Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fiye da ta kowacce mace me gata"sambatun da Hammad yake kenan sanda ya farka a asibiti.allurar bacci aka masa ko zaa samu sauƙin sambatun.

A can sansanin ƴan gudun hijira ko masu kawo sadakar abincine suka zo dan haka kowa da gudu yaje ya hau layi,banda Zahra wacce cinyoyinta ke mata mugun ciwo,zaune take ta kife kanta akan guiwowinta tana kuka,

Haka aka gama rabon abincin ita bata samuba,se hanne ce ta sammata nata.shima daƙyar ta iya ci sabida bakinta ɗaci yake mata.

Haka suka kwashe tsawon kwanaki uku,Zahra zuwa lokacin bata iya ko tafiya sede rarrafe,ga wani ruwa data rasa ko na menene dake bin cinyoyinta.tayi kukan tayi kukan har ta gaji.gashi ba suturar arziƙi ke garesu ba haka take zaune ƙuda na bin ta.hanne kanta yanzu ta gujeta sabida warin da zahran take.

Duk sanda zaa kawo abinci zahra bata samu sabida ƙyamarta da akeyi,hakan ne yasa take fita daga sansanin da rarrafen taje,bakin titi tayi bara dan ta samo abinda zata ci.cikin ikon Allah kuma tana samowar seta koma gefe taci ta ɓoye sauran.

Acikin sati biyu duk wanda yaga Batulun inna bazece ita bace,gaba ɗaya ta sauya,tazama abar tausayi.

Acan kaduna ko,lamarin na hammad ba sauƙi,dan gaba ɗaya kwakwalwarsa tasamu matsala,a birkice yake,arana seya kira ƴarfillo yafi so dubu,kuma yana dukan duk wanda yazo kusa dashi.

Hakanne yasa aka nemo iyayenshi sukazo aka basu shi domin suje su nema masa lafiya.

Allah sarki,a ɗaɗɗaure aka sashi a mota sabida dukan da yakeyi,shima seda aka masa allurar bacci sannan akai nasarar fita dashi.

Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Hammad,me hamshaƙin me kuɗine,wanda sunanshi ya kewaye ko ina a ƙasar nan harma da ƙasashen ƙetare.ƴaƴanshi biyu Hammad da Surayya,se matarsa hajiya maryam,dukansu asalinsu ƴan gombe ne.


Alhaji ba abinda yakeso a duniya sama da ɗansa Hammad,duk wani buri nasa na duniya akan Hammad ya ɗorashi,lokacin daya ga halin da ɗan nasa yashiga kuka yake da idonsa kamar ƙaramin yaro.dan shi dama a dole yabar Hammad ya shiga aykin soja,dan kawai ya nuna yana sone.

Hammad matashine ɗan kimanin shekara 30 da haihuwa,bayan kammala karatunsa na secondry,mahaifinshi oxford university ya tura shi inda ya karanci gynocology,wato likitan mata,inda yasamu sakamako me kyau bayan kammala karatun.
Lokacin daya dawo gida nigeria,seya samu ƙasar na cikin yanayi na fama da rashin tsaro,ana kashe mitane basuji ba basu gani ba,wannan dalili ne yasa Hammad da Amininsa jameel suka faɗa aykin soja,wanda mahaifin hammad yasaki ƴan mazan kuɗi aka basu manyan muƙamai,bayan sun samu horo na musamman asansanin sojoji dake NDA kaduna. sunason taimakawa ƙasarsu da dukkan ƙarfinsu.


Wannan kenan.

Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*



*8*


A harabar gidan yayi parking,tun kan ya gama tsayawa Hajiya da Muhammad suka fito,cike da damuwa yafito daga motar,sannan yayi umarnin da a ɗaukota akaita boysquater dake gidan.

Ba musu masu tsaron lafiyar tashi suka ɗauketa kamar yadda ya buƙata,ba hajiya ba hatta Muhammad ya kaɗu dajin warin da takeyi,haka aka wuce da ita ciki.

Jummai da Asabe Masu aykin gidan hajiya ta kira bayan sunzo tace"ku kwashi kayan wanka maza kuje kui mata wanka,ku tabbatar da cewa komai na jikinta kun wanke ganinan zuwa"

Amsawa sukayi da sauri suka wuce aywatar da abinda tace.kallonta takai gun Muhammad wanda gaba ɗaya Babu annuri a fuskarsa tace"Muhammad bari inje in dubata bazan jimaba zan dawo"

"Mummy wannan warin fa ze iya cutar dake,gaskiya da aba direba ita yakaita asibiti,nan akwai matsala"ya faɗi cikin yanayin damuwa.

"karka damu bari in dubata ba abinda ze sameni"ta faɗi sannan ta juya ta bi bayan su jumman.

Se a lokacin Muhammad ya ƙarasa gun mahaifinshi yana murmushi ya ɗan rusuna yace "sannu daddy"

Dafoshi yayi yana murmushi yace "Yauwa ɗan gidan daddy ya hanya,ya kuma hajiya da jikin"

"hanya Alhmdllh,hajiya kuma ta warke sosai"

Daga haka suka shiga ɗan taɓa hira kaɗan suna jiran hajiya ta fito suji in agidan zata diba mara lafiyar ko asibitin zaa tafi.

Hajiya lokacin data shiga toilet ɗin kusan kukane yakusa kwace mata ganin yadda gaban mara lafiyar ke shirin lalacewa.

Safa tasaka sannan ta tara ruwa me zafi,tasa detol,sannan ta tsomata acikin ruwan ta fara wanke gurin,wayyo Allah na gurin yauƙi yake gashi har wani kore kore yake,ga uban wari.

Hajiya na fara wankewa tsananin azabar da zahra taji yasa ta farkawa daga suman da tayi ta kwalla wata ƙara.

A gigice Daddy da Muhammad suka nufi boysquater ɗin,sede suna shiga jummai ta dakatar dasu a falo ta hanyar shaida musu wanka ake mata.

Kimanin awa guda Hajiya ta kwashe tana sauya ruwa tana wanke gurin Zahra kuka take iya ƙarfinta tana kiran sunan Allah.

Kan kace me tuni wannan azababben wari ya tafi se ɗan wanda baa rasa ba,doguwar riga ta marasa lafiya hajiya tasa mata sannan suka ɗaukota zuwa ɗakin da hajiya ta ware domin kula da marasa lafiya na gida,ba abinda babu aciki.

Kan gado ta ɗorata,sannan ta fara wanke duk inda taji rauni sakamakon bigeta da mota tayi.seda tagama tsab sannan ta buɗe gaban nata ta kawo fitilar likitoci ta haska,sosai tausayinta ya kamata,wannan sashin ba ɓangarenta bane shiyasa bata fahimci ko matsalar menene ba.

Kashe fitilar tayi sannan ta rufeta,tasa jummai ta kawo mata abinci,ayko kamar tsohuwar mayunwaciya haka takecin abincin har ta cinye tasha ruwa,

Magunguna hajiya ta bata,sannan ta kwantar da ita ayko kamar jira bacci yayi awon gaba da ita,sosao tausayinta ya taɓa zuciyar hajiya,yarinya ƙarama amma ta haɗu da matsalar taɓin hankali,dan atunaninsu su dika mahaukaciyace.

Falo ta dawo gun su muhammad da Alhaji tace cikin damuwa "Alhaji ni nayi nawa,sede yarinyar nada matsala a al'aurarta,shine nake ganin ko de A kaita Hammad Hospital ne,kaga can akwai kayan ayki zata fi samun kulawa,tunda can dama na ɓangaren mata ne"hajiya tace cike da damuwa.

"wanne irin Hammad hospital,menene zaay mata acan wanda ɗanki Muhammad baze iyaba,ko kin raina kwarewarsa ne,da har kike cewa akaita wani guri bayan ga abu agida"cewar Alhaji yana duban Muhammad.

"Mummy zan dubata ingani insha Allahu baze gagara ba,abinda zaay mata a wancan asibitin nima shi zanyi insha Allahu"cewar Muhammad.

juyawa hajiya tayi yabita abaya zuwa inda Zahra take kwance tana bacci.

Safa yasaka a hannu sannan ya kunna fitilar likitoci ya matsa da ita gabanta hajiya ta buɗe masa gaban na zahra.

A Hankali ya duƙa yana kallon gurin,yasa hannu ya ruƙo wannan tsoka dake lilo itama ya ƙare mata kallo, tsawon mintuna arba'in ya kwashe yana karantar gurin sannan ya ɗago ya cire glass ɗin fuskarsa,sosai damuwa ta bayya na a fuskarsa idanunsa sukayi ja,tsigar jikinshi har tashi take yace "mummy fyaɗe aka mata,kuma a ƙalla ya kwashe watanni da yi matan,kuma anji mata ciwo agurin,wanda sanadin hakan ta kamu da yoyon fitsari,ga infection me ƙarfi daya kama gurin wanda in baayi da gaske ba ze iya rikiɗewa yakoma cancer"

.Salati mummy tayi sannan tace"oh ni jamaa yaushe zasu fara tsorom Allah ,yarinya ƙarama a haike mata wannan wanne irin cin zarafine"

"mummy muje inyi list na abinda zaa buƙata,dan akwai buƙatar ayi mata ayki yau ɗinnan ayi mata plushing ɗin infection ɗin sannan a ɗorata akan magani"cewar Muhammad bayan ya cire safar dake hannunsa ya wanke Hannunsa suka fito ransa Aɓace ya rasa dalili,ko kaɗan baya ƙaunar akawo masa yara an musu fyaɗe ransa ɓaci yake ji yake da ze ga wanda ya aykata musu ba makawa seya kasheshi .


Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*7*

*Bayan shekara ɗaya*

"Modibbo ɗiyata zata mutu a sansanin ƴan gudun hijira,kataimaketa!!!! kataimaketa!!! kataimaketa!!!!!!!!!"

A Razane ya farka daga baccin da yake,wani gumine ya karyo masa me zafi,gudun AC dake ɗakin ya ƙaro,sannan ya samu guri yazauna yana tunani gameda mafarkin da yake yi da Hauwa ƙanwarsa,wacce sanadin faɗan da akayi a garinsu yasa ta ɓace wanda sunyi cigiya har sungaji.

To shi wannan mafarkin da yake da ita me yake nufine,yau kusan kwana uku kenan seyayi mafarkin,ɗiyarta to dama ta haihune ko ya abun yake,a iya saninshi hauwa nada matsalar rashin haihuwa,kuma mijinta ankasheshi a faɗan da akayin.

Haka de yayi zugum shi kaɗai a ɗaki yana tunani,to shi wanne sansanin ƴan gudun hijira zashi,?taya ze iya gano ƴar da be san kamanninta ba,?to bama wannan ba shin mafarkin gaskiya ne?wainnan tambayoyi sune ke yawo a kansa da ya rasa amso shin su.

Haka ya kwana be runtsa ba,da gari ya waye bayan yayi sallar asuba ɗakin matarsa ya nufa,

Da faraarta ta taso ta tarbeshi,bayan sun gaisa ne,tace cike da kulawa"Alhaji naga kamar kana cikin damuwa?"

"Hajiya kwana biyu ina cikin damuwa,hauwa kullum se tazo amafarkina tana cewa in taimaki ɗiyarta,a sansanin ƴan gudun hijira ni na kasa gane kan wannan lamari wallahi"ya faɗi cike da damuwa.

"ka kwantar da hankalinka baban Muhammad,wataƙila akwai wani abu me muhimmanci gameda mafarkin nata nide ashawarata da ka fara duba sansanin ƴan gudun hijirar kagani ko wani taimako suke buƙata yasa hauwan ke zuwa ma a mafarki"

"kema kin kawo shawara hajiya,zanyi hakan in yaso duk week end na dinga zagayawa guraren da ƴan gudun hijirar suke,dan abun akwai ɗaure kai wallahi"

Haka de suka gama jajantawa modibbo ya miƙe ya fice zuwa ɗakinshi,wanka yayi ya kimtsa sannan ya dawo dinning suka ci abinci,agurin cin abincin ne yace "Munyi waya da Muhammad ɗazu ya shaidamin ƙarfe biyu na rana zasu iso, kuma hajiya babba jikinta da sauƙi,shiyasa ze taho,ki tanaji komai,ni zan fita,zan jima kan in dawo"

murmushi Hajiya tayi sannan tace"lalle Muhamnad yaci saa da hajiya babba ta barshi yataho,ita da tace se ta masa aure sannan ze dawo"

Dariya sukayi irin ta girma sannan yace"hala ta masa matar ne shiyasa tabarshi yataho"

Miƙewa yayi yana kallon agogon hannunsa yace"hajiya bari in ƙarasa office,zamuyi waya,in kuma naga da lokaci zan ɗan leƙa sansanin ƴan gudun hijira dake nan kusa"

A dawo lafiya tay masa sannan ya fice da hanzari,bodygurd ɗinsa suka mara masa baya.

Ƙarfe huɗu modibbo ya baro office,bayan yayi sallar la'asar,kai tsaye wani gidan abinci ya nufa, domin yaci abinci kamin ya wuce sansanin ƴan gudun hijirar.

A kan idon Zahra motocinsa suka faka,tana can ɗayan gefen titin,da ɗan saurinta ta taho tsallako titin dan tasamu tayi bara agunsu ko zasu taimaka mata,dan kwananta biyu yau bata ci abinci ba,agalabaice take ga ulcer ta data tashi,yanzu ko gabanta ya koma ciwo,yana fitar da wani wari me ɗaga hankali,ko giftawa kayi ta gunta se kaji warin,shiyasa duk inda tayi ake korar ta,hakanne yasa take samun kan bola tayi zamanta,gudun kar akoreta.

Cikin rashin sani mota tayi ciki ciki da ita lokacin da take ƙoƙarin tsallakowar.

Ƙarar burkin motar ne,yaja hankalin mutane da dama, ciki harda modibbo dake ƙoƙarin shiga gidan abincin.

Da gudu me motar daya bugeta yabar gurin be tsaya ba.
A Hanzarce Modibbo yayiwa bodygurd dinshi umarnin su ɗauko wanda aka buge susa a mota,

Hakan sukayi,sede warin da takeyi ne,ya hanasu kuma shiga motar da sauri suka ja baya har modibbo ya ƙaraso.

Warin shi kanshi ya ɗaga masa hankali,shiyasa be tuhumesu me ya hanasu shiga motar ba.

Tsayawa yayi shima yana nazari kamin ya ciro waya ya kira matarsa kasancewarta likita,tana ɗagawa yace"Hajiya akwai emergency yanzu wani ya buge wata mahaukaciya kuma ya tsere,in kaita asibiti ne zaki je yanzu ko in kawota gida?"

"Gaskiya ka kawota gida sabida muhammad be daɗe da dawowa ba bazan iya fita in barshi ba,amma in kukazo naga yanayin lalurar dole se anje asibitin semu tafi".

Yana kashe wayar ya faɗa motar da kansa yaja,da gudu suka shiga sauran motocin suka mara masa baya zuwa gidan.

Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*



*9*


A daren duk abinda ze mata yayi mata,iya azaba zahra tasha ta,duk wanda yaganta seya tausaya mata,haka ya gama komai,sannan ya barota kwance kamar matacciya.

Ɗakinshi ya wuce kai tsaye kan kujera ya faɗa yana maida numfashi,wayarshi tayi ƙara da sauri yakai idonsa gurin,Amininsa kuma babban likitan mata na asibitin Hammad Hospital,shi ke kiransa.

Ɗagawa yayi ya kara wayar a kunne yace "ya kake?"
Daga can ɓangaren ya amsa masa "kaganni wallahi se yanzu zan bar office,tun safe ina asibiti har na gaji,"

"munyi ɗaya kenan,nima yanzu fitowata daga wani aykin gaggawa kenan?"

"Wallahi da naso in shigo gidanku yau sabida gobe weekend,inaso in je falgore dubo ƴarfillon nan inga ko zaa dace,to se kuma ayki ya riƙeni,dama so nike in ce ko zaka rakani"

Murmushi muhammad yayi me sauti sannan yace"na gaida na ƴarfillo,Allah de ya yanke maka wannan wahalar,"

Dariya dukansu sukayi,sannan daga can ɓangaren yace "aboki bazaka gane bane,wallahi ina matuƙar tausayawa yarinyarne shiyasa"

"Na jima da fahimtar hakan,kaga in Allah yasa ka ganota kuma kaga tayi kalata kaga shikenan seka aura min ita,adena cemin gouro"muhammad yafaɗi yana dariya.Dan yasan ya tsokano abokin nasa,ilai kuwa bece komai ba ya kashe wayar.

Wata dariyar muhammad yayi sannan ya ajiye wayar ya miƙe ya shiga wanka dan jikinshi duk ciwo yake,danma mummynsa na gurin tana taimaka masa.

Tsawon watanni biyu zahra ta kwashe Muhammad ke kulawa da ita,zuwa yanzu ƙafa tasamu tana tafiya kaɗan kaɗan.

Sosai take samun kulawa agurin mummy,safe darana da yamma ita ke mata wanka,ga ruwan zafi datake yawan sata aciki ta zauna.

Zahra farinta yasoma dawowa ga wata ƙiba da tayi kamar ba mara lafiya ba,yanzu komai takeso tana samu,sede ba uhm ba uhm uhm ido kawai take binsu dashi ko wanne lokaci.

Yau zaune suke ita da hajiya a falo tana bata kankana tana sha,Muhammad ya shigo falon,bayan sun gaisa da hajiya ya dubi zahra sannan yace "hajiya jikin yarinyat nan da sauƙi,yakamata akaita asibitin mahaukata aduba lafiyar kwalwalwarta,shurun tayi yawa"
Kamar jira yana saukewa zahra cikin muryar marasa lafiya tace"lafiyata ƙalau ni ba nahaukaciya ba ce"

Ba muhammad da hajiya ba hatta daddy dake ƙoƙarin shigowa falon yayo mamakin maganarta.


Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*11*


Muhammad tsawon sati guda ya kwashe ba inda yake zuwa sabida firgicin da yake ciki,sosai zancan auransa yasakashi,a damuwa,

Zahra sanda mummy ta sanar mata auranta da muhammad sosai taji daɗi,sabida taga ɗan uwanta ne,ze rufa mata asiri,dan haka bata da damuwar komai aranta.burinta Allah ya nuna mata lokacin.dan ita tun haɗa idonta dashi na farko taji ya kwanta aranta.

Sosai walwalarta da jin daɗinta ya ƙaru agidan ba mummy ba har daddy ya fahimci hakan,wani sanyi yakeji aransa sabida ya mata abinda takeso.

Mummy gyara zahra take da duk wani abu data san baze cutar da lafiyarta ba,,cikin ƙanƙanin lokaci zahra tayi wani kyau na musamman fatarta ta murje tayi fari har wani sheƙi take,gashi yanzu ba wata rama ajikinta,sema wata ƙiba data mulka,zahran inna kenan matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha shida.kyakkyawa ajin farko,


Saura kwana biyu ɗaurin aure,muhammad na zaune a lambun gidansu zahra ta ƙaraso gurin,yana ganinta ya ɗauke kai kamar be ganta ba,murmushi tayi dan tasan baya sonta,ita ko sonshi take dan haka zatai haƙuri da duk wani halinsa har shima ya sota,gefenshi taje ta zauna,kamshin da take ne yasashi ɗago kai ya dubeta,sannan ya maida kansa gefe.

"yaya dama inaso in baka haƙuri ne akan auran dolen da zaay maka"
Ɗagowa yayi ya dubeta rai aɓace yace"au auran dolen ni kaɗai zaayiwa kenan ke banda ke?"

Murmushi tayi kumatunta suka lotsa tace"banda ni gaskiya,kai de za'a yiwa,ni auran nagani inaso za'a min,"ta faɗi a kunyace.

Tsayawa yayi,yana ƙare mata kallo,tattaro hankalinshi yayi gaba ɗaya kanta,hannunta ya kamo ya dibeta a tsanake yace"zahra ni kikeso?"yayi tambayar a tsanake.
Murmushinta me sanyi tayi sannan tace "Tunda naganka,naga kuma irin taimakon daka ba rayuwata da lafiyata,yaya muhammad naji ina sonka,wallahi da gaske nake har raina"ta ƙarasa maganar kamar zatai kuka.

Yatsun hannunta yake kallo,sannan ya ɗago ya dubeta yace"zahra to ya zakiyi in kika fahimci ba matsuguninki a zuciyata?"

"addua zanyi,wataran zaka soni"ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

Murmushin takaici yayi sannan yace"to in kuma ba kya cikin kalar matan da nake so fa?"

"Zanyi ƙoƙarin maida kaina kalarsu insha Allahu"tabashi amsa.

"to ay ni zahra gaba ɗaya kin min ƙanƙanta a aure,taya zan iya zaman aure dake?"

"wataran zan girma yaya,in zama babba,sede ko kace sauran wanine baka so,inaga shine kawai dalilin daze hanaka aurena"ta ƙarasa maganar tana kuka,

Runtse ido yayi maganar na masa ciwo a zuciyarsa,a hankali ya dubeta yace"to naji zahra tashi kije kar mummy ta nemeki,"

Miƙewa tayi a hankali,tabar gurin tana waigenshi.

Shima miƙewa yayi yaja motarsa zuwa Hammad hospital dan ya sanar da amininsa halin da yake ciki,dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa.


Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*10*


Murmushi mummy tayi ta dafo kanta tace "ɗiyata sauƙi yasamu kenan?"
Murmushin itama zahra tayi ta sunkuyar da kai ƙasa,
Daddy ne ya ƙaraso gurin ya zauna sannan yace"dama wannan lokacin nake jira kuma gashi Allah ya kawo mu,zamu so ki sanar damu ko ke wace ce,dan musan taya zamu taimakeki ki koma ga danginki"

Hawayene ya zubowa zahra tasa hannu ta goge,sannan tace"ni bani da dangi,baffana yayi hatsari ya mutu,innata ƴan bindiga sun kasheta,tade taɓa shaidamin muna da ƴan uwa a gombe,kawu modibbo amma sun bar gomben kuma batasan inda zata gansu ba"

Kallon kallo suke tsakanin hajiya da Alhaji,bakinsu har rawa yake gun jefo mata tambayar"ya sunan innar taki na Aynihi?"

"hauwa'u sunanta"ta basu amsa.

Rungumota hajiya tayi jikinta tana hawaye tace"tunda nake kallon fuskarki naga kamar nasanki,amma na kasa gasgata hakan,ashe ko ikai fuskar hauwa nake gani ataki fuskar,Allah mungode maka"

Daddy sosai yake murna da ganin ɗiyar ƴar uwarshi,hotunan inna nada ya nunawa zahra ayko murmushi take tana faɗin"innata ce wannan dama kunsanta"

Daddy ya gabatar mata da kanshi da iyalinshi a matsayin dangin nata yamata bayanin komai,ayko itama kuka tasa najin daɗin ganinsu.

Shide Muhammad abun koma masa yayi kamar a film,daga neman shawarar akaita gidan mahaukata shikenan abu ya juye ta komo ƴar uwarsa.

Basu bar falon ba se da dare yayi sosai anata hira,sosai daddy yasaki jiki da zahra wacce yake kallo amatsayin sauran danginsa da suka rage masa a duniya.

Washe gari da safe bayan muhammad ya duba zahra,cire safar hannunshi yayi ya janyo kujera ya zauna yana fuskantarta,ita de tunda ta fahimci shine ke dubata kunyarshi takeji,da ƙyar take iya haɗa ido dashi.
"zahra kin bada labarin komai naki,amma baki sanar damu wanda kuma ya miki fyaɗe ba?wanda a matsayinmu na ƴan uwanki zamu so musani"muhamnad yace cikin tattausar murya.

Hawayene ke biyo idonta a hankali tace"na barshi a matsayin sirrina,don Allah karka kuma tambayata"ta faɗi cikin kuka.

Taɓe baki yayi sannan yace"bazan kuma ba,amma kisani in ni baki faɗa min ba dole zaki faɗawa mijinki ay"yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.

Hankalin zahra yayi ƙololuwar tashi jin furucin muhammad,tabbas dole zata sanar da mijinta wannan mugun labarin,duƙar da kanta tayi ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.

A haka mummy ta shigo tasameta,sosai hankalin mummy yatashi janyota tayi jikinta tashiga tambayarta abinda yafaru,cikin kuka zahra tace"mummy yanzu rayuwata a haka zata ƙare kenan,bazan taɓa aureba,in ko zanyi auren dole sena cewa mijina anmin fyaɗe? inde hakane nida aure har abada"ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Tausayintane ya kama mummy ta shiga rarrashinta da duk wata kalma me daɗi,da ƙyar tayi shuru.

Mummy ɗakin daddy taje tasameshi yana shirin fita,ganinta cikin yanayin damuwa ne yasa ya nemi guri ya zauna yace"hajiya lafiya kuwa?"

Cikin damuwa tace"Alhaji yarinyar nan na cikin damuwa gameda fyaɗen da aka mata, baka ganin akwai buƙatar a binciko ko waye a hukuntashi sannan asa shi dole ya aureta?"

Shuru Alhaji yayi na ɗan lokaci sannan yace"nemo ko waye beda wani amfani,fyaɗe de anriga an mata,ba abinda ze sauya hakan,kuma ni modibbo inde na isa da Muhammad to tabbas shine ze auri Zahra,dan shi kaɗai ze rufa asirinmu"

Mummy itama ta gamsu da bayanin na alhaji,dan haka kwarin guiwa ta ƙara bashi kan ƙudirin nasa,sabida Allah yasani tana tausayin zahra matuƙa.

Alhaji be samu zama da Muhammad ba seda dare bayan ya dawo daga gun ayki.
Lokacin daya sanar dashi hukuncin daya yanke akanshi da zahra muhammad kaɗanne beyi fitsari a wando ba sabida firgici,bakinsa har rawa yake yace"daddy don Allah kayi haƙuri kabar maganarnan,nifa bana sonta,gaba ɗaya zahra nawa take da har zaay batun aurenta,ni tayi min ƙanƙanta daddy pls"
Yafaɗi kamar zeyi kuka.

"muhammad ba shawara fa nake nema ba,hukuncin dana yanke nake faɗa maka,wannan duk raayinka ne,ba nawa ba,nan da wanne lokacine zahra zata iya warkewa gaba ɗaya" daddy ya buƙata cikin haɗe rai.

Jikin Muhammad a sanyaye yace "wata guda"

"nasa lokacin auranku nan da watanni biyu masu zuwa,na ɗauke maka komai,kaje ka fara shiri"daddy ya faɗi sannan ya miƙe yabar gurin.


Muhammad na zaune kamar wanda aka dasa,yama rasa me zeyi yaji sanyi aransa,da ace ze iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.

A Hankali ya miƙe ya nufi ɗakinshi jiki a sanyaye ya faɗa gado yana nazari,shide gaskiya tayi mishi ƙanƙanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaɗen da aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ƙatuwa ne.


Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*12*



A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito ya taka zuwa office ɗin aminin nasa.

Da sallamarsa ya shiga office ɗin cike da fara'a ya taso suka rungume juna,suna ɗan dukan juna a baya,sannan suka koma kan doguwar kujera suka zauna.

Muhammad ne ya fara magana cikin yanayin damuwa"Abokina ina cikin damuwa fa,?"

"wacce irin damuwace wannan,?"abokin nasa ya buƙata cike da kulawa.

"jibi daddy ze ɗauramin aure da wata ƴar ƙanwarsa,na rasa inda zan tsoma raina".

A razane ya miƙe tsaye yana ja da baya,take duk wani annurin fuskarsa ya kauce kamar wanda yacewa gobe ze mutu.

Cikin kakkausar murya yace"HAMMAD kana nufin alƙawarin auren ƴarfillo daka lalatawa rayuwa yatashi a banza kenan?"

Miƙewa muhamnad yayi ya ƙaraso kusa da abokin nasa ya dafa kafaɗarsa yace"JAMEEL kafi kowa sanin irin son da nakewa ƴarfillo,wallahi babu macen dana keso a zuciyata sama da ita,kullum jameel bana iya bacci sabida ita,wallahi akan ƴarfillo zan iya ɓata ran kowa,sede itama wannan dazan auran akwai abun tausayi game da itan,kwatankwacin kaddarar data faɗawa ƴarfillo itama hakanne,wallahi zan auri yarinyar ne,kodan jihadin da zanyi na auranta Allah ya kawomin ƴarfillo na cikin sauƙi,pls jameel in baka fahimceni ba bame fahimtata"muhammad yayi maganar kamar zeyi kuka.

Waigowa jameel yayi,ya dubi hammad yace "b haka bane hammad ay kai mijin mace huɗune,bana de so ne sanadin auran da zakayi ka mance da ƴarfillo shine yasa"

"har abada bazan mance da ita ba jameel,kuma zanci gaba da nemanta har se inda ƙarfina ya ƙare"Muhammad yafaɗi cike da tabbatarwa.

Jameel kwantar masa da hankali yaci gaba dayi akan auransa da zahra,inda yace ya daure yayiwa daddy biyayya hakanne zesa in ya kawo ƴarfillo ya amince ya aureta.

Sosai Muhammad ya gamsu da shawarar aminin nasa,duka yakaiwa jameel yace yana dariya"wato jameel,da ace yadda kanka ke kawo wuta haka zuciyar ka take da nigeria batayi asarar soja ba,amma wai daga harbi ɗaya a baya,sega resigning letter wallahi ka bada maza,ay gashi nan ka ƙare a kallewa mata al'aura,da wuri zaka makance"ya ƙarasa maganar yana dariya.

Duka jameel yakai masa yace"ay duk namijin da baya gudu baya tsawon rai,da asara gara gidadanci,taya na hango lahirar nasha da ƙyar zan bari a ƙarasa ni,kaima kaga zaka iya ne shiyasa baka fita ba"

"bazan taɓa barin aykin soja ba Jameel sede in ze shiga tsakanina da ƴarfillo to tabbas zan fita".

Haka de sukai tayiwa juna barkwanci,basu rabu ba se dare,agajiye muhamnad ya dawo gida,zuciyarshi fal farinciki kamar yaga ƴarfillonsa.

To bari mu waiwaya baya😄

Kowa ta turo data se in ci gaba😎


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*Ummu Airah,Asmau shareef,mmn minister,mahaƙurci mawadaci,da sauran wainda suka turomin kati da data,nagode sosai Allah yasaka da alkhairi,ya ƙara buɗi na alkhairi,naji daɗi*.


*13*



Bayan Mahaifin Hammad ya ɗaukeshi zuwa nema masa magani a ƙasar rasha,anci baƙar wahala kamin asamu kansa ya dawo seti.
Cikin nasara akai masa aykin ido ya samu sauƙi,watanni bakwai suka kwashe a ƙasar sannan ya warware suka dawo gida nigeria.

Koda wasa Hammad be taɓa faɗawa kowa abinda ya ayƙatawa ƴarfillo ba,sede kullum cikin nemanta yake,be taɓa gajiyawa,sadaka sallah da addua cikin yi ike.

Jameel sojojin agajin gaggawane suka tsamoshi aruwan daya faɗa,taimakon gaggawa suka bashi,nunfashinshi yadawo,oxygen suka sa masa sannan akasashi a mota zuwa babban asibitin sojoji dake kaduna.

Cikin nasara akai masa ayki aka cire bullet din da aka harbeshin.yasha jinya kan yasamu ya warke,shiyasa yana warkewa ya ajiye aykin soja.

Tare sukai karatu da amininsa a turai fanni ɗaya,shiyasa jameel ya koma inda yafi wayau.

Hammad hospital asibitine da mahaifin Hammad ya gina masa tun yana turai karatu,azuwan yana dawowa seya fara ayki,amma fafur Hammad yace soja zashi beson asibitin.

Haka Mahaifinsa ya haƙura,aka rufe asibitin,badan yana so ba sedan ba yadda zeyi.shiyasa da jameel yabar aykin sojan ya miƙa masa asibitin domin yaci gaba da kulawa dashi.

Hammad sunan yasamo asaline daga wani abokinsa bature,da be iya faɗin Muhammad ba se dai yace Hammad,mutuncin dake tsakaninxa dashine yasa Muhammad maida sunan nickname ɗinsa,sabida

Please Login or Register in order to submit comment