Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma ta idanu ne
kawai na ga iyakar gudun ruwanta. "
Haka dai Muraisu ya yi ta sake-sake a cikin
zuciyarsa har ya gaji, shima saí ya kishingida a
jikin wata bishiya.
Abinka da gajiyayye, bai dađe da kishingida
ba sai barci ya kwashe shi.
Bayan 'yan dakiku kadan kuma sai Husnaila
ta farka.
Koda la bude idanu ta tsinci kanta a cikin
wani iin daji na musamman sai ta takarkare ta
tsandara uban ihu. Muraisu ya farka firgigit! a
razane, dabbobin cikin dajin kuwa, hatta sauran
Rananan kwari da tsintsaye sai da suka razana, suka
kama guje-guje.
Duk dabbar da tayi arba da su Muraisu sai ta
yıyo kansu:
Nan fa aka kasa uban tserc tsakanin su
Husnaila da dabbobin dajin gaba daya.
Babu abinda zai baiwa mutumn mamaki face
Lsananin gudun da Muraisu da Husnaila ke yi
tamkar akan iska suke yinsa ba a kan kasa ba.
Duk su biyun sun yi matukar mamakin irin
gudun nasu, domin tamkar walkiya suke gifta
komai, sai dai karfin gudun nasu duk ya zama na
banza, domin duk sa'adda suka waiga bayansu sai
su ga dabbobi kusan guda dubu daf da su.
Duk inda suka dauke
dabbobin suke sa nasu.
sawayensu
anan
da
Babu abinda ya fi firgita su Muraisu face
cafka
kawo musu
yadda dabbobin ke
bakunansu, don su cinyesu, musamman wani katon
Zaki wanda idan ya wangame bakinsa sai ka ga
kamar ijiya mai zurfi da fadi aka bude.
Sai da su Muraisu suka shafe sa'a guda cif!
Suna falfala natsanaicin azababben gudu, sannan
suka hango wani katon tsauni a gabansu.
Basu tsaya jiran komai ba suka hau kan
tsaunin a guje, har sai da suka je can. samansa
sanann suka waigo baya.
Bisa mamaki, sai suka ga gaba dayan
dabbobin sun tsaya a kasan tsaunin đayansu bai yì
yunkurin hawowa ba.

Al'amarin da ya matukar basu mamakia ke
nan, Kawai sai suka zube kasa a saman tsaunin
suka kama haki, da fitar da numfashi da saurí da
sauri.
A sannan nc fa kishirwa ta ischsu, kuma
gashi
babu damar shawagi a kasan tsaunin tamkar an
basu gadin abinda ke kan tsaunin.
A dai-dai wannan lokaci ne Husnaila ta dubi
Muraisu cikin harara da fushi ta ce, "Ya ya aka yi
ka kawoni cikin wannan daji?"
Koda jin wnanan tambaya sai Muraisu ya yi
murmushi ya ce, "Ba wannan tambayar ya kamata
ki yí mini ba a yanzu, kamata ya yí ki tambayeni a
ina zamu samu ruwan sha?"
Husnaila ta sake murtuke fuska ta ce, "Ba
ruwa ne a gabana ba. Ka mayar da ni inda ka
daukoni, domin ina da bukatar na koma gida kafin
magariba tayi".
Koda jin wannan batu sai Muraişu ya bushe
da dariya har da bingirewa Kasa, sannan ya nutsu
ya ce, "Ai idan har kin ga kin fita daga cikin dajin
nan sai kin yi kwanaki uku cikakku a cikinsa!"
Cikin fushi da mamaki Husnaila ta mike tsaye
ta ce, "Ai kuwa idan ka ga na kara koda dakika
đari ne a cikin wannan daji sai idan bana
numfashi. "
Koda gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta
fara saukowa kasan tsaunin. Muraisu ya bita da
kallo kawai ko motsi baiyi ba daga inda yake
zaunc.
Lokacin da ya rage saura bai fi taku biyar ba
ta iso kasan tsaunin, sai kawia ta ga wannan
ma ta haikan
Zaki ya taso
turmusheta. Ba shiri ta juya da baya da gudu ta
koma kan tsaunin inda Muraisu yake.
Koda ganin abinda ya faru sai Muraisu ya
kama yi ma ta dariya. Al'amarin da ya kara
tunzurata ke nan, ta kamu da tsananin fushi. Bisa
dole taje gefe daya, nesa kadan da inda Muraisu
yake zaune itama ta zauna.
Babban abinda ya i daurewa Husnaila kai shi
ne, ya ya ita da bata da tsoro ko kadan amma taji
tana tsoron dabbobin wannan dajı?
Kawai sai ta dubi Muraisu ta ce, "Wai shin
wannan wane daji ne muka shigo?" Muraisu ya yi
ajiyar zuciya sannan ta ya ce, "VWannan shi ne dajin
KIRZUFA! Kanar yadda na gaya miki da farko sai
mun yi kwana uku a cikinsa ni da ke, a sannan ne
na sami
Zan sauya miki rayuwarki, kuma
soyayyarki, mu tafi izuwa birninmu na Lairuf mu
yi aure".
Kafin Muraisu ya gama rule bakinsa tuni
Musnaila ta tofa masa yawu a fuska,
Cikin tsananin fishí ya mike tsaye zumbur! ya
zare takobinsa, itama saí ta mikc Zumbur! ta rike
mashinta suka fara kallon-kallo, har gaba dayan
jikin Muraisu na tsuma saboda fushi, domnin a íva
rayuwarsa ba a taba yi masa iin wannan
wulakancin ba a matsayinsa na dan Sarki, kuma
gawurtaccen jarumi.
Husnaila ta dubcshi a wulakance ta ce,
"Na
tsancka! Kuma na tsani dukkan zuril'arka, Har
abada ba zan ta6a sonka ba, kuma ní da dan uwana
Sarki Ishmar sai mun baje birninku, mun konc
dukiyoyinku, mun kame matanku da 'ya'yanku sun
zama bayinmu. Mazajenku kaf sai mun kashesu",
Koda jin wannan batu saí Muraisu yaji ya
tsani lusnaila kamar yadda yaji ya tsani
mutuwarsa. Duk wannan tsananin kyawu nata sai ta
rama kamar dodanníya a idanunsa.
IHar ya yunkura zai afka ma ta su yi yaki, sai
ya tuna cewa ai sihiri ne a jikinta wanda ya sa ba za
ta laba son wani da namiji ba face ta ci ta sha daga
abubuwan da ke cikin wannan daji na Kirzufa na
tsawon kwana uku.
Koda tuna wannan al'amari sai jikin Muraisu
ya yi sanyí, ya fasa afkawa Husnaila ya koma ya
zauna. Koda ganin haka, sai itama ta koma inda
take ta zauna.
A sannan ne fa kishirwa ta ci gaba da
addabarsu. Babu shiri suka mike tsaye suka kama
yawo akan tsaunin kowannensu na neman ruwa,
amma babu ko alamarsa.
Duk sa'adda suka leko kasan tsaunin kuma sai
suka ga wadanann dabbobi suna nan suna kewaya
tsaunin, jira kawia suke su sauko su afka musu,
Bisa dole suka hakura.
Lokacin da 'yan sa'oi suka kara shudewaa sai
magariba ta doso kai, gari ya fara duhu, a sannan
ne tsananin kishirwa tasa suka baje a kasa suka
kama num fashi sama-sama kamar za su muti. Sai
da kowannensu ya fara suma, kwatsam! ba zato ba
tsammani sai hadari ya gangamo aka fara tsawa da
walkiya gami da wata irin gagarumar iska mai
karfin gaske. Kafin a jima ruwan sama ya tsuge
karmar da bakin kwarya.
A sannan ne Muraisu da Husnaila suka
farfado, sai kowannensu ya wangame bakinsa suka
kama shan ruwan, har sai da suka koshi, sannan
suka dawo cikin haiyacinsu, sai dai babu inda zå su
fakewa wannan ruwan saman, dole suka hakura
ruwa yai ta dukansu har izuwa tsawon sa'a guda,
sannan ruwan saman ya dauke dif.

Nima Kuma Wanga Ruwa Yana Daukewa Nima Na Dauke Daga Typing hhhhh

Zan dakata anan sai kuma wani lokaci
Zamu cigaba
Insha Allah
Likes and comments
Domin hakan na sa mu cigaba
Ga masu shA award whtsp grp
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU
Littafi Na Biyu (2)
Part C
Na Abdulaziz Sani M /Gini
AA Misau Ke Magana

MURAISU DA LUSNAILA SUKA MIKE TSAYE SUKA
kallo juna kowa ya kau da kai.
A wannan lokaci ngar jikin Husnaila ta dame
sakamakon wan saman da aka laftla, hakan ne
yasa surar jikinta ta baiyana karara a ili tamkar
tsirara take,
Roda Muraisu ya ganta a cikin wannan hali
sai ya ude ya dimauce vaji ya kamu da tsananùn
sha'awa, amma sai ya danne zuciyarsa ya juya ma
ta baya.
Lokacin da suka leko Rasan tsaunin sai suka
cika da mamaki, domin babu dabbobin dajin a
wajen ko guda daya.
Da yake suna jin yunwa matuka, sai suka
sauko daga kan tsainin. Suna saukowa sai suka
tsaya cak! Muraisu ya juya ma ta baya don baya
son ya ci gaba da ganin tsiraicinta.
Cikin fushì Husnaila ta bude baki ta ce,
"Saboda me za ka rinka juya mini baya alhalin
kaine ka kawoni cikin wannan masi faffen daji? To
ka sani cewa ni yanzu yunwa nake ji, saboda haka
sai ka je ka nemo mìni abìnda zan įi"'.
Tana gama fadin hakan taje ta zauna akan
wani dutse.
Cikin matukar harzuka Muraisu ya juya a
fusace ya ce, Yadda kike takama ke yar Sarauta
ce nima haka nake. Ni da ke kowa ta sa ta fissheshi
a cikin wannan dajı. Idan ma za ki iya sai ki yi
kokarin fita daga dajin".
Koda gama fadin hakan sai Muraisu ya juya
ya tafi ya bar Husnaila a zaune tana binsa da kallo
gami da harara da tsananin kiyayya, taji kamar ta
ruga kansa ta tsircshi da mashin da ke hannunta.
Muraisu ya ralsa izuwa cikin dajin Kirzufa,
domin neman abinda zai ci, wata irin iska mai
karfin gaske ta fara bugawa, bishiyoyi suka kama
rangaji kamar za su kakkarye su fadi kasa.
Da yake dama an tafka ruwan sama sai dajin
gaba daya ya dume da sanyi, gashi kuma magariba
ta yi, duhu ya fara.
Nan take Husnaila taji ta kamu da tsananin
tsoro, kuma gashi saura kiris Muraisu ya bace ma
ta da gani, domin ya yi nisa sosai daga inda take
hangoshi.
Kawai sai ta mike zumbur! ta ruga da gudu
izuwa inda yake tana rike da mashinta, ta riskeshi
suka jera suna tafiya, amma ko kallon juna ba su yi
- ba, kuma kowannensu fuskarsa a murtuke take.
Haka dai suka wanzu suna ta ta fiya a cikin
dajin suna hange-hange da waige-waige ko za su ga
abinda za su iyaci ya magance musu yunwar da ke
addabarsu, amma babu.
Hatta bishiyoyin dajin babu mai fure a jikinta
bare a samnu dan itaciyar da za a iya ci.
Sai da Muraisu da Husnaila suka shafe kusan
rabin sa'a suna tafiya a dajin basu ga koda tsuntsu
ba ko wata karamar dabba wacce za su lya rafkewa
su yanka su ci.
A dai-dai wannan lokacin ne suka jı sun gaji
likis, saboda haka sai suka tsaya suka zauna a kasa
dirshan suna haki.
Duk sa'adda suka kalli juna sai kowa ya harari
dan uWansa su kau da kai.
Kwatsam! ba zato ba tsammani sai suka ga
wata katuwar jimina mai giman ban mamaki ta
sauko daga sama ta dira a cikin wadansu ciyayi ta
kama kiwo abinta.
Nan fa Husnaila da Muraisu suka dubi juna
suka yiwa kansu inkiyar su tashi su afkawa jminar
domin su sami abinda za su ci.
Lokaci guda suka mike tsaye a tare. Muraisu
ya zare takobinsa, ita kuma Husnaila ta mikar da
mashinta suka durfafi inda Jiminar takc. A wannan
lokaci Jiminar ta juya musu baya tana ta tonon kasa
da bakinta.
Koda Jiminar taji motsin taiya a bayanta sai
ta dago da kanta tå tsaya cak! kamar gunki suma
sai suka tsaya cak amma da Jiminar ta ci gaba da
tonon kasa sai su ma suka ci gaba da durfafarta.
Da suka ga ba ta sake tsayawa ba sai suka
ruga da gudu izuwa kanta. Manufarsu ita ce, su-
soketa da makaman hannunsu.
Koda ya rage bai fi saura taku daya jal a
tsakaninsu da Jiminar ba, sai ta waigo cikin bakin
zafin nama ta makesu da dogon wuyanta.
Saboda karfin makuwar sai da suka yi sama
da baya suka fađo kasa a tare a matukar galabaice.
Duk su biyun sai suka raina dukkanin jarumtakarsu
suka san cewa tabbas sun shiga dajin Kirzufa.
Kafin su yunkura su mnikc tsayc sai jiminar la
taso musu haikan, nan da nan ta iso garesu ta karwa
Husnaila wawar caka da tsinin bakinta. Cikin zalin
nama Muraisu ya fisgo Iusnaila daga inda take
kwance. Bakin Jiminar ya caki kasa, ya nutsc gaba
daya a cikinta.
Koda Jiminar ta zarc bakinta sai ga rarmi
zururu mai tsawo da fadi wanda za a iya binne
jarini a cikin.
Nan fa aka fara masifa ffen artabu tsakanin
Jinina da su Muraisu, la wanzu tana mai kai musu
suka da tsirin bakinta, su kuma suna buge bakin na,
lá da makaman hannunsu.
Duk sa'adda makaman nasu suka hadu da
bakin na la sai ka ji Rara Ral! kamar karfe da karfe
ne suka hadu.
Sai da suka shafe lokaci mai dan tsawo suna
Wannan gumurzu, ya zamana cewa sun kasa taba
jikin Jininar domin ta fisu nama, kuma gashi ko
kadan ba la gajiya, su kuwa sai suka fara sarewa.
Ana cikin haka ne Jiminar ta shammaci
Ilusnaila ta kai ma ta wawar suka a cinyarta, duk
da cewar IHusnaila ta gocewa harin da dukkan zafin
namanta amma sia da kaifin bakin jiminar ya
yanketa.
Wani inn dogon yanka tamkar da takobi aka
yanketa.
Take waycn ya dare, jini yai feshi. Ilusnaila ta
kurma uban ihu ta sulale kasa sumammiya.
Koda ganin abinda ya faru ga IHusnaila sai
Muraisu ya fusata ya yi zumbur! ya daukì mashin
IIusnaila ya hada da takobinsa ya ci gaba da yakar
jiminar. Ya rinka kai ma ta muggan hare-hare da
takobi da mashi cikin matukar fushi da zafin nama.
Bisa dole jiminar ta rinka ja da baya, amma
kuma wani lokacin saì ka ga la taso masa da
dukkanta itama ta kuntalashì tana korashi baya.
A haka ta sảmu shima ta yankesbi da kaifin
bakin na ta, har sau uku.
Yankan farko a hannunsa na dama nc, na biyu
a kaladarsa ta hagu, na uku kuma a gadon bayansa,
sai gashi jinio na zuba a jikinsa har jiri na đibarsa,
amma saboda yana da dakakkiyar zuciya irin ta
maza bai fadi kasa ba, kuma bai fasa kaiwa jiminar
hari ba.
Ana cikin haka sai Jiminar ta sami nasarar
buge takobi da mashin da ke hannaycnsa suka fadi
kasa, kuma ta matseshi ta hanashi daukar
makaman.
Bisa dolc Muraisu ya fara ja da baya, gashi
bayansa wani katon dutse ne, idan har ta kuresgu a
jikin dutsen ba makawa sai ta hallakashi tunda ta
cika hanya babu ta inda zai iya tserewa.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke
nan, zuciyarsa ta karaya domin bashi da sauran
wata dabara a zuciyarsa da zai iya kubular da
kansa.
