Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dago kai ya kalle ta wai ita bata yadda ba tayi kwalliya ya fada cikin ranshi....kuma fa kwalliyar ta tsumoshiπŸ˜‚amma sai ya basar yace"xauna zamuyi mgn.,xama tai kan kujera ya dalla mata harara yace sauko kasa saukowa tayi ....

"Akan maganar da daddy yayi ne na aurenmu.ki gaggauta sanar musu baki son auren kina jina ?idan kuwa kika kuskura akayi wannan auren to kinyi babban kuskure dan ni ba sa,an auren ki bane kije can ki nemi bakauye irinki ki aura wanda bai waye ba.....shiru yayi yana jiran jin abinda xata fada"'

Ganin bata da alamun mgn yasa ya daka mata tsawa,...ba dake nake ba ko ni sa,an wasanki ne.? Juyar da kai tayi tana turo baki cikin kunkuni tace toh kai kaje ka fada mana.....what... Bayan hannunsa yasa ya bige mata baki sosai taji xafi dan haka tasa kuka ...I will slap u idan baki rufemin baki ba mara kunyar yarinya kawai.,". Ina gaya miki idan kika sake akayi wannan auren ko?xaki raina kanki "
Tashi ki bani waje ,yi tayi kamar bataji shi ba ....ba dake nake ba.. Ya fada a fusace yana shirin kai mata mari..da gudu ta tashi tabar dakin tana kuka......
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu hanan)

30_35

A falo ta samu aneesa na kallon tashar Bollywood dan akwai ta da son Indian film.,


Ganin tana kuka yasa ta saurin mikewa tana tambayarta lpy?.ba yah najeeb ne ba ya dake ni ....what duka fa kikace? Eh mana bakina ya buge min kuma har ynx xafi yake min,rikota tayi tace am sorry sis kyale yah najeeb....


"Relaxing ya kara yi kan kujerar daya ke ya sauke numfashi.. Baiyi xaton yarinyar xatai masa musu ba...kodayake...ai dama ba kunya gareta ba.dole ya kara yimata warning.


******
Habeeb ne ke kallon najeeb daya dafe kai ya rasa abinda ke masa dadi a duniya...gashi ko jiya saida daddy yayi masa maganar ya fara shiri"'.mummy ma sam taki goya masa baya...table din da habeeb ya dakane ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi.ajiyar heart ya saki tare da lumshe ido, haba abokina what's wrong with u....uhm " yan kwakinnan sam baka da nutsuwa pls...tell me....ido ya bude ya kalli habeeb yace gsky abokina ina cikin problem... Ina yarinyar daka ta6a gani agidanmu ka shiga gaida mummy?... Tunani yadan yi sannan yace "....yeah na ganeta ko ba wannan beautie din ba...mtssss najeeb yaja wani dogon tsaki yana harararshi..banxa namamajo..dariya habeeb yayi yana nuna kirjinshi da hannu shi nine namamajo ko?". Eh din na fasa fada maka damuwar tawa.am sorry pls mutumina fada min.harararshi ya karayi sannan yace wai ita za,a auramin .....Wow abokina Allah sanya alkhairi kunfa dace am very very happy.... Baki najeeb ya saki yana kallon habeeb ,kai fa mugun dan iskane wllh ya ina fada maka banson yarinya kana wani cewa kana murna?look... Najeeb shawarace xan baka kayiwa su daddy biyayya baka san irinta whl suke ba.tun wuri ka canxa ra,ayinka kar daga baya kaxo kana*
DANA SANI....*Allah ya kiyaye akanwa xanyi DANA SANI?"
Bari kaji ni ko digon sonta babu cikin xuciyata kuma baxan ta6a sonta ba...kafada ya daga tare da ta6e baki yace xamu gani ai.....;!*ni kayimin ma shigar sauri ai dana kafa gwamnatina habeeb ya fada cikin salon tsokana ...ynx ma ai bata 6aci ba zaka iya xuwa banxa kawai.. Tashi ka fitar min a office ya fada yana mikewa hadi da sanya wasu takardu cikin brief case dinshi".
"Oh korata ma kakeyi? Eh din na koreka.....tashi yayi yace ba komi ango ya sunanta ne?banxa yayi masa dan yaga alamun yau habeeb tsokana yake ji ,brief case dinshi ya dauka yace in ka gama iskancinnaka ka rufo min kofar...........





Ummu hananπŸ™‹πŸ»
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu
hanan)

35_40

"Najeeb ne xaune gaban mummy sai magiya yake faman yi mata akan afasa auren,.tsaki tayi tace baxaka daina wannan maganar ba ko?....kasan kuma idan daddyn Ku yaji sai ranka yayi mummunan 6aci,
Ji yayi kamar ya fashe da kuka wani haushin Hannah ne ya Kara kamashi..."

Ranar asabar mummy taga har sha daya ta wuce najeeb bai fito ba

Hannah ta kirawo tace taje ta kirawo shi yaxo yai breakfast ba don ranta yaso ba ta nufi dakinshi,. "Sai da ta dan jima atsaye sannan ta kama handle din kofar ta bude .da sallama ta shiga baya falon kamar xata juya ta koma sai tai karfin halin nufar bedroom dinsa". Kwance ta hangoshi kan bed dinshi yayi ruf da ciki "'wai ance kazo abinda yaji kenan yayi saurin juyowa a fusace yace ke wace irin mara hankali ce xaki shigomin daki ba sallama dan karamin bakinta ta turo tace to ba nayi ba.,
Mikewa yayi ya nufota daga shi sai boxer da singlet juyawa tayi da sauri xata bar dakin,. Wllh kika fita nida ke ne,....tsayawa tayi tana turo baki, gabanta ya karaso yace"'ke karamar mara kunya ko?...maxa kimin kneel down,... Dan Allah kayi hakuri ta fada kamar xatayi kuka.kinyi ko sai na kwada miki mari tuni kwalla ta fara xubo mata tsugunawa tayi harararta yayi yace " oya hands up hannu ta daga ....xan shiga wanka saura kuma ki tashi xakiga abinda xan miki,ya shige bathroom dinshi. Kamar ta tashi ta gudu sai kuma ta fasa dan ta fuskanci wannan yah najeeb din mugu ne....wllh "sosai Hannah ta gaji sai faman mutsu2 take sai daya dade kafin ya fito ashiryen shi cikin dark blue din jeans da farar riga sosai kayan suka amsheshi sai kamshi yake xabgawa,.ido suka hada da ita ya watsa mata harara Dan Allah kayi hakuri ta fada hawaye na xuba bai tanka taba sai phone dinshi daya dauko daga kan bed ya xauna kan kujerar dake kusa da ita ,."

Ya dora kafa daya kan daya "ido ya lumshe ya bude ahankali yace me yasa baki fadawa su daddy baki son auren?...bai jira answer ba yaci gaba" last warning dina dake idan kika sake akayi wannan auren ina tabbatar miki rayuwar prison xai fiye miki sauki fiye data gidana...dan banga me xanyi dake ba ko digon sonki babu cikin raina kuma 4ever baxan ta6a sonki ba.am hearing me?....kai ta girgixa, good get out.... Da kyar ta iya mikewa ta fita awani corridor ta tsaya ta goge fuskarta ...dakinshi ta kara duba tace Allah ya isa mugu kuma wllh baxan ta6a yafewa ba,"*karar rufe kofarshi taji dan haka da sauri tabar wajen. Afalon ta sami mummy da aneesa, kallon ta mummy tayi tace "Hannah sai ynx?....mummy tadan yimin gyaran bedroom ne ,najeeb ya fada yana shigowa falon juyawa tayi ta kalle shi wata muguwar harara ya wurga mata yai mata alamun idan ta fada xata gane kuranta,karasa shigowa yayi ya gaida mummy aneesa kuma ta gaisheshi.ita kam Hannah dakinsu ta wuce tadan kwanta ta huta cox abinda mugun nan yayi mata...


Ummu hananπŸ™‹πŸ»
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu hanan)

40_45
"Cikin lkc kankani shirye2 suka fara kankama!,najeeb kuwa tamkar ba shine angon ba sai habeeb ne keta faman hidima,.";;

" Ranar alhamis tun safe Hannah da aneesa ke ta faman shiri don tafiya sabon layi xataje yi musu sallama, kuma najeeb ne xai kaisu cox direban ya tafi gida mahaifiyarshi bata da lpy. Sai da mummy ta nuna masa 6acin ranta sosai kafin ya yadda xai kaisu.10:46am najeeb ya shigo main falo cikin wata danyar shadda marron color sai walkiya take baisa hula ba sai kanshi daya sha gyara yana ta kyalli hannunsa daure da agogo kirar hublot baki sosai yayi kyau, ba kowa falon dan haka ya nufi dakin mummy knocking yayi ta bashi ixnin shiga .axaune ya sameta kan praying mat ta idar da sallahr walha tana azkar gaisheta yayi sannan yace ya shirya ."okay suma din ina tunanin sun gama dan tun asuba suke ta shiri ko bacci basu koma ba,ta fada tana murmushi. mikewa tayi tace bari in musu mgn sai su sameka a mota ko?...,okay mummy ya fada shima yana mikewar,tare suka fito ta nufi dakinsu Hannah shi kuma ya fice ,ashirye ta samesu tace toh ai saiku fito Ku tafi yana mota yana jiranku,toh mummy suka hada baki wajen fada."!sallama sukayi mata suka dau kayansu suka fita ,amota suka sameshi sai harare2 yake aneesa ce ta fara shiga Hannah ta daga kafa kenan da niyyar shiga wata uwar tsawa daya daka ne yasa ta saurin yin baya afusace yace"uban waye direbanku?...."I said waye direbanku"jiki na rawa Hannah ta bude seat din gaba ta xauna dan ta rasa miyasa ynx tsoron shi take ji.sosai stupid girls kawai ya fadi yana Jan tsaki, kunna motar yayi ya bata wuta sannan ya fixgeta da karfin tsiya daga Hannah har aneesa ba Wanda bai kifa ba,tuni dama baba lado maigadi ya bude gate don haka ba jira ya fice."tafe suke tamkar kurame ba mai mgn sai dai idan sun had a ido da aneesa ta mirror su ta6e baki ba damar magana.😁.
Da tafiya tai nisa ma Hannah barci ta fara abinta ai yana ganin ta fara barci ya daka mata duka acinya afirgice ta tashi tana sosa inda ya dake ta dan dukan ya shigeta harara ya balla mata yace"waya baki ixnin yimin barci a mota?...oya tashi ko kuma in saukeki anan saiki fi jin dadin barcin nan da katsina shine xaki wani fara barci, bata ce kala ba don abin yafi karfinta dan xatai barci ma sai ta fada masa kenan?...."dole ta wartsake dan ta hadu da Wanda yafita iya rashin M.

Suna xuwa Hannah ta fita da sauri ta shige gidan tana kwadawa gwaggo kira kayansu ma sai aneesa ce ta shiga dasu.gwaggo kam baki har kunne sbd ganin yadda "yar lelenta ta koma," ruwa ta kawo musu suka sha.ta xuba wani a kwanon sha tace aneesa ta kaiwa direba, sai sannan suke ce mata ai da yah najeeb sukazo.baki ta rike tace oh ni "yasu kuma sai ya tsaya awaje?sai kace wani bako......maxa je kice ya shigo mikewa tayi ta leka ta fada masa ta dawo," sai da ya dan jima kafin ya shigo ,ya xauna kan tabarmar data shimfida masa suka gaisa itakam gwaggo ma kunyarshi take ji.ruwa tasa aneesa ta kawo masa hada ido sukayi da Hannah data lafke ajikin gwaggo sai shagwa6a take xubawa hararta yayi itakam ko ta kanshi bata bi ba dan yau cike take da farin cikin ganin gwaggonta,"bai wani dade ba ya Mike yace xai tafi ,da wuri haka najibu?....murmushi yadan yi yace ehh gwaggo ina da abinda xanyi idan na koma,toh ai shikenan Allah ya kiyaye hanya.ameen gwaggo, kudi ya xaro daga aljihunsa masu yawa ya ajiye agabanta,a,a har da wahala haka?...ba komi gwaggo, godiya ta dinga yi har ya fice.duban Hannah tayi data ke makale da ita tace"tashi kije kuyi sallama mana,shagwa6e fuska tayi tace ai munyi a,a tashi mana baki ga tafiya xaiyi ba?...badon taso ba ta Mike ta fita amotar ta sameshi ya xiro kafa daya waje gabanshi ta tsaya ba tare data yi mgn ba dagowa yayi ya kalle ta adakile yace' waye xai kwashe muku kayan dake both?....., maza kirawo aneesa Ku kwashe "juyawa tayi ta kirawo aneesa ya bude musu both din suka kwashe tsarabar da sukayo ,.
Suna fitowa suka ga har ya tafi hada ido sukayi suka ta6e baki.... Kai aneesa wannan yayan naki fa sai a slow murmushi aneesa tayi tace xai canxa ne kai Hannah ta girgixa tace uhmm banga alamun hakan ba.,juyawa sukayi suka koma cikin gida.! Satinsu daya direba yaje ya dauko su don ya dawo Hannah ta sha kuka especially ma da gwaggo nayi mata nasiha....



******
" Toh biki dai yaxo dan yau ake yin kamu gida ya cika taf da "yan uwan mummy dana daddy, a harabar gidan akayi kamun inda aka yiwa wajen decoration yayi kyau sosai, amaryah Hannah kuwa ba,a maganar kyawun da tayi!.sanye cikin gown silver mai touch din golden color mai hade da shoes dinshi da purse " yan uwan mummy kuwa sai yabawa suke da kyawun surukar tasu don mai gyara ta musamman mummy ta dauko sai sheki take.washegari kuma akayi dinner saida mummy tayi wa najeeb da gaske sannan yaje dan da farko cewa yayi baxai je ba.sai 12:00am aka tashi....


Ummu hanan😍
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu hanan)

Kuna ina ne? "yan mmn humaira novels gaisuwarku daban ce. Mmn humaira, mmn aliyu, siddiqah,musty mom,shakunerh,daddy's Angels, faixah,ummi elmustapha,Fatima umar,mmy siyama,rukky hassan,mmn meenah,Zainab tofa,mmn ilham,khadijatul iman,madinatu lemamu,ummu batuul.kai oll members of group Allah yabar xumunci da kaunar juna.😍😘😍😘🀝#ana tare#

45_50

" Washegari asabar al'umma da dama suka shaida daurin auren NAJEEB ALIYU TIJJANI da HANNATU AHMAD TIJJANI akan sadaki dubu dari.aranar ma sai da akayi mother's night Wanda mummy ta hada,sai lahadi aka kaita gidan ta dake rijiyar xaki wanda daddy ya mallakawa najeeb plat ne sai shegen kyau,aneesa ta Mike tace toh amarya mu xamu tafi.rikota Hannah ta karayi tace wllh tsoro nakeji pls ki bari sai anjima gsky sis tafiya xamuyi wata "yar kanwar mummy ce surayya tace aneesa mu bari angwayen suxo mana ido ta xaro😳a,a wllh ni nasan halin mutuminnan kuxo mu tafi kawai, mikewa tayi tana kuka tace Allah saina biku danni tsoro nakeji Dole suka koma suka xauna."



"A can gidan daddy kuwa najeeb ne kan bed dinshi yai dai2 yana danna system dinshi, habeeb ne yace" wai kai mallam me kake nufi goma fa harta wuce banga kana shirin tafiya ba.to ina ruwanka banxa dan sa ido,nida barin gidan nan sai gobe ,"mansoor dan uwansu daga bauchi yace ban gane sai gobe ba?....ya za,a kai maka amarya yau kace baxaka gidan ba?.....why?...habeeb ya kalli mansoor yace"kyale dan iska kawai wllh ko ka tashi ka shirya mu rakaka ko ynx inje in fadawa mummy,. Banxa yayi masa yaci gaba da danne2nshi,mikewa habeeb yayi yana shirin fita....da sauri najeeb ya aje system din ya diro daga kan bed din,rikoshi yace wai kai da gaske kake?..harararshi yayi yace"ok ka dauka wasa nake?..am sorry my friend bari in shirya,." 'Bathroom ya shige yayi wanka ya fito ya shirya cikin wani yadin filtex fari mai asalin kyau da tsada.!ya dora hula ya daura agogon Rolex ahannunsa.masha Allah mutumina kaga yadda kayi wani kyau na musamman?....gsky wankan fa yayi ba karya,dole ka sumar da amarya yau da wannan gayunnaka,wani kallon banxa ya watsa masa ba tare da yayi mgn ba..."!


"Da sallama suka shiga dakin su surayya suka amsa musu,.duban aneesa najeeb yayi yace xaman me kuke da baku tafi gida ba?...ya fada fuskar nan kamar bai ta6a dariya ba,..am dama yan...xu xamu ta...fi ta fada tana mikewa gami da daukar bag dinta ,..habeeb yace Ku tsaya saimu kaiku tunda dama xan maida mansoor..toh anan dai habeeb da mansoor suka yiwa ango da amarya nasiha tare da addu'ar xaman lpy,...sukayi musu sallama mikewa yayi xai musu rakiya,habeeb yace kaga mallam mun yafe wannan rakiyar .ai bakai ka sani fita sukayi cikin harabar gidan, suka shisshiga mota sai habeeb daya ja najeeb gefe yace" pls my friend... dan Allah ka daina nunawa yarinyar nan kiyayya ynx fa duk wani nauyinta ya rataya bisa wuyanka kaji?...abokina?...ta6e baki yadan yi yace okay nop,dafa kafadarshi habeeb yayi yace "that's gud my friend...yawwa sai daya maganar kabi ta ahankali kaga yarinya ce nasanka da bin abu xafi2 hannunshi dake kan kafadarsa ya wurgar ya jefa masa harara yace " kai wannan ya dama shege,sosai habeeb yake dariya daga nan ya shige mota ya tayar suka bar gidan,!.. Najeeb kam sai daya dade atsaye a wajen hannayensa xube cikin aljihun wandonsa ya rasa meke masa dadi sam ya rasa abinda yasa bai son yarinyar, ajiyar xuciya ya saki ya nufi gate din yasa kwado ya rufe sannan ya juyo ya shige falon gami da kullowa........



Ummu hanan😘
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu hanan)

50_55

"Kai tsaye part dinshi ya nufa yasa key ya bude sosai wajen ya tsaru yayi kyau, kan bed ya cilla phone dinshi da keyn motarshi," kayanshi ya cire ya daura towel ya shiga bathroom yayi wanka ya fito,3qtr yasa fari da "yar karamar riga mai yankakken hannu."!
ya haye bed ya kwanta dan karamin tsaki yaja cikin ranshi yake fadin ;" da ace yarinyar xa6inshi ce yasan da tuni yana can yana kwasar garaπŸ™ˆto wannan kuwa sam baya sonta bare har akai ga batun sha'awarta...."


"Hannah kuwa dama bata sa ran dawowarshi ba dan haka tayi kwanciyarta bayan tasa kayan barci,!dai tunanika ne birjik suka bijiro mata,wai sunan first night dinsu kenan kowa yana dakinshi. Tsiyar a hada ka da wanda bai sonka kenan,....uhm kodayake wannan masifaffen ina tunanin ko wadda yakeso ce saiya dinga nuna mata halinsa😏
ahaka dai sarkin iya snatch ya saceta,....*


" Da asuba ta tashi tayi sallah ta kara komawa bacci don agajiye take liqis,."


"Kamar daga sama taji an dala mata wani uban duka a bayanta,atsorace ta tashi. eye to eye sukayi da najeeb daya hade girar sama data kasa yana jifanta da wani matsiyacin kallo cikin karfin hali tace " yah najeeb ina kwana?? da ban kwana ba xaki ganni?.... Kinga ba wannan ne ya kawoni ba ki tashi kije ki gyara min part dina sannan ki share duka gidan nan kiyi moping again kije ki bawa flowers ruwa ya fada ba alamun wasa,shiru tayi tana kallon shi don ta rasa abin fada."....ba magana nake miki ba ya fada afusace, da saurin ta ta daga kai tace toh,tsaki yaja kana ya fice daga dakin...kallo ta bishi dashi,lallai da aiki babba agabana.agogon dakin ta kalla taga 7:4am.mikewa tayi ta fita a falo ta sameshi yana aikin nashi na danne2 a system kwance kan doguwar kujera,.... gabanshi ta karaso tace ina ne side din maka??..kallon ta yayi up and down yace "wai ke dabbar inace?...haka ake yiwa miji magana?wllh su daddy sun gama dani da suka hadani da wannan abar.sosai maganar ta sosa mata rai amma saita daure dan ynx su Hannah anyi hankali sosai ga hakuri hakan ya samo asaline kuma daga nasihar da mummy keyi mata kullum,durkusawa tayi tace" inane wajan??makauniya ce ke?...ya fada idanunshi kan system, tashi tayi tana goge idonta da hawaye suka fara xubowa..."


*wata kofa ta nufa da take kyautata xaton nanne shiga tayi ta fara wanke bathroom sannan ta gyara gadon,ta share tayi moping ta fesa air freshner dakin ya dauki wani daddadan kamshi,.janyo kofar tayi ta dawo wajen shi ta durkusa tace yah najeeb na gyara..
Sai daya dauki fin minti biyar sannan yace kije ki bawa flowers ruwa kafin nan na tashi daga nan sai ki gyara,..a sanyaye ta tashi ta fita daga falon taje ta basu ruwa gabadaya ta gaji,..bata tarar dashi a falon ba Dan haka ta fara gyarawa duk da ba wani datti amma dai gara tayi dan gujewa masifar wannan bawan Allahn da aka hadata dashi,......"

"Bayan ta gama da nan ta tafi dakin ta shima ta gyara,gsky su mummy sunyi kokari ta fada ganin irin uban tsadaddun kayan da aka jibga mata...wanka tayi ta shirya cikin gown ta atamfa red color,mai kawai ta shafa sai powder da lipstick amma duk da haka sai da tayi kyau,parpumes kala2 ta faffesa daga nan ta shiga kitchen dan hada breakfast, sakin baki tayi tana karewa kitchen din kallo ganin irin dukiyar da aka narka tamkar ba,a san ciwon kudin ba,
Tea ta dafa dayaji kayan kamshi sai chips da kwai
Kan dining ta shirya, tunani ta shiga yi ta kirawo shi ne ko kuwa ta kyale shi,xuciyarta ce ta bata shawarar tayi masa mgn yaxo yayi break
Dakinshi ta nufa knock tayi taji ba,a amsa ba,karfin hali tayi ta kama handle din kofar ta murda ta shiga, kwance yake kan sofa yana latse2a a system.... Tsaki taja cikin ranta tace aikinshi kenan daga masifa da jaraba sai latse2n tsiya a system ko waya😏
" karasawa tayi ta dan rissina tace "yah najeeb na gama break yana dining, harara ya watso mata yace kinga nayi kala da Wanda xaici wannan jagwalgwalon naki..??.get out of my room... Ko kuma ynx kici duka.," juyawa tayi ta fita tana tunanin wane irin hali ne da yah najeeb?..sam bashi da tausayi ga masifa ita dariya ma maganar ta bata wai jagwalgwalo??.....sai dai kar a kuma tunda abincin dayake chi agida ai su sukeyi zama tayi ta cika tunbin ta dan ta fuskanci in ta biyewa wannan man din sai hawan ruwa ya kamata,😁.


*Bayan ta gama ta dawo nan kan 3sitter ta kwanta tana buga games awayarta,....karar bude kofar shi taji xuwa yayi ya wuce ta bai ko kalle ta ba,binshi tayi da kallo sanye yake cikin shadda ash color rigar bata kai har kasa ba...bai saka hula ba sai kwantacciyar sumarshi data sha gyara ta ke ta faman kyalli ,ya fito an angon sakπŸ‘ŒπŸ»sosai yayi mata kyau ainun,!daf da xai fita falon tace adawo lpy bai juyo ba bare ya amsa yasa kai ya fice,....dama bata sa ran amsawar tashi ba,ahankali ta saki ajiyar πŸ’—,kwana daya tal ! a gidan miji har ta fara fuskantar mtsl,cigaba tayi da abinda take har bacci ya kwasheta...."


*Ahankali ta bude idonta daga baccin daya dauketa suka sauka kan katon watch clock din falon dake facing dinta,12:54pm tashi tayi ta nufi kitchen ta dora girki jallof din taliya & macaroni tayi da yaji spices da kayan lambu,gabadaya gidan ya dume da kamshin girkin sai coconut drink data hada tasa a frige abincin ta juye a karamar warmer don iya cikinta ta dafa tunda maigidan baya cin jagwalgwaloπŸ˜„...
Wanka tayi,tayi light makeup ta shirya cikin doguwar riga pink color mai adon manyan stones ash agaban rigar mayafin rigar ta daura,wow na fada lkcn da nake lekota ta bayan kofa dan dauko muku rahoto,."sallah tayi sannan ta fito ta xubo abincin a plate da lemon kan kujera ta xauna,....taci...bayan ta gama ta maida kitchen ta dauraye plate da spoon din ta dawo falon,karamin tsaki taja gabadaya kadaici ya isheta,.....phone dinta ta jawo da niyyar calling din aneesa,knocking din kofar da akayi ne yasa ta fasawa.,ajiye wayar tayi taje bakin kofar ta tambayi waye??...voice din aneesa data jine yasa ta saurin budewa cike da murna aneesa ce da wasu "yan uwan mummy su uku aunty salma da aunty rabi sai aunty hauwa,rungume juna sukayi da aneesa cikin doki daga nan suka shigo falon,! Har kasa ta durkusa ta gaishesu,cikin sakin fuska suka amsa aunty rabi ce tace ina najeeb din??....
Murmushi tayi tace ya fita,ya fita kuma??...suka hada baki wajen fada ido suka hada da aneesa, am..eh wai anyi kiranshi ne daga office ta fada cikin sarkewar halshe,aneesa kam tasan ta fadi hakanne dan ta kareshi,...mikewa tayi da nufin kawo musu ruwa aunty hauwa tace" yi xamanki Hannah tafiya xamuyi,da wuri haka?...eh wllh muna komawa xamu tafi mu kace bari muxo muga gidan amarya jiya bamuxo kawo ki ba,aunty salma ta fada tana mikewa tsaye suma din sukayi! Amma dai banda aneesa ko?...ta fada cikin marairaicewa ido😳
Ido aneesa ta xaro tace"a,a tare xamu tafi..baxan xauna ba,aunty rabi tace ki xauna mana aneesa ki taya ta hira xuwa lkcn daxai dawo mana..ita dai aneesa bataso xama ba,!sallama sukayi musu sukayi rakiya.sannan suka dawo....


Ummu hanan😍
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu hanan)

55_60

β˜…"Can bedroom dinta suka shige suka dasa hira sai dai sam Hannah bata fa'dawa aneesa irin problem din data fara fuskanta,.
Bayan la' asar suka shiga kitchen sukayi girki lafiyayye.hadi da guava drink suka juye cikin warmer,.... 6:10pm aneesa tayi shirin tafiya!Hannah tace "ki kira mummy mana a turo miki driver,.. Kai ta girgixa tace a,a xan hau napep kawai....Allah sis kamar kar ki tafi,Hannah ta fada idanunta cike da kwalla..rikota aneesa tayi tace" plz mana sis ai nasan ynx yah najeeb din xai dawo,...haka dai sukayi sallama ta tafi......"

β˜…Aranar harta kwanta najeeb bai dawo ba duk tsoron gidan ya kamata,!


"Toh haka dai xaman nasu yaci gaba da tafiya, Hannah ta koma tamkar " yar aiki sam bata da isasshen hutu....wani lkcn ma idan tayi gyaran sai yace bai yi ba dole ta kara maimaitawa,
Tun abin baya damunta harta fara sa damuwar cikin ranta...kusan kullum mummy na kiranta a waya ta tambayeta ko akwai wata mtsl in yana yi mata wani abun ta fada mata,..sai dai tace lpy lau baya yi mata komi...."

Kwance take kan bed dinta ta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On DANA SANI
avatar
ishaq-abdulhamid

10 months ago

Reply

I love the book

Please Login or Register in order to submit comment