Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dan Haka ta hade Rai ta nuna batasan komaiba

Tace Ni yanzu nabil azamana na mahaifinyar,ka Kuma me baka shawara Zan baka wasu shawarwari da zasu anfaneka Amma seni da Kai

Nabil yace mommy Ni yanzu nakeso muyu mgnar muje ko dakin,kine

Tace to tashi muje

Nabil yace daddy muna zuwa kaima da mgnar da zamuyi da Kai Kuma gobe kashirya mazagai zamu tare wajan iya da baffah

Hajiya Fatima da nabil daki suka shiga bayan sun zauna

Tace nabil shawarar da zan baka itace ka koma isilamiya cikin biyu ayi Daya ko anemo maka malami Yana koyamaka karatu agida ko kashiga ta malam liman da ke unguwarnan daga magariba ne da Isha akwai Kuma na bayan sallar Isha zuwa karfe goma nadare kazabi Daya kana zuwa karkayi girman Kai ko wata kunya Babu kunya wajan neman ilimi daga Ni har shatuwa bamasan halayanka da kakeyi nafarko maganar Yan aikin gidannan kacire musu dokar in sun ganka suna durkusawa har se kabar wajan kacire wannan dokar in sun ganka Kuna gaisawa cikin mutunci da girmamawa Amma Banda wannan durkusan har kasa Babu Kai Babu Kuma korar wani Dan aiki dake gidannan ko karkashinka Kuma wayanda ka Kora ada ko kabatawa Rai a Yan aiki du kabisu kabasu hakuri Wanda kaga yadace kayiwa alheri kayi Masa se maganar gudu da mota atiti babushi yanzu kudena Kai da yaranka kudena daukan hakkin talakawa Kai da su yanzu se girmamawa da Basu sadaka Kuma wannan kudin da kake rabawa abokanka suna aikata sabon Allah da kudin kadena ka koma rabawa talakawa maganar Jin kide kide du kadena ko karage ka koma Jin karatun Qur'an zuciyarka zatai sanyi zaka rage zafin zuciyar da kake dashi du in kashiga isilamiya zakaji waazi akai Kai abubuwa da dama insha Allahu du Zan na fadama ahankali kadaure kadena kazama me adalli da hakuri ga kowa kaji nabil kakoma mutunta Mata da darajasu kadena cewa ka tsanesu

Yace to mommy du naji Kuma zanyi isilamiyar ta malam liman zan shiga nafi karuwa da wasu abubuwan sosai

Tace yauwa nabil Allah yaimaka albarka

Nabil yaji mgnar hajiya Fatima yafara zuwa isilamiya hajiya Fatima da kanta taje har gidan malam liman Tai Mai bayani Akan nabil zefara zuwa isilamiyarsa ta maza magidanta da matasa Tai Mai bayani halin da nabil yake ciki Kuma Yana yawan temakawa da yawan yin waazi Akan zamantakewar Dan Adam ko malam liman yaji Dadi da Jin bayanin hajiya Fatima Akan nabil
ranar da taje ranar nabil yafara zuwa da magariba

hajiya Fatima taji Dadi sosai yanda taga nabil yafara canja halayansa ko Jin Waka yarage sawa yanzu ko abokansa basosai yake shiga harkarsuba har gida suke zuwa nemansa Amma Haka zasu hakura sukoma jiki bakwari gashi yanzu yarage yiwa abokan nasa bushaSha kamar da ko yajema baya Basu komai baya Kuma dadewa Yan aikin gidansu kuwa sunsamu yancin kansu Babu takura tsakaninsu da nabil Babu durkusawa har kasa ga kyauta da yake ta yawan yimusu kowa yaga canji Akan nabil mutanan garima sun sheda canjawar nabi almajirai in yafita Haka yake raba musu sadaka Dan Allah yadawo Masa da shatuwa lfy wayanda da ko almajirai bayasan ganinsu karatu kuwa alhamdulillah Yana fahimta sosai daga anbiya Masa zerike ga yawan waazi da malam liman yake tayi Kuma Yana shiga kunnan nabil sosai Kuma Yana anfani dashi motocinsu yanzu in sun taho ako Ina memakwan kade,Kaden da akeji da amotocin yanzu kuwa karatun Qur'an akeji natashi in adaki yake ko afalo abin da yake sawa Kenan karatun Qur'an ko gudu da motoci in Yana ciki yanzu andena yanzu kowa yaban nabil yake da samasa albarka ko sarkokin da yake sawa da irin shigar da yakeyi da su fentin kansa yanzu du yadena zarya kuwa amazagai Babu adadi wajan baffah Akan ya temaka ya dawo Masa da shatuwa ga ciwan mararshi yatashi sosai saboda yawan tinanin shatuwa da tinanin garar da yakwasa awajanta hajiya Fatima yanzu tafara tausayin nabil garama yayi sosai yakoma shuru shuru Babu wannan zafin ran da akasansa dashi

da nabil yaga baffah baze bashi amsaba Akan shatuwa Kuma baze dawo da itaba yayanke shawara ko baffah be saniba bare minister yaje ya Nemo gidan iya bakaramin rashin mutunci iya Tai masaba Amma be amsa mataba wajema yanema yazauna Babu korar da batai Masaba Akan yafice Mata daga gida nabil ko akansa yaki kulata Kuma yaki tafiya Dole ta sauko ta saurareshi aikuwa nabil Nagama fada Mata halin da akeciki Tai tsalle ta dire tace batasan zanceba tahau kuka wiwi Akan se annemo Mata shatuwa nabil da yaga haka yai ta tunzurata tana dada Hawa shima har da tayata kuka su baffah sun batar musu da shatuwa

Iya tace Ashe dandaudu me zamanman wando zaka canja kazama mekirki haka har kafara San shatuwa kaima Ashe dai kaima kyakkyawane haka kaboye kyan da Allah yai maka ka koma kamar matamaza nifa da kashigo ban ganekaba se da umaru yai min bayani yace Kaine tukunna na ganeka aiyanzu Kuma Ni da Kai Babu fada munshirya tinda kanasan shatuwata saura Miss Miss Shi,ai wannan uban naka bashi da mutunci baze Dena abinda yakeba Aishi basan shatuwa yakeba Kuma nasan be damuba da batan shatuwa kabarni dshi du zamu hadu Daman da tamu dashi yanzu dai katashi mutafi wajan usuman naji inda yakai Mana ita Kai Dan Miss Miss ka fadamin gaskiya ko dai ubanka Miss Miss yasai da shatuwa bamu saniba takuma fashewa da kuka Ni wlh da magunan yace na kawo Masa wlh Zan kawo Masa ba se yasai da shatuwa ba kumafa agabanka har alkawari naimai in yafara mutunci Zan tara Masa maguna na kawo Masa har gida takuma fashewa da wani kukan

Nabil du dadamuwar da yake ciki se da yafara dariyar maganar iya Yana mamakin karfin Hali irin nata agabansa tana zagemai uba

yanzu damuwa taiwa minister yawa saboda ganin halin da nabil keciki na damuwa gashi minister najin kunyar zuwa wajan baffah yabashi hakuri akan batan shatuwa haka Dole yacire kunya yaje har gida yasamu baffah yabashi hakuri Kuma ya rokeshi Akan Dan Allah in yasan inda shatuwa take ya dawowa da nabil ita

baffah dariya shima yafara Yana kallan minister

Baffah yace Kai sani ko dai mafarki kakeyi ko da yake ai ba kunyace da kaiba in dai Akan nabil ne komai ma zaka iya kaga abinda nake gayama Kenan yanzu gashi yadawo San matarsa Yana ta nemanta yashiga damuwa gashi kaima kadamu kazo kana tayashi neman matarsa Amma da idanka yarufe kadinga rashin mutunci da abin kunya yanzu kaima cewa zakayi ka goyi bayan auran shatuwa da nabil ko Dan baka da kunya kariga du kagama zubar da girmanka na uba a idan shatuwa yanzu ai kadada hankali kakuma dau darasi Akan abinda yafaru Nan gaba San nabil yakuma rufema Ido wlh Fatimace me San nabil bakaiba yanzufa ko shuryuwar nabil baka saniba Ni nasani baka da lokacin tarbiyarsa se ta munamai gata yanzu da ba Fatima mahaifiyarsa da kacuci nabil har karshan rayuwarsa tashi kabani waje se nayi shawara Akan mgnarka

Haka minister yadawo Abuja jiki Babu kwari

Iya ce da nabil sukazo har gida wajan baffah Kan mgnar shatuwa iya nazuwa tafashewa baffah da kuka tana ruwan masifa yafito Mata da shatuwa Dan Miss ne yazo yagaya Mata shatuwa tabata Kuma yasan komai har da hajiya Fatima nabil na gefe Yana Jin Dadi tinda iya tasa Baki fole afito Masa da matarsa

Baffah hararar nabil yahauyi yace to kaji Dadi ka fado Mata hankalinka se yakwanta Mara kunya Daman matar taka tana da Rana haka ban saniba ai da cewa kayi baka Santa ko kamanta na tinama to inkai yanzu kana santa itakuma in tace Bata Sanka Naga yanda zakayi Dole ai ka saketa

Kunne nabil yatoshe yace bazan iyaba wlh Babu saki Ni da ita Kuma jikina yabani itama yanzu tana sona Dan Allah ka dawomin da matata baffah wlh ba nabil din da kasani bane da

Baffah yace bani da lokacinka se kutashi mutafi Abuja wajan Fatima tinda yau in Allah Yayarda komai zezo karshe kabar mutane su huta da Kai da kakar taka Wai iya yaushe Kuma nabil yazama jikanki kuma kuka Dena fada

Tace ai yanzu mun shirya Kuma shinake gani azaman shatuwa tinda kun batarmin da shatuwa Kuma shi ne mijinta Ashe Dan Miss Miss na da kirki Haka ban saniba bakaga yanda yake yomin siyaiyaba har kudi yake bani su umaru ma hidima yake Tai musu Ashe yafi ubansa miss miss kirki tasa kuka

Shi nabil yanzu kome iya zatace akansa shi da ubansa baya Jin haushi dariyama take bashi

Baffah da su iya Abuja suka tafi sun Isa lfy minister nagida se ganin baffah da nabil da iya yagani nabil na rime da faggwan kayanta suka shigo

iya Kai tsaye wajan minister taje ta zauna kusa dashi tace to miss miss Allah yadawo Dani Ina shatuwa Ina matar taka Fatima itama Ina Mata kallan me kirki Ashe ka goga Mata mugun halinka ko se wani hararata kake kana zaremin Ido du baze tsorataniba ka fitomin da jikata kawai inma magunan kakeso NASA umaru yatara maka yakawo maka kafito da shatuwa kafin inmaka rashin mutunci

Hajiya Fatima tace yihakuri iya kijira zuwa anjima Zan rakaki inda shatuwa take kici abinci ki huta tukunna kirabu da alhaji Ni da kaina Zan kaiki

yau su Amina zasu dawo gida nanjeria mijinta yagama kwas dinsa har ma kwanaki suka Kara bayan wata shidan da sukayi zokuga murna wajan shatuwa ga kiba tayi ga Kyau takara tadada fari sosai ga turanci tanaji yanzu sosai ga yanzu in anganta bazaace tayi rayuwar kauyeba misalin karfe takwas na dare jirginsu ya iso nanjeria hajiya Fatima ce tatura direba ya dauko Amina da shatuwa Kai tsaye gidan minister aka shige dasu shikuma mijin Amina da yaranta gida suka shige se Amina Taraka shatuwa zata shige gidan nata mijin


Lokacin da suka dawo nabil be dawo daga isilamiyaba iyace da minister da baffah kadai agida shatuwa da taga iya har da kuka iyama kuka tafafa tana mamakin girman shatuwa da kyan da takara iya bakin masifa yamutu se murna ake tayi jikalle tadawo


Tace Allah sarki nabilu Yana Ina yazo yaga shatuwa ta dawo yaro Dan albarka ai ingaya Miki Dan miss miss yajansa yanzu du baya masifar Nan da yakeyi


Takalli Amina kema yannan yar Ina yabanki sallah Zaki kasa alwala Ashe kema kinbi halin Miss Miss har dake asace shatuwa

Kafin Amina Tai mgn Sega nabil yashigo dauke da sallama abakinshi cikin nutsuwa yake tafiya gawani kamshin turaransa da yacika wajan kansa akasa yashigo bema kula da suwaye afalanba shatuwa Ido takura Masa tashi tayi tsaye tana kallanshi Yana dago Kai sukai Ido hudu da juna




















New writer's



Hakan Take
*Husba'ahfama*❤👸
*'YAR KWALLIYA*🥳💃



👝👝👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝
👠👠👠
👝👝
👠

💄💅 *DAN MINISTER* 💅💄
🦚🦚




Written by *Husba'ahfama*


*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*

Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*





15-16








Ido suka hau mustsikawa suna dada kallan juna

nabil yace ko dai mafarki nakene ban saniba

Shatuwa itama wajan Amina takoma da sauri tace anty Yaya nabil ne wannan Naga Babu shigar da yakeyi ajikinshi ko sarkar Babu

Dariya dukansu suke musu Amina tace nabil ne shatuwa Kinga yacanja ko

Tace eh anty

Rada akunne Amina takewa shatuwa kardai kimanta da du abinda nagaya Miki kifaja ajinki kafin ki saki jiki dashi Amma Naga ke kanki rawa yake niyar ba da kanki kikeyi ke ko Ina se kin nuna wautarki ta ke rikwan kakace

Kafin shatuwa tayi mgn
Nabil yakaraso wajan shatuwa yasa hannu yatabata yaji dagaske itace ba mafarki yakeba hannu yabude almar tazo shatuwa Amina takalla taga Amina na harararta ai shatuwa Bata da mu da gargadin da Amina take mata da Ido na taja ajinta taje da sauri tafada jikinshi suka rungume juna suna dariya

Nabil yace Aisha ina Kika shiga nake ta nemanki meyasa Kika gujeni kinsan wuyar da nasha akanki kinsan halin da nake ciki saboda rashinki Ina kikaje du tsawan wannan lokacin nake ta nemanki waye yasaceki

Shatuwa tace ba anty Amina bace ta daukeni ta gudu Dani america baffah da mommy ne suka sata ta gudu Dani Wai Dan muna fada Ni da kai yanzuma se da taga nayi fishi da ita na dameta da kuka sannan tadawo Dani har cemata nayi yanzu mungirma mundena fada Ni da Kai Amma anty Amina Bata yardaba har da yimin fada tafashe da kuka

Amina hanu tadora aka tazamo daga Kan kujera ta zauna akasa tace shikenan angudu ba a tsiraba goyan Kaka Kenan akwai wauta daga temako se yazama lefi

Nabil ransa yabaci kallan su amina yafara Yana rungume da shatuwa Yana rarrashinta yace yanzu Ashe Daman du rokwan da nake Tai muku kunsan Inda matata take kukaki ku temakeni ku dawo min da ita se da itama ta dameku tukunna kuka dawo da ita anty Amina meyasa kikai Mana Haka kinsan halin da Dan uwanki yashiga akan hakan da kikayi baffah har da Kai mommy kema haka wlh daga yau Kar Wanda yakara dauke min Mata ba da saniba Allah bazan yardaba yishuru aishata gidanmu zamu tafi yanzu rabu dasu daga yau Kar wanda yakuma zuwa yace kizo kuje wani wajan ba da saninaba karki Kuma yarda kibi kowa kinji

Tace to Kuma ai kace katsani Mata baka sansu Kuma Nima kace baka Sona Ni bazan bika gidan kaba bayan baka Sona Kuma bakasan Mata Ni awajan mommy Zan zauna ko anty Amina ko nabi iya mutafi mazagai tare

Muryar nabil narawa yace haba Aisha kuskurene ko Ada da nake fada rashin sanine Amma yanzu nagane gaskiya wlh yanzu nasan darajar Mata Kuma Ina girmamasu ako Ina suke ta dalilinki nasan darajar Mata aduniya nasan Kuma wacece mace kema wlh Ina sanki Aisha Ina kaunarki bazan iya rayuwa in Babu keba kin Zama wani bangare na jikina karki min Haka Dan Allah ki temakeni kiyarda mu tafi gida yanzu karkisa su baffah suyi Mana dariya daddy da iya kusa Baki ku tayani bawa Aisha bawa

Shatuwa tace Babu ruwansu wannan tsakaninmune Suma ai shedane agabansu kasha fada baka San Mata ba sau dayaba ba sau biyuba

Kwacewa tayi daga jikinshi ta haura sama da gudu tana kuka aminace tabi bayanta da sauri nabil shima binsu zeyi

baffah ne ya hanashi binta yace nabil zauna muyi mgn da Kai Kar kadamu zamu tayaka Bata hakuri zata hakura katsaya yanzu muyi mgn dakai kasan shatuwa na da gaskiya ko tinda kowa yasan akidarka takin du wata mace arayuwarka Kuma daga Kai har ita kunsha fada a gabanmu kun tsani junanku Dan Haka muma muka rabaku muka dauke shatuwa ka Dena ganinta Kuma mu munzata temakwanka mukayi tinda bakasan Mata itama baka Santa Kuma nine jagoran aurama ita tinda itama tana tsoran dokarka takin mata kawai kasaketa mukoma da ita mazagai inda tafi wayo nasamu wani me Santa na auramai

Setin zuciyarshi nabil yadafe da hannu yanamai da numfashi Dakar yace Dan Allah baffah kabar wannan mgnar wlh ko amafarki bazan iya sakin Aisha ba bare da hankalina yanzu ko da tsautsayine da Kuma rashin sani Amma yanzu wlh nadena bazan kumaba Kar ka rabamu muna kaunar junanmu ko itama tana sona tana dai tsoran akidatane na kin Mata Kuma yanzu na Dena itama Kuma wlh Ina Santa in karabamu mutuwa zanyi rayuwata takare kunrasani kenan

kuka yafara kamar wani karamin yaro idanunshi na kakkafewa Yana neman sume musu

Ai minister besan sanda yaganshi gaban nabil yadagoshi Yana jinjigashi Yana Kiran sunanshi karka mutu nabil anbarma shatuwa indai itace farin cikinka shatuwa takace Babu me rabaku Nima Ina tayaka San matarka bazan Bari arabakuba ko da abinda na malkaka aduniya ze Kare Akan abarma shatuwa wlh du Zan bayar in kamutu Ni Kuma yazanyi baffah Dan Allah kayi hakuri kacire mgnar rabuwa tinda yagane gaskiya Nima Kuma nagane gaskiya na baka hakuri Dan Allah kayafe Mana daga Ni har nabil iya kisa Baki za a raba shatuwa da nabil kina kallo kinki cewa komai Fatima kiyiwa baffah mgn zamu rasa danmu shatuwa kizo kiga halin da mijinki yake ciki baffah ze rabaku kizo kice kema kina sanshi Dan Allah kiyi hakuri da du abinda yafaru abaya kiso mijinki

Iya sarkin kuka tace rabu dasu Miss Miss aidu jinshi nake Babu wani rabasu da za a yi ainima Ina da hakki akansu tinda jikokinane wlh bazan Yarda arabasuba Dan Miss Miss tashi kaji nabaka shatuwa har abada takace rabu da usuman ai kana da kirki yanzu Nima Ina sanka saura miss miss Naga shima yadan Fara mutunci tashi kayi hakuri anfasa rabaku Fatima mikomin ruwa mesanyi nabashi yasha ko giyarku ta yanbirni me sanyinnan tsiyayo akofi na duramasa abaki yasha wajan kunfa,kunfar Nan Zaki zubo zatafi rike Masa ciki

Hajiya Fatima tace to iya ikwan Allah ko Yaya se kinsa mutane dariya har da giyar Yan birni me kunfa Kuna shaaninku ke da alhaji kunyi amanku kun lashe kuku kadai su alhaji an saduda anga dangwal zemutu har da bawa shatuwa hakuri tatafi tana dariya

Ruwa me sanyi takawo hade da lemon da iya tace ruwan aka Fara shafamai afuska akabashi wani yasha Yana bude Ido wajan baffah yatashi yaje da rarrafe kamar wani yaro saboda jikinshi Babu kwari yakwanta Akan kafarsa yaishuru Yana Mai da numfashi saboda mgnar ma inyayi kirjinshi ciwo yake Daman Kuma bawata lfyce da Shiba du yawan tinanin shatuwa yasashi rashin lfy

Baffah kansa yahau shafawa da hannu yace Allah yaimaka albarka nabil yanzu na yarda kana san shatuwa Kuma zaka riketa Amana daga Kai har sani yanzu na yarda da ku alhamdulillah burinmu yacika na ganin kun shiryu ka kwantar da hankalinka Ni bazan rabaku da shatuwa ba tinda kana santa gatanan Amana nabaka ita ka riketa hannu binbiyu kabawa marada kunya kanunawa duniya mace Yar gatace awajanka Kuma Mata abin darajawane da girmamawa aduniya da idan kowa dadu wani da namiji kadau matarka kutafi gida Allah yabaku zaman lfy Allah yabaku zuria tagari je kakirata kutafi kayi hakuri da dauke maka Mata da mukayi baka saniba

Murna nabil yafara har da rungume baffah Yana ta godiya minister ma Babu kunya yake tayiwa baffah godiya Yana murna iya se washe Baki ake ana hawaye tana taunar goranta

Amina da tabi shatuwa daki duka takaiwa shatuwa abaya tana dariya tace Ashe kina da hankali kanwata aini nazata shirme zakimin Akan yanda natsara Miki Ashe kina sane adai tausayawa Dan uwana Dan Naga yagama macewa Akan sanki kema Kuma nasan kina san Dan kaninnawa ai da bakibi abinda natsara mikiba da munbata da ke

Shatuwa zatayi mgn Kenan nabil yaturo kofa yashigo kallan Amina yafara yace nifa wlh anty tsoranki nake yanzu tinda Kika sacemin Mata Kuma yanzu tsoran ganinku tare da aisha Zan dinga ji Dan Nagano yanzu kece malamarta itakuma dalibarki to malama ayi hakuri Zan tafi da matata gida tahuta tagaji sosai tanasan hutu duda kinmin lefi Dole nai Miki godiya Yar uwata ngd Allah yabiyaki anty Amina da gudun mawar da Kika bada baffah da mommy sun yimin bayani du abinda yafaru Kuma nagane

Amina nasiha takuma yimusu sosai meratsa jiki tace Ni zantafi kanwata se yaushe ko se naganki

Kai shatuwa ta daga Mata tasa hannu tarufe idanta tana dariya

Amina tace ai nasan amsar da zan samu Kenan awajanki kanwata zuwa gobe zansa akawo Miki kayanyakinki har abincin safe du zansa akawo muku asha soyaiya lfy Ni natafi wajan nawa mijin nabarshi shikadai agida tafice tana dariya

Amina nafita nabil yatako zuwa gaban shatuwa Ido yakura Mata Yana murmushi itakuma Kai ta sunkuyar kasa takasa had a Ido dashi wani kwarjini taga yayi Mata yacika Mata Ido

Yace Aishata babu mgn amaryar nabil jikokin iya ikwan Allah ko bakiyi murnar ganinaba har yanzu fishi kike Dani Baki huceba nasan namiki lefi ranar da zamu rabu Dan Allah kiyi hakuri ko temaka Miki banyiba

Kai tadago tana kallanshi fadawa tayi jikinshi tarungumeshi tafara mgn ahankali tace Ni Babu lefin da kai min ai hakkinkane mijina lefinka dayane zuwa biyu awajena kabini da mugunta ranar baka ragaminba katashi ka tsallakeni bakaji tausayinaba ko temakona bakayiba wannanne kadai yatsayemin araina Dan Haka na dada yarda baka Sona Kuma Dan katsani Mata kai min Haka Kuma bakaga wuyar da nashaba nadade Ina jinya saboda da Kai takara mgnar cikin shagwaba da kukan kissa

Dada birkita nabil tayi lokaci guda yaji yashiga wani Hali mararshi yaji tafara murda Masa saboda yanda take dada shinshige Masa jiki ga shagwabarta dada rudashi take jiyayi kafafunshi bazasu iya tsayawaba janta yayi zuwa Kan gadan dakin suka zube bakinta yakamo yahada da nashi sun Dade ahaka sannan yabarta suna Mai da numfashi Dakar yafusgo mgnar bakinshi yafara mgn

Aisha nidai bazan gaji da Baki hakuriba yanzu tinda Allah yadawo min dake lfy zakiga irin kaunar da Zan nuna Miki da gata da kulawa se kin manta kowa kin kuma yarda nabil masoyinkine na gaskiya kinji amaryata yasumbaci goshinta tashi mutafi gida kihuta kintafi kinbar mijinki da ciwanshi me wahalar dashi kin lasawa mijinki Zuma me Dadi kin dada jefashi agogin bege sefa kinyi hakuri da Ni aisha Dan mijinki jarimine ba rago bane

Ita Bata gane me yake nufiba tana kwance Akan girjinsa se shakar kamshin jikinsa take dagota yayi suka tashi tsaye kansa tahau kalla tana dariya tsalle tayi ta shafo gashin kansa taduba hannunta taga bakomai dariya tasa tace ai nazata bakin fenti kakoma shafawa gashin Kan naka Ashe ainahin gashin kankane yanzu Yaya nabil yabar shigar Mata yadena sa fenti akansa wlh naji Dadi yayana Kuma mijina naji dadin canjawarka kamafi kyau yanzu wlh kamar bakaiba kakoma balarabe mijina yadena shigar Mata da zame wando

Murmushi yayi shima yace ko Ni yanzu wlh shigar Bata burgeni Kuma naji Dadi da denawata yafaranta ran matata aikema kin canja sosai my baby gashi har wannan kwalliyar ta Yan mazagai kin Dena kin koma Yar birni muje gida bacci nakeji kema nasan agajiye kike ga mijinki na neman temakwanki

Hannunta yakama suka sauko kasa suka samu su iya nahira afalo lokacin Amina tashige gida shatuwa se wani sunne Kai take abayan nabil

iya tace au Dan miss miss Daman Kuna ciki tindazu ai munzata kun tafi Kai Dan miss miss ka kwacemin shatuwa kaga ko takaina batayi ta mijinta take

Dariya hajiya Fatima tayi tace ai iya sedai kiyi hakuri nabil yakwace Miki shatuwa mijinta zatabi shatuwa Kuma ta kwacewa alhaji nabil

Dariya minister yayi yace ai nayarda Ni shedane nabil yazama na shatuwa Kuma jikan iya

dariya kowa yasa nabil yace Dan Allah su baffah kuyiwa iya mgn tadena kirana da Dan miss miss daddy Kuma Wai miss miss take kiranshi nace Mata bahaka ake fadaba Taki yarda nace in Bata iya kiraba takirani da ainahin sunana nabil shima din da tatashi Kira se da tabata sunan Wai nabilu se kace wani tsoho kuma iya daga yau sunan matata Aisha kidena kiranta da wata Shatuwa nasoke wannan sunan daga yau

Iya tace ko sannu babana wlh baka isaba Shatuwa take Kuma Haka NASA Mata tin tana yarinya ban,yarda ana kiranta da aishaba kaima in nakiraka nabilu in kaki amsawa wlh Dan miss miss Zan kiraka dashi aikaine kakira kanka da sunan tin ranar da aka kawo Shatuwa gidannan Kuma naji mutane da yawa na kiranka da Dan miss miss shi Kuma ubanka Miss Miss ake kiranshi ko amazagai haka kowa yake cemasa ko bahakaba usuman

Baffah yai dariya yace hakane iya rabu dashi kowa yasanshi da Dan miss miss

Nabil hannun Shatuwa yakama yace zo mutafi Aisha baffah ma yakoma bin raayin iya su daddy se da safe mun tafi gida iya se goben in kinzo dada ganin gidanmu baffah Dan Allah karka tafi ban saniba

Ficewarsu sukayi zuwa gida Shatuwa se sunkuyar da Kai kasa ake ba bakin mgn

Iya tace a lanlai Shatuwa Dan Miss Miss ya fitsareki yakwace,minke da gaske ku ganifa ko akanta ba tadamu zata bishiba murnama Naga tanayi Kuma mun Dade bamu haduba ko tace aguna zata kwana tarufe Ido tabi mijinta ko kunya Babu ko sallama Babu se wani sunsunkuyar da

Please Login or Register in order to submit comment