Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akayi masa d'inki mai yankakken hannu irin na zaman gida gaban rigar da bayanta anyi aiki da farin zare wanda yake nuni da tambarin masarautar, a nutse ya bude akwatin nan naga tarin agoguna da manya manyan zubonan azurfa kala kala sai sheqi sukeyi, agogo mai sarqa yasa a hannunshi na dama kana ya zura wasu zubonan azurfa a tsayunsa guda biyu na hagu da dama, zubonan suyi masa kyau sosai da sosai. ya mayar da a kwatin ya rufe ya dauki hular yana gyarata hula ce aka d'inkata da wani irin yadi mafi akasari ma masu saurata suke amfani da ita tsayin hular ne ya bashi dariya ya dinga duba hular yana tunanin ajiyeta ya bar kansa a haka sai dai yayi dubarar lankafe saman ta ya rage mata tsayi yasa a kansa kana ya zura takalman dake gabanshi masu kalar hular .....Gaban mirror ya tsaya yana sake duba kansa, murmushi ya dinga yi yana shafa siririn sajen fuskarsa lallai malam bahaushe yayi gaskiya da yake fad'in kowa ya bar gida to gida ya barshi, yaushe rabonsa da sanya manyan kaya a jikinsa, sai yaga shi kansa ya k'arayiwa kansa kyau da kwarjini wannan zungureriyar hular da yake wa dariya yaga tayi masa kyau sosai ta sake fito masa da kewayayyar fuskarsa mai dauke da k'ayataccen sajensa, ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya bar gurin mirror kai tsaye hanyar fita daga dakin ya nufa...........Yana fitowa Haruna dake tsaye kamar gunki a kofar dakin yayi kasa da kansa tare da fadin"Barka da fitowa." Ba tare da yace masa komai ba ya wuce cikin falon.....Nan ya ganta a hakimce a kan kujera k'afarta d'aya kan 'daya tana sakar masa kyakkyawan murmushi...........Idonsa a tsaye a kanta ya samu guri ya zauna cikin d'aya daga cikin k'ayattatun kujerun dake kewaye da falon Wani irin zama yayi irin na masu mulki yasa mata idonsa yana kallo fuskarsa babu d'igon annuri.
Gimbiya Lawisa cikin iyayi da iyawa ta ma'kale murya tare da fadin "Barka da fitowa magajin sarki inayi maka barka da dawowa masarauta lafiya."
falon shuru yayi bayan gama maganarta tana jiran amsarsa taji shuru bece komai ba, dago kai tayi tana kallonsa taga yana ta kallon jikinta.......Yarima Ali na da muguwar d'abi'ar san mata dan ko acan amurukan ma shagalinsa ya sha da matan turawa da bakaken fata amma duk kulafucinsa bai ta'ba zina ba sai dai romancing nan yake biyawa kansa bukata, yana da bala'in san mata masu kyau da k'irar jiki, Gimbiya Lawisa nada kyau da lafiyayyan jiki shiyasa ya gaza dauke idonsa daga kanta sha'awarta ce ta d'arsu a zuciyarsa. Ganin tana kallonsa tana murmushi yasa yayi gyaran murya da kyar yace."Daga wane 'bangare kike.''? 'Yar dariya tayi tana kallonsa tace"Yanzu dan Allah baka gane ni ba ? nice fa Lawisa ta gurin Baba Ciroma 'kanwar Moddibo."'
Sajensa ya shafa har yanzu babu fara'a a fuskarsa yace."Ya za'ayi na gane ki bayan rabona daku sama da shekara goma lokacin dana bar gida ina tsammanin baki kai shekaru bakwai a duniya ba."
Tace"Eh hakane kam shekaruna takwas a lokacin daka tafi karatu amma kuma ni kaga ban mance da kai ba."! Shuru yay yana kallonta, Ta cigaba da cewa"Wannan dalilin ne yasa ma na shirya gagarimar walima domin taya ka murnar dawowa gida lafiya.'' Murmushi yayi yana kallonta yace."Nagode 'Kanwata inaso naga ana nuna kulawa akaina nayi farin ciki sosai da wannan karamcin yaushe ne kika tsayar da taron.

Cikin farin ciki da jin dadi tace"Naji dadi sosai daka kar'bi magana ta da mahimanci nagode sosai sannan kuma ranar jumaa ne ranar dana tsayar domin taron walimar." Da ragowar murmushi a fuskarsa yace."To shikkenan Allah ya kaimu ranar lafiya."
Falon yayi shuru Lawisa sai sa'ke-sa'ke take a cikin ranta tana tunanin ko kawai ta fad'a masa tana sonsa tunda taga nan da nan ya kar'bi maganar da ta kawo masa da muhimanci.....tana kokarin tayi magana......Aunty Safiyya d'aya daga cikin yayyunsa ta shigo falon bayanta wasu bayi ne mata guda biyu suna dauke da tire din abinci kai tsaye can gurin daining suka..........Aunty Safiyya ganin Lawisa a zaune tana murmushi yasa tayi saurin kallonta ta kalli 'kanin nata sai kawai taji farin cikin ganinsu a tare lallai babu shakka Lawisa zata taimaka musu gurin ganin bukatarsu ta biya a kansa.....Cike da farin ciki gami da nuna jin dad'i tace"A'a k'anina soyayya akeyi ne.'' Kansa ya sunkuyar qasa bece uffan ba.
Ita kuwa Lawisa sai murmushi takeyi na jin dadi tana kallon aunty Saffiyan tana sunkuyar da kanta.
Kusa dashi taje ta zauna kamar gaske ta dafa kafad'arsa da fadin'' A gaskiya nayi farin cikin ganin ku a tare dama babban burinmu a yanzu kayi aure ka sake zama babban mutum to alhamdullilahi tunda ma 'yar gida za'ayi towo na mai na ne abun yayi dad'i nasan kuma iyayenmu zasuyi farin ciki mutuka, kuma inaso na tabbatar maka da cewar kayi sa'ar matar aure domin dai Lawisa babu abinda ta nema ta rasa na bangaran kyawun hali ga uwa uba kyawun sura."

Ya d'ago kanshi a nutse yana kallonta "Aunty Safiyya waye yace miki soyayya muke? fitowa ta kenan daga daki na sameta a zaune dan sai da ta gabatar min da kanta na gane cewar famliy nace, tazo tana sheda min walimar da ta shirya domin murnar dawowata gida wannan shine dalilin daya saka kika gan mu a tare."
*BINTA UMAR ABBALE*

Shearing 👏🏻👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_




*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah)
13&14
Aunty Safiyya a nutse take kallonsa kafin tace"Kai kuwa Magajin sarki meye laifin Lawisa dan Allah kada kaje ka dauko mana ta waje gwanda ka duba a cikin gida ina ganin kamar haka zaifi alkairi." Shuru yayi mata tare da sunkuyar da kansa. Tace"Idan ka auri 'yar uwarka a ganina sai kafi samun cikakkiyar kulawa kuma tabbas hakan zai faranta ran iyayenmu dan Allah ka duba maganata da kyau kaji ko."! har yanzu kansa na sunkuye a kasa ya'ki kallonta ballantana ya bata amsa. mirmushi tayi tare da mikewa da fadin"Miskili kenan to kai dan Allah da irin wannan halin naka wacece zata iya zama da kai idan ba 'yar uwarka ba? babu macan da zata juri wannan wulakancin naka."
'Dago kansa yay yana kallonta cikin rashin walwala yace."Aunt Safiyya mai yasa kuke yi min irin wannan kallon ne? wallahi ban san ya ake wulakanci ba a rayuwa ku lura da kyau da'bia tace rashin son doguwar magana shiyasa nayi shuru na kyale ki amma duk irin maganganun da kikeyi ina jinki."

Murmushi tayi tana kallonsa tace"Eh ni zan fadawa kowa hakan d'abi'ar kace shiyasa ma ai nace bama so ka auri bare gwara ka auri ta gida domin sai tafi jurar zama da halayen ka." murmushi yay wanda ya tsaya iya lab'bansa yace."Aunt Safiyya ki bar wannan maganar dan Allah.'' Jin abinda yace yasa Lawisa saurin kallonsa gabanta na faduwa lallai wallahi tasa rai ganin aunty Safiyya ta shiga maganar yasa take jin tamkar ma ta aure shi ta gama.

Aunty Safiyya ta kalleta tare da fad'in "Lawisa kina sonsa ko."? babu kunya tace" Eh aunty. " murmushi tayi tare da kama hanyar fita tana fadin"Ba zan tafi gida ba har sai na bari an tashi daga fada na fadawa maimartaba halin da ake ciki.
Da sauri ya dago kansa yana kallon bayanta cike da mamakin jin abinda ta fad'a......Fuska a kirne ya kalleta da fad'in "Tashi ki fitar min a daki wato dama abinda ya shigo dake kenan? waye ya fad'a miki ina sha'awar auran zumunci dake."?

Lawisa gabanta ya dinga faduwa tana so tayi magana amma ta kasa saboda tsabar kwarjin da yayi mata gashi ya tsareta da idanunsa masu girman da furgita mara gaskiya.

A sanyaye ta miqe tana gyara alkyabbarta hanyar fita ta kama ranta sai tafarfasa yake yi lallai wai duk wannan kyawun nata da kyawun surar jikinta bata burgeshi ba hakika taji takaicin tsawar da yayi mata meye laifinta da zaice baya sha'awar auran zumunci da ita.......masu take mata baya ganin ta fito fusace yasa suka shiga hankalinsu da sauri suka rufa mata baya suna sunkuyar da kansu 'kasa.............

****
Cikin saurin na fito daga gurin mu domin zuwa duba dawakan da babana ke hidimarsu tun safe dana zuba musu abinci ban sake zuwa duba su ba saboda yini mukayi wankin kayanmu nida mahaifiyata wannan dalilin ne yasa ban je gurin da wuri ba............Ina daf da shiga kofar dawakan na hangeta ita da masu take mata baya, sanin halinta naso a girmamata yasa na sunkuyar da kaina qasa har suka karaso gurin nace" Barka da yamma ranki shi dad'e." banza tayi min bata amsa ba sai hararata take ni kam ban san me yasa ta tsaneni ba tsakanina da ita harara ne da kallon banza. Ganin taki amsawa yasa da sauri nayi nufin shiga kofar......Naji ta daka min tsawa da fad'in "Ke! mahaukaciya dawo ki tsaya a inda kike ko nace ki tafi ne."? Cike da mamaki nake kallonta kafin nace" Ranki ya dad'e na gaishe ki kin'ki amsawa me kike so nayi miki a yanzu ina da uziri zan zubawa dawakai abinci."
Kallona naga tanayi tana girgiza kanta, ni kaina sai da na gama maganar nazo ina nadama sabida nasan na tarowa kaina jaraba, ni haka nake bana barin magana a cikina idan mutum ya gaya min biyar sai na fada masa goma gashi bani da tsoro ko kad'an cikin dubbanin mutane aka ajiye ni zan iya kwatar kaina saboda ina da baki.

Inda nake tazo ta tsaya tana yi min wani irin kallon raini! kafin na ankara naji yawun bakinta a fuskata, da sauri na dago kaina ina kallonta........Tana wani irin huci! tace"Yanzu Sumayya a matsayinki na makaskanciyar baiwa a gidan nan har kina da damar tsallake umarnina nace miki ga abinda nake bukata kice kina da uziri."?

Hannu nasa na goge yawun data tofa min nace"Ranki ya dade ki gafarce iya bakin kokarina nayi miki na baki girmanki na risina na gaishe shin to dan Allah dan annabi me kike so nayi miki ."
Mari! ta kwad'a min a kumatuna kafin na dawo daidai ta sake waska min wani a d'aya gefan! Ido jawur nake kallonta ina jin tamkar nima na fitar da hannu na rama! marin......hannu ta daga kawai tana nuna ni tsabar b'acin ran dana kuntunka mata ya hanata magana, a rayuwar Gimbiya Lawisa tun tasowarta a gidan sarautar babu wanda ya ta'ba yi mata gardama akan umarninta sai Sumayya......Juyawa nayi zan shiga kofar dawakai ta janyo faffad'an wuyan rigata aikuwa a take rigar ta yage da yake rigar ta yadi ce mai dogon hannu zanin kuma na shadda kamfala shine uniform din mu a cikin gidan mata zani maza wando amma dai duk ranar jumaa muna sanya tufafi masu kyau domin girmama ranar haka ma ranar sallar 'karama da babba sarki nayi mana d'inkuna na atamfofi muyi ado domin murna da zuwan ranar.........Hannu nasa da sauri na dafe wuyan rigar ganin yana kokarin sab'ulewa. Tsira mata ido nayi rai a 'bace! nace tsirara zakiyi min ne? kada fa ki manta kema macace idan kinyi min tsirara a idanun jama'a kamar kin tonawa kanki asiri ne."
Wani marin ta sake bani tana huci! ni kuma mirmushin takaici nayi hannuna dafe da kuncina ina kallon ikon Allah........Jama'a ne suka taru a gurin sai bata hakuri suke harda masu durkusa mata, Buba ta kalla dake riqe da shar'be'biyar bulala tace"Bani bulalar nan." Da sauri ya mika mata yana fadin "Tuba take ranki ya d'ad'e."........Ganin ta d'aga bulalar zata shaud'a min yasa nayi saurin fizgewa na nannad'eta a hannuna sai kawai muka tsirawa juna ido nida ita jama'ar dake gurin da ita kanta mamakin karfin halina suke.........Ta girgiza kanta tana kallon Buba tace" Inaso ka samo igiya mai kauri ka daure mata hannuwa da kafafu yau nayi al'kawarin sai naga karshen taurin kanki."..............Kallonta kawai nake tsabar takaici da bakin ciki yasa nake jin kamar na zazzabga mata bulalar dake hannuna, ina kallon Buba ya tawo da murtukekiyar igiya gabana ya yanke ya fad'i ganin ya nufo inda nake....................yasa na juya baya ina neman mafaka babu dan duk ko ina mutane ne sun kewaye mu, tsugunawa nayi a kusurwa hawaye ya kwace min, Buba babu tausayi yazo ya shiga kici kicin daure min hannuwa da kafafuna sai tirje tirje nake ina haurinsa amma sai da ya samu nasarar daure ni tamau! gwiwowina a kasa kaina a sunkuye na soma jin saukar bulala a gadon bayana.......tsabar taurin kaina yasa na kasa motsi ina dai jin radad'in bulalar na ratsa min jiki amma saboda na nuna mata a banza takeyi yasa na daure.........Gimbiya Lawisa sai da jikinta yay sanyi ganin ko gezau na 'kiyi ballanatana na nuna mata ina jin zafin bulalar, tunani tayi ko itace ba ta iya bulalar ba rai a 'bace tace"Buba zo kayi mata ka tabbatar da cewa ta ratsa jikinta shegiya basamudiya yanda take da wannan gansameman jikin dama ai duka ba zai ratsa ta ba." Gefe ta koma tana haki! dan ba karamin galabaita tayi ba.'' Buba cike da bin umarni ya daga bulalar zai shaud'a mata, muryarsa ta katse masa hanzari.....Kafatanin jama'ar dake gurin suka juya suna kallonsa ganin ya nufo gurin ne yasa kowa yayi k'asa da kansa har ita Lawisan sunkuyar da kanta tayi......Cikin nutsuwa ya 'karaso gurin aka bud'a masa hanya ya shiga har inda nake durkushe! ta 'kasan idona nake kallonsa yana tsaye hannuwansa duk biyun a baya sai kalle kalle yake a gurin kafin naga ya kalleta babu fara'a a tare dashi yace."Yace."Meke faruwa ina zaune Haruna ke sheda min ga jama'a sun taru kuma kina gurin saboda haka inaso nasan abinda ke faruwa."
*BINTA UMAR ABBALE*

Shearing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_




*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA''ATU S YARI*
(Kainuwa dasha Allah✊🏻)
15&16
Ganin yanda ya tsira mata idanunsa gami da sake tamke fuskarsa ya sanya jikinta yay sanyi tana jin tsoron ya tozarta a gaban wa'inda suke ganin kima da mutuncinta.........Cikin kokarin aro jarumta tace"Tunda nake a cikin gidan nan babu wanda ya ta'ba yi min musu akan umarnin da zan bashi sai wannan ba'kar yarinyar mai fuska irinta ba'kar akuya ta raina ni sosai sai kace ni din abokiyar adawarta ce, gabad'aya mutane suna gaisheni suna bani girma da mutuncina amma ita kokarin ratse ni take ta wuce ina ganin ko wane irin hukunci nasa ayi mata ya dace da ita sabida ta kasa mutunta ni."

Wani irin kallo yake min tamkar yana kallon abu mai muni! koda yake ban sani ba ko shima ya hango munin nawa da mutane suke fad'arsa wannan dalilin yasa da sauri na sunkuyar da kaina kasa zuciyata tana wani irin zafi! ta k'asan idona nake kallonsa sai ya mutsa fuska yake yana kare min kallo.

A dan sace na dago kaina muka had'a ido dashi! da sauri na kalli inda ya k'urawa ido a jikina.....Cikakken kirjina dake cike dana shanu naga yana satar kallon inda rigata ta yage, nasa hannuna da sauri na sake rufe gurin ina jin wani mugun haushinsa ni ban san meye a jikina ba da maza suke lalacewa gurin kallona, ni dai nasan bani da wani cikakken kyau ga shegen baqi sai kace me? ban sani ba ko nonowa na da suka rinjayi kirjina ne ke d'aukar hankalinsu ko kuma mazaunai na wanda suka cika bayana tamkar suyi magana ni kaina na san a fiska ban cika kyau ba amma na amince da cewar a jiki na cika cikakkiyar macan da kowane namiji yake bukata.

Da sauri na dago kaina ina kallonsa jin kamar yana magana cikin 'bacin rai! Aikuwa fad'a sosai yakewa Gimbiya Lawisa gami da nuna mata muhimancin mutun komai lalacewar dan adam tunda Allah ya karramashi to kaima sai ka mutuntashi." Gimbiya Lawisa cikin takaici take kallonsa sam bata dauka zai goyi da bayan yarinyar ba, ranta a 'bace ta bar gurin yaranta suka bi bayanta da sauri.......A nutse yace."Kowa ya koma bakin akinsa." Minti uku gurin ya watse kowa ya nufi inda yake....Hannuwansa na goye a baya ya tsirawa kasa ido yana kallo, cikin zuciyata nace"Anya kuwa wannan guy yana da lafiya gaskiya da matsala a tare dashi duba da yanda yake nacin kallon 'kasa sai kace wani makaho.
Rigata na dafe na yunk'ura da kyar na mike tsaye. nayi nufin shiga kofar dawakai naji maganarsa.
"Koma ki tsuguna inaso nayi magana dake." Da sauri na tsuguna tare da sunkuyar da kaina kasa.......sai da yaja dogon lokaci sannan yace.''Me yasa bakya mutunta Lawisa ko mahaifinki nada rawani a masarauta shiyasa kike gani tamkar daidai kike da kowa."

Maganar tayi min ciwo sosai amma sai na daure wa zuciyata dan saboda nasan bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane....."Ranka ya dad'e wallahi ina mutunta ta ina gaisheta a duk sanda zamu hadu itace dai ta tsane ni ban san me yasa ba kuma ko yanzu kafin al'amarin nan ya faru sai da na gaisheta tukkuna, maganar rawani kuwa mahaifina ba kowa bane a cikin masarautar nan fyace bawa mai d'aukar d'awainiyar dawakan dake cikin masarauta, sunana Sumayya sunan mahafina Lawi."

Shuru yayi yana kallonta yana tuno ranar daya dawo ranar da take cewa ba zata tsaya a rana ba ." Babu annuri yace."Okey kece ranar dana dawo kika nuna gazawarki akan tsayuwa a cikin rana ko."?
sunkuyar da kaina nayi gabana na faduwa.....Ya 'bata fuska sosai yace."Ke da bakin ki kin fad'i cewar babanki bawa ne wanda nasan a cikin bauta aka haifi iyayensa, sannan aka haifeshi shi kuma ya haife ki to me zai sanya ke! kike nunawa masarauta gadara gami da rashin girmama dik wanda yake sama dake."

Shuru nayi mishi dan banga rashin kyautawar da nayi ba, iyakacin bakin kokarina ina girmama duk wanda ya dace na girmama a masarautar to ban san kuma wane girma zan bata ba.

Tsaki yaja yace."Tashi kije amma kada ki sake kwatanta abinda kikayi a wannan masarautar wanda keda muqami ko kuma ya gaji sarauta shine zai nuna iko akan komai amma banda ke da kike a matsayin baiwa 'kasa da sama to wane gadara da izzah zaki nunawa mutane? kinyi sau biyu kada kiyi na uku idan kika sake da kaina zan hukunta ki."

Cike da mamaki nake kallonsa nace"Ranka ya dad'e a gafarce ni watakila maganar da zan fad'a ba za tayi maka dadi ba, sai nake ganin ita izzar da kake magana akanta ai ba abu ne mai kyau ba izzah! da buwaya gami da iko duk na Allah da Annabi ne, wani Sarki ko mai wani mulki dashi da muqarabbansa duk aro Allah ya basu kuma idan suka kauce hanya akan mulkin da Allah ya basu dole a lahira Ubangiji ya hukuntasu saboda haka ni banga ma'anar wannan maganar da kayi ba dan izzah! na d'aya daga cikin munanan ayyuka."


Kawai naga ya tsira min ido yana kallona fuskarsa tamkar hadarin dake dab da zubar da ruwa! sunkuyar da kaina kasa nayi na dafe a kasan gurin da hannuna nace"A gafarce ni idan maganar da nayi ta 'bata maka rai."
Mikewa nayi na shige kofar dawakan wanda ko ban juya ba nasan bina yake da kallo.

Ya jima tsaye a gurin yana kallon kasa! mugun mamakin yarinyar yake da kalaman da tayi wato tana nuna masa ba zata bi umarninsa ba, tana nuna masa shi din jahili ne be san abinda yake ba tunda gashinan a cikin maganarta har tana kawo masa hadisai! tunda yake ba'a ta'ba katse masa hanzari ba idan yana magana sai yarinyar yana da kyau ya nuna mata muhimancinsa a cikin masarautar.

Koda na gama abinda nake a ciki na fito samunsa nayi a tsaye a inda yake sai kace wani dogari yana tsaye hannu a goye a baya sai kallon kasan gurin yake yi, na girgixa kaina tare da kokarin ratse shi na wuce.

Gyaran murya yay kafin yace."Tsaya nan gurin." Da sauri na tsaya nayi kasa da kaina, karasowa yay ya tsaya daf dani har ina jiyo wucin numfashinsa, gabana ya shiga faduwa fuskata na dago na kallesa, naga sai kallona yake da tamkakkiyar fuskarsa, tsoro ne ya shiga jikina nace"Dan Allah kayi hakuri ranka ya dade wallahi ban fada maka magana ba dan na bata maka rai nayi nufin tunasar da kai ne akan abinda ka manta.

Cikin fushi yace."Kina nufin ni jahili ne kome."? Na girgixa kaina da sauri nace"A'a ba haka nake nufi ba." numfashi ya fesar mai zafin gaske yace."Kada na sake fad'in wata magana ki kawo min hadisai gami da fad'ar Allah yace annabi yace na fiki sanin munin abinda kike magana akai ni inayi miki magana ne akan girmama na sama dake a matsayin ki na baiwar dake karkashin masarauta yasa nace miki lallai ki girmama wanda yake saman ki amma tunda taurin kai zakiyi akan umarnina duk ranar da Lawisa ta sake daukar hukunci akanki zan bari tunda haka kike so.

A sanyaye nace"Yanzu na fahimci maganarka insha Allah zan kiyaye zan kuma cigaba da girmama wanda ke sama dani.

Ba tare da yace komai ba ya janye daga kusa dani ya koma gefe guda ya cigaba da kallona. ajiyar zuciya na sauke gabana na fad'uwa na kallesa, naga sai kallona yake ikon Allah mutumin wai kallon k'urrular me yake min ni ba kwalliya nayi ba ba komai ba amma ya dame ni da kallo......yagaggen wuyan rigana na riqe da sauri na bar gurin tafiyata na hard'ewa nasan idanunsa ne ya janyo min hakan.

Har sai data 'bace daga gurin sannan ya dauke idanunsa daga hanyar da tabi, yarinyar bata da wani cikakken kyau a fuska amma kuma Allah yayi mata kyawun sura tamkar ita tayi kanta, dugowa mai garin jiki gami da cikakken kirji da fad'in qugu wuyanta a cike dam!dam da wani irin guru-guru ba'kar fatarta lafiyayya lukwi lukwi sai she'ki takeyi abin sha'awa, shi kam tunda yake ganin ba'ka'ken fata bai ta'ba cin karo da fatar data burgeshi ba irin nata.....mirmushi yay gami da shafa siririn sajensa, hakika yarinyar da a waje take to babu abinda zai hanashi romancing da ita dan yayi masifar sha'awarta matsalar kawai yarinyar bata kai matsayin da zai had'a jiki da ita ba, makaskanciyar baiwa ce wacce take ci da sha a k'ar'kashinsa, daba dan haka ba da duk yanda zaiyi sai ya yaudareta ya mori albarkatun jikinta......Fitowa yayi daga gurin cikin sanyin jiki gami da rashin kuzari yake tafiya, kai tsaye sashen mahaifiyarsa ya nufa yana tafiya jama'ar dake shige da fice a gurin na gaishe shi Haruna ne yake take masa baya har ya isa kofar sashen mahaifiyarsa Haruna ya bude masa kofar falon, yayi saurin matsawa gefe shi kuma a nutse ya shiga falon da sallama a bakinsa.....
*BINTA UMAR ABBALE*
[1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)



17&18
Tana kishingid'e a killace a guri guda da cazbaha a hannunta tana lazimi yau ita kadai ce a zaune a falon babu hadimai a kusa da ita ta bukaci zama ita kad'ai ne domin ta kad'aita kanta da mahallicinta shine da dalilin

Please Login or Register in order to submit comment