Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ta wulakantata kafin ta bude mata gidan, store din abinci a kulle yake, wani lokacin sai dai ta saka kudinta ta sayi abinci. Idan Yaya baya gidan to ita da babu duk daya suke, duk kokarin Janan akan su daidaita abin yaci tura. Ita cewa ma tayi gwanda ace fada suke yi akan wannan zaman doya da manja din.

Ita kuma tayi-tayi dashi akan ya bari ta koma wajen Anty Sa'a tunda suna Zaria yanzu, ko basa nan akwai kanwar mijinta da suke zaune tare a gidan sai ta zauna dasu, ko kuma ya kama mata gida a samaru, ko ma dai a ina ne, amma yayi fir ya ki. Ita kuma bata so ta takura mishi da maganar kada yace ko bata son zama da matar shi ne ko wani abu.

Sai a ranar naji cewa ashe ba mahaifinsu daya da Yaya Bilal ba. Mahaifinsu Yayan ya jima da rasuwa, bayan nan ne ta auri wani mutum a Kaduna, shine mahaifin Janan din. Sai lokacin na fahimci komi, ina ta mamakin dalilin da yasa Ummarsu take zaune a Kaduna bayan duk danginsu suna Zaria, nayi zaton ko aikine ya kai baban su Janan din Kaduna. Amma nayi mamaki, koda wasa basu taba nuna mata banbanci ba, ita ko su Harira diyar kishiyar Umma, basu taba nuna mata wani ki ko kyama ba.

Janan kuka take yi sosai lokacin da take bani labarin wannan, na rungumeta ina bata hakuri, don shine kadai abinda zan iya yi a lokacin, har ta gama kukan. Daga nan muka fito da littafanmu muka cigaba da karatu har aka kira sallah muka tashi muka yi, muka koma muka cigaba da karatunmu. Muna nan sai ga Anty Ameerah ta leko, tace muje mu debi abinci, Janan ta fita zata zubo mana abincin, sai gata ta dawo wai Yayan yace muje muci tare dasu. Tace haka yake, in dai yana gidan tare suke cin abinci. Na dauki hijabita na saka muka fita.
A falon sai na daga baki ina kallon ikon Allah, gabadaya mata ta rikide, ta koma kamar wata salihar kirki, kamar ba wannan matar da take amsa mana magana da dai-daya ba.
Sai nan-nan take yi damu, abinci kamar zata zuba mana a baki yadda take ta turo mana plates na varieties din abinci gaban mu. Tsabar mamaki ma ni kasa yin magana nayi. Lallai an saka Janan a cikin tsaka mai wuya. Idan har haka take mata, to lallai kuwa babu wanda zai yarda da cewa idan an saka mata yatsa a baki zata ciza, sai dai idan har tayi hakan a gabanka.

Muna gama cin abincin muka koma daki. Muna shiga na fara zuba magana, tsananin mamakin matar ya hana ni hada maganganu masu ma'ana ma, Janan sai gefe ta koma tana min dariya. Sai dana nutsu sannan na iya zama muka yi magana akan haka da ita.

Sai bayan sallar la'asar can, sannan na mike ganin cewa Yaya bashi da niyar barin gidan. Janan tayi-tayi dani akan in tsaya Yaya ya fito, nace mata ina da abubuwan yi ne a hostel, dole ta kyaleni na tafi.
Daga wannan rana ban kara taka kafata zuwa gidan Yaya Bilal ba har yau.


Karatunmu yaci gaba da tafiya cikin nasara. Ni da Janan duk bamu dauki karatunmu da wasa ba, duk da bamu yin topping, amma dai Alhamdulillah, babu abinda ya taba dawo mana.

Muna shekarar mu ta uku, Yaya ya sake yin wani auren, ya auro Anty Raheemah. Yadda ya rikice akan wannan auren, yasa na kara tsurewa da lamarin maza. Lokacin bikinsu da Anty Ameerah yadda yake ta rawar kai da zakewa, kai sai kayi zaton babu wata 'ya mace da zata sake yin daraja ko kuma a idonshi bayan ita, sai gashi tun ba aje ko'ina ba ya karo wani auren.

Janan tace ba karamin rikici suka yi da matar Yayan ba, har ta kai ga cewa ya fita ya bar mata gida, inda abin ya yiwa Yaya ciwo matuka. Ya karasa gyara gidan gadonsu, dama can ya fara gyarawa zai kai Ameerah din, iyayenta suka hana.

An dai yi biki lafiya, despite tashe-tashen hankulan da aka sha, amarya ta tare a gidan mijinta, Janan ma tayi kaura can.
Muna ta murna, a tunaninmu wannan zamu tafi da ita, tunda sa'ar mu ce ita, ashe yaudarar kanmu muke yi.

Raheemah da kannenta irin 'ya'yan mace dinnan ne. Zaku yi mamaki idan kuka ji cewa suna da uba da yake raye, kuma auren iyayensu yana nan, amma suna zaune separately. Duniya da son abin duniya ya rufe musu ido daga su har uwarsu, mahaifinsu kuwa mutum ne mai wadatar zuciya da tsoron Allah.
Tun yarintarsu, bin bokaye da malamai shine amsar tambayarsu da komi nasu. Kodayake, wanene a garin Zaria bai san da zaman Hajja Ladidi ba? Shi yasa tashin farko da naji wai Yaya zai auri daya daga cikin diyanta, abin ya bani mamaki kwarai. Sam ire-iren su ba irin wadanda yaya yake hulda dasu bane.

Kannen Raheemah biyu da suka tare a gidan su suke kara rura wutar dake cikin gidan Yaya Bilal. Su duka biyun suna karatu a jami'ar Kongo. Saboda haka suka baro gidansu dake Hanwa, suka koma can saboda ya fi kusa da makaranta. Duk da a zahirin gaskiya ba hakan bane. Haleemo da Salama sune yan kanzagin ta, sune masu zuwa garuruwa da kauyuka amso mata magunguna wajen malamai da yan tsubbu yayin da take gida ta mike kafa.

Sai da na yiwa Janan fatan dama a wajen Anty Ameerah ta zauna, tace mugun fata nake mata. A cewarta zama dasu Haleemo, duk da gallazawar da suke mata, yafi mata sau dubu akan zama da Ameerah. Don haka na kawo idanu na zuba mata. Don haka ban taba ganin laifinta ba don tana zuwa wajen Umma weekend ba duk karshen sati, watarana ma nima ina binta.

To da yake ita rayuwa babu abinda hakuri baya maka, gashi yanzu har zamu shiga shekararmu ta karshe, ko ma in ce mun shiga. Duk da har yanzu dai babu abinda ya canza, sai ma karuwa da yake yi. Tun basa cin karfin Yaya akan Janan, har suka zo suka ci galaba a kanshi. Wasu lokutan haka zai birkice mata kamar ba Yayan nan nata mai son ta ba, sau tari sai dai ta kira ni tayi ta kuka, ni kam sai dai inyi ta bata hakuri. Rabin abubuwan da ake mata a gidan nan, ko Ummarsu bata sani ba, tunda duk cikin danginsu babu mai zuwa gidan balle yaga halin da take ciki.

Shi kanshi Yaya din, yau da gobe ce tasa ya gane tana zaman gallazawa a gidanshi. Sai ma watarana da yazo ya tadda Sa'adiya wadda suke cewa Adi, kawar Raheemah din da take zaune a gidan, tana ta zagin Janan akan wai bata yi mopping din falo ba, ran Yaya ya baci matuka, ya tara su su duka ya ja musu kunne, kuma yace daga ranar duk wadda ta sake taba mishi kanwa a gidannan, sai ta bar mishi gida. Aikin gidan ma kuma daga ranar ya hana ta yi, ita ce dai taga dama taci gaba da yi, tunda kunnen kashi gareta. Duk yadda nayi da ita akan ta bari tunda yace ta bari din, kiyawa tayi. Don haka na zuba mata ido, ni dai nasan da ni ce, da zuwa yanzu su duka sun bar gidan.

To rayuwar dai haka ake yinta, yau dadi, gobe madaci, gashi yanzu wasu abubuwan sun zama sai dai a tarihi. Nan da lokaci kadan ma, zata bar musu gidan.





*








*☆⋆04⋆☆*





* ☆ *


Har washegari Lahdi ina jiran Baba ya turo min kudin mota, amma shiru kake ji, kamar an shuka dusa.
Na duba agogon dake daure a tsintsiyar hannuna, naga cewa karfe goma sha daya na safe ta wuce. Nayi kwafa. Wani text din na sake tura mishi. Sai can wajen karfe sha biyu da rabi naji karan shigowar text, na duba naga shine ya turo min kudin motar, nayi kokarin resisting takaicin daya tuko ni, zuciyata na tunatar dani gida za ni ba wani waje ba.
Sai da nayi sallah sannan muka yi sallama da Aylah cike da kewa. Ina shirin fita kiran Umar ya shigo wayata, ya sanar dani yana waje yana jira na, don haka na ciccibi akwatuna na fita.

Ya saka akwatin a bayan booth, ni kuma na bude gidan gaba na shiga. Ya shigo motar ya tashe ta. Sai daya tsaya a banki na ciri kudi, sannan muka tafi. Har tashar mota ya kaini. Sai daya biya min kudin mota, sannan ya min sallama. Na mishi godiya sosai. Allah ya taimakeni motar ta kusa cika, ba'a jima ba muka dauki hanyar Katsina.



*


Karfe biyar na yamma a cikin garin Katsina ta mana. Motar tayi karan karshe a cikin tasha, a gajiye na fito daga motar ina mika. Na rataya jakata a kafada tare da daukar dan madaidaicin trolley din dana sako kayan da zan bukata na fita daga tasha din. Shatar adaidata nayi har unguwar Magama inda gidanmu yake.

Madaidaicin gidane daidai masu rufin asiri. Na fita daga cikin adaidaita din bayan na biya shi kudin shi. Wasu daga cikin yaran gidan dake kofar gida suna wasa suka bazamo da gudu suna ihun min oyoyo, nayi dariya ina dukawa kasa yadda zasu ji dadin rungumeni sosai. Abbakar ya dauki trolley na, yayin da Auwal ya rike jakar hannuna, na kama hannun Mufeedah muka shiga gidan.

Matan gidan suna zaune a tsakar gida, Anty Alawiyya na dura kunun aya da take yi na sayarwa a cikin gororin ruwa, Anty Ramata kuma tana kofar kicin a zaune, ina zaton ita take da girki yau.
Duk suka saurara da abinda suke yi jin hayaniyar yara har muka shiga cikin gidan. Anty Alawiyya ce ta mike tana dan murmushi, "mutanen Zaria ne yau a garin? Ai bamu ji labarin zaki zo ba koda wasa!".
Nayi murmushin yake, dama a ina zasu ji? Na san koda wasa Baba ba zai fada musu ba. Ni kuwa dama ba waya muke yi dasu sosai ba, tunda na fara makaranta, babu wadda ta taba daga waya ta kira ni da sunan mu gaisa, sai nice idan naga an kwashi kwanaki nake kiransu haka nan dai, musamman ma don mu gaisa da yara. Kullum idan na dawo daga makaranta zancen daya, ne babu wani canji.

Na sauke Mufeedah kasa tare da gaidasu daya bayan daya, suka amsa fuska babu yabo babu fallasa, na tabe baki tare da ciccibar akwatuna na tunkari dakin daya kasance nawa tunda muka dawo Katsina.
Na ja nayi turus, sakamakon ganin kofar dakin a bude, abin ya bani mamaki. Na tabbata da zan tafi makaranta sai da na saka kwado na rufe kofar dakin, kuma ban bar dan makullin a gida ba. Babu wanda yayi tunanin yi min karin bayanin abinda yake faruwa, don haka na tura kofar dakin.

Abu na farko daya fara min sallama shine tarin kayana da aka hade waje guda acan karshen lungu, akwatuna daya kan daya, kwalaye bisa kwalaye, yayin da ilahirin tsakiyar dakin yake shake da tarkacen kayan Maryam. Na juya na kalli Saudah yar autar Anty Ramata dake zaune a kofar dakin mamanta dake kusa da dakin da nake, nace mata "waye yake kwana a dakina?".
Tace "Anty Maryam ce, Mama tace ta koma dakinki tunda kullum a kulle yake kuma tayi girma da zama a dakinta".

Nayi kwafa ina kallon Uwarta ta, nace "shine saboda tsabar bani da muhimmanci babu wanda yayi tunanin sanar dani?". Duk suka yi tsuru su biyun. Na sake yin kwafa tare da shiga cikin dakin. Ko karewa dakin kallo ban yi ba naje na dauro alwala na dawo dakin nayi sallah. Sai dana gama sannan na kira Umar na sanar dashi sauka ta, yayi min sannu da zuwa. Bayan nan na kira Janan itama muka gaisa, tana dariya tace "bana miki wayo, ni tun safe ina gaban Ummana!".
Nayi yar dariya, "ya miki kyau ai, Allah ne ma yasa motar tayi gudu sosai, kila da sai magriba zan iso ni kam".
Mun dan yi hira kadan da ita, har ta bani Umma muka gaisa, sannan muka yi sallama da ita.

Tashi nayi na fara gyara kayana da aka wulakanta a dakin, ina maida su ainihin wajen da suke da. Kafin a kira sallar magriba na kammala gyarasu tas. Nayi sallah, na zauna akan abin sallar nayi karatu kamar yadda na saba har aka kira isha'i nayi, sannan naci gaba da gyara dakin. Na share shi nayi mopping, na dauko room freshener dana saba yin guzurinta na fesa a dakin. Nan da nan dakin ya fito tas dashi, ba kamar yadda na same shi dazu ba kamar bana mahaukata.

Tun ina karatu naji alamun karan motar Baba alamun ya dawo gida. Kasancewar yau babu aiki nasan cewa daga shago yake. Zuwa yanzu nasan cewa ya ci abinci kuma ya huta, na dauki hijabina na fita zuwa dakinshi. Babu kowa a dakin na shi sai shi kadai. Na durkusa acan gefenshi na gaida shi, ya amsa. Da alamun yana cikin yanayi mai dadi, tunda har na zauna muka danyi hira dashi. Abinda sai lokaci zuwa lokaci yake faruwa.
Ban san me yasa ba, ni da Baba sam bamu cika shiri ba. Amma nafi kyautata zaton rawar kaina ce ta janyo hakan, tunda ya sha fada ba sau daya ba, ba sau biyu ba.
Sai da Ramata ta shigo dakin sannan na mishi sai da safe, na koma dakina, ko ince dakinmu.

Ina komawa shirin barci na fara yi. Bayan nayi Sallar shafa'i da wutiri, na samu gefen katifa na zauna tare da dauko wayata dana ajiye a kasan filona. Ina cikin chatting Maryam ta shigo cikin dakin.

Duk yan dakin Ramata, ita, Aliyu da Hareerah, da ita kadai muka fi dasawa. Sauran suna kan hudubar uwarsu na cewa 'yan uba, ba 'yan uwa bane! saboda haka bamu cika shiri dasu ba. Amma ita babu ruwanta ko kadan.

Tayi murmushi tana kallona, "yanzu Hareerah take fada min cewa kin zo, ina ta mamaki".
Nayi yar dariya ina kallonta tana zame after dress din dake jikinta, riga top mai karamin hannu da wnadon bakin jeans suka bayyana a jikinta, dariyata ta koma daga gida mai nuna alamun tambaya, nace "daga ina kike, kuma wannan shigar fa?".

Ta kalli jikinta kafin ta kalleni, "kawata take bikin birthday, shine na leka wallahi".
Na girgiza kai, "birthday party kuma sai da irin wannan shiga Maryam? Me yasa?".
Tayi dariya, "Yaya Na'ilah ke da kike makarantar jami'a kin fa fini sanin irin wadannan abubuwan. Yanzu 'yanmata ai sai da swagger! Idan mutum ba so yake a dinga mishi kallon taro-uku-sisi ba!".

Cikin mamaki nake kallonta, "ban san daga ina kika dauko wannan kalar abu ba Maryam, amma hakan bai kama ce ki ba gaskiya. Ta ya kike zaton Mamanki zata dauki wannan maganar idan taji irin shigar da kike boyewa a cikin hijabi? Don daga ji nasan cewa wannan ba shine karonki na farko ba".

Tayi dariya tana watso min wani kallo irin 'are you kidding me' dinnan Tace "me Mama zata ce kuwa? In fada miki gaskiya ita ta bani shawarar in dinga sanya after dress idan zan fita, in naje can inda zan je sai in cire saboda kada wani idon sani ya ganni a haka... Amma meye na wani boyo? Zamaninmu ne fa!".
Tunda ta fara maganar bakina a hangame yake a bude, Subhanallah! Yaushe yaran gidanmu suka fara bin wannan hanyar ne? Nasan cewa tsakanin iyalan dama babu hadin kai da kaunar juna, saboda tun farko basu ga hakan daga wajen iyayensu ba, amma wannan wani babban al'amari ne, wanda nake ganin idan har aka bari ya girmama, akwai matsala. To amma, abinda uwa take supporting da dukkan karfinta, waye yake da karfin hana ta?

Ta tunkari kofa zata fita tana furta, "bari in zo inyi sallah!".
Ina nan zaune ina ta saka da warwara ta dawo, ta shimfida abin sallah ta kalli gabas. Yadda take yin Sallar ma kadai abin zai baka mamaki. Kamar wadda bata taba taka ajin islamiya ba Raka'o'in data jero masu yawa yasa na fahimci cewa ba sallar isha'i kadai tayi ba.

Sai dana bari ta gama duk abinda zata yi, har ta kwanta sannan na dubi inda take, nace "ni kuwa a wani matakin karatu kike yanzu a islamiya?", na dai san cewa yanzu tana ss2.
Tayi dariya, "na kusa wata ma ni rabona da makarantar nan yanzu, yan ajinmu aka wa karin aji zuwa na yan sauka, ni kuma aka barni a ajin baya shi yasa na daina zuwa ma kwata-kwata".

Na tashi zaune sosai ina kallonta, sanin halin Maryam na saurin fahimta da ganewa yasa nafi jin dadin zama yi mata magana ko gyara akan wani abu, ba kamar Aliyu ba. Sau tari dan karamin gyara sai ya kaimu ga ya kalli tsakiyar idanuna ya zage tas kamar wanda yake jira dama.

Nace "kin san fa yanzu kece babba a gidannan Maryam. Kuma duk abinda kika yi, kannenki da suke tasowa shi zasu dinga yi. Yanzu idan basu ga yayarsu na zuwa makaranta ba, ta ya kike tunanin zasu samu kwarin gwiwar zuwa makaranta? Kinga ke dai baki da bakin cewa su zo su tafi, tunda kema ba zuwa kike yi ba. Sannan dubi dai irin shigar da kika yi yanzu, ya Baba zai ji, kuma me kike zaton zai ce duk ranar da yaci karo da irin wannan abu da kike yi? Maryam, kinga ke diya macece, sannan yarinya, kada ki bari rudin duniya da abokai ya rude ki, ki saka kanki cikin rayuwar da tafi karfinki. Shiga irin wannan da kike yi ta nuna jiki, ki shiga cikin kawaye ana ta cakuda da maza, akan wane dalili? Ina kika baro tarbiyar gidanmu da kuma al'adarmu ta hausa/fulani?".

Tayi kasa da kanta a kunyace, "wallahi Yaya, Mama ce take cewa in dai ba za'a hada mu da yan ajinmu ba, sai dai in daina zuwa makarantar. Kuma ita take sawa inyi shigar. Ranar ma ana bikin Na'imah dana sanya hijabi sai ta hau fada, tana cewa wai ni ban waye ba!".

Na girgiza kai cike da jimami, iyayen yanzu yawanci su suke bada gudummawa wajen lalacewar tarbiyar yaranmu. Uwa ce wai zata dorawa diya akidar yafa gyale da saka suturun banza, ita zata sanya mata akidar bin kawaye da samarin banza, daga karshe kuma idan lamari yazo ya bace bakinta ne zai fi na kowa wajen ihun cewa an lalata mata tarbiyar yara, bayan kuma itace tayi contributing wajen lalacewar tata.

Tsam na tashi na koma kusa da ita na zauna tare da dafa kafadarta, nace "idan tayi hakan ba laifi bane, tana so ne ki zama abar kallo, kamar tauraruwa. Sai dai, zaki iya zama fiye da hakan ma, ba kuma sai kin sabawa Ubangiji ba, kin gane?". Ta daga kai.
Nace "good. Saboda haka gobe zamu je islamiyar taku, zan samu malaman naku muyi magana dasu. Sannan don Allah, shiga ta banza mai nuna jiki, ki daina yin ta. Ko ba don ke ba, ki duba kimar da Baba yake da ita a idanun mutane, balle ke kanki idan baki kame kanki a matsayinki na ya mace ba, Maryam zaki ga kin rasa girmamawar mutane, kin fahimce ni?". Nan ma ta gyada kai.

Nayi murmushi cike da jindadi. Yanayin yadda jikinta yayi sanyi ya nuna min cewa taji, kuma ta dauki abinda nace. Na rungumota gefen kafadata ina kara yi mata bayanai da nasiha akan rayuwa. Daga karshe dai na janyo laptop dita na kunna mana kallo a ciki, babu TV a dakinmu sai na Baba dana matanshi, yawanci can muke zuwa muyi kallo. Ranar akan katifarta na kwana.

Tunda Baba ya tashemu sallar asuba ban koma barci ba. Ina gama azkar din dana saba yi lokacin gari ya fara yin haske, na fita na share tsakar gida tas. Na hada kayan wanke-wanke nayi, na shiga kicin na kunna wuta tare da dora ruwa wanda yara zasu yi wanka dashi na kuma dora musu abincin da zasu tafi makaranta dashi.
Har wajen karfe bakwai na safe ban ga motsin kowa a tsakiyar gidan ba. Matan sun riga da sun san dama ni nike ayyukan gidan, shi yasa daga ranar da nazo, har in bar gidan babu wadda take ayyukan gida. Duk da har yanzu Ramata bata sakar min ragamar ayyukanta ba, ranar girkinta ita take yin girkinta gabadaya, wanke-wanke da shara ne dai take bari na dasu. Hakan bai dameni ba.

Yanzun ma ina kan zuzzubawa yara taliyar dana dafa musu a cikin kulolim makaranta, sai gata ta fito daga dakin Baba. Kicin din ta shigo, na gaidata ta amsa. Tukunyar ruwan zafi ta bude, ta zuba daidai wanda zata hadawa Baba shayi ta fita daga kicin din.
Daya bayan daya yaran suka fara fitowa, na dauki kofi ina zuba zuzzuba musu. kowannensu yazo, sai ya duka ya gaida ni, ni kuma sai in mika mishi kofin shayi da biredi ya amsa ya tafi.
Maryam da take tsaye a gefena tun dazu, tayi murmushi lokacin dana mikawa Auwal nashi kofin shayin bayan na shafa kanshi.
Tace "shi yasa nake son ki zo gida wallahi, yaran nan sun fi behaving. Yanzu da ni ce da har yanzu ina nan ina ta faman su zo su amshi abincin, amma su ki".
Nayi dariya, "kin san yara sai da lallashi da lalama. Yadda nasan halinki na zafin kai dama, ta ina yara zasu dinga binki sau da kafa?".
Duk muka yi dariya ni da ita. Itama na zuba mata nata ta tafi ta karya.
Ban fita daga kicin din ba sai da duk suka tafi, sannan nima na zuba nawa nan tafi daki na karya.

Bayan na gama gyara kicin, wanda nasan idan ban gyara ba haka zan dawo in same shi. Musamman ma tunda yau da safe Ramata ta fita daga girki. Haka kuma Anty Alawiyya zata shiga tayi nata girkin ta barshi kaca-kaca. Na girgiza kai cike da takaicin halayen wannan matan.
Dana gama da kicin daki na koma shima na gyara shi. Kai tsaye wanka na fada, na sanya riga da zani na atamfa, dinkin single da fitted riga. Sallama na wa mutanen gidan na shiga cikin unguwa. Daya baya daya na bi gidajen makota muna gaisawa, daga karshe na dire a gidan su Kulsum, a raina ina ayyana sai da yamma sannan zan je nata gidan, in yaso bayan magriba sai in dawo.

Ina yin sallama a tsakar gida, na ja nayi turus ganin yar halas din a tsakiyar gida tana wa yarinyarta yar shekara uku, Muneerah wanka.
Tana ganina tayi murmushi, "saukar yaushe?".
Nayi dariya ina zama a gefenta, "jiya da yamma wallahi. Me kike yiwa mutane a gida haka tunda safiyar Allah Ta'ala? Inna ina kwana?". Na gaida Inna data fito daga cikin madafi. Inna ta amsa tana min sannu da zuwa.

Na kalli Kulsum, "ko dai awon ciki kika zo ne?".
Ta dan harareni, "wani irin awon ciki kuma ana zaman lafiya? Mu a gidannan ma muka kwana in fada miki!".
Jikina yayi sanyi da jin abinda tace, nace "kamar ya? Ban gane ba, wani abu ya faru ne?".
Inna tace "menene ma bai faru ba yar nan? Ai tafi wata daya a gida yanzu".
Naji zancen kamar wani saukar guduma a kaina, nace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!".

Inna ta girgiza kai kawai, "ai ke dai abin ba'a cewa komi Na'ilah. Sai dai abinda Allah ya kaddara dama babu makawa sai ya faru, sai hakuri kawai".

Na fara cira idanu tsakanin Inna da Kulsum, Babu wanda ya sake yin magana a cikinmu har ta gama yiwa Muneerah wankan, ta tsaneta cikin zani. Muna zaune ta shiryata cikin kayanta, ta tura ta zuwa wajen Inna. Kallo

Please Login or Register in order to submit comment