Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibitin nan baka ga abinda zai tayar maka da hankali ba.

Ranar an kai wata mata mai ciki asibitin. Kwanaki uku kenan da aka yi mata scanning, aka ga cewar dan cikinta ya rasu. Maimakon a yi inducing dinta, sai mijin ya ciccibeta suka koma gida. Wani abin karin haushi da ban takaici shine, mijin nata likita ne, duk da ba zan ce likitan ainihi ba tunda shago ne yake dashi babba da ake sayar da magunguna.
Tun shakaranjiya take nakuda, bai kaita asibiti ba sai ya kira unguwar-zoma. Ana ta kai da kawo dai, har jiya bata samu ta haihu ba, shine yau da safe suka tarkata ta zuwa asibitin. Ana maganar a dauketa a kaita Shika, domin a mata tiyata a cire cikin, rai yayi halinsa.
Abin gwanin ban tausayi da takaici. Ga ta da yara kanana wadanda basu gama mallakar hankulan kansu ba.

Har muka je inda muke hawa acaba, abinda muke tattaunawa kenan ni da Janan.
Ta kalleni tana canza muryarta zuwa alamun roko, "don Allah sis, kizo muje gida mana. Sai ki koma da yamma, kinji?".

Na harareta, "tab! Allah Ya kyauta wallahi. Ni kin ma ga tafiyata!".
Nayi saurin sa hannu ina kiran daya daga cikin yan acaban da suka yi jerin gwano, suna jiran fasinjoji.
Da sauri ta riko hannuna, "please, kinji? Don Allah!. Wallahi kwana biyun nan gidan babu dadi. Dama a wajen Yaya Bilal nake samu na dan ji sauki wasu lokutan, idan yana gida. To shima kwanannan sai a hankali. Tun jiya da yamma ya rikice, ko kallona baya yi wallahi. Yau da safe dana gaida shi, ko amsawa ma baiyi ba. Kuma ya hana ni yawo, balle inje wani wajen. Don Allah, muje ki dan debe min kewa, kinji?".

Gabadaya tausayin ta ya lullube ni. Wani irin bahagon zama suke yi da matar yayanta. Wani lokacin sai kayi kuskure kace irin zaman kishiyoyin nan ne da suke zabga dan banzan kishi suke yi.
Ba tare dana sake tunani ba, na gyada mata kai. Tayi tsallen murna tare da rukunkume ni.

Napep muka tara, bayan na ba dan acaban da muka kira hakuri. Unguwar PZ muka nufa, wadda bata da nisa da wajen da muke zuwa TP din.

Gidan Yaya Bilal, inda Janan take zaune, babban gida ne sosai. Daga nesa idan ka hango shi zaka yi tunanin irin family house dinnan ne. Sai dai su biyu ne suke zaune, shi da kaninshi Jameel, sai kuma matansu.
Kowacce tana da part dinta, masu fadi da nisa da kowannensu, ta yadda idan daya taga dama, zata kwashe watanni bata ga yar'uwarta ba.

Sashen gidan Yaya Bilal ake fara tardawa idan aka shiga gidan. Shima can din ya kasu kusan parts uku, duk da sauran biyun duk a kulle suke, dayan ne Janan take zaune ita da Raheema matar Yaya Bilal.
Shekaru biyu da suka wuce ne suka yi auren, basu ma cika da yin shekara biyu ba. Har yau Allah bai basu haihuwa ba.

Abu ne da naji kus-kus suna tashi akan cewa wai, wai Yaya Bilal din baya haihuwa. Saboda matarshi ta farko ma, Ameerah, wadda suka kwashe shekaru kusan shida a tare, auren saurayi da budurwa, bata taba haihuwa ba itama.

A hankali muka yi sallama cikin falon gidan, bamu ji motsin kowa ba, ko na TV babu, balle na mutane. Janan ta ja ni zuwa dakinta, ta koma kicin ta dauko mana ruwa da lemu.

Ina zaune a gefen gadonta, na dinga jiyo karar sautin kida tana tashi. Na kalleta, tana tsaye a gaban wardrobe tana nema mana kaya masu saukin nauyi da zamu saka.
Nace "wannan karar fa, daga ina take fitowa haka?".

Ta dan juyo ta kalleni, kafin ta maida kanta cikin closet din. "babu mamaki su Haleemo ne suke kallo!".

Na dafe baki, "wai dama yaran nan suna nan har yanzu?".
Tayi yar dariya, wadda take lullube da zallan takaici, "to dama ina zasu je? Ai suna nan a gidan nan, basu da ranar fita!".

Ta miko min Skirt dogo na wani yadi tare da riga, na amsa na fara zare kayan jikina, nace "to Allah Ya kara rufa mana asiri!".
Tace "ameen".

Ni tunda nake ganin gidan aure da cakudewar rayuwar aure, ban taba ganin irin wadda ta kama kafar ta gidan Yaya Bilal ba.

An saba idan aka yi aure, akai amarya ita daya zikal dinta gidan miji. Sai dai ita wannan abun nata ya bambanta. Koda aka kai amarya, sai kannenta guda biyu suka samu waje suka share, suka mike kafafu a gidan. _Marry one, get two free kenan!._

Watanni bakwai da kai amarya, Babbar kawar amaryar ta kaso aurenta, itama taje tabi layin jerin yan'uwanta dake gidan kamar wadda bata da gidan zama. Yanzu dai su ukun duka suna zaune a karkashin kulawar Yaya Bilal ne. Amma yar kanwarsa daya tilo dake zaune dasu, sun kasa riketa balle su kula da ita.

Kullum fata da buri nasu ta bar gidan, bin malamai, asiri, kissa da kisisina, babu wadda basa yi. Allah ne kadai yake kareta a gidan nan.

Tana gama sallatar azuhur, ta ja ni muka shiga kicin domin mu nemi abinda zamu saka a cikinmu. Muna cikin girkin Yaya Bilal ya shigo kicin din, ya amsa gaisuwar da muka mishi a kaikaice.
Ya kalli Janan yana wani cin magani, "ke ina Raheema take ne?".
A hankali kamar mai tsoron magana, tace "yanzu muma muka dawo, bamu sameta a gidan ba".
Bai kara cewa komi ba, ya fita daga kicin din. Ko me yake faruwa kuma yanzu? Na saba ganin kallon so da kulawa daga gareshi zuwa ga yar kanwar tashi, yau kuma naga wani abu daban.
Na kalli Janan dake kokarin hadiye kwallar data cika mata ido, cike da tausayi. Haka Allah ya halicceta mai sanyin hali, da sanyin zuciya.

Danwaken fulawa muka kwaba, daidai wanda zai dauki cikin mutum biyu. Duk kokarin da tayi na mu kara yawan fulawar, ki nayi. Saboda nasan saboda wannan lalatattun yaran take so muyi da yawa. Ni kuwa da in dafa abinci da hannuna, kattin banza su cinye, su goge hannu da tissue su kara mike kafa, karshe ni ce zan kwashe kwanukan da suka ci abincin ma, na gwammace in zauna da yunwa.

Muna gamawa, muka juye shi a cikin kula tare da gyara kicin din tsaf, kamar babu abinda aka yi. Janan ta wuce mana da kular daki, ni kuma na dauki plates da vegetables din da muka yanka nima na fita dasu.

A bakin kofar kicin muka ci karo da Salama, kanwar Anty Raheemah. Duk cikin kannenta babu wadda ta fita rashin da'a da rashin mutunci, shi yasa jininmu bai hadu ba, sam.
Ta wani tsaya kerere, ta kama kugu tare da kara babakewa akan hanya. Ko tayi zaton zagayeta zanyi in wuce? Na saki wani murmushin mugunta. Lallai yarinya har yau baki gama sani na ba.
Na tunkareta gadan-gadan. Da dai taga ina shirin bangajeta, sai taja baya. Na ja dan siririn tsaki a cikin raina, ina raya 'dama kin tsaya kin ga karshen wulakanci!'.

Ta wani daga murya, "ina namu abincin?".
Na kuwa tsaya cak, na juya na kalleta, "ban gane naku abincin ba? Kin daukeni aikatau din yi miki girki ne dama ban sani ba?".

Tayi gyatsine, "taya za ayi ki shigo har cikin gidan Yayata, kiyi girki sannan kuma ki k'i ajiye mana?".

Naji wata dariya na neman subuce min, nace "to sannu hamshakiya! Sarauniya mai girma!! Allah Ya bamu hakuri mu da bamu da gidan Yaya dake aure a gidan mutane, balle muje mu shimfida mulki a inda bai dace ba!. Girki ne, bamu yi daku ba. In kinyi zuciya, ga hanyar kicin nan, ki shiga ki girka wanda yafi wanda muka girka!".
Na juya na shige daki, tare da maida kofar dakin na rufe. Ina jin sautin maganganu da zage-zagen da take yi. Janan tace "ni dai wallahi da baki biye mata ba!".

Harara na jefa mata, "ai a haka suke samun damar taka ki kamar wata sakara. Ke dai da kika ga zaki iya, sai kije kiyi tayi. Ni kam, ba zan iya jure rashin kunya irin nasu ba wallahi!".

Kai kawai ta gyada, don tasan gardama dani ma bata baki ne.



Karfe biyar na mata sallama zan koma makaranta. Zuwa lokacin babu kowa a cikin gidan, muna jin lokacin da suka fita. Daidai bayan tagar dakin Yaya Bilal, na hangi wani abu daya dauke min hankali. Da sauri na kalli Janan, "kai! Kinga kuwa na manta jotter na akan gado, don Allah taimaka ki dauko min ita mana, zan jira ki anan!".
Babu musu tace "to!".

Tana bada baya, nayi sauri na karasa wajen. Da sauri na duka tare da yin bismillah, na fara hak'a. Kamar yadda nayi zato, wasu kullin abubuwa naci karo dasu. Da sauri na ciresu, na maida kasar na rufe kamar yadda take.
Ina komawa inda Janan ta barni, sai gata ta dawo. "Ni fa ban ganta ba, ko dai a asibiti kika barta ne?".

Na daga mata hannun dama ta, "ashe tana hannuna, sha'afa nayi".
Ta kada idanu, "ke dai shiriritarki tayi yawa wallahi!".
Muka jera da ita har zuwa inda zan hau bus. Sai da taga na shiga, motar ta tashi, sannan ta juya tana daga min hannu, tare da jaddada min dana isa cikin makaranta, in kira ta.
Dariya kawai nayi na gyada mata kai, wani lokacin haka take, kamar wata overprotective Yaya, ko Uwa.























*☆⋆02⋆☆*





"Haba Sweety, ni sai ki dinga cewa wai bana sonki saboda Allah! Bayan kin san cewa duk duniya bani da kamar ki!".
Ya fada daga can daya bangaren na wayar, whinnying kamar wani karamin yaro.

Na kada idanu sama, "To ai kai dinne sai ka dinga wasu irin maganganu da suke saka ni cikin shakku, Umar". I mean, ta ya mutumin da yake ikirarin saboda Allah yake sonka, kuma ya dinga kokarin dilmiya ka a duniyar 'sex chat?'. Kullum muka yi waya dashi, da kalar dirty maganganun da zai tare ni dasu, tun ina mishi alkunya, a tunanina zai fahimci zancen ya daina, har na fito baro-baro na fada mishi cewa bana son hakan, amma duk da haka bai fasa ba. Don haka nace mishi naga alamun cewa ba son gaskiya yake yi min ba, akwai abinda ya gani a jikina dai kawai. Nan ma yace ba haka bane, daga nan ya dan rage yin maganganun, note that 'ragewa' nace, ba dainawa ba. Ni kuma kullum ya dauko min maganar abinda nake ce mishi kenan.

Yace "to naji, shikenan. Ni dama na kula da cewa ba wani sona kike yi ba, son da nake miki yafi yawa!".
Nayi murmushi kasa-kasa, da wata ce kam, zai iya samun damar cin galaba a kanta da irin wadannan maganganun har yayi amfani da wannan damar ya samu abinda yake bukata daga gareta, amma banda ni. A tsaye nake kyam! Akan duk wata kalma da na furta, ko abinda na kudurta a cikin raina.

Nace "duk abinda kayi tunani hakan ne, Umar".
Ina jin dariyar daya saki mai sauti, wadda ta saka ni yin murmushi ba tare dana shirya ba. "Sweety na kenan! Shi yasa nake jin sonki kullum yana kara yaduwa a cikin sassan zuciyata wallahi. Amma yanzu Oga na ya shigo inda muke, zan kira ki anjima in shaa Allah, ok?".

Na girgiza kai, "babu damuwa ai, sai anjiman".
Nan muka yi sallama da juna, bayan ya manna min sumba ta jikin wayar. Kai kawai na girgiza, speechless, muka ajiye wayoyinmu.

Na sauke ajiyar zuciya tare da kurawa gadajen da patients suke kwanciya akai da suka kasance empty. Ban san lokacin dana dauka cikin tunani ba, sai da naji an dafa min kafada. Nayi firgigit! Na kalli gefen damana, Janan ce.
Murmushi na saki ina harararta cikin wasa, "wato tsabar shahara, yau sai karfe tara ma kika zo ko?".

Tayi yar dariya, "to me yafi raina? Tunda an riga anzo anyi supervising dinmu, mun kuma yi presenting dinmu, ai babu abinda ya rage mana sai chilling. Yaya Bilal ne ma ya tsaida ni da jira, wai sai na jira shi ya karya sannan zai zo ya sauke ni. Kinsan na fada miki mun shirya dashi".
Na gyada kai ina wasa da kan wayata, "yeah, haka kika ce. Yanzu idan muka gama ina kika nufa ne?".

Tace "yo ni ina na sani? Watakila in tafi wajen Yaya Sa'a Funtua, ko kuma Kaduna wajen Umman mu. Ke fa?".
Na harareta, "har wani tambayana ma kike yi? Bayan kin riga kin san komi?".
Tace "to kizo muje wajen Umman mu mana kawai? Tunda dai ko kin je gidan ma ba wani jimawa zaki yi ba?".
Nace "lallai ma, watanninmu kusan shida a makaranta fa, ban leka gida ko da wasa ba, kuma kinsan idan muka dawo hutu ma ba wani hutu zamu samu ba, gwara inje dai kawai".
Ta kada kai gefe guda, "ai shikenan. In ka ki ji, ba zaka ki gani ba. Amma ai ba a goben zaki tafi ba dai ko?".
Nace "a'ah, sai ranar assabar in Allah Ya kaimu".

Kiran da daya daga cikin nurse din ta kwala mana, shine ya katse mana hirar da muke yi, muka tashi muka tafi wajen data kira mu.

Ranar ma karfe daya muka tashi. Janan ta sake ja na zuwa gidan Yaya Bilal, wai in taya ta hada kayan tafiya. Yau mun ci nasarar samun Anty Raheemah a gida. Tana zaune a falo sun kure kida ita da kannenta, wasu suna rawa, wasu kuma a zaune kawai suna kallonsu. Muka musu sannu da gida, suka amsa a kaikaice. Bamu kula su ba muka wuce dakin Janan abinmu.

Da yamma wajen karfe biyar, na mike ina rataya jakata. Janan ta shigo dakin hannunta rike da wasu ledoji biyu, tace "Yaya Bilal zai shiga Samaru yanzu, yace zai rage miki hanya".
Na zaro ido, "what? No!! Kada ma ya wahalar da kanshi wallahi, zan bi bus kamar yadda na saba".
Ta harareni, "jibe ta don Allah! To ya riga yace zai kaiki, yanzu haka yana jiranki ma a waje. Sauri yake yi, yau a gidan Anty Ameerah zai kwana, kuma dawowarshi daga Kaduna kenan, so yake yi yaje ya huta".

Na dafe kai, "to menene na wahalar dashi akan cewa ya wani sauke ni a school? Da kin barshi yaje ya huta abinshi".
Tace "sai kiyi kuma, tunda sabonki ne yin korafi. Yaya dai yana waje yana jiranki, idan kin tsaida shi, damuwar ki ce. Gashi Umma tace a kawo miki".

Ta miko min daya daga cikin ledojin hannunta, na leka kaina cikin ledar. Turare ne, kayan biscuits da chocolates har da yan kunne da takalmi mai kyau. Umman su Janan tana yi min wani kallo ne kamar yadda take kallon Janan. 'Diyarta, 'ya kuma mafi soyuwa a gareta.
Duk wani abu da zata yiwa Janan, sai ta hada da ni. Ko ina nan, ko bana nan, ko ina sane, ko bana sane, zata bani da hannunta, ko ta bada a ajiye min.
Shi yasa nake matukar girmama matar. Ko ba don alkhairin da take yi min ba, don yadda take daukata kamar diyarta. Idan nayi wani abu da bai dace ba, zata kira ni ta zaunar dani, ta bani duk wata shawara da uwa ta gari ya dace ta bawa diyarta, ta tsaya daram, akan kafafunta, wajen dora ni akan hanya, duk da cewa bamu hada ko digon gumi ni da ita ba.
Ko a hakan kadai aka tsaya, wallahi ta gama min komi. Balle kuma ayi zancen irin alkhairanta a gareni.

Duk abinda zata yiwa Janan, ba ta taba bambanta mu, sai dai ko kala da tsayi.

Na kalleta ina murmushi, "Madallah da wannan sako, lallai Umma ta gano ni. Bari in koma sai in latsa mata kira inyi godiya. Na gode kwarai".
Tayi dariya, "ai fa! Yanzu ke dai mu tafi, kada Yaya ya gaji da kira".
Kamar yana ji, sai ga kiranshi ya shigo wayar. Ta daga tana ce mishi gamu nan fitowa, ban san me yake ce mata ba, na dai ji tana cewa "minti daya!". Ta ja hannuna muka tafi.
Sai da na leka ta dakin Anty Raheemah muka mata sallama, sannan muka fita ni da Janan.

Yaya Bilal yana cikin motarshi a zaune, ya zuro kafarshi daya waje. Kyakkyawan takalmin D&G baki, budadde na fata yana ta sheki a kafar tashi. Na gaida shi kafin na zagaya ta daya gefen na shiga gefen mai zaman banza.
Janan ta leko tana min Allah ya kiyaye, yayin da Yaya ya tashi motar muka fita daga gidan.

Tafe muke a cikin motar, babu wanda yake furta uffan. Sai sautin wakar "earned it' ta weekend dake tashi a nutse. A hankali nake bin wakar, ba lallai ka sani ba sai idan ka kalli bakina sosai, inda zaka ga yana motsawa kawai ba tare da sauti ya fita ba.

Idanuna suna ta tagar gefena suna kallon cikin garin Zaria. Na dinga jin alamun idanu a kaina, nasan cewa zargin hakan ne kawai nake yi a cikin raina. Da abin ya girmama, sai na juya a hankali cikin dabara, na kalli inda Yaya Bilal yake, idanunshi straight suna kallon gabanshi. Na girgiza kai, dama sai da nace zargine nake yi.

A kofar Bitmas Bakery naga yayi parking motar. Ya kashe tare da fita daga motar yana muttering "excuse me!". Wanda ba don na juya a daidai lokacin idanuna sun sauka akan fuskarshi, na ga bakinshi ya motsa ba, ba zan ji mai yace ba.
Na zaro wayata a cikin jaka ina dubawa don in rage kadaicin zama.

Bayan kimanin mintuna biyar da fitarshi, naji an kwankwasa gilashin tagar motar, gefen inda nake zaune.
Na daga kai, naga Umar a gefen a tsaye.

Nayi murmushi tare da sauke gilashin kasa, "hey handsome, me kake yi anan?".
Shima yayi murmushin, "wai mun tsaya ne zamu sayi fruits fa, ina jiyowa kuma sai na ganki. Daga ina?".
Nace "daga gidansu Jan. Tare muke da Yaya Bilal, zai sauke ni a makaranta".

Ya gyada kai, "uhmmn... Ya shirye-shiryen tafiya gida? Jibi zaki tafi ko?". Nace "ehh!".

Yana nan a tsaye muna hira, Yaya Bilal ya dawo. Kwata-kwata ban ga wucewar shi ba, sai da ya bude motar ya shigo. Na kalli Umar ina murmushi, "handsome, bari mu wuce ko?".
Ya gyada kai, "Ok Sweety, zamu yi waya ko?".
Na jinjina kai, "in shaa Allah. See you!".
Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, "hey, bari in miko miki fruits".

Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, "ta gode, sauri muke". Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada.

A main gate na kalleshi nace "Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?".
Yadda kasan bango, haka ya maida ni. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige ta cikin makarantar.
A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya,
"na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah".

Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, "karbi mana, kina bata min lokaci!".

Nasa hannu biyu na karba, nace "nagode, Allah Ya amfana". Yace "Ameen" a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel.

Sai bayan sallar magriba dana gama komi, na bude ledar. Bread ne da roll cake da suke yi a wajen guda biyu, da ice cream biyu shima. Na dauki daidaya na mikawa Ayla, tana ta min tsiya, wai "lallai yau Umar ya tuna damu!". Dariya kawai na mata na koma gefe ina cin nawa. Sai da na gama ci sannan na tashi na hau hada kayan tafiya gida.
Bayan na gama, na turawa Baba sako akan cewa zan taho ranar Asabar, ya turo min kudin motar tafiya gida.

Washegari muka je asibiti muka yi bankwana dasu. Daga nan muka yi bankwana da Janan, itama ranar Lahdi zata tafi Kaduna wajen Umma. Ni da ita kuma sai idan mun dawo hutu.
Na dawo hostel na karasa shirya kayana, wadanda zan bari anan kuma na hade su waje daya tsaf na rufe da mayafai saboda kura. Na share waje na zauna ina jiran kudin mota.





_*NA'ILAH!*_



Mahaifana su duka biyun, asalin yan garin Gashua ne. Mahaifina, Alhaji Al-Hassan Hannafi, cikakken haifaffen garin Gashua ne. Iyayenshi hausa/fulanin dake cikin garin ne, duk da cewa sun rasu tun ma kafin a haifeni, sai sauran dangi na nesa-nesa kawai. Yayin da mahaifiyata, Yana, ta kasance ruwa biyu. Mahaifinta Barebari ne, mahaifiyarta kuma Shuwa Arab.
Kakana Bako Audu, shahararren malami ne, Kakata Fatima da muke kira da Fatsu, ta kasance mai sana'ar sake-saken kaya, a cewarta tun tana budurwa.

Mahaifiyata ta kasance kyakkyawar mata, fara, doguwa, mai dogon hanci da dogon gashi da dara-daran idanu masu tsari. Babu abinda ta bari na Fatsu. Allah Ya hore mata hakuri, Kawaici da kawar da kai. Aurenta da mahaifina ya kawo yar matsala a tsakanin danginsu ta fannin mahaifiyarta, su a sonsu ta auri dan uwanta ta fannin uwa, ko Barebari, amma ta kafe. Sai kuma matsalar rashin aiki, don a lokacin da suka yi aure, ya gama kammala degree dinshi akan banking and finance, amma bai samu aiki ba. Jajircewar Bako ce kawai tasa aka yi auren, suma kuma dangin nata suka hakura.

Bayan auren nasu da kadan, ya samu aiki da bankin GT, anan cikin Gashua din, ya fara zuwa aikinshi.

Yaya Mudatthir shine 'Da na farko a wajen iyayenmu. Shekaru biyar cur ya bani.
Yawancin rayuwar yarintata a gaban su Fatsu da Bako nayi ta. Ba kamar Ya Mudatthir daya dauko kamanni da suffofi da halayen Mama kamar tayi kaki ta tofar, ni babu abinda na dauko nata sai yanayin idanuwanta da kuma dogon sassalkan bakin gashinta. Bayan haka, gabadayana Bako Audu ce. Ina da tsayi na daidai-wa-daida, da zubin halitta mai daukar hankali. Shi yasa bana shiga mai fitar da surar jiki. Kalar fatata baka ce, wasu kuma su kan ce wankan tarwada. Ko ma dai wace iri ce, ina jin dadi da alfahari da kalar fatata. Kalata mai sheki ce, sannan fatata mai taushi ce.

A halayen Mama kam, zan iya cewa tsafta da wasu halayen na dauko nata. Hakuri na kadan ne, sannan bana daukar wulakanci ko kadan, ko daga wajen waye kuwa. Bako ya kan ce shi duk cikin danginsu bai ga mai hali na ba, zafin kai, kafiya da taurin kai. Ina da rikakken ra'ayi, idan nace zan yi abu, to zanyi. Idan kuwa nace ba zan yi ba, mai canza min wannan magana kam sai ikon Allah.

Munyi zama mai dadi da iyayenmu, a dan abinda zan iya tunawa na rayuwarmu da wanda Mama ko Ya Mudatthir suke bani labari, Babanmu ya so mu, mutum ne mai son iyalanshi da kuma kyautata musu. Duk da cewa bashi da wani hali na azo a gani, amma rayuwarmu Alhamdulillah, babu abinda muka nema muka rasa.

Wannan kafin ya auro bakar ashana Ramata kenan. Lokacin da aka yi auren, Ya Mudatthir yana makarantar maza ta kwana a cikin Yobe. Ni kadai ce a cikin gidan, sai su Mama.

Tunda aka yi auren wannan, muka nemi walwala da kwanciyar hankalinmu muka rasa. Muka nemi Babanmu, Mama ta nemi mijinta, duk muka rasa. Rayuwar gidan ta koma kadaran-kadahan, yau daci gobe b'auri. Babu wani armashi. Ance wai ba'a kure mai hakuri, amma ni na gani akan idanu na, ranar da aka kure hakurin Mama a gidan nan, ranar da ta daga baki tace hakurinta ya kare.
Ranar ce Baba yasa belt ya zane mu ni da ita a tsakiyar gidanshi, akan naman kaji.
Ya kai mata nama ta soya, aka nemi naman a dakinta aka rasa. A cewarshi, satar nama take mishi idan ya kawo, dama kullum idan ya kai nama a soya sai ya ga babu wani bangare.

Mama tace "haba Malam, in rasa abinda zan daukar maka a gida sai nama? Tunda muke zaune da kai, na taba daukar maka abu ba tare da saninka ba?".

Budar bakin amaryar Baba sai cewa tayi, "kenan kina nufin ni na dauki naman ko kuwa me?".
Mama tace "ni ban ce ba, amma haka bai

Please Login or Register in order to submit comment