Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a dadare saboda rashin sabo, abinci kowa yaje ya dauki nashi, Nima aka Miko min wani Dan mitsitsi cikin karamin roba, na karba na aje Amma naki ci saboda bana ma jin Yunwa, suna Gama ci Siyama ta janyo nawa ta cinye, Mino na Mata magana Ummaah tace ta barta dama ni na xo na datse musu abincin su. Yaya ya dawo da kifi a Leda ya dauki abincin shi yace nazo naci me kifi, ni Kuma since from childhood bana ketare tayin kifi saboda yadda Abbu ya Saba min cin kifi kullum se mun ci a dinner. Ina ganin Kifin naje na zauna Siyama ma ta taho ya dinga bamu muna ci har ya Gama naje nace ma Ummaah ta wanke min hannu, ruwa kawai ta zuba min na cuda tace naje, nace Mata ai se an saka detergent sanann zai fita, se ta koreni Wai Ina Mata iyayi. Ban wani Kara sakewa ba saboda karnin da hannuna yake na dameshi ya maida ni gurin Abbuna.

" Jarabar ka tasa ka dakko ta,seka maida ita ai"

Ya Mike ya Kama hannuna muka tafi, Ina zuwa na samu Abbu ya fita, se na zauna wajen Hajiya Ina Mata hirar school, se dare ya dawo da Kifin shi. Naci nayi bacci, bayan fita ta Hajiya ta nuna Masa lallai ya kamata ya kaini maiduguri Koda su Basu neme ni ba to shi ya kamata ya Kai ni na gansu, idan sun cigaba da nemana kansu idan Basu Kara ba shi dai ya sauke wannan nauyin. Washegari muka tafi Kano muka bi flight zuwa maiduguri, ya kaini na gaida kakkani na duk sunata borin kunyar Wai Basu San min koma Abuja ba, se zuzzuta yadda na girma nake Kama da Mama suke. Akazo zau tafi na dinga kuka bazan zauna ba hakan shima ya hakura muka tafi tare. Kawata Dana fara Yi a school namesake Dita ce, sunan ta Amina Abubakar Rogo, gari kadai ya banbanta sunan mu. An tashi school drivern mu duka Bai zo daukar mu ba, muna zaune inda muke Zama mu jira na Bata book Dina Wanda tsayin shi bazai Shiga cikin backpack Dita ba haka itama, inda water dispenser ke aje naje na tsiyayo ruwa nasha sannan nayi discarding cup din sannan na dawo na karba book Dina, kafin na zauna Nanny ta shigo cikin sauri, nayi sauri na nufe ta Ina rungume ta nace

" Nanny!"

Ta shafa kaina ta karba book Dina, da food box dina da Kuma backpack Dita nayi waving Amina muka tafi. Tun cikin mota nake Mata complain Yunwa nake ji, tace ai ta Gama abinci, nace Mata Abbuna ya dawo tace ai yace se dare zai dawo. Muna zuwa gida na wuce dakina da gudu na dauki waya nayi dialing wayar office din Daddy, Yana picking nace Masa yaushe zai dawo yace nayi hakuri naci abinci zai dawo da daddare, ba yadda naso haka na yadda mukai sallama. Akazo wanka nace ni fa da kaina zanyi da kyar na yadda Nanny tayi min.

Ina zaune Bayan maghrib a dakina na tasa drawing book a gaba dasu pencil colors da water color Dole se na zana picture Mama da Abbuna dake rungume Dani on my first birthday,

" Where's my princess?"

Naji muryar Abbu Yana tahowa dakina, na yadda drawing book din na taho a guje gurin shi na rungume shi, ya daga ni sama ya wulla ni ya cabe nayi dariya na rungume shi. Tare mukaci abinci sannan na raka shi yayi Dan walk cikin compound dinmu sannan Muna dawowa Nanny ta min wanka yazo ya zauna gefena Yana tambayata yadda school ta kasance a hakan nayi bacci sannan ya tafi. Haka yake min kullum indai Yana gida to zai zauna side bed Dina har se nayi bacci. My father my world!




AFIYYA is not free, pay 300 into 3091721807 A'isha Hassan kwalam, first Bank of Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258.




Shatttzzzx
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: 💔 AFIYYA 💔

Four (Free)

✍️ Ayshatuuu



Karfe takwas malamin dake zuwa yimin karatun islamiyya yazo, an riga anyi min wanka nan ma se da akai rigima Dani Dan seda Abbu yazo yace yayimin alkawarin ranar birthday Dina ranar Zan fara wanka da kaina, I was super happy na yadda Nanny tayimin , ta shiryani cikin riga da skirt na lace, tea ta bani Nasha sannan ta rakoni parlor na zauna bayan na Gama gaida malamin, gaba daya karatun na one hour ne sannan ya tafi na cire hijab na dawo daki na tafi gurin Abbu. Na samu ya Gama shiryawa for breakfast so a dakin shi muka ci abinci. Bayan mun Gama yace na dakko home work Dina se muyi tare dashi, na wuce dakina na kawo backpack Dita da dayan littafin, Yana dauka yace

" Princess wannan ba littafin ki bane ai"

Na karba littafin daga hannun shi trying to confirm, dama ban iya spelling Ringim ba amma nasan six letters Suka hada ringim, ni Kuma gashi Naga four letters, sauran sunan irin nawa ne. Nayi shiru se can nace

" Abbu canjawa mukai da Amina da Zan Sha ruwa"

Ya dafe kanshi sannan Bai ce komai ba ya Ciro waya ya Kira class teacher din mu, ita ce ta fada Masa address din gidan su Amina, yasa Nanny ta canja min casual wears din jikina zuwa wata English gown, aka saka min hula da takalmi, tayimin packing chocolate kamar yadda Abbu yace a bani nakai wa Amina. A garki suke nan muka je, Abbu yayiwa security din bayani, Babu jimawa Sega wani mutum ya fito, Yana zuwa ya gaida Abbu yace mu shigo, Yana fada Masa su Basu ma gane cewar Amina ba book dinta ta kawo ba. Ciki mukaje tana ta Wasa da siblings dinta, seda ta ganni sannan ta taho hade da Jan hannuna nayi Wasa, Dole Abbu ya tafi ya barni a gida se yamma ya dawo ya tafi Dani, that's how Maman Amina ta Zama a figure a cikin rayuwata.

Duk Sunday Abbu zai kaini salon, zaa wanke kaina sannan a yanke min farce, ayimin kitso, idan na zauna Baku labarin yadda Abbu ya kula Dani Zan karar da duk wani karfina kafin na shiga gundarin labarin. Abbuna ya min duk wani Abu da uba da uwa zasu min, akwai abubuwan da kake rasawa kake samun makamancin su Amma nikam har na koma ga Allah nasan bazan samu madadin Abbu ba. Rooks cousin dita ce, mahaifiyar ta ita ce Mummy Maryam, kanwa wajen Abbu. Mijinta Dan sarkin Ringim ne Daddy. Tun da ta haifi Rooks ya samu aiki a NY se ya tafi dasu can dama field din daya karanta was international relations. Ban Santa ba se lokacin da nayi birthday Dina na shekara takwas Abbu yace zai kaini Newyork gurin Aunt dina. Banyi wani murna ba saboda ni nafi son kawai na zauna a gida Ina gannin Abbuna. Ya Mana Visa komai dasu passport ya zama ready mukaje Ringim nayi ma Hajiya sallama, se muka biya Kano wajen Uncle Tijjani Abbu ya kaini Naga Basma da Bata wuce 40 days ba. Tunda Naga yarinyar nayi tama Abbu shagwaba Nima se ya siyo min Baby, se da Anty Salma tace min naje idan na dawo zata hada Mata Kaya se na tafi da ita gidan mu. Bamu Kara kwana uku a Nigeria ba muka wuce NY, Mummy tazo airport ta dauke mu, Rooks na makaranta, inata kallon gidan, da dakin Rooks din komai na fulla ne yayi kyau sosae. Na dinga kalla with so admiration a idanuna Ina fatan inama nawa dakin haka yake. Mummy ta shigo tana min murmushi tace

" So daughter."

Na matso inda take na zauna ta shafa kaina tana ta murmushi tace

" Feel at home, Rooks ba zata Jima ba zata dawo. Yaya yaje ya huta zai dawo kinji"

Na gyada kaina Ina rarraba idanuna na rashin sabo, abinci ta kirani naci a parlor, Ina fara ci se ga Daddy da Rooks sun dawo, da gudu ta shigo hannunta dauke da backpack dinta, ta rungume ta tana shafa kanta tace Mata

" Afiyya tazo"

Ta juyo ta kalleni sannan ta kalli mamanta, se Kuma ta wuce dakin ta. Abbu yazo da daddare har lokacin bamu magana da Rooks ba kamar she's not happy nazo gidan su, Abbu washegari ya tafi ya barni shima seda aka fita Dani Dan da ya dawo kuka nayi tayi Bai zo ba. Kwana biyu na sake jiki itama Rooks ta saki jikinta Dani, seda nayi sati uku anan kafin na koma gida,shi ne mafarin sabon da mukai da Rooks.







Rayuwa ta cigaba da tafiya, Junaidu har ya Kai matakin shiga karamar secondary, Babu Kuma abinda ya sani haka dai kawai akai gaba dashi ya bar makarantar ko Allah zaisa su huta. Babu jimawa karatu ya kankama nanma ya bude sabon babin iskancin shi, baya zuwa makaranta ko Kuma yazo a makare Kuma kafin a tashi ya sallami kanshi, anan ma ya fara hada gang na bad boys Yana koya musu duk abinda ya iya. Ana haka ya shiga aji biyu daf da karshen term akai fada a gidan su. Ya dawo da yamma ya cake da abubuwan da yake zuka, Yana shigowa gidan Ashe Fatima ta bawa yarta zainab ta siyo Mata kayan Miya, yarinyar wani ya karbe kudin a hanya tana zuwa gida tace ai Junaidu ya karbe kudin. Tunda taji zance tace ai wallahi ko kasa da sama zata hade se an biya ta kudinta ta gaji da dibar albarkar da yake musu a gidannan, jiya ya daki yayanta kawai darajar zaman tare yasa ba tayi magana ba, yau Kuma gashi ya kwace kudi a hannun yarinya, me ake da haihuwar irin su, da kamar Dan Allah bani, inama da akazo haifar shi barin shi akai... Maganganu marasa Dadi Hajja Huwaila na gefe tana bakace ko dago kanta batayi ba balle ta maida martani, a ranta fada take Dan kuka me jawo uwarshi jifa, Hasiya ta fito ta kalla Fatima da har lokacin Bata bar mita ba tace

" Ke kuwa kin tabbatar shi Junaidu ya karbe kudin, kinsan yarannan sun iya karya"


" To idan bashi ba waye, shi din bako ne a gidannan da ita zainab zata kasa gane fuskar shi?"

" Ba bako bane Fatima Amma maganganun da kike fada sunyi nauyi da yawa mahaifiyar shi fa ta nan, ai da kunya"

Ta tabe baki yace

" Wannan ku ya Dana, tunda ta Haifa se ta bada tarbiyya tunda ta gagara bayar wa se ta bude kunnuwa ta saurari me zamu fada kudina se an biya ni"


Kafin Hasiya tayi magana se Suka ji maganar Junaidu a zaure yana fadin

" Zan babballa kashin ki wallahi shegiya me Kama da mayu, kin tashi ko Sena hada Miki jini a fuska"

Da gudu salama ta shigo, tayi Bayan Fatima wadda ke tsaye tana jiran taga da wa yake, shigowa yayi a lokacin kana kallon shi kasan yasha wani abun, gaba daya idanun shi sunyi jawur tafiyar shi ma Babu nutsuwa, dakin Hajja ya nufa Fatima da ganganci se ta rike Masa riga,

" Allah ya Toni asirinka, se ka fito min da kudina kafin na mare ka a gidannan"

Ya kalleta sannan ya kalli hannun ta da ta Kama rigar shi ta rike gam yace

" Ke dallah sakeni, wanne kudi kike magana anan?"

Ya fada Yana kicinayar kwacewa, ta Kara rikewa tana fadin

" To meye Dan kace min dallah Naga uwar data haifeka baka gaishe ta, ka Zama Dan shayeshaye meye Dan ka zageni, kudi se ka fiton dashi"

Hannun shi yasa ya doke nata yayi gaba abinshi, Amma Bata hakura ba tabi shi ta Kara Kama shi, a zuciye ya juyo Yana juyowa ya hambare ta, aikuwa se gata a zube a kasa, har mamakin karfin Junaidu nake, yayanta sukai kanta, Hajja Huwaila ta mike itada Hasiya sukai kanta, bakinta da hancin ta se jini suke saboda makewar da yayi Mata. Dake salama tafi wayo tana ihu ta tafi ta Kira Malam dake dakin shi, aikuwa ya fito lokacin an maida Fatima daki se kuka take wallahi ba zata yarda ba, Malam ya shigo ya tsaya yayi Shiru ya rasa me zaice saboda yadda zuciyar shi take kamar zata fito ta bakin shi. Hajja Huwaila daki ta koma ta sameshi yayi daidai ya ware fanka Yana bacci, ta daka Masa duka, ya bude idanun shi yayi tsaki ganin ita ce, ya juya Dan gyara kwanciyar shi ta fara fadin

" Tashi ka fitar min daki na, kaidao Allah ya wadaran halinka, bakai halin arziki ba San"

Dake ba fada ne da ita ba,shi kanshi a sanyaye take fadar hakan. Ya Mike ya nufi tsakar gida zai fita sega Yan sanda sunzo Kama shi Wai Fatima yayanta Ashe DPO ne anan division din Kazaure.





Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, Aisha Hassan kwalam, First bank of Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258



Shatttzzzx💔 AFIYYA 💔

Five (Free)

✍️ Ayshatuuu



DPO ya turo yaran shi akan suzo su tafi da Junaidu, kunsan yadda Yan sanda suke na Nigeria kamar haushi dama suke ji balle Kuma an tabo kanwar DPO Kuma kunsan se inda man su ya Kare, suna zuwa sukai handcuffing din shi Suka tafi dash, mutane suka taru a kofar gidan Dan ganin kwakwaf, malam Yana ciki ya tasa Fatima a gaba ya zuba Mata idanu, ita Kuma ta bawa banza ajiyar shi. Da ya tabbatar ba zatai magana ba se yace Mata

" Nayi tunanin hakurin da na baki zakiyi hakuri kiga hukuncin da Zan yanke, Amma kin nuna min kinada Dan uwa"

" To Malam Naga kaima dai Junaidu a gidannan ya gagare ka, kana kallon dukan da yayi min da da karar kwana sede a Kira ka ace maka na mutu"

Bai ce Mata komai ba ya fito daga dakin nata, Kan shi har juyawa take saboda yadda ran shi yake a bace, dakin Hajja Huwaila ya nufa ya sameta tana kuka Hasiya na gefen ta

" Hasiya ni nasan Junaidu Bata jin magana Amma nasan bazai karba kudi daga hannun zainab ba, idan sata ya fara daga dakina zai fara..."

Hasiya tace

" Yanzun duk wannan ba wani amfani, kizo muje mu samu Malam ayi bailing shi"

Ta girgiza Kai tace

" A'a gwara a barshi su daka yadda itama Fatima zata ga an Rama Mata, ni abinda ya Bata min Rai Sharron Sara, wallahi Dana haifi barawo gwara ace kaf garinnan yafi kowa shaye shaye"

Anan Malam yayi gyaran murya yayi sallama ya shigo, Hasiya ta Masa sannu sannan ta fara kokarin fita ya dakatar da ita, seda ya zauna sannan yace da Hajja

" Kukan me kikeyi? Addua Zaki Masa Allah ya shirya ki Amma kukan ki kamar karar shi kike wa Allah"

Ta goge hawayen ta amma Bata ce komai ba, ya dubi Hasiya yace ta Masa bayanin abinda ya faru, tiryan tiryan ta fada Masa, ya Gama ji sannan ya fito ya kwallawa zainab Kira, tana dakin Babarta ta fito, yace ta biyo shi daki. Idanunta sunyi raurau ta bi Bayan shi zuwa parlon shi. Seda ya zauna sannan ya fara takbayarta cikin lallami Wanda ya karbe kudin a hannunta, se tace Masa kudin ne Suka Fadi ita Kuma tasan mamanta zata dake ta shiyasa tace Junaidu ne ya kwace. Ya Mata fada sosae akan karya da Kuma husumar data hada a gidan sannan yace ta tafi.











Bayan mun dawo daga NY da sati daya na koma makaranta, Abbu ya maida min dakina na Barbie kamar yadda mummy tace mishi, dama naje makaranta ne Ina dawowa Naga har wallpapers duka an canja min, na dinga ihun murna Ina dariyar farin ciki, Nanny na zaune sede tayi murmushi kawai tana kallona. Da ya dawo na rungume shi nace

" Abbu kaga dakina yayi kyau, ya koma na Barbie!"

Yace min haba dai? Na jashi inata nuna mishi se yace shi ya saka aka gyara min, na Kara rike hannun shi nace

" Abbu thank you!"

Ya shafa kaina yace idan nayi addua na dinga cewa Allah ya jikan Mama ya Mata Rahma, ban taba manta wannan maganar ba Kuma duk abinda zanyi se na Yi Mata wannan adduar. Da sati ya Kama ne ranar Saturday Bayan islamiyya classes Dina nayi home work, mukai Baki, ban taba ganin su ba so banma sansu ba. Har parlor Abbu ya kawo su Ina zaune kan sofa Ina kallon cartoon din Bob the builder a MBC 3. Suna Zama na gaishe su, daya daga ciki ya dubi Abbu yace

" Ta girma Babyn, Allah ya jikan Halima"

Abbu yayi murmushi Yana shafa kaina dake gefena ya zauna yace

" Lokaci gudu yake Yi ne, gashi ta kusa Gama primary na"

Suka gyada kansu in agreement da abinda Abbu yace Suka fara hirar mutuwa, nidai anan nayi bacci jikin shi.

" Nasan ba lallai sakon da muka zo maka dashi yayi maka dadi ba, Amma Babu yadda zamuyi muma Yan aike ne"

Abbu ya gyara Zama Yana sauraran kawu na, kanin Mama ne

" Munyi shawara last week se muka ga ya kamata ace min karbi Afiyya daga gurin ka, she needs a mother's care"

Abbu yayi murmushi yace Yana kallona

" Afiyya Bata bukatar wannan, nasan ko na amince ku tafi da ita ba zata zauna ba balle ma Nima bazan bada ita ba gaskiya saboda lokacin da nake tunanin zaku karbe ta Babu Wanda yace zai karba, yanzun Kuma ita kadai nake gani na cigaba da rayuwa. Kuyi hakuri Zan dai dinga kawo ta Dan ta Saba daku, Kuma se ku dinga zuwa yadda zata gane ku"

" I knew bamu kyauta ba, a lokacin idan mu karbe ta gani muke it will break you more, shiyasa muka bar maka ita, to yanzun ta fara girma she needs a mother ba komai zaka iya Mata ba"

Ya girgiza Kai yace

" Afiyya needs only me, akanta tasan batada uwa ni ne ubanta ni ne uwarta, bana son na dagula Mata lissafi Kuma. Beside Kun riga kun  Yi missing chance din ku na rike ta"

Duk yadda sukai Akan Abbu ya Basu ni yaki, they threatened him Amma dukda haka yaki amincewa haka suka tafi ko abincin da aka hada musu Basu ci ba. Wannan shi ne abinda ya fara hada gaba tsakanin dangin mamata da Abbu, su a ganin su duk lokacin da suke so suna da right su karbe ni shi Kuma ya nuna musu akasin haka. Daga wannan se suka shafe batuna cikin rayuwar su Suka manta cewar suna da ya a wani gurin. Shima Abbu se ya tattara su ya kyale su kawai ya zuba musu idanu. Rayuwa ta cigaba da tafiya har na Gama primary school dina. A wañnan hutun Abbu ya dakko Hajiya dani da kawu Sa'idu da Nanny muka tafi saudiyya aikin hajji, acan muka samu Uncle Babawo yazo daga Central Lancashire inda yake msc acan. Tunda yazo kullum zamu tafi harami gurin shi nake zuwa ya rike ni, har Hajiya na cewa Uncle Babawo ya kwace wa Abbu na ni, ni Kuma Kama take min sosae da Abbu, though bani kadai na fada ba, kamar su day Abbu ta baci shiyasa nake son shi, Sabida I see my father in him. Da muka Gama aikin hajji se ni da Abbu muka tafi Paris saboda yayi min alkawarin zai Kai no Naga Eiffel tower. Harda Uncle Babawo muka tafi sauran Suka juya Nigeria. Kwana nan mu uku muka koma Nigeria muma. Nigerian Turkish college nan na samu admission nayi joining Js1 din, har lokacin tare muke da Amina tunda babanta ya tambayi Abbu se yace Masa ai Turkish college zai kaini shima se ya nemawa Amina can muka tafi tare. Baa boarding muke ba day mukeyi, so Abbu se yasa driver kawai yake daukar mu ya kaimu, har gida muke zuwa daukanta mu maida ta, ita Kuma duk ranar Friday Mom dinta zata zo ta dauke mu muje gidan su na wuni. A kwana a tashi kullum rayuwa tafiya take, ni ina Kara girma kamannina suna Kara fitowa da mamana, idan ka ganni sak uwata, komai nata irin nawa ne. Tamkar tayi kaki ta tofar haka nake da ita.




Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria. Send evidence through 09063467258





Shatttzzzx💔 AFIYYA 💔

Seven (Free)

✍️ Ayshatuuu



Bayan Malam ya Gama sauraron duk bayanan zainab se ya sakata a gaba Suka tafi police station Dan ita kadai ce zata saka ayi bailing Junaidu. Tunda dama it's din ta hada husumar so seta Zama wadda zata warware ta. Lokacinda Suka Isa gaba daya Junaidu ya canja kammanni saboda dukan da ya Sha, tunda Suka shiga DPO yace a lallasa masa shi har se ya gane baa dukan mace. Ga Junaidu da bakar zuciya haka yaki Basu hakuri se amsar dukan yake. Malam na Isa yayi ma officers din dake tsaye a reception bayani,  daya daga ciki yace Masa

" Malam kawai ka tafi Dan bansan ranar belin wannan gaggararren Dan naka ba"
Malam ya gyara tsayuwan shi yace

" Idan ba zaku damu ba Ina son magana da DPO din ku"

Daya daga ciki yace

" DPO baya gari yaje headquarter acan Dutse"

Malam ya gyada Kai yace

" Idan ba zaka damu ba ko Zan samu num..."

" Baya cikin aiki, kaga Malam Muna ganin girmanka a gurinnan, tunda munce ka wuce kawai ka tafi"

Malam ya Kama hannun zainab Suka fita a station din, haihuwa kenan sanadin ta Babu abinda bazai same ka ba walau sharri walau khairi, shi Bai taba zuwa police station ba Amma dalilin Junaidu yau shi ake cewa ya fita duk girman shi da darajar shi.

" Ai da ka sani ka tatse shi wallahi, malaman nan kudi be dasu, yaran Yan siyasa ne fa"

Dayan yace

" A'a gwara dai a kyaleshi saboda wannan Yana da connection da manyan mutane kada mu jawa aikin mu"

Yana zuwa gidan ya tarar da fada ya barke tsakanin Fatima da Hasiya, Hajja nata kokarin raba su Amma sunki, sede suka hi sallamar shi sannan cacar bakin da suke ta lafa, Bai ce musu komai ba ya nufi dakin shi, Amma kowacce Tasha jinin jikinta, Hajja ta bi Bayan shi ta sameshi zaune ya kurawa guri daya idanu, he looks disturbed. Zama tayi tana fadin

" Malam kayi hakuri kada ka Bari abin Junaidu ya dameka, adduar shiriya ita ce zata rabamu dashi"

Ya gyada Kai Amma Bai ce komai ba hakan ya tabbatar Mata ba zaiyi magana ba, se ta tashi ta fito dukda tana son taji yadda aka Kare a station din Amma Bata son damun shi, Kuma alamu sun nuna baayi nasara ba, tunda ya shigo babu Junaidu. A tsakar gida taji zainab na fadawa Hasiya yadda sukai a station da officers din, hankalinta ya Kara tashi to Amma ya zatayi? Sai dai ta zubawa sarautar Allah idanu. Wasawasa magana se ta Zama babba tun Malam yana zuwa wajen police din suna Masa yawo da hankali har ya kyalle su, Fatima Kuma sunyi magana da DPO akan se Malam ya Bata hakuri sannan zai sake Junaidu. Ko fahimtar abinda take nufi yayi se ya kyaleta Bai ce da ita komai ba Amma se ya kaurace Mata, kwana biyu da tayi a dakin shi magana ta fatar Baki Bata hada su ba, hankalin ta yayi mummunan tashi, washegari wajen azahar se ga Junaidu an sako Shi, fuskar shi ta kumbura saboda duka, ga jikin shi da duk shatin bulala a jiki. Hajja Huwaila ta daura ruwan zafi tasa yayi wanka, ta gasa Masa jiki sannan ta shafa Masa man zafin da Hasiya ta kawo Mata. Yaci abinci ya kwanta a ranshi Yana saka next abinda zaiyi!











Na karasa gaban gadon tareda jijjiga Abbu, Amma a hakan nan dai yake kwance lifeless, Babu digon numfashi dake jikin shi, gaba daya jikin yayi sanyi, kwayar idanun shi a rufe tamkar me bacci, hakan ya tabbatar min daga baccin aka zare Masa Rai. Naja baya da sauri tareda rufe bakina da hannuna Ina jin ilahirin jikina Yana rawa kamar ana kada min mazari. Hajiya na kuka ta fita yayinda ni banyi kukan ba sede Ina tsaye a gaban shi Ina fatan Nanny ta buga min gefen gado na ta tashe ni tace min na tashi zanje makaranta, Amma ba mafarki nake ba, idanuna biyu it's happening in reality Abbu is no more.  Nayi shiru ban masan me zuciyata ke sakawa ba a wañnan lokacin, bazan iya Baku labarin yanayin da na shiga ba nasan dai I was more than shattered. Babu wata kalma da Zan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment