Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yin da na iso garinmu a cikin dare, sai na nufi gidana. Ina shiga dakina sai na sami matata kwance da wani bakin mutum a kan shimfidata, suna zance suna raha da dariya tare da sumbatar juna.
Yayinda taga nayi tsaye ina kallonsu cike da mamakin wannan abu da na gani, na daga cin amana, sai ta yi sauri ta tashi ta dauko wani ruwa a cikin kasko, ta yi wani zance na sihiri a cikin ruwan, sannan ta watsa mini shi a jiki ta ce, juye daga siffarka ta mutum ka koma ga siffar kare. Nan take na zama kare. Suka kore ni waje cikin duhun dare, suka mayar da gida suka rufe.
Bayan matata da mutumin nan sun kore ni daga gidana, sai na kama hanya inatafiya ban san inda nake nufa ba. Ban gushe ba ina tafiya har na kai cikin kasuwa. Na sami wata rumfa nan na kwanta kafin gari ya waye. Ashe rumfar nan ta sarkin fawa ce.
Da gari ya waye, mutane sun fara fitowa kasuwa, sai ga sarkin fawa ya iso ga rumfarsa. Yayin da ya gan ni ina cin kasusuwan da aka watsar, sai tausayina ya kama shi, ya ja ni ya shiga gidansa da ni domin ya ba ni abinci.
Muna shiga gidan sarkin fawa sai ‘yarsa ta yi sauri ta rufe jikinta da mayafi, ta ce da mahaifinta, baba, me ya sa ka shigo mana da namiji cikin gida? Sai mahaifin ya tambayeta, ina namijin?
Ta ce, wannan kare namji ne, matarsa ce ta sihirce shi, ni, ina da ikon kubutar da shi. Yayin da ubanta ya ji zancenta, sai ya ce, na roke ki domin Allah, ‘yata, ki kubutad da shi!
Ta riki wani kasko da ruwa a cikinsa, ta yi zance bisa gare shi, ta kwara ruwan bisa gare ni, ta ce, fita daga wannan sura ya zuwa ga surarka ta farko! Nan da nan kuwa na koma mutum, kamar yadda na ke da farko.

Daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ
(magana jari)05 HIKAYAN TAJIRI DA IFRITU

Labarin tsohona uku mai alfadara.

Ta ce, wannan kare namji ne, matarsa ce ta sihirce shi, ni, ina da ikon kubutar da shi. Yayin da ubanta yaji zancenta, sai ya ce, na rokeki domin Allah, ‘yata, ki kubutad da shi!
Ta riki wani kasko da ruwa a cikinsa, ta yi zance bisa gare shi, ta kwara ruwan bisa gare ni, ta ce, fita daga wannan sura ya zuwa ga surarka ta farko! Nan da nan kuwa na koma mutum, kamar yadda na ke da farko.
Na yi godiya gare ta, na ce da ita, ina son ki sihirce mini matata tamkar yaddata sihirceni. Sai ta ce, to. Ta bani wani ruwa, ta ce, in je'in watsa mata shi yayin da take barci, in ambaci duk surar da nake so ta koma, za ta koma nan da nan.Na karba, na yi godiya, na nufi gidana.

Bayan na shiga gidan, sai na iske matata tana barci. Na yayyafa ruwa bisa gareta, nace, ki fita daga wannan sura ya zuwa ga surar alfadara! Nan da nan ta zama alfadara. Ita ce wannan alfadara da kake gani, ya shugaban ifiritai. Yayin nan tsoho ya waiwaya gare ta ya ce, ko wannan gaskiya ne?Alfadara ta rauda kanta, wato tace, na’am.
Yayin da tsoho mai alfadara ya gamazanta labarinsa, aljani yayi raurawa da farin ciki, ya ba shi sulusin jinin tajiri da ya wanzu, sannan yabace a cikin iska yana mai farin ciki da wadan nan labarai da ya ji, ya bar Tajiri da tsofaffin nan.

Tajiri yayi wa tsofaffin nan godiya akan kubutar da shi da suka yi daga hannun ifiritu. Sannan kowa ya kama gabansa.

MUNGODE ALLAH WANNAN SHINE KARSHEN HIKAYAN. TAJIRI DA IFRITU...

Ga kuma wata hikayar datafi wannan ma'ana dadin saurare wacce take kunshe da labarai kala-kala.Itace==> HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU.

akwai wani mutum tsoho, masunci, yana da mata d'aya da 'ya'ya uku, ya kasance talaka ne, bai ajiye abincin yau ba ballantana na gobe. Kullum yakan je kogi ya kamo kifi ya kai kasuwa ya sayar ya sayo abin da za su ci. Yana da wata al'ada mai ban mamaki, duk lokacin da ya tafi su, yakan jefa komarsa sau hud'u ne kawai, daga nan sai ya nad'e ta ya tafi da kifin da ya kama ya sayar, idan ma bai kama komai ba a jefawa hud'un nan, to ba zai yi ta biyar ba, sai dai ya koma gida haka nan, ranar su kwana da yunwa.
Wata rana ya fita da Azuhur zuwa ga yankin bahar domin yin su, da ya isa ya shiga cikin ruwa daga bakin gaba, ya jefa komarsa ciki, ya juya ta, ya kuma juyawa, sa'annan ya jawo ta, ya ji ta da nauyi,ya fitar da ita daga cikin ruwa. Yajuye abin da ke ciki, bai ga komai ba face ciyawa. Ya kakkab'e ta ya sake jefawa karo nabiyu cikin ruwa, jim kad'an ya jawo ta da kyar saboda nauyi, har rigarsa ta bi ruwa. Ko da ya juye abin da komarsa ta d'ebo, bai ga komai na daga kifi ba face mataccen jaki. Da ya ga haka ya yi bak'in ciki, ya ce a ransa babu tsimi babu dabara face daga Allah mai girma da d'aukaka, neman wannan abinci nawa daban al'ajabi yake, yayin nan ya wake wad'annan baitoci:
"Ya mai bayarwa a cikin duhun dare,
Ba da dabara ko wayo ba,
Na dogara gare ka ya Razzak'u,
Kai ke azurta mu ba don k'ok'arinmu ba."

Bayan ya gama rera wannan wak'a, ya jefar da mataccen jakin, ya wanke komarsa yashanya ta, ta sha iska, ya d'auke ta yashiga cikin ruwa sosai sannan yajefa ta kashi na uku yana maicewa Bismillahi. Koma ta nutse cikin ruwa, yahak'ura har ta nutse sosai. Ya jirkita ta, sannan ya fara jawo ta zuwa tudu, ya ji ta nannauya fiye da jefawar farko da ta biyu, ya yi farin ciki domin ya zacikifi ne.
Ko da ya juye abin da ke cikin koma, sai ya tarar da karafuna da matattun tangaram da duwatsu da yashi da laka, babu komai na daga kifi. Yayin da ya ga haka ya yi bak'in ciki mai yawa, ya rera wannan wak'ar:

"Yarayuwar zamanina ki fahimta,
Idanba ki fahimta ba ki yafe ni,
Haryanzu ba a ba ni rabona ba,
Haryanzu ba a yi hukunci a kaina ba,
Nafita bid'ar arzikina na ishe ya k'are,
Sau da yawa jahili yakan ga abin b'oye,
Sau da yawa ilimi kan b'ace wa Malami."

Masunci yazubar da tarkacen da komarsa takwaso, ya wanke ta, ya nemi gafara ga Allah bisa wannan wak'a da yayi. Da komar ta sha iska ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa, wannan karon ya kutsa nesa cikin ruwa, ya d'aga kansa sama ya ce, ya Ubangiji ka sani cewa ba ni jefa komata fiye da sau hud'u a rana, na jefa sau uku ban sami komai ba, Allah ga ta hud'u kuma ta k'arshe zan jefa, kanufe nida samun abin da zan ci, ni da iyalina. Ya ambaci sunan Allah, ya jefa komarsa karo na hud'u.

Bayanya dad'e yana juya ta, sai ya jawo ta zuwa tudu, wannan karon ta fi koyaushe nauyi. Da ya fito da ita da kyar, ya juye abin da ke ciki, babu komai face yashi da wata yar batta (kwalba) k'arama, ta farin k'arfe, girmanta bai wuce a saka ta a cikin aljihu ba,an lik'e bakinta da darma, anbuga hatimin Annabi Sulaimanu a saman murfin.. Nantake saiga ifritu ya baiyana,,,

Wannan kadanne daga cikin wannan hikayar' ta masunci. Saidai ita damu gabatar da itace acikin zauren maisuna.ZAUREN HIKAYA. wanda kudin rijistar shiga zauren 500 kacal. Zamu gabatar muku da hikayoyi 30 ne acikin zauren. Wanda bayan sallah zamu budeshi insha allah. Idan anbude zaku samu cikkaken karin bayani akan zauren

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment