Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*





PAGE 1




Wata matashiyar buduruwa na hango a zaune akan tabarma,tana ta guga,dagani kayan mijinta take gogewa Muhibba kenan,wacce bata fi wata Biyar da aure ba,gidanta madaidaicin gida ne,dan wanda take aure ba mai k'arfi bane,Palo d'aya ne da d'akuna biyu,sai kitchen da toilet,Mijinta Abdulmajeed Mallamin Makarantar primary school ne,dai dai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah,auren soyayya suka yi,Muhibba tana da kirki sosai ga kyauta,tsafta awajenta ba a magana,Dan inka shiga gidanta kamar karka fito sabida kamshi da tsafta da gidanta ke dashi,kayan mijinta data wanke take gogewa taji ana kwankwasa gidan,d'aga murya tayi tace "Waye"? Ji tayi an k'ara kwankwasa wa batare da anyi magana ba,mik'ewa tayi ta nufi k'ofar Dan taga wa ke kwankwasawa,doguwar Riga ce a jikinta tayi parking ba dankwalli akanta,daga bayan k'ofar ta Dan tsaya ta bud'e k'ofar tana leko da kai Dan taga waye, wani irin fad'uwa gabanta yayi jikinta ya d'au rawa sakamakon tozali da tayi da wata farar mata mai tsayi,idonta manya manya girmansu ya wuce misali,tsayinta ma yayi yawa, farinta wani irin d'aukar ido ya ringayi,gashin girar ta jajaye,haka ma leb'enta,murmushi wanan matar tayi mata tace"kiyi hakuri na zo na takuraki da kwankwasa k'ofa Dan Allah fitsari ne ya matseni shine nakeso ki taimaka min inyi dan bansan kowa anan ba," Muhibba tunda tafara magana gabanta ya tsananta fad'uwa ta kuma kasa addu'a dan matar yanayinta abar tsoro,Dan zata iya cewa tunda take ba ta tab'a ganin mai irin tsayinta ba,d'aurewa tayi tace cikin rawar baki " lah bakomai shigo kiyi" da sauri matar ta shiga ciki,ta tsaya atsakar gida,Muhibba kuwa kamar tabar gidan da gudu Dan wani irin tsoro ne ya rufeta,gashi tana so tayi addua ta kasa,d'aurewa tayi ta shiga tayi hanyar da band'akin yake tace mata "bismillah ga band'akin akwai ruwa aciki" gani tayi matar ta nufo ta kamar ba tafiya take ba turota ake, ware ido tayi tana kallonta cikin tsananin tsoro da tashin hankali,dasauri tabi k'afarta da kallo taga babu alamar k'afa illa ma doguwar Riga dake jikinta kawai dake Jan kasa,jikinta ne ya d'au rawa kafin tayi yunkurin yin wani Abu wuf matar ta shige band'aki ta rufo k'ofar,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" muhibba tace cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba hanyar waje tayi da sauri taje ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallon band'akin shiru shiru matan nan bata fito ba,tsoro ne ya k'ara rufe Muhibba ta d'aga murya tace " Baiwar Allah har yanzu baki gama ba" shiru taji,ba ayi magana ba,hakan ne yasa tayi waje da gudu ta nufi gidan dake kallon gidanta,gidan surayya makociyarta ce suna mutunci sosai da ita,bubuga gidan taringayi da sauri tana kallon gidanta,Surayya kin bud'e k'ofar tayi sai data ce "Muhibba kin tabbata kece"? " nice mana yi sauri ki bud'e min"bud'ewa Surayya tayi ahankali ta leko da kanta itama kana ganinta kasan a firgice take,da sauri Muhibba ta shige kafin tayi magana surayya tace " kema kinganta ko" ? Cikin tsananin tsoro Muhibba tace wacece"? Cikin sauri tace " bakiga wata farar mata mai kama da aljana ba,gidan nan tazo wai na taimaka mata fitsari takeji tuni na rufo k'ofata dan wlh baki ganta ba kamar ba mutum ba" tunda surayya tafara magana jikin Muhibba yafara rawa gabanta in banda fad'uwa babu abinda yakeyi d'aurewa tayi tace " Innalillahi wa inna ilahi rajiun Surayya na shiga uku na lalace,wlh tazo gidana tunda ta shiga band'aki taki fitowa har yanzu, nashiga ukuna D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO zan janyo wa kaina balai Dan Allah zoki rakani inga mai take yi a band'aki tunda zu,Wani irin tsalle surayya ta buga tayi gefe tace " wa tab bazan iya rakaki ba,wane tsautsayine ya kai ki kika barta ta shigar miki gida,wlh wanan da gani ba mutum bace Aljana ce," ai tun kafin Surayya ta rufe bakinta,Muhibba ta d'ora hannu aka taringa kuka tana ta shiga uku ta lalace " Yanzu surayya ya zanyi wlh tana cikin band'aki har yanzu bata fito ba," sallati Surayya tayi tasa hijabinta tace "muje in rakaki Allah yasa ba aljana bace.
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*





PAGE 2




Rik'e hanun juna sukayi suka nufi gidan gabansu in banda fad'uwa babu abinda yake,Dan Muhibba har wani gumi take,suna zuwa k'ofar gidan,Surayya tayi sauri ta koma bayan muhibba,muhibba ita kuma taja da baya da sauri ta juyo tana kallon surayya "Haba Dan Allah surayya mai yasa kike min haka ne ko bazaki rakani bane"? Muhibba tace cikin rawar baki dan kiris take jira ta zuba aguje sabida tsananin tsoro,Surayya cewa tayi " kijiki da wani zance in bazan rakaki ba zan biyoki ne,kawai dai tsoro nakeji dan wlh Matan nan dak'yar in ba aljana bace kinga tsayinta kuwa",katseta Muhibba tayi da sauri tana k'ara ja da baya tace "haba Surayya ya kike kuma tsoratamu Dan Allah muje ki rakani insha Allahu ba aljana bace,muyi addua kafin mushiga ciki," na yarda zamu shiga ciki amma ke zakiyi gaba in biki abaya, Surayya tace tana k'ara lab'ewa abayan Muhibba,hanunta Muhibba ta rik'e gam, suka fara adduoi sai sun je zasu shiga sai su dawo aguje,sai da sukayi haka sau uku ana hud'u Muhibba ta d'aure suka shiga gidan,a bakin k'ofa suka tsaya suna kallon band'akin,yana nan arufe kamar yanda yake,cikin tsananin tsoro Muhibba tace " baiwar Allah Dan Allah ki fito har yanzu baki gama bane karki cuceni D🅰G🅰 T🅰IM🅰KA miki" motsi suka jiyo daga band'akin sukayi waje dagudu,
Surayya kuwa cikin kiftawar ido ta shige gidanta tana k'ok'arin rufo k'ofa Muhibba ce tayi saurin shigewa tace " Surayya wai mai haka ne mai yasa
Kika gudu kika barni ai da kin tsaya munga fitowarta inkece kinsan bazan miki haka ba ko" d'aga wuya Surayya tayi tana kallo k'ofar gidan Muhibba tace "kiyi hak'uri Muhibba wlh tunda naga wanan matar na rasa nutsuwata,wlh wani irin tsoro nakeji kinga bari mu samu namiji ya shiga ya dubo mana ita" kuka Muhibba ta fashe dashi tana " innalillahi wa inna ilahi rajiun nashiga uku ni Ummi( sunan da iyayenta suke kiranta dashi) D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na janyowa kaina masifa," tsayuwar lifan a k'ofar gidan Surayyan ne ya katse mata maganar da takeyi,Ayuba mijin Surayya ne ya dawo,da sauri Surayya tayi waje ta gayawa Mijinta abinda ya faru sallati yayi ya kalli Muhibba dake tsaye abakin k'ofa tana ta kuka,tambayarta yayi yanda akayi,ta kuma bashi labarin abinda ya faru, addu'a yayi aransa yace su biyoshi abaya,tsoron da sukeji ya d'an ragu sakamakon sun samu mai taimaka musu,Muhibba tana daga bayansa Surayya kuma tana daga bayanta ahaka suka shiga gidan,Band'akin ta nuna mishi ya nufi band'akin yana addu'a su kuma suka tsaya daga bakin k'ofa suna kallon band'akin,in banda fad'uwa babu abinda gaban muhibba keyi,"Auzibikalimati tamaaa•••••• Ayuba ya karanta har karshe ya tura k'ofar ahankali tura k'ofar yayi gabad'aya yaga ba kowa,juyowa yayi ya kalli su Muhibba dake Neman sakin Fitsari a wando sabida tsananin tsoro,durk'ushewa tayi a lokacin data ga ba kowa a band'akin kuka ta fashe dashi tana nuna band'akin " Wlh Aljana ce ta shiga band'akin nan,ta ina ta fita,oooo ni Ummi D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na Janyo wa kaina" Mijin Surayya rufo k'ofar band'akin yayi,yayi hanyar waje, suka bishi dasauri,Dan Surayya har tayi gaba,Ayuba tsayawa yayi yacewa Muhibba "ki kwantar da hankalinki babu kowa a gidanki watak'ila ma idonki ne yake gane miki kinga wata ta shiga band'akinki" dasauri Surayya ta katse shi tana "Wlh Ayuba Aljanace Nima naganta da idona Dan gidana tafara zuwa,Ina ganinta na rufe k'ofata Dan wlh Baka ganta ba kana ganinta kasan ba mutum bace,bansan tsautsayin daya sa Muhibba ta barta ta shigar mata gida ba"jikin Ayuban ne yayi sanyi daya ji abinda Surayya tace, Muhibba kuwa ta k'ara rushewa da kuka tana " Allah yasani T🅰IM🅰KONT🅰 nayi bansan Aljana bace ni yanzu mai zancewa Abdul,gashi ya kusa dawowa ko girki ban d'ora ba" Ayuba kwantar mata da hankali yafa yi yana "karki damu muhibba ai Allah yaga zuciyarki T🅰IM🅰KO kika yi niyyar yi,Insha Allahu Allah bazai bata ikon cutar dake ba",juyawa yayi ya kalli Surayya dake zare ido yace mata "jeki rakata ta d'ora abincin lokaci na tafiya,", da sauri Surayya taja da baya "Ayuba wlh ni tsoro nakeji Dan baka ga matar bane" wani kallo ya watsa mata taja bakinta tayi shiru,"wuce ki rakata bana San shashanci ke kin isa ki ga aljana da idonki" "Nima fa ban d'ora girki ba" "eee wuce kije zan d'ora mana ai Nima na iya girkin" Ayuba yace yana janyo hanunta,Muhibba ita dai tana tsaye,tana kallonsu,a zuciyarya kuma tana tunanin yanda zata kwashe da Abdulmajeed Dan yana da tsatsauran raayi Dan yasha yi mata warning akan kwashe kwashe,Dan lokacin da take amarya yaran makota haka suke cika mata gida,ita kuwa dayake ba ruwanta murna takeyi ta Shiga tsakiyarsu suyi ta hira sai da Abdulmajeed ya taka mata birki tukuna,dan ko kawayenta daina zuwa gidanta sukayi Dan sunce Mijinta baya San mutane,Yanzu idan ya dawo ta bashi labarin abinda yafaru batasan wane irin mataki zai d'auka akanta ba,"ki wuce mu tafi ki d'ora girkin" Surayya tace a lokacin da ta tsaya a gefen Muhibba,gaba Muhibba tayi Surayya ta bita abaya,sai da tafara lek'a band'akin taga a rufe yake tayi sauri ta shiga gidan,tana addu'a k ayan data goge tafara kwashewa ta kai d'aki ta nad'e tabarmar data shimfid'a tasa abayan k'ofa,ta rufo d'akin,Kitchen ta shiga da sauri ta kunna risho ta d'ora ruwa,duk abinda ta keyi idonta na kan band'akin Surayya dake tsaye abakin k'ofa itama band'akin take kallo Dan jira take taji motsi ta d'iba aguje,Muhibba ruwan da ta d'ora ko zafi bai yi ba ta wanke shinkafa ta zuba,Dan gabad'aya a tsorace take,Allahn daya taimaketa tun safe tayi miyarta,Salad da tumatir ta d'auko Dan ta yanka,Surayya motsi taji asaman kwanun gidan tayi waje da gudu,Muhibba wurgi tayi da wuk'a da salad d'in Hanunta itama tayi waje da gudu,atsakar gida ta Tarar da Surayya tana maida numfashi Ayuba dake k'ok'arin d'ora musu jellof d'in taliya na tambayarta mai ya faru,ce mishi tayi motsi taji asaman kwanu,tsaki yayi yace ta wuce su koma Muhibba ta gama girkin,k'in tafiya tayi atakaice sai da Ayuba ya rakasu ya tsaya abakin k'ofa,Muhibba tasamu ta gama abincin,aranar Dan turaren data ke yiwa gidan bata samu tayi ba,ballantana azo ga wankan da takeyi tayi kwalliya ta jira dawowar Abdulmajeed kamar yanda ta saba,gidan ta kulle bayan ta gama abincin ta tafi gidan Surayya Dan ta jira dawowar Abdulmajeed Dan bazata iya zama a gidan it a kad'ai ba, Dan taga alamar Surayya a takure take.













Ana kiraye kirayen Sallahr Magriba Abdulmajeed ya dawo,Muhibba fitowa tayi daga gidan Surayya Dan tagane k'arar Lifan d'inshi,binta yayi da kallo a lokacin daya ke sauk'owa daga lifan d'in,had'e rai yayi yace " ke kuma mai kike jeyi a gidan mutane da magriban nan,share tambayar daya yi mata tayi tace " Sannu da zuwa" "tambayarki nake mai kika je yi agidan mutane da magriban nan kinsan na hanaki shige shigen nan banaso," itama had'e rai tayi tace " yanzun nan fa na shiga gidan abinci na kai mata dan batajin dadi" tsaki yayi yace "uwar San gwaninta ni bud'e min k'ofa na Shiga da machine d'ina,nufar k'ofar tayi gabanta na fad'uwa sai addu'oi takeyi a zuciyarta,Shigar da lifan d'in yayi ta bishi abaya,sai da yayi parking a tsakar gida,ya nufi inda generator yake ya tayar,Muhibba tunda suka shigo ta tsaya daga bakin k'ofa tana kallon
Band'akin Dan gani take kamar matar tana ciki,Abdulmajeed ganin ta kame awaje d'aya ne yasa ya zuba mata ido, " keeeee" wani irin tsalle tayi ta nufeshi a firgice,"kallon mamaki ya bita dashi yace ", ke lafiyarki kuwa mai yake damunki?dasauri ta daidaita nutsuwarta dan bataso Yagane halin da take ciki,tace "bakomai mai kagani," binta ya k'arayi da kallo tunda daga sama har kasa,yace " Kin ganki fa da kayan dana fita nabarki sune ajikinki har yanzu,gidan ma wani iri ba kamshin daya saba well ke kika sani tunda kince ba komai,zuba min ruwa inyi wanka zafi nakeji" Abdulmajeed yace yana shiga d'akinsa,da Sauri tabi bayansa Dan wani irin tsoro ne ya rufeta dayace asa mishi ruwa a band'aki,Abdulmajeed juyawa yayi yana kallonta a lokacin da yake k'ok'arin cire rigar jikinsa, "wai bakiji mai nace bane ki zuba min ruwan zanyi wanka,wai yau Muhibba mai ke damunki ne?", juyawa tayi, tayi hanyar waje gabanta na mugun fad'uwa,adduoi taringa yi ta nufi band'akin Dan ta d'auko bokitin wanka, tura k'ofar tayi bakinta d'auke da addu'ar Shiga band'aki, wani irin razananan k'ara ta saki tayi baya da gudu sakamakon ganin rigar da matan nan ta sa atsaye,babu alamar mutum acikin rigar.
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l


*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*




*TRUE LIFE STORY*





PAGE 3




K'aro suka yi da Abdulmajeed daya taho band'akin a guje,kankameshi tayi sosai tana nuna band'akin in banda rawa babu abinda jikinta ke yi,"ke Wai mai yake damunki ne menene acikin band'akin? Abdulmajeed yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,k'ara kankameshi tayi tana nuna band'akin,gaba d'aya ta firgice,tsaki yayi yace " wlh wani sain idan kika yi Abu kamar a rufeki da duka,ni cikani inga abinda yake cikin band'akin,yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,ina ai k'ara rungumeshi tayi gam tana kuka sai gumi take,haushi ne ya rufe Abdulmajeed daya ga taki magana sai nuna mishi band'aki take,yakice ta yayi da k'arfi daga jikinsa ya nufi band'akin Muhibba ta saki wani k'ara ta bishi aguje ta k'ara rungumeshi,adai dai lokacin daya bud'e band'akin yana k'arewa koina kallo,babu abinda yagani daya wuce butocin data dura Ruwa aciki,sai mudubin dake jikin bango,tsaki yayi ya d'auki bokitin wankan,Muhibba kuwa tana mak'ale abayansa,janyota yayi ta dawo gabansa yace " Muhibba Wai yau mai yake damunki ne ko dai gamo kika yi?Yanzu menene a cikin band'akin nan daya baki tsoro,banasan irin wanan wasan Sam ya kamata ki sani,idan ina cikin mode din wasa kin sani, idan bana cikin mode d'in wasa ma kinsani,dan haka in wasa ma kike min ki daina banaso"magana take sanyi amma inta tuna murd'adden Halin Abdulmajeed sai ta fasa dan ita kanta wani sain tsoronshi take ji dan har mamakin yanda akayi ta aureshi take,duk da yana da wuyan sha'ani wani sa'in dan akwai shi da tsare gida,wuceta yayi yaje ya debo ruwan wankan yakai band'akin,ganin yana k'ok'arin rufo k'ofar ne yasa tayi sauri ta k'arasa band'akin dan wani irin tsoro ne ya rufeta,had'e rai yayi yace " menene?" Hawaye ne ya hau zubo mata tace "dan Allah bari na jiraka a band'akin kayi wankan tsoro nakeji wlh" ayanayin da tayi maganar ne yasa yaji tausayinta yace to "k'aro mana ruwan wankan sai muyi wankan tare dan dama bakiyi wanka ba,ni yau bansan mai yake damunki ba" da Sauri ta kinkinmo bokitin ruwan ta shiga band'akin dashi,jikinta sai rawa yake Kalle kalle tafara yi dan gani take zata iya ganin wanan matar,Abdulmajeed brush ya farayi,hakan data gani ne yasa itama ta matsa jikin mad'ubin dake rataye aband'akin ta zura hannu a d'an kwandon dake mak'ale ajikin mudubin dan ta d'auko brush d'inta da MacLean itama tayi brush,kamar cewa akayi ta kalli madubin,matar nan ta hango a mudubi tana tsaya ajikin bango tana mata murmushi hakoranta amadadin farare jajaye ne,wani irin gigitacen k'ara ta saki ta zube a band'akin a sume,sallati Abdulmajeed yayi ya kinkimeta yayi waje da ita, a d'aki ya kwantar da ita, ya debo ruwa yazo yana yayyafa mata,ajiyar zuciyar tayi ta bud'e idonta ahankali,kuka ta fashe dashi ta rungume Abdulmajeed tana "Abdul na shiga uku na lalace D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na janyo wa kaina masifa laifine dan na taimaketa,meyesa take San cutar dani" duk maganar da take kuka take jikinta na rawa,Abdulmajeed d'agota yayi yana share mata hawaye yace " Muhibba mai ya faru wa kika taimakawa? Ki fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan ni ina dawowa nasan ba dai dai kike ba,dan gabad'aya a firgice kike" tunanin Muhibba ta fara yi na ta fad'a mishi gaskiyar abinda ya faru,wani tunani tayi kwanakin baya wasu 'yan mata sun zo lokacin Abdulmajeed yana nan, 'yan matan suka ce ta taimaka musu da ruwan sha,shigowa tace suyi tayi musu jagora har palo,ta debo musu ruwan suka sha daga nan kuma hira ta b'arke musu kasancewar mata akwai saurin sabo,suna cikin hirar Abdulmajeed ya shigo yace su fita su bar mishi gida,jiki na rawa suka bar gidan,aranar Abdulmajeed kwana yayi yana mata fad'a kamar ya daketa,Ya kuma ce mata duk lokacin da ta k'ara barin bakon mutum ya shigo masa gida,sai ya d'auki mumunan mataki akanta,da wanan tunanin tak'i gayawa Abdulmajeed gaskiyar abinda ya faru,Abdulmajeed ganin tayi shiru tak'i magana ne yasa yaji ransa na b'aci wani irin tsawa ya daka mata yana " ina tambayarki kin yi shiru wa kika taimakawa yake Neman cutar dake" jikinta ne ya hau rawa tsoron Abdulmajeed ya rufeta magana tafara yi tana kuka "wata tsohuwa ce dazu tazo bara tace na taimaka mata da sadakar abinci,shine na bata,ta tafi,tunda ta tafi take tsoratani duk Inda nayi sai na ganta"wani mugun tsaki yayi ya mik'e "Dana San abinda kika yi kenan wlh ko saurarenki ba zanyi ba badai bakya jin magana ba ki cigaba watak'ila ma aljana kika taimakawa,ke gaki uban yan San taimako,hanyar waje yayi ta bishi da gudu,tana tsaye a band'akin yayi wankansa ko kallonta bai yi ba,itama cire kayanta tayi dasauri ta watsa ruwan duk abinda take yi idonta a rufe dan gani take inta bud'e idonta zata iya ganinta,a tsakar gida ta k'arasa sa towel dan Abdulmajeed fitowa yayi ya barta a band'akin,alwala tayi tabi bayan Abdulmajeed daya shige d'akinsa yana shimfid'a sallaya,doguwar Riga tasa ta zura hijabinta ta tsaya daga bayansa,sai da suka yi sallar magriba kafin suka yi isha,Muhibba addua ta ringayi a sujadar karshe tana addua'r Allah ya rabata da sharrin matar da ta taimaka wa,Abdulmajeed Palo ya nufa bayan sun shafa,biyo shi tayi da sauri ko hijabin jikinta bata cire ba, a tsakiyar palon ya zauna inda ta jera abincinsa,zama tayi ta ta d'auki plate tafara zuba abincin jikinta sai rawa yake dan har yanzu tana ganin fuskar matar a idonta,ajiye plate d'in tayi a gabansa bayan ta zuba mai abincin,bismllah yayi,yafara cin abincinsa Muhibba kuma ta zauna tayi tagumi tana hawaye,"ke bazaki ci abincin ba kenan"? Abdulmajeed yace batare da ya d'ago ya kalleta ba,Share hawayen daya zubo mata tayi tace " a koshe nake bana jin yunwa" Abdulmajeed d'agowa yayi ya kalleta ya ajiye cokalin Hanunsa,yace," Wai Muhibba kukan mai kike yine,wani ne ya aike ki bawa tsohuwa abinci,ke kika fi kowa San kiyi taimako,haka kika ga sauran makotanki nayi,ban hanaki taimako ba amma na fad'a miki kinsan irin wayanda zaki na taimakawa dan tun daga lokacin da Aunty Ainau (yayarsa) ta bawa Almajiri sadaka ta kamu da rashin lafiya mai tsanani sai da akayi dagaske aka gano Ashe almajirin nan ba mutum bane Aljani ne,Ashe kud'in nan da ta bashi sadaqa dashi ya ringa cutarta sai da aka runga adduoi ana sauk'ar qurani kafin ta samu lafiya,wlh tunda ga lokacin nake tsoron in taimakawa Wanda bansani ba,dan kai da zuciya d'aya za kayi taimakon amma akarshe Wanda ka taimakawa ne yake cutarka shiyasa nake hanaki kwashe kwashe," tunda ya fara magana taji wani tsoro ya kuma rufeta,matsawa tayi kusa dashi da sauri tana " Abdul yanzu ya zanyi wlh bansan ba mutum bace"tace tana fashe da kuka,"ki kwantar da hankalinki kiyi Addu'a insha Allahu,Allah bazai bata ikon cutar dake ba,this would serve you a lesson next time zaki San irin wayanda zaki ringa taimaka wa,yanzu dai ki zuba abincin nan kici sai na raka ki kiyi alwala kizo ki kwanta,"Abdulmajeed yace yana bud'e kular abincin,dak'yar taci cokali uku ta ce mishi ta koshi,kwashe kwanukan yayi da kansa ya kai kitchen, yace mata tazo tayi alwalar,alwala tayi a tsakar gidan kanta a sunkuye dan gani take inta d'ago zata iya ganin Matan nan,d'akinsa ta nufa dasauri ta rufo k'ofar,dan Abdulmajeed har ya kwanta,shiryawa tayi cikin kayan barci,ta fesa turare ta kwanta agefensa kamar zata shige jikinsa sabida har yanzun a tsorace take,tashi yayi zai kashe fitilar d'akin tayi sauri ta rik'o shi "dan Allah Abdul karka kashe wutan d'akin wlh tsoro nake ji" wani kallo ya watsa mata yace " kin tab'a ganin nayi barci fitila a kune,kashewa zanyi dan bazan iya barci ba ina barshi a kune,ke kika sa tsoro aranki amma ina gefenki mai zai tsorata ki,"sauk'a yayi ya kashe fitilar d'akin tayi sauri ta runtse idonta da k'arfi dan tuni duhu ya mamaye d'akin,yana kwanciya ta rungumeshi gam,shi kuwa ya lalubo bakinta ya fara kissing d'inta,duk abinda yake idonta a rufe yake gam,ko kwakwaran motsi bata yi,shi kadai yayi kidansa yayi rawansa,sai wajen k'arfe biyu ya k'yalleta aikuwa nan da nan barci yayi awon gaba da ita, wajen k'arfe hud'u ta juya da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment