Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na saba miki a
cikin maganganun dana fadamiki"
.
Bisa mamaki sai yaga fuskarta ta fadada da
murmushi , sannan ta rike kafafunsa suka mike tsaye
tare, ta dubeshi da kyau tace
.
"Ya masoyina na rantse da wata ko kadan baka bata
mini rai ba, kawai na tausayawa rayuwarka ne .
Hakika sai yanzu na tabbatar da cewa mahaifina yana
mulkin zalunci, domin an tauye hakkinka dana
iyyenka , A matsayinku na bil'adama da ba
dabbobiba, bai kamata ace baku da sutura ba face
walki, tabbas inda nasan cewa akwai irinku a
garinnan da tuni na kai muku "
.
Shuraih ke magana
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yaji duk tsigar
jikinsa ta tashi, jikinsa yayi sanyi, ya kura mata idanu
kuma ya kasa cewa komai . Mabaruka na ganin
sauyin........
.
Kash kuyi hakuri makaranta fallen littafin ya lalace
akalla dai fallen daya lalace yakai goma sha daya.
Amma zanyi kokari na dan bayyana muku abubuwan
fallen ke kunshe da shi cikin gaggawa
.
Shuraih kemagana
Boka gulmanu yazo ya samu sarki abul dinar ya sanar
dashi cewa" lallai wannan yaro kar ya wuce kwana
uku bai yi wannan tafiya ba kuma a sanar dashi cikin
wata uku kacal akeson ya dawo tare da bishmalu"
.
Sarki abul dinar ya dubeshi cikin mamaki yace " yakai
sarkin matsafa shin meyesa kace haka "
.
"Aljanina ne ya sanar dani haka kuma ya tabbatar
min muddin bai bar garinnan cikin kwana uku ba toh
tabbas zaiyi nasarar shiga birnin duma kuma ya
dauko bishmalu"
.
Sarki abul dinar najin haka yai umarni ga wani
bardensa. Dayaje ya sanar da jarumi ashwar cewa
cikin ya tabbata cikin kwana uku ya fita daga garinnan
ya nufi birnin duma , sannan wata uku gareshi
muddin wata uku ta gota koda da kwana dayace to ko
yazo da bishmalu wannan gari to tabbas ya fadi
.
Wannan shine abin daya afku a fadar sarki abul dinar
.
Shidai mahaifin bishmalu wato sarkin Misra ya auri
wata kyakkywar mata , ita wannan matar duk wanda
ya aureta mutuwa yake sakamakon sarkin aljanu
kifyan dayake matukar sonta koda sarkin misra ya
aureta sai aka ringa tsorota da shi ana mai kashedin
ya rabu da ita ,
Wata rana ya fita farauta shida baradensa suna cikin
jeji sai sukaji wata murya ta barke da dariya sannan
akace da su "ya kai wannan sarki mai taurin kai lallai
ka rabu da wannan mata taka don ita mata ta ce ni
kadai"
.
Sarkin misra na jin wannan batu yace karyarka tasha
karya baka isa karabani da mata ta ba ......
.
Wata sarka yagani ta shake wuyansa nan take ya
ringa makyarkyata .
Can sai yafadi wata kalma sai wannan sarka ta tsinke ,
,
Baraden suka juya tare da sarkin misra suka dawo
cikin gari
.
Toh fa tun daga wannan rana ne wani ciwon kai mai
tsanani ya addabi sarkin misra.
Wannan ciwo ta hana shi sakat domin idan ta tashi
mai tamkar zai mutu haka yake .
.
Koda matarsa taga wannan ciwo taki ci taki karewa
sai ta tafi wajen boka ta sanar dashi wannan ciwon
na sarki take bokan ya bata wata laya yace ta dauara
layan awuyan sarki.
.
Tazo ta daura layan , aiko tana daurawa sarki ya ji shi
garau tamkar wata ciwon kai bata taba samun saba a
duniya.
.
Ana nan ana nan rannan sai matar sarkin misra ta
samu ciki ,
Sarkin misra yai murna kwarai , bayan cikin ya cika
wata tara sai ta haife santalelen yaro wanda tsabar
kyaunsa ma ana zaton aljani ne
.
Sarkin misra yayi murna kwarai amma mai hade da
bakinciki sakamakon mutuwar matarsa yayin
haihuwa ,
.
Aka saka ma yaron suna bishmalu ,
Wata rana da daddare sarkin misra yai mafarki da
wani garjejen aljani yana rike da dansa yace mai" tun
da ka kashe mata ta toh na dauki danka daga yau
yazma dana baza ka sake yin arba da shiba.
Har ka mutu
.
Washe gari sarkin misra ya farka baiga bishmalu ba
yai neman duniya amma bai ganshi ba daga bisani
yaje wajen boka toh ananne boka ya tabbatar mai da
cewa dansa yana nan a raye wani hatsabibin sarkin
aljanu ne ya sace shi ya kaishi birnin duma sunan
wannan aljani kifyan
.
Sarkin misra ya tura sadaukai , jarumai da dama
amma duka ba labarinsu
.
Daga karshe ya hakura ya sadakar
Amma sabi da bakin ciki kullum cikin kuka yake yanzu
haka yana fama da wata irin cuta , wannan cuta anyi
magani anyi magani amma ina taki warkewa ,
Amma bokansa ya fadami duk randa yai arba da
dansa bishmalu toh zai warke daga wannan cuta .
.
Wannan shine takaitaccen tarihin bishmalu daga
bakin shuraih 99%
.
.
Koda ashwar ya sami sanarwar sarki abul dinar kan
cewa ya gaggauta barin garin kafin kwana uku
.
Sai yayi shiri
Tsoho makabul ya iso gareshio dauke da wasu
makamai , mashine da takobi sai kuma kibiya
.
Tsoho makabul ya mika mai yace " amshi wayannan
makamai kasani wannan bokan daya fadamana cewa
zakayi gagarumar shahara a duniya shine ya bamu
wayannan makamai yace duk sa'adda ka girma in
damka ta a hannunka.to yanzu lokaci yayi "
.
Ashwar ya amsa yana mai godiya ga tsoho makabul
Zuwa asuba ashwar yagama shirin shi sannan
yarubuta wasika ya bawa tsoho makabul kan cewa in
gimbiya mabaruka tazo ya bata sannan ya sanar da
ita shi yatafi .
.
.
Bayan fitarsa daga birnin sarwaliya ya yanki daji yaci
gaba da tafiya
Sudai wayannan makamai da tsoho makabul ya bashi
sihirtattun makamaine
1.acikin makaman akwai wata mashi wadda duk abin
da aka soka da ita to fa saide wani bashiba ita
wannan bashi har dutse fasashi take ta tarwatsa shi
sannan ta wuce
2sai wata kwari da baka wanda shi wannan kwarin I
zan har ka harbata toh zataje ta cake duk wadda kake
bukata ta cakeshi sannan ta dawo cikin gwafanta
itama wannan kwari tana huda dutse sannan ta
tarwatsa shi
.
(Har yanzu dai ni shuraih hakuri nake baku
sakamakon lallacewar sauran fejin kuma ni kaina
nasan bazan baku labarinnan yadda take ba amma
zan dan kokarta)
.
3sannan kuma akwai wata sihirtacciyar takobi wadda
take da kaifin tsiya koda bishiya aka sara da wannan
takobi toh anan take zai bushe sannan ganyayyen
bisansa su bushe yafadi kasa.
Shi wannan takobi idan dare yai sai kaga yayi haske
inda zai haskaka ma marikinshi hanya
.
.
Wata rana ashwar ya kwanta yana barci saiyayi
mafarki a cikin mafarkin nasane aka sanar da shi
cewa akwai wata gari agabansa izan ya shiga garin
kada yaci komai ko ruwa ne kada ya yadda yasha
,
Koda ya farka daga barcin ne sai yaga mai ai safiya
tayi sannan rana ma ta fito .
Tafiya kadan yayi sai ya hangi wani gari agabansa
batare da shakkar komai ba ta dumfari wannan garin
yana shiga cikin wannan gari sai yaga wani tsoho
yana noma koda tsohon ya gansa sai ya kariso
gabashi suka gaisa bayan sun gaisa ne tsohon ya
dauko wasu dabino ya mika ma aswar.
.
Har ya kai hannu zai karba sai kawai ya tuna da
mafarkin da yayi jiya da daddare .
Sai yafasa amasar wannan dabino.
Tsohonnan yayi yayi da ashwar ya ci dabinon amma
ashwar yaki sai wannan tsohon ya tashi mai haikan
yana so ya kasheshi koda ashwar yaga haka sai ya
zaro takobinsa ya fille kan wannan tsohon sannan ya
ci gaba da tafiyarsa izuwa cikin garin
.
Shidai wannan gari sarkinsu ya kasance mugune
kuma azzalumi , yana bautar wani dodone kuma
wannan dodo kullum sai an yakama sa bil'adama
yasha jininsa , kullum barade sukan fita zuwa
farautar mutane, sukuma mutanen garin yayin da
baki suka shigo gari sai su yan yamesu da abubuwan
makulashe wanda aka zuba amaganin bacci aciki
kana ci shikenan naka yaja
.
Yayin da dakarun sarki masu farautar mutane suka
fita farauta izan har basu sami mutum ba sai sudawo
izuwa birnin su a cikin mutanen gari sai ayi kuri'a duk
wadda tafada kansa toh shine za'a yanka wa dodon
da sarkin ke bautawa ya shi jininsa.
.
.
Ashwar na zuwa kasuwar wannan gari sai jama'a
suka yanyameshi dakayan ciye ciye shikuma duka ya
basar yace musu bayaci
Koda sukaga alamar cewa ashwar bazaici kayan ciye
ciyen ba sai suka hasala suka haiko masa da nufin su
kamashi
Koda ashwar yaga haka ai saiya ciro takobinsa yaringi
saransu yayin dasuka ga ashwar yayi musu muguwar
barna sai suka rabu dashi
.
Can sai gawasu dakaru nan sun kama wani mutumi
ma'abocin fararen kaya sun yiwa wannan mutumi
jina jina suna tafaman jansa akasa
.
Koda suka kariso gaban sadauki ashwar sai
shugabansu yace dashi kai wa ne ne kai da harzaka
shigo cikin birninmu sannan kayi mana irin wannan
ta'adi
.
Ashwar yace dashi ni bakone
.
Shugabar wannan dakaru ya zaburo domin yakama
ashwar aisai aswar yai wa shugabar dakarun karo
afuska,
Sai gashi ya baje akas ko shurawa baiyiba da jama'a
suka suka ga haka sai gudu, sauran dakarun da suke
tsaye suka ce da wa Allah ya hadasu in ba ashwar ba?
Ashwar baiyi tunanin amfani da makami ba a wannan
fada, don haka hannu da kafarsa ne makamansa cikin
kankanin lokaciya tarwatsasu.
.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kuyi hakuri in kunji nayi kuskure ku gyara min
.
Muhadu a part 1C
,
Littafin Amdulaziz sani/m gini(kings of adventure
stories)
.
Domin sada zumunci mu hadu a page dina na face
book https://facebook.com/Shuraih-99-296485144050085/
.
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%BABBAN GORO
.
Littafina day (1)
.
Part 1C
With shuraih 99%
.
Typing :- http://facebook.com/shuraih.usman
.
Ashwar ya kwance wannan dattijo , sai ya hangi wasu
dakarun sun bullo da kwari a hannayensu. Ashwa ya
yunkura yai alkafira izuwa inda dokinsa yake , ya ciro
mashinsa ya rike a hannu daya yana majajjawa da shi .
Dattijo ya koma bayansa ya buya . Dakarun nan suka
sako ruwan kibau , ashwar yai ta kadewa da mashin
hannunsa , har kibiyoyin nasu suka kare , sai suka zare
takubba suka yiwo kansa anan nefa ashwar yayi tunanin
yazama wajibi yayi amfani da makami.
Don haka sai ya matsa jikin dokinsa ya dau takobin nan
nasa zabbau , nan fa wuri ya yamutse, barade na kai
masa sara da suka yana karewa , shi ma yana kai musu ,
sai da aka sami sa'a guda ana wannan fafatawa sannan ya
karar da su.
.
Koda ya waiga bayansa sai yaga dattijannan akwance jini
na zuba ta gefen cikinsa . Ashwar ya ruga gareshi ya
sunkuya ya dauke shi . Faruwar hakan keda wuya ya
hango wata bataliyar ta irin wadannan dakarun da yayi
fada dasu , wadannan dakarun yawansu ya ninka na baya
sau uku. Badan tsoro ba sai don ya ceci yaruwar wannan
dattijon
Ashwar yayi sauri ya haye dokinsa rungume da dattijon
yayi cikin jeji a sukwane , dakarun suka bi bayansa amma
cikin kankanin lokaci ya basu rata mai yawa , har ya bace
musu ,
Dole suka hakura suka koma da baya.
.
Yayin da ashwar ya fuskanci sun tsera wa wadannan
makiya , sai ya tsaya a karkashin inuwar wata bishiyar , ya
sauko da dattijon nan yayi masa shimfida ya kwanta ,
sannan ya dauko wani dogon rawani daga cikin jakarsa ta
daure cikin dattijon don tsaida jinin dake zuba .
.
Ashwar ya dubi dattijon a yayin dayake kakarin mutuwa
yace "yakai babana sanar dani inda zan kaika kusa ayi
maka magani"
.
Dattijon ya yunkura cikin karfin hali tare da taimakon
ashwar ya hada bayansa da jikin bishiya ya zauna ,
numfashinsa na fita sama-sama yace
"Yaro kada ka wahalar da kanka ,ni tawa ta kare , kasani
daga nan zuwa garinmu tafiyar wata guda ce , nafito daga
birnin Nurul islam ne , garine na ma'abota Addinin
musulunci , abin dayasa kaga wadannan mutane sun
kamani suna tayi mani azaba , saboda sun ga ina bautar
ubangijin musulunci ne ina sallah"
.
Koda da jin wannan batu sai ahwar ya tuno da labarin da
tsoho makabul ya bashi dangane da maganar boka akan
daukakar da zai samu aduniya , nan take ashwar ya sake
tallafe tsohon nan akirjinsa yace
"Tuni ina da labarin wannan Addini naka , kuma nayi
imani dashi a zuciyata shigar dani cikinsa"
.
Dattijon yayi wani irin tari mai ban tsoro idanunsa suka
kakkafe kamar ya mutu , amma sai numfashinsa ya sake
dawowa yace a cikin karamar murya "yakai wannan
saurayi ka saurari abin da zan fadi yanzu ka maimaita shi,
idan kayi haka ka zama musulmi.
.
Nan take dattijon yai kalmar shahada , daa ashwar yakasa
kunnensa da kyau dai dai dattijon na gama fadin kalmar
ransa ya fita ,
Shi kuma ashwar sai ya maimaita kalmar shahada,
sannan ya mike ya haka rami ya binne dattijon yasa
alama a kabarinsa , sannan ya hau dokinsa da nufin
tunkarar birnin Nurul islam
.
Kwanci tashi ashwar nata tafiya a cikin jeji kwana da
kwanaki bai sake gamuwa da komai ba face namun jeji,
wasu sai yayi kallon kallo da su , wasu kuma ya fafata da
su ko su tsere da kansu don ganin wuya ko kuma ya
hallaka su , shi kansa ashwar sai da ya dunga mamakin
irin wannan baiwa daya keda ita ta sadukantaka da
jarumta da kuma rashin tsoro, ya tuno da cewa tun baifi
shekara goma sha ba , mahaifinsa ke tafiya da shi farauta
jeji, da hanunsa ya sha kama 'ya'yan kura da damisa ya
murde mudu wuya su mutu.
.
Tafiya dai taci gaba har ya sami kwana talatin cif , duk
tsawon iyakar kwanakin nan ashwar yayi a lissafe suke a
kwalkwalwarsa , kuma arubuce jikin kefen takobinsa , ba
dan komai ba yayi haka ba , sai don kada ya wuce
wa'adin da sarki abul dinar ya diba masa ba komawa gida
, sau tari idan ashwar ya tuno da gimbiya mabaruka sai
yayi ta yan wake wakensa ta soyayya shikadai cikin
tsakiyar dokar daji,
In banda tsuntsaye da suke tayashi da sautin kukansu, ba
ya samun mai tayashi debe kewa
.
Kwatsam ya hangi karamin gari a gabansa , kai tsaye ya
tasamma garin har ya isa , da zuw a ya iske gaba dayan
mutanen garin sanye suke cikin kamilar sutura mazansu
da matansu, musamman ma matan ko'ina a jikinsu a
rufe yake , kwayar idanunsu kacal ale gani Abin da ya fara
riska shine wani gini wanda ya iske mutane a kofarsa
suna ta shiga, wasu kuma sun tsuguna suna wanke
gabban jikunsu da ruwa. Daga can kuma sai yaga wani
daga cikinsu ya hau bisa wani tudu dake jikin wannan gini
yana wasu maganganu masu kama da karatu, aciki
karatun ne ya ji ya ambaci kalmar nan ta shiga musulunci
wadda marigayi dattijo ya biya masa .
Koda jin haja sai farin ciki ya lullube Ashwar. Ya gane
cewa wannan gari shine Nurul islam
.
Shuraih 99% nake ce daku
.
Ashwar ya sami wuri ya tsaya , ya sauka daga kan dokinsa
ya tsaya cak yana kallon mutane suna kallonsa. Jim kadan
sai yaga kowa ya shiga cikiN dakin nan, mutum daya ya
wuce gaba saura suka tsaya bayansa aka fara wani aiki
mai kama da bauta . Ashwar na tsaye yana lekensu da
mamakin abun da sukeyi har dai suka kammala , suka
firfito wannan mutum wanda ya shugabanci aikin bautar
ya nufo inda ashwar ke tsaye
.
Balarabe ne fari , kuma dogo kyakkyawa, shekarunsa zasu
kai hamsin da doriya, kamar yadda yake balar
Abe haka dukkanin sauran mutanen garin suke
.
Da zuwa ya kalli ashwar yace" yakai wannan bako daga
ina kuma me ya kawoka birninmu"
.
Da ashwar yaji wannan tambaya acikin yaren daya sani
ne wato larabci sai murna ta kama shi, nan take ya
kwashe labarinsa tun daga farko har karshe ya zaiyana
masa . Duk wannan abu dake faruwa sauran jama'ar gari
na tsaitsaye a gefe suna kallo.
.
Ashwar na gama bada labari ,sai wannan mutumi ya
rungumeshi yace "ai ka zama dan'uwanmu tunda ka
shiga Addinin Musulunci, wannan daki daka gani mun
shiga masallacine ne inda muke sallah, wannan dattijo
daka gamu dashi a wancan gari na baya daga cikinmu
yake, kuma yaje ne isar da sakon Allah ga wadannan
makafirta , shi yasa suka tsareshi suka yi tayi masa azaba .
Kashe shi da sukayi kuwa sun taima ka mashine, don
yasamu shahada babban rabo a wajen ubangijin
musulunci"
.
Balaraben ya kara da cewa "Ni sunana Imamu Hamid , ni
ne shugaba a wannan gari yanzu tunda Allah ya kawo ka
garemu sai ka zauna awannan gari don kasab yadda ake
bautar Allah kuma ka fahimci Addini , tabbas ubangijin
musulunci mai taimako ga bayinsa ne , wadanda suka
dogara dashi , tabbas zaka nasara a bisa abin daka fito
nema . Izan har baka kaucewa dokokin Allah ba"
.
.
Nan take Imamu Hamid ya rukke hannun ashwar ya tafi
da shi izuwa gidansa. Gaba daya garin kuwa ya cika da
labarin zuwan jarumi ashwar , da kuma ababan al'ajabin
da ke tattare da shi
.
Ashar ya zauna a garin Nurul islam har tsawon sati uku
inda ya koyi ibada har da karatun alkur'ani daya ke Allah
yabasi kaifin basira cikin 'yan kwanakinnan ya samu ilmi
mai yawa, kuma ya karbi littatafai na sauran fannonin
ilimin Addinin kamar tauhidi da dae sauransu, ya
kudurce a ransa zai ci gaba da neman ilmin addini a duk
sa'add ya sadu da masana.
.
Ranar da ashwar ya cika kwana ashirin da uku a wannan
gari na Nurul islam, a rannan yai sallama da su Imamu
Hamid aka kawo guzuri mai kyau aka bashi , ya yi godiya
sannan yai bankwana dasu , yatafi yana mai bakin cikin
cikin rabuwa dasu, suma suna yi, sakamakon shakuwa da
albarkar HASKEN MUSULUNCI(next book insha Allah)
.
LoKacin da ashwar yayi dan nisa da gari , sai rubuta
adadin kwanakin da yayi ajikin kufe na takobinsa, ya
lissafa dana baya sai yaga a halin yanzu ya cimma wata
uku saura kadan, ya zamana kenan baifi saura wata guda
da 'yan kwanaki ba wa'adin da aka dibar masa ya cika ,
wannan yasa hankalinsa yayi mummunan tashi , domin
ko abirnin inda Nurul islam bai samu wanda ya taba jin
labarin inda birnin duma yake ba.
.
"Yanzu yaushe nasan inda wannan gari yake har naje na
dauko bishmalu ,sannan na koma garinmu duk a cikin
wadannan kwanaki?"
.
Tambaya ce wadda ashwar yayi wa a zuciyarsa , kuma shi
kansa baisan amsarta ba .
.
Bayan kamar rabin sa'a yana tafiya , sai hadari ya hado ,
nan take ruwa ya kece kamar da bakin kwarya ,dan haka
sai ashwar ya ruga karkashin wani dutse ya fake , ya
daure dokinsa a jikin kafarsa sannan ya kishingida , cikin
yan dakiku kadan bacci ya saceshi.
.
Yana cikin wannan baccine dokinsa yayi haniniya yaja
kafarsa , ashwar ya tashi ya duba bai ga komai ba ,
Kawai sai ya koma baccinsa. Dokin ya kara haniniya a
karo na biyu . Ashwar ya farka a fusace ya mike ya dada
dubawa ko'ina bai ga komai ba , sai yayi tsammanin
dokin nasane yake bukatar yayi kiwo, don haka sai ya
kwance shi ya koma baccinsa .yin hakan keda wuya ,
kawai sai yaji saukar wani abu ajikinsa , yana bude ido
yaga raga ta rufe shi, wasu dakaru kimanin su arba'in na
ruke da ragar da makamai sun kewaye shi
.
"Tashi mu tafi " daya daga cikin baraden ya fadi.
.
Kada ku manta kuna tare ne da shuraih 99%
.
Ashwar ya dubeshi ya dubi sauran, ya tabbatar babu
imani a fuskokinsu, da farko yayi niyyar ya ganar dasu
kuransu, amma sai yace a ransa
.
"Bari dai naga gudun ruwarsu"
.
Batare da gardama ba ya bisu izuwa wani gida aka sa shi
cikin wani daki aka kulle har magariba ta kawo jiki.
Wannan tsarewa da aka masa batazo masa da illa ba sai
dai rashin sallah da kuma dokinsa da yake tunanin ya
bace a jeji, gashi duk makamansa na fada na jikin dokin .
Ashwar yadaga hannunsa sama ya roki Allah yasa wannan
tsarewa ta zame masa alheri
.
Washe gari wannan tawaga data kamo ashwar suka taru
acikin gidan , gaban ubangidansu, inda dayansu da ke
bayanin cewa basu samo koda tsuntsu ba sai wani yaro
da suka samo yana ajiye a cikin daki.
.
"To yaushe zaku cinyeshi? Ko kuwa kun fison ku gama da
tsofaffin da ku ka kamo tukunna"
.
Gaba daya sukace ai sunfi son yaron, saidai yayi musu
kadan, dan wani ma bazai samu koda rabon kunne daya
ba , nan take ubangidan wadannan mutane yayi musu
sulhu, akan a fito da naman gaba daya a cinye don kar ayi
fada.
Wannan zance gabadaya a kunnen ashwar akayi shi.
Don haka sai ya cika da mamaki daya ji ana maganar a
cinye dan adam kamar yadda ake cin naman dabba.
.
"Ni kuwa naga ta yadda za a cinyeni ina ji ina gani"ashwar
ya fadi cikin zuciyarsa.
.
Dankari makari,lallai yau akeyinta inji 99% ke magana'
.
Jim kadan aka bude dakin da ashwar ke ciki, abinci ne aka
kawo, wani gajeren mutum ne kato ya shigo da shi cikin
wata karamar tasa ko sallama babu ya ajiye , ya juya ya
fita aka garkame kofa, ashwar ya dubi abincin na yaga bai
san irin saba gashi yana jin yunwa amma sai yafara wasi
wasi ko yaci ko ya bari.
Tabbas yasan dae mutanenan kafiraine baisan ma koda
me sukayi abincin ba. Kawai sai ya yanke shawarar yayi
baccinsa na jiya da baikarisa ba , nan take ya bingire yai
ta sharara barci kamar wadda yake cikin gidansa
.
Kwatsam yaji wata murya a sama ance " tashi mu tafi"
.
Yana bude idanunsa yaga wasu kartine suk uku.
Ashwar ya tashi bako musu suka sa shi agaba sai wajen
babbansu , wani katone mai tumbi, ya saki ciki sai kace
garwa. Cikin tsawa ya dubi kattin yace
.
"Ku ajiye shi anan ! Ku fito da tsofaffin"
.
Ashwar ya zauna yana kallon ikon Allah sai yaga an fito da
mutane sun fi dari, nan dai yaga anjera su gaba daya alayi
kamar masu shirin tada sahun sallah,
Hardashi ahwar din
Mai katon cikinnan ya tashi da kyar ya fara zagaya su
ashwar, bai dafa kowa ba sai wani tsoho wanda ko
kyaleshi akayi ya kalli kisan da za'aiwa sauran zai iya
mutuwa don tsananin firgita , don ko ayanzu ma baisan
cewa yana fitsari a wando ba , jikinsa na kyarma tamkar
mai mugun zazzabi , nan take karti suka kama wannan
tsoho suka jefa shi cikin wata katuwar tukunya wadda ke
karkashin wata murhun wuta na dafuwa, ruwan ya
cikinta sai zabalbala yake ,
Ai kamar hadiyar kwayar gero haka tsohonnan ya lume
cikin tukunyar , ko tarinsa ba'a jiyo ba.
Wasu karti su biyu da suke rike da ludayin tukunyar suka
hada hannayensu hudu suka tura ludayin zuwa karkashin
tukunyar suka tsamo.
Sai ga gangar jikin tsohonnan ta motse kamar curin
nakiya, gaba daya fatar jikinsa ta sutale duka akansa kuwa
babu silin gashi koda daya , atakaice dai ya dahu yai
lugub . Ja daya za aiwa tsokar namansa ta rabu da uwar
jiki.
.
Koda ganin wannan al'amari sai ashwar yai salati yace"
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
.
Kafin a ankara ya suri kato guda ya mai dashi bulala , yai
ta dukan sauran kattin , nan da nan gida ya rikice da ihu
da kuwwa , katon nan da ke zaune a kujera kamar kula
sai kujerar ta karye ya fado ji kake tim! Bama kafiran
azzaluman mutanen ba wadanda ma aka kamo don
acinye saida suka gigice.
Tsoffin cikinsu suka shiga wani hali don wasunsu ma sun
fado sun ture abincin . Azzaliman kuwa duk sun firgice
sun dimauce , wasu su kayi waje da gudu wasu suka yiyo
kan ashwar wato masu karfin halin kenan , shi kuwa yaci
gabada da rugurguzarsu suna zubewa kamar mai kada
karmami. Musulman da aka kamo suka hau salati.
.
Bayan da ashwar ya sumar dana sumarwa ya kashe na
kashewa , masu gudu kuwa suka tsere ya rage saura
shugaban masu cin naman mutanen nan kadai, kwance
akas ya kasa tashi bare ya gudu, sai nishi yake da kyar ,
nan take ashwar ya kaimasa wawura ya sunkuce shi sama
duk girmansa ya zama na banza , don tamkar ashwar ya
daga buhun audiga ne, tsundum ya jefashi cikin wannan
tukunya mai zabalbala , jama'a gaba daya suka rugo
wajen ashwar suna yi masa godiya da sa albarja ashwar
ya fice ya bar su suna ta murna da wake-wake .
Wani abin mamaki yana fitowa daga cikin gidan sai ya
iske dokinsa tsaye kamar dama yasan da fitowarsa yanzu,
Ashwar ya kalli dokin yayi murmushi sannan yace
"Daga yau nasa maka suna ganjarma"
,
Kai masu karatu nafara gajiya fa 99% ke magana
,
Ashwar yayi tsalle ya haye kan ganjarma , ya sukwane shi
zuwa cikin jeji.
Wannan shine abin daya faru ga jarumi ashwar, bayan ya
baro garin Nurul islam
.
.
Naga kamar bakwason littafinnan
Anya kuna son inci gaba kuwa
.
.
Littafin abdulaziz sani/m gini(kings of adventure stories)
.
Typing:- Shuraih Usman
Tel' 08133209890
.
.
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
Shuraih Usman
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%BABBAN GORO
-------------------------
Littafina daya
.
Part 1D
.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman
.
Al'amarin kifyan sarkin aljanu kuwa wanda gidansa yake
cikin karkashin kasa , a tsakiyar ruwa, rabon daya fito tun
lokacin daya bayar da tsaron bishmalu dan sarki kan'anu
na misra
.
A halin yanzu bishmalu ya zama saurayi dan shekara
sahirin da biyar. Kuma a iya tunaninsa bai da wani uba
wanda ya fi kifyan , amma bai taba ganinsa ba a zahiri sai
acikin madubin tsafi
.
Fitowar sarki kifyan keda wuya aka lullubeshi masu
gaisuwa nayi, masu bambadanci nayi shikuma sai ya hau
kankaragarsa ta mulki ya zauna , sannan yace aje a zo
masa da dansa , nan take aka zo da bishmalu , bishmalu
ya durkusa yayi gaisuwa.
.
Kifyan yace" na fito ne domin ganinka , dakuma son
gabatar da wani muhimmin zance a gareka , wanda baka
san dashi ba , yanzu ne lokacin da zan yi maka bayani ka
fahimta tunda ka mallaki hankalin kanka .ya kai bishmalu
ka dubi kowa dake cikin fadar nan ka dubi kanka ,zaka ga
cewa ba irin kirar halittar ka bane , domin mu aljanune
kai kuma bil'adama ne, to kasani kai ba dana bane .
iyayenka bil'adama ne kamar kai , ni sato ka nayi tun
kana jariri sakamakon laifin da mahaifinka yai mini, ya
auri matar dana ke so"
.
Nan take kifyan yai nuni da hannunsa izuwa wani
madubin tsafi ! Sai ga hoton sarki kan'anu kwance bisa
gado a turakarsa yana jinya.
.
"Wannan shine mahai finka, daga nan zuwa inda
mahaifinnan naka yake tafiyar wata da watannice . Kasani
ya kai bishmalu son dana kewa mahaifiyarka shine ya
dawo kanka a yanzu.
.
Kifyan ya sake nuni da hannunsa izuwa wani madubin
tsafi sai ga hoton ashwar bisa doki a dokar daji yana
tafiya.
.
"Wannan wani jarumine da ake kira ashwar , wanda ya
taho da niyyar fitar dakai daga cikin gidannan ya mai da
kai hannun babanka, amma bai san cewa yayi babban
kuskure ba , har duniya ta tashi ba wani mahalukin
bil'adama daya isa ya shigo cikin fadata"
.
Kifyan na gama wannan jawabi ya tuntsure da
mahaukaciyar dariya wadda tasa gidan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment