Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

izgili sarki ya kalle shi kallon wulak'anci yana jinjina kai haka nan muryansa d'auke da wani irin yanayi mai kama dana mutumin da yayi shaye² ya furta
    "Malam waye kai..kuma daga ina..??"
   Marin daya tsinka masa ya sashi hantsilawa,cikin tsananin mamaki ya d'ago kai a fusace ya kalleshi
   "Kan uba..! Kai har ka isa ka sa hannu ka mare ni..!? Waye kai nace..?? Dawa kake tak'ama da har zaka sa hannu ka mare ni..!?"

     "Ubanka ne..!"
   Ya bashi amsa muryansa d'auke da wani irin izzah yana sake zabga masa wani sabon marin,dafe chicks sarki yayi kafin ya sake d'ago fuskarsa dake cike da tsananin fusata,tabbas ko ba'a fad'a ba a wannan karon kam marin yafi na farko shigarsa,,magana yake son sake yi amma ina bai samu wannan damar ba,dan yadda ya sake d'auke shi da wani gigitaccen marin,yayin da a duk lokacin da yayi nufin yin magana kafinma ya kaiga yin maganar sai ya sake samun k'arin mari,,sai daya jera masa su sun kusa sha biyar amma sarki bai fasa ba,saboda masifar taurin zuciya irin nasa,dan kansa kuma ko da yaji azabar ta isheshi sai ya maze,,a karo na karshe kuma koda yaji saukar marin sai bai iya d'agowa ba,dan a duk lokacin da zai sake marin sa ji yake na biyun tamkar ya zarce na farko azaba,cikin hargagi sarki dake sunkuye kan babu yadda zai yi ya shiga magana cikin d'aga murya da hargowa
   "Wai kai to waye ne..kuma ina ruwanka,me nayi maka ma da zaka zo kana duka na kamar wani dank'a..??"
    Dundu ya sakar masa a tsakiyar bayansa wanda ya sa shi yin plat a k'asa had'e da canyara ihun azaba mai razanarwa wanda shi ne dalilin daya janyo hankalin su GOJE zuwa kansu,cikin sauri duka ai gasu sun nufo gurin da son duba abunda yake faruwa,sai dai ko da suka yi arba da sarki kwance a k'asa nan suka yi turus suna masu kallonsa had'e kuma da sake kallon Sabina da har lokacin itama tana nan a kwancen kamar yadda suka barta a d'aure tamkar hunhun goro,sake waigawa suka yi suna masu kai kallonsu akan matashin da suka gani wanda basu san ko waye ba nd kuma basu san mene ne actual abunda ya samu sarkin yake ihu ba
    "Dallah dan uwarku me kuke yi a tsaye..?? Ku k'addamar mas..!"
   Sarki ya fad'a yana share kwallar azaba data ziraro masa,,ba tare da sun ko tsaya tambayar sarki ba'asin abunda ya same shiba,coz su dai sun ganshi a baje a gurin,amma furucinsa kad'ai sai yasa suka yi kan matashin a guje suna fad'in
    "Aaahh! K'arya ne wollahi.."
   Murmushi ya saki mai ciwo sannan ya kallo inda take kwance,a hankali ta shiga mirgina masa kai gefe tana mai yi masa alama da "A'a",amma bai ko saurareta ba saima sak'on harara daya aika mata sannan ya janye idanunsa akanta,tun kafin su kaiga k'arasowa inda yake tuni ya kai hannunsa had'e da fizgo wani ice dake kafe a gefe yana daidaita rik'on sa a hannunsa da jiran isowarsu,dai² kwaurin ILA ya kallo yana saitawa dan dama shi ne akan gaban,yana zuwa kusa da shi tunma kafin ya farga tuni ya ajiye masa shi akan k'ashin,ihu ya saki na azaba kafin ya dawo hayyacinsa ya sake d'ora masa a baya,birki GOJE yaja da yake bayan ILA cikin sauri ya juya aguje zai koma inda ya fito,nan take matashin shima ya take k'afarsa ya bishi suka shiga tsere a tsakanin gurin,,a hankali Sabina ta lumshe idanunta tana mai godiya ga Allah (S.W.T) daya kawo mata maceci,,dai² lokacin ne kuma ihun GOJE yasa ta saurin bud'e ido tana karkata kanta zuwa gefen data tsinkayo ihun nasa,kwance ta hango shi a k'asa yana birgima,haka nan matashin shima bai saurara masa ba sai shimfid'a masa icen yake a duk inda yaga dama,tun GOJE yana mirginawa da k'arfinsa yana bashi hak'uri har sai daya gagara,,a hankali ya d'ago kansa lokacin daya tabbatar GOJE yayi laushi sannan yasa hannu ya yafito su ILA da sarki da suka yi tsugune suna kallonsu tamkar monkeys (birrai),,ILA cikin tsoro dan yadda yaga anyiwa GOJE duka yasa shi k'ank'ame jikinsa yana fad'in
   "Dan girman zatin Allah Yallab'ai kayi min rai,,wollahi ni dai babu ruwana..dama ni ban sansu ba yanzun na fara ganinsu.."

  "A gidan uwarka..D'an shegiya,,wollahi tare muke duka mu uku Yallab'ai.."
   Sarki ya fad'a shima cikin damuwa dan yasan matuk'ar suka samu hanyanr guduwa tofa shi zasu bari a tsaka mai wuya
   "Ban tambaye ku wannan bayanin ba,,cewa kawai nayi ku zo.."
   Matashin ya fad'a cikin husky voice d'insa daya sake firgita su ILA
   "Dan girman Allah Yallab'ai wollahi mun san munyi KUSKURE,,,amma dan girman Allah kayi hak'uri,, munyi maka alk'awarin baza mu sake ba.."
   Lower lip d'insa ya rik'o yana kallonsu
   "Baza ku zoba kenan..??"

  "A'a ranka ya dad'e,,wollahi zamu zo.."

    "Ahaaa! Ku zo nan..!"
   Ya fad'a yana nuna musu inda yake tsaye da icen hannunsa nd yana sake d'aure fuska,kasa tasowa sukayi kowanne jikinsa sai kyarma yake yana kallon d'an uwansa dan sun san matuk'ar suka kai kansu gare shi jibgarsu zaiyi kamar yadda yayiwa GOJE
   "Baza ku zo ba kenan..? Ni kuke so na zo..??"
  Ya sake tambaya cikin matuk'ar d'aure fuska
  "A'a Yallab'ai wollahi bama saika zo ba..Zamu zo da kanmu.."

   "Ok..! Maza kada ku b'ata min lokaci.."

  Nok'ewa suka ci gaba da yi,nan ya jinjina kai yana nufar inda suke kai tsaye,suna niyyan sake guduwa shima yana binsu,a hakan ya shiga tafka musu icen sai da yayi musu duka dukansu,bayan ya tabbatar baza su moru ba,ya kalle su yana fad'in
     "Maza ku kwance ta..!"
   Basu bari ya gama fad'a ba suka yi wuf duka su ukun kowanne ya kama nasa b'angaren har sai da suka kwance ta daga mugun d'aurin da suka mata,,a hankali tasa hannu ta rik'e hijab d'inta bayan ta janye shi daga kan fuskarta,wanda sai a lokacin ne y'ar kyakykyawar fuskarta ta bayyana sosai a zahiri saboda yalwar haske dake bayyana hudowar rana,idanunsa akansu duka lokacin data kaiga zira hijab d'in a jikinta,idanunsa sukaa sauka a kanta,mummunan fad'uwa gabansa yayi wanda yasa shi saurin dafe chest yana fad'in
    "Laa'ilaha illallah..!"
  Idanunsa ya d'an lumshe a hankali sannan ya bud'e su still ya sake ajiye su akanta,itanma shi take kallo coz sai a yanzun ne itama ta samu damar kallonsa ba kamar a d'azun ba da take kwance kuma lokacinma bawai yana tsaye ne a guri guda ba nd hankalinta duka a time d'in baya tareda ita,,d'an murmushi tayi masa tana had'e hannayenta duka biyu yayin da hawaye suka fara ziraro mata,cikin melodious voice nata mai kama da ana busa sarewa ta furta
   "Hak'ik'a na godewa ubangiji (S.W.T) bisa aiko ka da yayi a dai² lokacin daya cancanta,domin ka zama mace ci a gare ni,,tabbas na tabbatar ubangiji maji rok'on bayinsa ne shi yasa ya aikoka gareni,,a yau da ace baka zo ba Allah shi kad'ai ya barwa kansa sanin abunda zai iya faruwa da rayuwata,, na gode³ sosai Ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairinsa..!"
   A hankali take maganar amma yadda take ajiye kowane harafi tana bashi hak'k'in sa,kai baka ce za'a sameta a irin wannan yankin ba,,kallonta yake without yana blinking na eyes d'insa,har ta dasa aya a lokacin da kuka yaci k'arfinta,sheshshek'ar kukanta ne ya sashi dawowa duniyarsa,wanda nan take ya d'an sake lumshe idanunsa a hankali yana jin saukar wani irin yanayi a gaba d'ayan jikinsa,lokacin daya bud'esu kuwa akan su GOJE ya sake sauke su cike da tsantsar bak'in cikin irin d'abi'ar da suka so gwadawa kamar yarinya kamarta,haka nan muryarsa cike da bak'in ciki ya girgiza kai yana fad'in
  "Ku yanzun baku ji kunya ba..?? Ace kunyi k'ok'arin ketawa yarinya kamar wannan haddi..?? Me kuke nema da baza ku samu a jikin manyan mata ba sai ita..?? Tayi muku wani abu ne..??"
  
  "Yallab'ai wollahi Sarki ne ya samu tare mata hanya,,wai kawai dan ya nuna yana son aurenta,,to kawai sai aka yi rashin sa'a tsohonta yak'i yarda,,shi nefa ehh kawai mu kuma muka yi ehhh k'ok'arin k'addamar mata..!"
    Fuska yayi squeeze cikin jimami ya maimaita
      "Kuka yi k'ok'arin k'addamar mata..!? Kai baka ji kunyar fad'ar haka ba..??"
    Kai ILA ya sunkuyar da yake dama a cikinsu duk ya fisu tsoro,cike da takaicinsu matashin ya d'an sake kallonta,har lokacin ita kuwa Sabina bata fasa kukan ba,cikin tausayawa ya jinjina kai sannan ya sake kallon su GOJE yana fad'in
      "Tabbas kun ci sa'a a yau bana cikin mood d'in da zansa a kama ku a d'aure,,buh ku sani daga yau wannan shi ne zai zama na k'arshe matuk'ar kuka sake kwatantawa ba wai ina nufin a kanta ba,A'a akan koma waye lallai ne zansa a d'aure min ku,,,kun fuskanta ko..??"
     
     "Wollahi Yallab'ai bama zamu sake ba in sha Allah..!"
     Jinjina kai ya d'an yi sannan yace
     "Maza kuje ku bata hak'uri,,nd make sure ta hak'ura idan kuma ba haka ba...!"
     Bai gama rufe baki ba duka suka durkusa a gabanta fad'i suke
      "Dan girman Allah Aunty Sabina ki yafe mana,,,mun tuba wollahi,bama za mu sake ba, idan kuma har muka yi miki ko da kallon banza nema mun yarda ki sanar masa a kaimu caji ofis a kulle..!"
     A hankali Sabina dake gefe a tsaye ta kalli yadda suka zagayeta kamar zasu shige cikin k'asa dan ladabi,,idanunta ta d'an lumshe a hankali kuma ta saki d'an murmushi,,duk abunda ake akan idonsa yana tsaye a bayansu ya hard'e hannayensa bisa chest d'insa,yadda tayi murmushi sai yasa beautiful point d'inta lotsawa,shima lumshe idon ya tsinci kansa da yi sannan ya d'an yi murmushi,,aifa murmushin da Sabina tayi nan yasa ILA juyawa da sauri cikin murna ya furta
      "Yallab'ai wollahi ta hak'ura kaga ma har murmushi tayi,,dan girman Allah,idan har kana k'aunar mahaifanka kaima ka yafe mana..!"
    Saurin bud'e lumsassun idanunsa yayi,tabbas sai a lokacin tunanin sa ya dawo dai² saboda ambaton iyayensa da ILA yayi,a hankali kuma sai ya d'ago tsintsiyar hannunsa ya kafa idanunsa akan waterproof bluetooth smart anniversary watche d'insa,nan take a gogon ya nuna masa 7:40am,a hankali ya dafe kai yana fad'in
     "Ya salaam..!"
     Dan yadda ya tamawa lectures d'in yau amma sai gashi wannan uzurin ya gifta masa ba tare daya koma ba bare ya shirya ya shiga lecture d'in,d'an siririn tsaki yaja sannan ya kallesu da sauri yana fad'in
      "Ku b'ace min a nan,,kada ku sake fuskokin ku su k'ara bayyana a idanuna,,idan ba haka ba zaku ga yadda zanyi da ku..!"
    Rigegeniya suka fara yi wajen tashi,sai dai jikinsu duka yayi tsami buh a hakan sai da suka yi godiyar dole daya sake sasu suyi mata sannan kowannensu ya shiga jan jiki suka d'auki hanyar barin wajen,,,lokacin daya rage daga Sabina sai matashin nan ya d'an sake kallonta yana fad'in
      "Ina kika nufa yanzun..??"
    Duk da tambayan yazo mata a bazata dan ita kam tana can duniyar wasa da gefen hijab d'inta,amma sai bata amsa masa ba bare ta d'ago ta kalleshi,sai daya sake maimaitawa sannan ta d'ago kanta a hankali tana sauke idanunta idanunta can wani gurin daban,sannan cikin sanyin ta tace
      "Gida zanje..!"
   
   Sai daya jinjina kai yaja numfashi sannan ya ce
    "Ok..! Muje na raka ki.."

    "A'a ka barshi kawai bama saika jeba,,haka ma na gode sosai..!"
  Kallonta ya d'anyi ya tab'e baki cikin husky voice d'insa ya sake furta
  "Ba shawararki na nema ba,cewa nayi muje,,nd kiyi hankali kema,coz ba ko wane magana nake fad'a ake min musu ba..Saboda haka let's go..!"
   Ya k'arasa fad'a yana mai sake d'aure fuskar sa,,,saurin kallonsa tayi sai dai shi d'in bai ko kalli inda take ba,dan wani sabon d'aure fuskan da yayima nan take sai yasa gabanta ya shiga fad'uwa,,babu yadda ta iya haka nan bata da zab'in daya wuce bin umarnin sa,dan haka sai kawai ta wuce kan gaba shi kuma ya shiga binta a bayan ba tare da sun sake cewa ko a bane suka ci gaba da nausawa ta cikin shuke²n har zuwa lokacin da suka kai ga fita daga cikin gonakin suka sake d'aukan hanyar da zata sada su da rugar ta *MALAM SHEHU MAI DARASU.*  
   Sunyi tafiya mai d'an nisa kafin su isa ainihin castle d'in da rugar take,,tun daga nesa lokacin da suka nufo k'ofar gidansu,Sabina ta hango mahaifinta tsaye a k'ofar gidan kamar mai jiran k'arasowan su,sam bata kula da yanayin da yake ciki ba dan haka da murnarta taci gaba da nufar k'ofar gadan²,ko data isa daf da shi d'in kafin ta kai ga shigewa cikin gida nan sai ta furta
   "Babanah.. Barka da safiya,an tashi lafiya..?"
  At once kuma tana durk'usawa a k'asa fuskarta d'auke da yalwataccen fara'a,,sai a lokacin idanun baban Sabina suka sauka akan mutumin dake tsaye a bayanta d'in,ba tare da Sabina ko shi kansa matashin sun ankara ba sai kawai suka ji saukar mari wanda duka yasa su d'agowa suka bishi da kallon tsantsar mamaki...

  *Tofa..wannan shi ne farawa da bismillah,,,, ko waye aka mara haka,,Allahu a'alaam..*

#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*Our Aunty Meelat,d one n only,ever,,da girman kujeran ki👍,alkhairin Allah yaci gaba da kasancewa tare da ke da ahalinki a duk inda kike,,har kullum ke alkhairi ce a gare mu,kuma muna alfahari da kasancewa tare da ke,,ki jima kiyi k'arko,,tsawon rai mai amfani,farin ciki ako da yaushe,tare da fatan rabb ya raya zuri'ah bisa sunnah,ubangiji ya ci gaba da kare mana ke sharrin mutum da aljan,,fatanmu har kullum mak'iyan ki suyi tsawon rai suna masu ganin ci gabanki a rayuwa ciwon rai yana ci gaba da nuk'urk'usar rayukan su...💞*


*3*
_#Apologies_

Fuskarsa cike da tsantsar mamakin dalilin da yasa dattijon ya mare shi yake binsa da kallo,sai dai ya kasa bud'e baki yayi masa magana bare ya tambaye shi dalilin da yasa hakan ya faru,al'halin yasan bai masa laifin komai ba,hasalima dai yasan basu tab'a had'uwa ba bare yace ko yayi masa wani laifin before,nd a yanzun da suke tsaye shi ne farkon fara had'uwarsu da juna,,ita kanta Sabina ko data d'ago fuskarta wanda k'aran saukar marin ne yayi sanadin d'agowan nata cikin tsananin mamaki mai had'e da damuwa ta furta
"Babah..!?"
Sai dai ko kafin ta kaiga sake yin magana tuni baban nata ya d'aga mata hannu alamun tayi masa shiru kada tace da shi komai,cikin matsananciyar damuwa sai ta ja baki tayi shirun kamar yadda ya umarceta,amma kuma sai me? Sai taga Baban ya sake cak'umo saurayin yana niyyar sake marinsa a karo na biyu,,da saurinta ta matso jikin Baban ta rik'o gefen rigarsa,murya cike da tashin hankali take fad'in
"A'a Babah kada ka dake shi..Dan girman Allah kayi hak'uri ka rabu da shi,,bai yifa laifin komai ba..!"
Cikin tsananin mamaki ya waiwayawa yana kallonta ba tare daya aikata abunda zuciyarsa take umartarsa dayi ba
"Sabina wuce ki shiga gida..!"
Baffanta dake tsaye a bayansu ya ambata yana hararan sBaban nata daya cakumo saurayin,a hankali ta shiga girgiza kai hawaye suna zirarowa daga idanunta cikin muryanta mai tattare da fargaba ta furta
"A'a baffa,,bazan iya shiga ba,,dan Allah ka bawa Babanah hak'uri,,kace masa kada ya dake shi..Dan Allah.. Laifin me yayi !?"
Yadda take yi yasa dukansu daga baban nata har baffanta d'in suka k'ame a gurin tamkar wad'anda akayi sculpturing nasu suna binsu da kallon mamaki.
Kuka sosai sarki yake rusawa a tsakar gidan,yayin da matan gidan da y'an matasan samari kamarsa sai bashi baki suke da fad'ar maganganu marasa dad'i akan lamarin daya afkun,,daga can gefe kuwa ita kam y'ar dattijuwar dake zaune wacce duk abunda ake a gidan sam tak'i yarda ta kallesu bare har suyi tunanin zata tanka musu,hasalima ita ji tayi abun bai kwanta mata ba shi yasa ko kallo basu isheta yi ba,ta ci gaba da faman iza wuta abunta,,hak'uri suke ta bashi amma kamar wanda ake zugawa sam yak'i yin shirun,a haka dai da suka ga abun yafi k'arfinsu sai duk mutanen suka shiga fashewa d'aya bayan d'aya, har sai daya rage saura bai wuce su biyu ba,wato shi kad'ai da kuma wata mata dake rik'e da shi,wanda ta shiga jansa suka fara tafiya da niyyar barin gurin suna tafe tana yarwa da waccan matar magana cikin jin haushi,,har sun d'an matsa a gurin sai sarki ya faki idanun jama'a yayi wuf ya nufi hanyar fita daga gidan,a dai² k'ofar fita ya lab'e daga jikin dangar gidan yana lek'en waje fuskarsa da matsanancin farin cikin abunda ya fara hangowa,ba tare da tunanin komai ba ko AL'AMARIN zai canja yake lek'e abunsa,,lek'awarsa a dai² lokacin karaf sai suka had'a ido da shi,wanda yasa take k'irjinsa ya bada mugun sauti,haka nan ko da suka yi arba da matashin daya gama jibgarsu d'in bada jimawa ba,sai kuma ya ga Sabina tsaye tana kuka nan sai ya d'an saki murmushi dan yasan babu yadda za'ayi iyayen nasuma su yarda da abunda zata ce tunda yazo ya gama yi musu famfo,,wani killer smile matashin ya saki mai ciwo dan kuwa ko babu komai zuwa yanzun ya fahimci abunda ke kan faruwa,sai dai har lokacin yana rik'e a hannun baban Sabina dan kuwa bai sake shi ba,shima kuma baiyi k'ok'arin k'wace jikinsa daga gare shiba,yana nan tsayen still yana jiran ganin abunda zai sake biyo baya
"Ke Sabina me kike son nuna mana ne..?? Ki wuce ki shiga gida nace..!"
Kai taci gaba da girgizawa idanunta har lokacin suna zubar da hawaye,dan ita kam bata fahimci kan abunda yake faruwa ba,baffanta da yayi mata magana ko da yaga haka duk da yana cikin tsananin mamaki sai ya tsinci kansa da tambayarta
"Sabina shin kina nufin wannan ba shi ne wanda aka ce ya kama ki a bayan gari ba..??"
Da matuk'ar mamaki ta juya ta kalli baffanta da yake maganar sannan tayi saurin sake kallon sarki da yake lab'e a bayan baffan ta kuma kalli Babanta daya saka kunne yana jiran yaji me zata ce
"Me kace baffa..?? Wannan d'in aka ce ya kama ni..?? A ina aka yi haka..? Waye ya fad'a..!?"
Ajere tayi ta sakin tambayoyin ba tare data jira baffan ya amsa mata d'aya ba tana kuma kallonsa fuskarta d'auke da matsanancin mamaki,,suma kallonta suke da mamakin kamar yadda take yi musu
"Ke bana son shashancin banza,,ki fad'a mana abunda yayi miki yanzun nan,,shin gaskiya ne ya rik'e ki ko A'a..??"
Bakinta ta toshe hawaye na sake mata tsere akan y'ar fuskarta tana kuma girgiza kai,Babanta kam da zuwa wannan lokacin ya gama k'ulewa cikin tsawa ya furta
"Ki yiwa mutane bayanin abunda yayi miki kin tsaya mana shirme..Me kike jin tsoro ne..??"
Kai taci gaba da girgizawa kamar wata wace ta samu matsalar ji da magana,buh duk da irin tsawar da baban yayi mata sam ta kasa magana,,baffanta daya fara fuskantar akwai matsala nan ya matso kusa da inda ya kama hannunta,cikin tausasa murya ya kalleta tare da cewa
"Sabina ina so ki bud'e baki kiyi min magana,shin da gaske ne yayi miki wani abu..??"
Kai ta girgiza alamun A'a,,Babanta kam tuni ya gama zuwa wuya da shirun ta a lokacin,ko da ganin ta sake girgiza kai cikin masifar fad'a mai tafe da b'acin rai yace
"Dan ubanki baza ki yi magana shi ne baza ki iya ba,kike karkad'a mana kai,,mun zama sa'anninki ko..!?"

"Kayi hak'uri Baba..!"
Muryanta cike da tsoro tayi furucin
"Sabina kalle ni nan,,maza kiyi min bayanin abunda ya faru kinji ko,,ai ni na tambaye ki, dan haka kada ki ji tsoro kin ji ko..!?"
A hankali ta sake furta
"To baffa..!"
Kai ya kad'a mata sannan ya ce
"Da gaske ne wani abu ya faru dake a bayan gari...!?"

"Ehh baffa..!"
Ta ambata tana sunkuyar da kai k'asa,a fusace Babanta ya d'aga hannu da niyyar marin saurayin,baffanta yayi saurin fad'in
"A'a *AMINU* kada kayi haka,,me yasa kake son aiwatar da abunda zuciyarka ta umarce ka ne..?? Al'halin har yanzun baka tabbatar da gaskiyar abunda ya faru ba..?? Har kullum ina horonka da kafin ka yanke hukunci ka fara tsananta bincike akan komai,,ba daga an kawo maka magana kace zaka hau kayi hukunci ba,saboda na tabbatar ba ko wace magana ce ake fad'an ta take zama gaskiya ba..!"
Huci kawai baban Sabina yake amma bai so aka ce d'an uwan nasa ya dakatar da shi ba,dan yadda yaji maganar nan a yanzun bashi da burin daya wuce ya hukunta duk wanda ya tab'a masa tilon y'arsa mace da yake ji da gani da ita,wacce a kullum cikin taka tsantsan yake da rayuwarta,haka nan cike da burin ganin ya aurar da ita ga mutumin k'warai kamar yadda addini yayi umarni da iyaye su zab'awa y'ay'ansu mazaje na gari
"Kin tabbatar abunda kika fad'a min haka ne Sabina..?? Kuma abunda d'an uwanki yazo ya fad'a haka ne ya farun..??"
Kanta ta d'aga ta kalli baffan idanunta da zuciyarta cike taf da alamomin tambaya akan mene ne sarki yazo gida ya fad'a..??
"Dake nake Sabina da gaske ne wannan matashin yayi miki wani abu..??"
Wahalallen yahu ta had'iye dan kuwa ko babu komai yanzun itama ta fara fahimtar abunda yake faruwa da dalilin da yasa shi lab'ewa yana lek'en su,,wanda a tak'aice ta gano cewa sarki yazo gida ya fad'a musu k'arya da gaskiya,duk da bata san mene actual d'in abunda ya fad'a d'in ba har yanzun,sai ta sake had'iye yahu,sannan a hankali ta girgiza kai ta bud'e baki da kyar tana cewa
"A'a baffa ni babu abunda yayi min..Bai yi min komai ba face taimakona da yayi.."

"Kin tabbatar babu abunda ya faru tsakaninki da shi..??"
Ko kafin tayi magana Babanta cikin masifa ya tari numfashin baffan da cewa
"K'arya take Yaya baka ga yadda take k'ik'k'ifta idanu ba,,wato kema kin zama munafuka ko..? Har kin samu damar da zaki dunga bin samari ko *HAFSATU..??* shi kenan ai,kije ki aikata duk abunda kika so,bazan tab'a hanaki ba,amma ki sani sai Allah yayi mana sakayya ni da mahaifiyarki,,irin wahalar da muke sha akan ganin mun inganta rayuwarki,,shi kenan kije ki aikata duk abunda kika so,ni ko mahaifiyar ki babu wanda zai hana ki,,kinji ko tunda haka kika gani yayi miki.."
Cikin tsawa baffa ya kalle shi a fusace ya kira sunan sa
"Aminu..! Ka dawo hayyacinka,ka kuma san irin maganganun da bakinka yake ambata,,kada kaje garin son ka farantawa wasu ka b'atawa wasu,sau nawa zan fad'a maka y'arka ba irin wacce za'ayi ta kawo maka tsaigumi akanta bace ka hau ka zauna..?? Me yasa baka jin magana ne kai kam,,yanzun idan da ace MALAM na raye ai babu yadda za'ayi nayi maka magana kaki saurarena,amma saboda yanzun bani da daraja shi yasa nake fad'a maka kana tsallakewa,shi kenan kaje kayi dukma abunda kaga dama kaji,karka fasa kaima..!"

A hankali baban ya sauke kai k'asa alamun bai ji dad'in furucin yayan nasa akansa ba,cikin girmamawa da ladabi kuma ya furta
"Kayi hak'uri yaya,amma ni gani nayi ai babu yadda za'ayi d'an uwanta ya k'irk'iro irin wannan maganar ya fad'a mana.."

"Koma dai mene ai sai dana fad'a maka mu fara yin bincike muji ko..??

Please Login or Register in order to submit comment