Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin m b yace zayadinga turo sani sale yana kula da aikin kodayatafi inma anabukatar wani abu sajan dinnezai kawo yayi musu alheri yatafi baibar kauyanba saida yakoma yayi sallama damu indayakawo kudi yabaiwa baba yace kadinga sawa jidda tana sayomaka lemo da nama kanaci kakara murmurewa yadubeni kicigaba da hakuri dakula dashi kema inanan inanazarin taimakon dazanmaki nace to nidai nafison nayi karatun addinina kobansamu nazamaninba yayi murmushi yafita nataso nabiyoshi inatsaye akofar gidanmu yashiga mota saida yajuyazai tafinatuna natsaidashi da hannu yatsaya naciro agogon daga zanina indana adanashi nace gashikabawa bakon gidan maigari yayi shiruyana sontuna wanene haka nace damuka gamagyara dagin baba zayawanke hannuwansa shine yace inrikemasa saikuma yamanta lokacin yagane wanake nufi yace oho sajan sani sale nace damahaka sunanshi yayi murmushi taredacewa eh ammake mekikasa masa ina dariya nace bakwan gidan maigari yasake murmusawa yace nikuma dan birniko kekumafa nakarkatar dakai nace yar kauye yaja motarshi yatafi yana murmushi cikin zuciyata nace shi inaga baya dariya saidai murmushi lokacinda yashiga gida shidda saura husna tadawo daga makaranta kenan tazo tatareshi taredayi masa sannu dazuwa sukashiga cikitare tanayimasa tambayar inayaje haka takalminsa duk tabo yace daga kauye gurinsu haja daidai lokacin basma dakekwance cikin kujera tana kallonsu tana fara a tatashizaune tadubi m b dama kauyekaje yazauna kusada ita su haja sunagaishsheki tayatsina fuska bataredata amsa gaisuwarba tace mekajeyi yafahimceta sosaibatason mutan kauye yace niyashafa abinda najeyi yatashi yayiciki basma tabatarai
[29/09 12:45 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito

34.......Tadubi husna wanilokacin saizuciyata tayita rayamin cewa zanyi nadama nangaba akan auran bello husna tazauna inda yatashi tadafata taredacewa sobome kikacehaka talumshe idanu hawayenda sukacika indanunta sukazubo tace bello komainashi rufarufa yakemin saiyayi tafiya bansaniba nibanida darajar dazaicemi zanjewaniguri husna tace husna tarike hannunta taredacewa anty basma kifahimci wanene brother bayason hayaniya kuma yanada zurfinciki yandabaya shiga rayiwar wani haka bayason ashiga tashi nibance zanshi rayiearshiba atilis yacemin zanyi tafiya husna tace kilakuma saboda abindayafarune bayafada haryanzu sainangaba idankunko ma zamasosai babuzargi atsakaninku m b wanda kejin dukmesuke fadaya fito daga dakin yakalli basma yace kingirmi husna sosai ammataki tunani gashi tahango abinda yakamata acekin gano inanufin kisanwaneneni menakeso mekebaniso dahalin da mukeciki yanzu dakuma wanda zamushiga nangaba
Basma tataso tazokusa dashi takwantar da kanta akafadarshi nafahimta amma inzakayi tafiya kafadamin hakama inzakadawo yajuyada itagabanshi taredacewa mazan dakikaga insunyi tafiya sunadokin sanarda matansu cewagasunan dawowa tosunasa ransamun tarbatamu samman inanufin delicious tadagakai tadubeshi damuwarka kenan abinci ammakaki samomana kuku yace hakanan zamuyita maneji inmunje indanasamu aiki masamu masu aikin acan husna tamike tanufidakin basma wanda yazama natatunda basma dakin m b take kwana kangado tafada tareda zube takardunta kan gadon rigingine takwanta aranta takeraya cewa Allah yasa bilal dinta yazama kamar bello taban garan soyayya tadtakula yasan soyayya bello amma inkaganshi hakazaka zatacewa mace bata ishehi kallobama balle yasaurareta donkoyashe adaure yakegashi dara ayi nabala i don inyace abuto garama kahakura don inkaki kainezakasha haushi doshikam bazaicanzaba muskiline gakamunkai kota ina dan uwannannata yayi wayartace takatseta gazatonta bilaldintane ashema hajiyartace tadaga tasoma gashsheta hajiyar bata amsagaisuwartaba tace ancemin kinagida su bello husna tace am hajiya gidanmu bakowa

Inayawan tunaki da safina shine dady yace indawo gidansu anty basma hajiya tace lallai husna bantabaganin marakishin mahaifiyartaba irinki dukfadin kano kirasawanda zaigurinsa kizauna saiwanda yaraba auran uwarki da ubanki
Sukatozarta uwarki akotu tace to hajiya yaya zanyini hajiya tace kitahonan abuja karatu inkasar kikesonbari zakiyi dadynkuma dayanuna sankai yakai bello waje yayi karatu nahakura ba aganiba tonagaya miki kitahonan dady naku aibaikai kwatannawa mahaifin akudiba husna tace hajiya kiyi hakuri dady bazaibari inzoba takatseta dacewa wato tambayarshi zakitsayayi sushafa kawaisuji bakyanan ainima inada hakki kanki husna tarasa mezatace itadaiko lokacinda mamansu take gidansu intamatsa musu sujehutu kukatakeyi batasonzuwa saboda sunayara in hajiyar takaisu su uncle nasir saisuyi tamasu wasan banza sunacire musu pant kumadata fadawa hajiyar saitakaryata donhaka batason zuwa iyaye mata muyihattara mulura da yaranmu mata komaikusancinki da namiji kadakisakar masa yarki sakak komai kankantarta Allah yashirya manazuri a hajiya tace kinyishiru kokinanufin sunfinine

Dady kansa adaure yace bangane nufinkaba inkadubi kesdinmu da hajiya shiwa kawai dady ya isa misali irinhujjojin danakawo da shaidun dana kawo dakuma irin hukuncin da alkalin yayanke bai dace ace hajiya shiwa tafito yanzu ba kwatakwata kwananawa yadan dakata kafin yacigaba dady irinaduk bazasukai labariba akasar nan dominbazanyi aiki da cinhanci ko cin amanaba yaciro hannun shiwanda akaharbeshi daga riga yanunawa dady dubiwannan da acikine ko akirji dayanzu nazama

Dayanzu nazama dan gida akiyama dady yazaro idanu garin yaya yayi murmushi donkawai nace bangoyi bayan zalunciba donhaka dady inason ka kwantar da hankalinka kamin addu a toshikenan muhammadu Allah yayi maka albarka yasakaje cikin sa a kadawo cikin sa a saidaizanyi rashinka kusadani sannan yabatun maidakinka kuma yajidadin batun namahaifinsa cikin murmushi yace zanfaratafiyane ingayanayin gurin sannan inzo intafidasu harmada husna dady yace tosu dawonan gidan tundanima gidan ya isheni bakowa saiyan aiki sannan inkuntashi tafiya banda husna saboda itama alhaji bashir yayimin tadin auransu da dan wansa bilal ninenace sudan saurara tagama karatu m b yace shikenan Allah yasa alkairi dady yace amin sannan yace yauwa gawadannan takardun katafidasu wajanka ka adanasu duk wadannan abubuwan dasuka faru sabodasune bamutaba zamanayi makabayani gamedasuba m b yashiga dubatakardun dakidaki hannayen jarine mahaifinnasa yazuba harguda uku
[29/09 5:27 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
35....
Daya akudu daya anan arewa dakuma aturai nan america yadago idanunsa yadubi mahaifin nasacike dazargi sannan yace dady inakasamu wadannan makudan kudin dady yafashe da dariya sannan yace muhammadu kenan kasandaini cikakken bakanone ba aikin kwamnati natsayamawaba inakasuwanci inkakula zakaga ananangida nasaka hannunjari dashekara shidda sannan nasaka awaje yacigaba tareda ciro takardun yana nunamasa wannan itace ta waje lokacinda nayi ritaya daakudin sallamata da ribar wasukayayyakina nahada nasaka wannan hannunjarin haryanzu m b kallonsa yakea tamkar baigamsu da batunba danhaka dady yamike yanufi dakinsa diyari yadakko yamikawa dannasa gashi kajedashi gida kaduba dakau kwashe takardun kajeka adanasu yace to dady saimunyi waya
Zankawosu basma din yace to sukayi sallama dukdayasi abinda mahaifinnasa yafadi gaskiyane ammayanaso yagamsu cikindare ko ince farkon dare yanazaune yana yanakaranta duk abinda dan littafin boye sirrikan yakunsa anannema yaga haduwar mahaifinsa da mahaifiyarsa harzuwa rasuwarta dahalinda dady yashigalokacin sannan yaga haduwarsu da hajiya shiwa harzuwa randa yasaketa wato a kotu sannu ahankali haryafada kan bayanan dukiyoyinsa ayyikan dayayi kalar kasuwancinsa harzuwa yanzu yanumfasa cikeda gamsuwa lallai dadynnasa tunda yasanmeyakeyi komainasa cikintsari gashikuma dukiyarsa maitsafta saidaizaya bashishawara yadawoda dukiyarsa cikin gida maimakon waje sannan babu abinda yaburgeshi cikin dan littafin kamar indayace hajiya hairo nagar tacciyar macece wadda hartakoma ga ubangijinta yana alfahari da ita domin samun irintasai wanda Allah yayiwa baiwa kodaya watsoruwa yakwanta yanatunanin lallai mahaifinsa sunyirayiwa maikau inama zaisamu cikakken tarihin zamansu basma tayijuyi tareda laluboshi nantake yamatsa kusada itayasake rungumota tareda jamusu bargo yanason basma somaitsanani inyanamanneda itasaiyadinga jintamkar yadiyeta donso itamanata bangaran hakane tanason bello fiyeda kanta tayarda dashita amince dashi tareda mikamasa rawuwarta musamman yanzu dayazama shine uwa kuma ubanta hakannan danginta
Ranar dazaitafi tashin darezasuyi dohaka misalin shabiyu narana yakwashesu zuwagidansu dady yayi sallama dasu basma ce kata faman batarai suyomasa rakiya harwajan mota husna tajuya takoma cike da kewarsa basna tajingina kanta dajikin motar cikin damuwa tunjiya yake aikin lallashi yabude motar yajawotaciki yamannata da kitjinsa haba basma saikace yaunenasoma tafiya nabarki gawaya kudayaushe munatare dazarar nagagurin zazomutafi dakyar yalallasheta tahakura tafito shikuma yaja motarshi yatafi tarazasu tashidonhaka tun tarasaura sajan sani yakaishi filin jirgi cikin sallahun dabarmasa harda gininsa nakauye donyace inyazocan zaidinga sauka da iyalansa sannan yamanta da batun jidda konace abin yashige masa saidasuka tashisunmayi nisa atafiya wato asamakenan sannan tafadomasa saida gabansaya fadi yajingina bayansa da kujera yanatunanin cewa sallahun jidda shine abunafarko azuciyarshi dazaya barwa sajan saigashi yamanta amma insha Allahu dazarar yasauka zaikirashi kuma kafin yadawo zaiyanke abiyi shidai auranta yanzu zaizama barazana ne dazaman lafiyarsu da basma dontunkafin suyi aure take jaddada masacewa batasan kishiya amma Allah yasaka agaba shikeyin maganin komai

Babana jikinshi ya murmure yasamu saukisosai tuni yasoma fitanema saidai watasabuwar masifar da babagaje takuma tadowa itacewai baba yabaiwa yaya auwwalu dakinsa shikima baba yace inyatashi inazaije gafilinan yagina daki yanda yan uwansa sukagina rigimatayi tsamari zagin baba itada yayanta abinhar mamakiyake bani tamkar bashine mahaifinsuba nikuwa in abinyashawota tokaina takehucewa takamani tanada waitunkan auran uwata mijinta yacanzamata tasanadina harsakinta yayi yazabeni cikin yaya shekace nikadaiya haifa cikin kwanakin nida babana munshiga cikin damuwa todayake bikin saba an watane wato ishin da bakwai gawata ranar takama lahdine to ranar asabar nadawo tallan gyada sainasamu kayan baba akofar daki antilesu ankulle kofar da kwado nannagane lallaisu dagaske sukeyi koda baba yadawo inakallonsa yazubawa kayan idanu sannan yayi murmushi yaje ya ajiye zabirarsa ta aski kusada kayan dakinsa nawaje indayake aski in anzogida nan yashare ganinyana tafita dakaya nannatashi nima natayashi yamaida kayan dakinwaje ranar bikin dayake nima nasamusake gidan binto nayini tataimakamin dantana takashemin kwarkwata nayi wanka hartabani kyautar kaya riga dazani da mayafi harda takalmin soso nadubeta inagodiya sannannace gaskiya wanka rahamane binto kinji yanda naji iskanashigata kota ina tace harma kinyikaufa kaiyya wannekau gurina nakallali yanda binto tayihaske sai abinda takeso zataci nan rogontane da kuli gakwadon ramarta cankuma ga dawarta da wake tadora nace kai binto kinhuta dubeki fes dake kici abinda kikeso cikin tausayawa tadubi jidda kuluwa Allah yanasane dakenasani idan rana tafito tafin hannu bazai karetaba kidan kara hakuri kadan inaji ajikina zakizama wani abunangaba nadubeta da murmushi sannan nace da ita kinafadine dan injidadi kumanaji shikenan dazan tafi aina tana tsifarkai akofar dakinta nace inayini aina u fuska tayamutsa tareda dakaudakai binto tace aina u bakijibane tajuya tadubi binto magana kike binto taja tsaki sannan tace muje kinji

Bayannatafi binto tadawo tadubi aina u babukau abinda kikeyiwa kuluwa ta tabe baki indai kinga nakula kuluwa to aure tayi domin koyaushe ado cemin yake bashi daburin matabiyu inhar dolene to saidai jidda binto tace ke aina u kincika shirme to in Allah yayi matarsace yazakiyi aina u tace Allah yakiyaye wannan kazamar binto daitawuce tabarta nan tana ta aibatani inashiga gida babagaje tadubeni awulakance to uwar gantali daga ina kuma nace gidan binto tace matsiyaciya almajira taroko kaya in inaso kisakane aizansaimiki tunda kikaga nahakura da tallan abinci dakikemin dolane kihakura da tsafta nafison ganinki cikin datti aminanta da dija sukasheke da dariya taredacewa kinsan kan duniya gaje itama cikin dariya tace ni innaki mutum duniyama saitakishi dan ubansa tanunani gamisalinan bantakai kwabona gidan wani malamiba ammadana sakoshegiya kungantanan kutuma bazaitayaba bare maiyatsu dija tace shekara shahudu bamashinshini aitagama bandaro sarai tace wayasani kotakanta banabi bare insami tarihidai nakeson takafa akauyannan kobayanzuba adinga labarin yarinyar nandata tsufahar tamutu babu aure jin abinnasu yayi yawa sainafita nazaga bayan runbu kusada awakinta nazauna nazabga tagumi inason inyi addu a ammabansan mezanceba yawancin lokaci saidai ince Allah yasakamin akwana atashi asarar mairai inji yanmagana har angama ginin gidan m b saidai babu wanda yasancewa gininsane dayawa sunazata ginin adone tunda ansan filinsu maigarine ko inasailabari gidan akauyanmu dama makwaftanmu gidan ginin bulodabulone ammazubin gargajiyane daga wajen gidan akaudogon dakali dabaranda sanna gamasallaci babba shikirar nabirnine naji anacewa sallar juma a za adingayi tundadama sai anje garko akeyin juma a akwau soraye guda biyu zaure kafin kashiga tsakar gidan dakuna ukune saikicin saibayi tsakar gidan malaleda siminti gafenti yasha dagawajema fenti kalabiyune ruwan makuba daruwan madara harciki munshiga kallo inata mamakin kyawun gidan azotona nimana adone nace lallai aina u sunyi gida
[29/09 5:30 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
36.
Nakalli baba dakeyin shanya nikuma inacuda masa kaya muna wankine arafin gonar maigari babayana shanyawa nacewai baba masallacinna da ado tagina yausheza a somayin sallah acikinsa donnaga tuntuni akagama ginawa yace aibana ado banena yaronnan muhammadu ne wanda yakaini birni asibiti danbirni har gidan yace kwarai har gidan najinjina kai taredacewa mutane sunatacewa gidan ado gidan ado yace a a filinsane nawajan mahaifiyarsa daya gada shineyasa akagina nace to zaizaunane agidan yayi murmushi taredacewa jidda kenan tambayarki tayiyawa toni inazansani kila inyazo da iyalinsa zaidinga sauka nace to ninakosa ingako wannetaimakone yakecewa zaimin ammazanso ace makaranta zaisani baba yakalleni nikonafison kiyi aure dazainemi jinsanraina dazance yasamo miki miji abirni kodamai gadin gidansane indaizai rikeki nayidan murmushi azuciyata nace wazai ganni abirni amma afili sainace baba niwama zaisoni yace kidaina fadin haka jidda domin falalar ubangijinki tanadayawa cikin zuciyata nace Allah kayayemin kuncin danakeciki

Shikuwa m b tuni aiki yayinisa kumayasamu gidansa maikau da motarsa wanda office sukabashi kumayanajin dadin aikin kodabai cikazamaba yawanci aturasunanne aturasucan dukda hakayanaso yadawo da iyalansa nankusa dashi hakaduk lokacin dasukayi waya da ita damuwarta itace yazoyatafi da ita cikinhaka sukasamu watanni uku sannan yasanar matatasoma tasoma saran zuwansa kowannalokaci tuntana lissafin kwanaki dagaranda yace mata yana tafe hartadaina idanutazuba ranar wata juma a wadda husna kanwarsa bazata tabamantawaba da itaba saigashi yadira da rana tsaka dukkansu murnasuka shigayi basma da husna suka rurgumeshi saidai kash dukda uwaryunwar dayakeji saidai yasha ruwa ko jus saboda kuku bayanan an aikeshi kasuwa basma tana kwance jikinshi husna ce takawo masa ruwa yadubi husna yace dady fa tace yatafi ofis dinsa yace yanzu hakayake fama darashin kulawarku gashi dadyna bayason zama dayinwa husna tace uku yanayin komai nanyafita gidan cin abinci danyacika cikinsa kuma danlalacewa harda cewa dan Allah yayo musu tsarabar icecream dady yashigo da daddare misalin takwas yataddabaki sunajiransa yan gidansu bilal ne saidai basujimaba sukayi sallama sukawuce dady yashigo falo yasanar dasucewa yan gidan su bilal ne maison husna m b yakalli husna waddata saddakai kasatana murmushi amarsu kenan dady watanawa kukatsaida cikin jimama dady yazauna yace bello sunzo dawani batune nadaban dukkansu sukadubeshi tuni gaban husna yasoma dukan uku dady yace husna kihakura da yaron nankawai yanzu abinda waliyansa sukefadamin wai mamansa tace bazaya aurekiba mahaifiyarki taso tayi kisankai har kotu husna tazaro idanu taredacewa dady waya fada musu innalillahi wa inna ilaihirraji un saikuma tasakuka tanacewa dama hajiyarshi batasona nakula damukaje dubota a asibiti batada lafiya ammasaiyace bahakabane nan basma tarungumeta suka shiga rarrashinta m b yace kicigaba da addu a sister kinji
Lokacin kwanciya m b yaja matarsa gefansa nada donbazai iyanisa da itaba husna itakadai takwanta tanacikin kuka bilal yakirata takidagawa yanatakiranta hardai daga karshe ta dauka hankalinsa atashe yace husna dan Allah kiyihakuri muhadu gobe musan menene mafita ni inasonki kumanagaya mata inban aurekiba saidai na mutu babu aure bayan haka kuma nagaya mata inma gaskene laifin mahaifiyarki daban laifinki daban husna dai shiru tamasa sai shashshekar kuka waddahakanne kekara dugunzuma zuciyarshi dagakarshe da kyar yalallasheta akancewa zasu hadu gobe shiru tayi tarungumi filo tunita bazama duniyar tunani inda watazuciyar take tabbatar matada cewa hajiyar bilal batada laifi don tana dahujja dama laifin mahaifiya zai
Zaishafi danta shikuwa m b rayiwarsu sukaci shida matarsa yana son basma tamkar ransa itasai yanzu tagane cewa data rabuda m b tabisu hajiya shiwa data jibga asarar da bazata maidataba bello tahir yasan rayiwa sala sala insuna tare takan mantada kowa dakomai shine dalilin dayasa take matukar kishinsa batason kokusa wata mace takalleshima cikin kwanakin daya dibone suketa shirin tafiya gashi tafiyar takama harda husna m b yace zaya tafida ita tunda gayanda abubuwa suka kasance gameda auransu da bilal itamata amince tabisudin tunda bilal yanunama cewa bazayaja da mahaifiyarsaba saidai suyita addu a shiysataga garama tatafi kozata mantadashi amma anya zata iyamantawa da bilal kafin ranar tafiyarsu m b yaziyarcisu haja dauke da tsarabarsa kasancewar ranar alhamisce yasamu tuni angama gininsa yashamamaki yaso yaje yadawone aranar ganin kammaluwar masallacin yasashi yanke shawaran kwana inyaso gobe juma a sai abudeshi dasafe saiyawuce nibanma san danbirni yazokauyanba saida yammacin ranar alhamis din danaji anashelar za abude masallacin juma a gobe narasa indazan ganshi gashishikuma baizoba saida daddare babagaje ta aikeni gidansu dija inroko mata miyar tafasa harta kofar gidan maigari nabi dannaganshi ammabanganshiba saidai motarshi namatsu inganshi nice hargidan su binto mukagaisa tace sai inanace rokonmiya zanje gidan dija nazaci danbirni yazonan tace dadai yaya ado nananne shine zaizonan wani abune nace a a zandai gashsheshine haka nahakura nakoma gidan dija nakarbi miya tanamita itadai gaje shegen kwadayine da ita ga yar banzar rowar tsiya mamaki yacikani dija dazagin babagaje
[29/09 6:31 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
37.....Duk yanda suke kodayake itama babagajen tanazagin dijan Allah kauta wannan amintakar inakomawa gida babagaje har rankwashi tazubamin iyakarfinta wainaje nazuna tuwanta yasankare shagon baba natafi inda baba yake kwana shine yakesanar dani zuwan danbirni gurinsa yakumanunamin kudin dayabashi naciji yatsa taredacewa kash baba yace menene nace danbirni yayimin alkawarin zaitaimakeni kilama yanzu yamanta baba yace baimantaba kuma saida yatam bayeki yanasane zakiganshi kobayanzuba washegari guri yayi guri mutane dadama sunhalacci bude masallacin bayan kauyanmu baharda makotanmu naji ance harda kamsila da ciyaman nimaba abarni abayaba damani uwar yankallo yaukan nasamu nayi guri yacika sosai harda matan aure kunsan kauye daga indanake inakallon sanda danbirni ya iso bamataba har mazan gurinda nakezaune inajinsunacewa kai wannan dantahalikin Allah yayi masakyau ga iyatsara ado nayarda dasu ga iyakarya hula kunsan bakano gurin ajiye hula kamshinsa kuwayacika gurin kodan nasan kamshinnasane oho sheda akayi nasiha gamida tuna tarwa inbanmantaba naji malaman suna horan al umma dasuyi koyi da halin bello tahir

Gurin yin sadakatu jariya sannan akasoma dabude gurin matso ruwa nannasaki baki inakallon zubar ruwa dagajikin wasu yan karafuna nisoma nake ingadaga ina ruwan yakefitowa nagadai garijiyacan daga gefe sannagawani kokarfene ko robace dirkekiya dagasama inacan inakallo har akabude masallacin bansaniba inanan inakallon katon bututun zance komenene aciki oho binto tadafani ketundazu inakwalamiki kira kinacan kina kallon tankin ruwa kedai bakiraina abinkallo nace sunansa kenan tomenene aciki tace ruwa nakuma kallon tankin kingani nadan girgiza kailallai birni tayi dariya nace binto hakada tsohon ciki kikafito taharareni jiyakinga yaya bellon nace a a sai ananna ganshi nasoma kallon indanaganshi binto tace nazo mujegidansu muci abinci duk da inamatukar jinyinwa ammabaso kallo yawuceni donhaka naceda binto nakoshi inagurin akagama komai kowayawatse har akakira sallar wanka ta juma a sannan nabar gurin shawaranayi inje ingaida haja dukda shekaran jiyancanma naje hanayi mata shara nashiga da sallamata natsugunna nagaidasu maman su binto nashiga dakin haja tana sallah nimanadau butarta naje nao alwala nazo nayi bayan na idar muka gaisa nadau tsintsiya inashare mata dakin taredacewa haja banganki wajan bude masallacinba tace aiko naje kuluwa bandai jimaba saboda kafafuna basujuri tsayiwaba nadawo gida nace banlura dakeba nakwashesharar naje nazubar nadawo na kakkabe mata gadon tadinga samun albarka taredacewa daman tunsharar shekaranjiya dakikayimi asma u cemasharar kumasuntafi biki kauyansu babarta nace Allah yadawo dasu lafiya nazauna daidai lokacinda takecewa nace dagoro ammadaidai wannan lokacin sunfisani aiki dandai yau juma a ce kiladanaje goro zandauka amma aikin danakesha yanzu yafinada saunawa aikin matansu yaya auwalu harwanki don rashida matar auwalu wani lokaci saitace baifitaba kuma dole nasake wankewa ko yayita jibgata gashi matartashi bawai tagirmeni bani haja tace cinzaline kawai sallamar danbirnice tatsaidamu dagamagana yashigo da kamshinsa bayan mun amsa

Sallamar kusada haja yazauna kangado tareda dora hannunsa akafadarta tace kunkammala komaikenan yace eh yanzu sai gida gobemuwuce harda husna natsugunna nagashsheshi yace a a jiddace nace eh kaina yanakasa nace angode babana yace min kabashi kudi bai amsaminba yace jidda sainaga kinkara ramewa haja tace badoleba yazatayi da masifar gaje harda surikanta guda biyu dakumasu yayannata tamkar baiwa itace deboruwansu wankisu shararsu ga girkin gidan gabadayane harsu kuma itakeyi gabadaya gatallan goro da gyada shiruyayi tamkar medaukar karatu koyaushe tunaninsa wanne irintaimako zayayimata yaciro wayarshi yashiga daddannata sajan sale yakira cikin harshen turanci yakemagana dashiyatam bayeshine yaya maganarsu takwanaki akan jidda sajan yayi shiru cikinzuciyarsa gaskiya yarinyar batayi masabasam dukda maigidannasa yafadamasa taimakone m b yace kayishiru yace sai ahankali maigida wallahi tsofaffina sunkiyarda acewarsu zanmaidasu mutanan banza saida sukagama magana da iyayan yarinyar danake nema sannan zanzodawani batun banza m b yace to bazakahada biyun bane zanbaka gidana daya nakarkasara kona doraya kazaba shiru sajan yayi gakoshi gakwanan yinwa dinfakenan dayatuno kamannin jidda saiyace gaskiya maigida sai ahankali yace tokatuntubi mahaifan nakamana kafinnataso anjima insunyarda harsadaki zanbiya inyasosai asakabikin sajan yace saidaihakan zankiraka duk yandamukayi zahiri baikira kowaba hasalima basu dade da haduwa da budurwar tasaba shidai bayason bakar mace amma idanyatuno da kwautar da maigin nasayace zaimasa saiyaji kamar yayarda dagakarshedai yajajirce kancewa bazai auretaba nikuwa da ake abunkaina bansan mesuke cewaba kallonsama nakeyi kowanne yarene wannan abindama nakesonsani shine koyasan abindayake fadi abarhannunshi redi o cekomecece niduk azatonama shikadine yake maganarsa jim kadan la asar tayi jinbaicemin komaiba nace to haja zantafi gida nadubeshi nace kasauka lafiya yace to jidda saiwatarana nasake kallonsa sannan natafi zuciyata cike dacire tsammani

Taimako daga gareshi haja tadubeshi nidai inason yarinyarnan muhammadu don Allah babu wani dauki dazakai mata tanuna turaman zannuwan dayazomata dasu tace tace naso inbata dayadagaciki adinka mata ammanasani gaje kwacewa zatayi yace barimuyi la asar Allah zaikawo mafita bayansu idar da salla zamayayi yanatunanin yanzu idan sajan yakifa koyaba danjuma maiwanki tsakiyayi gaskiya baisan asalin danjumaba jidda tana bukatar wanda zaikulada ita injiwata zuciyar in akayila akarida irinwuyar rayiwar datasha kamatayayi tasamu miji wandazai jida itadadin rayiwa matuka hakannan koyamatsawa sajan ya aureta balallaibane yakula da ita dobayasonta

Yanzuyaya zayayi kenan yasaketuna cewa shimafa yataba shiga irinwannan halikoyace bedade dafitaba mashi namiji kenanma bare ita mace kuma yarinya yasauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu sannan yamike yanacikin tafiyane zuwa gidan maigari sajan yakishi yasanarmasa dangisa sunce bazi auri mata biyuba Allah daiyasa banbata makaraiba m b yace kokusa zansan yanda za ayi yadubi haja narasa yanda zanbullowa lamarin jidda ninenama alkawarin zantaimaketa ammagashi narasa yazanyi haja tace bakafa rasaba zaka iya auranta kamaryanda ado yayiniyya m b yaware idanu yanakallon haja sannan yace in aureta inkaita ina tace ga gida kagina ni ainazacida kaginashine donka auri yarinyarnan ka ajiyeta dangaskiya zuciyata bata aminta da matarkaba yayi dan murmushi itamatanada kirki kuma tana sona haja tace nidai indazakayi hakan dazanfi kowa murna yace shikenan bari inkira dady na cikin waya lokacin dayakira dady saida yatambayeshi yana gidane yace a a yanzunnan yafita daga masallaci yana hanyar zuwa gidan yace dady sirrine tsakanin da da mahaifi mata akabani anankauyan su haja gashinigobe zanwuce naganta kuma tamin banaso kosu husna susasni inasoka kira baba maigari kabashi iziniya karbamin inyaso saisusaka rana duklokacin danadawo sai ayibikin dady yayi shirucan yace mezaya jamaka kara aure bello yace babu ammabazan iyakinkarbar yarinyarba kuma addinina baihanaba hasalima da biyu akace infara dady yace shikenan zankirashi yanzu abin abinkamar wasasai gashi maigari dakansa yatashi shida liman sukazo gurin babana neman aure na baba daicewa yayi yabashini sadakama shizaibada sadaki su maigari sukace a a yabada sadaki dubu talatin dukiyar aure dubu hamsin yace yanaso ayibaikone zaitafi kasar amerika inyadawo sai ayidaurin aure baba harda hawaye saidai yarokisu maigari akansu sakaya abinsaboda babarta kowayasan halinda takeciki akauyannan maigari yace babu damuwa nan yayi haramar tafiya bayan dawowar su maigari kamar yabitagidan su jidda saidai bayaso yaganta shedan yacusamasa tsanarta

Saikawai yawuce sunsake tattaunawa da dadynsa akanbatun aurannasa sannan yasake jamasa kunne kancewa yakula da basma sannan yayi kokari yasanar da ita batun auransa yace in Allah yayarda ranarce kuma daddadare bilal yaziyarci husna dahar takifita yanda yadinga aike sai basma tace taje taji yace yazo yayi bankwana da ita doya samulabarin zata tafi u s tareda yayanta tace kai mutane basu dagadon mutum ammasuna da gadon gulmarsa bansaniba nima tajuya tanuficiki yanata kiranta batajuyoba yadafa goshinsa zuciyarsa cikeda damuwa baisan wanne irinso yakewa husnaba shikuma m b daya kalli basma saitabashi tausayi yasani datasan abinda yafaru yau akauye hakika
Akarshen labarin zakuga bankarasa tunanin da m b keyiba iyagurinne ya yage kadan dagasama kuyi hakuri

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar

Please Login or Register in order to submit comment