Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dan kuwa a duniya Babu abinda bazai iya yiwa Mahmoud ba matuqar Bai sabawa addininsaba saidai wannan Alfarmar tayi gabas shi yayi yamma Dan kuwa babuta yanda za'ai ya auri 'yar daya Haifa sosai,
Yar Amininsa dasuka taso tare hakama 'yar zainab,
Yana iya tuno ranarda shine ya biyawa Aminin nasa sadakin auren mahaifiyarta saikuma tayaya za'a kawo mgn irin wannan,

Ranar haihuwarta ya tuno da hadarin daya faru Wanda ta sanadinsa yahadu da tasa lalurar da haryanxu yake tareda ita ta rashin iya biyawa iyalinsa buqatar aure
To tayaya ita dinma datake yarinya Idan ya aureta zai sauke Mata nata haqqin?
Wannan abune da bazai iya ko tunaninsa ba Dan ko 'yar zainab Bai sake ganiba tun tana jaririyarta daya taba ganinta,
Dan Haka wannan al'amarine Mai girma da bazai faruba
Girmansa da duniya take gani tamkar shiga haqqine garesa agansa da auren 'yar cikinsa.....

Maida bayansa yayi ya jingina jikin lafiyayyar royal cushion set din Dake palon nasa Yana Dan rufe fararen idanuwansa ya bude cikin muryarsa Mai nutsuwa irinta masu kwanciyar hankali da murza rayuwar dala yace"

Mahmoud maganar buri da fatanmu na hada zuria wannan wani maganane dabam da mukai fata Kuma Allah Bai cika fatan ba Wanda ko bamu hada Zaria ba kariga ka zama zuriata tunda Muka zama Yan uwan juna,
Maganar bani aure kwata kwata bashineba sbd za'a shiga haqqin yarinya sbd kasan Ni din ba mazauni bane banada lokacin kowa saina aiki,hakama babu aure atsakanina da 'yayanka Dan kuwa kallon Yaya nake musu,
Idan akwai matsalane a gidan ka sanar Dani Zan inganta rayuwarta tako Ina,
Zan Bata kowace irin rayuwa kakeson nabata basai da aureba...

Kamar yanda yasan Abban akan abinda yake so dagewa Abban yayi cikin azabar ciwon daya taso Masa gadan gadan yace"

Amatsyina na ubanta nine nake rokonka cikin qasqantar da Kai Turaki ka dauketa ka tafi da ita,
Idan bazaka auretaba nabaka ita halak malak Dan Allah ka inganta rayuwarta,
Batada kowa bayan Ni Ina rokonka daka zame gatanta tana cikin maraicin uwa da uba,
Shi kadaine rokona dakuma burina da gata kacal daya dazan Mata tsawon rayuwat..........

Bai qarasaba take bakinsa ya juye sbd ciwon yagama tasowa gabaki daya take ya sake fadowa daga kujerarsa ya zube qasa Yana fitarda wani irin zufa da kumfa idanuwansa na juyawa...

Daidai shigowar Laylah daukeda ruwan dumi data debo da qaramin towel zata Dan gasa Masa qafafunsa..

Mummanar faduwa gabanta yayi ta dire kayan hannunta tayo kansa cikin mummunan yanayi tana Kira sunansa cikin iya sautinta Mara qarfi sosai Dan wahalar rayuwar tagama cinye qarfinta shiyasa komai nata a sanyi take yinsa Wanda bayan sanyin jiki hardana wahala data Gama cunyeta.

Kamosa tayi tana Kiran sunansa dukkanin jikinta na rawa sosai Kamar yanda na Abban keyi
Tana kokuwar dagasa saiga abdullahi yashigo
Shima da gudu yaqaraso cikin tsananin tashin hankalin ganinsu ahakan hankali tashe da babban sauti yace"

Meya samesa?lafiya?

Kasa magana tayi sbd halinda tariga tashiga da ganin Abban hakan sai kawai ta sauke kanta tana rintse idanuwanta bayarwa hawaye sun fito ba dan tuni qamewar zuciya yagama busar da hawayenta tuntuni Dan kuka gareta wahalar banzace shiyasa Bata kuka Dan ko taso tayi kukanma Baya zuwa....

Jiki na rawa Abdullahi ya fitarda wayarsa ya lalaubo numbern Dr Abbakar ya Danna Masa
Yana dauka cikin rudu yake fada Masa halinda Abban yake ciki take Dr Abbakar din ya kashe wayar Yana cewa ga motar asibiti Nan zuwa yanzu.

Kafin motar asibitin tazo tuni Abban yayi nisa
Abdullahi daya Gama firgicewa cikin tashin hankalin sai jijjigasa yake Yana Kiran sunansa Dan karya qarasa yin nisan Amma tuni Abban yayi nisa
Ganin hakan ta dafa bangon Dake palon sbd Jin kunnuwanta Kamar suna rufewa Dan dummmm takeji sai can taji kalma daya
Kanta ta dafe da hannu daya yayinda dayan take dafe jikin bango dashi idanuwanta sun kada sunyi jajir Babu abinda takeji Kamar tsananin radadi a zuciya da cikin kwanyar kanta Wanda ake Kira da asalin _Depression_

Su Momy Basu San abinda yake faruwaba Saida motar asibiti tazo kofar gidan aka shigo aka daukesa cikin gaggawa aka fito dashi sai alokacin Sa'adah ta fito da Dan sauri daidai Ana fitowa da Abban Wanda babu alamar numfashi atate dashi
Gabanta yayi mummunan faduwa hankali tashe ta kalli kofar palonsa datasan Laylah na ciki ta nufi palon cikin tsananin firgici tana Kiran sunan Laylan da zuwa lokacin kunnuwanta basa jin komai sai idanuwanta dake gani Suma ba sosai ba
Da gudu Sa'adah ta qarasa gurinta tana Kiran sunanta da qarfi tareda tallafota jikinta sbd sulalewa da laylan ke neman Yi qasa.

Laylah
Laylah
Meya samu Abban?
Meyake faruwa?
Kina Jina kuwa?
Karki rufe idanuwanki Laylah kalleni,
Kina bani tsoro
Dan Allah bude idanuwanta sosai ki kalleni,
Meyasa samu Abban?
Kina lafiya kuwa??
Laylah.. Laylah.. Laylah.

Sunan Momy Sa'adah din ta kwala da qarfi cikin tsananin firgici tana cewa"

Momy kizo Dan Allah Laylah ma mutuwa zatai tabarni
Na shiga uku,
Momy....Momy Dan Allah kizo...

Momy dake zaune jagwab a Palo tana tsiyayar hawaye bayan tafiyar da akai da Abban tanajin Sa'adah Amma takasa motsawa Bare ta tashi saima wani irin sabon mawuyacin halinda take sake Shiga akan komai dayake faruwa tanajin radadinta na shekaru Yana ninkuwa sbd har cikin ranta ba rayuwar dataso su gudanarba da Mahmoud da 'yarta,
Meyasa komai ya lalace musu Haka,
Ina amfanin hakan,
Ta Rasa yanda zatai ta gogewa zuciyarta komai shiyasa tata zuciyar take cikin qunci fiyeda Mahmoud din Dan kuwa takasa cirewa,
Takasa daina Jin zafin na sabuntar Mata koyaushe,
Tabbas da Bata ganin Laylah da zata iya dannewa,
Amma koyaushe ta wayi gari taga laylan ko taji motsinta saita tuno Kunci da baqin ciki tareda mawuyacin halin data shiga duk akan wannan al'amarin da Mahmoud yabarta acikin quncin da sanin aurensa yayi Ashe yabarta tana bibiyar Yan uwanta gurin tallafa Mata da 'yarta.

Hawaye takeyi sosai tana buga kanta akan kujera zuciyarta cikin qunci Mai girma yayinda Sa'adah keta ihun Kiran momyn cikin tsananin firgici da nata hawayen Dan kuwa wannan ne Karo na farko da Laylah tashiga irin wannan halin Dan har wani kakkarwa jikin laylan keyi.

Ganin ba wani taimako daga kowa yasa Sa'adah zame Laylan daga jikinta da sauri jikinta na rawa ta debo ruwan zafin da laylan tashigo dasu tun farko tazo tazubawa laylan da yawa a fuskarta tana Kiran sunanta cikin fatar tadawo hayyacinta....

Kamar bazata dawo hayyacin nataba sai gashi ta bude idanuwanta ta zubawa fuskar anty Sa'adah din dake kanta cikin firgici tana jiran farkawarta....

Batareda ta motsaba ta maida idanuwanta Kan hancin anty Sa'adah din Dake digar da jini alamar habo
Duk da halin datake ciki sai data Kai hannu Kan hancin Sa'adah din da qaramin sauti tace'

Jini hancinki anty Sa'adah.

Da sauri Sa'adahn ta saketa tana tare hancin cikin mamaki da Dan sauran firgicin data Shiga na halinda Laylan da abban suke ta miqe tana juyawa da sauri ta fice zuwa waje hannunta toshe da hancin ta nufa bakin fanfo ta kunna tana gogewa da hannunta tana wanke hannun a fanfo.

A sulale Laylah ta fito ta nufi dakinta ta shige ta zube qasa Kan dadduma tareda cusa kanta cikin qafafunta kanta na tsananin sarawa kamar zai juye
Gashi Babu Wanda zata tambaya Ya Abbanta sai lokacinda Abdullahi yadawo,
Shin Abbanta Yana Raye kuwa
Kokuwa shima ya rasu ya barta a duniyar da Babu komai acikinta sai son zuciya da zabi.

Ta bangaren Sa'adah tana Gama wankewa ciki tayo ta nufi dakin Momy data bar palon Takoma dakinta ta zauna bakin gado tareda dafe kanta dake tsananin Mata ciwo itama
Ta qaraso gurin momyn ta zauna gefenta tareda riqo dayan hannun momyn da idanuwanta sukai jajir itama idanuwanta suka ciko da hawayen tausayin momyn cikin tsananin kulawa da sanyin jiki tace"

Inshallah wata Rana Zaki komai ya wanke daga zuciyarki
Kici gaba da daurewa ahakan yafi kibar zuciyarki ta ri jayeki
karki Bari shedan yafi qarfinki,
Wata Rana zakiji zuciyarki ta saki gabaki daya
Amma Dan Allah Momy ki sassauta muku ku dukan sbd zuwa yanzu Babu Wanda baya cikin mawuyacin hali acikinku,
Abba lafiyarsa da rayuwarsa gabaki daya acikin jarabawa suke
Ta yanda ma ko yaso neman yafiyarki bazai iyaba Dan Allah Momy ki saki komai kibar rayuwarki tasamu salama da nutsuwarda kowace irin zuciya ke samu.
Na Miki alqawarin idan ganin Laylah ne damuwar daga ranar da nayi aure zanbar gidan Nan Zan tafi da ita bazata sake dawowa ba har sai ranarda zuciyarki ta samu aminci da ita wannan shine alqawarina agareki umma sbd bakisan iya qaddarar da Allah ya rubuto a tsakaninki da itaba Dan kuwa dagani har ita bakisan waye Zai zana gatankiba alokacinda tsufa ko ciwo ya riskeki,
Inaji ajikina Laylah zata zame Miki farin ciki abin alfahari Inshallah
Amma saikin bar zuciyarki ta amsa qaddarar da Allah yariga ya rubuto a tsakaninku wadda ta Dade da wucewa ki yadda cewa Laylah 'ya ce daga wata uwar.

Ko motsawa momyn batayiba Dan kuwa sosai takejin nauyi Mai qarfi a zuciyarta,
Ita kanta tanason yayewa zuciyarta uqubar datake ciki Dan kuwa tsawon shekarun itama batayisu cikin farin cikiba ko kadan saidai Haka Allah ya halicceta da tata zuciyar riqon Mai qarfi.


Har tsakiyar dare Babu wani bayani daga asibiti sai zaman jiran tsammani da kowa keyi a dakinsa batareda kowannensu ya rintsa ba.

Laylah daqyar taga safiyar ta waye Mata tayi sallah hakanan ta fito tafara ayyukan Dake kanta batareda jikinta ya bayyanarda halinda zuciyarta take ciki ba,
Sa'adah da itama Bata cikin walwalar sbd tunanin Halinda Laylan take ciki da Abban danma takira abdullahi taji jikin Abban Wanda har lokacin Ba wani labari Mai Dadi
Tafito Dan Taya Laylah aiki sbd rage Mata damuwa duk da tasan Bata nunawa.

Ganin irin yanayin laylan na sanyi data qara yasata dauko wayarta takira Mata Abdullahi ta miqa Mata wayar cikin qarfin hali ta tambaya jikin Abban
Abdullahi ya tabbatar Mata da Abban Yana Raye saidai kam Yana kwance Babu wani Sauki saidai daga ubangiji.

Adduar samun lafiya Tai Masa ta miqawa Sa'adah wayar tana cewa"

Nagode anty Sa'adah.

Dafa kanta Sa'adah tayi tana cewa"

Kiyi kokari ki fitarda damuwarki zakiji sassauci cikin zuciyarki.

Wani irin murmushi kawai tayi tana cigaba da juye ruwan Lipton din data dafa acikin flask.

Itada anty Sa'adah yau sukai aikin abincin Rana kafin Anty Sa'adah din tasata tayi wanka tace ta shiryo suje asibitin.

Cikin sanyi ta shirya suka nufa asibiti a napep
Koda suka Isa Abdullahi bayanan yaje gida wanka da cin abinci ya Dan huta kafin yadawo Dan Haka su suka wuni a asibitin
Takasa dauke ido daga kan mahaifinta da cikin lokaci qanqani ciwo ya qarasa zabgesa Dan kuwa fuskarsa tuni Tayi wani irin rama Mai tsanani raunar da zuciyar duk wani Mai qaunarsa.

Anty Sa'adah ma zuru tayi ta zuba Masa nata idanuwan tanajin tausayin kanta da Babu shaquwa tsakaninta da mahaifinta Wanda Momy da 'yan uwanta ke nesantata dashi sbd cusa Mata Jin zafinsa akan abinda yayiwa momyn saidai har ga Allah tasan akwai tsananin tausayi da qaunar mahaifinta cikin ranta,tana nesanta kanta dashi sbd karta qarawa momyn takaicinsu Abban da Laylah
Saidai Bata iya nesanta kanta da Laylah Dan lura da hakan shine abinda Abban yafi so da kauna
Ta zabi tasakasa farin ciki daga nesa ta hanyar bawa Laylah dukkanin kulawarta da qaunarta.
#MAMUH#



👇👇👇Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete 👇👇

Mamuhgee @Arewabooks

*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin TAYAYA ZATA KALLA AMININ MAHAIFINTA A MATSAYIN MIJINTA?_*
*_Qaddararsuce wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*

Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261


My



*_Mamuhgee 8_*
_ArewaBooks@Mamuhgee_

Yini sukai a asibitin sai dare suka koma gida suka Bar Abdullahi
Koda suka Isa gida Momy na kwance a daki zazzabi Mai qarfi ya kwantar da ita Dan Haka cikin daren Laylah tahau wani aikin ta Dora Mata ruwan tea da maganinta na Hausa data fiye Sha takawo Mata lokacin Sa'adah na zaune gefen gadon tana Mata sannu cikin kulawa ita ta karba maganin da tea din Laylah ta juya ta fice taje ta rufe gida tadawo tayi sallar ishai da basuyiba acan asibiti tayi dakinta ta kwanta tareda rufe idanuwanta kawai.

Washe gari tunda safe tayi dukkanin ayyukanta tayi wanka ta zauna ko anty Sa'adah zatace suje asibiti sai gashi batace din ba
Momy ce kawai ta shirya ta fice zuwa asibitin Dan ji daga likitoci dake jiranta.

Lokacinda Dr Abbakar yagama yimata bayanin Abban yariga yashiga coma sai ranarda Allah yayi ikon tashinsa shiru tayi tareda qurawa Abban idanuwanta dasukai jajir
gabaki daya kamanninsa sun sauya
Oxygen ne a bakinsa Wanda yake Dan taimakawa rayuwarsa datake hannun ubangiji Dan Jan numfashin duniya,
Fuskarsa tayi haske fayau kamar Wanda babu digon jini a jikinsa
Ta sauke Kai tana Jin inama zata iya dawo da baya gaba data dawo musu da bayarsu dasuke su kadai daga ita saishi
Tabasa dukkanin kaunarta da kulawarta data Saba basa,
Bata buqatan Yan uwanta ko nasa su kadai takeson suyi rayuwa
Idanma zaiyi aure saiya fada Mata ta rarrashi zuciyarta ta dauka
Amma duk wannan bazai yiyuba sbd wannan shine asalin hukuncinta sakamakonta na bujirewa iyaye.

Duk yanda taso kasa daurewa tayi bayan fitar Dr Abbakar Saida wasu irin hawaye masu tsananin zafi da Daci suka kubuce Mata ta Sunkuyar dakai sunata gangarowa Kan fuskarta zuwa kirjinta ta rintse ido kukanta yafara fitarda sauti ahankali Mai tsima zuciya.

Ta Jima cikin wannan halin tana kuka Mai quna da radadin zuciya kafin ta danne ta share hawayenta tareda goge fuskarta ta miqe ta fice batareda tambayar kudin lalurar asibitinba sbd sanin asibitin da likitocin asibitin duk na Turaki ne Wanda takanas sbd qarin lalurar Abban ya budeta Dan Haka komai na Abban a asibitin na musamman ne ko sisi basa biya.

Gida tadawo tashige daki tashige ta lalubo nata maganin Hawan jinin tana kokarin fitowa neman ruwa saiga Laylah tashigo dakin daukeda ruwa a jug takawo Mata masu Dan sanyi ganin tadawo cikin zafin Rana da ake kwadawa.

Qurawa jug din idanuwanta dasukai jajir tayi Momy tayi tanajin idanuwan na kokarin sake cikowa da hawaye ta miqa hannu ta karba jug din da cup ta aje tana zubawa tasha maganinta batareda ta dago ta kalli fuskar Laylah dinba wadda itama tuni ta sauke Kai tareda juyawa zuciyarta na sake karyarwa da yanayin data ga momyn aciki wadda itama ta tabbatarda rayuwar kawai takeyi ba acikin Jin dadiba sbd damuwar dukkanin komai da komai ma.
Bayan fitar Laylah komawa Momy tayi ta kwanta bakin gado tareda rufe idanuwanta dasukai ja da nauyi tanajin yanda zuciyarta ke azabtar da ita.

Itama laylah kasa komawa dakinta tayi ta zauna tsakar gidan sbd rashin sanin mezatai,ga Anty Sa'adah na daki sbd yauma wani irin habo tayi Mai yawa Wanda yasata kwantawa ko zata samu damarsa Wanda take ganin zafin da ake zubawa yau dinne yasata habon jinin ta hanci duk da Bata taba yinsaba sai jiya dakuma yau dinma dayazo Mata.

Yini tayi Babu kowa daya fito daga momyn har Anty Sa'adah din
Kowa da halinda yake ciki
Itama daurewa kawai takeyi Amma tana cikin tsananin pressure da wani irin yanayi datake ji Wanda ake Kira da asalin depression Dan kuwa ko numfashi tayi Jin takeyi kamar mutuwa zatafi Mata sauki akansa,
Batada Wanda zatai magana dashi kokuma muamala dashi dazai rage Mata tsananin nauyi da zuciyarta take ciki akan halinda Abbanta take ciki.

Haka aka kwana gidan Babu motsin kowa
Washe gari ma Haka suka wuni sbd ciwon Kai Mai qarfi sosai ya kwantarda Momy
Anty Sa'adah ma da ciwon gabobi ta tashi yau din sbd kwanciyar data wuni jiyan akan nosebleed din datai Dan Haka yau gabaki daya hankalinta a juye yake Haka ta juye da aikin kulawa dasu ga tunanin abbanta Dan Haka itama sai ciwon yashigeta na zazzabi Mai qarfi sbd kasa ko cin abinci datai
Koda akai kwana biyu ahakan gabaki daya ta birkice depression yayi Mata tsanani Dan kuwa ko kalma daya Bata samu Wanda ta furtawaba
Dan kuwa anty Sa'adah sosai zazzabin ciwon gabobi ya kamata har Saida Momy taga tsananin al'amarin ta tilasatawa kanta danne nata ciwon ta tashi takai Anty Sa'adah asibitin sukabar Laylah ita kadai a gidan sai alokacin ta zauna tsakiyar dakinta tareda cusa kanta cikin qafafunta wasu hawaye datafi shekara nawa Bata zubda ba suka gangaro da idanuwanta dasukai jajir Dan kuwa ko taso kuka da dama Bata iyayi Dan baya zuwa Amma yau gabaki daya Tama rasa Yaya take,
Wane yanayi takeji,
Menene amfanin wannan rayuwar tata da Babu kowa aciki sai ita kadai da zuciyarta da tunaninta tareda quncinta.
Hawayen na gangarowa daga cikin idanuwan nata wani irin kuka yazo Mata Mara sauti ko kadan Dan ko qarfin kukan batada Dan Haka ta sulale ta kwanta agurin tana rintse idanuwanta.




A asibiti Saida suka Bata layi kafin suka samu ganin likita Dan Dan sunyi lattin zuwa,
Dunata likita yayi tareda rubuta Mata magani akan Tasha idan kwana biyu Bata warware ba zasu Mata wasu test saisu gani idan wata matsalarce babba.

Cikin ikon Allah kwana biyu tanashan maganin saigashi ta warware sosai Takoma walwalarta sai Alokacin ta lura da Sosai Laylan ta firgice kamar wadda tafara samun damuwar qwaqwalwa sai Kuma hankalinta ya tashi Dan Haka saita qi cigaba da zuwa makaranta tafara kokarin ganin ta dawo da Laylan daidai.

Asibiti ta ringa kaita gurin Abban kullum suna dubosa ko hakan zaisa tadawo daidai Amma sai hakan yake qara dagula Mata komai sbd duk ta kalla Mahaifinta ahalinda yake ciki komai sake rikice Mata yake musamman da Dr Abbakar ya tabbatar musu da Abban Yana Nan ahakan sai abunda Allah yayi kodai ya tashi kokuma daga hakan shikenan Allah ne kawai yasan abunda ya yanke akansa.

Ranar da akai musu wannan bayanin duk da anty Sa'adah tashiga wani halin itama Amma ganin halinda Laylan tashiga duk da Bata cewa kala sai hakan yayi mummunan daga Mata hankali da kuwa a bayyane tafara fahimtar depression ne yake neman juya kwakwalwar Laylah din
Haka tashiga mayuyacin halin neman mafitar tallafawa rayuwar Laylah din Dan kuwa alqawarine ta dauka zata cikawa Abba burin bawa Laylah kyakkyawar rayuwa Inshallah.

Ta bangaren Momy ganin yanda kowa yake cikin mummanan Hali na rayuwa yasa ta Amincewa umma Jamila Akan buqatar ayi auren Sa'adah ko ita zata samu ta fita daga wannan qaddarar rayuwar tasu taje gidanta tasamu rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwarda su suka rasa ahaka suka share kusan wata biyu.

*****
Zaune suke a palon gidan Momy na zaune shiru ta zubawa Sa'adah da duk ta lalace sbd rashin kwanciyar hankali ido tanaji tsananin tausayinta Dan kuwa a yanzune ta tabbatarda son da Sa'adah kewa Laylan Mai qarfi ne Dan kuwa wani irin so taga tanai Mata tamkar Wanda uwa kewa danta,
Ta tattara karatu ta daina zuwa tsawon watan biyu ta tattara rayuwarta gurin kokarin dawo da Laylan daidai wadda yanzu bayan idanuwa datake zubawa kowa ko magana Bata iyayi Dan kamar qwaqwalwarta ta tabu gashi basuda wani kudi ko arzikin nema Mata magani sai momyn ta zubawa sarautar Allah idanuwa Dan kaf Yan uwanta tasan bazasu bada taimakonda za'a nemawa laylan lafiya ba sai itama yanayin laylan yafara tabata sbd Sa'adah da al'amarin ya taba sosai Dan hatta ayyukan gidan sun dawo Kan Sa'adah da kula da laylah wadda ba jinyar kwanciya takeba jinyar qwaqwalwa take.

Cikin 'dan zafi umma Jamila ta kalli Momy kafin ta maida kallonta Kan Sa'adah dake zaune gabansu tace"

Yanzu Zainab kina kallo Sa'adah zata lalata rayuwarta da kanta gurin kulada Mai ciwon qwaqwalwa bayan tanada rayuwa Mai kyau datake jiranta Amma ta kafe akan bazatai auren ba matuqar baza'a barta ta tafi da wannan Mai Kama da Marmaid din ba,
Ta Yaya kike tunanin za'a Kai budurwar Amarya dakinta ace anhadata tafiya da wata budurwar?
Waye mijin zai kalla a tsakaninsu?
Waye Zaifi Shiga ransa tunda kinsan ko a kyau da sigarsu ba daya ba
Waccar din kinaga daukan idone da ita duk da batada lafiya ga maza yanzu baka Basu Amana,
Gskia nidai ban amince ba
Babu inda za'a tafi da wannan yarinyar musamman yanzu datake kamar Mai ciwon qwaqwalwa..

Numfashi Momy ta sauke tana rintse idanuwanta cikin yanayi na gajiya da komai da komai na rayuwa ta bude Baki ahankali tace"

Sa'adah banida wani sanyin idaniya a yanzu bayan ke Dan Haka fatana da burina ganin kinyi aure kin samu ingantacciyar rayuwa,
Naga qaunar da kikewa Laylah nayi Miki alqawarin har abada bazan rabaku ba saidai aure Dole zai rabaku
Idan inganta rayuwarta kikeson Yi Dan ki rabata da zama Dani bayan tafiyarki namiki alqawarin barin ta tafi tayi tata rayuwar gidan nata auren Dan kuwa Abbanku ranarda ciwon Nan zai kwantar dashi Aurenta yaso badawa Dan dauketa daga gareni sbd kuna ganin nice ukubarta....

Shiru tayi wani Daci da qunci na sake mamaye zuciyarta sbd ita kadai tasan radadin datake ciki na duk abubuwan dake faruwa.

Da mamaki umma Jamila take kallonta da cewa"

Aure Kuma?
Hala dai Abdullahi zai bawa aurenta?
Amma kuwa za'a tauyesa da yawa yaron Nan
Yana fama da jinyar uban Kuma yanzu sai a basa wata kayan lalurar.

Girgiza Kai Momy tayi jiki amace da damuwa tace"

Ko a hali na ciwo Mahaifinta ya bayyanarda cewa nida 'yata mune daga baya,
Dan kuwa inda ya bayarda aurenta guri ne daba gurin wasan kowaba Dan kuwa ko yayane sarakuna suka samu wannan matsayin sai anmusu barka bare anan....

Mamakine yakama umma Jamila ta kalli Sa'adah wadda duk ta yamutse gwanin tausayi tace"

Tashi kije idan nagama da momynki Zan dawo kanki Dan kuwa aure Babu fashi Kuma Babu inda Zaki tafi da ita.

Miqewa Sa'adah tayi ta juya ta nufi hanyar dakinta da tuni ta maida Laylah dakin nata tashige
Momyn tabita da idanuwanta dasukai laushi cikin sabon tausayin 'yarta da hakanan takejin sabon son yarta akowane safiya Yana qara qarfi aranta
Gashi duk ta rame tasawa ranta damuwa da Jin Kamar tanada hannu acikin kowane Hali Laylah tashiga.

Kallon tsaf umma Jamila tayiwa Momy Kai tsaye tana Shirin magana Momy ta datasan tambayar dazatai Mata ta katseta da cewa"

_*ABU TURAB TURAKI*_ ........

Da wani irin mamakin kasa gasgatawa ta kalli momyn ba tsayawa komai ta Dora tata tambayar da cewa"

AB TURAKI dai wannan Dana sani?
Aminin Mahmoud din?
Wannan dai Mai yiwa masu kudinma wuyar gani?.....

Kasa magana Momy tayi ta gyadawa umma Jamilan Kai tana maida bayanta jikin kujera ta jingina.
#MAMUH#


👇👇👇Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete 👇👇

Mamuhgee @Arewabooks

🔥🔥🔥🔥🔥
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261



*_Mamuhgee 9_*

_ArewaBooks@Mamuhgee_

Wani irin tunani Umma Jamila tashiga zuciyarta na juya zancen Dan kuwa Sam ba zancene dazakayi gangancin yardaba lokaci daya duk da tasan Momy ta wuce ace tana qarya ko Wasa da magana irin wannan
To Amma Kuma tsakani da Allah duk Mai lafiyayyan hankali bazai yarda da Jin maganar auren Mutum Kamar AB TURAKI ba lokaci daya ya yarda musamman da yarinya 'yar cikinsa 'yar Amininsa dasuka taso tare....
Roqan Alfarma Mahmoud yayi Amma tabbas wannan magana bama Mai karbuwa bace ga kunnuwan mutane jama'a bare shi Turakin,
Bayan hakan ko 'yayan manyan attajirai bazasu iya kishi da matarsa ba wadda duk Wanda ke bibiyar labaransu a duniya yasan mace ce datake zuba wata irin Rayuwar hutawa da Jin Dadi sbd babbar damar da Allah yabasu ta arziki da suna hakama ga kyawu duk da shekarunta sun Dan fara ja Amma sbd Bata taba haihuwaba yasa Bata daina zuba rayuwar data Saba da itaba,
To irin wannan ko masu aikin gidan tako Ina sunfi Laylah din bare Matar gidan har aje Kan Mai gidan kankat Wanda ita kanta Matar tasa saita share lokaci Bata gansaba bare wani Mahmoud da wata 'yar sa Mai Kama da aljanar ruwa.

Girgiza kanta tayi tana kokarin yakice zancen karta cinnawa kanta hauka da tunanin maganar tana zaman zamanta
Kallon Momy tayi tana cewa"

Wannan zancen mafarkin Mahmoud ne kawai da firgicin ciwo daya taso Masa mudai muyi Mai fusshemu
Kisake tabbatarwa Sa'adah Babu inda zata da wannan yarinyar hakama yau idan nakoma Zan sanarwa honourable dasu Alhaji Qarami da wannan Dan uwan Mahmoud din Dake can nijar shima zansa Alhaji Qaramin yakirasa Kan zuwansu commissioner neman auren Sa'adah din tunda sun takura akan basason asaka dogon lokaci Dan akwai tafiya agaban yaron zuwa Greece dakuma Sa'adah din zaije shine Dan batada hankali take cewa zata tafi da wanni.
Kisani idan Kika Baki rufe ido kin tsaya akan al'amarin ba Haka zata dage ta lalata rayuwarta akan wadda ba'a da tabbacin menene ya sameta,
Zan tafi zuwa gobe Inshallah zaa karba komai nasu.

Har umma Jamilan ta dauki keys din motarta da Jakarta ta fita

Please Login or Register in order to submit comment