Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9:51AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: [12:30PM, 7/1/2017] mrs j moon: *RAYUWAR BAHIJJA*
Didecated to mumm Abdul *(bebeelo)*

Dasunar Allah mai rahama maijin qai.

*01*
"Queen queen!! Shine kiran da wanani matashin saurayi keta ta fad'a da qarfi amma wacce yake kira tayi kunnin uwar shegu dashi.
Da sarsarfa ya sha gabanta yana qare mata kallo fuskansa d'auke da murmushi. Taja gyefen hijabinta ta rufe fuskanta tana dariya qasa qasa.

Ya dungure mata kai "kunyar qaryane wannan kikeji queen, kinaji ina ta kwallamiki kira amma kikayi banza dani ko?
"Uhmm yaya bilal kenan, ta yaya xan ansa maka irin wanna uban kiran akan hanya. Tana fad'an haka ta rabe ta wuce da sauri yabita suka jera taja ta tsaya ta kafeshi da idanu shima kallonta yakeyi.
Cikin muryanta mai sanyi tasoma magana "don Allah yaya bilal katafi abinka sabida ba girmanmu bane yin hakan, ko kamanta kaid'in dan gidan sarki ne ni kuma 'yar gidan liman. To inkamanta natuna maka yanzu, yin hakan ba girmanmu bane don haka na had'aka da Allah kabar biyoni kana tareni. Ta juya tana mai gyara ruqon littafan islamiyyarta tayi tafiyarta batare da ta ko waigoba.
Sututi yayi yana vin bayanta da kallo yana ayyna dirinta tare da surarta aransa. Ahankali ya furta"lalai inkin girma za asami shamshaqiyar budurwa, ya cije babansa na qasa tare da sosa sumar kansa wanda ke nannad'e sai kyalli keyi irin na fulanin usul 'yan daji.

Ya juya xuwa majalisarsu ya zauna shiru batare da yacewa kowa qalaba, tunanin maganganun qaramar yarinyar ke mishi yawo a brain sosai take bashi mamaki intana magana cikin natsuwa da hikima, kuma komi tafad'a mai amfani ne yaja ajiyar zuciya tare fa cewa " 'yar baiwa bahijjata. Duk suka xuba mishi ido alokaci daya kuma sukasa dariya hara ya watsa musu yaja tsaki ya bar musu wurin
[1:35PM, 7/1/2017] mrs j moon: Da sallama tashiga gidan, gwagwgo bintu ce ta amsa. Taqarasa kusa da ita tad'an russuna tace "barka da yammaci gwagwgo ya jikin nana? "Barkanmu bahijja, nana tasami sauqi har na aiketa. "Madallah Allah yaqara lafiya "Amin kedai 'yar albarka. Murmushi tayi tare da qarasawa ciki.

Bataga gwogwgo lanti ba don haka ta tube kaynta tasa na aiki ta soma cika randunar da ruwa sanna tasoma haramar d'ora sanwar dare.
Cikin qannanin lokaci ta dai daita wata qatuwar tukunya amurhu sannan tayi sanwar wata madai daiciya da alama ta miyace babbar kuma ta tuwo.
Tana tankad'en gari Nana ta iso cikin fara'a tace "sannu adda bahijja da aiki "yawwa sannu kema, ya qarfin jikin naki? "Nawarke ai.
Ta dubeta ta girgiza kai "anya Nana ba rashin lafiyar qarya kikayiba kuwa? Darita saki tare da matsowa kusa da kunnen bahijja cikin rad'a tace ban iya qarin siran da akayi ba shi yasa nace cikina na ciwo sabida tsoron dukan malam mamunu. Dan qwashin kanta tayi tasaki qara zata gudu ta damqe hannunta tace "don Allah dakamin kubewan can daxan kad'a "angama maa.
"Ina gwagwgo taje? "Taje wurin magani, wai tanaganin adda hindu mayu sun kamata. "Toh fa aina ta had'u dasu? Oho mata, kinsan dai halin gwagwgo da iya habbaka bala'I, komi yasameta tace jifanta akayi ba aciwon Allah d'akinta sai da sanadi don kawai rashin wada taccen imani.
"Uhmm to Allah ya kyauta, yakuma bata lafiya "Amin dai kam.

Tana tuqin tuqin tuwo gwagwgo lanti tadawo tare da hindu.
Tana yimata sannu da dawowa tayi banza da ita tashige d'aki fuuuu Nana ta tabe baki tamiqe tashige lungunsu.

Tsaf tagama aikinta ta nemo gwagwgo bintu ta kwashe mata domin baza ta iyaba kuma tasn kotakira gwagwgo tasan baxa takulataba.

Aguje hindu tafito tayi baki rariya tasoma sheqa amai bahijja ta tai maka mata ta d'auraye bakinta tana tajera mata sannu wanda bata amsa ko d'ayaba.
Ta ratayo jikkanta ta leqa "gwagwgo sai na dawo. Cikin kumfar baki ta amsa"kada Allah yasa kidawo lafiya, shegiya mai baqin hali, mai kama da aljannu kawai bacemin dagani ko intaso in dakaki. Da sauri tafice tana sharan kwallah.
Awaje ta had'u da malam ya cire mai hansin yabata yayin yabama nana ishirin suka russuna kakayi mishi godiya.

Yauma ita da nana suke ta kicikicin d'ora abincin dare duk sunyi zufa sakamakon itacen ruwa ba bugeshi yaqi kamawa kuma gwagwgo bintu batanan, sai hawaye suke na shaqan hayaqi. Hindu na zaune tana kallonsu ko sannu takasa ce musu sai qorafin hayaqi ya isheta qaurins zaisa mata ciwonkai.

Malam ya shigo hayaqi yayi masa maraba tuni yasoma tari ya hango su nana cikinsa suna ta fifitawa ga kuma hindu zaune ta hard'e qafafu.
Cikin zafi yasoma kiran "lanti lanti!!! Tafito d'aki tana gyara d'ankwali alamar barci takeyima.

Wani kallon banza yawatsa ma yace "aikin mikikeyi kikabar yra na aiki cikin wannan hayaqin? Tasoma sosa kai narashin gaskiya ganin takasa kare kanta ya d'ora da cewa to na soke sa su girki irin wannan mai yawa daga yau. Ya juyo yana kallon hindu yace "tashi muje chemist adubamin ke. Ahankali ta miqe tasanyo hijab.

"Kufito waje nace ya umurci su bahijja, suka fito idanu duk yayi ja sai xufa suke sharewa. "Inbanda rahin imnai irin naki lanti mi yara 'yan shekaru 12 xasuyi miki a kitchen? Kai Allah yashiryaki dai.

Sallamar gwagwgo bintu yakatsema malam bambamin fad'ansa.
Ya amsa sallamar yayin da su nana suka rungumeta suna murnan ganinta. Malam yace
"Yaewwa bintu tafi da hindatu chemist ayi mata gwajin bitsari da jini muji mike damunta "to malam. Ku kuma kuzo muyi bitan karatunmu najiya suka amsa da"toh atare.


*BARKA DA SALLAH TO YOU ALL*🙋🏻🙋🏻🙋🏻 Allah SWA ya amsa ibadarmu amin.


*mrs j moon*
[9:51AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: [8:55AM, 7/3/2017] mrs j moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(bebeelo)*

©Safiyya

*02*

Ad'akin malam sukayi sallar magriba, sabida gudun fad'an gwagwgo. Amma duk da haka basu tsiraba domin tanajin fitan malam xuwa masallaci taxo qofarshi tayi tayin ruwan bala'I ita kad'ai kamar wata karya. Sai da tagaji dan kanta tayi shiru amma bini bini xatace iskancin banza da wofi.

Sai bayan isha'I su hindu suka dawo. Gwagwgo bintu sallah tayi haramar gabatarwa batare da bata lokaciba.

Kururuwan ihun hindu yaja hankalin al ummar gidan duk suka taru sukayi cirko cirko suna sonjin dalilin ihunta wanda taqi bari alaman dukanta akeyi.

Gyaran muryan malam yasa mutanen suka watse.
Bakin qofar lanti ya ja yatsaya tare da cewa "lanti ba kya da imani ne daxaki tasa yarinya kina bugu alhalin kinfi kowa sanin batada lafiya, ko so kike ki kasheta ne? Tafito duk ta had'a xufa ta hankad'o hindu ta fad'I qasa faf.
Cikin d'aga murya tace "malam gatanan tafada maka uban da yayi mata ciki agarinnan kuma wallahi babu ruwana cikin lamarin domin bansan ta inda ta kwaso wannan abin kunyarba.
Wani kallon tuhuma malam yawatsa mata atake ta sunkuyar da kai narashin gaskiya. "Bintu! "Na'am ta amsa tare da bitowa hannunta riqe da tasbaha tana ja, ta durqusa gefensa tace "gani malam.
Ahankali yace "minene sakanakon gwajin da akayi? Tamiqa mishi takardu guda biyu tare da cewa "ayi haquri bisa lamarin abi komi asannu. Bai amsa takardunba yace "fad'amin abinda ke ciki inji, caraf lanti ta amshe "ai da kaduba dakanka dayafi tunda ita ba...."ke!!!!! Waya sakoki bakin ki ciki da zaki ki tsoma? Malam kenan ya katseta cikin tsawa. Taja da baya tana aunawa bintu harara kamar idonta zaigad'o qasa.
"Ina sauraronki bintu. Ahankali tasoma magana "malam ayi haquri tare da dangana domin wannan abu qaddarace da ga Allah, taja numfashi tacigaba sakamako dai baida dad'in ji domin antabbatar da hindu na d'auke da juna biyu na tsawon watanni uku da sati biyu, kusan watanni hud'u kenan.

Innalillahi wa inna ilaihin raji'un!! Abinda malam yayi tananatawa kenan yana sharce gumi dama yayi xargin hakan zaifaru sabida ganin yawan amai datakeyi ako da yaushe inya tambayi mikedamunta ace malaria da shawara.
Ya sauke dubansa kan hindu da sauri ta ja dabaya tana rawan jiki tasoma cewa"Allah malam sharrin shaid'anne da kuma matsawan gwagwgo akan sai na saida talla tas ko ina zanshiga inje in saida shi, amma don Allah malam kayafemin bazan qaraba wallahi natuba, tafashe da kuka ma tsanani tana cewa "kin cuceni gwagwgo banyi dacen uwaba kaicona.

Malam xuciyarsa kamar wuta yaja dabaya yafice batare dayace komiba.

Lanti da watsama hindu wani lafiyayyen mari wanda saida ta fad'I tasaki qara tace "wallahi kuma sainafad'a gaskiya komi zakimin. Tako soma dukanta baji bagani ta ko ina tana zaginta "shegiya 'yarbanza ina ruwana don nasa miki tallah sai kice nace kibi maza, ita bahijja bata zuwa tallan ne dabatayo gantaliba saike uwar jarabara, to wallahi ahir dinki naqarajin sunnana abakinki tam, ta tureta tashige d'aki tana zage zagen banza tare da ajama gwagwgo bintu Allah ya isa wai ita tayima hindu asiri tabi maza har ta kwaso abin kunya.


*mrs j moon*
[11:49AM, 7/3/2017] mrs j moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(bebeelo)*

©Safiyya

*03*
Gwagwgo bintu bata kulataba taja su bahijja suka shige d'aki wanda duk jikinsu yayi sanyi. Xuwa can hindu tashigo dakin gwagwgo bintu ta duqa agefen qofa ta sunkuyar da kai tasoma magana cikin muryan kuka "don Allah gwagwgo kitai makeni malam yayafemin kada ya koreni, nasan inkinsa baki zai huce.
Asannu bintu tasoma da cewa"hindu baki kyautama rayuwarkiba sam kinbata wayonki kuma kinzubarma da gidanku qima a idon al umma kam, "nasan bayiwa rayuwata adalciba amma ina roqonki da ki taimakeni ki mance rashin kunya dana riqa yimiki abaya wallahi duk gwagwgo ke sani amma yanzu natuba na daina Allah. "To madallah Allah yashige mana gaba, kuma insha Allahu malam zai d'au abin asannu. "To nagode gwagwgo "bakomi tafi kije ki kwanta tamiqe tafice jiri na d'aukanta.

Arba tayi da malam tare da qaninsa aguje ta juya d'akin gwagwgo bintu, arazane ta tareta tana tambayarta "ke da waye kuma? Bata bata amsaba malam ya shigo ya fizgota yayi waje da ita gwagwgo bintu ta biyoshi tana cewa haba malam kabita asannu mana, inrai yanaci hankali ke nemosa, don Allah kada ka doketa. Bai kulataba ya isa wurin inda qanninsa suke tsaye yatura musu ita yace "ku casamin ita har sai tafad'a muku gaskiyan wanda yayi mata ciki. Ciki!!!!!!! Kuma malam? Suka tambayeshi atare, bai amsa musuba ya shige d'akinsa a fusace.

Faruqu sarkin zuciya tuni yasa qafa yyi ball da ita ya xare belt yasoma xuba mata ta ko ina yana cewa yau saidai uwarki ta haifi wata mara tarbiyan amma kedai yau sunarki marigayiya.
Ihu takeyi tana fad'in "natuba baba xan fad'a dogari ilyane kuma gwagwgo ta sani ita tasani in nemo mata kud'I ko ta halin qaqa, afusace gwagwgo lanti tafito tayo kanta tana cewa sharri xakiyimin komi? Faruqu dai dai yadaga belt zai xubawa hindu yaga zuwa lanti aiko ya dage ya lafta mata a mazaunai tasaki qara tayi baya tana sosawa.

Dakyat gwg bintu tayi nasaran tsaida faruqu ya bar dukan hindu ganin xai yi kisan kai.
Ta taima mata ta kaita d'aki ta roqi lanti da kada taqara bugunta don Allah, cikin ruwa bala'I ta amsa "to kanwa uwar gami 'yar baqin ciki munafuka burinki yacika sai kimaza kiqarawa bokanki kud'I tunda aiki yayi kyau 'yata tabi maza, itadai gwg bintu tayi shiru tana kallonta xuwacan tajuya zatafice taji gwg lanti tace "kuma banyafemikiba Allah yasakamin akan 'yarki Nana, insha Allahu ita har qanjamau zata d'auko domin kuwa burina taxama magajiyar karuwai.
Ahankali gwg bintu tadawo daf da gwg lanti cikin matsanancin bacin rai tasoma magana "ba Amin va lanti, baqin baki yayi ta koma miki kanki da yardan Allah kamar yadda yanzu ya koma miki gashinan 'yarki d'auke da abin kunya duk don sakamakon mugun fatanki akan marainiyar Allah Bahijja, kinta kurawa rayuwarta kin hanta saqat kullum burinki mugun abu yasameta, alhalin tana cikin gatanta kika rabota dashi, to ta Allah ba nakiba lanti, baqin bakinki yasami bishiyar tsamiya kuma aniyarki tayi tabinki har yauma tanadi, taqarasa da fad'in axxaluma kawai mai mugun nufi, tafice tabar gwg lanti baki bud'e cike da mamaki wai yau bintu ce ke fad'a mata magana haka bako jin shakkanta, uhm lallai gobe sammakon zuwa gidan 'yar goje yakamani in zana mata abinda ke faruwa domin samo mafita.

Washe gari malam nadawowa masallaci yatara kowa na gidan a dakinsa.
Bayan an gama taruwa yayi sallama tare dayin gyaran murya sannan yasoma da cewa "duk kanmu munsami labarin iftik'in da ya affawa rayuwarmu na samuwar cikin jikin hindatu ta gurbatacciyan hanya, to abisa da haka ni malam yusufu na soke talla agidana akan kowani yaro na gidannan kuma in nasami wani yaqi bin wannan umurnin to za agamu da bacin raina, dafatan anjini suka amsa "eh.
Yacigaba "hindatu kuma zata haife cikin jikinta in Allah yaso sannan bazamu tuhumi dogari ilya akan maganarba sabida ba fyad'e yayi mataba da kanta kaje don haka inta haihu sai abashi d'ansa ko 'yarsa inyana so.
Kowa yayi shiru yana jimani sai sautin kukan hindu ke fita ahankali mai tsuma zuciyan mai saurare.

Tararrafa gaban malam tace "kayimin rai malam ka yafemin natuba kuma ka taimakeni acire cikin don Allah wallhi bana sonsa bazan haifi shegeba wallahi banyafema gwagwgo ita da ilya. Afusace gwg lanti ta fallmata mari bata maida nunfashiba malam ya sauke yatsunsa biyar afusknta saida yayi mata maruka hud'u masu kyau sannan yace "lanti zan tsige igiyata akanki in har baki shiga hankalinkiba, cikin zubar hawaye tafice dakin.

Malam ya dubi hindu yace "baxa axubda cikinba sai kin haifeshi, shine hukuncin daxan miki ta fashe da kuka tana fadin na bani na lalace.


Qauyen kwara kwara qauyene mai tarihi sosai to anan garin malam yusufu ke zaune da iyalansa kuma shine limamim garin gaba daya.

Yana da mata biyu lanti da bintu. Baya da 'ya'ya da yawa su hud'une duka duka lanti uwar gida keda uku bintu nada daya itace nana.Ado d hindu da musa yaran lanti.

Bahijja kuwa 'yar yayan lanti ce tunda babanta yarasu ta taho da ita tuntana 'yar shekara bakwai yanzu takai shekaru biyar ahannunta kuma taqi kaita ganin mamanta ko sau daya sannna sukuma tayi musu surkulle sunkasa zuwa ganinta sam.

Lanti jaraba laqabinta aqauyen.
Kowa yasanta da masifa amma sosai take shakkan mijinta malam domin tasan bai d'aukan iskancinta.


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: [10:50AM, 7/5/2017] mrs j moon😊: *RUYUWAR BAHIJJA*
Deducted to mumm Abbadul *(Bebeelo)*

©Safiyya
*04*
*BUKAR LAMI'DO LGEA PRIMARY AND SECONDRY SCHOOL*
Makarantace daya tilo dake hanyar shigowa garin kwara-kwara, qauyen dake cikin egabi local government ta cikin garin kaduna state.

Ankafa makarantar da dadewa amma mutanen garin sunqi habbakata ta dalilin qin kawo yaransu makarantar sabida da rashin wayewa akan ilimin boko.
Yaran sarkin garin da liman sukad'ai suka soma karatu amakarantar sabida iyayen sun aminta da ilimin sannan sune masu fad'a aji, sai daga baya kum "yan tsirarun mutane suka soma sanya 'ya'yansu gaba gaba har yazamanto fulanin dajin suma sun sako nasu ciki, ganin ta bunqasa sosai yasa aka gina musu secondry sai suka hade sunarta.

Aqasar bishiyar d'orawar dake harabar makarantar yarane matasa su uku suna xaune akan wata sallaya mai fad'i duk sun duqufa suna rubutu bisa ga alamu assignment sukeyi.

Xuwa can dayansu ta rufe littafinta tare da furta "Alhamdulillah. Wacce ke gefenta ta d'ago tana kallonta "badai har kingamaba? "Gashinan idonki yabaki amsa. "Uhmm lallai Bahijja kinji dad'inmi ke komi baya miki wuya sam musamman darasin turanci da lissafi. Murmushi tasaki tare da matse hannayenta wuri d'aya sukayi 'yar qara sannan ta amsa "kema wasa kikasa aranki maryam amma da komi baya miki wuya, sabida haka kima kanki fad'a kikoma kamar da yadda nasanki da maida hankali akan karatu. "To qawata xan dage insha Allahu "to Allah ya yarda "Amin. Tamatsa kusa da dayan wacce take ta tsaki tana tura baki, kunnen ta bahijja taja da qarfi wanda sai da tayi ihun axaba, tana liliya kunnin tana hararanta tace "wallahi adda bahijja nakasa samo amsa ne shine abin yabani haushi har nayi tsuki amma kiyi haquri namanta kintsani tsuka sam. "To naji iya surutu, tana dariya ta motso jikin ta tace "to adda taimakamin insamo amsa ko na tsira daga bulalan mr.Joshua.

Cikin taqai taccen lokci taga yimata bayi tare da samo amsar, cikin jin dad'I tace "Allah yabiyaki da aljanna addata mai sona"Amin maryam ta amsa wacce itama ta kammala aikinta.
Nana ta cigaba da cewa "wallahi mr Joshua baya da imani kuma bai wani iya kayarwaba sai uban cewa kungane? Inba a amsaba yabi kowa da bulala akan dole ake cewa angane alhalin ba agane komiba, maryam ta amshe da "wallahi kam maganarki hakane Nana, dawani qaton muryansa kamar ana buga duro, aiko suka sa dariya har da kyalkyalewa, ita dai Bahijja murmushi tayi domin bata fiye yin dariyaba.
Tace dasu "shiyasa ba kugane koyarwansa sabida kun rainashi "uhm adda Bahijja kenan, kedai kinji dad'in kinga kina ganewa amma Allah kowa yasan baya bayani mai kyau ko yaya musa naji yana maganar baya fahimtar komi "wani musan? Maryam ta tambayeta. "Na gidanmu mana; dariya ta kwashe dashi har tana riqe ciki, cikin fushi Nana tace "miye haka wai? Ta tsagaita da dariyan tana mai cewa "gani nayi yaushe yazo makaranta da zaisan malamin dake koyarwa da kyau da mara kyau. "Uhmm kumafa maganarki hakane maryam, yaya musa baison karatu sam daga boko har addinin, inaga qila wurin abokansa yaji suna fada, "to saidai haka kam.
Bahijja tayi shiru tana sauraransu zuwacan taja ajiyar zuciya duk suka kalleta idanunta lumshe tana murmushi. Maryam ta dafata "ya akayi kuma haskenmu kuma matar yaya bilal. Idonta ta bude sai kuma taqara kullewa, cikin sanyin muryanta tasoma magana "kewar ummata da yaya bashir ya dameni sosai akwana kinnan. Inajin lokaci yayi da zan nemi ganinsu koda gwagwgo bata saniba zan tsere intapi wurinsu. Cikin jimami Nana tace "Adda Bahijja kinsan garin dasu kene? Kuma zaki iya gane hanyane? Hawaye ya zubo mata ta share da bayan hannunta sannan ta amsa "bansan hanyaba Nana amma nasan sunar garin. "To ki haquri adda watarana zakigansu yanxu kada ki gudu wani abu yasameki na cutarwa ahanya. Maryam tace "Eh Bahijja ki haquri inkinyi aure sai mijinki ya kaiki. Cikin jan ido muryanta na rawa tace "wallahi bazan bari sai nayi aureba. Ko angaya muku ni zanyi aure a qauyennan ne? Duk suka zaro ido maryam tace "garin namune qauye kuma? Bata amsaba ta miqe tabi hanyar ajinsu inda aka rubuta js 2A.


*mrs j moon*
[12:40PM, 7/5/2017] mrs j moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*

*05*
Suna dawowa daga islamiyya Nana ta dubi Bahijja "Adda mu shiga gidan Adda hindu mudubo jikinta naji dadana dazun tana fadawa malam xata dubota wai bata da lafiya. "Subbahanallahi! Allah yabata lafiya "Amin.

Hindu ta haife cikin jikinta amma yazo ba rai, watan ta hud'u da haihuwa tsohon saurayinta kamal yafito neman duk da sukan da 'yanbani na iya sukeyi masa akanta na tayi abinkunya me zaiyi da ita amma yayi kunnen shegu da su sabida iyayensa sun amince masa, ba adau lokaci mai tsayiba aka sha biki ta tare gidan mijinta, yanxu haka ciki tasamu mai laulayi sosai.
Basu juma suka fito ta rakosu har bakin zaure tana yi musu huduba akan suriqe mutuncinsu banda kwadayi domin shi yakaita yabaro abaya gashinan har yanzu tanbon bai bartaba danjin miji suna goranta mata in har wani abu yahadasu duk da bashiga shirginsu take yiba.
Bahijja ta amsa "kada kisa damuwa Adda hindu, ki bar kulasu, mu kuma kiyi tayi mana addu'a Allah zai karemu "to Bahijja xan qara akan wanda nakeyi, suka amsa "mungode. Tana murmushi tace "kugaidamin da su gwagwgo Nana kice dadarki gobe ta aikomin da dafaffiyar xogale,"to. Ke kuma kiyi ta haquri da gwagwgo "tam Allah yaqara mana haquri da juna "Amin.
Ana sallar magrib suka isa gida. Gwg lanti tana kicikicin tuqa tuwo. Ahankali Bahijja ta qarasa tace "sannu da aiki gwagwgo, kallon banza ta watsa mata batare datace qalaba, jiki asanyaye ta qarasa dakin ta dauko buta zatayi arollah tana fitowa gwg Lanti tasawo kai aiko sukayi karo da juna, batayi wata wataba tasoma zabgawa Bahijja mari tana kaimata bugu da qafa ta ko ina, kuka takeyi cikin sauti mara qara don haka bawanda yajita balle akawo mata dauki. Tuni hancinta yasoma zuban jini da gefen bakinta. Nana ce taxo kawoma mata littafin tajwid d'inta taga abinda gwg Lanti keyi ta kwalla ihu gwg bintu ta kwaso da gudu tayo qafar Lanti, salati tasa sadda taga Lanti kan Bahijja tana duka kamar tasamu sa'arta.

Sai sannu gwg Bintu take jeramata baya ta ceceta ahannun gwg Lanti wanda takusa illah tata haka kawai don rashin imani irin nata.
Malam nadawowa sallah Nana ta fada mishi tana kuka afusace yazo yasami gwg Lanti yayi mata tas kuma yace daga yau intaqara dukan marainiyar Allah bai yafe mataba, daganan ya tasata sukatafi chemist, ahanyarsu na dawowa yayi tamata nasiha na tayi haquri yakusa hadata da ummanta kwanan nan insha Allahu. Aiko tanajin haka tasoma murna tana dariya kamar ba itace mai kukanba.

Yau suke saukan AL-QUR'ANI mai girma ita da Nana da qawarta maryam kuma k'anwar bilal.
Bilal da maryam Ya'yan sarkin garinne kuma sarkin abokin malam
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment