Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

Ya zauna yana ta tumurmusar
dukiya, yana ci, yana sha cikin bushasha
yana ta rabar da zinariya da azurfa da jauhari. Kullum cikin cin nama yake da shaye
– shaye da yawan dariya ga kuyangi suna
masa wak’ok’i yana musu kyaututtuka. Bai gushe ba yana wannan d’abi’a har abin da
ya mallaka gaba d’aya ya k’are ya zamana ba shi da komai duk abin da ya mallaka ya
fice daga hannunsa, sai wata kuyangarsa
guda d’aya da ya mallaka daga mahaifinsa. Ita wannan kuyangar ta kasance babu kamar ta wajen kyau da cikar halitta da k’oshi da
hankali da ladabi biyayya. Ta fi ragowar kuyangin wajen ilmi da iya magana mai dadi.
Ta nak’alci yadda za ta jawo hankalin mutum zuwa gare ta, ta san yadda za ta rarrashi
masoyinta. Idan ka gan ta za ka yi
tsammanin watan sha’aban ne ya tsaya
saboda idanunta masu haske, tamkar an
gina su da lu’ulu’u, suna walk’iya kamar
kaifin takobi, jikinta kullum ba ya rabo da
k’amshi da taushi da ni’ima. Kundukukinta
kamar nunanniyar tuffa. Bakinta matsakaici
kamar hatimi, hak’oranta jere reras kamar
kibiyoyi. Jikinta mai kyan gani abin so ga
kowa domin bai zama ramamme ko mai
yawan k’iba ba. A taka’ice dai ita ta kasance
kamar yadda mai wak’a ke cewa:
Idan ta gabato ta fitinar da zuwanta,
Idan ta tafi nan ne abu mafi azabtuwa
Ta fi wata haske ta yi kama da rana
Kyawunta shi ne abin so ga duk kowa
Tana jan hankalin duk wanda ya gan ta da
kyanta da iya maganar ta mai cike da
tattausan lafazi da murmushinta ko
dariyarta. Musamman idan ta haskawa
mutum kyawawan fararen idanun nan nata.
Da yake Abu Hasan ya karkatar da dukkan
dukiyarsa ya zamana ba shi da komai sai ita,
ga shi kwana uku kenan ba su jefa wani abu
a cikinsu ba kuma ba su samu barci ba, sai
kuyangar ta ce da shi, “ya shugabana, ka kai
ni wajen Sarkin Musulmi Khalifa Haruna
Rashid ya fanshe ni.”
ka nemi biyana dinari dubu goma, hakan zai sa
ka samu biyan bukata daga damuwar da ka
shiga. Idan ya nuna cewar na yi tsada sai kace masa, “ya Sarkin Musulmi wannan kuyangar da kake gani k’imar kudinta ya fi
haka ma, amma ka jarraba ta da kanka ka gani ta fuskar ilmi da hankali. Domin ita
wannan kuyangar babu misalinta, kuma ba
ta dace da wani ba face kai.” Ta sake
gargadinsa cewa, “kada fa ka sallama ni
k’asa da abin da na fad’a maka, domin
wannan kud’in araha ce ga makamanciyata.”
Ubangidanta ya kasance bai san darajar ta
da k’imar ta ba, amma jin za ta kai wannan
darajar sai ya d’auke ta ya tafi da ita wajen
Khalifa ya shaida masa kamar yadda ta hore
shi. Khalifa ya dube ta ya ce, “yaya sunanki?”
Ta ce, “sunana Tawaddud.” Sannan ya ce,
“ya ke Tawaddud a wanne fannin ilmi kika
gwanance?” Ta ce, “ka sani ya Sarkin
Musulmi ni inda da ilmin nahawu da furu’a da
wak’ok’i da tafsiri da hisabi da k’ismi da
labarun mutanen farko. Kuma na san
Alk’ur’ani mai girma, na karanta ta fuskar
ruwayoyi bakwai da goma da kuma goma
sha hud’u. Na san yawan surorinsa da
ayoyinsa da haruffansa da kalmominsa. Na
san tsakiyarsa da rubu’insa da sumuninsa
da wuraren sujjada da k’irgen adadin
haruffan sujjadar. Na kuma san ayoyin da
aka shafe da wadanda ba a shafe ba. Na
kuma san surori Makiyya da Madaniyya da
sababin saukar da aya ko sura. Na san
hadisan Annabi da tarihi da hik’ayoyi da
labarun da ake kokwanto a kan ingancinsu.
Na san ilmin sanin rauhanai na san na
mutanen Hindu da na Falasd’inawa da
hikimomin jiya da na yau, na kiyaye da yawa
ilmin ma’ana da na bayani. Kuma na nak’alci
ilmin magani da kuma iya kad’a molo yadda
zan kad’a shi na b’ata zuciya da yadda zan
buga shi ya faranta rai. Haka nan na san
yadda za a kad’a shi a yi rawa da inda za a
kad’a a yi shiru kawai. Idan na yi ado na
fitinar, idan na shafa turare a fitina da ni. Na
zama babu wanda zai k’aru da ni sai wanda
yake da ilmi mai zurfi mai hangen nesa.”
Yayin da Khalifa ya ji wannan bayanin nata
sai ya yi mamaki saboda k’arancin
shekarunta da yadda ta iya bayani cikin
hikima da lafazi mai dad’i. Ya waiwaya ga
Abu Hasan ya ce, “bari na aika a kirawo
ma’abota sani da za su yi mata tambayoyi
kan abin da ta ce tana da shi na daga ilmi.
Idan ta kasance ta amsa dukkan tambayoyin
zan saye ta a wajenka, bisa kud’in da ka
fad’a kuma na k’ara maka wasu a kai. Amma
idan ba ta amsa ba, to babu wanda ya
cancanta da ita sai kai.” Abu Hasan ya ce,
“cikin farin ciki da so da yarda ya Sarkin
Musulmi.” Khalifa ya rubuta takarda zuwa
birnin Basra ya ce a kirawo masa Ibrahima
d’an Siyyari. Ya kasance masani ne a fannin
balaga da wak’e. Ya ce kuma ya taho da
masana Kur’ani mai girma da malaman
hikima da masana ilmin maganganu da
masana ilmin taurari da mahukunta da
masanan ilmin Hindu da Falsad’iya da hisabi.
Shi Ibrahima ya kasance duk ya fi su sanin
wad’annan ilman ya aika duka suka zo suka
tafi da hanzari domin amsa kira.
Yayin da suka isa fada suka zazzauna
Khalifa ya bayyana musu dalilin kiran su
sannan ya aika aka kirawo kuyanga
Tawaddud ta shigo ta yaye lullub’i ta nuna
kanta kamar walk’iyar tauraro. Khalifa ya sa
ta zauna a kujerar zinariya ta gaishe da
jama’a cikin murya mai taushi da fasahar
harshe, sannan ta ce, “ya Sarkin Musulmi, ka
umarci wad’anda suka hallara nan daga
malamai da masana ilmin taurari da masana
hindiya da falsad’iya su yi min tambaya duk
irin wadda suka ga dama.” Khalifa ya ce da
su, “ina so ku yi jayayya da wannan kuyanga
bisa abin da take tak’ama da shi na daga
ilmi cikin sha’anin addininta. Ku tambayi
hujja game da irin abin da ta fad’a.” Suka
amsa, “mun ji mun bi ya Sarkin Musulmi.” A
nan Tawaddud ta sunkuyar da kanta alamar
gaisuwa ga Sarkin ta ce, “a cikinku wanene
masanin shari’a da fik’ihu wanda ya nak’alci
Alk’ur’ani da hadisai?” Sai wani ya mik’e ya
ce, “ni ne wanda kike tambaya.” Ta ce, “to yi
tambayar ka gare ni.” Ya ce, “shin kin karanci
littafin Allah mai girma kuma kin san aya
shafaffiya da wadda aka shafe ta da ita? Kin
san adadin ayoyinsa da haruffansa?” Ta
amsa, “na’am na san wad’annan duka. “To
tunda haka ne zan miki tambaya a kan farilla
wajiba da sunna k’a’ima.
Ya ce ya ke kuyanga wanene ubangijinki?
Wanene Annabinki? Menene a gabanki? Ina
ne alk’iblarki? Su wanene ‘yan uwanki?
Menene tafarkinki?”
Ta ce, “Allah shi ne ubangijina, Annabi
Muhammadu mai tsira da aminci su tabbata
a gare shi, shi ne Annabina. Alk’ur’ani shi ne
a gabana, d’akin Ka’aba nan ne alk’iblata,
musulmi su ne ‘yan uwana. Sunnar Annabi
Muhammadu ita ce tafarkina.”
Khalifa ya yi mamaki da irin kalamanta da
cikar fasahar ta duk da k’arancin shekarunta.
Mai tambaya ya cigaba, “ya ke kuyanga, da
me ake sanin Allah?”
Ta ce “ana sanin Allah ta hanyar fahimta.”
Ya ce “menene fahimta?”
Ta ce “fahimta iri biyu ce; da wadda take a
b’oye da wadda take a bayyane.”

Zanci gaba insha allah gobe02 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

kuyanga tayi bayaninta sosai, tana cewa, “fahimta iri biyu ce; da wadda take a b’oye da wadda take a bayyane. Fahimta b’oyayyiya ita ce wadda Allah mai girma da d’aukaka ke halittar mutum da ita, yana bayar da ita ga wanda ya
so. Amma bayyananiyar fahimta kuwa ita ce
wadda mutum ke samu ta hanyar neman
ilmi.” “Kin amsa daidai.” In ji malamai. “To amma
ina ne mazaunar hankali?” Ta amsa da cewa “Allah ta’ala kan jefa shi a
cikin zuciyar mutum, daga nan sai haskensa
yakan tafi zuwa k’wak’walwa daga nan ya
tabbata kenan.”
“Wannan haka yake.” In ji malami mai
tambaya. Sannan ya ce, “ta yaya kika san
Annabin Allah?”
Ta ce “ta hanyar karatun littafin Allah da
wasu alamu da kuma tabbatattun hujjoji da
karamomi.”
Ya ce, “haka ne.” Daga nan ya ce, “fad’a min
game da shika-shikan Musulunci da sunna
k’a’ima.” Ta ce, “shika-shikanMmusulunci
guda biyar ne, na farko shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah mad’aukakin
Sarki, kuma Annabi Muhammadu bawansa
ne, manzonsa ne. Na biyu tsaida sallah, na
uku bayar da zakka, na hud’u azumin watan
Ramalana, sai cikon na biyar shi ne aikin hajji
zuwa ga d’akin Allah mai alfarma ga wanda
ya samu iko ga haka. Sunna k’a’ima kuwa su
hud’u ne; dare da rana, rana da wata, sune
suke kusatar da rai da buri su k’arar da d’an
Adam, bai sani ba cewa a kullum suna
kusatar da shi ne zuwa ga ajali.” Ya ce, “haka
ne. To ki fad’a min game da tabbatar imani.”
Ta ce ‘wad’annan su biyar ne, sallah da
azumi da hajji da kuma jihadi a tafarkin Allah
da nesantar haram.”
“Haka ne, to ki fad’a min abin da ke
k’arfafawa zuwa ga sallah.”
Ta ce da malamin “aniyar bauta zuwa ga
Allah, ka san kai bawa ne ka bi shi.”
Ya sake tambayar ta “wad’anne wajibabbun
sharud’d’a ne suka zama tilas a cika su kafin
a kai ga yin sallah?”
Ta ce “na farko tsarki da suturce al’aura da
nisantar kayan k’yale – k’yale da tsayawa a
wuri mai tsarki da fuskantar alk’ibla da
daidaita tsayuwa da niyya da kabbarar
harama.”
“Haka ne, to fad’a min abin da ake fita daga
gida domin sallah.”
Ta ce “ana fita da niyyar bauta zuwa ga
Allah.”
Ya sake tambayar ta “ da wacce niyya ake
shiga masallaci?”
Ta amsa “da niyyar bauta wa Allah.”
“Don me muke fuskantar alk’ibla a
sallolinmu?”
“Domin cika umarni uku daga K’ur’ani mai
girma da umarni d’aya daga hadisi.”
“Fad’a min game da sallah? Menene
farkonta? Menene k’arshenta? Me ya
haramta ta?”
“Ana yin sallah cikin tsarki. Rashinsa na
haramta ta. Farkonta shi ne kabbarar
harama, k’arshenta shi ne sallama.”
“Menene hukuncin wanda ya bar sallah da
gangan?”
Ta ce “an rawaito daga ingantattun hadisai
cewa duk wanda ya bar sallah da gangan ba
tare da wani dalili ba, to ya bar addinin
Musulunci.”
kuyanga ta rik’a bai wa malamin nan amsa daidai yadda ya tambaye
ta, shi kuma yana cewa, ‘haka ne.’ Sai ya ce, “ina so ki fad’a min menene ma’anar sallah?”
Ita kuwa ta ce da “Sallah ita ce wata hanyar ganawa tsakanin bawa da ubangijinsa, kuma
tana da darajoji guda goma su ne, na d’aya tana haskaka zuciya, na biyu tana haskaka
fuska, na uku tana sa yardar Arrahamanu, na
hudu tana fusatar da shaid’an, na biyar tana maganin masiba da bala’i. Na shida tana
juyar da muguntar abokan gaba, na bakwai
tana rub’anya lada. Na takwas tana hana yin
azaba a ranar lahira, na tara tana kusantar
da bawa zuwa ga ubangijinsa, tana kuma
hana shi aikata miyagun ayyuka, na goma ita
ce ginshik’in addini.”
“Wannan batun gaskiya ne, menene mabud’in
sallah?”
“Alwalla ko taimama.”
“Menene mabud’in taimama?”
“Niyya da kuma ambaton sunan Allah
mad’aukakin Sarki.”
“Menene mabud’in ambaton sunan Allah
mad’aukakin Sarki?”
“Cikakken imani.”
“Menene mabud’in cikakken imani?”
“Ban gaskiya ga Allah.”
“Menene mabud’in ban gaskiya ga Allah?”
“Sakankancewa.”
“Menene mabud’in sakankancewa?”
“Biyayya.”
“Menene mabud’in biyayya?”
“Kad’aita Allah da dagewa wajen bauta
masa.”
“Fad’a min game da farillan alwalla.”
“Farillan alwalla guda shida ne bisa
mazhabar Imamu Shafi’i, Muhammadu d’an
Idrisa, Allah ya yi musu rahma. Niyya yayin
wanke fuska, wanke fuska, wanke hannaye i
zuwa gwiwar hannu, shafar kai, sai wanke
k’afafu i zuwa idon sawu. Da kuma
jerantawa.
Sunnonin alwalla kuma guda goma ne, yin
bismilla da wanke hannaye kafin tsoma su a
cikin k’warya, kurkure baki, shak’a ruwa da
fyacewa. Shafar gaba d’ayan kai da shafar
kunnuwa da sabunta ruwa a gare su. Da
kuma tsettsefe gemu mai kauri da tsettsefa
yatsun hannu da na k’afafu da soma gabatar
da dama kafin hagu da yin wanki uku – uku
tare da jerantawa.
Idan ka gama alwalla sai ka ce, “na shaida
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,
kuma Muhammadu bawansa ne, kuma
manzonsa ne. Ya Allah ka sanya ni cikin
bayinka masu tuba, kuma ka sanya ni cikin
tsarkaka. Tsarki ya tabbata gare ka, yabo
naka ne kai d’aya. Na nemi gafara a gare ka,
ina tuba gare ka. Domin a ruwaito hadisi
daga Annabi mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi cewa, ‘duk wanda ya
karanta wannan addu’ar bayan ya yi alwalla,
za a bud’e masa k’ofofin aljanna ya shiga ta
wadda ya ga dama.”
Malami ya ce, “kin yi gaskiya, idan mutum ya
yi nufin yin alwalla a ina mala’iku da
shaid’anu ke tsaya masa?”
“Idan mutum ya yi nufin yin alwalla, mala’iku
kan sauko su tsaya a damansa, sannan
shaid’anu za su tsaya a hagunsa. Idan ya
ambaci Allah a farkon alwallarsa sai
shaid’anu su gudu. Daga nan sai mala’iku su
yi masa laima ta haske da fukafukansu,
kowannensu yana da fuffuke hud’u, suna
tsarkake sunayen Allah mai girma, suna
nemar wa mutumin gafara gwargwadon
lokacin da ya kasance yana alwallar bai yi
magana ba. Amma idan a farkon alwallar bai
yi bismilla ba sai shaid’anu su kewaye shi,
mala’iku su juya ga barin sa. Sai shaid’anun
su sanya masa waswasi cikin alwallar har ya
yi nak’asu a cikin ta. Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce,
“kyakkyawar alwalla na korar shaid’an, ta
fusata shi.” Sannan an rawaito yana cewa,
“idan wata masifar ta fad’awa musulmi a
lokacin da ba shi da alwalla, kada ya zargi
kowa sai kansa.’

ZANCI GABA03 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

“Me mutum ya kamata ya soma yi da zarar
ya farka daga barci?”
“Ya kamata ya wanke hannunsa sau uku,
kafin ya tsoma su a cikin k’warya.”
“Menene farillai da sunnonin wankan
janaba?”
“Farillan su ne, niyya, game jiki da ruwa da
sadar da ruwa ga dukkan gab’ob’i, ana nufin
ruwa ya tab’a dukkan sannan jiki duka na
daga gashi da fata. Sunnonin kuwa su ne a
fara da alwalla sannan cuccud’a jiki da
tsettsefe gashi da jinkirta wanke k’afafu sai a
k’arshen wanka.”
Yayin da yarinya
ta bayyana wa malamin farillan wanka da
sunnoninsa da na alwalla sai ya ce, “kin yi
daidai, yanzu fad’a min dalilan da ya sa ake
yin taimama da farillanta da sunnoninta.”
Ta ce, “dalilan bakwai ne, rashin wadatar
ruwa ko jin tsoron kada ruwan ya k’are, zama
a wurin da babu ruwan da ya kamaci alwalla,
rashin lafiya, ko karaya a gab’b’an alwalla da
samun rauni a gurbin alwalla. Farillanta guda
hud’u ne, su ne; na d’aya niyya, na biyu
turb’aya, na uku bugun k’asa na farko, na
hud’u shafar fuska da hannaye. Sunnoninta
su ne bugun k’asa na biyu da juyowar shafar
hannu da kuma gabatar da dama a bisa
hagu.”
“Menene sharud’d’ai da farillai da kuma
sunnonin sallah?”
“Sharad’an sallah guda biyar ne, in ji ta “na
d’aya tsarkin gabb’ai, na biyu suturta al’aura,
na uku cikar lokaci da sakankancewa da
ganin wani. Na hud’u fuskantar alk’ibla, na
biyar tsayawa a wuri mai tsarki. Amma
farillan sallah guda goma sha biyu ne; niyya
da kabbarar farko da tsayawa bisa karatun
fatiha da ambaton bismillah har k’arshenta a
bisa mazhabar Imamu Shafi’i. Da ruku’u da
daidaito cikin ruku’un da daidaita zama da
nutsuwa a cikin zaman, da sujjada da
nutsuwa cikin sujjadar da zama tsakanin
sujjadai biyu da nutsuwa a cikin zaman da
tahiyar k’arshe da zama a gare ta da salati
ga Annabi mai tsira da aminci su tabbata a
gare shi. Da kuma sallamar farko bisa niyyar
fita daga sallah da ambatonta.
Sunnoninta kuwa su ne, kiran sallah da
ik’ama da d’aga hannaye yayin kabbarar
harama da addu’ar shiga sallah da neman
tsari daga shaid’an da cewa ‘amin’ a
k’arshen karatun fatiha da karatun sura
bayan fatiha da kabbarori yayin tashi tsaye
da fad’in, ‘Sami’Allahu li man hamidahu’ da
kuma ‘Allahumma Rabbana wa lakal hamdu.’
Haka kuma da bayyanawa a wurin da ake
bayyanawa da sirintawa a wurin da ake
sirrantawa da zaman tahiyar farko da
karatun tahiyar farko da salati ga Annabi a
tahiyar farko da salati a farkon tahiya da
kuma sallama ta biyu.”
“Kin fad’i daidai, in ji malam, “ fad’a min a kan
me zakka ta wajaba?”
Kuyanga sai ta amsa masa, “zakka ta
wajaba a kan dinari da azurfa da rak’umi da
saniya da akuya da alkama da shinkafa da
sha’ir da gero da dawa da gyad’a da wake
da auduga da zabibi da dabino.”
Ya amsa, “wannan haka yake, a cikin nawa
ne zakka ke fita daga dinari?”
Ta ce da shi, “babu zakka a kan abin da yake
k’asa da misk’ali ashirin na dinari. Idan ya
kai misk’ali ashirin za a fitar da rabin misk’ali
zuwa ga abin da ya samu na abin da ya
zarta haka. Ma’ana idan dinari ya kai misk’ali
ashirin ko fiye za a bayar da kaso d’aya bisa
arba’in na yawansa a matsayin zakka.”
Sai ya ce da ita, “zakkar azurfa fa?”
Ta amsa,“ita ma kamar dinari take.”
“Zakkar farin kud’i fa?” Ya tambaye ta.
Ta ce da shi, “abin da ya kama k’asa da
zambar d’ari babu zakka a kan sa, amma
daga zambar d’ari zuwa sama ana fitar wa a
kowace dubu kud’i hamsin.” Ma’ana ana
kasawa arba’in a d’auki kaso d’aya.”
Sai kuma ya tambaye ta da cewa “to yaya
zakkar hatsi take da sauran kayan amfanin
gona?”
Ta ce “daga dami talatin zuwa abin da ya yi
sama ana fitar da kowane goma dami d’aya.”
“Yaya zakkar rak’uma take?” Ya tambaye ta.
Sai ta ce da shi, “a dukkan biyar ana bayar
da tunkiya ko kuma a had’a ashirin da biyar
a bayar da rak’uma mai ciki.”
Sai ya k’ara da cewa “yaya zakkar tumaki da
awaki take?”
Ta ce “tunkiya ko akuya ake fitar wa a duk
guda arba’in.”
“To mene ne azumi?” Ya sake tambayar ta.
Sai ta amsa da cewa “azumi shi ne kamewa
daga cin abinci ko shan abinsha da jima’i da
kiyayewar amai da gangan, duk wannan ana
yin su da nufin ibada. Wajibi ne a kan
kowanne musulmi baligi, maza da mata,
‘yantattu da bayi sai dai ga matar da ke cikin
haila ko bik’i. Kuma azumi yana wajabta ne
da ganin jinjirin watan Ramalana, wanda
shaidu biyu adilai suka hak’ik’ance da ganin
sa. Da kuma labarin ganinsa da aka bayar
daga wanda za a yarda da gaskiyar
maganarsa. Akwai daga wajibansa shi ne
tashi bisa niyyar azumin a kowace safiya da
kamewa daga ci da sha da jima’i.
Sunnoninsa kuwa sun had’a da jinkirta sahur
da gaggauta bud’e baki da barin zance face
na alheri da zikiri da karatun Alk’ur’ani mai
girma.”
“Wannan bayani haka yake,” ya ce da ita
“fad’a min abubuwan da ba sa b’ata azumi.”
Sai ta yi wuf ta ce, “shafa mai da shafa kwalli
da k’urar hanya da had’iyar wani abu da fitar
maniyyi a cikin mafarki. Da ganin mace
ajanabiyya da tsaga jiki da k’aho duka
wad’annan ba sa b’ata azumi.”
Ya ce da ita, “haka yake, to labarta mana
game da sallar idi.”
Ita kuwa sai ta ce, “raka’o’i biyu ne a kowace
sallah. Kuma suna cikin salloli na sunna. Ba
a kiran sallah, ba a tayar da ik’ama. Amma
ana cewa, ‘a daidaita sahu’ sannan sai a yi
kabbara sau bakwai a raka’a ta farko, bayan
kabbarar harama. A raka’a ta biyu kuma
kabbara biyar ake yi, bisa koyarwar
mazhabar Imamu Shafi’i kenan, Allah yayi masa raham

ZANCI GABAO4. HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

bayan yarinya ta
gama yi wa malamin nan bayani a kan sallar idi a gaban Sarki Musulmi sai ya ce, “kin fad’i
daidai, to fad’a min yadda ake sallar kisfewar
rana ko wata.” Yarinya ta ce, “ba a kiran
sallah ko ik’ama, raka’a biyu ne kowace, ana
yin ruku’u biyu da tsayuwa biyu da sujjada
biyu, sannnan a yi zaman tahiya, a yi
sallama.”
Ya ce ‘ to fad’a min yadda ake sallar rok’on
ruwa.”
Nan ma sai ta ce da shi “raka’a biyu ce, babu
kiran salla, babu ik’ama. Bayan an yi sallama
limami zai gabatar da hud’uba sannan a rok’i
Allah gafara kamar yadda ake yin hud’uba a
sallar idi. Bayan nan sai a yi addu’a cikin
k’ask’antar da kai.
Sai ya tambaye ta “yaya ake sallar wuturi?”
Ta ce masa “ita salla ce mafi k’aranci raka’a
d’aya, mafi yawa raka’a goma sha d’aya.”
Sai ya ce “yaya ake sallar walaha?”
Ta ce da shi ‘sallar walaha ana yin ta bayan
hudowar rana, mafi k’aranci raka’a biyu, ma fi
yawa raka’a goma sha biyu.”
Sai ya juya ya ce da ita “me kika sani game
da i’ittikafi?”
Ta ce da su “i’ittikafi sunna ne ana zama a
masallaci ana ibada.”
“Menene sharud’d’ansa?”
Sharud’d’ansa, na d’aya niyya, na biyu kada
a fita daga masallaci sai domin biyan
buk’ata, na uku babu cud’anya da mata na
hud’u ya zamana ana azumi, na biyar ban da
zancen duniya sai na alheri.”
“Fad’a min abin da ya wajabta aikin hajji.”
“Na farko cikar hankali da Musulunci da
samun ikon zuwa. Shi kuma wajibi ne ga
musulmi sau d’aya a rayuwa.”
“Menene wajibabbu a aikin hajji?”
Wajibabbu su ne, harama da tsayuwar arfa
da d’awafi da safa da marwa da kuma aske
gashin kai.”
“Menene farillan aikin Umra?”
“Harama domin ta da d’awafi da tafiya cikin
ta.”
“Menene sharud’d’an harama?”
“Cire d’inkakkun tufafi, da nisantar turare da
nisantar aski ko cire gashi da nisantar yanke
farce da nisantar farauta ko kisan namun daji
da kuma nisantar jima’i.
“Menene sunnonin hajji?”
“Fadin Labbaikal lahumma labbaika da
gewaye d’akin Ka’aba da ban kwana da
wurin kwana daga Muzd’alifa da jifa da
duwatsu.”
“Menene jihadi? Menene sharud’d’ansa?”
“Jihadi shi ne yak’i domin d’aukaka kalmar
Allah. Sharud’d’ansa su ne fita a kan kafirai
idan suka auko muku, samun jagora da bin
umarninsa. Da tsayawa yayin gwabzawa da
abokan gaba.
Sunnoninsa su ne kwad’aitar da jama’a bisa
yak’i a kan tafarkin Allah domin fad’ar Allah
mad’aukakin Sarki cewa, “ya kai annabi, ka
kwad’aitar da musulmi akan fad’a da kafirai.”
“Haka yake, menene sharud’d’an ciniki da
sunna tasa?”
“Sharud’d’ansa su ne jawabin mai kaya da
amincewar mai saye, kada mai sayarwa ya
zamana bawa ko yaro k’arami ko matar wani
wad’anda ba su da ikon sallamawa. Sannan
a gujewa riba da dangoginta.
Sunnoninsa kuwa su ne, daddalewa kafin a
rabu, domin hadisi ya zo cewa, mai tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yana
cewa, “masu ciniki su daddale kan komai tun
kafin su rabu.”
“Fad’a min abin da aka hana sayensa da
wani abu.”
“A bisa wannan na tuno da wani hadisi
ingantacce cewa an ruwaito daga Nafi’u
cewa Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya hana musayar
busasshen dabino da d’anye, ko busasshen
b’aure da d’anye ko dafaffen nama da
d’anye. Haka nan musayar d’anyen mai da
soyayye da dukkan abin da ya kasance iri
d’aya ne na daga abinci wanda aka sauya
masa kamanni. Watau duk wani na’uin abinci
da ya zama iri d’aya ba a musayen su.”
Yayin da malamin nan ya ji dukkan bayanan
kuyanga, ya hak’ik’ance abin da ta fad’a
daidai ne, ya gamsu da ilminta da zurfin
tunaninta da sanin fik’ihunta. Ya hak’ik’ance
ba zai iya kayar da ita a wajen tsantsar ilmi
ba. Ya ce a ransa, “Babu makawa sai na
k’ure ta a gaban Sarkin Musulmi ta hanya
mai sauk’i cikin dabara.” Ya dube ta ya ce,
“ke yarinya, menene ma’anar alwalla a cikin
lugga?”
Ta ce, “ma’anarta shi ne tsarkake gabb’ai
daga datti.”
“Menene ma’anar sallah a cikin lugga?”
“Ma’anarta fata nagari.”
“Menene ma’anar wanka a cikin lugga?”
“Ma’anarsa tsarkakewa.”
“Ma’anar azumi fa a lugga?”
“Azumi a lugga yana nufin kamewa.”
“Ina ma’anar Zakka a lugga?”
“Zakka tana nufin k’ari a kan dukiya.”
“Fad’a min ma’anar aikin hajji a lugga.”
“Hajji a lugga na nufin ziyara.”
“Ina ma’anar jihadi a lugga?”
“Jihad na nufin kiyayewa ko k’ok’artawa.”
Daga nan malamin ya yi shiru.
saboda ta gama yanke masa duk wani hanzarinsa da kuzarinsa. Ya tsaya kan dugadugansa ya dubi Sarkin Musulmi ya ce,
“ya Sarkin Musulmi, hak’ik’a wannan
kuyanga ta kasance mafi sani daga gare mu
a fannin furu’a.”
Kuyanga Tawaddud ta ce, “ina neman iznin
Sarkin Musulmi na yi wa malamin nan
tambaya
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment