Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muku amfani da ita ta nuna bayyana muku halin da na shiga, Wanda kadai ya rasa iyaye shi zai fahimci me nake nufi. Ina nan a tsaye na fara jin koke koken mutane, Ina tsaye na tsira Masa idanu, Kawu Sa'idu da wasu daga cikin Yayan sarki Suka shigo, duka Ina tsaye aka fara kokarin shiray shi, nasan an ja hannuna an fita Dani, but bazan iya cewa waye ba, kowa kallon shi kawai nake na Zama tamkar statue. Gidan kafin wani lokaci ya cika dam da mutane, se kuka suke Amma gani nake duk yadda suke ji ba zai Kai yadda nakeji ba. Mummy Maryam da Rooks Naga sun shigo, ta rike hannun Mummy dake wani irin kuka tamkar ranta zai fita Amma Ina nikam nawa idanu ne. Seda aka fito dashi cikin makara sannan na Mike tsaye, Kawu Tijjani yazo ya rike hannun na idanun shi se hawaye ke fita yace

" So ki Masa addua"

Haka na bi bayan shi na zauna gaban gawar, my Father,my love, Abbuna, abokina, uwata da ubana? Shi ne a cikin makara ya tafi, ya mutu Kuma bazai dawo ba. Se na kankame shi na saki wani kuka me daci Ina fadin

" Abbu why will you leave me? Bansan kowa ba, you're my everything Abbu ya zanyi rayuwa yanzun..."


Na kasa karasawa saboda gaba daya na shide, ban Kara farkawa ba se Bayan awoyi goma da wasu abubuwa sannan na farka a firgice Ina Kiran sunan Abbu, Nanny dake gefena tayi saurin rungume ni a jikinta tana kuka, tana rungume ni nasan ita ce Dan haka na saki jikina na fara kuka bance komai ba Amma radadin da nakeji a cikin zuciyata ya wuce gaban na rubuta muku. Allah sarki Abbu ya tafi ya barni se nake jin inama Nima na mutu na huta, Babu abinda ke tsoratar Dani shi ne na tuna Wai Dole Zan rayu Kuma Babu Abbu.


A cikin gida an kaishi makabarta a wañnan yammacin, itama Hajiya tunda aka dawo da abinda aka lullube shi ta mike se kuwa ta yanke jiki ta Fadi, Babu shiri aka dauke ta se Kano asibiti, kafin suje ta rasu itama, Dan hakan mutuwar se ta hade Mana, ga ta Abbu ga ta Hajiya, kowa ka kalla kasan ba karamin blow sakon ya bashi ba, a lokaci guda Allah ya nufi tafiyar su! Rayuwa kenan. Kwana uku gida ya watse Nima aka sallamoni a asibiti , na dawo gidan kowa ya kalleni yadda na rame na lalalce lokaci daya se hawaye ya fita a idanun shi, fada min rasuwar Hajiya ta Kara daga min hankali Amma ban nuna ba Dan ko magana banayi, bana kuka se idan Babu kowa na zauna nayi kuka na share hawayena, a Rana ta biyar Yan maiduguri suka zo, suka Mana gaisuwa, Mummy da Nanny ke kaina wajen tabbatar da naci abinci Kuma Ina nan, wani lokacin ji nake kamar na gudu na fada ruwa Nima ace na mutu da wannan kuncin da nakeji a cikin Raina. Da zasu tafi sukace suna so su tafi Dani nan Mummy ta nuna musu ita zata tafi dani Dan hakan se suka Mana sallama suka tafi, wani lokacin Ina jin inama na bisu may be da duk haka Bai faru ba, to Amma idan na kara wani tunanin se Naga duk abinda ya faru Dani dama is already written in my book, Dole ne ya faru Dani. Ranar sadakar bakwai aka watse ranar nayi kuka Dan Ina zaune kowa ya dinga bajewa sede su shafa kaina su ce min nayi hakuri, nayi kuka na rashin gata, na rashin madafa na rashin sanin yadda rayuwa zata zo min. Abinda kadai ya rage min shi ne Nanny da Rooks. Nanny ta zauna gefena tace

" Ki ci abinci kinji, ko so kike kiyi rashin lafiya?"

Ina kuka nace

" Meye amfanin naci abincin, Abbuna ne ya mutu fa Nanny, banida kowa Nanny"

Ta rungumeni tana shafa min baya hawaye itama na bin fuskarta, tausayi na na dawainiya da ita, shigowar Mummy da Uncle Babawo yasa na Mike na nufe shi, ya rike hannuna Yana lallashina, se akai saa nayi shiru har Nasha tea. Fita sukai Shi da Mummy tace

" Ina ganin Zan tafi da ita kawai, kallonta is breaking my heart"

Ya shafa kanshi Yace

" Ita ce abin tausayi Kam, da nayi aure ni Zan dauke ta Amma Zan bar Miki kawai"

Washegari Suka zauan meeting akan fate Dina, Mummy ta dubi kawu Sa'idu da mamaki tace

" Yaya Sa'idu ni Zan tafi da Afiyya tunda kaga dama ta Saba da Rooks"

Ya dago idanu ya kalleta yace

" A'a ba zata je gidan wani ta zauna ba watarana ayi Mata Gori ni Zan rike ta"

Kawu Tijjani yace

" Eh da wannan dukda nasan Daddyn Rooks bazai taba haka ba, dama mafi Dadi ace mu mazan muka riketa. Sede Yaya ka Bari na tafi da ita kawai"

Ya Kara Bata fuska yace

" Ni Zan rike ta anan Ringim, magana ta kare"

Mummy ta hade Rai tace

" Yaya Sa'idu in har bazan dauki Afiyya ba to kaima ba zaka dauketa ba, Allah ya gani sede Tijjani ya tafi da ita, ya zaayi yarinya ta tashi a Abuja a dawo da ita Ringim"

" Ke wawiya ce Maryam, ke baa Ringim din aka haife ki ba? Mutuwa kikai da Kika girma anan. Kunji maganar banza"

Haka dai sukai ta musu aka tashi Babu dadi, Mummy tace musu Dole suyi fighting din Kawu Sa'idu ita Bata yadda dashi ba, washegari da suka je aka raba gadon Abbu, sannan aka raba na Hajiya nan ma yace se de a bashi nawa anan ne Uncle Babawo ya fito da will din Abbu kan dukiya ta ya damka ta a hannun Uncle Babawo haka kawu Sa'idu ya hakura. Bansan me ya faru ba kawai se dawowa sukai sukace Wai a gidan Kawu Sa'idu Zan zauna, Nanny ta bi Mummy dake ta kuka ganin Ina kuka Dan taji me yasa bazan zauna hannun daya daga cikin su ba, Mummy tace itama ba yadda zatayi she can't fight him. Ina ji Ina gani aka tattara kayana duka aka maidani gidan Kawu Sa'idu Kuma yace Nanny ta tafi maiduguri!




Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam first Bank of Nigeria, send evidence through 09063467258




Shatttzzzx💔 AFIYYA 💔

Eight (Free)

✍️ Ayshatuuu




Cikin kiftawar idanu na rasa koma, mahaifina, gatan da nake dashi da komai na tashi banida kowa da Zan kalla na Kira a matsayin Wanda zanyi kuka a kafadar shi. Ina zaune Nanny ta Gama hada kayanta taxo ta zauna gefena ta rike hannuna cikin barbarcin da take koya min Kuma na dauka sosae Dan duk maganar da zakai Ina ji, Kuma Ina mayarwa sede ba can sosae ba.

" Kiyi hakuri nasan komai zai canja, Amma kiyi hakuri kiyi addua, n samu kawun ki Tijjani jiya na tambaye shi tunda Anty Maryam Bata bani amsa ba, yace Yallabai yace su amince da duk hukuncin da kawun ki Sa'idu zai yanke, shiyasa suke Masa biyayya. Ki sani zamanki a gidan shi kamar biyayya kike ga Yallabai, kiyi musu addua Zan dinga zuwa duk lokacin da na samu dama. Ki rike maraicin ki kiyi amfani da illimin ki, kiyi hakuri Allah Yana tare dake..."

Nayi ta kuka da hannunta cikin nawa Amma ko sau daya ban manta abinda Nanny tace ba, haka Ina kallo ta tafi ko waiwaye babu, dukda ta hada min kayana tsaf tace da Mummy ita ba zata iya ganina na koma wannan gidan ba. Mummy da yamma ta Gama hada kayan su da Rooks Dan washegari zasu tafi NY, Muna daki na idar da sallar laasar, Rooks ta zauna gefena mukai shiru se can tace

" I'm going to miss you Afeey"

Na Dan Mata murmushi Amma bance komai ba, ta Kara gyara Zama tace

" Promise me duk halin da kike ciki Zaki fada min?"

Na Mika Mata hannuna nace Mata na Mata alkawari, shigowar Mummy tasa mukai shiru, ta zauna ya nade kafafun ta sannan tace Rooks ta fita zamuyi magana, haka ta mike ta bamu guri. Mummy ta Jima ta na yimin nasiha wadda na rike ta tsaf sannan tace duk abinda nake so na Kira su zasu bani. Nace Mata to , Bayan maghrib muka shirya se gidan Kawu Sa'idu, na taka zauren da kafata Ina jin kuncin a cikin zuciyata, tun a lokacin na fahimci duniya zancen banza ce, Babu wani Abu da zai daure. Suna zaune an kunna wasu kwayaye Yan kanana an sakale sun haska tsakar gidan, suna zaune akan tabarma Hafsa nata kuka, yayinda Mino ke wanki se Ummaah su na raba abinci, akwatina na da aka kawo tun Rana suna aje a gefe yadda aka barsu, mazan Basu nan. A hankali kamar kwai ya fashe min a ciki na tako na zauna gefen Siyama inda Rooks da mummy Suka zauna, ni na fara gaida Ummaah ta amsa tana cewa Mummy Bari ta karaso. A cikin su Babu Wanda yayi min magana Nima haka, seda ta gama sannan ta dakko kujera ta dawo gefen Mummy ta zauna, nayi jugum Ina bin gidan da kallo, Ina ayyana wacce rayuwa zanyi Kuma a gidan, gidan Kato ne sosae, sede anyi rashin basira a ginin, an bar katon tsakar gida Amma Kuma anyi dakuna biyu kawai se kitchen Wanda bama amfani take dashi ba se bayi guda daya, ta can gefe wajen zauren gidan shi ne dakin dasu Yaya suke ciki, gidan mu na Abuja ya fado min, my spacious bedroom, parlon mu, garden da komai na jin dadin rayuwa. Ina wannan tunanin har bansan sun Gama magana ba se da naji ta taba ni sannan na kalleta ta min alamar na tashi , na kuwa Mike na bi bayanta, Mino ta raka mu dakin, Babu komai se katuwar katifa an gyara ta da bedsheet, daga nan Babu komai, Mummy ta gyara min zaman akwatina na, ta nuna min komai inda yake sannan ta dakko kudi tace min na boye inda ga amfani dashi kadan kadan idan ya Kare zata Aiko min da wani. Ta Kara min nasiha sannan ta tafi ta barni a tsaye a tsakiyar dakin nayi shiru Ina tuna Abbu. Bansan iyakar lokacin da na dauka a tsaye ba seda naji muryar Mino tace min nazo Ummaan su na Kirana, na fito a sanyaye naje na tsaya nace

" Gani!"

" Dallah samu guri ki zauna"

Na koma na zauna aka Miko min Yar karamar silver da tuwo a ciki, na kalla tuwon ban ma gane miyar dake ciki ba saboda abinda aka haska gidan dashi ya fara disashewa, na wanko hannu na saka hannu na tasting miyar first se naji kuka ce, na Dan saki jiki naci Amma se half way naji cikina ya koshi, Dan hakan na tsame hannuna Amma tsoron cewa nake na koshi, se na ta juya hannuna a ciki, se can naji Hafsa da Siyama dake bayana sun fara fada, hankalina haya kansu Amma Ina jin fadan sede ba zance ga dalilin fadan ba, Ina zaune naji Mino tazo kaina tace

" Ummaah Bata cinye ba"

" Karba ki bawa Hafsa, ni abinda ya rage anan na babanku ne dasu Baba"

Nayi saurin cire hannuna tace min

" Kin koshi?"

" Kar ta koshi Mana, tun karfe nawa na zuba Mata abincin, Wasa ake?"

Haka Suka karba abincin Suka bawa Hafsa, na mike na wanke hannuna ina share hawayena na tuna yadda Abbu zai ta lallaba ni har se naci abinci, na wanke fuskata nayi alwala nazo nayi sallah, Ina cikin sallahn naji sallamar Yaya, daga yanayin yadda yake fadin

" Ina Afiyya?"

Nasan Yana cikin farin ciki, Amma response din Ummaan su ya Sagar Masa da gwiwa

" To uban shishiggi, daga shigowar ka ko ni baka tambaya ba se kanwar uwarka Afiyya, gaba daya ku tsaya ki jini man, Afiyya tazo ta zauna bance kowa ya zurfafa muamula da ita ba, bana son kawance ko shishigge mata, ba wata bace, itama ya ce kamar kowa. Ka dauki abinci kaci"

Yayi shiru duka suna sauraron ta, Yaya yace

" Kai Ummaah, Afiyya abar tausayi ce fa, ya zaai ba zamu jata a jiki ba"


" Mhmm kanwar uwarka ba, Dole Ina fada kana mayar min"

Baice Mata komai ba ya dauki kwanon shi ya fita, na Jima a zaune sannan nace da Mino dake zaune gefena,

" Zanyi bacci, Ina Zan kwanta?"

Ta kalleni sannan ta kalla gefen Ummaan su tace cikin kasa da murya

" Ko fadawa Ummaan mu"

Nayi shiru Ina tsoron tunkarar ta, anan nayi ta guangyadi sauro ya samu ya cije ni son ranshi, se Susa nake, can Siyama ta tashe ni tace naje mu kwanta, haka na Mike nabi bayanta, Ina ayyana yadda zamuyi bacci akan katifa mu hudu, lucky enough Ina zuwa na tarar an Yar min da Yar karamar katifa irin 6x6 dinnan, net ta Mika min na daura, na rike net din Ina tunanin to ya Zan daura, Mino ganin Ina tsaye ta min bayani tana jin motsi tayi shiru, se na fahimci they all want to be nice tsoron iyar su suke. Wani irin dauri na Masa na Shiga na kwanta, gaba daya ya kwanta a fuskata Dan haka da asuba na tashi nayi alwala naji fuskata kamar an zuba Mata barkono, na cije bakina Ina kokarin danne azabar da nake ji, a hakan nayi sallah duk suna bacci Basu tashi ba, gwara Yaya Ina ban daki naji motsin shi. Anan bacci ya daukeni se fadan Hafsa da Siyama ya tasheni, na tashi na cire net din fuskata na azaba kamar zata kwakwabbo, na gaida Mino dake cemin na tashi na kwashe kayan shimfida ta, nace Mata

" Kinga fuskata zafi take min"

Na fada Ina yatsina fuska, da a gidan mu ne da tuni na tada hankalin kowa kilan se an kaini asibiti, ta taba fuskar tace

" Net ne, zai warke kinji"

Na gyada kaina, anan ta nuna min yadda Zan saka yau sannan na kwashe kayan muka fito, ta bani tsintsiya Wai nayi shara, na kalla tsintsiyar na kalla tsakar gidan na saki ihu a kaina, Ina neman agaji a gurin Allah!




AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam first Bank of Nigeria, send evidence to 09063467258.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment