Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/3, 12:57 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*

_page_ *1.*

_Na_
*Rahma Kabir*✍🏾

Mototaci ne guda uku suke tafe bisa hanya aguje, dukansu gilas d'in motocin masu duhu ne, mota ta farko dake gaba bodyguard ne a ciki.
Sai na tsakiya motar d'auke yake da tsadaddun 'yan mata su uku wanda ba zasu wuce shekaru Ashirin da biyu (22yrs) ba a duniya.
*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena.

K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin wak'ar tamkar sune suka rerata, sunayi suna rawa da jinsu da kad'a kai, kana ganin su kaga 'ya'yan gata, cike suke da farin ciki fal da nishad'i, domin ba suda wata damuwa ko matsala a rayuwansu.

Motan baya itama na bodyguard ne, suke marawa motan Queen baya.

Wani Matashin Saurayi wanda bai wuce shekara Talatin ba (30yrs), yake tafiya cikin sauri domin ya amso wa Ummansa nik'an masara da k'anwarsa Khadija ta kai ta aje, saboda zata wuce tallan kwai, hankalinsa yayi nisa sosai cikin tunani, baisan yahau kan titi ba. Meena ce taja mugun burki, ji kake k'iiiii kad'an ya rage ta buge shi, Aryan tsayawa yayi cak ya runtse ido yana fad'in *Innalillahi wa inna ilaihir rajuun* jira yake motan ta bigeshi domin ya riga ya sadak'ar motan zata kad'eshi,
Cikin b'acin rai Queen Basma, Leema, Meena duk suka fito a motan, haka bodyguard suka yi parking akan hanya suka fito rik'e da bindigogi, cikin k'ank'anin lokaci suka had'a gosilo, mutane suka fara taruwa, ganin bindiga ne yasa kowa ya kama kansa, Queen Basma ta k'arasa kusa da Aryan bodyguard suka take mata baya, tsadadden k'amshin turarenta ne ya dawo da hankalin Aryan jikinsa, domin ji yayi wani k'amshi na ratsashi, bud'e ido yayi a hankali yayi tozali da kyakkyawar fuskan Queen wanda saida gabansa ya fad'i, nan take tsoro ya ziyarce shi, kallon k'asa da sama Queen Basma ta bisa dashi cike da jin haushinsa, kyamansa taji saboda wani irin warin zufa dake tashi a jikinsa, tattaro miyon bakinta tayi ta tofa masa a jikinsa tare da toshe hancinta da hankacif, juyawa tayi ta kalli d'aya daga cikin bodyguard d'inta, cikin sauri ya k'araso, Aryan baiyi aune ba bodyguard d'in ya kifa masa kyakkyawan mari guda biyu, Leema ce ta k'araso cikin isa tace

"Hee, Marin ma kad'ai ya ishe shi" sai ta juya tana kallonsu Meena tana murmushi, ta kuma cewa
"babies mu wuce kar mu b'atawa kanmu lokaci akan wannan mahaukacin, kunsan duk muna da abinyi a gabanmu".
Dakyar Aryan yaja k'afansa zuwa gefen hanya, zuciyansa cike da k'unci, su kuma su Meena suka shiga mota suka wuce.

Tsananin damuwa ne Aryan ya tsinci kansa a ciki, sai ya fara zancen zuci yace,
"shi dai talaka kullun shi wulak'antacce ne a idon jama'a, Allah kai ka haliccemu kayimu ma banbantan jinsi, kaine mai girma, ka saka mini da kyakkyawan sakayya" wani guntun hawayen ya sauka a kuncin sa, ba abinda yake k'ara masa bak'in ciki sai irin yanda Queen Basma ta tofa masa miyau, murmushi yayi na k'arfin hali ya girgiza kai a fili ya furta "Rayuwa ce" sai ya wuce inda zashi.

Sai gabda Magrib ya kaiwa Umma nik'an masaran, ya sameta ta rafka tagumi, sallaman da yayi shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data fad'a, nisawa tayi ta amsa tace
"Aryan ya akayi ka dad'e ga ruwan sanwan ya tausa harya fara k'onewa" zama yayi a tabarma dake tsakar gidan yace
"Umma kiyi hakuri naje basu nik'a ba saida na jira suka nik'a shiyasa na dad'e" Umma tace
"Allah sarki, ba damuwa tunda mun samu nik'an yanzu zan gama insha Allah"
Nan ya zauna yana mata hira tana aikinta har aka kira sallan Magrib ya wuce masallaci.

Ta b'angaren su Queen Basma kuwa gidan hutawanta suka wuce, musamma tasa aka gina mata shi dan hutuwa. K'aton gida ne babban flat wanda ya k'unci kayan alatu a ciki, ginin zamani aka yi shi a tsakiyar babban fili, filin gidan za a iya pakin mota goma, sai daga can gefe ruffa ne mai d'auke da kujeru da table a tsakiya, an tanaji wannan wurin dan hutuwa, wurin zagaye yake da shukokin furenni masu fidda k'amshi mai dad'i, sai kuma daga bayan gidan katon swimming pool ne wanda aka sanya masa ruwa mai kyau da tsafta, in ka kalli ruwan har kashe ido yake dan haske, lokaci-lokaci ake jenye ruwan ana sauya wani. Daga gaban swimming pool d'in akwai wata yar k'aramar k'ofa wanda sai sadaka da cikin garden(lanbu), ya k'unci bishiyoyi na kayan marmari (fruits) da kuma kujeru na hutu dan shawakatawa, wurin ya had'u matuk'a.

Suna shiga cikin gidan suka shiga babban falo, basu zauna ba sai ko wacce ta nufi d'akinta kamar yanda suka saba, falo ne mai d'auke da d'akuna guda biyar ko wanne da ban d'aki a ciki (toilet), d'akin faro shine na Leema wanda aka k'awata shi da kayan Sarauta a matsayinta na gimbiyar 'yar Sarkin Kano.

D'aki na biyu shine na Queen Basma wanda aka  kawatashi da kayan more rayuwa, an kashe mak'udan kud'i sosai, a matsayinta na 'yar shugaban k'asa.

Sai d'aki na uku na Meena ce, wanda shima aka k'awata shi da dukiya, amma bai kai na Queen ba, a matsayinta na 'yar gomna.

D'aki na hud'u kuma an sanya masa kaya dai-dai misali, sun bar d'akin na masaukin bak'insu.

Sai kuma d'aki na biyar, tsadaddun kayan motsa jiki ne a ciki, wanda ko wani lokaci sukan mota jikinsu a ciki. Sai katon kitchen dake gefe yaji kayan amfani.
Wannan gidan musamnan Basma tasa mahaifinta president ya gina mata shi, bayan dawowarta daga k'asar England karatu, kasan tuwar sunyi karatu tare da Leema da Meena yasa ta sanya ko wacce aka shirya mata d'akinta dan soboda tsananin shak'uwar su kullun suna tare.

Queen ce ta fito daga ita sai best da pant ta d'aura towel a k'ugunta, hanyar k'ofar baya tabi ta bud'e, direct wurin swimming pool ta wuce, tana isa ta cire towel d'in ta fad'a cikin ruwan ta soma iyo, suma su Meena haka suka fito cikin shigar da Basma tayi, cikin ruwan suka shiga suma suka fara wanka, ko wacce na abinda ya shafeta.

Sun kai misalin Rabin awa a ciki kana Meena ta fita a ruwan, ta zauna a kujeran hutawa dake bakin swimming pool d'in, wani jaka naga ta d'auka ta zage zip d'insa, sigari ta ciro tare da leta, sai ta kunna mata wuta ta hure, kana ta kwanta a bayanta tana zuk'ar sigarin tare da fidda hayak'i sosai ta hanci da baki.

Leema ma fita tayi ta zauna a kujeran hutuwa nesa da Meena kad'an, wayarta ta d'auka ta fara chart da abokin harkanta, murmushi take zubawa ita kad'ai da alama tana jin dad'in hiran.

Queen Basma tana cikin ruwan ta tsaya da wankan cikin fad'a tace ma Meena
"Malama kinsan na hanaki wannan shirman muddun ina wuri ko, ya zaki kunna sigari ya rik'a cutar damu, kuma kinsan bana son warinta" cike da d'aure fuska Meena tace
"To maida damuwarki zan kashe shikenan?" sai ta kashe ta jefar, bud'e jakanta ta kuma yi ta d'auko kwalban syrup tace cikin gatsali,
"in kin hanani shan sigarin to ba zaki hanani shan wannan ba, don ita ba hayak'i". Basma take ta fito cikin ruwan ta d'auki towel d'inta tare da gallawa Meena harara tace
" kanki kike cutarwa" taja tsaki ta wuce cikin falo. Meena itama ta bita da harara bata ce komai ba, Leema ta kalleta ta kwashe da dariya tace
"wow ina son fad'anki da Basma, domin kullun sai kinyi abinda bata so a wurin nan, ita kuma kullun sai ta tanka miki". Tsaki Meena taja tace
"Ke kuma 'yar sa ido, to ya isheki, kije ki cigaba da iskancin ki, gwara ni bana bin maza" ran Leema ne ya sosu, ta d'aure fuska, nan take sarauta ya motsa mata, tashi tayi tabi bayan Basma. Meena ta bita da dariya tace "na dai rama".

Leema ta samu Basma sanye cikin riga iya cinya ya kamata, ta sanya wakar music sai tikar rawa takeyi tana mota duk sassan jikinta, tsaki Leema tayi tace
"zaki damu mutane da wannan wak'ok'in shirme" cikin fad'a Basma tace
"ina ruwanki, naga kowa yanayin abinda ya dameshi ne, ki shiga d'akinki kiyi chart da samarinki ban takuraki ba, nima ki barni inyi rawata", hararanta Leema tayi bata tanka mata ba, Meena ce ta shigo falon idunanunta sunyi jawur saboda ta shawu, joining d'in Basma tayi suka cigaba da rawa ba tare da ta canza shigar dake jikinta ba.

Saida aka kira sallan magrib kana Basma ta kashe wak'ar, duk suka wuce d'aki, wanka ta fara yi tare da d'auro alwala, jallabiya ta sanya wacce take sallah dashi ta sanya hijab ta tayar da sallah, bayan ta idar tayi duk azkar da ake karantawa da yamma, ta d'aura da Addu'a, Al'Qur'ani ta shiga karantawa cikin muryanta mai zak'i, tana zaune a haka har aka kira sallan Isha'i, sai ta rufe Al'Qur'ani ta gabatar da Sallan Isha'i.

Bayan ta idar ta mik'e ta sauya shiga cikin doguwar riga har k'asa yar kanti, ta kamata sosai tun daga samanta har k'ugu, daga gwiwa ya bud'e kad'an har k'asa an masa tsagu. Ta busar da gashinta da hand dryer, ta sanya mai ta kamashi da ribon a tsakiyan kai, ta bar jelan gashin yana reto a bayanta, ta d'auko hular mulki na Queen ta aza a saman gashinta, turare ta fesa masu dad'in k'amshi, ta sanya siririn sark'an goal a wuyanta tare da d'an kunne, a gogon hannu ta sanya da zobe, tayi kyau sosai, sai ta sanya takalmi dogo mai igiya, haka ta d'aureshi har k'auri, saida ta k'arewa kanta kallo a madubi sosai kana tayi wani murmushi wanda yake k'ara fidda kyanta, sai ta nufi falo cike da takun k'asaita.

Kallon-kallon su Meena da Leema suka yi saboda irin had'uwar da Basma tayi, sai suka ga tasu wankan ba komai bane saboda Queen ta lashe duka wankansu. D'aukarta photo suka farayi kala-kala, suna mata kirayi tare da kurantata, a kullun Basma in dai zasu fita zuwa club irin wannan shigan takeyi, amma fa ko wani shiga da kalarsa domin sai afi watanni bata maimaita wani shigan da tayi ba, ko wace rigan daban.

Bayan sun gama d'aukarta photo, nan suka had'u suka yita selfee, suma su Meena sunyi kyau ba laifi, shigan dogayen riguna sukayi tare da barin sumarsu  ya zuba a bayan su, kansu ba d'ankwali, dogayen cover shoe suka sanya sunyi kyau sosai amma fa basu kai Basma ba.

Fita sukayi suka shiga mota dukansu a seat d'in baya suka zauna suka sanya Basma a tsakiya, driver ya jasu, tare da bodyguard suna gaba, da kuma masu rufa musu baya sai club.

Aryan ya dawo daga sallan Isha'i, ya samu su Umma a tsakar gida kan tabarma suna cin abinci, shima zama yayi a shinfid'ar da yake mai girma ne, Khadija ta mik'e ta isa kitchen ta kawo masa abincinsa, bud'ewa yayi tare da cewa "nagode Dija", sun kammla cin abinci dukansu sai Aryan ya kai dubansa inda Dija ta zauna yace
"Khadija meyasa in kika fita tallan kwai bakya dawowa gida da wuri" marai raicewa tayi tace
"Yaya Aryan wallahi ba kasuwa ne shiyasa nace bari na k'ara lokaci ko zan saida duka, ka gafa tun shekaran jiya Umma ta dafa min amma har yau bai k'are ba" shuru yayi na 'yan dak'ik'a kana yace
"ai Dija mutum baya wuce rabonsa, ni dai dan Allah ki rik'a dawowa da wuri kuma duk inda kike ki tuna matsayinki da rik'e mutuncinki"

"tom Yaya Aryan insha Allah zan kiyaye" Umma na jinsu tace
"Aryan gwara ka rik'a mata fad'a, d'azu ma sai bayan magriba ta dawo" yace
"ai Umma wallahi ni da ina da hali da Dija ta daina tallan nan sam bana sonta" Umma tace
"to Aryan ya zamuyi, haka Allah ya rubuta mana, ya zancen rumfanka an gyara kuwa?" gyara zama yayi yace
"Umma ba kud'in gyara shiyasa na koma gefe ina aikina inna samu kud'in zan gyara, gashi yanzu cinikin sai Addu'a tunda Lawal ya dawo kusa dani ya kwashemin customers d'ina" Umma tace
"karka damu insha Allah in kud'in kwai ya taru zan baka ka gyara runfar, batun kuma Lawal ka rabu dashi kowa rabonsa zai ci, muyi ta Addu'a Allah ya kawo mana karshen wannan hali da muke ciki". Duk suna amsa da Ameen kana suka cigaba da hiran duniya.

*Muje zuwa...*🤔

*_Rahma Ce_*
[8/3, 12:58 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *2.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Su Basma suna isa club, suka wuce cikin hol d'in, mutane ne sosai a ciki maza da mata, daka gansu kaga 'ya'yan manya, tsautsayi ne zai kai d'an talaka wurin, kid'a da sauti ke tashi kowa na zaune, kamar yanda suka saba zuwa suna da nasu wurin zama na musamman, duk suka zauna, aka cike musu wurin da kayan motsa baki, wani kyakkyawan Guy ne yazo kusa dasu suka gaisa Amma banda Basma domin bata shiga harkan Maza, Leema ce ta mik'e saurayin mai suna Jalal ya rik'ota ta kugunta suka wuce tare da hiransu na masoya, fita sukayi a wurin suka wuce cikin hotel da club d'in ke ciki. D'akinsa ya bud'e suka shiga, kamar suna jirace da juna suka fara kaiwa juna sak'onni, nan da nan suka rikice suka lula duniyar shashanci, Allah ya shirya Ameen, nan na fito na basu guri.

Ita kuma Meena ta mik'e ta wuce group d'insu na mashaya, wurin mata ne da maza a had'e, suna ganinta suka fara ihu, wuri suka bata ta zauna ta fara aikawa da syrup.

Queen itama Abokan rawanta suka matso kusa da ita nan suka d'unguma zuwa saman dandamali, nan fa kowa hankalinsa ya tashi ganin Basma ta hau, hayaniya ya k'aru suka fara ihu domin sunyi missing ganin rawan Basma, aka d'aura mata best wak'arta na music d'in labarawa, Queen Basma ta soma rawa mai ban mamaki tamkar ba jikinta take k'aryawa ba, sai wuri ya kuma hautsibewa da ihu, dama abinda Basma keso kenan, mutane suka fara mata yayyafin kud'i masu taya ta rawa suka k'ara dagewa farin ciki ne ya rufe su domin sunsan yau zasu kwashi kud'i. Dan in sun gama Basma cewa take a basu kud'in su raba.

Sai da taci rawa mai isarta kana ta sauka ta samu guri ta zauna tana maida numfashi, sauran 'yan rawar suma suka sauka, aka kwashe kud'in su tas aka basu, farin ciki ya gama rufesu domin yau sun samu kud'i sosai, suna alfahari da Queen data zama star d'insu.

Sai misalin k'arfe ukun dare suka dawo gida, ko wacce ta nufi d'aki ta kwanta, nima saina tayasu rufe k'ofa nace saida safe.

*Washe gari*
Da misalin k'arfe takwas na safe Aryan yayiwa Umma sallama ya wuce kasuwa kamar kullun, yana isa rumfansa hawaye ya ciko fal idonta, girgiza kai yayi saiya bud'e k'aton buhu da yake kasa kayan miya, haka ya karkasa tumatur, tarugu, sai tattasai, samun wuri yayi ya zauna daga inda rufin shagonsa ya kifa ya rab'e, sai ya rafka tagumi ya fara tuno rayuwansu.

*ASALIN ARYAN? "*

Sunan mahaifinsu Aliyu, Asalinsu fulanin Gombe ne, mahaifinsa ya rasa Iyayensa tun yana k'arami, a wurin k'anin Baffansa ya tashi Malam Mu'azu, ya had'ashi da yaransa su biyu Aisha da Ibrahim ya rik'e. Matarsa Inna Amina suna kiranta da Inna Lami ta rik'e Aliyu Amana tamkar ita ta haifeshi, duk inda Aliyu yake Khalil na wurin, sun tsaku sosai makaranta tare suke zuwa, ga k'anwarsu Aisha suna ji da ita.

Wata rana Inna Lami ta aiki Khalil kasuwa shuru-shuru bai dawo ba har aka d'auki tsawon lokaci, abu kamar wasa Khalil ya b'ace anyi niman duniya amma ba amo ba labari, Malam Mu'azu da Inna Lami sun shiga tsananin damuwa, tun ana kwana d'aya da b'atan Khalil har ya d'auki tsawon wata ba'a ganshi ba balle aji labarinsa. Haka su Inna suka runguma Aliyu da Aisha suka barwa Allah lamarin sa da Addu'an Allah ya bayyana musu Khalil ko a mace ko a raye. Aliyu kuwa har rashin lafiya yayi saboda rashin d'an uwansa.

*Bayan shekaru*

Aliyu ya gama diploman sa a b'angaren kasuwanci, yana da shekaru 26. Aisha kuma tana da shekara sha takwas Malam Mu'az ya had'a Aliyu da Aisha auren zumunci, basu damu ba dama suna son junansu saboda akwai shakuwa mai k'arfi a tsakaninsu, Ana d'aura musu Aure sai suka tare a wani gefe daga cikin gidansu.

Bayan wata biyar da aurensu wani abokin Malam Mu'azu yazo Gombe mai suna Alhaji Sani, Malam yayi masa kyakkyawan tarba, d'aya tashi tafiya ya rok'i Malam akan ya bashi Aliyu ya tafi dashi Abuja tunda yayi karatu, ya d'auke shi aiki a companyn sa, da farko Malam bai yarda ba, amma daga baya saiya amince bisa sharad'in sai dai Aliyu ya tafi da matarsa, Alhaji Sani ya amince, cikin kwana biyu suka shirya sai garin Abuja.

Alhaji Sani mutum ne mai kirki, ya siyawa Aliyu k'aramin gida mai d'aki ciki uku da kicin da ban d'aki, sai kuma filin tsakar gida k'arami madaidaici a unguwar suleja, ya kuma siyan masa mashin da zai rik'a zuwa aiki. Farin cikin wurin Aisha da Aliyu baya misaltuwa, Aliyu ya fara aiki a company Alhaji Sani a matsayin Massinger. Sukan ziyarci Gombe duk bayan watanni biyu ko uku tare da alkhairai masu yawa.

*Bayan wani lokaci*
Aisha ta haifo d'anta Namiji suka sanya masa suna Aryan, Aryan ya tashi cikin kulawa da gata na iyaye, sun sanya shi makaranta mai kyau da tsada, Aryan yaro ne mai hazak'a b'angaren boko da islamiya, ga kuma natsuwa, gashi da kyau sosai, da ka ganshi gaka Asalin bafula tani, hakan yasa yayi farin jini sosai a makarantansu.

Aryan yana da shekara takwas Aisha wanda Aryan yake kiranta da Umma ta haifo 'Yarta kyakkyawa khajida, tun tana k'arama Aryan yake matukar son k'anwarsa duk abinda ya samu tofa na Khadija ce daya sanya mata suna Deeja.

Arya ya kammala  secondary school Khadija na primary 5, mahaifinsa ya nima masa makaranta a kadpoly Kaduna ya tafi ya fara karatun computer science, cikin ikon Allah da mai da hankali ya kammala, shekarunsa uku a makaranta ya dawo da cirtificate d'insa na diploma, ya koma Abuja lokacin Deeja ta shiga jss3 a secondary. 

Wata rana Aliyu ya wayi gari da matsanancin ciwon ciki Abu kamar wasa, zuwa yamma yace ga garinku, wannan family sun shiga tashin hankali sosai da rashin Mahaifinsu, karma ace maka Aryan da yayi mugun sabo da mahaifinsa, mutanan Gombe suka zo saida akayi arba'in sannan Inna ta tafi, sun so su Umma su tattara su koma Gombe amma Alhaji Sani yace su barsu anan, yana so Aryan ya cigaba da aikin Mahaifinsa, haka suka amince badan ransu yaso ba.

Aryan ya fara zuwa aiki a company Alhaji Sani, tunda ya fara zuwa ya fara samun matsaloli, wasu daga wurin aikin suka sanya masa ido saboda sunga yanda Alhaji sani ke nan-nan dashi. Daga karshe suka yi masa sharri bayan shekaransa guda da fara aiki Alhaji Sani ya koreshi.

Aryan yayi kuka sosai rayuwa tayi musu k'unci abinda za suci wuya yake musu cikin k'ank'anin lokaci duk suka rame suka lalace, Khadija ta daina zuwa makaranta domin ba kud'in school fees, Allah yasa ba haya suke ba domin da gidan su kawai suka tsira. Dole yasa Aryan ya fara bige-bige, Umma kuma ta soma wankau a gida da haka ne suke samun abincin da zasuci, Aryan yayi yawon niman aiki Amma bai samu ba, wani wurin inya je sai suce mai Digree suke nima, ba suda kud'in da zai koma karatu dole yasa ya soma dako a kasuwa. Allah ya taimakeshi ya samu baro yana amfani dashi wajen dakon. Da wannan kud'in baron ne ya samu ya kafa runfa a cikin kasuwa yana biyan kud'in hayan wurin, ya fara saida kayan miya, abu kamar wasa sai sana'ar ya amshe shi, da haka Deeja ta koma makaranta ya cigaba da biya mata school fees, Umma kuma ta daina wankau saboda sanyi ya fara mata illa, sai ta samu jari ta fara dafawa Deeja kwai tana saidawa, in ta dawo makarantan boko saita fita tallan kwai, da yake duk sunyi saukar Al'Qur'ani, boko kawai take zuwa.

A daddafe Khadija ta kammala secondary school, tunda ta gama Aryan yaso nima mata school of health ta cigaba amma ba kud'i, burin Khadija ta zama babban likitan mata amma ba hali. Samari sosai take da su amma Yaya Aryan ya hanata hira, saida Umma ta sanya baki ya fara barinta tana fitan ma wani malaminsu na ialamiyan da ta gama mai suna Musa. Soyayya sosai suke yi, sun fara zancen Aure Iyayen Musa suka hana shi aurenta saboda akwai yarinyar da suka zab'an masa, wannan dalilin ne ya kawo k'arshen soyayyan Dija da Musa. Tun daga nan Dija ta tsani soyayya burinta yanzu bai wuce ta samu ta cigaba da karatu. Aryan yazame mata uba duk abinda 'ya budurwa take buk'ata Aryan ya tsare mata shi, ta maida hankali sosai wajen tallan kwai.

Aryan runfansa ya rufta tun daga wannan ranar komai ya dagule masa cinikinsa yaja baya, wata biyu kenan da rushewan rumfansa. Ana cikin hakane mak'ocinsu Malam Lawal yaje ya kafa tashi rumfan kusa dana Aryan da hakane Malam Lawal ya kwashewa Aryan customers, ya zamana Aryan saiya fita kasuwa ya dawo gida baiyi cinikin kirki ba.

Aryan saurayi ne matashi mai cikar kamala, yanada tsayi amma dai-dai misali, yanada kauri, kuma fatarsa mai haske ne, yanada dogon hanci da dara-daran ido,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment