Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ASOKORO ba dan akwai go slow, akwai wata short cut hanya dazanbi yanzun nan zakiga munkai ranki shi dade".



Chat me up directly by clicking on this link
https://wa.me/+2347012181461



_This is the only free page of this book, like I said, wanan novel din bakaman normal novel dina bane, I interviewed so many couples, I want to show the world inda akafi samun matsaloli arayuwan auren mu tayau and how to go about it. I trust my fans, u all knows yanayin rubuta, ku gyara zama, wanan littafi shine ga darasi gakuma dadi, lemme say it again please 🔞, anybody less than 18 shouldn't read this book, thank you._

Chat me up directly by clicking on this link https://wa.me/+2347012181461


_This book is 2k, idan kinaso pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank and send evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting_









💫 _MATAN ASOKORO_ 💫





✍🏾M SHAKUR

_RANAKUN POSTING *SUNDAYS*, *TUESDAYS,* *FRIDAYS*_


_DAN GIRMAN ALLAH KARKI KARANTA THIS BOOK IN BAKI BIYABA, KUJI TSORON ALLAH_



EPISODE 2️⃣




Ko alamun taji magananshima batayiba saima cigaba da danne dannenta datayi awaya tana chatting a group dinsu na ASOKORO WIVES, gajiya tayi saikawai ta ijiye wayan sabida yanda kanta kewani irin sarawa datarasa maisa, sanan gently ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido. "Hajiya wai lapiyanki kalau"? Bude idanunta tayida sauri jin Murtala yasake mata tambaya ta madubin mota suka hada ido dan gajeren wahalallen tsaki taja tamaida idanunta ta lumshe su ahankali back, maida hankalinshi yayi kan tukin harsu ka shigo ASOKORO District, Usman katsina street suka shiga yay horn agaban wani makeken mansion da tsayawa bayaninshi aikine ganin ba'a bude gate dinba yasa yace "auuuu kullum saina manta abin nan" yay maganan yanadan juyowa ya saci kallon Hajiya yaga tana kaman bacci danhar lokacin idanunta a lumshe yasan inda idanunta biyu datamai bala'i kan kullum saiya mantada remote din da ake bude gate dinsu dashi, remote din dake motar yadauka ya danna gate din yabude sanan yasa kan motan suka shiga cikin gidan gate din yarufe kanshi, kafin ahankali yabude kofa yafito sanan yazagayo ta bangarenta yabude kofa tareda bending kanshi cikeda respect yakira sunanta ahankali danya tadata daga bacci. "Hajiya, Hajiya" dan bude idanunta tayi ahankali tazubasu akanshi awulakance, baidamuba yace "mun iso gida ne daman saisa natadake" yunkurowa tayi tanajin kaman kanta zai fice amman saita daure tafito hakan yasa shima ya matsa yakoma baya, fitowa tayi daga motar ta tsaya da kyau da sauri tasake kulle idanunta jin wani irin jiri take gani hakanan all of a sudden, hakan yasa Murtala daya koma baya yace "Hajiya karkice nacika tambaya amman kaman bakida lpy wlh, duk jikinki ya nuna hakan" bude idanunta tayi tazubamai wani matsiyacin kallo dayasa yaji cikinshi ya murda ahankali yamaida kanshi kasa, daukekai tayi tace "kwasomin jakata da wayata" tai maganan sanan tajuya tafara tafiya gashi daganan parking space zuwa flat dinta dadan tafiya, amman hakan take tafiya ahankali dai dai gudun kartaje tazube dan bamatasan meke damuntaba jitake kaman sauran kiris jikinta yakasa daukanta, akwai staircase haka dazai sadata da kofan shiga flat dinta ahankali take hawa staircase din cikeda karfin hali irin nata da kyar ta iya daga kafanta tahau na karshe batasan meya faruba tadaijita akasa sharaf, sanan kuma taji ihun Murtala sama sama, kara lumshe ido tayi tabude sanan taga Murtalan agabanta ya tsugunna ya haukace yakasa tabata sama sama takeji yana Hajiya, Hajiya, sake lumshe tayi tabude batasan meke going on ba tadaiga waya akan kunnenshi saikuma kawai taji yadauketa, kadan kadan take bude idanunta she could feel and see yanda heart dinshi ke beating, ke racing sosai na fargaban kar wani abu yasameta saikuma dip ta dauke wuta.


Kwantarda ita yayi akan katafaren doguwan kujeran dake falon cikin jerin hadaddun kujerun dake wajen, sanan yatashi da sauri hannunshi har rawa yake ya shiga dailing number Alhaji for the second time yamugun damu dudda yasan Hajiya was never nice to him but still baisan wani abu yasameta.......



Wajen 30 big men ne zaune awani babban conference room, sunci uban suit, wani hadadden magidanci mutum dake zaune kan kujeran CEO ne ke magana yana bayani da turenci, ringing dawayanshi yasakeyi for the forth time yasa yakalli wayan, daukan wayan yayi a hannu yatashi tareda fadin "excuse me" sanan yafita daga conference hall din yakara wayan akunnenshi, kafinma Murtala yay magana yashiga balbaleshi da masifa. "Ka kirani kace tasuma nace ka dauketa ka shiga da ita ciki zan kira Dr, basaika jiraba, saidamuna kake da kira kasan wani irin meeting nakeyi ne? Kaiwani irin wawan bakauyen yarone wai? In nagama I will call d Dr yazo yadubata, kawai yanzu ka tsaya tareda ita, karka barta ita kadai, babu abinda zai sameta ai Hassana is a strong woman she will be fine" ya katse wayan zai maida a aljihu saikuma yaciro yama kashe wayan gabaki daya dan yasan Murtala baida hankali he will keep calling him this meeting is very important anjima idan suka gama zai kira Dr su yasa yaje yadubata, da sauri yawuce yakoma ciki wearing a smile akan face nashi yace "sorry gentlemen let's continue"......




Jikin Murtala har bari yake gabaki daya yama rasa maizaiyi gashi babu kowa gidan, dan ka'idan su shine ma'aikatansu basu kwana, da maid, gardener da sauransu duk dasafe suke zuwa suyi aiki sutafi, koma sunanan shibaisan mezaimataba, yana tsaye kanta chan yaga tai wani irin nishi ta bankare ta tashi, saikuma tafara Jan numfashi kaman numfashinta naso yadauke tana kakkama wuyanta, tsugunnawa yayi gaban kujeran cikeda damuwa yana tura hannunshi a aljihu yana ciro wayanshi zai sake dailing number Alhaji yace "Hajiya meke damunki na shiga uku, Hajiya badai mutuwa zakiyiba" ina Hajiya bamatasan wayeke akanta ba, yay dailing number kashe, sau uku yana kira wai akashe daidai lokacin tafado dagakan kujera tana nishin idanunta na kakkapewa shibaimasan meyakeba kawaidai yaganshi ya dauketa ko nauyinta bayaji yafita da ita daga dakin yawuce yabude mota yasata yagyaramata kafafuwa yarufe sanan yashiga gaba danna remote yayi gate yabude yasakai yafice aguje yana tuki yana juyowa yana kallonta yanda yaga tana battling da numfashi yasa kawai yasaki kuka. "Hajiya kiwa Allah karki mutu, kar yan biyu sudawo Marayu wayyo Allahna" kawai shima yahau kuka kaman yaro, wani babban government asibiti dakenan a ASOKORO yakaita yay parking yana kuka sosai yay cikin asibitin yana ganin wani Dr yafito shida nurse kawai fizgo hannun Dr yayi yana kuka sosai, Dr ma tsorata yayi dan yadauka mahaukaci ne yace "Malam lafiya"? Cikin kuka Murtala yace "Hajiyata batada lpy likita zoka taimaka mata dan Allah bata iya numfashi" jin maganan dayayi yasa Dr yabishi Nurse din dasuke tarena binsu har motansu yakaishi yabude Dr naganin yanda takeyi yama nurse alamu data kawo gado dasauri nurse tajuya shikuma Dr yashiga motan trying to help her yabude mata baki yana tambayan Murtala dake kuka har lokacin yace "meya sameta"? Cikin kuka sosai yace "kaman kanta keciwo saita sume saikuma tafara nishi haka" daidai ankawo gadon da za'a daurata, kallon gadon yayi ya kalli yanda Dr da Nurse ke kokarin cirota su sakata agado yace "ina zaku kaita"? Dr da hankalinshi baya kanshi yace "ward mu mata treatment" dasauri yace "likita karufamin asiri kabata magani anan cikin mota kokamata allura kawai mutafi yan gidansu basa kwanciyan asibiti sunada likitansu na gida, yanzu ma babu kowa agidan ne" likitan baimabi takanshi ba dan daga gani kasan illiterate ne, idan yabar matarnan within good 10min heart dinta zai daina aiki tamutu dan as it is ma yanzu heart dinta is very weak, ciki sukaida ita Murtala nabinsu abaya yana gayamusu zasu sashi a matsala, suna shigarda ita emergency room suka rufo kofa hakan yahanashi shiga, zama yayi akasan wajen yana share hawaye na tausayi dakuma fargaban irin fadan dazaisha awajen Hajiya da Alhaji yau yamusu asalin karambani wlh.



Yana zaune wajen wata nurse tabude kofa tafito yana ganinta yatashi da sauri yace "Ya jikin Hajiya"? "Da sauki, yanzu munsamata oxygen and per hour is 15k, yanzu anaso kai deposit din naira dubu hamsin" da sauri ya kalleta yace "eh dubu hamsin" gyadamai kai tayi tace "yes inba hakaba bazamu cigaba da treatment dinta ba, yanzu dai ansamu munyi stabilizing situation din idan kabiya kudine zamu cigaba" shiru yayi kaman wawa saikuma yace "kucigaba to bari naje nadauko kudin agida" Nurse din tace "you have an hour daga yanzu zuwa Magrib" juyawa yayida sauri yafita yaciro wayanshi yana dailing number Alhaji amman har lokacin akashe, rasa yanda zaiyi yayi yawuce yakoma mota yaja motar yakoma chan gidan, bangarensu boysqutars dakinsu yawuce direct, wata katuwar ganamasgo yayi yabude sanan ya shiga cirowa yana ijiyewa kan katifa sanan yaciro watayar leda baka yakoma gefe ya zauna yabude ledan albashinshine dayake cirewa yayi saving duka duka 80k ne yamaida ledan ya kulle sanan yatashi yafito daga dakin dasauri lokacin ana shirin kiran salla komawa asibitin yayi yabiya kudin komi yarike sauran 30 a aljihu sanan yatafi masallaci kafin yadawo yasake samun wuri gaban dakin ya zauna yasake ciro wayanshi yay dailing har lokacin wayanshi akashe abin yabatamai rai amman kuma meruwanshi shidan aikine tashi yayi yawuce masallaci jin ana kiran isha'i yayi yafita waje yaje yasha shayi da indomie sanan yadawo yasake zama awajen shiru babu wanda ya cemai wani abu har bacci yasake kwasheshi yay kwanciyanshi kan yar kujeran yana sharara baccin shi gwanin ban tausayi kana ganinshi kasan yagaji.....





Kaman an tsikareta tabude idanunta ahankali tanabin inda takeda kallo tabbas tasan nanba gidanta bane, ahankali tajuyarda kanta karin ruwa datagani dakuma oxygen da akai hanging datagani yasa ta lumshe ido dan tagane she's sick but inane nan? Yunkurawa tayida kyar ta tashi tazauna tanadanjin jiri kadan, sanan ta kakkalli gefenta but babu jakanta babu wayanta balle takira wani, sakebin dakin asibitin tayida kallo taga emergency room ita kadaine aciki nothing to talk about wanan wani irin local daki takene, jitayi warin asibiti da dakin keyi na irritating nata yasa cikeda karfin hali irin nata ta yunkura tasauka daga kan gado tana zura takalminta takama karfen da ruwan kejiki dasauri ta lunshe ido, ahankali taja tasaka hannu tabude kofan tafita tana tafiya kaman zata fadi, tabi wajen dakallo babu kowa a wajen kaman ance ta kalli side dinta Murtala tagani ya kudundune jikinshi kan kujeran wajen yana bacci yana sosa hannu daga gani kasan sauro ke cizonshi, tsareshi tayida idanu ranta nabaci mesa zaikawota irin wanan asibitin, wani irin sarawa kanta yayi sabida bacin ran dataji saikuma wani irin mahaukacin jiri yazomata tai baya zata fadi tana kokarin rike karfwn da ruwanta ke sagale shikuma yabugi bango yay lara hakan yasa firgigit Murtala yafarka tareda dagokanshi ganin Hajiya idanunta na juyawa tana kokarin faduwa but tana kokarin hana kanta yasa yawaniyi tsalle yace "Hajiya" tareda tarota tafada kan kirjinshi, ko kawo wani abu baiyiba kawai yadauketa chak dukya rude sanan yaja karfen ruwan yabude dakin yace "mesa kika fito Hajiya aidakin kirani" ahankali tabude idanunta tana kallon fuskanshi yanda damuwa yanuna ko'ina akan fuskan, kirjinshi nabugawa fat fat fat tsoron karta fadi dayaji yasa taji something that is very very strange azuciyanta, she just wish and wish inama Baban Khalid ne haka looking so worried and so concern about her datafi kowace murna aduniyan nan. "Hajiya!" Firgigit tafarka daga tunanin dataje ashema harya zaunar da ita kan gado, cikeda damuwa yace "menene kikeso maiyasa kika fito tsakar daren nan? Jirifa ke mugun damunki? Meke miki ciwo yanzu? Nakira Dr"? Tunda yakemata tambayoyin take kallonshi saida yagama sanan tahade rai tace "ubanme nakeyi awanan kazamin asibitin? Wayakawoni nan?" Shiru yayi yasaukarda kanshi kasa shidaman yasan yayi laifi. "Ina maka magana kamin shiru Murtala!" Tadakamai tsawa dayasa tasake kama kanta dasauri jin kaman zaifita tace "wa....." ganin yadago kanshi ya kalleta yasa tahadiye sauran wash din tai maza ta cire hannun tasake daure fuska zatai magana yace "Hajiya dan Allah kiyihakuri kinji, bakida lafiya baki bukatan hayaniya da fada ko fushi, kinajin sauki zan gayamiki komi kinji Hajiya" ahankali tajinginar da bayanta da bango tanadan yatsine fuska tace "ka kira Alhaji? Meyasameni, mesa kakawoni nan"? Yanda tamai maganan babu wasa yasa yace "kina sauka akan mota kika fita kin fara hawa stairs kawai naganki akasa kina wani irin nishi........." nan yagayamata komi har zuwa yanzu, dan murmushi tayi tace "ayya meeting din must be very serious, jeka kiramin Dr" tai maganan kaman bakomi da sauri yafita daga dakin, daidainan hawayen data rikesu tunda yafara gayamata abinda yafaru yazubo mata sharrrr yanzu inda ace Murtala bai kawota wanan kazamin asibitin ba dahaka zata mutu abanza, Baban Khalid bai kira Dr ba saima kashe wayanshi dayayi irin ko ajikinshi dinan, baimaso adameshi da batun rashin lafiyanta yana aikin office, Baban Khalid Mijine wai ko Makiyi? Ta tambayi kanta! Jin alamun tafiya yasa da sauri ta share hawayenta tass, daidai anbude kofa Dr yashigo Murtala biyedashi yana kallonta yace "Hajiya kuka kikayi"? Wani irin mugun kallo tamai tace "fita daga dakin nan zanga Dr" babu gardama yajuya yafita yarufomusu kofa, Dr yay murmushi yace "why are u treating someone that saved your life today like this"? Murmushi yayi yakaraso gabanta yana gyara karin ruwan yace "I understand he's your driver, but koma a direban ne i must applaud his effort, I am telling u dabadan guy dinan ba we would've lost you by now, at the time daya shigo dake this hospital inda ace kin kara just 5min without seeing a Dr da heart dinki yadaina aiki, haka yashigo dake he was crying sosai" dasauri ta kalli Dr tace "crying"? Murmushi Dr yayi yace "abin yabaki mamaki ko kema, aiko kuka sosai kaman yaro wai dan Allah mutaimaki Hajiyan shi, ya tsareni wai a mota zan miki treatment baki zuwa asibiti da kyar fa yabari muka shigodake that zakiyi fada" for the first time tadansaki murmushi iya lebe, saikuma ta kalli Dr tace "what is wrong with me Dr, maisa nai passout like that"? Kujera Dr yaja yazauna sanan yace "kinada wata damuwa ne, is there anything wrong with you or bothering u"? Wani kallo tamai saikuma ta tabe baki tace "ni babu abinda kedamuna, namaka kala damai damuwa ne kakemin wanan tambayan" shiru Dr yayi yana kallonta, daga this magana datayi yagane yes tanada damuwan but she's the hard and strong type no need to even pressure her bazata fadimai ba hakan yasa yace "some of your results are out, some kuma sai gobe dasafe, kinada hypertension, and heart dinki at this junction is very very weak, bawai kinada ciwon zuciya or anything bane no! Just that heart dinki is weak, dole ki kulada kanki tsantsa dam at any point u can just collapse kimutu, dole kicire ma kanki damuwa, you should put yourself first before anything and anyone, kome kikasani dat will make u happy just be doing it, duk wani abu dake baki damuwa da matsala avoid it, I am sorry idan maganan nan yazo miki like this, I see u are strong u can handle it, and I also believe now that I tell u you will do all u can to keep yourself happy and healthy, so just do that" tunda yafara maganan tai shiru tana sauraronshi harya gama, sanan ya kalleta yace "any question" murmushi tayi kaman ba ita yabama wanan hard details din on her health ba, tace "i want to leave dazaran gari yawaye how much is my bill zan muku transfer" da sauri Dr yace "is not advisable for you to leave kibari mugama miki treatment, and issue of bill kuma your driver yayi taking care of that" da sauri ta kallai saikuma tasauke kanta ta kwanta akan gado tace "once it's morning am leaving, I have my Dr he will take it from here" yanda take maganan zaka gane bawai permission take magana ba, murmushi Dr yayi yasakai yafice yasaba da irin matan nan masuji dakansu ga shegen girman kai da fadin rai shidai Murtala na zaune bakin kofa yaga Dr yafito yawuce hakan yasa yatashi ahankali yabude kofan kaman matsoraci yaleka hada ido sukayi da Hajiya yanda tabishida kallo ba kyaftawa yasa yasauke idanunshi kasa yace "Hajiya dama na leko nagaya miki ina nan bakin kofa idan kina bukatan wani abu kawai kidan bubbuga wanchan drawer inajin karan zan shigo kinji" yanda ta tsareshi da idanu batare datace wani abuba yasa ahankali yajuya yamaida matada kofa yarufe ahankali tasauke ijiyan zuciya itama tarufe idanunta.




Hakanan tasami kantada mikarda hannunta zuwa kan drawer kaman mai tsoron drawer tadan buga kadan kafin tagama janye hannuwanta tadawo dashi jikinta taji anbude kofa da sauri karasowa gabanta yayi yadukar dakanshi kasa cikeda girmamawa yace "Hajiya gani, me kikeso? Nakiramiki likita ne"? Samin kanta tayida bude idanuwanta kadan ta kallai saikuma ta dauke kanta ta kwanta akan gadon taredajan bargo ta juyamai baya sanan ahankali murta chan kasa tace "ga kujera kazauna anan, waje akwai sauro gari na wayewa zamu tafi" "angama Hajiya yanda kikeso haka za'ayi ranki shi dade, Allah karamiki lafiya Hajiya" yay maganan yana daukan kujeran ya matsarda ita baya zuwa chan jikin bango sanan ya zauna, yaso zamanshi awaje atleast yadan mike hakarkari akan kujeran amman wanan dole sai zama yatsine fuska yayi yana gyara zama ya jinginar da kanshi ga bango sanan ahankali ya lumshe ido yana sauke ijiyan zuciya, ko 2min ba'a yiba bacci yay awon gabadashi sai minshari waaaauuuuuu! Juyowa tayida sauri ta kallai jin yanda yake munshari kaman rago, ahankali ta gyara kwanciyanta tana binshi da kallo tundaga kan kafarshi dake cikin silisaf din gida, yanada babban kafa dan diddigenshi ma awaje yake silifas din yamai kadan ga kafarshi fara itama, sai bakin wandon jikinshi na jeans dayay datti sosai, yatsine fuska tayi tabi rigan da kallo itama tai datti gashi kirjinshi very huge ga fadi gakuma cika kaman yana daga karfe, ahankali tasauke idanunta kan wuyanshi fatarshi suli suli gadan gemunshi dabaida wani yawa, saikuma tasauke idanunta akan fuskarshi ahankali tafadi azuciyanta Murtala fa mugun kyakkyawane, kauyanci darashin son gyarane yasa yake hakafa, and he is so innocent, despite the fact bata sakinmai fuska, batamai murmushi kullum cikin fada takemai dudda mugun tsoronta dayakeyi dan yana mugun jin tsoronta samada Alhaji ma dan yana hira da Alhaji sosai, itako bayayi da ita, but despite all of this he saved her life, yamata abinda ko mijinta baitaba mataba, she's so grateful to him dudda bata nunamai ba but har kasan zuciyanta taji dadin abinda yamata and for the first time duk tsanan nan datamai na dan kauye ne bai iya karatu ba duksai taji yakau. Kiran salla dataji anyi yasa tadan gyara kwanciya tace bari atada sallan asuba saita tadashi sutafi gida she needs a very clean and hot shower, lumshe idanunta tayi ahankali tana sauke ijiyan zuciya komida Dr yafadi mata suna kara mata yawo akanta, how will she stay happy now, kodai ta tattara taje gidansu tazauna cikin family tane koda na one month ne, but tana zuwa za'ai sensing something is wrong and Baban Khalid ma zai yardane yabarta taje gida tai one month, sarawa da kanta yayi yasa tahakura da tunanin tasake juyowa tazuba idanunta kan Murtala lokacin ana shirin tada sallan asuba. "Murtala" takirashi ahankali, firgigit yabude idanunshi dake cikeda bacci ya kalleta hada ido sukayi da sauri yatashi tsaye yana sosa kanshi yace "Hajiya gani, akira likita ne? Mekike bukata"? Girgizamai kai tayi softly tace "tafi masallaci kai salla kana dawowa saimu tafi" gyadamata kai yayi yajuya yana tafiya ahankali yafita tabishi da kallo ita karan kanta tasan yagaji.



_Hi Ladies let's deliberate small on this issue. Yanzu if Hajiya start developing something ma Murtala will you all blame her or blame mijinta?_

_zuciya batada kashi, kuma zuciya aba ce da bata tambayan permission dinka kafin taso abu, idan tarasa abu anan dazaran tasami abun awani wuri saita fara son abun, hakane ko bahaka bane ladies?_

_Alhaji Alhassan Bakori ya kyauta abinda yayi???_

_mezakuce game da Murtala our 26yrs old driver that is simply doing his work? Mekuke ganin nan gaba zai faru tsakanin shi da Hajiya?_


_so far what have you learnt in this page??_


07012181461 chat me up a watsapp this is my number.









💫 _MATAN ASOKORO_ 💫




✍🏾M SHAKUR


EPISODE 3️⃣



6 nasafe dot yashigo tareda Dr, duk zaune suka sameta abakin gado, Murtala dake gefen Dr ya rusuna yace "ina kwana Hajiya" ko kallon Murtalan batayiba ta kalli Dr yace "i told you am leaving" dan murmushi Dr yayi yakaraso inda take rikeda da wata yar paper da pen yace "I just need you to sign this then u can go" karban takardan tayi tana karanta content din yace "is DAMA form, discharge against medical advice" signing tayi tabashi sanan tasauka daga gado ahankali harda dan gudu Murtala yakaraso gabanta yace "Hajiya zaki iya tafiya kona daukeki kokuma na dauko miki kujeran guragu"? Yanda yayi maganan saida yasa murmushi yadan subuce mata daga baki kawai tawuce tai gaba tabishi yabita abaya harzuwa motansu, baya yabude mata tashiga ahankali tazauna yarufomata kofan sanan yakoma gaba ya shiga yaja motar, itakuma tadauki jakanta dake kasan motan tabude taciro wayanta dake ciki hakanan tasami kanta dacire lock din wayan ganin babu miss call kodaya na Alhaji yasa ta maida wayan ta ijiye ta kauda tunaninshi aranta, har gida suka karaso ya danna remote gate yabudu ga mamakinta saitaga motan Baban Khalid direbanshi na wanke motan, tunkafin ta sauko direban ke gaidata, fitowa tayi ahankali rikeda jakanta Murtala yafito yashiga gabanta yamika mata hannu yace "kawo jakan narike" girgizamai kai tayi tace "jeka huta kayi kokari" sanan tawuce shi, juyawa yayi ya kalleta sanan yace "Hajiya zaki iya wuce benen"? Chak ta tsaya jin tambayanshi har ranta taji diran maganan kaman zata juyota kallai saikuma ta daure bata amsashi ba tashiga hawa benen dazai sadata da kofar shiga falon ta, tanajin muryan Murtala yana Alhamdulillah Hajiya tawuce batare data sake sumewa ba, Emus sannu da aiki, shikuma Emus yana sai yanzu kaganni, bude kofa tayi ahankali tashiga falonta.




Zaune Alhaji yake kan dogon kujera dagashi sai wata white jallabiya hannunshi rikeda remote yana kallon tashar CNN dayan hannunshi kuma rikeda mug na lipton yana, jin anbude kofa yasa yadago kanshi ya kalleta hada ido sukayi yace "Hassana ina kika kwana"? Kaman bazata kulashiba tajuya tamaida kofan tarufe sanan tajuyo ta kalleshi ahankali tace "asibiti" da sauri yadaura hannunshi asaman goshinshi yace "laaaa kinganni fa ba shaf na manta wanchan direban yaron naki yakirani ba nacemai bari nagama meeting zan kira Dr yazo, kwata kwata bamu gama meeting dawuri ba, I came back very late dakina nawuce na kwanta sai this morning ma naga bakinan ashe" jitayi wani abu ya tsayamata awuya saikuma ta daure takakalomai murmushi batare datace komiba tashigo zatai stairs yace "ina magana kuma zaki wuce" juyowa tayi ta kalleshi tace "kace mene"? Wani kallan kallo yamata yace "fushi kikeyine I told u meeting nake saisa ban kira Dr ba na manta, but bagashinan u are fine ba, ainasan ki u are a very strong woman" ahankali tace "Allah ko, tom godiya nake" tana maganan tajuya da sauri tai sama gudun kar hawayen dake gabda zubomata yazubo yagansu kofar dakinta tabude tashiga ta maida dasauri tarufe saikukan yazo sosai tacigaba da dannewa tasaki jakanta awajen tabude bathroom dinta da sauri tabude tap tafashe da kuka sosai jikinta har wani bari yake, what is this life? Is her husband husband ko enemy? This is the second time take tambayan kanta, tayaya za'ace mutumin da aka dauramusu auren, akace cinta shanta, suturanta, lafiyanta komi nata yatashi dagakan iyayenta yakoma kanshi yadawo mata haka, ankira bawan Allahan nan ancemai tasume she's unconscious, yama kashe wayanshi batare dayakira Dr ba, yadawo baima dubata adaki ko lafiyanta lauba, sanan yaganta yanzu koyace mata yajiki, so yanzu idanda tamutu baidama hassara saidai yaranta suyi kuka ko, she's not his business, baima sonta dan saikanason wani zaka damudashi, jin kanta yafara sarawa yasa dole ta tsayarda kukan tawanke fuskanta tareda kashe tap din tacire riga tai wanka da ruwan zafi sosai tadauro towel tafito daga bayin,

Please Login or Register in order to submit comment