Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sanarwa me martaba,,rungumeshi tayi tana godiya ckn jin dadi tare da fatan Allah yasa a dace don tasan me martaba baxai k'i ba,mikewa sukayi suka fito suna manne da juna,suna zuwa kofa suka saki ita tayi bangarenta shikuma yanufi b'angaren me martaba.




*Karku manta littafinnan na kud'i ne na maidashi free saboda murnar sabuwar shekara 2020,,To matukar bana samun comment's yanda nakeso zan maidashi na kud'i maganar gaskiy,.*






*COMMENTS*
*&*
*SHARE**'Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟*
{Historical fiction}





*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻



*SURAYYERH B.ABDUL*

Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k*


Special gift to my besty Rabin raina *UMAMATU UMAR ADAM*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


Munfara biki yau kuma zamu gama ranar Sunday,, banyi muku alkawarin typing a y'an kwanakinnan ba amma idan nasamu time zanyi,idan kunjini shiru sai zuwa Monday insha Allah.


*PAGE 9*


Duk inda yarima sameer ya gifta zakuga bayi suna zubewa suna gaisuwa,shikam fuskar nan a had'e bai ko daga musu hannu balle ya amsa,yana shiga fada ya tadda me martaba da waziri da alamun magana sukeyi don su biyu ne,sallama yayi sarki da waxiri suka amsa fuskarsu dauke da murmushi,,fuska ba yabo ba fallasa ya gaishe su suka amsa,,ckn kulawa mai martaba yace "Yadai yarima lpy ko???",, gyara zamansa yayi yace " lpy klau me martaba dama muna Neman izininka ne zamu koma India a sake dubamu saboda princess ta damu da yawa",,girgiza kai me martaba yayi ckn tausayawa yace "Ku kwantar da hankalin ku yarima komai lokaci ne karku damu,kuma babu damuwa insha Allah saiku shirya tafiyar,,waziri ne yace " Yarima yana godiya ranka ya dad'e,,godiya shima yarima yayi sannan yasanarwa me martaba haihuwar kanwar gimbiya jalila,sannan yasanar masa dagacan zasu wuce India amma batare zasu tafi ba zaizo yasameta,, ckn farin ciki me martaba yace "Jiya sarki abdulkhareem yakirani yafadamin haihuwar,babu damuwa dagacan din sai ku wuce"sundan jima suna hira kafin yarima yai musu sallama ya tafi.


Yau muwadda tunda ta tashi daga bacci take wani matsanancin ciwon kai,,sosai ta daure har tabaro gidan iya bata gane ba don bataso tasani tashiga damuwa,da wuri tazo tayi dukkan ayyukan data sabayi,dakyar ta iya yimusu chips da wainar kwai,sannan tai musu farfesun kifin ruwa da hadadden kunun gyada, tadafa ruwan tea tazuba a flask,gajiya tayi da tsayuwa saboda yanda takejin jiri yana dibarta,zamewa tayi da durkushe a wajen ta dafe kanta tana fitar da wani huci me zafi,da alama zazzab'i ne ya kamata saboda rawar da jikinta yadauka kuma yayi zafi rauuu,,ta shafe fiye da awa daya a haka kafin gimbiya jalila da yarima sameer su fito,yauma kamar kullum shigar su iri daya suna rike da hannun juna,hango muwadda a tsugunne yasa gimbiya jalila tayi tunanin ko bacci take yi,kwafa tayi a fili tace " Yarinyar nan sai na koya miki hankali don na fuskanci kin haukace yanzu,, sakin hannun gimbiya jalila yarima yayi yafita amsa waya,karasawa tayi kusa da muwadda ta zuba mata rankwashi wanda yahana muwadda ko motsawa saboda azaba,don ji tayi tamkar an fuzge mata kai,,ganin haka yasa gimbiya jalila tayi tunanin kamar raini ne yahana muwadda dagowa,,a fusace ta hankad'ata ta bugu da bango saida tayi k'ara saboda tsananin azaba,, dago idanunta tayi da sukayi jajir suna zubar kwalla takalli gimbiya jalila,, durkusawa tayi ckn rawar murya irin ta mara lafiyan da ya galabaita tace "Allah ya huci zuciyarki ranki shi dad'e, ayimun Afuwa banda lpy ne",,, A fusace gimbiya jalila tace " Bakida lpyr uwarki!!Y'ar iskar yarinya,to ko suma kikeyi ni baidameni ba don ba kaunarki nake ba,na tsaneki!!!! Dallah taso kibawa mutane abinci!!!ta fad'a a tsawace,,jiki na b'ari kuyanga muwadda ta mike, dai² lkcn yarima sameer yadawo,zama yayi tayi saving dinsu,tana tsaye a kansu har suka gama,dauke Warmer's din tayi tamaida kitchen tadawo ta gyara wajen,gimbiya jalila ce cikin tsana da wulakanci tace "Keee k'ask'antacciya wuce ki kiramin jakadiya",,, Dasauri tafita gudun kartayi laifi,,tana tafe tana had'a hanya kamar zata kifa,wata kuyanga tagani a hanya ta tambayeta ina jakadiya,amsa mata tayi da tana b'angaren amarya,,tana shiga tazube tana gaida amarya ckn muryarta da bata fita sosai,,da kulawa amarya ta kalleta tace " Yadai muwadda kina lpy kuwa???,,wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata masu zafi,dasauri tace "Eh..eh..ranki ya dade lpy ta kalau ,dama gimbiya jalila ce tace nakirawo mata jakadiya",,, Shiru amarya tayi tana kallon muwadda,kallonta ta maida kan jakadiya tace " jeki kiran da ake miki",,,mikewa tayi taimata sallama ta fita,kuyanga muwadda tana durkushe kanta a kasa tunda ba'a bata umarnin tashi ba,,da kulawa amarya tace "Muwadda matso nan",, Dasauri muwadda tadago idonta tasauke akan amarya don ganin tana nuna mata kusa da ita a matsayin wajen da zata zauna,,dasauri tashiga girgixa kai alamun a'a,,amarya sallamar kuyanginta tayi yaxama daga ita sai muwadda,tasowa tayi tanufo wajen da muwadda ke tsugunne,jin takunta ne yasa muwadda dagowa dasauri,wata iriyar zabura tayi tamike tare da hada hannuwa biyu ckn rudewa tace " Don girman Allah ranki ya dad'e ki koma wlh zan karaso,,murmushi amarya tayi ganin yanda muwadda ta rud'e,ba musu takoma tazauna,ajiyar zcy muwadda tayi ckn sanyin jiki ta karaso wajen amarya ckn muryarta me sanyi tace "Gani ranki ya dad'e",A hankali amarya takai hannunta ta ta'ba goshin muwadda,"subhanallah",, Tafada tare da dauke hannunta dasauri,ckn kulawa tace " Haba muwadda meyasa bazaki fada bakida lpy ba???,,kanta yana sunkuye takasa cewa komai sai hawaye da ke tsere a kuncinta,ckn rashin jin dadi amarya tace "muwadda idan bakida lpy kidinga Neman uzuri kina zama a gida kinji???Ai lpy tafi komai",, Gyada kai muwadda tayi a zuciyarta kuwa cewa tayi ", Ashe da najawa kaina bala'i",, Wani abu amarya ta danna saiga daya daga ckn kuyanginta tashigo tadurkusa tareda fadin " ranki shi dad'e gani"batareda kallon banza da raini ba tace "Kawowa muwadda abinci sannan ki kiramin likitan da yake kula da bayi", Ckn tsananin girmamawa tace " Angama ranki ya dad'e,nabarki lpy",,muwadda a ranta tace "Kukam kunji dad'in ku kunyi dacen uwar daki"don ita ynz haka tunanin abinda zata koma ta tarar na rashin dawowarta da wuri take yi ,dawowar kuyangar nan tayi dauke da hadadden abinci da lemuka da ruwa tareda fruit's aka ajiyewa muwadda,,kinci tayi kanta yana kasa saida amarya tace " muwadda kici mana kisha magani",,Tsakura tafarayi kadan² don ita idan tana rashin lpy matsalar ta kenan batacin abinci saboda indai taci sai tayi amai,aikuwa takai loma ta uku tafara yunkurin amai,da gudu ta mike tafice daga dakin, can gefe ta durkushe tadinga kwararo amai kamar zata amaye y'an hanjin ta,abinda yabawa muwadda tsananin mamaki bai wuce ganin amarya a kanta ba tana jero mata sannu ckn tausayawa,,wata iriyar kaunar matar ce ta shigeta don mu'amala ba shiga tsakanin su takeyi ba batasan halayyar amarya ba,,nan amarya tasa aka wankewa muwadda amai sannan suka koma ciki aka kawo mata sababbin kaya, wanka tasata taje tayi sannan tasa kayan,,tea ta hada dakanta tanufi bakin muwadda xata bata,dasauri takauda kai kanta a kasa tace "Ranki ya dade xansha da kaina",, girgixa kai amarya tayi,badon muwadda tasoba amarya tadinga bata balaifi tasha dad'an yawa,kuma ikon Allah balayi amai ba,nan likita yazo ya dubata akai mata allurai,ba' a jimaba bacci yai gaba da ita",, Kafeta da ido amarya tayi tanajin yarinyar ranta fiye da dukkan sauran bayin gidan,haka kuma tana tausaya mata,gata masha Allah akwai tsananin kyau,sai takeji inama muwadda a bangaren ta take,tasan muwadda akwai tsananin biyayya da rashin surutu,gulma da sa ido irin na gidan sarauta duk bata ckn shirgin,abinda ke gabanta kawai take yi.




