Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani alhaji mai mata biyu har ta haihu,duk da wulakancin da take sha hakanan take zaman hakuri. Hindatu kuwa tana nan tare dani a Abuja ta soma karatunta a jami'a, hakanan Abba da nake jinyarsa saidai yanzun jikinsa da sauki sosai. Waziri ma ya matsamin na maidoshi gabansa inajin hakan zaiyi tunda shima Abban yace ya gaji da zama gidana saboda kunyar hasina. Duk da dai yanzu gidane na kashin kaina."

Tasleem tayi shiru,tabbas rayuwa abar tsoro ce. A sanyaye ta kara tambayarsa

"Ina labarin Ridwan kuma?"

Murmushi Abdullah yayi

"Allah Sarki,abbansa fa ya jima yana fushi dashi har korarsa yaso yi na hana. Amma yanzu yayi aure yana zaune acan London wajen uncle dinsa da matarsa Jidda. Yaransu biyu ma,daya taci sunanki dayar kuwa sunan mamansa."

Tayi murmushi kawai.

*****
Washegari yaya abdullah yana tafiya,itama ta shirya koda ta yiwa mamma sallamar komawa wajensu inna bata ko kalleta ba. Haka nan ta wuce a sanyaye.
Da la'asar Liman ya tura ayi kiranta.....!


'YAR BARIKI

©Rufaida Omar

(55)

Bata kawo komai ba ta mike ta yafa mayafinta ta nufi dakin Liman jikinta akwai yanayin sanyi wanda tun dawowarta daga gidan mamma take cikinsa. Koda inna ta tambayeta ta amsa da babu komai.

Yana zaune yana duba wani littafi na hadisai yaji sallamarta wanda hakan yasa shi ajiye littafin a gefe yana mai amsawa fuska a sake. Ta shigo tana yamutsa fuska kadan kafin ta soma kokarin zama tana fad'in

"Nidai wannan tsohon kana neman matsamin fa,yanzu kuma menayi aka d'agoni bama a tarbeni da 'yar shila ba."

Yayi dariya

"Shak'iyiya,wanda kika ci bai isheki bane a k'aro maki gobe? Nutsu don magana zamuyi."

Ya soma da yi mata doguwar nasiha akan muhimmancin aure wanda tun daga haka tasha jinin jikinta,kirjinta kuma bai bar bugu da sauri da sauri ba. Saida ya kammala sannan ya bijiro mata da bukatarsa na neman amincewarta kan batun aurenta da Haris.

Cikin tsananin mamaki da fargaba ta dubeshi

"Shi Haris dinne yace yana sona baffa?"

Jin dadi game da amsar da zai bata yasa Liman yin wata 'yar dariya

"Shakka babu,harisu ne yazo da batun kamar yasan fatanmu kenan ni da aminina. Kuma munyi na'am da batunsa nasan bazaki watsa mana k'asa a ido ba kasancewarki yarinya mai biyayya."

Tayi k'asa da kanta,nan da nan abokan hirarta suka ziyarci fuskarta(hawaye). Ina ita ina Haris wai? Haris yasan abunda yake kuwa? Me zaiyi da sauran maza? Sam bazata bari ta cuci mai niyyar taimakonta ba,kai ta kasa gaskata da gasken shine yayi tayin auren nata.

"Kuyi hakuri bafamfa,bazan iya aurensa ba!"

Nan take annurin dake saman fuskarsa ya dauke,tamkar bai taba dariya ba ya koma Abdulmaleek Hussein dinsa sak!

"Nufinki zaki bani kunya ne Tasleem? Toh bari na fadamaki wallahi tunda nake da Aminina tun zamanin kuruciyarmu dayanmu bai taba zuwar wa dayanmu da bukata ba munyi watsi da ita. Baki isa ba Tasleem! Ko uwarki k'arya takeyi na nemi bukata awajenta tak'iyi,na takaice maki ma aminina shine ya wuce gaba wajen aurenta da Ubanki tun a farko domin a baya banso tayi nesa har haka ba. Ki tashi ki barmin d'akina,aure kuwa keda Harisu saidai idan anyishi ki mutu."

Daga haka ya maida fuskarsa gefe babu wata walwala a samanta.

A sanyaye tasleem ta mike tana k'ara mannewa da abokin hirarta harda sheshshek'a.

Kallo daya tayi mata kafin tabar murza robb a hancinta

"Lafiya kuwa?"

Cikin kukan dai ta labarta mata yanda sukayi da Liman,inna taja tsaki gami da fadin

"Allah Ya kyauta,ina goyon bayan Liman,wannan hukuncin yayi. Domin kuwa samun yaron mutunci irin Harisu a zamanin nan akwai wuya. Nikam dari bisa dari na amince kuma banga aibu da aurenku ba. Budurwa sharab dake,ai wallahi sai yanda kikayi dashi ta hanyar biyayya da kissar d'iya mace."

Ji tayi tamkar magana take yab'a mata,da sauri ta mike ra shuri takalmanta batayi wata wata ba ta fada gidan gwaggo Hajara bazata kwana a gidan ba. Meyasa Haris zaiyiwa rayuwarsa haka? Duk a zatonta jihadi yake niyyar yi don tausayinta batasan kudurin da Haris ke shirin yi ba. Gwaggo Hajara ma yabo da hamdala ta shiga yi,ai ita kam tun farkon ganinta da Haris takeso aure ya kullu tsakaninsu sai gashi Allah Ya amsa. Nan tayita lallashin tasleem gami dayi mata nuni akan illar bijirewa umarnin babba.

******

"Nayi zaton ai da Zahra za'a hadashi?"

Murmushi Malam yayi kafin ya bata amsa

"Ya kike wata magana kubra? Da Zahra da Tasleem basu da wani bambanci a wajena. Tunda yaro ya nuna yanason Tasleem sai a bisu da addu'a inajin hakan zaifi."

Ba haka taso ba sanin da tayi Zahra ita kadai take iya gayawa sirrinta,kuma ta tabbatar mata cewar tana son Haris. Bata hakura na dai ta k'ara muskutawa

"Malam fadamaka ne banyi ba amma hakikanin gaskiya Zahra banda alkunya ya hanata magana tana son Haris kwarai dagaske,mezai hana a had'a mishi su biyu duka a aura mishi na tabbata Harisu bazai watsa mana k'asa a ido ba."

Malam ya dubi hajja kubra a mamakince

"Harisun ya gayamaki yana da ra'ayin mata biyu da wurwuri haka ne?"

Ta girgiza kai,zatayi magana ya dakatar da ita

"Bazan hanaki abunda kikaga zaifi ba,saidai ni da kaina bazan tunkari Harisu da zancen ba. Ki tuntub'eshi da kanki idan yaga zai iya toh nawa bai wuce daura aure ba."

Ranta ya d'anyi sanyi jin hakan. Tana matukar kaunar Zahra,bata tab'a tsayawa kula samari ba sai gashi rana tsaka ta kamu da son Haris wanda har ta kasa b'oye mata ita kuwa mezaisa ta kasa yin wannan kokarin gareta?

"Shikenan Malam,Allah Ya zab'a abunda yafi alheri. Zan gwada hakan."

"Ameen." Kawai yace mata kafin ya nemi ta kawomishi furarsa.

******

Momi tayi wani murmushi kafin ta rausaya idanuwa

"Ka kwantar da hankalinka Kb,na tabbatar maka baby zata dawo. Bata komai saida shawarata. Koda ya tabbata auren zatayi na tabbatar maka da cewar zata nemeni bada jimawa ba. Nima ban sameta a waya ba,saidai nasan wacece baby tunda har ta furta maka tabar wannan harkar tabbas da gaske takeyi. Mu kuwa a sharuddan kungiyar,lallai idan mace zata bar harka sai ta tattaro mana dukkan kadarar data mallaka cikin harka idan kuwa ba haka ba zamu hanata auren gaba daya muyi sanadiyyar gurb'acewar dukkanin rayuwarta wanda nake da yak'inin Baby bazata iya ba. Yanzu kawai mu jirayi dawowarta."

Kabir ya jefa hannu aljihu ya zaro bandiran kudi 'yan dari bibbiyu har uku ya dire a kusa da Momy yana murmushi

"Ga wannan asha ruwa,burina ta dawo na ganta."

Tana taunar cingam gami da wani irin murmushi na duniyanci ta dauki kudin a wulakance tana juyawa kafin ta watsa mishi kallo tana fari da ido

"Bukatarka zata biya da zarar Baby ta dawo. Zanbi kowacce hanya don ganin ta amince da aurenka."

Ya shafi suma yana dariya kafin ya jinjinawa Momy

"Dakyau momynmu,anjima zanbi jirgi zuwa Abuja,sai naji wayarki."

Daga haka yasa kai ya fice yayinda Momy ta bishi da murmushi na musamman.


'YAR BARIKI

©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(56)

Kwance yake akan restingchair a farfajiyar gidansa daga can poolside. Idanunsa a lumshe fuskarsa ma'abociyar kyau da kwarjini sai shek'i takeyi. Yammacin juma'a ne,garin yayi luf luf sai wani ni'imantaccen iska ke busowa da kamshin k'asa kasancewar da safiyar yau din anyi ruwa sosai. Sanye yake da jar t-shirt,da wando wanda da kad'an ya rufe gwuiwoyinsa.

Sallamar isah mai gadinsa ne ya sanyashi bude idanunsa yana mai amsawa bayan yayi kokarin danne damuwar dake shimfide kasan ransa.

"Yallabai kayi bak'o yace a sanar dakai cewa Deen Bukar ne."

Jin sunan wanda ya jima baiji daga gareshi ba ya dago yana murmushi

"Kayi mishi iznin shigowa isah."

Matsakaicin saurayi ne,mai d'an kiba. Yana sanye da kananun kaya shima,kallo d'aya zakayiwa bak'ar fatarsa ka fahimci yana hutawa sakamakon lukui lukui da tayi. Ganinsa yasa Haris mikewa tsaye yana bayyana hakoransa a waje cike da farin cikin ganin oldclassmate dinsa na Malaysia. Deen Bukar. Rungume juna sukayi suna masu dariya kafin su cafke.

"Shegen sama,deen kana hutawarka,irin wannan k'iba kamar ba soja ba?"

Deen yayi dariya yana nunoshi da yatsa

"Zaka fara ko Gent? Toh ai kaine za'ace baka aikin komai. Ka ganka kuwa?"

Sukayi dariya kafin Haris ya dauki wayoyinsa da tab

"Bismillah."

Suna tafe suna hira har suka shiga falon Haris wanda ya k'ayatu iya k'ayatuwa. Haris yayi kiran kuku dinsa,Henry. Ya sanyashi ya kawowa bak'onshi abun motsa baki. Bayan tafiyar henry ya dubi deen

"Sai fa hakuri kasan abunka da gwauro."

Deen yayi dariya

"Kai ka sowa kanka,ya dace ka nemo mana mata musha biki. Gashi dai twins dinka(yaran deen) suna k'ara girma. Kb fa,ya labarinsa?"

Haris yayi dariyar yak'e

"Yana nan da bebinsa d'aya,Nasreen."

Deen ya jinjina kai lokacin Henry ya iso ya soma zuba mishi juice a kofi.

"Banji dadin rashin aurenka Gent,ko still now tsoron matan kakeyi?"

Haris yayi murmushi

"Aure lokaci ne Deen, sannan idan nace ma ina tsoron matan na yanzu ai ba laifi bane."

"Magana ta fito,kacemin kawai tsoronsu kakeyi."

Murmushin dai Haris ya k'ara yi kawai,shi kadai yasan matsalarsa. Duk sadda ya tunano da tafiyarsu kazaure a gobe damuwa kadai ke dabaibaye zuciyarsa.

"Last two months ai,inajin 5th of may ne,na hadu da wani kamar KB naka a Ni'ima hotel da wata baby. Naso nayi mishi magana duk da dai ina kokwanton ko shi d'inne tunda kaga bazan kawo har yanzu KB yana yayin wasu bebs din ba tunda he's married. Kafin ma nakai wajensu sunyi gaba,na rako oganmu ne wajen wani abokinsa. Saidai yanzu kace yana ina ma?"

Haris ya kara zuciya da lamuran KB, yana kara jin kwarin gwuiwar auren Baby don ya fahimci ita kadai ce yake tarayya da ita yanzu. A zahiri ya murmusa

"Hum, bana zaton shi ka gani dai,mutumin dake zaune a Abuja ba."

Deen ya tabe baki yana mai daga kafada kadan

"Zai iya yiwuwa."

Daga nan suka share zancen,zuwan Deen shi ya mantar da Haris damuwarsa sukayita hira yana bashi labarin yanda wasu rundunarsu ke fama da matsalar boko haram,bai bar gidan ba saida sukaci girkin henry. Bayan magriba ya wuce.

*****
Abdullah kuwa,koda ya koma Abuja bai rufewa Abbansa komai dangane da halin da Tasleem ta shiga ba. Abba yayi kuka kamar me a karshe yayi nadamar watsi da rayuwar yaransa da yayi wanda sanadin hakan gashi har karuwanci diyarsa wacce ta samu kyakkyawar tarbiyya tayi. Abdullah kuma ya sanarmishi da zancen aurenta da za'ayi da Haris din kamar dai yanda Baffa ya sanarmishi kafin barinsa Kazaure. Abba yaji dadi matuka musamman jin cewar Haris din da kansa ya amince zai rufawa diyarsa asiri yana sonta ba tare da kowa ya tilasta mishi ba. Sannan kuma ya d'okantu da ganin tasleem ko don ya nemi gafararta,amma Abdullah yace mishi ya saurara dai tunda can gidan basu san komai ba. Ya hadashi a waya da baffa ya nuna amincewarsa dari bisa dari ya kuma nunawa Baffa ai tasleem ikonsa ce. Baffa yaji dadi matuka,bayan hakan ne ma ya nemi tasleem yayi maganar gareta.

Wannan kenan!!

*****
RANAR ASABAR!!!!



'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(57)
Kabir yana zaune a falonshi bayan ya kirayi wayar
Momy har zuwa lokacin babu kwakkwarar
magana ta inda Baby take. Ya damu kwarai,har
abun yana neman shafar walwalarsa. Daidai
lokacin Yasmewn ta zauna tana amsa waya cikin
dariya ta karashe maganar data soma tun kafin
shigowarta da cewa
"Aa yayana,mudai kam kada a tsawaita mana
lokaci munason shan biki da wuri."
Ta danyi shiru a nishadance tana sauraron amsar
da Haris ke bata,yayinda KB ya mike zaune yana
zuba mata ido cike da dumbin mamaki.
"Toh Allah Ya tsare hanya,agaishemana dasu
Malam."
Daganan ta katse wayar ta ajiye.
"Sorry prince,abinci saura kad'an."
"Wane yayan naki ne zaiyi aure?"
Tayi mamakin tambayarsa,bata dauka koda wasa
baisan da zancen ba kuma ganin agabansa aka
danyi maganar tafiya kazauren a kano duk da dai
ba'a fadada zancen yanda zai fahimta
"Baka da labarin sanya ranar auren Yayana
za'aje yi Kazaure?"
Ransa ya baci jin tambayt daya kalleta matsayin
rainin hankali
"Da ina da labarin zan tambayeki ne?"
Ganin ransa ya baci yasa ta sanyaya murya
domin yanzu batason batamishi ko kusa
"Kayi hakuri,ganin yanda kuke dashi shiyasa nayi
zaton bazaka rasa sanin komai ba. Ni kaina
bansan cikakken zancen ba. Amma Daddy ne ya
turashi Kazaure zab'ar matar aure cikin yan
uwanmu. Kuma yanzu ya zab'a shiyasa Malam
ya nemi ganinsu gaba daya harma dasu Daddy
din."
Kb jikinsa yayi sanyi, me ya yiwa Haris da zafi
har haka? Duk irin shakuwarsa amma ya kasa
sanar dashi labarin aurensa? Ya jinjina kai kawai
baice uffan ba.
"Hadomin Coffee."
Ta mike ta fita itama din dai ta lura yayan nata
saboda abunda KB yayi gareta ne ya kullaceshi
wanda ba halinsa bane(wato kullata).
Shi kuwa KB wayarsa ya dauka ya kira Haris
dake shirin tayarda mota zuwa gidansu Daddy
don tafiya. Kamar bazai dauka ba sai kuma ya
dauka da sallama.
Kb ya amsa yana yar fara'a kafin yace
"Wani tsastsauran laifi nayi da har dan uwana
kuma aminina ya kasa sanarmin da batun
aurensa har haka? Inda aminci kamata yayi ma
ace a bakina Princess(yasmeen) zata soma ji ba
bakinka ba. Haba Haris,abun har yakai haka?
Allah ma munayin laifi gareShi ya gafarta mana
ballantana dan adam?"
Ya karashe a sanyaye gwanin tausayi domin
hakikanin gaskiya KB yana kaunar Haris kwarai
dagaske,kauna ce mai tsafta tun suna yara suke
yiwa juna. Jin yanda ya narke murya yasa Haris
sauka daga fushinsa,shima cikin sanyin murya
yace
"Dan uwan nawa ne ya kasa saita rayuwarsa,ya
kasa fahimtar hatsarurrukan dake cikin sab'awa
Ubangiji. Banda wannan babu wani abu dake
had'ani dashi."
"Oh come on my friend,tuni na watsar da wannan
hanyar wallahi. Just ita ke wahaldani ga kuma
fama da rashin sanin inda take amma daman
banda ita komai na watsar. Ka tayani addu'a."
Murmushi Haris yayi na mugunta
"Bakomai,itama zaka mantata har abada in sha
Allah. Zan tayaka addu'a. Barni hakanan,Daddy
suna jirana."
"Toh ango,yaya sunan matar.."
Kafin ya karasa Haris ya katse kiran yana
murmushi
"Da sauran lokaci Kb,bazan amince ka rusamin
komai ba."
Daganan yayi ribas ya fita kasancewar tun
shigarsa mota isah ya wangale gate din.
*****
Rashin samun wadataccen bacci da kuma
matsanancin kukan da baby tasha a daren ya
janyo mata ciwon kai matsananci da zazzabi
wanda ya sanyata lafkewa saman darduma tun
bayan sallatar Asubahi da tayi. Gwaggo Hajara
tayi shigowa dakin wajen sau biyar amma bata
tashi na gashi har rana tayi sosai domin lokacin
wajejan karfe sha daya na rana. Ganin bata da
niyyar motsawa ne,yasa Gwaggo tashinta
"Wai lafiyarki kuwa 'yar nan? Wane irin bacci
kikeyi hakane?"
Jin muryar Gwaggo yasa baby bude ido kadan,
ganin yanayin baby yasa ta taba wuyanta
"Ikon Allah wannan bandejin kuma fa na kanki?
Jiya dankwalin kanki bai barni na lura ba,ga
jikinki da zafi ashe masassara kikeyi baki fada an
nema maki magani ba? Bari na aika kemis din
Abdulaziz a amso maki magani. Kokarta ki tashi
ki sanya ko kunu a cikin naki."
Ta karashe tana kokarin mik'ar da Tasleem
zaune,dakyar ta mike tayi azamar rike kanta
sakamakon sarawar da yakeyi.
Ta daure ta wanko bakinta ta dawo tasha kunun
kadan,saidai fa tuni cikinta ya hau murd'awa
saida ta ruga bandaki ta amayar dashi tas!
Gwaggo na mata sannu. Bayan ta kamota sun
fito take fadin
"Haba jama'a,ana kokarin yi maki gata amma
kina facali da damarki? Harisu yaron arziki ai ba
abun gudu bane."
Ita dai tasleem batace uffan ba,da gwaggo zata ji
labarinta da bata amince da aurawa namiji irin
Haris 'Yar Bariki ba. Dakyae ta iya hadiyar
magungunan ta sha ruwa sai kuma bacci ya
dauketa a saman gadon bayan ta ja bargo ta
kudundune jikinta saboda sanyin da takeji yana
damunta duk da kasancewar rana ake kwalawa.
******
"Kace ashe harisun sun iso kenan?"
Tambayar da taji Gwaggo na yiwa wanda batasan
ko wanene ba. Tashinta daga bacci kenan,ba laifi
zazzabin ya d'an sauka saidai ciwon kan.
Batasam takamaiman karfe nawa ba saida taji
muryar Baharu na fadin
"Ya iso gwaggo,shiyasa Baffa yace nazo nayi
kiranta su gaisa."
"Toh ai shikenan,bari na gani ko jikin nata yayi
sauki."
Jin gwaggo na kokarin shigowa tayi saurin
mayarda idanunta ta rufe gabanta na bugu fat
fat......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(58)
Ta taba goshinta taji sanyi radau wanda ya
tabbatar mata da saukar zazzab'in. A nutse
gwaggo ta hau bubbuga kafarta
"Tasleem,tasleem."
Ta bude ido sannu sannu kamar mai baccin
gaske.
"Na'am gwaggo."
"Sannu ko? Ya jikin naki?"
"Alhamdulillah."
"Haka nakeson ji,maza daure ki tashi,Baffa ya
aiko kiranki ku gaisa da bak'i."
Kamar zatayi kuka tace
"Banjin dadi fa gwaggo."
Gwaggo ta hau lallab'ata
"Haba d'iyata,meyasa bazaki kasance mai hakuri
a rayuwa ba? Babu amfanin bijirewa maganar
manya. Ki tashi kije ai ba auren kikaga anyi ba.
Mu dage da addu'ar zab'in Allah."
Haka tayita kashe mata jiki da maganganu,Baby
ta mike ba don taso ba.
"Toh nidai ki sanya a daukomin akwatina sai nayi
wanka."
Gwaggo tayi dariya
"Ai shikenan babu komai d'iyata ta kaina. Shiga
kiyi abinki don ma kayana bazasuyi maki ba ai da
shi zan baki."
Murmushi baby tayi kafin ta soma kwab'e kayan
jikinta.
****
Ta fito wanka sai kuma ta rasa suturar sanyawa.
Manyan kayan daman kala biyar ne. Uku
atamfa,biyu kuma shaddoji suma kyautarsu akayi
mata. A karshe dole ta dauki daya cikin shaddojin
nan ta sanya ba don taso ba. Shaddar brown
ce,tasha surfani anyi mata riga fitet hakanan skirt
din yayi d'as a jikinta saidai hakan bai boye 'yar
ramar da tayi ba. Ta sanya dankwalinta tayi
dauri wanda ya rufe bandejin kanta,ta kudurta
suna tafiya zataje kemis a fidda mata.
Kai kuzo kuga baby acikin hadaddiyar shaddar
nan. Batayi kwalliya ba kwata kwata,toh auren da
bata murna da yinsa kuma ma me zata nunawa
Haris bayan shi d'in daban ne a komai. Ta fesa
turaruka masu fisgar hankali wanda har gwaggo
dake waje saida tayi mata magana
"Kai tasleem,turaren nan kodai na maza ne? Kibar
amfani da turare mai k'arfi haka kina mace."
Batace komai ba ta maida ta ajiye,ita kam anya
zata iya daina shafa turare? Da kamar wuya don
ma'abociyar son kamshi ce. Ta zura takalminta
sai kuma ta rasa mayafi. Kawai saita janyo na
mamma da tun zuwanta take yafawa ta yafashi.
Gwaggo Hajara ta dubeta tana zabga murmushi
sadda ta fito
"Ko babu kwalliya kina da kyawunki diyata ta
kaina saidai muje na baki wani mayafi ki sanya
wannan ya tsufa da yawa."
Murmushi kawai baby tayi gabanta bai bar bugu
ba,taji kwallah ta taho mata saidai tayi azamar
maidasu. Baharu ya shigo karo na biyu yana
sallama ta amsa. Baki ya washe
"Antina wallahi kamar bake ba. Kullum k'ara kyau
kike."
Ta d'an harareshi ya kyalkyale da dariya
"Kamar kinsan kuwa surukan naki ne ya
tambayeki shine nace bari na turo masa ke."
Surukanta? Ta nanata a ranta,ita fa jikinta yana
k'ara yin sanyi. Mamaki takeyi ace wai Haris ke
sonta,haka kawai tsoronsa yayi mata dirar
mikiya. Tunaninta ya katse sa'ilin da gwaggo ta
fito rike da wani mayafi kalar ruwan madara(wato
surfanin dake jikin shaddar)
"Fiddo wannan ki yafa wannan."
"Kai gwaggo ashe kinsan kalar gayu." Cewar
Baharu. Baby dai kamar kurma ko don bata fiye
son yawan magana bane? Oho. Amma batace
musu uffan sai murmushi na dole.
Suka jera Baharu yana bata labarin yanda
surukan suka yaba da wannan auren ji sukeyi
tamkar a daura auren ma a yau.
"Wallahi anti angon nan naki burgeni yakeyi kana
ganinsa kaga dan boko kuma wayayye amma ko
kusa bashi da wulakanci ko girman kai. Kunyi
bala'in dacewa dashi wallahi."
Ta dubi Baharu zatayi magana ta fasa
sakamakon ido hudu da sukayi da Haris ya fito
yana amsa waya. Sanye da manyan kaya amma
babu babbar riga, kansa sanye da hula. Sai taga
yayi mata kyau da kwarjini sosai,shi kansa
Baharu saida yaga yayi mishi kwarjinin. Ya daure
fuska yana mai kauda kansa yana mai juya musu
baya ya cigaba da wayarsa da alama dai da
kanwarsa yakeyi. Ta sunkuyar da kanta yayinda
kwallah suka cika mata idanuwa. Daman tasan
ba sonta yakeyi ba. Har suka is a daf dashi bai
bar wayar ba hakan yasa tayi cikin gidan,zata
karasa can wajensu inna,Baharu ya dakatar da ita
da cewa
"Ki soma shiga suna nan d'akin fa anti."
Ta gyada kai kawai,gabanta na faduwa tayi
sallama. Dukkansu suka amsa kafin ta shiga
kanta yana k'asa. Su kuwa su Abba ganin
surukar tasu nan da nan fara'arsu ta k'aru bare
ma Malam Hussein wanda yaji tamkar diyarsa ce.
Ta gaishesu a ladabce,suka amsa kafin ta
tambayesu hanya. A karshe Malam Hussein ya
kara jin ta bakinta sannan yazo mata da batun
cewar ba ita kadai Harisu zai aura ba(kamar
yanda suka zauna sukayi zancen da yaransa
abba da daddy da hajja kubra,Haris ya amince da
hakan ga mamakinsu. Itama Zahra tayi na'am
tana mai farinciki saboda son da takeyiwa Haris
mai girma ne.),hankalinta ya tashi jin wannan
zancen. Saidai ta daure tunawa da nasihar
gwaggo tace ta amince da bakinta. A karshe suka
sanya mata albarka ta mike ta fito kanta na
k'asa suna zubar hawaye. Jikinta kuwa rawa
yakeyi gabanta na dukan tara tara sakamakon
tunanin daya darsu a zuciyarta na cewar lallai
d'osanawa Haris ita akayi,daman Zahra yakeso.
Tana kokarin sanya takalminta amma jikinta rawa
yakeyi,ta dunguro zata fad'i tayi azamar kai
hannu da niyyar dafe bango saidai taji ta dafa
hannun mutum. Da sauri ta dago idanunta ya
sauka akan kyakkyawar fuskarsa,taja baya bayan
ta sakeshi.
"Sorry." Ta furta murya na rawa,ya matso saitin
kunnenta ya soma magana
"Kina tsammanin sonki yasa na amince zan
aureki ne Tasleem? No! Lik'amin ke akayi,ni
kuma babu yanda na iya na kaucewa maganar
magabatana. Zahra itace zab'ina! Abar kaunata!
Zan aureki bisa kaddara kawai!"
Ta juyo da sauri, ganin numfashinsu na gogar
juna tayi azamar ja da baya tana kallon
fuskarsa,murmushin mugunta kawai yakeyi mata
a zahirin gaskiya kuwa daurewa kawai yayi domin
cin zarafin dan adam baya daga d'abi'arsa. Ya
daga mata gira yana murmushi
"Idan kinga zaki iya,muje zuwa toh..."
Daga haka ya wuceta ya fita ya fasa shiga dakin
ma. Kawai tayi ciki a guje takalmin da bata
sanyaba kenan...!!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(60)

Takai mintuna biyar kafin ta kammala saidai kuma jin yanda hayaniya da shewar murna ta cika dakin inna ya hana Tasleem fitowa yayin data kifa goshinta jikin kofar bandakin tana rusar kuka. Ta tabbata an daura aurenta da Haris akan sadaki dubu hamsin. Shikenan Haris ya samu damar wulakantata da cin zarafinta. Yan uwanta sun kasa fahimtar Haris ba kaunarta yakeyi ba. Ta bandakin tana jiyo muryar Baharu yana labarta musu cewar ai Haris ne ya nemi a daura auren a yanzu,Abba(alhaji Aliyu,mahaifinsa) yana fadan wane irin gaggawa ne haka? Liman yace hakan shine daidai tunda gashi an hadu domin har mijin Mamma,Dad yana wajen wanda shine ya zama wakilin tasleem aka daura auren kawai. Zahra ma an daura saidai an bar tarewar sai nan da wata daya bayan an kammala shirye shirye. Nan dakin ya dauki kabbara cike da sowar farin cikin jin wannan labari. Tana jin sadda d'iyar Dada(dada matar kanin Liman daya rasu take zaune gidan) wacce take zawarci sakamakon mijinta daya rasu da jimawa,wato Hafsa ta tahowa tana buga kofar tana fadin
"Fito kin kunshe kanki a bandaki,komin abunki fa sai mun murjeki da lalle." Aka kwashe da dariya kafin dai kowa ya tattara ya fice. Saida taji shiru sannan ta fito,

Please Login or Register in order to submit comment