Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita

Karar shatuwa du tacika falan shi nabil ma bejiba be kula da minister ba har yanzu bare iya dagudu sukayo wajan su iya alokacin Nabil yasamu yafara zubawa shatuwa bulalar ajiki saura kadan ayi tafiyar ruwa da iya nabil Ido yarufe yazubawa iya wannan wayar T.V itama ajiki lokaci guda iya tacika wajan da Kara Dan tsabar rudewa rasa inda zata shiga tayi Kai kanta wajansu takuma yi wajan guduwa yakuma dagawa yazubawa iya ajiki shi du ya dauka shatuwa yake zanewa saboda idanshi yarufe da zafi yakuma ruda iya tai hanyar waje dagudu tsutsayi Tai Kan cikin miyar kubewar Nan se jitayi anyi sama da ita tadawo kasa rimm wani marayan ihu tasaki ko mutsin kirki takasa tana kwance male,male cikin miyar kubewa garama minister shi yayi karfin Hali azaune yake Yana jinyar kanshi

Ana Haka motar su baffah da Amina tashigo gidan ihun da sukaji nafitowa daga cikin gidan gamasu aiki du awaje sunyi jugum,jugum suna,jin abinda ke faruwa aminace Tai saurin shiga ciki taci Karo da iya da minister ahanya

ihu tasaki tace su mommy kuzo kuga ikwan Allah yau abin nayine gasu iya da daddy anshemesu kushigo ahankali yau abin yayi zafi miyar danyan kubewace azube duka afalan

Cikin dabara suka samu suka shigo wajan dakar suka rabasu suka rabu Hajiya Fatima tarike hannun nabil Taki sakinshi Amina itakuma tarike shatuwa jansu sukayi suka zaunar da su Akan kujera Suma suka zauna

Kuka Hajiya Fatima tasa tace nabil kakaryamin alkawari ko yanzu kunga danyan aikin da kukayi ku kalli iya da alhaji du kun dokesu da bamuzoba kashe kanku zakuyi da Allah be kawomuba

Se lokacin nabil yaga minister da iya Hakuri Nabil yai tabawa Hajiya Fatima kukan da take Yana dada tadamai hankali Yana dada Jin tsanar shatuwa aransa

Shatuwa tace lah iya yaushe kikazo har da daddy

Baffah yace yimin sharu ta Ina zakusan sun zo kun shiga filin dambe Ni yanzu babu wata nasiha da Zan Kuma muku Dan ko karatune yaci ace kun dauka Dan Haka nagama yanke hukuncin abinda yadace Dan Haka yau nayarda iya muzo tare da ita taga jikarta Ashe daraban abinda ze faru Kenan

Yakalli su minister da har yanzu sun kasa motsi yanzu ai kunga abinda nake gudar muku gakunan da alama du kanku kunji ciwo ajiki kadan ma Kuka gani Kar kuyiwa kanku fada Kar kuyi kokari kuhada Kan yarannan se ku tashi mutafi gida

Iya tace wlh usuman karfin siyane da jikanka Ina ganinshi kamar kajin turawa bawani karfi zeyiba Ashe ba daganan takeba Kai me zamanman wando me ka dinga shaudamin ajiki wace irin bulala kayi anfani da ita ta fashe da Kuka

Amina dariya takewa iya

MINISTER Dakar aka kamashi yatashi tsaye akasashi amota iya Kuma aminace ta kamata tasata amota suka shige gida gaba Daya amota se ruwan masifa take tawa minister shikuma yaki kulata takansa yake

Nabil Daman yau da ciwan mararshi yatashi daurewa kawai yake har yakula shatuwa sukayi fada dare nayi yazo kwanciya ciwan Mara yatashi sosai kamar ze mutu Dakar yasamu yakira Dr dake dubashi awaya yagaya masa abinda ke damunshi

Dr yace gaskiya yallabai kayi hakuri wlh Babu abinda Zan iya yimaka na temako ayanzu Dan tintini namaka bayani Babu abinda zaa iya iyimaka kawarke inba aureba Kuma anmaka maganinka matarka ko tayi tafiya ne in banisa tayiba kasa ta dawo gida yaimai sallama yakashe wayar

Nabil juyi yai tayi yahada gumi sosai tinani yafara yanda ze je yasamu shatuwa da wata bukatarsa bayan shi yatsani Mata kamarsa ai inyayi haka girmanshi yafadi Zama ta dada rainashi da azaba ta dameshi bema,san sanda yasauko daga kangado yai hanyar dakin shatuwa Yana dafa bango Dakar yasamu yakai kanshi kofar dakin shatuwa hannu yasa yabude kofar dakin yakwayi sa,a dakin nata abude lokacin tafito daga wanka daga ita se tawul daure ajikinta

Ihu tasa tace me kazo yi dakina da wannan daran me yakawoka ko kayi mantuwane bananne dakinkaba ficemin daga daki ko natarama mutane ko kazo mukara wani bawa hammata iskarne

Shi ko Jin abinda take fadama beyiba gadan gadan yayo kanta yadagata sama cancak ya wullata Kan gado yahau kanta dukanshi kawai takeyi tana ihu tana cizanshi har da yakushi ko ajikinshi bema san tanayiba ta maganin matsalarsa yake gani yake in beyiba mutuwa zeyi Dan shi yasan me yakeji hanyarsa yafara nema Babu Bata lokaci yasamu yashige dakarfi

Wata mahaukaciyar Kara tasaki

Naguda daganan ango da Amarya asha soyaiyar Dole 😂


YAN DAN MINISTER fans

Sekunzo jinyar shatuwa






















New writer's


Hakan Take
*Husba'ahfama* ❤👸
*'YAR KWALLIYA* 🥳💃
👝👝👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝
👠👠👠
👝👝
👠

💄💅 *DAN MINISTER* 💅💄
🦚🦚




Written by *Husba'ahfama*


*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*

Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*







13-14









Nabil yawahalar da shatuwa sosai Dan gaba,daya baya hankalinsa saboda wata sabuwar duniya da yaji yashiga Wanda betaba shigaba se yau ita tana kukan azaba da Kiran iya da kawayanta Babu Wanda Bata kiraba har da su amina shikuma kukan dadin da be taba jiba yake surutaikuwa Babu Wanda beyiba har da yiwa baffah godiya shatuwa da wuya tayi wuya numfashinta daukewa yayi batasan sanda nabil ya bartaba bayan komai yanutsa rungume shatuwa yayi Yana ta Mai da numfashi jiyayi gabadaya ciwan da yakeji na Mara Babu kamar an dauke Masa wani Abu me dauyi ajikinshi wani baccine me nauyi yadaukeshi be farkaba se da gari yawaye sosai Ido yabude ahankali yaji mutun ajikinshi da sauri yaduba yaga shatuwa ce kallan inda yake yahau yi abinda yafaru jiyane tsakaninsa da shatuwa yadawo Masa kurawa shatuwa Ido yayi yaga ko motsi batayi ranarne yakare Mata kallo yaga yanda ainahin kalar fuskarta take yadade Yana kallanta irin rashin mutuncin da take Masa yatuno yakuma tuno abinda yashiga tsakaninsu adaran jiya wani tsaki yasaki yatashi afusace yasa kayansa yai hanyar waje har ze fita yatuno ko motsi bega tanayiba dawowa yayi yatabata yaga kamar Bata da Rai ruwa me sanyi yadauko ya kwara Mata takuwa saki wani marayar Kara tsaki yakuma Jah yai ficewarsa ko kallan halin da take ciki beyiba ko damuwa bare ya temaketa Yana dada Jin haushin kansa da yazubar da girmanshi kamarshi yaje ya aikata haka da shatuwa Kuma gashi shi yatsani Mata garin yayama shi yashiga dakin ta tinani yake tayi har yashiga dakinshi Yana shiga wanka yaje yayi bayan yagama shiryawa kasa Zama agida yayi yai ficewarshi gurin da yake shakatawa

Baffah se da yasa aka nemo me gyaran targade yagyarawa minister targadensa da gocewar kashin da yayi yafada yaji wajan gyara Dan gurin yayi tsami sosai

Iya tinda suka dawo takasa motsa jikinta barinma hannunta gabadaya jikinta ciwo yake Mata ga hannu yaki motsuwa itama se da akasa me gyara yaduba Mata hannunta yaga tasamu tsagewar Kashi ahannunta na dama aikuwa kafin agyara hannun ansha daru da ita Miss Miss kuwa takira sunansa ba adadi tana Masa ruwan masifa shi da nabil

Amina ce tazo da safe baffah ne yasa tazo da mgnar da zasuyi tasamu baffah abangaran da yake sauka yasa aka Kira Masa hajiya Fatima bayan sun gaigaisa

baffah yafara mgn yace to Kan mgnar mu na kiraku wannan shawarar da nayanke itace mafita insha allahu Kuma za a dace Amina tinda tafiyar Taki ke da mijin naki tazo zuwa kwas,din da zejeyi america kutafi tare da shatuwa tinda shi mijin naki yace tare zaku tafi Kuma sani na da gida acan america gidan nashi zaku sauka har mijin naki yagama kwas,din da zeyi na wata shida Dan Allah ki dada kokarin da kikeyi Akan Wanda kikeyi Akan shatuwa muma anan zamuyi iya namu kokarin Kan nabil har musamu abinda mukeso awajanshi Dan shiryuwarshi itace shiryuwar sani itama shatuwa hakane Dan Haka yanzu tinda kince yau da yamma zaku tashi zuwa America kije kisa shatuwa ta shirya ki hada,mata du abinda yadace ki tafi da ita gidanki lokaci nayi se dai ku tafi ko tanan karku biyo da ita Kuma karki Bari nabil yasan kece Kika tafi da shatuwa ko iya bazata San da tafiyar jikartaba Dan hakafa na yarda muka taho da iya dan Tai sallama da shatuwa Kinga karshe ga abinda yafaru itama bazata,san shatuwa tayi tafiyaba in bahakaba komai baci zeyi yanzu Fatima takira megadin gidan nabil ta tambayeshi ko nabil nanan yace bayanan yadade da fita Danhaka sekiyi sauri kije ki dauketa Kuma ko lokacin da wowarku yayi inhar dukansu Basu shiryu yanda mukesoba baza a dawo da shatuwa ba har se munga sun koma yanda mukeso

Amina tace to baffah Amma aganinka iya bazata damekaba Akan kafito Mata da jikarta kasan halintafa da rigima

Hajiya Fatima tace Nima tinanina kenan Kuma wannan matakin da kayanke Kan nabil da shatuwa baffah shine dedai Allah yabamu sa,a ni wlh daga iya har alhaji rigimar tasu dariya take bani garama nabil da shatuwa suna da dalilan abinda yafara hadasu fada tin farko Amma iya da alhaji Basu da wani dalili alhaji nabil yake tayawa fada iya Kuma shatuwa Kuma wlh Ina guje musu ranar da nabil da shatuwa zasu shirya zasuji kunya sosai mudai muna gefe kallone namu tasa dariya

Baffah yace rabu dasu gani sukayi zasu iya Ni abin takaicima sani ne mecewa indai Akan nabil ne ze ajje mukamin minister agefe in dokuwane shi da iya su doku Allah yaganar da su gaskiya; karku damu da iya danta umaru wato mahaifin shatuwa yasan komai Akan tafiyar Kuma yabamu goyan baya akai ita,kuma iya nasan yanda Zan shawo kanta har Allah yasa shatuwa ta dawo se Naga tafitarku Amina sannan zamu koma mazaigai Ni da iya Allah yakaiku lfy ku dawo lfy maza tashi kitafi Allah yai muku albarka

Amina gidan su nabil tasa direba ya kaita tana shiga taita sallama taji shuru ta dauka ko bacci sukeyi Kai tsaye dakin shatuwa tashiga ganin halin da shatuwa take ciki ko motsin kirki Bata iyawa tana kwance abin tausayi yadagawa Amina hankali tambayarta tafara me yasameta ko nabil ne ya daketa shatuwa Babu bakin mgn se kuka shima da kyar takeyi yaye bargwan jikin shatuwa da tarufu da shi tayi ganin yanda jini yabata inda take kwance yayi mugun tada Mata hankali Dakar ta rarrashi shatuwa tafada Mata abinda yafaru tsakaninta da nabil Amina taji Dadi sosai da haka tafaru tsakaninsu kafin shatuwa tabar kasar ita taiwa shatuwa wanka ta gaggasa Mata jikinta Taji tausayin shatuwa sosai ganin barnar da nabil yai Mata ita ta gyara ko Ina na dakin har zanin gadan se da ta wankeshi a injin wanki tayi du abinda yadace sannan takama shatuwa suka fito tasata amota da kayanta suka fice asibiti tatara Kai shatuwa aka dubata sannan suka shige gidan Amina yamma nayi wajan karfe shida jirginsu yatashi zuwa America baffah da Hajiya Fatima ne suka rakasu har sukaga tafiyarsu sannan suka dawo gida

Nabil tinda yaje wajan da yake hutawa tinanin shatuwa da abinda yashiga tsakaninsu yake ta dawo mishi ko Ido yarufe abinda yafaru yake gani ga fuskar shatuwa da take ta Masa yawo a idanshi kide kiden da ke tashi awajan da wakar du yau ji yayi basa Masa Dadi tinani yafara to da yafito yabarta awannan halin waye ze temaketa in tamutufa Kuma ko bakomai ai ta dalilinta yasamu lfy jiya Kuma yaji dadin da be taba jiba Daman mata na da wannan Ni,imar Haka me Dadi har da wannan ballagazar Mara mutuncin to yanzu waye ya temaketa ko tamutu fitowata daga gida jiyayi gabansa yafadi besan lokacin da yasaki wata karaba yafara mgn kamar zararre A,A,A Bata mutuba to Wai meyasa nake tinaninta Wai meyake faruwa da nine abokansa da sauran mutanen da ke wajan kallansa suke tayi suna mamakin me yasameshi yau haka Babu me bakin tambayarsa saboda kowa yasan halinshi wajan mota yanufa da sauri ze shiga dagudu yaransa suka rufamasa baya suka bude Masa motar Yana shiga sukaja suka fice dagudu zuwa gidansa

Motar ko Gama tsayawa batayiba yabude yafito da gudu,gudu sauri,sauri yashiga gidan jiyayi gabanshi yayanke yawani mugun faduwa dakin shatuwa yashiga dagudu yaga bataciki yaje da sauri yabude bandaki yaga bakowa aciki dakin yahau kalla yaga ko Ina tsaf angyara Babu alamun mutun yakwana acikinsa kangadan yakalla yaga agyare anma canja zanin gadan gabadaya fita yayi yahau duba ko Ina nagidan nanma be gantaba dagudu yatafi wajan masu gadi Yana tambayarsu da tsawa Ina matarsa

Jiki na Bari sukahu bashi amsa Suma Basu gantaba ko fitarta Basu ganiba

Yace Babu wata ko wani Wanda yashigo gidannan bayan fitata yatafi da ita

Sukace eh yallabai Babu kowa Kuma mu bamuje ko inaba muna wajannan da wasu sun shigo da mungani

Yace wlh inhar tabata kome yasameta kunsan Allah bazan barkuba Ni dakune to meye anfaninku agidan tinda baza kuyi abinda aka daukekuba korarku zanyi yau,yau dinnan bazaku dada kwanarmin agidaba dukanku se na kulleku kuje kuyi tinani ku fitomin da ita kannaje nadawo

Gida yatafi wajan su hajiya Fatima ko sallama beyiba yabanko dagudu Yana dube dube kamar me neman wani abin daga hajiya Fatima har baffah babu wanda yai Mai mgn yisukayi kamar Basu ganshiba dakunan gidan yahau dubawa be gantaba falo yadawo wajan su baffah yazauna yakwanta Kan goguwar kujera yarike kansa yarufe Ido kamar me bacci shi yasan meyake damunsa ga wani ciwankai da zazzabi me zafi na damunsa

Baffah ne yace nabil yau ko mgn Babu bare gaisuwa Ina matar taka

Nabil besan sanda yatashi zauneba Yana kallan baffah

Baffah yace ko dai baka da lfyne

Nabil yace lfyta kalau Daman batazo nanba

Hajiya Fatima tace wacece kake tambaya

Yace aa ba mgn nayiba

Komawa yayi yakwanta

Yace mommy a Ina tsohuwar Nan ta kwana

Kafin tabashi amsa sega iya tashigo

Iya naganin nabil tace me zamanman wando Ina shatuwa ko kakuma karyata ko baka,jina Kai min shuru

Ido nabil yabude suka hada Ido da iya batasan lokacin da taja bayaba

Tace nashiga uku Ni Aisha kuga idan mutun kamar gauta ko dai kakuma balballata Ina Nan bansaniba

Tashi yayi Yana hada hanya yai dakin da iya ta kwana nanma bega shatuwa ba dakin minister yatafi ya kwanta daga yarufe Ido se yaga shatuwa gashi San ganinta yake yarasa me yasa ga zazzabi yatakura Masa se rawar sanyi yake

Hajiya Fatima ce tashigo taga halin da yake ciki tace nabil baka da lfy bayannan Kuma da abinda ke damunka ka fadamin

Yace bakomai mommy kawai dai bani da lfyne

Tace to Alllah yabaka lfy Bari na kawoma magani tafice

Mgn nabil yahauyi shikadai kamar Mara hankali to Wai Ina taje ko an sacetane to ai babu Wanda yashigo gidana Kuma anty Amina tayi tafiya baza Kuma su tafi tareba tinda kwas mijinta zeje yi Kuma ai baffah da matsifanfiyar tsohuwar Nan baza su Bari atafi da itaba to yaushema Yar Kauye irin wannan zataje America ai ko jirgi Bata iya hawaba to waima meye nawa in tabata ba na hutaba da jarabar ta da ta wannan tsohuwar to Wai meyasa nake ta ganinta in narufe Ido ko Dan ta dalilinta naji saukin ciwan marata jiya Kai nabil manta kawai macacefa Kuma nafa tsaneta Wai meyasa naje nahada jikina da ita kazama Yar Kauye irinta tsaki yajah me karfi

Hajiya Fatima ce tadawo
Bashi magani tace Kai dawa naji kana ta mgn ko dai kun dada halinne Wai Ina shatuwa ana ta tambayarka kayiwa mutane shuru

Yace tana gida na barota

Mgni tabashi yasha bacine ya kwasheshi acikin baccin Yana ta mafarkin shatuwa da Kuma garar da yasha awajanta jiya kusan rabin baccin du mafarkinta yake

Iya da baffah sun koma mazagai Dakar aka lanlabata takoma da cewa tayi se taje tayiwa shatuwa sallama Kuma akwai nasihar da ta manta batai mataba

Shatuwa bakin America Tasha jinyar barnar da nabil yai Mata se da tawarke sosai Amina tasata amakaranta saboda shatuwa na da kokari Kuma Babu lefi tana ganewa turancine ake fama da ita in anyimata Bata gane wani abin in angaya,Mata da turanci se ta dawo gida take tambayar Amina me ake nufi da kalma kaza da turanci in Amina tabata amsa to tarike kenan karatu kuwa tana ganewa tamurje tadada fari sosai in ba ka santaba bazaka gane taba Amina tayi kokari sosai wajan dada wayar da ita yanzu shatuwa tazama Yar birni Kuma Yargayu acikin wata ukun da sukayi tsokanar da akasan shatuwa da ita yanzu du babu tazama saliha kamar ba itaba yanzu Abu dayane yake damun shatuwa da Amina ta kula dashi tana yawan tinani kome take lokaci daya zatai shuru ko mgn ake Mata bazata baka amsaba Amina tayi Mata tambayar duniyarnan meke damunta se tace Babu komai

Yau Amina nazaune adaki tana shayar da yarta shatuwa tashigo ta sameta tazauna kusa da ita Amina tace yadai kanwata Naga kamar da mgn abakinki

Shatuwa tace Daman tambayarki nazo nayi Dan Allah in mutun koyaushe na yawan se Tai shuru ta sunkuyar da kai

Amina tace cigaba Mana kanwata Ina jinki meye abin Jin kunya nifa Yar uwarkice

Shatuwa tace to anty in mutun nayawan tinanin mutun mekenan kamar Wanda kasani Kuma abokin fadanka Kai tayawan tinaninsa ko in kana bacci Kai ta mafarkinsa

Amina tace kafara damuwa dashi Kenan Kuma yanzu kana sanshi kekuwa kanwata meyasa kikemin wannan tambayar ko tinanin gida da su iya kikeyi

Ido tarufe tana dariya tace to anty bayan su mommy Kuna waya da su iya dah takuma,sa dariya

Amina dariya take ta dannewa Dan tagama ganota yitayi Bata gane me take nufiba tace karasa tambayarki du Zan Baki amsa

Kuna waya da Yaya nabil

Amina tace eh to muna waya da kowa Amma nabil gaskiya ba sosaiba iyama bama waya da ita

Shatuwa tace to in kunyi waya dashi Yana tambayarki yanake ko Ina nake ko bayayi

Tace aa gaskiya bayayi Kuma ai besan na taho da keba bemasan kina nanba

Hawayene yafara zuba daga idanta
.Amina tace menai Miki kanwata ko na Bata Miki Rai ban saniba

Tace aa abinne yabani haushi Ni fa anty kullin shi nake ta tinani ko bacci nake tinaninshi nakeyi yanzufa San ganinshi nake Amma shi be tabama tambayarki ko Ina nanba Daman anty besan kin taho daniba Kuma in yashiga wani halifa Kuma fa mijinane ai bebarniba muka taho Kuma kece memin waazi Akan hakkin miji kumafa kinsan iya wlh damunshi zatayi akaina in tazo Bata ganniba

Hamdalah Amina tafara tana murna tace to akwai dalilin da yasa muka taho dake se nangaba Zaki gane me ake nufi harshi nabil din Kuma mgnar fadan da kukefa yanzu nasan muna komawa zakuci gaba da abinda kuke Kuna rabawa kanku abin kunya agaban mutane ai basan junanku kukeba Kinga kuwa ai yanzu hankalinki kema akwance yake anraboki da abokin fadanka ko

Tace aa wlh ai Ni nadena fada Kuma ko me yaimin bazan Kuma kulashiba ai kinmin fada ga Kuma waazi inaji Akan Mata tabi mijinta sau da kafa in tayi zata shiga aljanna ai shima nasan yanzu yadena gakuma iya inasan naganta anty mu koma gida Dan Allah

Amina tace to kanwata karki damu munkusa komawa insha allahu komai yazo karshe ammafa naji Dadi ashedai anasan Dankanin nawa kanwata na San mijinta tanasan ganinshi

Dariya shatuwa tasa tazuba dagudu tafice daga dakin tanajin kunya

Amina Kiran hajiya Fatima tayi awaya tabata labarin yanda sukayi da shatuwa itama hajiya Fatima tabata labirin halin da nabil yake ciki dukansu sunyi farin ciki sosai

Nabil tin Yana boye batan shatuwa yanzu yakasa boyewa gashi yazu tinani yamasa yawa har Rama yafara yarage walwalar da yakeyi da ko fita yanzu bayayi sosai se dai yaje dakin shatuwa yakwanta in Kuma yagaji da kwanciyar yatafi wajan hajiya Fatima yau wajan hajiya Fatima yaje yasamu kuwa babansa minister nanan suna hira

Da sallama yashiga zuwa yayi yafada jikin minister yafashe da kuka me karfi yace daddy Kai da mommy ku temakeni tinaninta ze kasheni wlh Santa nake na Dena du abinda bakwaso in dai za a dawomin da ita mundena fada naje na roki baffah yace bemasan da batan shatuwa ba Kuma Allah yanzu inaga dasa hannunshi yasan inda take Ni har mommy ban yarda da itaba

Minister rudewa yayi yace alhamdulillah Allah na godemaka da kabawa nabil matar da yakeso ba wannan mahau

Kafin yakarasa nabil yarufe Masa Baki

Yace karka karasa daddy wlh bazan iya jure Jin ana zagintaba wlh Ni matata ba mahaukaciya bace da hankalinta nifa daddy ba wata matar auren da nasamo matata nake nufi Wanda baffah ya auramin Dan Allah gobe muje mazagai tare mubawa baffah hakuri ya dawomin da matata har in Kuma yaki mommy ma Taki to wlh se na Nemo gidan iya masifa na fada Mata anbatar Mata da jikarta Kuma bawasu bane su baffah ne ai nasan in taji masifarta,ma kadai ta Isa su dawo da ita Dan itama tanasan jikarta sosai

Minister Baki yasaki Yana kallan nabil bemasan sanda ya sauko daga Kan kujera yazauna akasaba Baki narawa yace nabil kakuwa San mekake fada kuwa ko dai da gaske kaima kabi layin Yan shaye,shaye abokanka inkuma ba hakaba to tsohuwar Nan da jikarta sun maka wani mugun abin sun kaika an haukatama zuciya akansu shikenan baffah zamu rasa nabil ai Dole naje har gida na ci mutuncin tsohuwa iya

Nabil yace wlh daddy karma kafara inhar kana sona to karka yiwa iya komai Dan ran shatuwa ze baci intaji Kuma zata dada guduna Nima Kuma yanzu inasan iya kome zatai min bazan kulataba Nima kakatace nidai abinda nakeso da Kai ka tayani Nemo shatuwa mukuma je mubawa iya hakuri mubawa baffah hakuri mukuma bazama neman matata adu inda take aduniyarnan

MINISTER wani gumine yake ta keto Masa duda sanyin esin da ke wajan zare Ido kawai minister yake tayi Yana kallan nabil

Me hajiya Fatima zatayi inba dariyaba har da rike ciki tasaki Buda tace Allah ngdma ranar muke jira yau gashi tazo Allah karabamu da abin kunya ko wana irine Naga yanda zaayi wajan zuwa gurin iya ba da hakuri da wajan baffah da alhaji yanzu Dan Allah bakaji kunyaba tin ba a je ko inaba ai ga abinda muke ta fadamaka Ni da baffah gashi kashiga fadansu yanzu zaka dawo kaji kunya gashi dai yaro yadawo yace yanasan matarsa saura iya ita Kuma zamuga yazatayi garama ita tsohuwace akwai shiruftun tsufa Kai kuwafa ai Babu wani tsufa da kayi Allah kadawo da shatuwa lfy muyi kallo muna daga gefe yanzufa tinda kana san danka seka Rakashi neman shatuwa da bawa iya da baffah hakuri du kuma se kamanta abin kunyar da kayi nasan yanda San nabil yarufema Ido ko cewa yayi kabawa shatuwa hakuri Bata zakayi ko to karma ku sakoni Dan bansan komaiba Akan batan shatuwa shine mijinta shi zefi kowa sanin inda matarsa take to mawai yaushe ta Bata ai kullin in yazo se na tambayeshi ya matarsa se yace lfy take har sako nake bashi yakai Mata du wayake kaiwa

Nabil zuwa gaban hajiya Fatima yayi yace mommy Haka mukayi da ke kinface kema kina Sona Dan Allah in kinsan inda matata take ki fadamin ko wani abinda na keyine bataso du ki fadamin wlh Zan Dena

shi dai minister har yanzo kallan nabil yake ko hajiya Fatima yakasa bawa amsa

Hajiya Fatima tace gaskiya abubuwa da dama bataso kakeyinsu Kuma ta fadamin Allah sarki har kuka take abin tausayi ko akansu ta guduma Allah masani Kuma ai badan Allah zaka denaba kaga Kenan in kaganta ta dawo zaka koma ruwa kaci gaba da halinka da bataso Kuma dada guduwa zatayi

Jiki na Bari yace wlh mommy nayiwa Allah alkawari Zan Dena danshi badan itaba tinda du kema kin fadamin Babu Kyau abinda nakeyi kecefa abokiyar shawararta kibani shawarar yazanyi na gyara ammafa wlh ko Ina iya take Sena Nemo gidanta na fada Mata halin da ake ciki dan itama ta Hura muku wuta kufito Mana da ita aini yau masifar iya ikwan Allah zata yimin Rana Kuma yanzu ita zanna gani inajin Dadi azaman shatuwa kafin aganta

MINISTER hannu binbiyu yasa yai tagumi Yana Jin ikwan Allah

Hajiya Fatima in takalli minister taga yanda yake ta raba Ido ga gumi na ta keto Masa dariyace take dada kamata Babu halin yi saboda nabil Kar yaga tana ta dariya yadau du maganganunta azaman Wasa ko yaudara zega Kuma tasan inda shatuwa take

Please Login or Register in order to submit comment