Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubu ladar kuɓutar da ni da ya yi."

Sai fatake suka ce, "Mu ma za mu biya shi lada kamar yadda ka biya shi, idan dai har ya kwance mu daga ɗauri." Daga nan sai biri ya kwance su, ɗaya bayan ɗaya. Suka yi sauri suka nufi inda jirginsu yake. Suka tarar ko allura ba a cire ba daga cikin jirgin. Suka shiga suka tuƙa da sauri, suka bar wannan tsibiri.

Bayan sun yi nisa da tafiya, sai Abu Muzaffar ya ce da su, "Ya ku fatake, ku cika alkawarinku ga biri." Suka ce, "Mun ji, mun karɓa." Kowa ya jawo jakar kuɗinsa ya ƙirga dinari dubu ya ba Abu Muzaffar. Shi ma ya ƙirga dinari dubu ya haɗa da waɗanda fatake suka ba shi, ya ƙulle su wuri guda. Sai ya kasance an tara wa birin nan kuɗi masu yawan gaske.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
06/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (4)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Bayan sun yi nisa da tafiya, sai Abu Muzaffar ya ce da su, "Ya ku fatake, ku cika alkawarinku ga biri." Suka ce, "Mun ji, mun karɓa." Kowa ya jawo jakar kuɗinsa ya ƙirga dinari dubu ya ba Abu Muzaffar. Shi ma ya ƙirga dinari dubu ya haɗa da waɗanda fatake suka ba shi, ya ƙulle su wuri guda. Sai ya kasance an tara wa birin nan kuɗi masu yawan gaske.

Suka ci gaba da tafiya, kwanci tashi, har suka isa birnin Basara. 'Yan uwa da abokan arziki suka tare su da murna, suka yi musu barka da zuwa. Abu Muzaffar ya tambayi mutane, "Ina yaron nan Abu Kasala?"

Nan take labari ya ishe uwata, ya Shugaban Muminai, ta zo wurina ina barci, ta tayar da ni ta ce, "Tashi ka tafi wurin Abu Muzaffar, na ji an ce jirginsu ya iso, ka ga me ya sayo maka. Wataƙila Allah ya sa ka sami abin kanka daga kuɗin da muka ba shi."

Na mutsuttsuke idona ina gunaguni, saboda an tayar da ni daga barci. Sai ba ce wa mahaifiyata, " To, riƙa ni in tashi."

Ta kama hannuna na tashi zaune. Na ce ta ɗauko mini takalmina ta sanya mini. Bayan ta sa mini takalmi, na ce ta riƙa ni in miƙe tsaye, kuma ta taimake ni wurin tafiya. Haka dai ta lallaɓa ni, kamar kwai, muka tafi ina jan ƙafafu, riga na taɗiye ni kamar zan faɗi, har muka isa bakin teku, inda fatake suka sauka.

Yayin da Dattijo Abu Muzaffar ya gan ni, sai ya tare ni da fara'a yana cewa, "Lale marhabin, barka da zuwa, ya kai wannan yaro, wanda kuɗinsa suka yi sanadin tsirar mu daga halaka, tare da yardar Ubangiji Maɗaukakin Sarki." Ya miƙo mini biri, ya ce, "Tafi da wannan biri wanda na sayo maka idan na gama kimtsawa zan aiko zuwa gare ka."

Na ja biri ga hannuna ina gunaguni, ina cewa, "Wallahi ni dai ban ga alfanun wannan biri da Abu Muzaffar ya sayo mini ba. Ta yaya biri zai amfane ni?" Da muka isa gida na ce wa mahaifiyata, "Kin matsa mini da dole sai na yi kasuwanci, kin hana ni more barcina. To, ga hajar da aka sayo mini nan, dube ta ki gani." Na nuna mata biri.

Daga nan sai na sami wuri na zauna, zuciyata cike da takaici. Ban daɗe da zama ba sai ga bayin Abu Muzaffar sun shigo inda nake. Suka tambaye ni, "Kai ne Abu Muhammadu Kasala?"

Na amsa musu, "I."

Daga nan sai ga Abu Muzaffar ya shigo da kansa. Na tashi na kama hannuwansa na sumbaci 'yan yatsunsa. Ya ce mini, "Ya Abu Muhammad, biyo ni zuwa gidana."

Na amsa masa, "Na ji, na karɓa." Ya shige gaba na bi shi a baya, har muka isa gidansa.

Ya ɗauko dukkan kuɗin nan da ya samu ta sanadin biri, da kuma kayan jauhari da birin nan ya tsamo cikin ruwa, ya ba ni. Ya ce mini, "Karɓi wannan, duka naka ne. Su ne ribar da aka samu daga dirhaminka biyar da ka ba ni." Ya kwashe labarin abin da ya faru yayin tafiyarsu ya gaya mini. Ya ɗauko akwatuna ya sa mini dukkan dukiyata cikinsu ya kulle. Ya kira wasu bayinsa ya ce su ɗaukar mini zuwa gidana. Ya kawo mabuɗan akwatunan ya ba ni. Ya ce, "Tafi da wannan dukiya, dukkanta mallakarka ce."

Na tafi da dukiya wurin mahaifiyata na nuna mata. Ta yi matuƙar farin ciki, ta ce, "Ya ɗana, lokaci ya yi da za ka watsar da wannan kasala taka. Ka ga dai yanzu Allah ya arzutaka da dukiya, yi maza ka tafi kasuwa ka sami rumfa ka fara kasuwanci."

Nan take kuwa sai na ji wani sabon karfi a jikina, ragwancina ya tafi, kamar cirar ƙaya. Ashe dai talauci shi ke kawo lalaci da kasala. Na sami rumfa a cikin kasuwa, na shiga saye da sayarwa gadan-gadan.

Kullum kuwa idan na buɗe rumfata sai mu zauna wuri guda tare da birin nan. Abin da na ci shi yake ci duka, abin da na sha kuma shi yake sha. Sai dai wani abin mamaki game da birin nan shi ne, kullum da safe ya kan bar ni, ya yi tafiyarsa. Ba ya dawowa wurina sai da tsakar rana, kuma idan ya dawo yakan zo da jaka ɗauke da kuɗi dinari dubu, sai ya ajiye ta kusa gare ni ya zauna. Haka yake yi kullum. Da wannan kuɗi da biri ke kawo mini kullum da kuma ribar da nake samu a rumfata, sai na zama hamshaƙin attajiri. Na mallaki gidaje da yawa, na sayi ganoki da lambuna. Na mallaki bayi da kuyangi, baƙaƙe da farare, masu yawan gaske.

Wata rana ina zaune a cikin rumfata tare da biri, sai na ga yana ta waige-waige, kamar mai neman wani abu. Na ce a cikin raina, "Me yake damun wannan dabba yau?"

Kamar ya ji abin da na faɗa, sai Allah ya buɗe masa baki, ya yi magana da gwalamniya, kamar yaro mai koyon magana, ya ce, "Ya Abu Muhammad!"

Yayin da na ji biri ya yi magana, sai na firgita don tsoro. Sai ya ce mini, "Kada ka ji tsoro, yanzu zan sanar da kai labarina."

Ya ci gaba da cewa, "Ka sani, ni maridi ne daga aljanu. Na zo wurinka ne domin in taimake ka, in fitar da kai daga cikin talauci. Yanzu kana ɗaya daga cikin manyan attajiran wannan birni. Lokaci ya yi da za ka saka mini da tawa buƙata zuwa gare ka."

Na tambaye shi, "Mecece buƙatarka gare ni?"

Ya amsa mini, "Ina so in haɗa ka aure da wata yarinya kyakkyawa, mai hasken fuska kamar wata daren goma sha huɗu."

Na dube shi cike da mamaki na ce, "Da yaya za ka haɗa ni aure da wannan yarinya, kuma wacece ita?"

Biri ya ce mini, "Gobe ka sanya tufafinka na alfarma, waɗanda suka fi kowaɗanne kyau. Ka hau alfadara wadda aka ɗaura wa shimfiɗa ta zinariya, ka tafi zuwa ga kasuwar 'yan harawa. Ka tambayi rumfar Sharif, idan aka nuna maka shi, ka shiga rumfarsa ka zauna kusa gare shi. Ka ce masa, ka zo neman auren 'yarsa wance. Idan ya ce maka, ba ka da arzikin da za ka auri 'yarsa, ka zaro jakar kudi mai dinari dubu ka ba shi ita. Idan ya buƙaci ƙari, ka ƙara masa. Idan ya kuma buƙatar ƙari, ka ƙara masa. Ina so ka saye shi da kudyi har ya amince da zai aura maka 'yar tasa."

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
06/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (5)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Biri ya ce mini, "Gobe ka sanya tufafinka na alfarma, waɗanda suka fi kowaɗanne kyau. Ka hau alfadara wadda aka ɗaura wa shimfiɗa ta zinariya, ka tafi zuwa ga kasuwar 'yan harawa. Ka tambayi rumfar Sharif, idan aka nuna maka shi, ka shiga rumfarsa ka zauna kusa gare shi. Ka ce masa, ka zo neman auren 'yarsa wance. Idan ya ce maka, ba ka da arzikin da za ka auri 'yarsa, ka zaro jakar kuɗi mai dinari dubu ka ba shi ita. Idan ya buƙaci ƙari, ka ƙara masa. Idan ya kuma buƙatar ƙari, ka ƙara masa. Ina so ka saye shi da kuɗi har ya amince da zai aura maka 'yar tasa."

Na ce, "Na ji, na karɓa. Gobe kuwa zan aikata kamar yadda ka umurce ni."

Washe gari na sanya tufafina na alfarma, na ɗaura wa alfadarata shimfiɗa ta zinariya. Na tafi tare da bayi goma, biyar na yi mini zagi, biyar na dafe da kuturi, har muka isa kasuwar 'yan harawa. Aka nuna mini Sharif yana zaune a cikin rumfarsa. Na sauka daga kan alfadara, na shiga cikin rumfarsa na gaishe shi, sa'annan na zauna kusa gare shi. Ya dube ni ya ce, "Mun yi murna da zuwanka. Ka zo ne domin ƙulla harakar kasuwanci a tsakaninmu?"

Na amsa masa, "I, na zo da wata muhimmiyar magana ce zuwa gare ka."

Ya tambaye ni, "Wace magana ce wannan?"

Na amsa masa, "Na zo neman auren 'yarka ne." Na sunkuyar da kaina kasa, ina jiran in ji abin da zai ce.

Ya dube ni da kyau, ya sake dubana, ya ce, "Ba ka da kuɗin da za ka auri 'yata, kuma menene asalinka da darajarka?"

Na zaro wata jaka mai ɗauke da dinari dubu na jan zinari, na miƙa masa, na ce, "Waɗannan su ne darajata kuma su ne matsayina, kamar yadda wani mai hikima ya faɗa, 'babban matsayin mutum ga sauran mutane ita ce dukiya.' Ko ba ka ji yadda aka faɗa ba a cikin wannan waƙa:

"Mai dirhami biyu shi yake da abin faɗa,
Zancen da yas so duk yakan furta a baki nasa.

Ka ga an tsare shi ana ta sauraren batu,
Shi ko yana ta isa da alfahari da iko nasa.

Sani dai saboda kuɗin ake masa fada,
Ba don su ba da ka tarar da ana ta ƙyama tasa.

Da zai yi ƙarya 'yar kaɗan ko mai yawa,
To sai ka ji jama'a suna ta yabo na zance nasa.

Amma talaka idan ya furto gaskiya domin a ji,
To za su ce ƙarya yake ta faɗa a zance nasa.

Ka sani kuɗi ne martaba a idon mutanen zamani,
Mai su yakan miƙe ƙafarsa yana ta mulki nasa.

Su ke zama harshe ga mai son yin batu,
Su ne makamin far ma duk maƙiya a yaƙi nasa."

Yayin da ya ji wannan waƙa sai ya duƙar da kansa ƙasa, ya yi jim cikin tunani. Can ya ɗago kansa ya ce mini, "Idan har da gaske kake yi za ka auri 'yata, to, ka ƙaro mini dinari dubu uku."

Na ce, "To."

Na aiki ɗaya daga cikin bayina cewa ya ruga gida ya ɗauko mini dinari dubu uku. Da bawa ya kawo mini kuɗi, sai na miƙa wa Sharif. Nan take ya tashi, ya kulle rumfarsa. Ya gaya wa abokansa attajirai maganar ɗaurin aurena da 'yarsa, ya kuma gayyace su zuwa gidansa domin su shaidi ɗaurin aurenmu. Ya juyo wurina ya ce mini, in tafi in shirya, nan da kwana goma za a ɗaura aurenmu da 'yarsa. Na koma gida cike da farin ciki. Na gaya wa biri yadda muka yi da uban yarinya. Ya ce mini, "Ka yi daidai."

Yayin da lokacin ɗaurin aure ya kusa, sai biri ya ce mini, "Akwai wani abu da nake so ka yi mini, idan ka yi mini wannan abu to zan ba ka dukkan abin da ka bukyata daga gare ni."

Na tambaye shi, "Mene ne wannan abu?"

Ya ce mini, "A cikin ɗakin da za ka tare da amaryarka, za ka ga ƙofar wani ɗaki a rufe da kwaɗo na tagulla. Ka fakaici idon matarka idan ta yi barci, ka tafi ga wannan ƙofar ɗakin, ka laluba daga ƙasan ƙofar za ka ji mubuɗin kwaɗon, ka dauka ka buɗe ƙofar. Idan ka shiga cikin ɗakin za ka ga wani babban akwati na baƙin ƙarfe, wanda ba ya da marufi. Daga cikin akwatin, a kowace kusurwa tasa, za ka ga wani farin ƙyalle abin rubucewa da ɗalamusai. Daga tsakiyar akwatin kuma akwai wani faifai cike da kuɗi. A bisa faifan za ka ga wani farin zakara a ɗaure, da wata baƙar laya a ƙafarsa ta hagu. Daga gefen akwatin kuma za ka ga macizai guda goma sha ɗaya, a ɗaya gefen kuma za ka ga wata wuƙa ta azurfa. To, ka ɗauki wuƙar ka yanke kan zakaran nan da ita, kuma ka yayyanke ƙyallayen nan masu ɗalamusai. Sa'annan ka kifar da akwatin. Daga nan sai ka yi sauri ka koma wurin matarka, ka kwanta. Wannan shi ne abin da nake so kawai ka aikata mini."

Na ce masa, zan aikata abin da ya umurce ni da shi.

Da ranar daurin aure ta zo, na tafi tare da jama'ata zuwa gidan Sharif. Aka rubuta takardar ɗaurin aurena da yarinya tare da shaidu, aka shafa Fatiha, mutane suka watse. Da dare ya yi na shiga wurin amaryata, na gan ta yarinya ce kyakkyawar gaske wadda harshe ba zai iya bayyana kyawunta ba, nan take kuwa tsananin son ta ya soki zuciyata, ya bi jijiyoyi ya mamaye dukkan jinin jikina.

Muka shiga zance da ita har na lura cewa barci ya soma cin ƙarfinta. Sai na tashi a hankali na duba daidai inda biri ya kwatanta mini, sai kuwa na ga ƙofar ɗaki kulle da kwaɗon tagulla. Na laluba daga ƙasan ƙofar na ɗauki mabuɗi na buɗe kwaɗon, na shiga cikin ɗakin. Na ga akwatin nan, na aikata kamar yadda biri ya bayyana mini duka.

Ina shirin fitowa daga cikin ɗakin kenan, sai na ga yarinya tsaye a bayana. Yayin da ta ga abin da na aikata, sai ta dafe kai ta fashe da kuka. Na ji tana cewa, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki. Babu shakka yau Maridi zai yi galaba a kaina."

Daga nan sai muka riƙa jin wata irin kururuwa mai ban tsoro, da rugugi mai ƙarfin gaske har ƙasan ɗakin da muke ciki na motsawa. Sai ga Maridi ya bayyana a cikin ɗakin, ya suri yarinya ya tashi sama da ita tana kuka.

Na yi tsaye kamar mutum-mutumi, ina tunanin abin da ya faru, ina zargin kaina bisa ga abin da na aikata. Ina nan tsaye sai ga Sharif ya shigo ɗakin da nake da sauri, yana kuka yana marin fuskarsa. Ya ce da ni, "Ya Abu Muhammad, me ya sa ka aikata wannan abu? Ka sani na aikata wannan sirri ne domin in tsare 'yata daga wannan mugun Maridi, la'ananne, wanda tun tsawon shekaru shida da suka wuce yake neman hanyar da zai sace ta daga gare ni. Amma bai yi nasara ba sai yau, babu amfanin zamanka cikin wannan gida, ka tafi ka bar mana gida."

Na fita cikin daren nan na nufi gidana, ina mai baƙin cikin abin da ya faru. Na nemi birin nan sama da ƙasa, amma ban gan shi ba. Sai na tabbata cewa lalle shi ne Maridin da ya sace mini amarya, watau da ma yaudara ta ya yi domin in ɓata sihirin da ya hana shi sace ta tsawon shekaru. Mai son abinka ya fi ka dabara!

Na zauna ina mai matuƙar nadama bisa ga abin da na aikata. Na riƙa marin fuskata don takaici. Haka na kasance har zuwa fitowar alfijir. Wata zuciya ta ce mini, "Menene amfanin zamanka a nan kana marin fuskarka? Tashi ka shiga duniya neman matarka."

Na fita daga cikin gidana, da sanyin safiya, na nufi bayan gari, amma ban san inda zan nufa ba. Na fita daga cikin gari, na shiga cikin daji, wanda ya kasance hamada ce, babu komai cikinta, daga rairayi sai rairayi. Na yi ta tafiya cikin rairayin nan har rana ta take ban tsaya ba. Na gaji tiɓis, ga kuma ƙishirwa ta soma koɗa ni, ba alamar ruwa gaba, ba alamarsa baya.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
13/05/2023
ARZIKI RIGAR ƘAYA (6)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Na fita daga cikin gidana, da sanyin safiya, na nufi bayan gari, amma ban san inda zan nufa ba. Na fita daga cikin gari, na shiga cikin daji, wanda ya kasance hamada ce, babu komai cikinta, daga rairayi sai rairayi. Na yi ta tafiya cikin rairayin nan har rana ta take ban tsaya ba. Na gaji tiɓis, ga kuma ƙishirwa ta soma koɗa ni, ba alamar ruwa gaba, ba alamarsa baya. Can da almuru, ina cikin tafiya ina jan ƙafafu, sai na ga waɗansu macizai guda biyu suna faɗa, ɗaya fari, ɗaya kuma rawaya. Sai na ga rawayan yana neman ya halaka farin. Na duƙa na ɗauki wani ƙaton dutse na kwantsama masa shi, nan take ya mutu.

Da farin macijin ya ga haka sai ya gudu. Zuwa can sai ga shi ya dawo tare da wasu macizan guda goma, dukkaninsu farare. Suka tafi wurin gawar wancan macijin, rawaya, suka yi mata kaca-kaca, sai kansa kawai suka bari. Daga nan suka koma inda suka fito. Ni kuwa saboda tsananin gajiya, da kuma wahala sai na faɗi durƙushe a kan gwiwowina. Ina nan durƙushe sai na ji wata murya mai daɗi tana waƙa, na waiga ko'ina amma ban ga kowa ba. Muryar ta ci gaba da waƙa tana cewa:

"Haka ƙaddarori kan taho gun taliki,
Yadda Jallah ya tsaro su ba mai kariya.

Allahu Rabbi yakan yi canjin lamari,
A cikin daƙiƙa ko a ƙibta idaniya."

Yayin da na ji waƙa amma ban ga mai yin ta ba, ya Shugaban Muminai, sai na tsorata matuƙar tsoro. Sai kuma na ji wata muryar daga bayana tana waƙa waɗannan baitoci:

"Yi farin ciki ya kai mutum ga agaji,
Da ka ɗauki Ƙur'ani yana maka nuniya.

Tsoro na shaiɗan ko mutum duka kar ka ji,
Domin kana bisa godabenmu na Anbiya."

Da na ji wannan waƙa sai na yi ƙarfin hali na ce, "Ina gama ka da Allah, Ubangijin talikai, waye kai?" Daga nan sai na ga mai waƙar ya bayyana a cikin siffar mutum namiji.

Ya ce mini, "Kada ka ji tsoro, labarin alherinka ya iske mu. Mu, muna daga cikin aljanun da suka bayar da gaskiya ga addinin Islama. Shin kai kana da wata buƙata da kake so mu biya maka?"

Na amsa masa, "Haƙiƙa ina da buƙata. Ina da matuƙar bukatar wani abu, domin kuwa musiba ta afka mini wacce da ɗai irinta ba ta taɓa afka wa wani ɗan Adam ba."

Sai na ji ya ce, "Ai kai ne Abu Muhammadu Kasala ko?" Bai jira na ba shi amsa ba, sai ya ci gaba da cewa, "Ya Abu Muhammadu, ni ɗan uwan farin macijin nan ne da ka taimaka, wanda ka kashe wa abokin faɗa. Mu huɗu muke 'yan uwan juna, ubanmu ɗaya uwarmu ɗaya. Dukkaninmu a halin yanzu kana da bashi a kanmu, wanda dole ne mu biya ka shi. Ka sani cewa birin nan da ya yaudare ka, maridi ne daga cikin kafuran aljanu. Ba domin ya yaudare ka ba har ka ɓata sihirin da Sharif ya yi, da babu yadda za a yi ya sace yarinyar nan. Domin ya daɗe yana neman hanyar da zai sace ta bai samu ba, sai da ya yi amfani da kai ka ɓata sihirin. Amma kada ka damu, za mu taimake ka, ka kashe shi ka kuma taho da matarka, domin alherin da ka aikata wa ɗan uwanmu."

Daga nan sai ya ɗaga kansa sama, ya yi wata irin ƙara da kururuwa mai ƙarfi. Yana rufe bakinsa sai ga gungun wasu aljanu sun bayyana a gabansa. Ya tambaye su labarin maridin da ya sace mini mata, sai ɗaya daga cikinsu ya ce, "Na san inda yake, yana can ƙarshen duniya a Birnin Tagulla, birnin da rana ke faɗuwa."

Sai aljanin nan na farko ya dube ni ya ce, "Ya Abu Muhammadu, ka tafi tare da wannan aljani, zai ɗauke ka bisa bayansa, ya kai ka har cikin Birnin Tagulla. Zai gaya maka sharuɗɗan da za ka bi duka, ka kashe maridi ka dawo da matarka. Sai dai ka kula, wannan aljani da zai ɗauke ka ba musulmi ba ne, don haka kada ka furta sunan Allah yayin da kake bisa bayansa. Idan kuwa ka ambaci sunan Allah kana bisa gare shi, to, zai jefar da kai ne, wanda hakan zai iya sanadin halakarka."

Na ce masa, na ji na yarda. Ya kira ɗaya daga cikin aljanun ya ce masa ya ɗauke ni ga bayansa ya tafi da ni zuwa Birnin Tagulla. Aljani ya matso kusa gare ni, ya duƙa ya ce, "Hau."

Na yi tsalle na haye bisa bayansa, ya kaɗa fukafukansa ya tashi da ni sama. Ya yi ta tashi da ni sama har na daina ganin ƙasa, duniyar ta koma mini tamkar hayaƙi. Muka yi kusa ga taurari, na gan su manya-manya tamkar tsaunuka. Na jiyo wasu muryoyi daga sama suna tsarkake sunan Ubangiji, shi kuwa aljanin nan sai ya takale ni da hira domin kada in kira sunan Allah.

Muna cikin tashi cikin iska sai na ga wani ɗan ƙaramin aljani cikin tsanwar tufafi, gashin kansa mai tsawo har bisa ga duga-dugan kafafunsa, iska na kwasar shi. Yana riƙe da wani mashi mai tsinin gaske, tsinin mashin kuma yana fitar da wuta.

Aljanin nan ya matso kusa ga kunnena, ya ce, "Ya Abu Muhammadu, ka ce babu sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. Idan ba haka ba zan soke ka da wannan mashi."

Yayin da na ji haka, da ma duk na gaji da rashin kiran sunan Allah da ban yi ba, sai na ce, "Na shaida babu sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne."

Ina faɗin haka sai aljanin nan mai tsanwar tufafi ya juya wurin aljanin da yake ɗauke da ni ya ce masa, "ka ce babu sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. Idan ba haka ba zan soke ka da wannan mashi."

Aljani ya ce, "Faufau!"

Nan take aljanin nan ya soke shi da mashi. Aljani ya kama da wuta, ya ƙone ƙurmus, ya zama toka. Ni kuwa na sulmiyo daga bayansa na yiwo ƙasa. Na rufe idanuna ina ta salati, ina kuma jiran in ji yadda ƙasusuwana za su ragwargwaje idan na faɗo ƙasa. Allah da ikonsa sai na faɗa cikin ruwan teku ƙundum, kamar an jefo dutse. Ashe kuma kusa ga wasu masu jirgi su biyar na faɗo. Suna gani na sai suka jawo ni, suka saka ni a cikin jirginsu.

Suka tarairaye ni har hankalina ya dawo jikina, sa'annan suka yi ta yi mini magana da wani irin harshe wanda ba na fahimta. Na yi musu alama cewa ba na fahimtar abin da suke cewa.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
17/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (7)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Suka yi ta yi mini magana da wani harshe wanda ba na fahimta. Na yi musu alama cewa ba na fahimtar abin da suke cewa. Suka ƙyale ni, muka yi ta tafiya cikin jirgi har kusan ƙarshen rana. Suka jefa komarsu a cikin ruwa suka kamo ƙaton kifi, suka gasa shi, suka ba ni na ci na ƙoshi. Haka muka yi ta tafiya har muka isa birninsu.

Suka kai ni ga Sarkinsu, wanda na fahimci yana gane harshena na Larabci. Na sumbaci ƙasa gabansa, na gaishe shi da ladabi. Ya kawo tufafi na alfarma ya ba ni, ya naɗa ni ɗaya daga cikin fadawansa. Na tambayi Sarki sunan wannan birni, ya ce mini sunansa Hannadu, yana daga cikin yankin ƙasar Sin. Ya hada ni da Wazirinsa domin ya nuna mini gari.

Muka zagaya da Waziri ko'ina cikin gari, ya gaya mini cewa, al'ummar farko da ta zauna wannan birni ba musulmi ba ne, sun kasance masu bautar wuta, don haka Allah ya yi fushi da su, ya mayar da su duwatsu. Na zauna a wannan birni tsawon wata guda, ban taɓa ganin wani birni mai yawan bishiyoyi da 'ya'yan itace ba kamar wannan birni.

Wata rana ina zaune a bakin teku ina shan iska, sai ga wani mutum ya zo wurina bisa ingarman doki. Ya dube ni ya ce, "Ba kai ne Abu Muhammad Kasala ba?"

Na amsa masa, "Ni ne."

Ya ce, "Kada ka ji tsoro, labarin alherinka ya iske mu."

Na tambaye shi, "Wane ne kai?"

Ya ce mini, "Ni ɗan uwan farin macijin nan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

1 Comments On HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA
avatar
musa-abdul

6 days ago

Reply

Littafin yanada matular dadi sosai

Please Login or Register in order to submit comment