Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa babbar mujami'arsu da take a k'ofar gidan shugaba Murtu,_
Da zuwan su Ashraf ya mik'awa humrat yar tsintuwa ya kutsa kai Acikin gidan SARKI murtu haka yasamu fadar Acike Amma bacikin yanayi mai dad'iba, Gawace yagani ajiye a tsakiyar fada mayafin 'Yar tsintuwa yagani Asaman gawar tabbas ba shakka wannan mayafinta nea Nan take hankalin sa yatashi sai rabon edo yakeyi Acikin fadar kamar marar gaisuwa cikin girmamawa yaje gaban sarki ya fad'i ya kwashi gaisuwa sannan ya gaida umman HAYBA da sauran manyan da suke wurin, zaune ya hango HAYBA tana masa murmushi SBD taji dad'in ganinsa hannu shima ya daga mata baik'ara kallonta ba sbd kunyar surukan sa da yakeji, a hankali sarki yake tako yana wuce mutanen da ke tsaye acikin fadar saida yakawo wurin Ashar yatsaya ciff yadafa kafad'ar sa, bud'e bakin Yace
"Ashraf a yanzu kaine jaruminda nake ganin zai iya rik'e ragamar wannan masarauta tamu kuma haka nake ganinka tamkar d'anda na haifa Nasan bazaka bari Aci mutunci wannan masarauta tamuba, yanuna gawar da yatsa kafin yace "wannan itace gawar babban jarumin wannan masarauta a daren jiyane a kayimasa kisan gilla kuma yazama dole kanemo maccen da takeda wannan mayafi Acikin garinna,
Domin itace takasheshi....!! da sauri Ashraf ya d'ago kai Azuce yace 'Yanxu anan 'yar tsintuwa takasheshi jikinsa yad'au rawa murya k'asa yace angama ranka yadad'e
Aka dauki gawar SARKI nea a gaba Al'ummar sa nabiye dashi suka fito zuwa wurin bauta HAYBA kuwa cike da farin ciki tarungume hannun Ashraf suna tafe sai murmushi take masa Amma kaff hankalinsa baya garesa, tunanin 'YAR TSINTUWAr sa, yakeyi shifa haryanxu baiyarda cewa itace tayi wannan babban kisan ba,
A bangaren su umma da humrat sun duk'ufa wurin bautar gunkin su yar tsintuwa na rungume a hannun humrat yayinda sarki da mutanen sa suka fito mutanen garin suka kwashi ihu ana Ambatar sunan sa, Amma a lokacin ransa abace gaba daya hankalinsa baya gareshi can edonsa suka fad'a akan kyakkyawar yarinyar dake rungume a hannun *humrat* d'arrr yaji abu azuciyarsa yayinda ya kifeta da kallo a lokacin da yaga tana k'okarin fixge jikinta tana nuna mayafinda ke saman gawar tana dukan bayan humrat, Azuci yace tabbas mahaifiyar waccan yarinya itace keda wannan mayafin d'aga murya yayi yace "kuzomin da waccan matar dake d'auke da yarinya..!!
Juyowar da humrat tayi sai k'atti tagani sunnufo ta da gudu tak'ara k'akkame 'yar tsintuwa ajikinta tarutsa cikin taro tana gudu haka suma suka biyota.....da adduna a hannun su,
*Acan wurin su Ashraf HAYBA tad'auke masa hankali tajashi zuwa cikin wani k'aton holl inda babanta yake tasa bauta shikad'ai idan yatashi wurine Lafiyayye Ank'awatashi da kayan ado na sarauta tasa Aka kawo musu kayan ciye_ciye dana sanyi aciki harda barasa,*
Suna fira suna ciye ciye HAYBA tana matuk'ar sOn Ashraf sun kusan 2 hours Suna fira gabaki daya tayiwa wani narkewa ajikinsa yasa hannu ya rungume ta zuwa jikinsa hakan yasa yamanta da halinda ya baro qanwarsa dake tare da Yar tsintuwa domin yasan komai zai iya faruwa idan taga wannan mayafin Nata, dake kan wann gawar "Ohh Yar tsintuwa ta, yafad'a da sauri yature HAYBA dake kwance a jikinsa yatashi daanufi yaje inda qanwarsa caraf yaji anrike masa riga "No Ashraf ba inda zakaje waikai mei yake damun kane Na fahimci ko kad'an bakason fira dani
dafa kafad'arta yayi yace "i'm HAYBA wlh ba hakabane i'm really luv u na rak'eki kibarni natafi Akwai matsala wlh tafashe da kuka tasake masa riga tajuya tayi cikin wani d'aki dake wurin haka shima ya juya yanufi mujami'a
_mamaki ya kama ta ranta yayi matuk'ar baci wannan shine karo na2 kenan tO wlh yau nida kaina zanje inkashe wannan_ *'Yar tsintuwar* tafad'a yayinda zuciyarta take cikin zafi
Via OHWπŸ“²πŸ“š
πŸ€πŸ’πŸ€
*RAMLAT*
_Yar Tsintuwa_
πŸ€πŸ’πŸ€
*_Written BY raheem jEgaπŸ“š_*
_πŸ’RaMlaTπŸ’_
*31_36*
```Haka Ashraf yake ratsa mutane kasan cewar jama'a sunyi yawa a wurin hakan yasa yajima baikai inda yabaro qanwarsa ba, jiyaye anbangaje saura kad'an yakai kasa A fusace yataso ya daga hannu da nufin kai bugu sai k'atti ya gani d'auke da takubba a hannun su, "sukuma wad'adannan wasuke nema nea ? Yafad'a azuci k'anwarsa yagani rungume da Yar tsintuwa sai gumi take tana waige2 hakan ya tabbatar mai da cewa tabbas ita suke nema,```
_A lokacin yakira sunanta muryarsa data jiyo tawaigo da k'arfi tace *"ASHRAFF* kamar tasake da kuka kasan cewar ta galabaita wani irin k'arfi yataso masa yashiga bangaje mutane yana gudu itama a wurinta gudun takeyi haka suma k'attin basu daina bibiyanta ba, kasan cewar ba hanya d'aya sukabiba Ashraf ya rigasu kai da zuwansa ya k'arb,i 'Yar tsintuwa hannunta yayi tsaye cakk a wuri d'aya cike da tsoro tace "ya Ashraf dan Allah mugudu tanajan hannunsa tana fad'in kazo mugudu ya Ashraf yadaka mata tsawa "NO Humrat kigudu nace....))_
Ganin yadda suka tunkaro inda suke hakan yasa ta face da gudu tanufi mujami'a inda umma take tafaman sambad'a bauta kamar mai shirin kuka tadafa umma tace "umma dan Allah mubar wurinnan nifa inajin tsoro "Aa humrat abin bauta yasan damu ba abinda zaifaru umma tafad'a sai wani waige2 humrat takeyi tazo gaban umma takama hannunta tace "pls umma kizo muje gida Akwai matsala umma dan Allah kizo muje pls umma ganin haka umma tabita suka kama hanya saure kawai suke suka nufi gida,
*A wurin Ashraf kuwa yanacan yana fafatawa da yaran gidan Shugaba murtu yayinda suka sanardashi Sarki yabasu izinin suzo da wannan yarinya Amma yace ba inda zasuje da ita kawai suka haushi da fad'a sunata kawo masa sara yana kaucewa saifamar maxgarsu yake duda hakan 'yar tsintuwa narike a dayan hannunsa, sannu sannu duk saidai yaga bayansu Amma sunyimai raunuku dadama dakyarr ya iyakai kansa gida,*
Tafe suka hangoshi d'auke da ita a bayansa Amma farar rigarsa bata kalluwa SBD tayi kaca kaca da jini da gudu humrat taxo ta rungumesa tafashe da kuka umma tazare edo tafara shirin hawaye tace "d'ana mei yasameka inace basanadin wannan muguwar yarinyar akayima wannan raununkan ba, ya girgixa kai Amma umma bata yarda ba taciyo kwalar ta tace kee dan ubanki banhanaki shigowa gidanna ba? da sauri ya daga hannu ya girgixa wa umma kai sannan tasaketa mik'ewa tsaye yayi ya kalleta Afusace yace "Wacece kee?
_Sai A lokacin tatabajin Ashraf ya mata magana cikin fushi sunkuyar da kanta k'asa tayi Alokacin shine na farko da suka farajin muryarta yayinda tace_
```"sunana RAMLAT Kumani yar garin YOBE cea Amma nayi kuskure daban sanarda ku koni waye ba bana son tuna baya shiyasa bansanar daku tarihina ba, ta d'ago kai ta kalli humrat tace "zanbar muku gidan ku nima banajin dad'in ina sakaku acikin matsala Amma kobayan wasu shekara zandawo bazan iya mantawa dakuba, Hawaye sukawo shaa a edon Ashraf ya d'aga hannu zaikira ta Akan tadawo umma tace "Aa d'ana kabarta tatafi ko a yanxu batagama kisan ba, humrat tafashe da kuka "Aa umma inason Ramlat dan Allah kada kibari tatafi....!! Haka umma tacije Ramlat takama hanya tabar gidan batasan inda zata dosaba, gashi kuma agari sai faman nemanta Akey```
A ranar haka Ashraf yayini jiki sakaka humrar ma duk taji badad'i an rabata da 'yar uwarta Allah kad'ai yasan enda Ramlat take a Yanxu,_
Labari yasauka a kunnen SARKi yajima yana kai kawo a cikin fada cike da mamakin Ashraf Azuciyar sa kuma tunanine k'arara a yanxu wane irin hukunci yadace da Ashraf dagashi har k'anwarsa, Abinda yaba mutane mamaki Tunda SARKI yasamu wann lbrn baik'ara yiwa kowa magana ba, jama'a sun k'agu suji abinda zaifito daga bakin sarki, Amma shiru kakaje baima kowa mgn ba, har dare yatsala babu wani imformation,
Misalin karfe 12:45Am na dare iska sanyi yafara k'adawa Ashraf dai barci yaga gareshi Yataso ya d'auko bargon da yake rufe dashi kana yaje a bakin window yayi tsaye yana kallon farin wata dayayi fari fess yajima. a haka sannan yasa hannu zaijawo tagar kwatsam yaga mutum zaune rik'e da tufafi a hunnunsa sanyi na dukan jikinsa yana karkarwa,
Fitowa yayi danganin kowaye Abin mamaki sai *RAMLAT* yagani batamasan da zuwan sa ba, cikin mamaki yakira sunanta RAMLAT...!!
```A tsorace tadago kai ta kallesa, Cikin muryar yaranta tace "ASHRAF yace "Na'am. Me yadawo dake....?```
Via OHWπŸ“²πŸ“š
πŸ€πŸ’πŸ€
*RAMLAT*
_Yar Tsintuwa_
πŸ€πŸ’πŸ€
*_Written BY raheem jEgaπŸ“š_*
_πŸ’RaMlaTπŸ’_
*36_40*
_Jin muryar sa, da tayi ta d'ago kai a tsorace tace "ASHRAF yace "Na am ralmat mei kikeyi anan? Ya tambeta shiru tayi ba amsa jikinta sai rawa yake kasan cewar sanyin da yake' sauka a lokacin tausayinta yakamashi ya rik'a hannuta da nufin yajata sushiga cikin gida tak'ara mak'alewa ta girgixa kai tace "Aa ya Ashraf dan Allah kabarni anan idan nashiga umma zatakasheni,_
```Yace "aa ramlat bazan barki anan ba, kizomuje ciki nasan yanxu umma tayi barci, ya lallasheta harya samu tabishi har Alokacin rungume take da wasu uniform na yara a hannunta ko a ina tasamo uniform d'in Allah masani, yajata zuwa d'akinsa ya azata kan gado yad'auko bargo yarufe mata jikinta nan take barci ya saceta wani daddad'an mafarki yaziyarce ta gata tana rayuwa tare da iyayenta kamar abaya dad d'intane yake mata wasa tana dariya cikin annashuwa, katsewar mafarkin nata shiya tada ita tatashi zaune tayi shiru tana tunani mafarkin da tayi hawaye ne suka biyo baya hannu tasa tana jijjiga Ashraf Amma ina yayi nisa Acikin barcin da yake taga bayada niyar tashi tasauko Ak'asa jikinta na kaekarwa sanyi nashiga jikinta ta d'auki tufafin da tazo dasu Alokacin dai dai hasken wata yafara fitowa tabud'e k'yauren gidan tafito takama hanya batare da Ashraf ya farka ba,```
Washe gari da ya farka yanemi Ramlat ba ita ba alamar ta, Al'amarin da yad'aure masa kai kenan Shidai haka yake ganin Abin kamar mafarkine ba gsky bane, kuma baisanar da kowa ba, shiru yayi yana tunanin faruwar wann Al'amarin zuciyar sa tafara raya masa cewa ramlat Aljana cea, yana cikin haka yajiyo kukan dawa kai tafe kamar zasu shigo acikin gidan jiyayi an shuro gambun gidan 'kattine guda uku suka ratso da dawa kai Acikin gidan sukaja birki ciff agabansa, d'ai daga cikinsu yayo ta kansa yatakashi da doki πŸ‡ ya fad'i k'asa kujerar da yake zaune akanta ta kare suka sashi tsakiya sai faman dukanshi sukeyi jikinsa yayi jinajina da gudu hayaniyar da tayi yawa shiyafito da humrat tayo kansa tana kiran sunan sa, ta fad'a jikinsa ta k'ank'ameshi tana kuka suka sauko akan dawakan suka k'waceshi daga jikinta saukar lafiyayyen mari taji a fuskarta, saida tafad'i k'asa
_Umma kuwa k'arar marinda akawa humrat yafito da ita da fitowar ta edon ta suka fad'a akan Ashraf k'asa kwance tasaki plate d'inda ke hannunta tayo kanshi tafad'i k'asa tana jijjigashi tana kiran sunanshi cikin murya kuka._
*"takama kiran wayyo Allah sun kashemun da'ana Ashraf katashi karka mutu dan Allah ko sauraren ta basuyi ba, suka d'auketa da k'arfin tsiya suka dorashi Akan doki suka kama hanya darect sai gidan SARKI MURTU,*
Har alokacin humrat kwance take bakinta na fidda jini umma ma haka sai faman kuka sukeyi suna sambatu,
A tsakiyar fadar suka saukeshi a fusace sarki yaxo yad'ago kansa,ya tofa masa yawu yace "tirr da halinka wlh kuma abin bauta yana fushi dakai, da ina d'aukarka tamkar d'ana ina ganin kaine zaka maida martabar wann gidan Ashe dakai ake k'okarin kashemin jarumai, kafad'amin a ina kab'oye wannan yarinya kuma wacece ita,? sai yawun jini kawai ke fita abakinsa baisamu damar bashi Amsa ba, Sarki yace "Ashraf yazama dole na hukunta ka dai dai da abinda ka Aikata, ya dubi fadawan da sukazo dashi yace "kuje dashi ku masa dukan tsiya harsai ya fad'a muku inda yarinyar take, d'ago kai Ashraf yayi ya kalli HAYBA da take tsaye ta kauda kanta da sauri duk da raunu kanda suke jikinsa Amma ta kanne tabarshi aka tafi dashi suna fita tafashe da kuka ta fad'a jikin mahaifiyarta,
```A wurin Ramlat kuwa bayan fitarta daga gidan su, Ashraf tazo k'arkashin wata bishiya tayi kwanciyarta misalin k'arfe 7:00am tacire kayan da ke jikinta ta saka wann unifm dake hannun ta tashirya kaff takama hanya yara ragani k'ana sanye da uniform irin nata tabi sahunsa idan ka ganta baxaka banbanta ta da d'aliban makarantar ba,```
_Sunkusa isa makarantar ta hangowa wata tsohuwa rik'e da jikinta a tsaye jikan nata sai kuka yake da sauri ramlat ta kutsa cikin mutane domin uniform d'in yaronne tasace tasaka' hartaxo ta wuce tsohuwar batare da taganta ba,_
Makarantar yarace maza/mata k'anana wadanda bazasu haura sama ga shekara 10 ba, haka take rabon edo acikin makarantar batasan kowa ba, bayan angama Asembly kowa ya wuce class d'insu tsaye tayi domin batasan class d'inda zataje ba dama ita bakaratun yakawo ta ba, tunda aka fara Asembly take kallon sa, har aka gama edonta na kansa, bayan yashiga Office d'insa tabishi a baya suku suku sai cikin Office, da zuwa tayi sallama ya Amasa batare da ya dago kai ya kalleta ba, sai rubuce rubucen sa, yakeyi shiru tayi batace k'alaba saida yagama rubutunsa A fusace ya d'ago kai yace "wacece ke dazakizo office d'ina kimun shiru me kikazoyi ?
Sai Alokacin tad'ago kanta ta kalleshi sukayi edo hudu da juna damm gabansa ya fad'i yace "kee dama baki mutuba, wayakawo ki wannan makarantar ? tace "shayine wata malama tace inkawo ma gashi a cupy a tsorace yazura hannun sa zaikarb'a jiyayi ta watsamai ruwan ACID ajiki kafin yamik'e tasake zubamai ruwan Afuska ya saki ihu yasulale a k'asa gashi ba kowa a lokacin ballai akawomai agaji tana gani haka tajuya da sauri tabar Office d'in
_A bakin k'ofar fita daga office d'in dai2 da shigowar wata malama sukaci karo da juna saida ramlat ta fad'i k'asa da sauri malamar tatada ita tace "sannu ko...!! Kallonta kawai ramlat tayi tawuce tana sauri tabar makarantar,_
*Da shigar malamar Acikin office edon ta suka fad'a akan principal d'in makarantar wani irin jiri ya kamata yayinda taga fatar edonsa duk ta d'aye*
```Da gudu tabaro Office tafito tana ihu nan take sauran malamai sukayo kanta d'alibai suka firfito da kowa ya fahimci abinda ke faruwa yara sai guduwa suke sunayi gida Ramlat kuwa tuni tajima dayin nisa mota tagani anyi parking ga Alamu pasinger ake jira da zuwa tafad'a Aciki ta samu kujera tazauna kowa sai kallonta yakeyi hakan yatayar mata da hankali jikinta ya d'au rawa sai wani rabon edo take tana kallon mutane.....))```
πŸ€πŸ’πŸ€
*RAMLAT*
_Yar Tsintuwa_
πŸ€πŸ’πŸ€
*_Written BY raheem jEgaπŸ“š_*
_πŸ’RaMlaTπŸ’_
*41_46*
_Zaune take cikin motar Amma har Alokacin hankalinta ba kwance yake ba, gane take kamar yanxu kamata za'ayi kallo d'aya zakai mata kagane Alamun marar gsky ce, wata matace dake kusa da ita ta fahimci halinda take ciki ramlat ta k'urawa matar edo duk lokacnda matar tajuyo sai ramlat ta kauda kanta da sauri haka suka sukewa junansu kallon tuhuma, har motar tacika driver yatada motar suka wuce_
A can makarantar kuwa komai yarikice d'alibai sai firfitowa suke sunayi gida, Al'amarinda yad'aurewa malaman makarantr kai kenan wayayi wann mummunan kisa? Itace tambayr da sukewa junansu, malamr cea talabar ta musu abinda duk yafaru a tun dga farkon had'uwarta da ramlat a lokacin da zatashiga office d'in yanayinda taga yarinyar a lokacn tabbas bana masu gsky bane, wasa_wasa Al'amari yayi nisa Labari ya watsu agari har a gidan SARKI,
Afusace yanufi wani kangon wuri inda aka ajiye Ashraf d'aure yake ajikin kujera yana cikin mummunan yanayi kasan cewar dukan da yasha kujera aka azawa SARKI yazauna suna fuskantr juna shida Ashraf, hannu yasa yad'ago kansa shiru yayi yana masa wani kallo cike da gadara jiyake kamar yasa hannu ya shak'esa, murya k'asa yace "ASHRAF me yasa kazab'i mutuwar ka Akan rayuwar ka? Wannan yarinyar wacece ita....? Kuma me yasa take kashe mana mutane? Sarki yafad'a afusace Amma shiru kakeji babu amsa abakin Ashraf,
_"Dakyau Nasan kobaka bani amsaba tozaka bada Amsa don wannan yanuna ta da yatsa, koda Ashraf ya d'ago kai wazai gani ((k'anwarsa humrat)) a daure cikin wani yanayi ana tunkud'ar k'eyarta da k'arfi aka turota tafad'i agabansa, da sauri Ashraf yace "Aa dan Allah kada mutab'amin k'anwata na yarda zangaya muku wacece_ ```"YAR TSINTUWA```
```Nan take ya kwashe lbrn ta kaff yagaya musu dga k'arshe yace "Kai babana ne kuma dole in sanarda kai bayaranka kad'aiba kaima nan zuwa Lokaci kad'an RAMLAT nanan zuwa kanka domin nasan bazata barka, inace kanada masaniya akan Alh Hamshi kuma kana d'ai dga cikin wadanda suka bada goyon bayan Akasheshi..))
Shiru Sarki yayi zuwa wani lokaci sannan yamik'e tsaye ya kalli fadawan sa, yace "kuci gaba da azab tardashi harsai yafad'a muku inda yarinyar take, humrat tafashe da kuka tafad'a jikin yayanta daky'ar suka cirota ajikinsa tan kuka tana fizge2 suka wuce da ita tana kallo ana dukansa da manyan itace_
*YOBE STATE*
```Bayan motar ta saukesu suka firfito kowa yad'au kayansa yak'ara gaba itama matar taje agefen titi tana jiran mai napep "Sannun ki Aunty da sauri tajuyo jin muryar da tayi. murmushi tayi kafin tace "wacece kee? Ramlat tace "d'iyar kice..!! Matar tace "uhm bakiyi k'aryaba yarinya domn na haifeki, Amma wacece ke?```
Ramlat tace idn nafadamiki bazaki kasheni ba,? Dariya tayi kafin tace "banda abinki wace uwa zata kashe 'yarta akan tabata lbr, wani shu'umin murmushi ramlat tayi kafin tace "Ni marainiya ce bnda kowa a yanxu saike nabiyo kine aunty sbd bnsan inda zanje ba, dn Allah kada kicutar dani namiki alqawarin idan mukaje gd zakiyi matuk'ar mamaki idan kikaji lbr na, shiru tayi tana kallon bakin ramlat "anya kuwa wann yarinya itace da kanta take wann mgrn ? tafad'a azuci kafin tace "Ohk zomuje gida "Amma ya sunanki tabata amsa "sunana Ramlat aunty hannun ta tarik'a suka tare napep darect sai unguwar sabon gari,
πŸ€πŸ’πŸ€
*RAMLAT*
_Yar Tsintuwa_
πŸ€πŸ’πŸ€
*_Written BY S.raheem jEgaπŸ“š_*
_πŸ’RaMlaTπŸ’_
*46_50*
```HAPPY JUMU'AT
MUBARAK```
*I'm sorry my fans 2 dayx da kukajini shiru bisa wasu dalilai dasuka tsaidani bt yanxu in shaa Allah i'm Okayy zakujini Akoda yaushe thanks u all fans))*
πŸ‘‡πŸ»
_Da zuwan su gida matar tad'auko abinci da ruwa taba ramlat, dama yunwa takeji saida taci mai isarta tasha ruwa ta wanke hannu matar tace_
```"to ramlat kinga wann gidan duk nawane kuma nikad'ai nake a ciki nagadi gidan ne a wurin mahaifina da yarasu shekara 1 data gabata, mu biyu ne a wurin mahaifinmu dagani sai yaya umar wanda ankashe shine sanadiyar ceton Abban mu dayajeyi a lokacinda 'yan adawa suka kawo masa farmaki don kawai suna son su mallaki wani babban filinsa, dake cikin k'auyen gurma.```
_Sunkashe min Abbana da yaya umar mahaifiyata kuma tarasu ne sanadiyar hawan jinin da takamu dashi bayan mutuwar Abbana wannan dalilin ne yasa nace bazanyi aure ba, harsai nad'auki fansa akan wad'anda suka kashemin iyaye,_
Sai gashi cikin ikon Allah ansamu wata k'ankanuwar yarinya takashe Wasu azzalumai 2 acikin k'auyen gurma wad'anda suna d'aya dga cikin wad'anda nake burin d'aukar fansa akansu dga k'arshe matar tace Sunana *SHU'UMA* wanna Shine kad'an dga cikin lbr na,
Guntu hawaye suka zubowa Ramlat tayi ajiyar zuciya tace "Aunty idan nace miki nice wadda nakashe wad'annan mutanen 2 zakiyarda kuwa?
Matar tad'an batse fuska tace "bangane ba, ramlat me kike nufu?
Ramlat tace "aunty shu'uma ina nufin nice wadda nakashe mutanen da kike magana acikin k'auyen gurma, wani irin kallo mai d'auke da mamaki shu'uma tayi mata tace
"Ramlat waike wacece kuma mei yasa kika kashesu, menene Labarin ki? duk a lokaci guda tajero mata wad'annan tambayoyi..!! Ramlat tasake da hawaye tace
```"Aunty nima wad'annan mutane sune suka kashe iyayena akan mahaifina yak'i basu goyon bayan su cinye wani filin marayu dake cikin k'auyen gurma wanda hakan ne yasa sukayi meeting dga k'arshe suka yanke shawarar kawarda shi, bazan tab'a manta wann ranar ba ranarda suka k'ona iyayena Acikin mota ranarda zamuje wurinda najima ina mararin zuwa arayuwata da hakan nasha alwashin duk lokacinda nagirma saina d'auki fansa akan cutarda iyayena da sukayi....wannan shine kad'an dga lbr na,```
_Ajiyar zuciya shu'uma tayi tace "Lallai ramlat yazama dole agareni natayaki d'aukar fansa domin mahaifinki yarasa rayuwar sane akan k'wato mana hakk'in mu da yajeyi wannan filin dakike magana tabbas filinmu nea da mahaifin mu yabari wanda a yanxu shine aka gina babbar makarantar da kecikin k'auyen gurma,_
Tashi ramlat tayi taje tazauna akan k'afafun shu'uma tana kuka "kiyi hakuri ramlat tashi kije kiyi wanka kisamu kiyi bacci idan kinfarka kizo muzauna muyi shawara akan hanyarda zamu b'ullowa wad'annan Azzalumai ramlat tad'ago tace kmar suwa kenan Aunty? Shu'uma tace *"SARKI MURTU da HONORABLE*
Bamusu suka tashi su duka bayan sungama shek'a wankansu suka canxa kaya Alwala sukayi sukayi sallar Azahar sannan suka kwanta dga lokacin ramlat tagane cewa shu'uma musulma ce kwance suke suna firarsu ta duniya dga nan sai barci
```Misalin k'arfe 4:00pm suka tashi sukayi sallah shu'uma tajayo ramlat tana nuna mata wasu wurare acikin gdn domin gidane babba mai manya itatuwa da wurin hutu iri-iri anan suka samu wata inuwa mai sanyi suka zauna suka shirya planing ta hanyarda zasubi domin cinma burinsu, ramlat ta k'ara samun kwanciyar hankali sosai fiye da zamanta gidan su Ashraf hakan yasa tasake jiki sosai da Aunty shu'uma da sukaga magriba ta gabato suka tashi suka koma cikin gida sukayi shirin Alwala,```
_Bayan sungama sallar magriba da isha'i dga nan suka fara shirin barci idan kaga SHU'UMA da RAMLAT saika rantse uwa da d'iyace..))_
_((Follow Me With My Facebook))_
https://mobile.facebook.com/Raheem-jega-Novels/976058029184366?ref=opera_speed_dial_freefb
*MY WAtsapp Group*
Raheem jega NovelsπŸ“š
+2347069242722
Via OHWπŸ“²
πŸ“šπŸ€πŸ’πŸ€
*RAMLAT*
_Yar Tsintuwa_
πŸ€πŸ’πŸ€
*_Written BY S.raheem jEgaπŸ“š_*
_πŸ’RaMlaTπŸ’_
*51_56*
*Washe Gari*
_Yau ranace kamar kullum Labarin mutuwar manyan yaran SARKI MURTU yasamu Honarable, tafiyace ya shirya ta mussamn shikad'ai saikuma direban sa, da excort d'insa guda zuwa gaisuwa a k'auyen gurma babbar motarsa ajiye take a harabar gidansa dirabansa shikad'ai yake jira suwuce,_
```Acan gidan Aunty shu'uma tunda sassafe suka tashi itada ramlat dama tunjiya sungama tsara komai ramlat tana sanye da farar rigar mai ratsin bak'i sai kuma sket baki na yara shu'uma tunda dga k'asa har sama komai nata bak'ine tayi shiga cikin bak'aken kaya banda edon ta ba abinda zaka iya ganewa ajikinta,```
```Sukazo dai-dai hanyar da honarable zaibiyo suka buya akan bayan wata bishiya tundaga nesa suka hango motarsa wata kaza naga shu'uma t d'auko ta yankata ta zubarda jinin kazar ajikin ramlat gaba d'aya rigar ramlat ta lalace da jini da sauri ramlat taje ta kwanta akan titi tayi lahu tamkar gawa....^^```
*Direban na k'arasowa honarable yace "dakata usman kataka birki nace..!!*
Yaja birki jikake "keyyyyyy suka fito honarable yad'ora hannunsa ajikinta yaji ko numfashi batayi ya duba ko ina babu alamar mutum d'aukota yayi cike da tausayi yace "usman kajuya motar muje hospital da sauri direba yayi riverse suka koma har Alokacin rungema yake da ita jiyake tamkar yarsa ce ajima kad'an yakai dubansa gareta,
```Shu'uma dake b'oye tana ganin hakan da sauri tafito akayi sa'a mai napep yabiyo tatsaida shi tayi masa kwatancen inda zaikaita basufi minti 5 ba yakaita a k'ofar gidan honarable tabashi kud'insa yatafiyar sa, tsaye tayi tana k'arema gidan kallo har alokacin fuskarta rufe take a hankali tanufi k'ofar shiga gidan tana kai gate taci karo da matar honarable zatafito da mota da sauri takoma baya gabanta na duka tajuya tamaida hankalinta akan titi kmar batasan da gidan ba,```
Saida tadaina ganin motarta sannan tajuyo takutsa kai acikin gidan tanatafiya sum-sum kamr mai gsky tana kai bakin k'ofar shiga palour taji ance "dakata malama wacece ke?
tsaye tayi cakk wuri guda itabata tafiba, kuma batace k'alaba, tsawa yadaka mata "ke malama magana nake abokinsa ne yadafa kafad'arsa yace
_"Aa Labbo wlh na rabaka ka mnta Alhj yace xayyi bak'uwa yau, hannu yad'ra abaki yace "nashiga uku ba shakka wannan kayan Alh ce_
Murmushi ya k'irkiro yace "hajiya dn Allah kiyi hkr wlh banxata keceba, dama Alh yasanarda mu zuwanki, kai kawai ta girgixa musu takama hanya sai cikin palour,
Labbo yace "nagode Allah yau dana rasa aikina dariya abokinsa yayi yace "Haba labbo aikai daganin irin wann shiga nata komai arufe basai anfad'ama ba kasan tsarabar Alhj ce, labbo yayi ajiyar zuciya yace "Allah yasa mudace.
Tsaye take a palour tana rabon edo idan tashiga wannan d'akin tafito tafad'a wancan kasan cewar gidan ba kowa da haka harta fad'a dak'in honarable tundaga bakin k'ofa sanyin A.C yafara d'ibarta da tsoro tsoro takai edonta akan wasu file-file dake ajiye akan wata Babbr Akwatinsa koda taduba duk file nea na gidaje da filaye harda na kamfanonin sa,
_Nan tashiga bincike duk saida tagama dubesu kaff bataga takardun filin mahaifinta ba, hannu tasa tabud'e Akwatin File tagani d'auke da sunan mahaifinta hakan ya tabbatar mata da cewa tabbas wad'annan sune takardun filayen mahaifinta d'aukowa tayi tabaro d'akin da sauri tamayarda nik'ab d'inta batare da kowa yaga fitarta ba, tatari mai Napep yace "hajiya ina zamuje tace "Sabon gari....))_
*HOSPITAL*
```Darect Asibitinsa, sukaje yashigo rungume da ita hannunsa da gudu Likitoce sukayo kansa ganin cewa honarable ne da kansa yazo da marar Lafiya hospital emergency room Akakaita yasanar da likita cewa sukala da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment