Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinsu sai a hankali,don uwar tasu cikin yawon biki da suna da gaisuwar mutuwa take. Koyaushe bata fiye zama gida ba duk fitarta da yaranta take tafiya(note! Ban taba rayuwar kowa ba!). Wannan ya janyo wala wala a karatunsu na addini,malaman har korafi sukeyi don har Abba sun samu sunyi magana dashi ya nuna za'a kiyaye saidai fa bata canza zani ba.

Wataranar juma'a da yamma na dawo daga gidan Waziri inda nakai ziyara ga aminiyata Juwairiyya,misalin karfe biyar da mintuna ne,direba ya faka. Na fito ina duban wasu matasa biyu tare da Hamza anan kusa da motar Hamza suna hira da kyakyata dariya. D'aya gajere ne,bak'i saidai kalar fatar ta haskaku tamkar dai na yan gidan hutu. Bashi da wani kyau na azo a gani yayinda d'ayan kuwa ya kasance dogo yana da d'an haske. Sannan yayi kama matuka da Raliya. Bazasu wuce talatin da wani abu ba,kansu wani dan iskan aski ne na yan duniya. Gashi duk sun matse cikin kananun kaya masu wanduna iyaka gwuiwa. Na dauke kaina kamar ban gansu ba zan shige gida. Tsawar da Hamza ya dakamin ce ta rud'a tunanina,na dubeshi. Jajayen idanunsa ya shiga zaremin,yace naje. Ba musu ta isa jiki yana rawa.

"Don ubanki baki iya gaisar da mutane ba? Ko bakiga Nura da Usman bane? Kina daukarsu bare ne? Toh don ubanki sun fiki matsayi a gidan nan."

Jin abunda yace na zumburo baki,a ganina rainin hankali ne ace wani can ya fika alhalin gidan ubanka ne. Naji an kaimin hauri da k'afa a bakin. Nura ne,gajeran ciki. Ya zaromin ido

"Barta Yaya hamza,ashe har wannan lokacin wannan yar iskar yarinyar bata nutsu ba. Tun tana 'yar ficikarta take tsula tsiya a gidan nan. Toh don ubanki tunda muka dawo garin nan keda gyatumar taki zaku magantu. Tashi kibar nan!"

Ya dakamin tsawa,ai da gudu gudu nayi ciki cikin ihun kuka. A falo na zube inata bori,Kulu da Mamma suka fito suna tambayar ko lafiya? Yaya abdullah kuwa bai nan yana tare da abokansa na unguwa suna ball. Na shaida musu abunda ya faru,Mamma taja tsaki

"Allah Ya kyauta."
Daga haka tayi gaba bata ko damu da wankemin jinin dake d'iga daga bakina ba. Kulu ta kamani mukayi bandakina ta wankemin bakin tsaf sannan ta sanyani na chanja kayan kasancewar sun b'aci da jini.

Result din Nura da Usman ba wani kyau sukayi ba,tun dawowarsu ma banda yawo da suka sanya a gaba basu da wani aiki. Ga yan mata da suke yiwa b'arin naira. Bayan bautar kasarsu Raliya ta sanya Abba ya nema musu aikin yi saidai babu wanda akayi dacen samarwa. A karshe tace ya basu jari. Nan ya basu kudade da yawa don suyi sana'a koda kasuwanci ne. Saidai ba wanda ya yunk'ura,karshe ma mota suka saya kowanne da tasa. Rayuwarsu ta baya sai abunda ya k'aru,neman mata kamar me don hatta da shaye shaye sukan d'an tab'a. Mamma tasha gargad'ina akan kar na kuskura koda wasa na dunga shiga sashensu. Baruwana dasu, naji gargadinta sosai duk da inajin haushinsu. A duniya babu wadanda na tsana bayan Abba sai su. Tsakanin Mamma da Abba kuwa,har ta manta rabon da Abba ya zauna sukayi hirarsu cikin nishadi har ma ya nemi shawararta akan wani aiki nasa, ko kuma ya sanar da ita abunda yake niyyar yi ko kuma yayi. Zuwa lokacin ma Mamma bata damuwa,idan da sabo yaci ace ta saba domin kuwa abun gaba yakeyi. Na takaice maka saida ya zamana Abba ko girkin Mamma bayaci,sam Mamma bata da kwana a gidan. Kiyayyarsa gareta tamkar an k'ara ne. Domin hana kawo abinci sashensa yayi,yace tayi zamanta a nata sashen idan yana da bukata ai yasan inda take amma anan ita ya lura bata da aiki sai korafi akan abunda baikai ya kawo ba. Tun ina zuwa sashen Abba da kaina duk da kwab'ar Mamma har nazo na daina domin ko kallo ban isheshi ba. Zafi ya hadewa Mamma,gashi ita ba suruka ba balle takai k'ara don tun Abba yan karami mahaifiyarsa ta rasu. Shi kadai ne a wajen mahaifiyarsa,a hannun mahaifiyar Alhaji Nasir,uwargida a wajen marigayi Waziri Ma'aruf wato mahaifinsu Abba,ya tashi. Itace komai nasa kafin itama ciwon sugar yayi ajalinta. Mahaifiyar Gwaggo sarai ita kadaice tsohuwar data rage a matan Waziri,sai yaransa su goma sha biyar cif. 'Ya'ya goman duk na uwargidan ne,sai Abba cikon na sha daya sannan ya yan amaryar waziri,uwar Gwaggo sarai,itace mai yara hudu.

Kwarai dukkansu matan sun watsar da Mamma,hatta da Gwaggo Sarai mai kawo mata tsegumin auren da Abba zaiyi a farko. Matar Waziri mai ci a yanzu,Alhaji Nasir,Hajiya Hajara. Itace suke mutunci sosai da Mamma don shekarunta bai wuce na Mamma ba. Itace kuma k'arama ta uku a matansa. Ita ta kasance mahaifiyar Juwairiyya.

Wannan kenan!!!

Mamma ta rame ta rasa meke mata dadi,Abdullah shine mai rarrashinta. Akwai sadda naji yana bata shawarar kodai zataje Kazaure ta sanarwa Malam? Don lokacin bai zama limamin juma'a ba,marigayi Malam Abubakar ne Limamin. Mamma tak'i. Yaya abdullah shine abokin shawararta wasu lokutan yanda ta suka shak'u ko ni da nake mace ba muyi wannan shak'uwar ba.

Rayuwa na tafiya da dadi babu dadi. Saida muka samu hutun watanni uku na makarantar boko,ina shirin shiga jss2 Yaya abdullah kuwa zai shiga Ss2,mukaje Kazaure ziyaran kakannina. Yan uwan mamma babu wanda bai firgita da ganin yanda ta koma ba. Sukayita tambaya tana cewa babu komai. Har Malam ma haka ta fada mishi. A karshe ta sanyamu a d'aki ni da abdullah ta k'ara kwab'armu akan kada mu sake mu gayamusu halin da take ciki. Ai kuwa bayan ta fita ziyarar yar uwarta. Naje na samu Malam,ina kuka na zayyane mishi komai na yanda Mamma ke rayuwa a gidan nan don har yan aikin Raliya sun fita muhimmanci a wajen Abba. Ga rashin kunya da yaran Raliya sukeyi mata,babu mai ganin girmanta musamman ma manyan. Malam ya fusata ainun,yace nabar kukan bari ta dawo. Ai kuwa Mamma tana dawowa nabar gidan da zummar lekawa gidan kanwar Mamma,Gwaggo Nusaiba......


'YAR BARIKI

©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(30)

"Maganar da nakeyi maka har ila yau,bansan takamaiman silar rabuwar iyayena. Abunda zan iya tunawa shine. Adaidai wannan lokacin da sakin ke daf da faruwa,Mamma ta shiga wani irin yanayi na yawan tunani da kuka. Nasha kamata a daki tana kuka,tambayar duniya nayi mata tak'i sanar dani. Ga Abba ma bai shiga sha'aninta,na fahimci ran girkinta saidai tayi mishi abinci takai ta juyo bata zuwa inda yake. Ta rame gaba daya, zuwa lokacin nayi hankali nasan menene ya kamata hakan yasa ban sanarwa Yaya abdullah ba duk kuwa da cewa muna yawan chatting dashi yayita bani labarin wata budurwarsa da yake fatan aurarta,Hidaya. Itama 'yar Kano ce karatu ya kaita London. Na gaji da ganin halin da Mamma ke ciki wannan yasa na tambayi kulu ko tana da masaniya saidai ta tabbatar min babu abunda Mamma ta gayamata,itama ta tambayeta amma ta nuna mata bakomai.

Wataranar alhamis na dawo daga makaranta ina mai murnar kammala paper dina na jarabawar karshe da mukeyi. Karab mukayi ido hudu da Yaya Usman tsaye a bakin motarsa sanye da kananun kaya tana shirin fita. Naja tsaki ganin yanda yake sakar mini murmushi,a fili nayi magana

"An girma ba'asan an girma ba."

"Tasleem."

Sunana daya kira yasa na tsaya don kuwa bai taba ambaton sunana ba saidai yace "ke."

"Zo nan."

Na nufi inda yake cikin tsabar takaici domin a rayuwa na tsani 'ya'yan Raliya gaba dayansu musamman ma wadannan agololin da suke mana karfin hali a gidan uba. Na isa na tsaya kerere gami da hard'e hannuwana a kirji fuska ba walwala don a yanzu sam bana tsoron ta kwab'e mana dasu. Inajin zan iya karawa da duk shegen da zai hanani taka rawata da tsalle a gidan mahaifina.

"Gani."

Na dauka zanji babu dadi sai ga mamakina cikin maganarsa mai sauri yace

"Inye,au yanzu an daina ganin girmana ko? Ba laifinki bane,kin isa ne don a yanzu kin zama biggurl."

Furucinsa yasa na dubeshi,ya dagamin gira hakora a washe, na tsuke baki gabana yana faduwa nadai daure nace

"Ina sauri ne,nagaji."

"Kada ki damu,nima saurin nakeyi zan fita. Tambayar da zanyi maki daman meyasa bakya shiga sashena? Kodai baki daukeni yayanki ba? Kin daukeni bare?"

Na kauda kaina don a zahiri ban fiyeson kallo ba. Banayi banso kuma a tsawaita yimin,saidai yanda na kula Usman mayen kallo ne. Muddin waje da mata baya saurarawa,yan matan dake gidan Waziri nasha jinsu suna korafin yawan kallonsa da son kulasu da yakeyi acewarsu haushin zuwansa sukeji saidai kuma abokin yayansu ne,Bukhari ba yanda zasuyi.

"Daman ai ba wani zumuncin mukeyi a tsakaninmu ba ballantana har na dunga ziyartar gidajenku. Babu laifi idan mun hadu sai adunga gaisawa."

Yayi mamakin maganata,har yayi dariya. Nikam wani lokacin ma mamaki yake bani,mutum mai zuciya da ashariya shine yake bina har haka?

"Gaskiyane Tasleem,komai ya wuce. Ke dince akwai rashin kunya sadda kina da kuruciya,amma yanzu tunda kin nutsu ai shikenan."

Na d'an tabe baki kafin naja kafata nayi gaba

"Ban sallameki bafa."

Ko kallonsa ban k'arayi ba domin na tsani rainin hankali. Ya tsayar dani da surutan banza. Da sallama na shiga saidai babu kowa a falon,na karasa dakin Mamma,kafin nakai na tsaya cak saboda maganar Mamma da naji cikin kuka.