A dai-dai wannan lokaci ne Husnaila ta
farlado daga dogon suman da tayi, ta ga abinda ke
shirin faruwa.
Koda ta tunkura da nufin la mike tsayc sai taji
ta kasa đomin kafarta tayi nauyi tamkar an aza ma
ta katon dutsc akai.
Kawai sai ta zuba ido tana jiran ta ga iin
kisan gillar da jiminar za ta yiwa Muraisu sanann ta
Juyo kanta.
Ya yin da ya rage bai fí saura taku biyar ba
kacal tsakanin jiminar da Muraisu ta kaishi jikin
dutsen da ke bayansa, sai kawai ya fusata ainun ya
daka wawan tsalle sama izuwa kan jiminar tamkar
an harboshi daga cikin baka.
A Saman ya kama wuyan jiminar da
hannaycnsa biyu ya murdeshi da dukkan karlinsa.
Ta ke wuyan jiminar ya karye ya bayar da
sauti kararas! Ta ke Jiminar ta yanke jiki ta ladi
kasa tim! Tamkar giwa ce ta fadi har sai da kasa
tayi girgiza, wala gagarumar kura ta tashi.
A sanann ne Muraisu ya yanke jiki ya fadi
kasa.
Maimakon ya yi kokarin yiwa kansa magani a
jikin raunikansa sai ya nufi inda Ilusnaila ke
kwancc da jan jiki domin ya kasa mikewa tsayc.
Yana isa garcta ya fiddo garin magani a
jikinsa ya shafe raunin cinyar Ilusnaila.. Ta ke ta
kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogịn
da taji ta sake bajewa a kasa sumammiya.
Nan take hankalin Muraisu ya dugunzuma
ainun,-yaji ya kamu da lsanänin tsoro, domin a
zatonsa Ilusnaila ta mutu.
Cikin ruđewa ya daure ya míke tsaye da kyar
yana tangadi, yaje ya dauko babbar ruwan shansa
ya budeta ya zazrAge ruwan akan Husnaíla.
Dama sa'adda aka yí ruwan sarma ne ya sarnu
ya cika battar ruwan.
Ai kuwa yana zuba ma ta ruwan saí ta farfado
tana mai dogon ajíyar num fashí. Koda ta bude
idanu ta fa Muraisu tsaye a kanta sai ta daka masa
tsawa ta ce, "Me yasa ka cecí rayuwata? Ka san
cewa na tsaneka fiye da yadda na tsani mutuwata?
Da dai a co kaine ka kubular da rayuwata
gwara dabbobin dajin nan su yí kaca-kaca da
sassan jikina su cnyc".
Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta
kama tafar fasa, yiji kamar ya sa takobi ya sare kan
IHusnaila saboda lakaici.
Amma da a tuno da birnin Lairus sai ya
danne zuciyarsa, ya mıke tsaye yaje ya koma can
gefe daya ya ratIna ya shiga yíwa kansa magani,
har sai da ya tsaida dukkan jinin da ke zuba a
jikinsa.
Bayan ya dz wo cikin haiyacinsa sOsai sai yaje
ya samo kirarcn wula ya ncmno kyastu ya kunna
wuta sannan ya 1arc wata wuka mai kaifi a ikinsa
ya rauna ya fcd: wannan jimina tsaf ya daddatsa
naman jikinta.
Da kyar ya dauki cinyar jiminar guda ya
soketa a jikin ítac mai gwafa ya shiga gasawa.
Da naman ya gasu sosaí, sai kawaí ya fara cin
abinsa ko kallon Husnaila bai ba.
Da yake itama a cikin bakar yunwar take saí
ta taho da jan kafa a zaunc don la kasa mikewa
tsaye, ta iso har gaban naman ta dinga yanka tana
Har duk su biyųn suka ci suka koshi basu kalli
juna ba, kuma dayansu bai ce uffan ba.
Duk wanda ka dubí fuskarsa sai ka ganta a
nurtuke tamkar an aiko masa da sakon mutuwa.
Ai kuWa suna gama. cin wannan naman ne
hadari ya sake gangamowa, aka fara wata iin
bakar guguwa wacce ta firgitasu la firgita dajin
gaba daya, domin nan take bishiyoyí suka kama
kakkarycwa suna zubewa kasa.
Kai duwatsu ma wadanda ba su cika girma ba
sai suka kama mirginowa akan kasa da kansu.
Ba shiri Muraisu ya mike tsaye ya ciccibi
Husnaila tamkar ya dauki dan karamin yaro ya
ruga da gudu izuwa cikin dajin yana neman malafa.
"Su kansu sauran dabbobin da ke dajin sun firgice
suna la gujc-guje suna shigewa cikin ramuka da
manyan koguna don su tsira da rayuwarsu.
Muraisu dai ba a son ransa ya dauki Husnaila
da hannunsa ba, sai don kishin kasarsa, sbaoda
lallai nan gaba yana son dansa ya ceto ratyuwar
jama'arsa daga sharrin abokan gaba.
Ita kuwa Husnaila, koda ta ga Muraisu ya
dauketa da hannayensa biyu tana rungume a
kirjinsa sai zuciyarta tayi bakikkirin ta kama
zancen zuci tana mai cewa, "Saboda me babban
makiyina zai taba jikina? Ai kuwa sai na yanke
wadannan hannaye nasa duka biyun wadanda suka
taba jikina!"
Muraisu na cikin wannan gudu ne ya hango
wani kogon dutse, kawai sai ya durfafi kogon kai
tsaye. lar ya kunna kai zai shiga ciki sai ya dawo
da baya ya tsaya cak!
ba wani abu banc yasa ya dawo da bayan ba
face ganin tsananin duhu a cikin kogon, kuma babu
mamaki akwai wata muguwar dabbar a cikin kogon
a la6e.
Kawai sai Muraisu ya ajiyc Husnaila a kas
sannan ya karyO wani icen bishiya kuna ya zura
hannu a cikin aljihunsa ya dauko duwasun da ya yi
kyastu da su a baya ya shiga kokarin kunna wuta a
|ikin wannan ice da ya karyo.
Da yake an yi ruwan sama a baya bada
dadewa ba da kyar da sidin goshi wular ta kama,
sannan Muraisu ya zare takobir sa ya shiga cikin
kogon, hannunsa guda na rike da icen mai wuta
yana haskawa.
Kogon bashi da zuri sosi, haka ma fadi,
kuma ko Rwaro daya bai gani ba a ciki. Bayan ya
tabbatar da lafiyar kogon sai ya ita ya dauko
Husnaila ya shigo da ita ciki, sannan ya ajiycta ya
sake lita ya nemo wadansu itatuwan ya kunna wuta
mai kari domin su ji dumi.
Faruwar hakan ke da wuya sai ruwa ya sake
kecewa kamar da bakin kwarya. A dai-dai wannan
lokaci nc tsananin gajiya tasa Muraisu ya fara
8yan-gyadi.
Yana cikin wannan hali ne lHusnaila ta faki
num fashinsa ta suri daya daga cikin itatuwan da ya
kunna wular da su ta maka nasa shi a nuka-
mukinsa.
Ta ke Muraisu ya baje a kasa sumamme har
jini ya bul6ulo ta cikin kunnensa ya zamana cewa
ko num fashi baya yi tamkar ya zama gawa.
Koda IIusnaila la ga la sami wannan nasara
sai ta cika da farin ciki, kawai sai ta mike tsaye da
kyar tana dingishi ta leka wajcn kogon lana kallon
yadda ruwan sama ke kwarara.
Ai kuwa bala jima ba a tsaycn sai ruwan
saman ya dauke dif!
Nan take ta fita itama tajc ta dcbo wadansu
itatuwan ta zubasu akan Muraisu. Sai da ta tabbatar
da cewa ta lullu6cshi da itatuwan san ann ta debo
itatuwa masu cin wuta ta zuba a kansu.
Nan da nan kuwa wuta ta sake kama itatuwan
da ke kansa. Kawai sai Husnaila ta juya ta fice daga
cikin kogon tana mai kyakyata dariy ar mugunta
cikin tsananin farin ciki domin ta san cewa ta gama
hallaka Muraisu dole ne wuta ta babbakeshi ya
konc kurmus!
Dama Husnaila ta fita ne ikec da ice mai cin
wuta don haska hanya saboda duhun dare. Kawai
sai ta ci gaba da tafiya ba tare da sanin inda ta dosa
ba a cikin dajin Kirzufa.
Koda ta fara nísa a cikin dajin tana Jiyo
gurnani da koke- koken dabbobi, kawai sai ta j
tsoro ya kamata. Al'amarin da ya matukar ba ta
mamaki ke nan, domin ita a saninta bata san wani
abu wai shi tsoro ba a rayuwarta, amma tunda ta
shigo dajin Kirzufa taji ta zama matsoraciya.
Kwatsam! Sai ta hangi wari kogon dutse a
gabanta, don hak a sai ta yanke hukuncin ta shiga
cikin kogon ta kırasa kwana a ciki, tunda ba zai
yiyu ta ci gaba da tafiya a cikin daren ba. Burinta
shi ie ta fita daga cikin dajin Kirzufa ta koma can
birnin Hutaira.
Lokacin da Husnaila la iso bakin kofar
wannan kogo sai ta tsaya ta leka cikin kogon tana
mai haska cikinsa da wutar icen da ke hannunta,
amma sai ta ga babu komai a ciki, duk da haka sai
ta kasa shiga ciki, dalili kuwa shi ne, ba ta iya gano
karshen kogon.
Kogo ne mai zurfin gaske, kuma mai lunguna
da sako-sako.
Nan take Husnaila taji tsoro ya dada baibayeta
har zuciyarta ta kama bugawa da karfi amma da ta
tuna cewa babu in da za ta iya kwanciya face a cikin
wannan kogo sai kawai ta kunna kai ciki.
Maimakon ta shiga can cikin kogon sai ta
zauna daga baki-baki. Bisa sa'a sai ta ga tarin
wadansu kiraran itatuwa a gefe daya. Al'amarin da
ya sa tayi zargi cewa lallai akwai wasu halittu a
cikin kogon, ko kuma dai sun shigo sun fita
Nan da nan Husnaila ta tara kiraren a gabanta
ta hada wuta sannan la kishingida a gaban wutar
tana jin dumi. Tsawon kusan rabin sa'a ba ta |l
motsin komai ba a cikin kogon, don haka sai ta saki
jikinta ta daina jin tsoro. Abinka da gajiyayya, nan
da nan sai Huśnaila ta kama gyan-gyadi. Ai kuwa
sai bárCi ya saccta bata sani ba.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga wadansu
irin jibga-jibgan Birirrika suna fitowa daga cikin
kogon dutsen,
Hakika girman wadannan Birirrika ya wuce
misali, domin komai jarumtakar mutum idan ya yi
arba da su dole ne ya razana saboda kwarjininsu da
muninsu.
Adadin Birimikan ya kai dari. Takun sawunsu ma
kadai ya isa abin tsoro domin yana haddasa
karamar girgizar kasa. Amma hakan duk bai sa
Husnaila ta farka daga barcin da take yi ba mai
nauyin gaske.
Lokaci guda Birirrikan suka kewaye Husnaila
su duka, suka zuba ma ta idanu kawai. Har sun
yunkura za su dasa wawa akanta sai suka jiyo
gurnanin Shugabansu.
Gaba dayansu sai suka ja da baya suka dare
hanya ta samu a tsakiyarsu.
Gurnanin da Shugaban asu ya yi ne ya sa
Husnaila ta farka daga barcinta a firgice! Koda ta
bude idanunta tayi arba da wadannan Biririka
zagaye da ita sai ta kwalla uban ihu cikin tsananin
razana.
A dai-dai wannan lokaci ne Shugaban
Birirrikan ya karaso gaban Husnaila. Shugaban
Birirrikan ya karewa Husnaila kallo sama da kasa,
kawai sai ya sa hannu ya dauko Husnaila da
yatsunsa biyu kacal tana ihu da kururuwa ya juya
da baya ya nausa cikin kogon, sauran Birimikan
suka take masa baya suna ruri da gurnani wanda ya
cika dajin gaba daya.
Husnaila tayi iya kokarinta akan ta zille daga
Cikin yan yatsun Birin nan amrna ta kasa duk da
cewa tana ta caka masa mashin da ke hannunta,
amma tamkar dutse ta kę cakawa, domin ko
kwarzanewa jikin nasa bai yi ba.
A wannan lokaci ne hankalin Husnaila ya
kara dugunzuma fiye da ko yaushe, domin ta san
cewa rayuwarta ta zo karshe donin babu ta yadda
za ta iya kubuta.
Bisa mamaki sai taji nadam a ta zo ma ta bisa
abinda ta yiwa Muraisu ta hallakashi. Tabbas ta san
Inda yana raye, kuma suna tare zai iya tabuka wani
abu a yanzu.
Duk da cewa Husnaila ta tsani Muraisu kamar
yadda ta tsani mutuwarta, amma a wannan karon
sai taji tana kaunar ganınsa.
A karon farko a rayuwarta sai taji hawaye ya
zubo ma ta, kuma tunanin dan uwanta Sarki Ishmar
ya fado ma ta a rai.
Nan take ta cika da mam akin yadda Sarki
Ishmar ya kasa sanin halin da tak e ciki, har ya kasa
aiko ma ta da agajin gaggawa a matsayinsa na
gagarumin matsafi....

Nima Kuma na cika da mamakin Ganin Masoyiyata yau ta manta dani bata nemeni ba Kuma ta kasa aiko mun da sako hhh

Anan zamu dakata sai wani lokaciBUSA A MUTU
Littafi Na Biyu (2)
Part D.
Na Abdulaziz Sani M/Gini
AA Misau ke Magana

Marubucin yaci gaba da cewa..

AIKO MA TA DA AGAJIN GAGGAWA A MATSAYINSA NA
GAGARUMIN MATSAFI.
Birimkan suka cì gaba da kutsawa cikin
kogon dutsen suna ta tafiya. Sai da suka yì yar
doguwar taiya mai tsawo sannan suka iso wanı
babban wuri mai cìke da bìshiyoyì da wata korama
a tsakiya wacce ruwanta ke gudana ta cikin dutse
yana kwarara izuwa cikin wanı kwararo.
Bishiyoyin da ke wajen duka sun yì 'ya'yaye
nunannu da danyu, kai da gani ka san cewa
wadannan Biimka suna jin dadin rayuwarsu a
Wannan wu.
Da isowar biimkan wannan wun sai aka
daure Husnaila a jikin wata bishiya da ke tsakiya
da wala inyar danyar jijiyar bishiya aka daureta
tamau, tayi ta wutsil-wutsil domin ta kwance kanta
ta kasa.
Nan fa tayi amfani da dukkan karfin sihirinta
domin ta kwance kanta amma sai ta kasa.
A sannan ne ta gane cewar babu wanì sihinin
tsafi da yake tasiri akan dabbobin da ke cikin
wannan dajì na Kirzula, dajin Bala'i da masifa!
Nan fa birirrik an suka kama dukan kirjinsu da
hannayensu tamkar ganguna- suke dogawa. Karar
bugun kirjin nasu ya cika dajin gaba daya
A wannan lokacı ne HuSnaila ta gane cewa
biririkan kirari suke yiwa shugaban nasu suna
zugashi akan ya alka ma ta.
Koda fahimtar hakan sai Husnaila ta ci gaba
da kwarara uban ihu. Shi kuwa birnin sai ya
durfafo kanta
Ya yin da ya rage bai fi saura taku uku ba
kacal a tsakaninsu sai kawai aka jiyo wani abu ya
taho da gudu ta baya. Lokaci guda gaba dayan
birirrikan suka juyo har shi kansa shugabansu.
Kafin daya daga cikinsu ya yi wani yun kuri
sai kawai suka ga mutum ya dako tsalle ya dira a
tsakiyarsu ya hausu da SARA DA SUKA.
Ba wani bane wannan mutum face yarima
Muraisu.
Al'amarin da ya matukar daurewa Husnaila
kai ke nan, domin a tunaninta tuni Muraisu ya dade
da konewa ya zama toka.
Abinda ya kara đaure ma ta kai shi ne, ko
alamar kuna babu ajikinsa.
Muraisu ya Wanzu yana mai sara da sukan
wadann

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment