Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yasa ta sallami bayin dake kusa da ita.

Tunda ya shigo take sakin murmushi idanunta a kansa har ya k'asara kan kilishin da take kishingide zaman raquma yay a gabanta tare da sunkuyar da kansa cikin tsantsar ladabi yace."Mamma barka da yamma." hannunta guda ta dora a saman kanshi tana shafawa gyaran murya tayi tana nuna masa cewar akwai abunda takeyi....Kansa ya dago yana kallonta sai ta nuna masa carbin dake hannunta tana murmushi had'e dayi masa nuni dacewar ya jira ta kammala.

Murmushi yay a nutse yasa hannu kan tire din dake gabanta wanda ke cike da kayan marmari.. tufa(apple) ya d'auka yasa a bakinsa ya gutsira yana sake gyara zamansa a gurin.

Kallonsa take tana murmushi mai ma'ana wanda kai kana ganin yanayin fuskarta zaka gane cewar tana cikin farin ciki kuma akwai soyayya da shaquwa mai yawa a tsakaninta da yaron nata.


Magajin sarki sai da ya cinye tufa(apple) uku tukkuna ta kammala lazimin a nutse tace"Babana barka da yamma." Ya dago kansa da sauri yace."Mammah barka dai ina fatan kin wuni cikin koshin lafiya." Yafadi maganar a sanda yake kokarin riko hannuwanta.

Tace."Lafiya lau na wuni ina fatan baka da matsala dan tun safe nake jiran shigowarka yau ba kayi shigowar safe ba ina fatan lafiya."

Zamansa ya gyara har yanzu kuma hannuwansa na rike da nata yace."Wallahi Mammah yau bacci na yini ina yi sai gefin la'asar na tashi nayi wanka wannan shine dalilin da yasa ban shigo mun gaisa ba."


Ajiyar zuciya ta sauke tace"To alhamdulillahi tunda lafiyarka lau dama akwai muhimiyyar maganar da nake so mu tattauna da kai."

Ya sake gyara zamansa cikin kulawa yace."Ina sauraran maganar Mammah." Da farin ciki ta tare da ita tace"Ashe bayan dawowarka gida kun shirya tsakaninku kai da Lawisa 'yar gurin Kawun ka Ciroma d'azu da safe maimartaba yake sheda min yanda al'amura suka kasance hakika naji dadi sosai daka za'bi matar aure acikin dangi ina ganin hakan sai yafi mana kwanciyar hankali da kai baki daya."


Shiru yayi kansa a kasa ya rasa abinda zaice. ashe sai da aunt Safiyya taje ta fad'i maganar wallahi shi ya dauka da wasa takeyi! tunda yake bai ta'ba sha'awar auran zumunci ba saboda gudun lalacewarsa yafi so ya fita waje yaje can ya auro saboda baya so ya auri 'yar dangi zumunci ya sake lalacewa dama a lalace yake shiyasa kwata-kwata baiyi na'am da maganar ba ashe sai da taje ta fadi maganar.

Fulani ganin yayi shuru tace."Babana ko akwai matsala ne? naga kayi shuru kana tunani kayi min bayani dan ba naso ayi al'amarin nan rayuka su 'baci idan ba kai ke son al'amarin ba to tun kafin tafiya tayi nisa a warwareshi."


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yana kokarin 'boye damuwar dake fuskarsa yace."Mammah ba wani abu bane yasa kika nayi shuru ina tunanin abinda aunty Safiyya ta aikata bayan nayi mata bayani cewar babu wata alaqa ta soyayya a tsakanina da Lawisa kawai tazo ta ganta ne a ranar dana dawo tazo tana sheda min cewa ta shirya walima domin murnar dawowata gida lafiya to ita kuma aunt Safiyyan shine take tunanin soyayya ce a tsakanina da ita.

Fulani shuru tayi tana mamakin al'amarin ta kalleshi a nutse tace"To yanzu wace shawara ka yanke dan gaskiya al'amarin yayiwa Maimartaba dadi bashi kadai ba har sauran 'yan uwansa sunyi farin ciki nima kuma naji dadin hakan idan kace ka janye maganar baza suji dadi ba.

Murmushi yay wanda ya tsaya iya le'bansa yace."Mammah bana fatan ranar da zata zo na 'bata muku rai dake da maimartaba tunda dai maganar nan ta fita har iyaye sunji to ina ganin babu damuwa zan auri yarinyar amma a gaba dole na 'kara aure mutukar Allah ya had'ani da wacce nake so."


Fulani murmushi tayi tana girgiza kanta cike da tsantsar farin ciki a maganarta tace"Ubana ina alfahari dakai mutuka ina jin dadin yanda kake kula dani da gudun 'bacin raina ina rokon Allah ya azurtaka da zuria masu albarka kamar yanda kake mana ladabi da biyayya kai ma ubangiji Allah yasa 'ya'yanka suyi maka.

Cikin sakin fuska ya amsa da ameen Mammana.! dama nace ina bukatar masu hidima a sashena domin wani sa'in hidima nayi wa Haruna yawa."

Cikin kulawa tace"Ayya ai wannan mai sauki ne ubana dama saboda nasan baka san hayaniya yasa na tura maka Haruna saboda nasan yana da nutsuwa amma insha Allahu zan sake turo maka mutum uku sun isa ko."? Yace."Yace mutum biyu ma sun isa sai su zauna su uku ina ganin hakan yafi" Tace."To shikkenan Ubana kada ka damu insha za'a turo masu hankali da nutsuwa.


***
Washe garin ranar bayan mun fito daga gurin karatu ni da Lahira muna tafe muna magana, Haruna yasha gabanmu yace."Sumayya Lahira kuje can b'angaran Fulani ana bukatar'ku.''

Kallonsa nayi nace"Haruna ina fata dai lafiya ba wani laifin mukayi ba." Yace."Babu komai ku kwantar da hankalinku sannan ba ku kad'ai aka nema ba har da sauran 'yan uwa.'' Ajiyar zuciya na sauke nace"Haruna dan Allah zan duba jikin babana kuje kawai na biyo bayanku daga baya."

Da sauri yace."Wai sumayya mai yasa kike gardama da umarnin masarauta akwai 'ya'ya da yawa da iyayensu suke halin rashin lafiya amma basa irin abinda kikeyi.

Hannu na d'aga masa nace"Haruna abinda yasa kaji nace haka sabida nike bashi magani yanzu haka Tambaya mahafiyata suna d'akin dahuwa(dakin girka abinci) suna aiki girka abinci kuma nasan idan naje bai zama dole a sallame mu da wuri ba shiyasa nace zan fara dubashi na bashi magani tukkuna.

Haruna yace."Ba za'a wani dad'e ba insha Allah kedai kawai ki shige muje." Girgiza kaina nayi na kalli Lahira dake rungume da jaka nace"Muje." Haruna gaba yayi da sauri muka rufa masa ba zuwa b'angaran Fulani.
A jere muka samu 'yan uwanmu bayi maza da mata sunja layi a bakin k'ofa kai tsaye 'bangaran mata muka nufa nida Lahira muka tsaya shi kuma Haruna da sauri ya bude kofar falon ya shiga ciku.....Surutai ne suka shiga tashi a gurin bayan shigar haruna falon dukkanin mu muna mamakin tara mu da Mammah fulani tayi sabida mun san da cewar ita din macace mai mutunci da karamci bata fiye tara mu taci mana mutunci ba kamar sauran 'bangarorin dake gidan, dukkanin mu dai addua mukeyi akan Allah yasa alkairi ne.

Haruna na fitowa muka bishi da kallo ya kalli 'bangaran maza da sauri yace."Ku shigo a nutse." Suka dinga shiga falon a nutse har suka qare, kusan mintina goma sha biyar da shigarsu suka fito kowa ya kama gabansa banda mutum biyu da suka ja gefe suka tsaya.

Haruna ya kallemu da fadin"Ku shigo a nutse." Da sauri muka tu'be takalman mu muka fara shiga daya bayan daya.

Zubewa mukayi a gabanta muna gaisheta.....Amsawa ta dinga yi cikin walwala tana kallonmu fuska a sake babu nuna 'kyama

A nutse ta dinga tambayar sunayenmu muna fad'a mata, ta d'ora idanunta a kaina fuskarta a sake tace"Sumayya ina tsammanin zaki fi 'yan uwanki kuzari da kazar kazar saboda haka ke kad'ai zan dauka a cikin ku zaki kasance daya daga cikin hadiman Magajin Sarki zaki dinga kulawa dashi da duk abunda yake bukata keda sauran 'yan uwanki amma su din maza ne Haruna da Isa da Hamza ke kad'ai ce mace a cikinsu."

Tunda take maganar gabana ke fad'uwa sam banyi farin ciki dajin wannan al'amarin ba ba dan komai ba sai dan sanin da nayi cewar bani da lokacin kaina na farko ina d'awaniyya da mahaifina na biyu ina kula da aikinsa dake cikin gidan ina nufin d'awainiya da dawakai, na uku kuma karatun dana k'wallafawa raina a kansa wanda ba kowane yake da ra'ayin yinsa a cikin masarautar ba, dama Maimartaba ya bude sashen karatu a gidan sabida mu, wanda yake da ra'ayi yaje ya dauki darasi na boko dana arabic wanda kuma baya da ra'ayi yayi zamansa to nida iyayena muna da ra'ayin karatu shiyasa suka goya min baya domun na samu ilimi yanzu haka mun kai izifi talatin a cikin al'kur'ani maigirma, sauran littafan addini kuwa nan ma mun sauke wasu 'bangaran boko ma ina fahinta sosai dan ina jin turanci amma ba sosai ba wannan dalilin ya sanya naji gabad'aya banji dadin a'lamarin ba


Cikin kokarin danne damuwata na kaskantar da kaina cike da ladabi nace"Godiya nake ranki ya dade hakika naji dadi mutuka da kika za'be ni a matsayin wacce zata kula da sashen Yarima ina rokon ubangiji Allah ya bani ikon daukar amanar da kika bani."

Cikin farin ciki Fulani tace."Babu damuwa Sumayya kuna iya tashi ku tafiya Haruna zai jagorance ku zuwa sashen nasa sai ku gabatar masa da kanku a matsayin wanda na turo ku.

A nutse muka mike mukayi mata sallama cike da ladabi muka fita daga falon, Haruna dasu Isa suna tsaye suna magana na kallesu fuskata babu walwala nace"Ku muje ko."? Haruna yace."Ke aka za'ba."? Daga masa kaina nayi na kalli Lahira nace"Dan Allah kafin ki shiga gurin ku ki duba babana ki bashi magani idan kuma Tambaya ta dawo shikkenan." Lahira tace"Kada ki damu insha Allah zan dubashi sai kin shigo.


Lokacin da muka isa b'angaran nasa a kishingid'e muka same shi cikin furanni yana sanye da 'kananun kaya gabansa kayan marmari ne cikin tire wayarsa yake dubawa fuskar nan a had'e! cikin zuciyata nace "Naga sanda zan ga dariyar guy nan kullum fuska babu rahama Allah dai ya kyauta."

Gabansa muka zube gwiwoyinmu a k'asa had'a baki mukayi gurin fad'in "Barka da hutawa Magajin sarki muna fatan mun same ka lafiya."! K'asa mukayi da kanmu bayan mun gama maganar.....

Shuru yayi mana kamar bai san damu a gurin ba, raina ya 'baci sosai aqallah mun kai minti goma a gurfane a gabansa kamar wasu masu neman gafara wannan wace irin rayuwa ce.

Kallonsa nayi a lokacin da yake kokarin gyara zama karaf! muka had'a ido kwarjini yayi min wanda yasa na ma'kale maganar dake raina nayi kasa da kaina gabana na fad'uwa guy ya tara duk abubuwan da ake bukata yana da kyau sosai gashi dogo abinda yafi birgeni a tare dashi manyan idanunsa wanda suke a lumshe k'wayoyin idanunsa basu cika fari ba sun d'an sirka da ja banta'ba ganin kwayar idanunsa tayi haske ba.
muryarsa ce ta katse min nazarin da nake.....
*BINTA UMAR ABBALE*

Shearing 👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_



*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
19&20
"Haruna wa'innan fa."? ya fad'a yana nuna mu da bakinsa.Haruna ya sunkuyar da kansa kasa cikin taushin murya yace." Ranka ya dad'e Mama Fulani itace tace nazo dasu domin su gabatar maka da kansu a a matsayinsu na wa'inda zasu taimaka min da d'awainiyarka."

Kansa ya sunkuyar 'kasa yana nazari kafin ya dago yana yi min wani irin kallo babu walwala a tare dashi yace."Mutum biyu nace kuma banda mace a ciki nafi bukatar maza sabida haka ke kina iya tafiya.'' Yana kallona ya 'kare maganar.

Dad'i naji ya rufeni jin abinda yace yasa da sauri na k'askantar da kaina da fadin"Godiya nake ranka ya dade.'' na yun'kura na mike tsaye risinawa nayi da fadin"A tashi lafiya." Da sauri nayi nufin barin gurin naji yace."Dakata." Nayi saurin juyowa ina kallonsa addua nakeyi a zuciyata kada yace ya fasa.

Gani nayi ya sunkuyar da kansa raina ya 'baci! nida su Haruna kasa'ke mukayi muna jiran muji abinda zece.........B'angaransa kuwa tunani yay kan cewar zamanta a sashen nasa zai iya taimaka masa ta wani bangaran shine dalilin daya sa ya dakatar da ita daga tafiya.

Kallona yayi a ya mutse yace."Meye sunanki ma."? Babu walwala a tare dani nace"Sunana Sumayya Lawi." Ya shiga girgiza kansa minti biyu ya kalli Haruna da fad'in " ka shiga dasu ciki ka nuna musu abinda ya dace akwai d'akuna a falo kuyi amfani da d'aya kai da 'yan uwanka ita kuma sai ta dauki daya inaso ku dawo sashena da zama har abadah kune hadimai na koda nayi aure."

Gabana ya dinga bugawa ina kallonsa kwalla na taruwa a idona nace"Ranka ya dad'e inada magana." Ya kalleni yana ya mutsa fuska. Saurin sunkuyar da kaina kasa nayi bakina na rawa nace"Ranka ya dade naji kana maganar mu dawo sashenka har abada ni ina da mara lafiya mahaifina bashi da lafiya kuma ni nake jinyarsa."

Kaina a kasa nake maganar ina kokarin mayar da hawayen dake kokarin zubowa.....shuru gurin yayi na kusan minti biyar kafin ya dago kansa ya kalli su Haruna da fad'in"Ku tashi kuje." Da sauri suka mike suna mika godiyarsu a gurinsa

Bayan barin su Haruna daga gurin na kai minti goma a tsaye be kula ni ba, sai duba wayarsa yake yi fuskarsa a murtuke. gabadaya naji gwiwowina sun sage na kalleshi inaso nayi magana ido muka hada dashi gwarjinsa ya hana ni cewa komai.

"Kina nufin kina tsaye 'kerere a kaina zanyi magana dake."? Ciki ciki ya fadi maganar, zubewa nayi gwiwa a kasa nace" Ranka ya dade a gafarce ni wallahi hankalina ne gabad'aya yana kan mahaifina."

Ajiyar zuciya yayi ya mike zaune had'e dayin wani irin zama na saurata hannunsa ya d'ora kan gwiwarsa, na kalli hannun yatsunsa guda uku na sanye da zubonan azirfa masu kyau sake sunkuyar da kaina nayi ina jiran jin ta bakinsa. kallona yayi a ya mutse yace."Mai yake damun mahaifin naki."? Da sauri nace" Daya daga cikin masu duba lafiya ya tabbatar mana da cewar hawan jini ke damunsa tsayin wata daya yana fama amma dai yanzu da sauki tunda an d'orashi akan magani.

Shuru gurin yay bayan na gama maganata, ya dinga kallon 'kasan kafet din da yake zaune kamar ba zaice komai ba daga bisani ya d'ago kansa tare da fad'in "Inaso kiyi min jagora 'bangaran naku domin na duba mahaifin naki."

Kallonsa nayi ina mamakin maganarsa, girarsa dake cike da gashi ya d'aga min domin so ya tabbarar min da maganarsa.

Nace"Babu damuwa ranka ya dad'e idan ka shirya zuwa yanzu sai nayi maka jagora." Ina d'urkushe a gabansa ya mi'ke a nutse yasa takalminsa yace."Tashi muje." Da sauri na mike ina karkad'e jikina.

Tsayawa nayi ina jira yayi gaba nabi bayansa ya nuna min hanya da hannunsa ba tare da yace komai ba na fahimci abinda yake nufi da sauri nayi gaba ya rufa min baya.


Yanayin tafiya ta da tashi ba daya bane koda na waiwaya sai naga nayi masa nisa sosai d'an tsayawa nayi ina jiran zuwanshi.....Bangaran shi kuwa tafiya kawai yake amma hankalinsa tuntuni ya tashi sakamakon yanayin tafiyar da takeyi sassan jikinta na motsawa mazaunanta ba 'karamin tayar masa da hankali yayi ba hakan ya sake sanya masa rashin kuzari da karfin jiki ya dinga tafiya tamkar wanda 'kwai ya fashewa a ciki gabad'aya sha'awarshi ta tashi yana so ya samu yarinyar da zata d'ebe masa kewa.

Sai da ya kusa zuwa dab dani sannan na juya na cigaba da tafiya.....Yarima Ali ajiyar zuciya ya sauke ya tsirawa faffad'an qugunta ido wanda yake juyawa cikin zanin kamfalar dake jikinta........ajiyar zuciya ya dinga saukewa yana kokarin danne abinda ke taso masa.

Koda muka shiga gurin namu Tambaya dake bakin rijiya tana wanke kwanuka mikewa tayi da sauri ganina tare dashi yasa hankalinta ya tashi tana tsoro ko wani abu ne ya faru, ganin ta razana yasa nace"Ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru Yarima zai duba jikin babana ne."

Zubewa tayi gabansa tana gaisheshi gami dayi masa godiya. Cikin sanyin murya ya amsa tare da bata umarnin mi'kewa.
Na kalleshi a nutse nace"Ranka ya dade bisimillah ka shigo." Takalmansa ya cire a nutse ya rankwafa domin shiga dakin dake gajeriyar kofa ce shi kuma ya kasance mutum mai tsayi shine dalilin da yasa ya risina domun shiga dakin.

Guri na shiga karkad'ewa wai ko zai zauna, sai naga yaja ya tsaya yana kallon babana dake kwance yana bacci.....Cikin rawar baki nace"Ka ganshi ko wallahi yana jin ji......! hannu ya daga min alamanun baya bukatar maganata, nayi shuru ina kallonsa sai kallon babana yake kafin ya kalleni yace"Ina maganin da kuke bashi."?
Da sauri na dauko na mika masa, ya jima yana duba magungunan kafin ya miko min da fadin"Kada ku sake bashi maganin ku ajeshi zamuje yanzu nasa Haruna ya samo masa wasu insha Allah zasuyi masa."
Da sauri nace"To mungode shima na hausan da muke bashi mu daina."? Kallona yayi da sauri yace."Bayan wannan maganin akwai wanda kuke bashi."? nace."Eh akwai na hausa wanda na kar'bo gurin masu maganin gargajiya."

Tsaki! yaja da fad'in"Jeki dauko min maganin nagani." Na mike da sauri na fita tsakar gida na samu Tambaya ta gama wanke kwanuka tana tsaye jikin bango (garu)ta rungume hannuwanta a kirji.
"Tambaya ina maganin da ki'ka jiqawa babana." Da sauri ta shiga wani daki dake tsakar gidan ta dauko maganin cikin bokitin roba madaidaici karba nayi da sauri na shiga dakin, na mika masa .

"Ajiye ki bud'e nagani." Ajiyewa nayi a kasan guri nayi yanda yace. Ni dashi gabad'aya tsirawa maganin ido mukayi ganin yanda yake wata irin kumfa ga wari na tashi a cikinsa.
Dauke kansa yay rai a b'ace yace."Rufe." Jiki a sanyaye na rufe ina kallonsa, Yace."Wannan maganin kwanansa nawa a jiqe."? a sanyaye nace"Zai kai sati biyu." Cike da taikaci yace." Waye ya fad'a miki ana had'a maganin hausa dana bature a tare? shuru nayi kaina a kasa.....Ya cigaba da cewa"Magani kun jiqa shi tsayin sati biyu yana kumfa wari na tashi a cikinsa amma kuna d'irka masa so kuke ku kasheshi."? Nayi saurin kallonsa ina girgiza kaina. Yace."To ko dan gaba ba'a hada maganin hausa dana bature a tare sannan kuma idan kun jiqa maganin hausa to kuyi amfani dashi a lokacin idan ya kwana daya biyu ku zubar dashi domin ya tashi a aiki amma magani tsayin sati biyu a jiqe kuna bashi dole ku kasa gane kansa.

Nace"Kayi hakuri zamu gyara insha Allah.'' Shiru yayi ya sunkuyar kansa 'kasa, na dinga satar kallonsa ina mamakin wannan d'abia tashi bini bini kallon 'kasa sai kace makaho........"Anjima bayan isha'i ki shigo ki kar'bar masa wasu maganin insha Allahu zai samu lafiya." Murya na rawa nace"To mungode ranka ya dade."
Ba tare da yace wani abuba ya rankwafa da niyyar fita daga dakin........Bayansa nabi naga suna sallama da tambaya, har soro na rakashi ina godiya uffan bece min ba har ya fita daga zauran namu.....na koma cikin gidan da sauri na shiga yiwa Tambaya bayani da yayi akan maganin gargajiyar da muka jiqa.
*BINTA UMAR ABBALE*

Kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_





*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
21&22
Sai bayan dana idar da sallar isha'i tukkuna na shedawa Tambaya maganar komawa ta 'bangaransa da aiki. shuru tayi tana nazarin al'amarin tace"Sumayya dole ne mubi umarnin masarauta bamu da za'bi sai abinda suka ce damu saboda haka na umarce ki kije ki kula da Yarima bisa amana ki kyautata masa kamar yanda zaki kyautatawa iyayenki." Nace"Tambaya babu wanda nake ji sai babana ki duba kiga halin da yake ciki gashi kema bakya zama sosai kullum kuna gurin girkin abinci bana so a barshi shi kadai a gidan shiyasa wallahi tunda naji maganar hankalina ya tashi."

"Sumayya duk abinda Allah yayi nufun zartarwa akan mahaifinki to ko muna nan ko bama nan bamu isa mu hana Allah ikonsa ba, saboda haka ki nutsu ki kwantar da hankalin ki cuta ba mutuwa bace insha Allah Allah zai tashi kafad'unsa."

Shuru nayi ina sa'ke-sa'ke a cikin raina.
Tace"Tunda kinyi sallah sai kici abinci ki tafi kada ki 'bata lokaci a samu matsala.
A sanyaye naje na 'Dauko kula ta abincin na had'o da plate na zauna inda na tashi abincin na zuba a plate nayi bisimillah a nutse na fara ci, Tambaya miqewa tayi ta nufi inda mijinta yake kwance, a hankali ta shiga kiran sunansa, bude idonsa yayi ya kalleta a hankali ya mayar da idon ya rufe, tace"Malam kaji maganar da muke tattaunawa ko.'' ? idanunsa ya bude ya kalli gefan da nake zaune ina cin abinci.
A sar'ke yace"Sumayya kibi umarnin masarauta ko bayan babu raina bance ki bijirewa masarauta ba domin baki da wani tushe sai ita iyayenmu da kakannimu duk a k'arkashin masarauta suka rayu a haka duk aka haife mu saboda haka nake umartar ki da cewar kiyi biyayya kamar yanda kika ga munayi a matsayin mu na iyayenki."

Muryata na rawa nace"Baba dan Allah ka daina maganar mutuwa insha Allahu zaka tashi ka cigaba da sabgogin ka cuta ba mutuwa bace." Murmushi yay yace."Sumayya kenan to ina rokon ubangiji Allah ya tashi kafad'una na cigaba da rayuwa a tare daku.'"
murya na rawa nace"ameen baba Allah ya baka lafiya." amsawa sukayi da "ameen" na mike na fita domin wanke hannuna.

Lokacin dana shiga dakin Tambaya na kokarin mikar dashi zaune domin ta d'aura masa alwala taimaka mata nayi mukayi masa alwalar ta gyara shi sosai yanda zaiji dadin sallah ya tayar da iqama a nutse! kallona tayi tace"Kiyi maza ka tafi mana." Sai Naji zuciyata ta karye tunda na taso ban ta'ba zuwa ko'ina na kwana ba kullum ina tare da iyayena
A sanyaye na juya ina goge hawaye da hannuna nace"Na tafi." Itama tambayan cikin alhini tace"Sai da safe." Jin kuka naso ya kufce min yasa nayi gaggawar fita daga dakin, takalmana dake bakin kofar dakin na zura na fita daga gidan.


Haruna da su Isa na samu a falon suna aikace aikace, gaisawa mukayi na nemi kan kujera na zauna ina rarraba idona a katafaran falon nashi daya gaji da had'uwa, ko wace kusurwa hotonshi ne a manne wani da manyan kaya na sarauta wani kuma da 'kananun kaya cikin hotonan nasa babu wanda yayi dariya a ciki fuska a murtuke tamkar wanda akayiwa dole gurin daukar hoton, muryar Haruna ce ta katse min tunanin da nake, na kalleshi inaso ya sake maimaita min abinda yake fad'a, Yace."Sumayya ba zama zakiyi ba zaki hau sama ne ki bubbuga idan ya bude sai ki sheda masa isowarki idan da akwai abinda yake bukata kiyi masa sai kiyi mu dai mun gama aikin mu zamuje mu huta sai ya b'ukace mu.'' Na kalleshi da fadin"Ina ne d'akin nasa."
Wata matattakalar bene ya nuna min da fadin''Kina kaiwa karshen benan za kiga wata kofa mai biyu nan ne d'akinsa sai ki danna wani abu a jikin kofar zai yi magana.

Nayi shuru ina sa'ke-sa'ke mi'kewa nayi na kama hanyar benan, da k'yar nake hawa benan sabida santsin ties d'in ina hawa ina ri'ke sandar benan gabana na fad'uwa! ajiyar zuciya na ajiye bayan na gani a kofar dakin
Sai da na daidaita nutsuwa ta tukkuna na danna abinda zai isar masa da isowata. shuru ba'ayi magana ba, nasa hannu akan abun na latsa da kar'fi! Naji muryarsa yana fad'in "Wanene." "Nice Sumayya.'' Murya a hard'e na fadi maganar. shuru har tsayin mintina goma bai bude ba jikina yayi sanyi kamar nayi tafiya ta sai dai na daure na cigaba da tsayuwa, motsin bude kofar naji nayi saurin ja gefe tare dayin kasa da kaina, koda ya bude kofar ban kalleshi ba nace" Barka da dare ranka ya dade."

"Barka dai shigo ciki." Yafada tare da juyawa cikin dakin. Dago kaina nayi da sauri na mayar dashi qasa sakamakon ganinsa da nayi d'aure da towel gabana ya dinga bugawa kasa shiga dakin nai nayi tsaye a bakin kofar ina tararrabi."

Zama yay gefan bed dinshi yana kallon bakin kofar, "Ke! ki shigo nace dake."! A tsawace ya fad'i maganar, shahada nayi na shiga yace." Kulle kofar." hannu nasa na tura kofar dakin ta rufe, tsayuwa nayi jikin kofar kaina a qasa nace"Ranka

Please Login or Register in order to submit comment