Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne da ka taimaka. Da sannu za mu saka maka da alherin da ka aikata mana." Ya cire rigarsa ɗaya ya ba ni, ya ce, "Karɓi wannan riga ka sanya, kada ka ji tsoron kome. Aljanin da ya ƙone tare da kai bawanmu ne. Tashi mu tafi yanzu in kai ka Birnin Tagulla."

Na karɓi taguwa na saka, ya aza ni bisa kuturin dokinsa, ya sukwane shi, muka tafi kamar iska. Cikin dan ƙanƙanin lokaci sai na gan mu a cikin rairayin hamada. Aljani ya ja linzamin doki ya tsaya, ya ce mini in sauka. Bayan na sauka sai ya nuna mini wasu tsaunuka guda biyu can daga nesa. Ya ce, "Ka tafi zuwa ga waɗancan tsaunuka, za ka ga hanya a tsakaninsu. Ka shiga ta wannan hanyar za ka hangi Birnin Tagulla a gabanka. Ka jira a wurin, kada ka shiga cikin birnin sai na zo na sanar da kai ƙa'idojin da za ka bi."

Na ce, "To."

Na kama hanya na nufi tsaunukan nan, na ga hanya ta bi ta tsakaninsu, na bi ta. Ina shigewa ta hanyar sai na hangi katangar birnin wadda aka gina da tagulla. Na je gun katangar na yi ta zagaya ta amma ban ga ƙofar shiga ba. Daga nan sai ga aljanin nan ɗan uwan maciji ya zo wurina, yana riƙe da wata takobi ta zinariya, an zane dukkan jikinta da ɗalamusai. Ya miƙa mini takobi ya ce idan ina rike da ita babu mahaluƙin da zai cuce ni. Ya yi mini fatar samun nasara, sai ya ɓace.

Aljanin nan bai daɗe da tafiya ba, sai na riƙa jin hayaniya da hargowa. Ban ankara ba sai na gan ni a tsakiyar wasu aljanu masu ɗan ƙaramin kai kamar ƙodago, da idanunsu a kan kirji. Suka tambaye ni, wanene ni? Na kwashe labarina na gaya musu. Sai suka ce mini, "Yarinyar da kake nema tana cikin wannan birni tare da maridi, amma ba mu san abin da ya yi mata ba. Mu kuma 'yan uwan farin maciji ne, wanda ka taimaka."

Suka nuna mini wata ƙorama wadda ruwanta ke gudu, suka ce, "Ka bi ruwan waccan ƙoramar, za ka ga hanyar da ruwan ke shiga cikin birni, ka bi ta wannan hanyar ka shiga cikin birnin."

Na tafi ga ƙorama, na riƙa bin ruwanta har na iso ga wani rami inda ruwan ke shiga, na shiga cikin ramin, na bi tsawonsa, sai ga ni a tsakiyar birni, a cikin lambu. Na ga yarinyar zaune bisa wani gado na alfarma wanda aka yi da zinariya ƙarƙashin wata laima. Dukkan itatuwan da ke cikin wannan lambu na zinariya ne, 'ya'yansu kuma nau'i-nau'i ne na ma'adinai. Wasu da 'ya'yan lu'ulu'u, wasu da na azurfa, wasu da na jauhari.

Yayin da yarinya ta gan ni, sai ta yi ajiyar zuciya, ta gaishe ni da harshe mai daɗi, ta ce, "Ya shhugabana, yaya aka yi ka shigo wannan birni?"

Na gaya mata dukkan abin da ya faru. Ta ce mini, "Ka sani ya shugabana, saboda tsananin son da wannan maridi ke yi mini, ya kwashe dukkan sirrinsa ya faɗa mini. Domin yana ganin babu wani mahaluki da zai iya shigowa wannan birni, balle in gan shi har in faɗa masa wannan sirri."

Ta ci gaba da cewa, "Ya gaya mini cewa, akwai wani sihiri wanda duk ya mallake shi zai iya lalata wannan birni. Sihirin na a jikin wani ungulu na baƙin ƙarfe, wanda yake ajiye a cikin wancan gidan." Ta nuna mini gidan. Ta ci gaba da cewa, "wanda duk ya mallaki wannan tsuntsu, to, dukkan ifiritai za su zama masu biyayya ga umurninsa. Maza ka tafi ka ɗauki wannan ungulu, ka turara shi da miski a cikin tasa. Za ka ga hayaƙi na tsahi, da zarar hayaƙi ya tashi dukkan ifiritai za su taho zuwa gare ka, babu ɗayansu da zai yi saura bai zo ba. Idan suka haɗu sai ka umurce su da dukkan abin da kake so su yi maka, nan take za su aikata shi. Tashi maza ka tafi da yardar Ubangiji Maɗaukakin Sarki."

Na amsa mata, "Na ji, na karɓa."

Nan take na zabura na nufi gidan nan da ta nuna mini, na shiga cikinsa na tarar da tsuntsun nan na baƙin ƙarfe. Na aikata kamar yadda yarinya ta ce, yayin da hayaƙi ya tashi, sai ga aljanu sun hadu, kamar fari don yawansu. Suka ɗauka gaba ɗaya, "Mun amsa kira ya shugabanmu. Me kake so mu yi maka?"

Na ce musu, "Ku ɗauro mini maridin da ya sace mini mata ya kawo ta wannan birni."

Suka ce, "An gama."

Nan take sai duk suka ɓace. Jim kaɗan sai suka dawo suka ce mini sun cika aiki, na sallame su. Na tafi wurin matata na gaya mata abin da ake ciki. Na tambaye ta, ko za ta bi ni mu koma kasarmu? Ta ce idan ta zauna nan ta yi me. Na ɗauke ta muka fice daga cikin birnin ta hanyar da na shigo. Muna fitowa sai na ga aljanun nan masu ɗan ƙaramin kai, waɗanda suka nuna mini hanyar shiga birnin.

Na tambaye su, ya ya za a yi mu koma ƙasarmu. Suka yi mana jagora har muka zo bakin teku, suka saka mu cikin jirgi.

Jirgi ya yi ta tafiya da mu cikin kyakkyawan yanayi, kwanci tashi muka iso Birnin Basara. Na tafi da matata wurin mahaifinta. Yayin da 'yan uwanta suka gan ta, sai suka yi farain ciki, farin ciki mai yawa. Na zaro sihirtaccen tsuntsun nan, na turara shi da miski, nan take sai ga aljanu sun bayyana. Suka ka ce, Ga mu! Faɗi buƙatarka, yanzu mu biya maka ita."

Na ce musu su kwaso mini dukkan dukiyar da ke cikin Birnin Tagulla, ta zinariya, da azurfa, da jauhari, da lu'ulu'u, da duk wani abu mai amfani, su kai mini shi a cikin gidana. Cikin ƙibtawar ido suka kwashe komai na birnin suka jibge a gidana, ko allura ba su baro ba. Na ce su kawo mini maridin nan da suka ɗaure.

Da suka kawo shi gabana, na ce, "Ya la'ananne, me ya sa ka yaudare ni?" Na umurci aljanu su ɗaure shi a cikin battar tagulla. Suka ƙudundune shi a cikin ƙuƙuma, na kawo darma na liƙe bakin battar, na sa aljanu suka ɗauke ta suka jefa cikin bahar. Muka zauna ni da matata cikin jin daɗi da farin ciki.

Ya Halifa, ka ji yadda na tara dukiya, wadda ni kaina ban san adadinta ba, tana nan jibge a cikin gidana da ke Basara. Wannan kuma ba dabara ta ba ce ko wayo, sai dai kyauta daga Mai duka, wanda ke arzuta bawa ta inda ba ya zato. Yanzu haka idan kana da bukar kudi ko wani abu daban, ko menene, sai in sa aljanu su kawo maka shi cikin ƙibtawar ido.

Yayin da Halifa ya ji wannan labari na Abu Muhammad Kasala, ya cika da mamaki, matuƙar mamaki. Ya ce a ransa, "Haƙiƙa arziki rigar ƙaya ne, kowa da inda yake ɗebo nasa!"

Halifa ya yi masa kyauta ta alfarma, maimakon tsarabar da ya zo masa da ita. Ya karrama shi matuƙar karramawa, sa'annan ya sallame shi, ya koma birnin Basara.

Wannan shi ne abin da ya zo mana, na daga hikayar Abu Muhammadu Kasala. Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki.

ƘARSHE.

Za mu kawo muku wata sabuwar hikayar mai ban mamaki, idan Allah ya kai mu ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
20/05/2023
This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

1 Comments On HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA
avatar
musa-abdul

6 days ago

Reply

Littafin yanada matular dadi sosai

Please Login or Register in order to submit comment