Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
WANNAN TSOHUWA' AJIYACE MUNTABA KAWO MUKU

HIKAYAR TAJIRI DA IFIRITU 1

A zamanin da, a wani babban gari, an yi wani babban attajiri, mai yawan dukiya, mai yawan tausayi da taimakon talakawa.
Wata rana attajirin nan ya fita bayan gari yawo shi kadai domin shan iska, sai ya tsaya domin ya huta a karkashin wata itaciya mai sanyin inuwa. Ya fito da gurasa da dabino da ruwa daga cikin jakarsa, domin ya ci ya kuma sha ruwan kafin ya wuce gaba.
Bayan ya gama cin gurasa sai ya dauko dabino yana ci. Yana cikin cin dabinon nan sai ga wani Ifiritu (aljani), mai girman jiki, tamkar itaciyar kuka, mai tsayin gaske, tamkar itaciyar rimi, da jajayen idanu, tamkar garwashin wuta. Ya fito rike da takobi a hannunsa, ya ce da wannan attajiri, tashi in kashe ka tamkar yadda ka kashe dana.
Tajiri ya ce, “Ta yaya na kashe danka?”
Ifiritu ya ce, “Yayin da ka ci dabino ka yi jifa da kwallon ya sami dana a kirji har ya fadi ya mutu. Babu makawa yanzu in dau fansa, in kashe ka tamkar da ka kashe shi.”
Tajiri ya ce, “Ka sani ya kai wannan Ifiritu akwai bashi mai yawa a kaina. Ka bar ni in tafi gida, tsawon shekara guda, in bai wa dukkan mai hakki hakkinsa, sannan in komo nan ka aikata abin da ka yi nufi a kaina, za ka same ni mai cika alkawari, haka Allah ya kaddara.”
Ifiritu ya yarda da bukata tasa.
Tajiri ya komo gida, ya fada wa iyalansa da danginsa da abokansa dukkan abinda ya faru da shi, suka yi ta kuka, kuma ya biya dukkan mai bin sa bashi hakkinsa. Bayan shekara guda ya koma inda suka hadu da Ifiritun nan ya zauna yana jiran fitowarsa.
Yana nan zaune yana jiran abinda zai same shi, sai ga wani tsoho tafe, ya na jaye da barewa, da igiya a wuyanta. Ko da tsohon nan ya iso wurin tajirin nan sai ya ce masa, “Bawan Allah, me ya zaunar da kai wannan wuri? Hala ba ka san cewa wannan wuri matattarar aljanu ba ne?”
Tajiri ya kwashe labarinsa da Ifiritu ya fada wa tsoho. Tsoho ya ce, hakika labarinka akwai ban al’ajibi da tausayi a cikinsa. Lalle ba zan bar nan ba sai na ga abinda zai kasance a gare ka. Ya sami wuri ya zauna.
Suna nan zaune, sai ga wani tsoho tafe ya na jaye da karnuka, bakake guda biyu. Tsoho mai karnuka ya yi sallama gare su. Bayan sun gaisa, ya tambaye su labarin zamansu wannan wuri wanda ya ke matattarar aljanu. Suka fada masa abinda ya ke faruwa. Da ya ji haka sai ya ce, lalle ba zan wuce ba har sai na ga abinda zai faru tsakanin Tajirin nan da Ifiritu. Ya sami wuri ya zauna.
Tsohon nan mai karnuka bai gama zaunawa ba, sai kuma ga wani tsoho tafe akan wata alfadara ramammiya. Da tsoho mai alfadara ya iso ya yi musu sallama, suka gaisa sannan ya tambaye su dalilin zamansu a wannan bigire. Suka labarta masa abinda ke faruwa. Shi ma ya ce ba zai wuce ba sai ya ga karshen wannan al’amari. Ya sami wuri ya zauna.
Tajiri da tsofaffi na nan zaune sai suka rika jin wata irin hargowa, mai cike da rugugi da tsawa da iska mai tsanani tana kadawa, kasa kuwa kamar za ta tsage saboda rugugi da kugi. Kura ta tashi ta murtuke ko’ina, ta rufe hasken rana, ba a ganin komai tamkar a tsakiyar dare.
Yayin da hargowar nan ta lafa, kura ta yaye wuri ya koma dai dai, sai mutanen nan suka ga Ifiritu a tsaye da takobi zararre a hannunsa, idanunsa ja wur tamkar garwashin wuta. Ya fizgo Tajirin nan daga cikinsu ya ce, tashi in kashe ka tamkar yadda ka kashe dana, sanyin zuciyata, farin cikin rayuwata.
Tajiri yana kuka yana kururuwa da hargowa, tsofaffin nan su ma suka fashe da kuka domin tausayin Tajiri. Sai tsohon nan na farko, mai barewa ya matso kusa da Ifiritu, ya durkusa ya ce, “Ya kai wannan Ifiritu, Sarkin Sarakunan aljanu, da za ka tsaya in ba ka labarina da wannan barewa da nake tare da ita, da ka ji labarin abin al’ajabi wanda ba ka taba jin irinsa ba, amma sai idan ka yi alkawarin za ka ba ni wani yanki na jinin wannan Tajiri.”
Ifiritu ya ce, “Na yarda idan ka ba ni wannan labari na ga ya kasance abin al’ajabi da mamaki zan ba ka sulusin jinin wannan mutum.”
Tsoho mai barewa ya yi godiya ya fara ba Ifiritu da sauran mutanen da ke wurin labarinsa, da abin da ya kasance a gare shi tare da wannan barewa, kamar haka:

Labarin Tsoho Na Farko Mai Barewa:
Tsoho na farko, mai barewa ya ce, ka sani ya kai wannan ifiritu, cewa wannan barewa ta kasance ‘yar baffana ce, na aure ta tun tana karama. Mun zauna tsawon shekara talatin da ita amma Allah bai ba mu haihuwa ba. Sai na sayi kuyanga, na mayar da ita sa-daka, Allah kuwa ya sa na haifi da namiji tare da ita. Yaron nan ya kasance kyakkyawa, mai kyawun sura abin so da kauna ga kowa.
Bayan yaron nan ya kai shekara goma sha biyar, sai tafiya ta kama ni zuwa wani birni daga cikin birane. Na debi guzuri na dukiya mai yawa domin ban san iyakar kwanakin da zan yi ba a wannan tafiya. Na tafi, na bar dana da uwarsa, da kuma matata, yar baffana a gida.
Wannan mata tawa, wadda ita ce wannan barewa da kake gani, ya kai wannan ifiritu, ta kasance masaniya akan bokanci da sihiri kala-kala tun tana ‘yar karama.

Gobe damu daura insha allahu
Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ02 HIKAYAN TAJIRI DA IFRITU

Labarin Tsoho Na Farko Mai Barewa

Wannan mata tawa, wadda ita ce wannan barewa da kake gani, ya kai wannan ifiritu, ta kasance masaniya akan bokanci da sihiri kala-kala tun tana ‘yar karama. Don haka bayan tafiyata sai ta sihirce yarona ta mayar da shi bajinin sa, uwarsa kuma ta mayar da ita saniya, ta aika da su wurin mai yi mini kiwon dabbobina a daji, aka saka su a cikin garken shanu.

Bayan wani tsawon lokaci na dawo daga tafiyar da na yi, sai ban ga dana da uwarsa ba, na tambayi matata inda su ke. Sai ta ce da ni, ai bayan tafiyarka, kuyangarka ta mutu, danka ya gudu ban san inda ya tafi ba. Wannan labari ya sa ni cikin bakin ciki da kunar zuciya har tsawon shekara guda.

Lokacin da sallar layya ta zo, sai na aika wa makiyayina da ke kauye da ya aiko mini da saniya mai kiba kuma mai maiko domin in yi layya da ita. Wannan mata tawa sai da ta san yadda ta yi dabarar da ta sa makiyayin nan ya aiko mini da sihirtattar saniyar nan, watau kuyangata, uwar dana, a matsayin saniyar da zan yanka.
Da aka kawo saniyar, na tashi na cire rigata, na dauki wuka, bayan an kayar da ita an daure kafafunta, na nufe ta da niyyar in yanka ta domin yin layya. Sai ta rika kuka da harbe-harbe, kamar za ta yi mini magana, amma babu baki. Sai tausayi ya kama ni, na ba wani yaron gidana wukar na ce ya yanka mini ita, ni kuwa na koma cikin daki.

Bayan an yanka saniyar nan, wadda ta kasance kuyangata ce aka sihirce, da aka fede ta sai aka tarar ba ta da nama da mai sosai, daga fata sai kasusuwa, ni kuwa niyyata in yi layya da dabba mai nama da mai da yawa. Ganin haka sai na sake aika wa makiyayin nan da ya kawo mini wani bajini mai nama da mai sosai. Matar nan tawa kuma ta sa aka kawo mini dan nan nawa da ta sihirce shi ya zama sa.

Yayin da aka zo da shi, yana gani na, sai ya tsinke igiyar da aka dauro shi da ita, ya rugo zuwa gare ni, ya yi kwance a gabana, kuma ya tashi yana kuki yana kuka, yana kewaya ni. Tausayinsa ya kama ni. Na ce, a mayar da shi a zo mini da saniya mai kiba da mai. Amma matata kuwa sai ta ce, ka yanka wannan sa domin yana da kiba kuma yana da mai sosai. Allah ya sa ban biye shawararta ba, domin tausayin shi ya riga ya kama ni. Aka mayar da shi.
Bayan kwana biyu, ina zaune, sai ga makiyayin nan nawa ya zo wurina, ya ce, ya shugabana, na zo ne in fada maka abin farin ciki da albishir. Na ce da shi, na’am, ina saurarenka.

Makiyayi ya ce mini, ya kai maigidana, na kasance ina da wata ‘ya tawa masaniyar sihiri, tun tana karama ta ke a hannun wata tsohuwa, kakarta, wadda ita ce ta koya mata sihiri. Jiya bayan na koma da bajinin san nan da ba ka yanka ba, sai na tarar da ‘yar nan tawa ta zo gida domin bukin Salla.

Yayin da na shiga da sa gida, ko da ‘yar nan tawa ta gan shi, sai ta rufe jikinta ta ce mini, ya babana, ta yaya za ka shigo mana da namiji, baligi, cikin gida? Bayan kuwa shi ba muharraminmu ba ne? Sai ta fashe da kuka. Na ce da ita, ina namijin da na shigo muku da shi? Sai ta daina kuka, sai kuma na ga tana dariya. Sai na tambayeta, me ya sa ki kuka? Me ya sa kuma yanzu kike dariya?
Ta ce dani, wannan bajinin da kake tare da shi, dan shugabanmu ne, Tajiri, amma an sihirce shi ne,

shi da mahaifiyarsa, kuma matar ubansa ce ta sihirce su. Amma abin da ya sa ni kuka shi ne, mahaifinsa ya sa an yanka uwarsa bai sani ba. Amma abin da ya sa ni dariya shi ne, zan iya kubutar da shi na mayar da shi ga siffarsa ta mutum, amma sai na yi sharadi da mahaifinsa.

Makiyayi ya ci gaba da fada mini cewa, na yi al’ajabi gayar al’ajabi, ban yi barci ba har hudowar asuba, domin na zo na sanar da kai wannan labari, ya shugabana.
Yayin da na ji wannan zance na makiyayina, ya kai wannan ifiritu, sai na ce da shi ya tashi maza mu tafi gidansa domin na ji sharadin da yarsa take so kafin ta mayar mini da dana siffarsa ta mutum.
Da muka iso, ‘yar makiyayi ta tare mu da murna, ta gaishe ni cikin ladabi da girmamawa. Da dan nan nawa ya gan ni sai ya taso ya zo ya kwanta a gabana. Na ce da ‘yar makiyayi, shin labarin da mahaifinki ya gaya mini ko gaskiya ne. Ta ce, na’am ya shugabana. Wannan bajimi da kake gani danka ne.

Na ce da ita, idan kika kubutar da shi zan ba ki dukkan dukiyata da ta ke hannun mahaifinki. Sai ta yi murmushi, ta ce, ka sani ya shugabana, ba ni da kwadayi akan dukiyarka, zan kubutar da danka amma akan sharudda guda biyu: Na farko, ka yarda na auri wannan da naka, na biyu ka barni in sihirce wadda ta sihirce danka da kuyangarka, ni ma in daureta cikin sihiri tsawon rayuwarta. Idan ka yarda da wadan nan sharudda, yanzu zan mayar wa danka da siffarsa.

Na ce, na amince da wadan nan sharudda, kuma na kara maki da dukiyar da ke hannun mahaifinki, ‘yar baffana kuwa, watau matata, kiyi duk abin da kika ga dama da ita.
Yayin da ta ji zancena ta dauki tasa, ta cika da ruwa, sannan ta yi wasu karance-karance ta tofa a cikin ruwan nan, sannan ta yayyafa wa bajinin san nan, ta ce, idan Allah ya halicce ka, ka kasance bajini, to kaci gabada zama bajini,

daga magana jari.. Yusuf a jibaga03. HIKAYAR TAJIRI DA IFIRITU:

Labarin Tsoho Na Biyu Mai Karnuka.

sannan ta yayyafa wa bajinin san nan, ta ce, idan Allah ya halicce ka, ka kasance bajini, to kaci gaba da zama bajini, idan Allah ya sa sihirce ka aka yi, ka juya ga siffarka ta asali, da yardar Allah madaukakin Sarki. Nan take sai ya juye ya koma mutum, kamarsa ta asali. Na aura masa ‘yar makiyayin nan, ita kuma ce ta sihirce ‘yar baffan nan tawa zuwa wannan barewa da kake gani, ya kai wannan ifiritu.
Idan wannan labari nawa ya kasance mai ban al’ajabi a gareka ina son ka bani sulusin jinin wannan Tajiri da ya kashe danka ba tare da ya sani ba.
Ifiritu ya ce, hakika wannan labari akwai abin al’ajabi a cikinsa, don haka na baka sulusin jinin wannan mutum.
Daga nan sai tsoho na biyu mai karnuka ya matso wurin Ifiritu, ya ce ni ma ina da labarin da zan baka akan wadan nan karnuka da kake gani, amma sai idan za ka ba ni sulusin jinin wanan mutum. Ifiritu ya ce, fadi labarinka mu ji. Tshoho mai karnuka ya fara labarinsa kamar haka:

Tsoho na biyu ma’abocin karnuka ya matso kusa da ifiritu ya fara bayar da labarinsa, ya ce, ka sani ya kai shugaban sarakunan aljanu, wadan nan karnuka biyu ‘yan uwana ne, ni ne na ukunsu. Mahaifinmu ya mutu ya bar mana gadon dinari dubu uku. Da aka raba wadan nan kudi aka ba wa kowa nasa, sai ni na bude rumfa a kasuwa ina ciniki a cikinta, ina saye ina sayarwa. Yan uwana kuwa suka tafi fatauci.
Bayan shekara guda, sai yan uwan nan nawa suka komo daga fatauci, babu komai tare da su na daga dukiya, duk sun salwantar da ita. Na ce da su, “Ya ‘yan uwana ashe dama ba sai da na ba ku shawarar kada ku tafi fataucin nan ba?” Su ka ce da ni, “Ya dan uwanmu ashe baka yarda da kaddarar Allah mai girma da daukaka da ya yi nufi akan mu ba?”

Na karbe su. Na rike su, na tafi da su gidana, na ba su abinci da sutura mai yawa, sannan na tafi da su zuwa ga rumfata ta kasuwa na ce da su na yarda su zauna mu yi kasuwanci tare da su, duk ribar da aka samu a raba ta uku dai dai, kowa ya dauki kashi daya.
Mu ka zauna akan haka har zuwa wani zamani mai tsawo. Sai wata rana ‘yan uwan nan nawa suka ce suna so za su koma fatauci tunda yanzu sun sami nasu jari, suka kwadaitar da ni akan mu tafi tare domin an fi samun riba mai yawa a fatauci. Na ki amincewa da in bar rumfata saboda na san ina samun riba sosai a cikinta.

‘Yan uwan nan nawa ba su gushe ba suna kwadaitar da ni akan zuwa fatauci har tsawon wasu shekaru. Daga karshe dai suka shawo kaina na amince da za mu tafi tare da su. Muka kidaya kudin da ke gare mu, muka ga muna da dinari dubu shida. Na ba da shawarar mu raba kudin nan biyu, mu bisne rabi a kasa mu tafi da rabi, koda tafiya ba ta yi kyau ba, idan mun dawo muna da jarin da za mu ci gaba da kasuwancinmu. Suka aminta da wannan shawara tawa.

Muka raba kudin biyu, muka bisne dinari dubu uku a kasa, sannan kowannen mu ya rike dinari dubu daya. Muka sayi kaya, muka gama ciko, muka biya kudin jirgi, muka haura cikin bahar maliya. Sai da muka yi wata daya muna tafiya a cikin jirgi, har Allah ya kai mu wani babban birni.
Bayan mun sauke kayan mu, muka shiga cikin birnin nan, muka fara ciniki, Allah kuwa ya sa wa kayan nan namu albarka, muka sayar da su duka. Muka ci riba har sai da kowane dinari ya koma dinari goma. Bayan mun huta a wannan birni tsawon wani dan lokaci kadan, sai muka yi niyyar komawa gida. Muka hada kudinmu, muka nufi bakin bahar maliya domin hawa jirgi.

Muna zuwa bakin gacin bahar maliya, sai muka iske wata yarinya wadda aka halicceta kyakkyawar halitta. Tana ganin mu, ta gaishe mu da ladabi, ta dube ni ta ce, “Ya shugabana, ko za ka yi mini wata alfarma guda daya, ni kuma in saka maka da wani abu dabam?” Na ce da ita, “Na’am, fadi bukatarki, zan yi miki koda kuwa ba za ki saka mini da komai ba.”

Yarinyar nan ta ce, “Ya shugabana, alfarmar da nake nema a wurinka ita ce, ina so ka aureni, ka tafi da ni garinku, ka aikata duk yadda ka so da ni a matsayin matarka. Hakika idan ka biya mini da wannan bukata, to ka yi mini alheri mai girma wanda ba zan manta da shi ba, sannan ni kuma zan saka maka da alherin da ya fi wanda ka yi mini.”
Yayin da na ji zancen wannan kyakkyawar yarinya, sai na ji tausayinta a zuciyata, na yarda da bukatarta. Na yi mata shimfida mai kyau ta alfarma a cikin jirgin da muka shiga. Na yi mata karimci na martaba ta. Yayin nan jirginmu ya mika cikin bahar maliya.

Zuciyata fa ta so yarinyar nan, so mai tsanani, na zamana ba ni rabuwa da ita dare da rana. Na shagala da ita ga barin yan uwana. Ashe duk kishi ya kama su ban sani ba. Kuma dama can ashe suna yi mini hassada game da yawan dukiyata da kayana. Kuma wannan tafiyar ma da muka yi ashe duk cikin shiri ne na su hallakani su kwashe dukiyata, Shedan ya rigaya ya yi musu huduba.

Sai da suka bari dare ya yi, kowa ya yi bacci a cikin jirgin nan, sai yan uwan nan nawa suka dauke mu, ni da matata, suka jefa cikin bahar maliya. Su na jefa mu sai na farka, matata kuwa sai na ga ta juye ta zama aljana,04. HIKAYAR TAJIRI DA IFIRITU:

Labarin Tsoho Na Uku Mai Alfadara.

Suna jefa mu sai na farka, matata kuwa sai na ga ta juye ta zama aljana,ta dauke ni ta yi sama da ni, ta kai ni kan wani tsibiri ta ajiye ni. Sai ta juya ta nufi inda jirginmu yake.

Dagari ya waye sai ga aljanar nan tadawo wurina ta ce, “Ni ce matarka. Tun lokacin da na gan ka tareda wadan nan yan uwa naka, nayi dubi izuwa zuciyarsu na gani cewa su sun zo da kai wannan fatauci ne domin su halaka ka, na kumayi dubi izuwa zuciyarka na ga kai mutumin kirki ne, kana tare da su ne tsakanink da Allah. Domin na kubutar da kai, shi ya sa na rikida kyakkyawar budurwa na nemi da ka aure ni domin in taimakeka. Amma yan uwanka sun cuceka, na yi fushi da su, babu makawa yanzu in kashe su.”
Yayin da na ji haka, sai na yi al’ajabi akan wannan al’amari, sannan na yi ta rarrashin ta ina ba ta hakuri a kan kada ta kashe mini yan uwa. Na gaya mata labarin yadda nake da su duka. Ta ce lalle ba makawa sai ta dulmiyad da su cikin ruwa tamkar yadda suka yi niyyar yi mana.

Na ce idan ta aikata haka hakika ta cuce ni domin yan uwana ne, sannan na tuna mata akan farkon haduwarmu da alkawrin da ta yi na saka mini da alherin da na yi mata. Da ta ji haka, sai ta dauke ni ta yi sama da ni, ba ta ajiye ni ba sai tsakiyar gidana a garinmu. Na je wurin da muka bisne kudin nan na tone su na dauka. Na je kasuwa na karbi rumfata ga wanda na ba wa haya da niyyar washe gari in koma ga kasuwanci na.

Dadare ina shiga gida sai na tarad da wadan nan karnuka guda biyu adaure cikin sarka. Su na gani na sai suka fara kuka suna kewaya ni, niban sani ba. Sannan sai ga matar nan tawa ta bayyana. Ta ce, “Wadan nan yan uwanka ne.” Na tambaye ta wane ne ya aikata haka gare su? Ta ce da ni ita ce ta aika da su wajen yar uwarta ta mayar dasu haka, ba za su koma ga siffarsu ta asali ba sai bayan shekara goma. Wannan shine hukuncin laifin da suka aikata maka.

Tsoho mai karnuka ya ci gaba da ba wa ifiritu da sauran mutanen nan labarinsa. Ya ce, ya kai ifiritu, shugaban sarakunan aljanun duniya, yau shekara goma ke nan da faruwar wannan abu, yanzu haka ina kan hanyata ta zuwa wajen yar uwar matata da wadan nan karnuka domin mayar da su ga siffarsu ta asali, sai na ga wannan mutum zaune da wannan tsoho mai barewa, na tambayi labarin zamansu nan, suka gaya mini. Wannan shi ne labarina da wadannan karnuka. Idan wannan labari ya zama abin al’ajabi a wurinka, ina so ka ba ni sulusin jinin wannan Tajiri da ya kashe danka.

Ifiritu ya yi mamaki da wannan labari matukar mamaki. Ya ce hakika wannan labari naka abin rubutawa ne a ajiye shi domin mutane su dinga karantawa har zuwa karshen lokaci. Na ba ka sulusin jinin wannan mutum.
Sai tsoho mai alfadara ya matso ya ce, ya kai shugaban aljanu, hakika labarina duk ya fi na saura banmamaki da al’ajabi, amma ba zangaya maka ba sai idan ka yi alkawarin za ka ba ni sulusin jinin wannan mutum. Ifiritu ya amince. Tsoho mai alfadara ya fara bayar da labarinsa mai cike da ban al’ajabi da kuma mamaki, kamar haka

Tsoho na uku mai alfadara ya gabata zuwa ga ifiritu ya fara labarta wa Ifiritu hikayarsa, ya ce, ya sarkin aljanu, babbar tutar aljanu, ka sani cewa wannan alfadara da kake gani matata ce. Watarana na yi tafiya zuwa fatauci, na bar matata a gida har tsawon shekara guda ban dawo ba. Ran nan sai Allah ya yi dawowata gida. Ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment