana kallon anty Sa'adah dake tsaye kanta shirye cikin Riga da skirt na embellished atampa dark brown da gyale Sai qamshi takeyi abunta tace"

Laylah maza tashi muje
Yi sauri na tare Mana Mai napep a kofar gida yanzu zamu dawo ba jimawa.

Tashi Laylan tayi tana miqewa tsaye tace"

Bari na fadawa Momy to.

Aa muje kawai tasani.

Jan hannun laylan tayi suka fito dama da Dan hijabinta a jikinta
Sam anty Sa'adah Bata wani damu data bari ta Dan gyaggyaraba kafin fitar itadai tunda ba tube Laylan takeba bata damuba.

Suna fitowa palon Momy na zaune har lokacin tanata wayoyinta anty Sa'adah tajata suka fice har lokacin Bata saki hannuntaba.

Napep suka Shiga Saida suka hau titi ta kalli Sa'adah din tace"

Anty Sa'adah Ina zamuje ne?

Dariya anty Sa'adah tayi tana Ciro wayarta daga handbag dinta da ake Kira taga Kiran Nasir ne Mai nemanta taqi dauka ta maida wayar jakar tana cewa"

Umma Jamila zatazo muje na karbo dinki kafin mudawo tagama yininta muna dawowa wucewa kawai zamuyi nida ita.

Ahankali ta dauke kallonta daga kan anty Sa'adah din tana maidawa Kan Hanya tareda sauke boyayyan numfashi.

Anty Sa'adah da Baki daukoni munfitoba ai sbd aikin abinci da wasu ayyukan duk gasucan nabari,
Umma Jamila ma banajin komai Akan yanda takemun ba komai bane tunda ta haifeni nesa ma
Dan Allah mu koma gidan Anty Sa'adah.

Wani kallo anty Sa'adah din Tai Mata tana sakin tsokin mamaki tace"

Bazamu koma din ba saina karbo abunda muka fito karbowa.

Shiru kawai Laylan tayi tana sauraren fadan anty Sa'adah din akanta duk da dai tasan duk yanda takeda tauri da danne Abu tareda boyewa duk umma Jamila tazo gidan sai idanuwanta sunyi kwanan rashin bacci da wani Hali ranar sbd tsanar da umma Jamila din take Mata itada abbanta Dan kuwa da dama shi kansa idan tazo gidan sai ya zubda hawayen boye akan 'yarsa Laylah Dan kuwa bayyananniyar tsana tayiwa Laylah da Abban duk da shi kullum maganarta ya girbi cin amanarsa gashinan yagani.

Suna isowa shagon Mai dinkin yacewa anty Sa'adah Bai kammala ba
Dama hakan takeson ji Dan Haka ta nema guri Suka zauna tace ya kammala zata jirasa.

Kallonta Laylah tayi tana kallon agogon shagon cikin nutsuwa tace"

Anty Sa'adah karfe daya saura
Ni Zan koma gida
Kinga ban Dora abinci ba Kuma kada Momy tanason wani aikin bana Nan ga Abb....

quiet please Laylah,
Bazan barki ki komaba Zaki jira nagama tunda Nina fito Dake zamu koma tare so just sit quietly muyi zaman jira,
Fushin Momy na rashin aikinki yafi Miki zuwan umma Jamila so dubu.

Shiru tayi sbd Bata iya hayaniya ba bare tayita magiya saidai hankalinta gabaki daya Yana Kan abbanta da momyn,
Dan kuwa har cikin ranta qaunar uwa takewa momyn shiyasa Bata qaunar ta Bata Mata Rai.
ga zazzabin dake cinta har lokacin.

Zama yayi zama sune har la'asar Basu koma gidaba sai qarfe biyar Adaidaita sahu ta ajesu kofar gida
Anty Sa'adah ce agaba taba bayanta riqeda ledar kayan anty Sa'adah din suka shigo da sallama tun daga tsakar tasan Bata kyautaba qin dawowa da wuri sbd Yar dattin da gidan yayi na iska da aka danyi kamar za'ai ruwa.

Kallon inda su momyn suke zaune tsakar gida Kan babbar daddumar baqin girman momyn sun Gama cin abincin da aka kawo musu daga gidan umma Jamila din tunda yau baai abinciba Nan gidan suna magana hankali kwanci saidai shigowarsu yasa bacin ran da umma Jamilan ke dannewa tasowa ta kalli Laylah bayan ta amsa gaisuwar Sa'adah data zauna gefenta tana daukan ruwan robar swan Dake gurin ta bude tana sha
Tace"

Zainab haryanzu kin kasa gane illar jini,
Shi Abu idan akace a jininka yake to saifa iko na ubangiji,
Kinada 'ya mace budurwa a gabanki da kikewa fatar samun miji na hutawa da Jin Dadi kike Bari suna fita tare da yarinyar nan?
Ta Yaya kike tunanin namiji daya zai kallesu idanuwansa su kasa tsolewa da wannan kodaddiyar fatar ta jinin gado,
Mahaifiyarta da mahaifinta akwai wani gadon dasuka bar Mata bayan na jinin cin Amana ne,
Magana daya itace na soke fitar Sa'adah da laylan daga yau karna ji ko a labari wannan umarni nane,

Shine kina zaune zata saka qafa ta ficeย  ko aikin abinci Babu idanma kinyi baqin kunya Dole kece da tsufanki Zaki shiga kicin girka abinci
Ke kenan Haka rayuwarki zata qare a bautar Mahmud da 'yarsa bakya tunanin Taki Yar?
To Allah ya kyauta,
Sa'adah ma Inshallah saiki fara shiri ki fadawa Mahmud din babban 'dan Alhaji Sadiqu commissioner Dake aikin Lawyer a Lagos munyi mgna daย  alhajin zasuzo neman aurenta
Allah yayi Kinga tasamu miji gidan Jin Dadi da arziki Kar aja wani lokaci ayi Mata auren tasamu ta tafi gidanta inda zatai irin rayuwar da kike Mata fatar samu
Kema Kinga kin samu nutsuwa shikenan Babu Wanda zakiwa wahalar nema saiki zauna abinda yazo kibasu Wanda baizoba saisu dangana shida 'yarsa.

Idanma bazaki iyaba Ni bayan auren Sa'adah din kiban laylan Dan masu aikina duk sun isheni wlh
Saina ringa biyanki kudin aikinta Kuna dawainiyar dashi kin huta ya komaima.

Momyn dai batace komaiba sai kayan wayarta datake dubawa tana hada Kan wani lissafi
Saidai fuskarta sosai ya bayyanarda farin cikin zancen mijin Sa'adah din da akai takumayi na'am da maganar auren saidai maganar Laylah batace kala ba duk da tariga tasan cewa tabbas Sa'adah tayi aure zamanta daga ita saisu Laylah din bazai musu dadiba su dukan Dan tasan zamanta a gidan zai iya karanci Dan kuwa zata saka kanta busy ne da yawon kasuwanci ta ringa Hana kanta zaman gidan sosai.

Itadai Laylah sallah tayo tazo tanata ayyukanta batareda ta dago Kai ta iya kallonsu ba bare ta nuna damuwar zance ko daya acikin zantukan sai kaida kawonta take tana aiki.

Anty Sa'adah ma shigowar zancen aurenta cikin maganar ya hanata saka Baki ta kare Laylah tareda sanar dasu burinta dataci alwashin duk ranarda tayi aure zata tafi da Laylah Dan inganta rayuwarta da ilimi Mai zurfi na boko.

Har akai magriba Bata Gama aikin abincin data doraba
su Kuma tuni Suka shige ciki suka bar wajen ta sake share tsakar gidan kafin ta sauke abincin ta zuba a kuloli takai musu tadawo ta gyara gurin,
Bataci nata abincin ba Saida tayi wanka tayi sallah ta dawo kicin din ta Dan ci kadan ta fito ta nufi gurin abbanta.

Zaune yake Kamar kullum Kan kujerarsa zugum Yana sauraron duk abinda yake faruwa a tsakar gidan
Maganganun Umma Jamila sun tabasa sosai sbd bayajin har abada idan ba aureba zai iya bawa wani Laylah,
Yasan a yanda yake dinnan tabbas yanaji Yana gani umma Jamila zata iya daukan Laylah kamar yanda tafada Wanda yasan tabbas duk juriya da hakuri irin na Laylah taje gidan umma Jamila rayuwarta tagama Shiga hawula'i Dan Haka bazai taba Bari hakan ta faru ba
Matuqar zasuwa Sa'adah aure yasan Laylah bazata qara Jin dadiba ko sassauci Dan Haka itama auren zai Mata a inda zata ingantu Koda Babu soyayya yasan zatai daraja.

Tana qarasawo gabansa ta zauna tareda abincin data debo zata basa ya kalleta da idanuwansa dasukai ja ya Mata alamar ta matso da hannu
Ta kallesa cikin sanyin jiki kafin ta matso din batareda tace komaiba takai kunnenta bakinsa
Cikin rawar muryar Dake tafe da kakari daqyar can qasa yace"

Zan Miki aure kafin auren Sa'adah zakije inda zakiyi rayuwa kema
Allah zai Baki farin cikinda sai sunyi Miki kukan Dadi da godiya su umma Jamila........

Wani irin faduwa gabanta yayi tsananin mamaki zancensa yasata bama firgici ba sbd tasan Babu wani maganar aure a rayuwarta yanzu,
Tayi aure tabarwa wayeshi Abban.

Kallonsa takeyi cikin nisa a tunani Dan batamasan Mai zatace Masa ba kafin daga baya ta miqe ta fice ganin dare yayi.
Tana fita abdullahi na shigowa yayi Masa alamar Kira tareda fadar sunan AB TURAKI daqyar alamar shiyakeson Akira masa
Take abdullahin ya fidda wayar Abban Dake drwer wadda aka aje sbd Kiran mutanensa da basa daukan sabuwar number Amma suna daukan me sunansa ya lalubo Numbern qasar AMERICA.
#MAMUH#


๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

Mamuhgee @Arewabooks

*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin TAYAYA ZATA KALLA AMININ MAHAIFINTA A MATSAYIN MIJINYA_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*

Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya๐Ÿ‘‡๐Ÿผ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261



*_Mamuhgee 6_*


_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._



****************"
_AMB & ALT PERM Rep AB TURAKI Res,_
_North Buckhead Atlanta,_
_Geogia USA._

Baqar Lexus Ls ce datake daukan ido baqa wuluk ta kutso cikin harabar mansion din bata tsaya ko inaba sai daf da kofar shigewa babban main hall(palon) dake fara Isa daga Shiga cikin gidan Wanda girmansa da tsarinsa da komai nasa na tsarin manyan turawa ne dan Babu inda yake nuni da asalin Mai gidan ba asalin Dan qasar bane,

Tsayawa motar tayi daidai kofar shigewar
Matuqin motar ya kasheta ya bude murfin motar yafito sanye cikin normal Riga da Wandon jin blue ya rufe motar ya nufi ciki hannunsa daukeda laptop fara Sol cikin wata qaramar transparent jaka,
Yana Isa kofar Shiga ya tsaya dakyau tareda Kai hannu ya Danna doorbell
Ya dakata Dan bada Koda tsawon mintuna biyune bawai Dan jiran a bude Masa ba sai Dan yasaba da Sam ba'a yiwa uban gidan nasa karauniya ko rawar jiki a tsanake yafi buqatar komai shiyasa duk rawar kansa da rawar jikinsa idan ka gansa agaban AB Turaki zakasan girmansa da matsayinsa gurinsa na daban ne.

Gyara tsayuwarsa yayi tareda Kai hannu Kai tsaye Kan mabudin kofar ya bude gabaki daya tareda shigewa Kai tsaye kafin ya rufo ya nufi hanyar dazata sadashi da inda yasan Turakin na can.

Da masu aikin gidan yafara cin Karo sunata aikin jere abinci a babban dining room Dake dayan gefen Haka ya amsa gaisuwarsu tareda wucewa ya shige kofarda zata kaisa babban palon Mai gidan na hutawa
Ya Dan buga kofar ahankali bada babban sautiba shima tsawon minti biyu ya jira kafin ya bude yashige Yana gyarawa jakar hannunsa riqo.

Zaune yake Kan 2 seater gabaki daya hankalinsa nakan jaridar dayake karantawa kyawawan idanuwansa farare tas suna Kan jaridar
Qafarsa daya nakan daya(crossing) gabaki daya qamshin turarensa na _Bois Elite_ dake sanyin qamshin ke kashe duk wani turaren dazaka saka ka tsaya kusa dashi,

Qafar turakin Dake harde ya kalla wanda suke farare tas kaman badasu yake tafiyaba su kansu har sheqin hutu sukeyi da zallar takalma masu tsananin tsadar dasuke shiga,
ya dan gyara tsayuwarsa Yana qarasowa gurin Turakin cikeda girmamawa ya zauna kujerar one seater dake can gefen Turakin ya dago jakar daya shigo da ita da murya Mai cikeda girmamawa yace"

Angama tura duka sakonnin
wasu ambassadors dinma harsun fara dawo da bayanansu
Amma na AMB Arabi baijeba
Da alama dai Kamar sakonsa sai yazama na aike Amma dai nasake turawa ta hanyoyi biyu zuwa goben idan Babu bayanin komai daga garesa Zan shirya sakon a takardu masu stamp zanje har Nigeria din sai na isar Amma dai su sauran ga bayanin komai dasukayo reply Nan saika duba.

Zaro laptop din yayi ya bude tareda kunnawa Kai tsaye ya shiga inda sakunan suke ya taso ya Dan matso tareda juyowa da Turakin gaban laptop din.

Ninke jaridar hannunsa yayi a hankali cikin nutsuwa da wata irin haibarsa da tsananin kwarjininsa dataketa cika idon A ABDOUL din ya ajiyeta Kan wadataccen table din Dake gabansa ya dago ya zubawa screen din laptop din idanuwansa farare
Da dan hanzari A Abdoul din ya qaraso ya ajeta Kan table din gabansa Dan yaduba dakyau ya koma ya zauna kujerar daya taso.

Shiru palon yayi sai Yar sautin makekiyar TVn Dake palon tana aiki yake tashi kadan.

Ahankali yake duba sakunan harya Gama kafin ya dago fuskarsa cikin nutsuwa ya kalli A Abdoul Kai tsaye da wata irin muryarsa Mai amsa Amon tsabar nutsuwa da kwanciyar hankali tareda wani irin kamewa yace"

Samun bayanan Amb Arabi nada matuqar mahimmanci Dan Haka cikin awa ashirin da hudu idan Babu wani bayani daga garesa ka shirya kaje da kanka din.

Yes sir,
Zan fara Shirin tafiya kafin mu samesa din.

Gyada masa Kai kawai Turakin yayi tareda Kai hannu ya dauki wayarsa Dake gefe aje tanata blinking light alamar Kira nata shigowa tun dazun din,
Zubawa sunan Kiran daya shigo wayar tasa idanuwansa batareda ta dauka Kiranba har Saida ta katse Kiran
Ya dago ya kalli A Abdoul daya zuba Masa ido Yana satar kallonsa Yana tunanin da ace mace ce wayar AB Turakin da tuni ta Dade da haukace tuburan sbd idanuwansa wani irin Hasken kwarjini da rikitarwa garesu Wanda shi kansa daya Jima Yana aiki tareda dashi kullum idanuwan Turakin suka kallesa rudewA yakeyi yaji baya iya ko dagowa,
Duk manyanci da shekarun Turakin bayajin Nan kusa akwai inda samari masu sabon jini ajiki zasu Shiga Bai shiga ya takesu ba Dan kuwa shi din wani irin ingarmane Mai cika idanuwa ga ladaftarwa.

Miqewa yayi cikin girmamawa yace"

Zan qarasa office na duba sauran schedules dinka na gobe,
Ahuta lafiya.

Ficewa yayi daga palon Yana Ciro wayarsa daga aljihu da aketa Kira shima yanajin vibration dinta ba Daman dauka Yana magana da Turaki.

Bayan fitar A Abdoul sake daukan wayarsa yayi yana kallon numbern Amininsa na har abada da baida tamkarsa Dan kuwa tamkar iyaye daya suka haifesu Haka sukejin suna saigashi banbancin rayuwa yasa sunyi nesa da juna duk da dai rashin lafiyar Mahmoud din tasake nesantasu da juna sbd tun farko yasa ya daukesa gabaki daya ya maidosa Nan qasar Amma issues na familyn Mahmoud din yasa abun Bai yiyuba Dan kuwa Basu aminceba sbd daga danginsa har na uwargidansa zainab Babu Wanda ya amince da hakan sbd suna tsananin fushi dashi akan aurensa da 'dayar zainab din Wanda shine sanadin auren Dan kuwa shine yakamata ya aureta Amma yarasa meyasa Sam alokacin ko kallonta yayi sai yanajin wani irin yanayi na Jin nauyi da kawaici,
Da kansa yakejin ko kalmar aure a tsakaninsa da ita ta haramta tashiga bare har akai ga yin shine dalilin dayasa Mahmoud din ya aureta Kuma har Allah yayi rasuwarta Bai dainajin yanayi na nauyin dayakeji akantaba duk da sun girmeta sosai saidai ya alaqanta hakan da kamuwar kanta da kawaicinta tareda tsananin girman datake basa.

Dan qaramin numfashi ya sauke ahankali tareda kallon agagon _patek phillippe_ dake daure a hannunsa yayi yana tunanin time na Nigeria adaidai yanzu
Ya saka Kiran Numbern tareda Kai wayar kunnensa ahankali har lokacin qafafuwansa na harde da.

*******
Abdullahi dayaga yanata Kira ba'a dagaba saiya kalli Abban cikin sanyi yace"

Ba'a daga Kiranba Amma kila zai Kira daga baya kasan irinsa Bai cika daga wayaba kowane lokaci.

Aje wayar yayi gefen Abban Yana cewa"

Bari naje nadawo kafin anjima sai asake kira.
Ficewa yayi Yana daga tasa Yar wayar da aketa Kira tun dazu daga chemist dinsa dayake aiki.

Fitarsa ba wani jimawa wayar tafara ringing
ta gefen ido Abba da yayi nisa a tunani ya kalli wayar yaga sunan TURAKI baro baro akai take zuciyarsa tahau tsalle jikinsa yahau karkarwar son adaga Masa wayar Amma Babu kowa akusa,
Hannuwansa Dake Dan motsawa suna karkarwa yafara kokarin dagawa suna rawa sosai Amma yakasa kaiwa Kan wayar bare ya iya dagawa
Haka yanaji Yana gani Kiran ya katse
Wani Kiran yakuma shigowa daga Turakin Amma Sam Abban baida halin dagawa,

Zufane ya jiqe Abban tako Ina sbd tsananin azabar kokari da tilasta kansa dayake akan daukan wayar sbd zuciyarsa datai rauni akan yarsa da batada kowa sai shi,
Hankalinsa yarigada yayi matuqar tashi akan maganar aurarda Sa'adah dazaai da abar Laylah da umma Jamila ke maganar dauka,
Dan Haka zuciyarsa Bata cikin nutsuwa ya dimauta sosai da maganganunsu Dan kuwa ko kusan karamin kisa akace umma Jamila zataiwa Laylah yasan zata iya sbd tsanar datai Masa shida Laylan bazata taba iya daukanta Dan aikiba kawai.

Yanaji Yana gani Kiran yaringa shigowa Yana katsewa Amma baya iya dauka take hawaye suka ciko idanuwansa suna gangarowa ga azabar ciwo daya taso Mata ataken sbd tilasta kansa dayayi gurin son daukan wayar Bai ankaraba sai fadowa yayi sosai daga kujerarsa zuwa qasa
Momy data fito daga palonta tana waya taji karar faduwar tasa duk da Bata tabbatarda ko shidin ne yafadin ta katse wayar tareda juyowa tana kallon kafar palon nasa kafin dai taqarasa ciki da tunanin menene ya fadin,

Ganinsa qasa zube yanata neman juya kansa cikin azaba yasata qarasowa gurin tana kai hannuwanta duka biyu ta kamasa da dukkanin qarfinta daqyar ta dorasa Kan kujerarsa idanuwanta akansa cikeda mamakin ta yanda ya Fadi saidai ganin halinda yake ciki da hawayensa dasuka kasa tsayuwa yasata kasa magana tafara gyara Masa zamansa.

Wayarsace takuma daukan wani ringing din da Dan sauran karfinsa daya rage Masa ya kalli wayar Yana bayyarda buqatarsa ta tadaukar Masa wayar Dan Allah.

Juyawa tayi ta kalli inda wayar take
take gabanta ya buga da ganin sunan Mai Kiran ta zubawa screen din wayar ido.

Hannunsa Dake rawa yafara kokarin dagawa da neman nuna yanayi magiya akan ta taimakesa ta daga Masa Kiran.

Har saaidata kusa tsinkewa takai hannu ta dauka wayar tareda receiving Kiran tana kaiwa Kan kunnensa Abdullahi na shigowa da sallama Dan Haka ta fasa ta miqawa Abdullahin wayar tareda juyawa ta fice daga palon.

Da sauri abdullahi yaqaraso gurin abban tareda Ciro earpiece ya jona a wayar ya sakawa Abban ya Dan fita Dan basa guri yayi waya Dan idan zaiyi waya da Turaki bashi guri akeyi har saisun Gama.

Akaro na farko da Momy taji zuciyarta takasa nutsuwa da wayar Abban da Turaki sai zuciyarta ke Bata Kamar akwai wani abun daban dan kuwa zaquwar Abban da yanayinsa daya bayyanarda 'dacin zuciya fiyeda kullum yasa taji tanason Jin abinda yake faruwa Dan Haka ta fasa komawa ta juyo ta dawo tana sako qafarta palon taji abinda Abban ke fada cikin kakari da kakkarwar muryarsa dake fita daqyar cikin tsananin azaba duk da likita ya hanasa takura kansa gurin mgn sosai Dan zai iya yiwa kansa illa Amma shine ya dage a hakan yake magana Dole?
Tabbas Yau tasake shaidawa da tabbarwa da Abban baya qaunarta da 'yarta tun farko shiyasa ya zabi yaci amanarta gashi ayauma tanaji da kunnuwanta ya fifita kaunar 'yarsa akan Sa'adah,
Ta Yaya zai bude Baki ya roki Turaki akan yabasa auren 'yarsa.....

Tu.raki.....akwai...alqa..wa.rin aure tsaka..nin yayana...da..naka..idan ba..ka man..taba?
Allah..Haka..yayi damu..Akan cewan...hakan...bazata...Yi..yuba...tunda.. Allah...bai...kawo....naka...rabon...na haihuwaba...
Ayau...Ina..rokonka..Alfarma ta qarshe...wadda banda...buri ko fatar data wuce wannan alfarmar....
Nasan Allah yabaka girma....da daukakanda...kafi karfin Abinda Zan rokeka sbd banbance....da dama....
Ka cika... alqawarin hada...zuria Dani daka dauka akan...hada yayanmu auren nabaka....'yata ka aureta.....wannan itace Alfarma mafi girma dazakamun da har abada...bazan daina... gode makaba....

Innalillahi wainna ilaihirrajiun" momy yafara fada cikin mutuwar tsaye da mamaki da firgici tareda zallar mamakin Abban Dan kuwa kobai Kai zancen qarsheba tasan 'yarsa daya ambata ba babbar yarsa yake nufiba 'yar Dayafi dauka 'ya ita yake nufi.

Dan Haka Bata tsaya qarasa Jin sauran zancenva ta juyo tadawo idanuwanta na rufewa cikin tsananin takaicin kanta da haryanxu taki yarda da Abban baya qaunarta tun farko shiyasa take qara haduwa da baqin ciki,
Tayaya zaiyi tunanin bawa Turaki auren yarinyarda ba itaba hatta uwarta ya girma?
Ta Yaya zaiyi tunanin bawa Turaki auren 'yar Aminiyarsa Dan kuwa akwai shaquwa sosai a tsakaninsu Kamar yanda tasamu bayani?
Tayaya zai bawa mutuminda ko manyan masu kudi ba kowa yake samun damar ko gaisawa dashiba sai daqyar bare wannan da Babu abinda yake cikin kanta bayan aiki Dan Bata gane kowane yare saina aiki bayan ga Sa'adah Nan duk da itama turakin ya haifeta amma tanada ilimin bokonda zai iya Dan nunawa duniya ita matsayin matarsa duk matarsa tafi gaban akawo macenda zata nuna Mata komai a rayuwa sai ikon ubangiji.

Daqyar qyashin da shedan ya saka Mata ya barta takai kanta dakinta duk da tsoro ma na abun yafi yawa Dan kuwa Turakin tasan Koda kalau Abban yake shi kansa yanzu Turaki saidai a waya badai ya ringa ganinsa ba
ta zauna bakin gado tana aje numfashinta dake fita daqyar daqyar.
##MAMUH#

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

Mamuhgee @Arewabooks

*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin TAYAYA ZATA KALLA AMININ MAHAIFINTA A MATSAYIN MIJINTA?_*
*_Qaddararsuce wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*

Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya๐Ÿ‘‡๐Ÿผ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261



*_Mamuhgee 7_*
Shiru ne ya ratsa ta bangaren Turaki Wanda zancen yazo Masa a wani iri

Please Login or Register in order to submit comment