"Kulu don Allah ki rikemin sirrina,nayi iyakar kokarin ganin na gyara zamantakewata da Abban Abdullah,saidai tamkar tunzurashi nakeyi. Bansan takamaiman abunda nayi mishi ba ya tsaneni. Kada ki sanarwa Tasleem komai dangane da abunda na fadamaki. Ayau zan koma garinmu,na bar maki amanar yarana Kulu. Bada son raina ba na rabu dasu. Haka Allah Ya kaddaro zamana da Abbansu bazaije ko'ina ba. Bari na tafi domin banason Tasleem ta iskeni....."

Shigar da nayi ba a hayyaci bane yasa sukayi turus gaba daya. Mamma ce rike da akwatin kaya sai jakar hannu,sanye cikin hijabi fuskarta tayi jazur ga hawayen da take fitarwa daya yana bin wani. A durkushe kuma Kulu ce ke kuka sosai.

Tsananin tashin hankali yasa naji kafafuwana sun kasa rikeni,kawai sai na zube a k'asa kafin nasa tafukan hannuwana na rufe idanuna ina kuka sosai. Mamma ta karaso ta ja hannuna na fisge naja baya ina kuka

"Ki rabu dani nace! Ba kin riga kin shirya guduwa ki barmu a wannan bak'in gidan ba? Kin shirya barinmu wajen azzalumin uban.."

Ta toshemin bakina da sauri

"Kina da hankali kuwa? Kada ki k'ara zaginsa,kada ki kara zagarmin...."

Na fisge hannunta

"Wa?! Waye naki? Mamma ki farka ya rigaya ya sakeki! Baya kaunarmu tunda bayason mahaifiyarmu. Shekaru nawa yana nunamana kiyayya? Babu wata shakuwa tsakaninmu dashi a matsayinsa na ubanmu,tunda nake da wayona ban taba ganin Abba ya tako zuwa sashenki domin duba lafiyarki daga kowace irin cuta data sameki ba! Mamma wallahi bazaki tafi ki barni ba! Nima bana sonsa bana kaunarsa! I hate me so..."

Marin data sakarmin ya dakatar dani, saidai ban fasa fad'i ba na mike naja baya ina kuka da karfin murya nace

"Saidai ki kasheni Mamma! Amma na tsani Abba! Na tsani Raliya! Har abada bazan taba son makiyin uwata ba kowanene!"

Na fice a guje,kayana na soma hadawa a akwati,kulu ta shigo ta sameni. Duk yanda taso ta hanani amma nak'i hanuwa. Na fito saidai Mamma tuni ta fice. Banyi wata wata ba nima na mara mata baya. Kulu na bina tana kwalamin kira saidai ko waigowa banyi ba.

*****
Ga wanda baisani ba,sai yace tare muka isa Kazaure da Mamma domin shigarta da mintuna nima na shigo. Malam na soma cin karo dashi yayi niyyar tafiya masallaci gabatar da sallar la'asar.

"A'a,matata daman tare kuke?"

Kawai saina sanya kuka,wannan ya fiddo mutan gidan. Ba karamin mamaki nagani akan fuskar Mamma ba,saidai batace komai ba ta juya ta koma ciki. Malam ya rikeni
"Lafiya kuwa? Meke faruwa ne?"

Cikin kuka na sanar dashi sakin da Abba ya yiwa Mamma. Matan suka hau salallami,Malam banda innalillahi wa inna ilaihir raaji'un babu abunda yake maimaitawa. Kafin ya numfasa yace

"Shiga kiyi sallah Tasleem,bari har na dawo daga masallaci."

Daga haka naja akwatina,ban yarda na shiga dakinsu Mamma ba,sai nayi zamana dakin Gwaggo Fatsima,matar kanin Malam, Yunus. A zatona Mamma zata shigo ta rufeni da duka,wanda na riga na kudurta a raina ko kasheni zatayi bazan koma ba saidai ko alamunta banji ba.

Malam sai bayan isha'i ya nemi Mamma. Sun jima suna magana kafin yayi kirana. Nan ya lallabani akan nayi hakuri na koma ga mahaifina na tubure mishi karshe na sanya kuka ina fadin sun tsaneni suma. Jin haka Malam yace Mamma ta barni na zauna. Mamma zatayi magana ya hanata yace na tashi na tafi. Bansan me suka tattauna ba,nidai burina ya cika tunda Mamma bata kara matsamin ba akan batun kome na daga ranar.....
'YAR BARIKI

©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(31)

Kwana uku da zuwana Kazaure,Mamma ta sakarmini sosai. Inajin dadin kauyen nan domin duk sadda naje kowa haba haba yakeyi dani. Sau da yawa Malam ya kanyi murmushi idan yaga nayi wani abun musamman yanayin maganata da yasha fadamin yana bashi mamaki,yakan ce ni nayi gadon waziri kakana bawai Abbana ba. Bashi kadai bama,hatta kawayena da wasu cikin yan uwana sunsha gayamin na fiye jin kaina da kasaita,wanda ya jima tare dani ne zai gane nature na ne haka bawai girman kai ko wulakanci bane kamar yanda wasu ke dauka suke kuma jin haushina.

Saida na cika sati daya cif a kazaure sannan saiga direbanmu. Nayi mamakin zuwansa,yayi sallama da Malam ya gayamishi cewar Abba ne yace yazo ya tafi dani. Malam ransa bai baci ba domin zuwa yanzu ya dawo daga rakiyar Abba. Ya lura abun nashi sai addu'a. Ya shigo yace na shirya na tafi. Ai kuwa na fasa ihun kuka,yayita ban baki shi da inna,kafin Mamma ta hadamin jakata ta jawoni daki tana rarrashi.

"Na sanki,yarinya kike mai basira da kula dakai. Kada ki sake ki bari shaidan yayi maki hud'uba Tasleem. Kibi matar ubanki sau da k'afa,kiyi biyayya ga mahaifinki kada ki sanya damuwar komai a ranki. Allah Yana tare dake."

Wadannan shine kalaman karshe da Mamma ta gayamin,wanda bani taba mancewa. Haka na share hawayena mukayi sallama da kowa nabi direbanmu muka tafi raina cike da bakin cikin komawa gidan mutumin dana fi tsana a rayuwata.

Babban tashin hankali dana tarar bai wuce ganin babu komai na Mamma a sashenta ba. Toh wai yaushe akayi kwasar kayanta ina Kazauren amma bansamu labari ba. Hankalina ya tashi,babu komai sai ragowar kayana dana Yaya abdullah a kwabobinmu. Na hau kwalawa kulu kira saidai tsit,na fito na tambayi Direba ina kulu. Kafin ya bani amsa sai ga Abba.

"Ta koma kauyensu ai."

Cewar direba,nikuwa kallon Abba nakeyi cike da tsanarsa. Ya kalleni fuskarsa a daure,kafin yace

"Ki sameni a falona."

Daga haka ya wuce,kamar bazanje ba sai kuma na nufi falon saboda tunano nasihar da Mamma tayimin. Yana zaune,daga shi sai matarsa dake b'antalar tuffa a nishadance tana ci. Na durkusa gefe bance uffan ba.

"Ke." (Sai ince da wayona shine sunan da Abba ke kirana kamar bai yankamin rago da Tasleem ba.)

Banko dubeshi ba saboda gudun kada kallon da zan mishi ya zamana na samun zunubi don kallone na tsana.

"Ki tattaro kayanki ki dawo sashen maminki da zama. Bazai yiwu abarki ke d'aya ba kuma kina mace a wancan bangaren. Don haka kizo ku hadu da yanuwanki don bana shakka akan kyakkyawar tarbiyya irinta Hajiya Raliya. Na tabbatar bazanyi kaico ba."

Raliya tasa dariya,wallahi Haris bansan sadda na jefeta da mugun kallo ba,banyi aune ba ta jefomin ragowar tuffan da take ci tana zaromin idonta masu razana matsoraci.

"Yar iskar yarinya ni sa'ar kice da kikeyimin wannan kallon?"

Abba ya dubeta da mamaki,sai naga ta bagarar tana murmushi

"Bakaga hararar da tayimin bane? Lallai sai nayi da gaske wajen gyarawa Tasleem tarbiyya domin na kula tayi nisan da batajin kira a gurbataccen tarbiyyar da uwarta ta bata."

Zuciya ta kaini bango,me suke nufi? Kenan suna tantamar tarbiyyar da Mamma tayimin? Muryar Abba ta katseni

"Tashi kije kiyi abunda nace. Hajiya Raliya bana shakkarki,na gaskata cewar zaki rike amanar dana damk'a maki. Zaki kula da.."

"Wai Doctor ya kake wasu maganganu ne? Yarinyar nan fa ba 'yar gwal bace. Haihuwata nawa,yara nawa kuma na raina? Yanzu ya kake zargin bazan iya kula da 'yar tsakon 'diyarka ba?"

Abba yayi murmushi,kafin naji me zaice nayi wuf na mike na fita saboda nagaji da ganinsu. Ji nakeyi da ace kisa halal ne ni zan zama ajalinsu."

Haris ya katseta cike da mamaki

"Wace irin tsana kika yiwa mahaifinki haka ke kuwa?"

Baby tayi murmushin takaici

"Bazai misaltu ba Haris."

"Bazai misaltu ba?!"

Ya nanata a ransa,baby ta share zancen ta cigaba

"Na dawo sashen Raliya,dakinsu Hamidah. Saidai na gwammace inama ban dawo Kano ba. Aikin sashenta tsaf ni nakeyi,ta sallami 'yar aikinta daya,dayar kuwa tace iyakarta kicin da baranda. Amma komai ni nakeyi. Bana k'in yi mata aiki,saidai idan ina aikin kallo daya zakayimin ka gane rashin sabo. Nan da nan nake gajiya. Abun kona ran bai wuce tarewar dasu Nura da Usman da kuma matansu,Bilkisu da Meena sukeyi ba. Kodayaushe suna nan suna kallo da hira tare dasu Hamida da Raliya tamkar zasu fasa falon. Ni ce zanyita zirga zirgar kaiwa da komowa wajen kawo musu abinci da abin sha. Bilkisu ce mai yaro daya,Junaid. Ya zamana ni na zama yar raino matukar tana sashen. Cire mishi pampers,goyashi,bashi ceralac da sauran ayyuka masu cimin rai. Ga wannan shegen kallon dana tsana a wajen Usman,duk sadda muka hada ido sai ya hau yimin murmushi yana kashemin ido,harararsa nakeyi alokacin saidai wai an tsikari kakkausa ko a jikinsa. Hindatu kadai ke tausayamin.

Bana kwanciya bacci saina kammala ayyukana. Abu daya naki yarda da gyarawa,dakin kwananmu,rantsuwa na yiwa Raliya a gabanta akan cewar bazan gyara ba tunda nikam shimfidata,Kafet ne. Sune masu kwanan gadon,bandaki kuma duk sadda zanyi amfani dashi zan gyara idan ta kama. Zata mareni naja baya nace wallahi ta mareni saina gayawa Abba. Nasan ba tsorata tayi ba,saidai bansan dalilinta nayin kwafa ta fice ta kyaleni ba. Hamida tayi wuf ta taso zatamin fitsara,ta juyo ta daka mata tsawa. Wai ita saita mareni din taga abunda zanyi,ganin uwarta ta hanata nayi murmushi nace "Kinci sa'a domin wallahi sai kin gane kurenki muddin kika tab'a jikina."

Jin haka ta harzuka ta daga hannu zata mareni,Raliya ta daka mata tsawa,ni kuwa na rike hannun na murdeshi ta fasa k'ara. Raliya ta iso ta hankadani ta janye Hamida sukayi gaba. Na rasa dalilinta nak'in daukar mataki akan hakan,saidai gaba mai tsanani ta shiga tsakanina da Hamida babu maganar dake had'ani da ita.

Ranar da zamuyi Graduation kuwa,ban nemi komai daga Abba ba hakanan ban gayyaci kowa daga bangarena ba. Yaya abdullah kadai na shaidawa ta waya, duk da har lokacin baisan Mamma bata gidan ba. Ya tayani murna yace inama yana nan dashi za'ayi. Yayimin alkawarin tahomin da kyauta ta musamman idan zaizo. Murmushi kawai nayi. Sauran kudadena na hada na biya komai da makaranta ta bukata. Ranar kuwa da sassafe na shirya,Hamida sunsan da maganar saidai basu cewa kowa uffan ba,hindatu ma ta shirya cikin uniform kamar yanda dokar makarantar tace dalibanta suyi a ranar. Ta dubeni"Zaki rigamu tafiya ko Tasleem?" Murmushi nayi mata na amsa da eh. Daga haka na dauki yar karamar handbag dana zuba kayan amfanina na fito sanye da rigar T-shirt na school da jeans na gida. Mukayi arba da Raliya,ta daure fuska "Ke kuma ina zaki? Kodayake wannan ba matsalata bace bazan hanaki yawon banzanki,aikina fa? Wa zaiyimin? Kada ki sake kibar gidan nan batare da kinyisu ba." Daga haka tayi dakinta,tsaki naja bana tsoron dukanta balle na Hamza,yau ranata ce babu wanda ya isa ya hanani zuwa makaranta. Ina waige waigen neman direba naji hon,ina dubawa naga Usman zaune a motarsa yana dagomin hannu yana murmushi. "Dan iska." Na fada a fili na kauda kaina.....




'YAR BARIKI

©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(32)

Kai tsaye wajen Baba Maigadi na nufa. Na tambayeshi ko direba yazo saidai ya sanar dani cewar matarsa ke nakuda yaje kaita asibiti ba lallai ne ya dawo nan kusa ba. Bakin ciki ya turnukeni,da ace na iya mota da duk hakan bata faru ba,gashi kuma koda yazo dole ne sai na amso mishi mukulli wajen Raliya domin shaf ina manta cewar mukullayen motar gidan a hannunta yake. Daidai nan Usman ya iso acikin motarsa,baba Maigadi ya tafi don budemishi gate.

"Zaki makara fa my sister,zo ki hau na saukeki."

Kamar nace bazan hau ba,saidai tunawa da nayi Abba kansa baya gari ballantana nasa ran dakewa zuciyata na amso kudin mota yasa banyi musu ba na shiga don kuwa bani da ko ficika. Ai daman kudin ubanmu ne suke takama dashi,babu laifi don alokacin Abba dayake am shanyeshi a rubutu ya k'ara bude musu shaguna kowanne da nashi a kantin kwari suna d'an maida hankali. Na shiga gidan gaba na zauna fuska a daure. Bai damu Usman ba ko kadan,sai bayan mun soma tafiya naji yace"Ba gaisuwa ko?"

Ni wallahi mamaki ma yake bani har lokacin ganin yanda yake yimim sanyi sanyi a yanzu. Banda niyyar gaisheshi,na dauke kaina ma. Yayi dariya"Ke kam don kinsan kin hadu shiyasa kike yiwa mutane yanga Tasleem. Hakane dalilin dayasa kike wulakanta masu zuwa gidan nan da sunan sunzo zance wajenki ko?"

Na watsa mishi harara,ko a jikinsa na kauda kaina bance uffan ba.

"Tasleem kina da kyau sosai kamar mominki ko ince kinma fita. Gashi Allah Yayi maki baiwar diri ko ta ina ke macece. Dole ki dunga yiwa maza yanga."

Na dauki surutan Usman a matsayin wofi,banko kara dubansa. Har muka iso yana zazzaga shirmensa don shirme na dauki zantukansa. Na soma hango take takensa,akwai abunda yake nufi a kaina saidai ko kusa ban nuna alamar na fahimci komai ba. Muna isowa na yunkura zan bude kofar ya dakatar dani ta hanyar cewa na tsaya. Na dakata,kudi ya mikomin har dubu uku ba musu

Please Login or Register in order to submit comment