Bayan jakadiya taje kiran da muwadda ke mata ne tabata umarnin za'ba mata bayi uku wad'anda xa'ayi tafiyar dasu,tashin farko jakadiya tace " Muwadda ta daya sai falmata,sannan nasiba,ina ganin wannan sunyi ranki shi dad'e",,Ckn gyatsine tace "yayi"wai ina kuyanga muwadda'n take???,ckn girmamawa jakadiya tace " Tana wajen hajiya amarya ",,Jin ance amarya ne yasa gimbiya jalila yin shiru don yarima na zaune a wajen.




Muwadda tasamu sauki sosai,tana kokarin kiyaye duk wani Abu da zaisa a dinga cimata mutumci amma hakan bai hana aci mutumcinta ba kp tayi laifin kp batayi ba,,,ana gobe tafiya aka sanar dasu,,muwadda bataji dadi ba Sam,amma ubaida ta kwantar mata da hankali xata rika zuwa wajen iya,itama iya bataji dad'i ba amma sosai ta danne ta nunawa muwadda bakomai tunda fa muwadda,,har ta gamsu dasu tasaki ranta,sauran da aka zab'a kuwa kamar suyi hauka saboda zasuhau jirgi,muwadda kuma wannan karonta na biyu kenan.



Yau takama tafiya,,jama'a sunfito anatayi musu adawo lpy,dukda basusan abinda zai kaisu India ba,sunje sumyiwa me martaba da sauran y'an gidan sallama,me babban daki dariyar keta kawai takeyi,a ranta take fadin " Wahala ce bata isheku ba,ku da haihuwa sai dai kugani anayi",,Amma a xahiri fatan alkhairee tai musu,, shi yarima bandashi a tafiyar yau,daga baya zai tawo,har airport suka rakasu ,basu jimawa jirginsu yadaga kasar Nigeria mahaifar gimbiya jalila don a masarautar kano take ",,,Danginta sunyi murna da ganinta,,itakam sai sake wulakanta su muwadda takeyi saboda isa,muwadda ta tafi da imanin mutane da yawa,hakan ba karamin sake hasala gimbiya jalila yayi ba don kowa yaganta sai ya tanka,,sai yaxama wulakancin muwadda daban ne,dama kuma tafi tsanarta,ana gobe suna yarima sameer yazo,,gimbiya jalila tana nanike dashi musamman yanda taga y'ammatan suna shishshige masa,donma shima ogan kansa ne wajen shan kamshi ,,anyi suna lpy jariri yaci sunan Abubakar,,anyi taro na karya da karya tareda ji da kai,su muwadda sunga ikon Allah,sunga inda ake wulakanta kud'i kamar bola,,washegarin suna suka wuce India,, bayan maghriba sukaje,a wani hadadden hotel suka sauka,bayan sunyi sallah sukaci abinci,yarima sameer ne yakira likitan da sukazo gani ya sanar dashi gobe zasu shigo asibitin,a ranar gimbiya jalila da su muwadda da wuri sukayi bacci saboda gajiya,banda yarima da ya dauro alwala yazo yadinga sallah yana rokon Allah yasa sunzo a za'a,,yasa sunada rabon ganin kwansu a duniya,,Sai kusan karfe hudu bacci ya dauke shi.


Washegari motoci har gida sukazo daukar su zuwa asibiti,,duk inda yarima ya gifta xakuga ana gaishe shi ckn girmamawa,har suka karasa office din likitan,,yana ganin yarima yataso da sauri suka rungume juna,ckn harshen turanci suka gaisa bayan yasa ancika musu gabansu da kayan motsa baki,sudai su muwadda suna tsaye suna gadinsu,sauran sai raba idanu sukeyi sungansu a wata duniya,,bayan sun dan tab'a hira ne likitan yajasu wasu daki yashiga dubasu,su muwadda suna wancen dakin ba farko,akalla yashafe fiye da awa yana dubasu kafin ya gama,hada kayan aikin yayi yamaida inda suke kafin yadawo ckn kulawa da damuwa a fuskarsa yafara musu bayani "A Gaskiya nayi iya yina amma narasa dalili kamar da dai har yanzu mahaifar gimbiya bazata iya daukar ciki ba,,sai dai inada shawarar da zanbaku dukda ban tabbatar zaku dauketa ba",,, Share hawaye gimbiya jalila tayi ckn rawar murya tace " Matukar zatasa naga jini na mezai hana mu dauka",,Kallon yarima sameer doctor yayi,,gyada masa akai yarima yayi alamun "Muna jinka",,, Gyaran murya yayi sannan yace " ina ganin me zai hana a dibi sperm dinku a hada a dasa a wata mahaifar sai ta haifa muku,ai danku ne shima",,,dasauri yarima ya kalleshi yana yamutsa fuska,yayinda gimbiya jalila takafeshi da ido tana murmu*'YANCIN BAYI*
{Historical fiction}




*STORY WRITTEN BY*✍🏻

*SURAYYERH B.ABDUL*

Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k*

Special gift to my besty *UMAMATU UMAR ADAM*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


*PAGE 10*


Ganin sunyi shiru ne yasa doctor yaci gaba da bayani"Ni a gani na hakan ba wata damuwa bane indai har zaku samu wadda za'ayiwa dashen,sannan.....Ya isa plz!!Cewar yarima sameer cikin kosawa da maganar doctor,kamar bayason mgn yace "wannan maganar Sam kabarta doctor don abine Wanda baxai yuba,akan me za'a dibi sperm dina Wai a zubawa wata,never!!,ai wannan cutar da wadda aka sawa ne,idan ma batada aure mene matsayin budurcinta???Idan tarasa Shi fa????,,Dasauri gimbiya jalila tace "To ai wannan Abu ne me sauk'i prince,me zai hana tana shiga watan haihuwarta sai ayi c.s a ciro Mana yaron namu??Kaga kenan baza'a samu matsala ba muma Kuma zamu samu cikar burin mu,,,,tunda gimbiya jalila tafara magana yarima yake yimata wani d'an iskan kallon Amma bakida hankali,tana gama magana yaja wani d'an iskan tsaki yamike cikin bacin rai yabar dakin,a ransa yana ayyana cewa lallai gimbiya jalila ta haukace,,,ganin haka yasa gimbiya jalila tamike tsaye idonta akan doctor tace "wannan ba matsala bace doctor zamu dawo Kuma za'ayi dashen",,Gyad'a Kai kawai doctor yayi badon ya yadda zasu dawo din ba don baiga alamar yarima zai amince da hakan ba saboda yanda yaga ya fusata Kuma yasan halinsa.

Su muwadda suna inda su gimbiya suka barsu sukaga wucewar yarima sameer kamar a fusace yake,ba'a Jima ba Kuma sai ga gimbiya jalila itama dai kamar tana ckn damuwa,kafin suyi wani yunkuri sukaji muryar ta a tsawace tana fadin "Don ubanku ku mahaukatan ina ne???Uban me kuke jira da baxaku wuce mutafi ba??!!!,dasauri suka rufa mata baya suka fito,suna fitowa suka hango d"aya daga cikin motocin da suka kawosu tafice daga hospital din,ko ba'a fadawa gimbiya jalila ba tasan yarima ne,shiga mota tayi su muwadda ma suka shiga tasu,gimbiya a ranta take fadin "duk abinda xanyi don ganin ka amince zanyi Shi yarima Kuma xaka amince ne,matsala ta daya bansan wa za'ayiwa dashen ba",,Kai tsaye hotel din da suka sauka suka nufa.


Yarima sameer ne tsaye gaban mirror yana taje hadadden gashin kansa da ke ta zuba kyalli gimbiya jalila tashigo da alamun itama tayi wanka saboda ta canja kayan jikinta,ta jikin mudubi ya hangota Amma Sam bai nuna yaji shigowar ta ba saima cigaba da shirinsa yayi hankali kwance,ganin haka yasa ta k'araso inda yake tarike turaren da yake fesawa idonta a kanshi,kawar da kanshi yayi tareda sakar mata turaren yadauki wayarsa yana kokarin barin wajen,,dasauri tasha gabanshi idonta taf da kwalla tace "Don girman Allah prince katsaya muyi magana,,Sam baiyi niyyar tsayawa ba Amma jin tace girman Allah yasa yatsaya tareda kafeta da shu'umin idanuwansa Mai dimauta y'ammata,,ajiyar zuciya tayi tanajin yanda kirjinta yake bugawa,dakyar ta saita kanta tace "Mene abin fushi kuma prince??Ai ni a gani na abin farin ciki ne,abinda muka jima Muna nema shekara da shekaru Amma why zakayi haka???,,cikin hasala yarima Sameer yace "Keee karki rainamin hankali nifa ba shashasha bane kuma inada hankali,inason ki fadamin ta yaya su Mai martaba zasu yadda da wanna banzar maganar,,saboda haka yakamata kisan abinda kike fad'a,neman haihuwa ai ba hauka ba ne,sannan ki kwana da sanin gobe zamu koma gida,yakarashe yana kokarin wucewa,dasauri tarikosa tareda sakin wani marayan kuka tana fad'in "prince wannan abin fa ba haramun bane,akanme baxaka tausayamin ba Naga kwaina a duniya,,wlh ina matukar kaunar yara don Allah prince ka tausayawa rayuwa ta karkamin haka,shekara bakwai da aure na fa Amma banda d'an da zankalla naji dad'i,don Allah kayimin wannan alfarmar Naga kwaina d'aya ma Tak a duniya don Allah!!!!!,,,A hankali yacire hannun ta daga rikon da taimasa ganin tana neman sauya Masa ra'ayi saboda jikinsa da yayi sanyi ganin yanda take garshek'en kuka sai tabashi tausayi,Amma da yake namijin duniya ne Sam bai bari ta gane ba illa ma d'an iskan kallon da yabita dashi kafin yarab'a ta gefenta yafice daga d'akin,kwafa gimbiya jalila tayi tana share hawayenta kafin a fili ta furta "Matukar dai ni d'ince jalila dolenka ka amince prince!!!.

Su muwadda ne zaune a d'akin hotel d'in da suka sauka,hira sukeyi jefi jefi maganar muwadda bata wuce "Eh" A'a",Saboda gabadaya hankalinta yana kan mahaifiyar ta,tanason sanin halin da suke ciki,tanason jin muryarta Amma ta ina??Tasan dolenta hakuri zatayi har zuwa ranar da zasu koma wadda sudai basu santa ba a matsayinsu na y'an rakiya wadda ba wata k'ima ce dasu ba,,ajiyar zuciya tayi kafin tamike cikin zazzak'ar muryarta tace "Zan d'an fita waje",,Nasiba ce tace "Ai Kam dai kwara kid'an fita kiga yanayin wajen Amma da kin kule a d'aki kink'i motsi,,hmm Koda yake halinki ne haka Sai kace wata jinin sarauta",,,gajeren murmushi muwadda tayi batareda tace komai ba tafita daga d'akin,don inda sabo ta Saba da yanda mutane suke cewa Wai idan tana Abu tamkar jinin sarauta ,jin Kai tareda Shan kamshi,Wanda ita a zahiri batamasan tana da su ba.

Tafiya takeyi Amma gabadaya hankalinta bayaga tafiyar,don kallon da tafito yi Sam bashi takeyi ba,,batai aune ba taji tayi karo da mutum ,,dasauri ta tsugunna sakamakon wayar wadda sukai karo da Shi da ta subuce ta fad'i,,dai² lokacin shima yakai hannu zai dauki wayar,,haduwar hannuwansu ne yasa muwadda dagowa dasauri Saboda wani shock da taji,tareda wani mugun laushi na kyakykyawan hannun gami da sassanyan kamshi da yake tashi,,ido hudu sukayi da *YARIMA SAMEER* Wanda yai sanadiyyar bugawar kirjinsu lokaci guda,a Matukar tsorace muwadda tamike cikin rawar murya tace "Don girma Allah yarima kayi hakuri wlh bansani ba,,,batare da yarima ya kalleta ba balle ya kulata yaja dogon tsaki Yana karewa hannunsa kallo tareda yatsina fuska ,jiyake kamar ya shaketa Saboda takaicin goguwar hannunta da nashi,ganin haka yasa muwadda taci gaba da fad'in "Don Allah ka tausayamin ranka Shi dad'e wlh....."Kee!!!! "Yarima yakatseta a tsawace Wanda yasa muwadda zubewa dasauri jikinta yana rawa,ckn hasala yace "Ke wace iriyar mahaukaciya ce mara nutsuwa????Baki iya magana d'aya ba ne??Kindamu mutane da surutu da wani k'azamin banzan bakin ki,mtsewww yaja tsaki yabar wajen,,,Cikin tsantsae takaici muwadda tamike tana share hawayen da yake tsere a kumatun ta,itakam Sam a rayuwa tarasa meyasa masu mulki suke son yiwa na kasansu wulakanci,sunason k'ask'antar dasu su a dole sun fisu,,jitayi gabadaya ma baxata iya fitar ba,jiki a sanyaye takoma d'akin su.


Yarima kuwa yaja tsaki yafi cikin kwando,,gabadaya ma kyankyamin hannunsa yakeyi,d'aki yakoma inda ya tadda gimbiya jalila tanata kwasar baccin ta, bathroom yafad'a,yashiga wanka,dirje hannun yadingayi sosai tamkar zai sauya wani,yanayi yana yatsina fuska yana jan tsaki,,yadauki lokaci me tsawo kafin yabarshi haka badon ya yadda yafita yanda yake so ba,,fitowa yayi d'aure da towel hannunsa Kuma wani karami ne sky blue colour Yana goge lallausan gashin kanshi dashi,,shiryawa yashigayi lakwai² skin tamkar wata gold,yadauki lokaci kafin yashirya cikin wasu hadaddun riga da wando yasa masu tsananin kyau da tsada,red nd black colour,sannan yadora jacket a sama,,kamshin sassanyan turaren sa ne ya farkar da gimbiya jalila,,a hankali ta bude idonta tana k'are masa kallo,,wata iriyar muguwar kaunarsa takeji a kowani sassa na jikinta,,a hankali ta zuro k'afafunta tasauko,ra mirror ya hangota Amma bai juyaba,tana zuwa tayi hugging dinsa ta baya ckn iyayi tace "My prince kayi kyau da yawa fa",,Gajeran murmushin sa yayi tareda mirginota tadawo gabanshi,ckn kulawa yace "Kema haka",,Dariya tayi tana k'ara makalkaleshi,ganin lokacin salla yayi ne yasashi zameta Yana fadin "Kije kiyi wanka Kema ni zanyi salla ne",,Dasauri ta rikoshi tasa gwuiwowinra a k'asa tana hawaye tace "Wannan Shi ne karon farko da natab'a neman alfarmarka a rayuwa ta prince,,idan bakayimin va wlh bakin ciki zai iya kasheni,,Zan koma ga mahalicci na da Wannan tabon na kunci,don Allah ka tausayamin ka amince tunda ba haramun ba ne,ko ckn sirri zamuyi abinmu babu Wanda zai sani,wlh zanyi yanda kowa zaiyi tunanin nice na haihu da kaina,,Wannan sirrinmu ne mu kad'ai,,,"Ita Kuma wadda za'ayiwa dashen fa???yajefa mata tambayar,,Dasauri tace "Zatasani Mana prince",,Idonsa a kanta yace "Wace ce ita????cikin zumud'i tace zansamo wlh prince Zan samo,,mikewa yayi yadauki dadduma yatada sallah don matuka karshe tabashi tausayi Kuma ta raunata mishi zuciya tayaji tayi zancen mutuwa,shiyasa har yakejin zai amince,musamman da gimbiya jalila tace Masa zasu iyayi a sirrance har ace itace ta haihu batare da me martaba da kowa yasani ba.

Ita kuwa gimbiya jalila kamar tayi hauka Saboda farin ciki,don yarima Yana sallah tana zuba tsalle,hangota takeyi kawai gata rike da baby,,addu'a tashiga you Allah yabasu namiji don Shi tafi so tunda sune masu mulki,,tunani tashigayi wadda za'ayiwa dashen,tanason yarinyar taxama kyakykawa,me hankali,me nutsuwa,uwa uba shiru me sirri,,tunani tashigayi a kaf bayin masarautar su Wace tahad'a siffofinnan,,naxari tashigayi Amma a iya tunaninta tagaxa samu,lokaci guda zuciyarta tabata *KUYANGA MUWADDA!!!*,,,A fili ta maimaita tabbas muwadda itace yarinya me tsananin sirri tareda tsoro,baxata taba tona sirrin ba,,mikewa tayi ckn farin ciki tana tsalle tashiga bathroom yin wanka.


Bayan gimbiya jalila tayi wanka tafito tashirya tayi sallah,,sunacin abinci da yarima tanata zubamasa hira Saboda tsananin farin cikin da take ciki,sanar masa tayi yarinyar da ta yanke shawara a kanta,,wani d'an iskan kallon bakida hankali ta wurga Mata,,cikin kissa tashiga yimasa abubuwa tana fad'a Masa dalilanta,da yaduba Kuma Sai yaga gsky tafad'a,,Amma Shi Sam baiso haka ba Saboda baya kaunar ko ganin muwadda Sam,,a Daren ranar suka Kira doctor suka sanar dashi,sosai yayi mamaki kafin yace gobe da karfe 11 na safe suzo da yarinyar ayi aikin tunda tashin yamma zasuyi,,a ranar gimbiya jalila tamkar ta zuba ruwa a k'asa Tasha Saboda farin ciki,,yarima Sameer kuwa yaga tsantsar soyayya tamkar zata cinyeshi a daren ranar.




*Plz kutayani addu'a Allah ya shirye ni nadinga typing akan lokaci🤪🤪don wlh naxama lazy wajen typing ynz😰*

```Typing error zaku iya cin karo da Shi don bansamu damar editing ba```shi.*'YANCIN BAYI*
{Historical fiction}



*STORY WRITTEN BY*✍🏻

*SURAYYERH B.ABDUL*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________



Page d'innan kyauta ne gareki *MUNAYAH* ta Kainuwa fitatttu,ina ganin comments d'inki kuma yana sani nishad'i,godiya tik'a tik'a.




*PAGE 12*



Wata kuyanga ce tayi sallama ta shigo parlour'n,cikn girmamawa ta zube a k'asa ta ce "Ranka shi dad'e yarima Yusufu ne ya ce yana so a mashi iso wajen ka",sai da ya b'ata lokaci kamar ba zaiyi magana ba sannan ya ce "A shigo da shi",godiya kuyangar ta yi sannan ta fice.


Da sallama yarima Yusufu ya shigo fuskarsa d'auke da murmushin da ya zame masa jiki, tasowa yarima Sameer yayi sukayi hugging juna cikn farin ciki,zama sukayi a had'ad'd'un kujerun da suka yiwa parlour'n k'awanya, yarima Yusufu ne ya kalli wajen da gimbiya Jalila take tana cin abinci,cikn tsokanarsa ya ce "Ahhh matar prince don kar na ce zan ci abincin ne ya sa aka k'i yimin magana?,tab'e baki ta d'anyi kafin ta yamutsa fuska,murya k'asa² ta ce "ya kake?, ba yarima Yusufu kad'ai ba kaf d'insu sun ga abin da tayi,amma dayake me sanyin hali ne shi kawai sai ya basar ya ce "ina lpy",.


Mik'ewa tayi tareda k'arasawa kusa da yarima Sameer tana wani iyayi ta ce "My prince zan je gidansu yarinyar can ynz",ta fad'a tana nuna Muwadda wacce ta juya bayanta tana kwashe kayan abinci, ba'a ganin fuskarta ta b'angaren da su yarima Yusufu suke,shiyasa ma sam bai ganta ba.

Yarima Sameer ya ji haushi da tayi masa maganar a gaban yarima yusufu amma ganin yarima yusufu'n ya sa ya gyad'a mata kai kawai alamun to,peck tai masa a kumatu kafin ta fice.


Juyowa Muwadda tayi da niyyar kai kaya kitchen, karaf suka had'a ido da yarima Yusufu,ta d'an tsorata da ganin shi don tana tsoron ya ja mata fitina,shiyasa tayi saurin kauda kanta ta fara tafiya,yarima yusufu da gabad'aya ya d'imauce da ganin Muwadda,wani irin abu yake ji yana fuzgarsa da k'arfin gaske game da ita,zuwa ynz ya tabbatarwa kansa zuciyarsa son Muwadda take yi,kuma da k'arfin gaske,shiyasa ya d'aura d'amarar d'auka tare da rungumar duk wani tashin hankali da zai tunkareshi a hanyarsa ta mallakar ta ,saboda ya riga ya sani ba k'aramin tashin hankali za'a yiba da mahaifan shi a matsayinsa na yarima yace wai zai auri baiwa,tab'osa d'in da yarima Sameer yayi ne ya sashi juyowa da sauri yana murmushi,shi ma yarima Sameer d'in murmushi yayi cikin k'aunar k'anin nasa ya ce "yadai?",sosa k'eya yarima Yusufu yayi kafin ya d'aga ido sama cikin shaukin soyayya ya ce "Wlh ina matuk'ar k'aunar ta",da sauri yarima Sameer yace "Wa kenan?",batare da ya bashi amsa ba ya juyo ya rik'e hannuwansa duka biyun ckn raunin murya yace "Wlh komai zan iya a kanta shiyasa nake tausayawa kaina,ban san cewa haka zafin so yake ba sai a kanta,don Allah yayana inason idan lokaci yayi ka taimake ni ka jajirce wajen ganin na mallake ta, shi ne mafi girman so da za ka nunamin a rayuwata saboda ita ce rayuwata".

Cikin tsokana yarima Sameer ya ce "Tabd'ijan!,wace ce wannan k'atuwar b'arauniyar da take neman rikitamin k'ani haka?,kuma y'ar wani sarki ce da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

1 Comments On YANCIN BAYI 1
avatar
fatima-abdullahi-5

11 months ago

Reply

Please how can i get the complete book

Please Login or Register in order to submit comment