Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kama girgiza ,
har sai da ya rufe bakinsa sannan gidan ya tsaya daidai.
.
Bishmalu ya dubi sarki kifyan yace " ya kai sarkin sarakai
badan kada ranka ya baci ba da nace kasa akaini wajen
mahaifina mu gana "
.
Cikin fushi sarki kifyan ya mangare bishmalu da iskan
bakinsa sannan yace" a kul nakara jin kace na kaika
wajen babanka"
.
'Da nine inba sai ankaini wajena babana ba ko ata masifa
99% ke magana
.
.
"To kasani daga yau duk kimarka ta zube a idanuna
gwarama ka kasheni na huta da takaicin abin daka yiwa
mahaifina"
.
Kifyan ya sake bushewa da dariya , sannan yadubi
fadawansa yace" ku na son wannan yaron ko kuwa na
kasheshi yanzunnan?"
.
Gaba daya suka rude da cewa " muna sonsa ya sarkin
duniya"
.
Wannan hayaniya ta fadawan kifyan tasa bishmalu ya
firgice ya fadi kasa sumamme,
Nan take sarki yasa akayi wani turare na hayaki , aka
fesawa bishmalu ya farfado, sarki ya sake dubansa yace
" Yanzu wakake so mu ko iyayenka"
.
Bishmalu yace" ku nake so, don ku ne kuka reneni , ban
san wadan can ba"
.
Koda jin haka sai fada ta rude da shewa , nan take
akayiwa bishmalu wanka ya zama dan sarki kifyan, aka yi
biki da gagarumat walima , bayan an kare, sarki kifyan ya
zagaya da bishmalu cikin fadodinsa guda ashirin da
bakwai da ke cikin wannan gida na sarauta, ya nuna masa
sirrikansa gaba daya banda sirrin inda ruhinsa yake.
.
Wannan shine abin daya faru tsakanin sarki kifyan da
bishmalu dan kan'anu na misra, wanda ke can kwance
cikin jinyar rashin lafiya tsawon shekaru ashirin da biyar.
.
.
Shuraih 99% ke ce daku
.
Ashwar na can cikin jeji ya kutsa kai , bai san ma inda
yake nufa ba . Kwanci tashi yaje wani gari , yasamu wasu
mutane a bakin kofar shiga ashwar ya sauka daga kan
ganjarma yayi wa mutanen sallama , sai yaga basu
kalleshi ba , ya kuma matsawa yai sallama , kawai sai suk
zabura wajen su goma shahudu suka kewayeshi, wani
daga cikinsu yace
"Kai yaro mene ne ya biyo dakai ta wannan kofar? Baka
sani ba cewa garinnan yana da kofofi hudu amma
wannan ta zama mallakinmu? Ba a wucewa ta nan sai
anbiya harajinka dana dokinka"
.
Ashwar ya dubesu a wulakance yace" menene kuma
haraji?"
.
Wannan batu ya harzuka gudansu, don haka sai ya zagaya
bayan ashwar da nufin ya sharara masa mari, caraf sai ga
hannunsa a hannun ashwar, ya zaci abin na wasa ne , sai
yaji ana rumurmutse masa hannu kamar gyale , mtumin
ya ringa ihu da sauran suka ga haka sai suka debi
sanduna suka rufe ashwar da duka titim! Titim!! Suna
bugunsa sandunan na karairayewa , tamkar akan dutse
suke bugawa . Gaba dayansu suka firgita da ganin
wannan al'amari, sai suka arce
.
Ashwar ya kada linzamin dokinsa ya shiga cikin gari . Yana
cikin tafiya yaga wasu 'yan mata su shida kyawawan
larabawa , sun debo ruwa a tulu daga rafi . Ashwar ya
dubi wadda tafi sauran kyawu yace " 'yan mata dan Allah
taimaka mini da ruwannan mana na sha"
.
Batare da jin kai ko wulakanci ba ta miko masa tulunta,
Ashwar ya karba ya kafa kai ya zuke fiye da rabinsa,
sannan ya miko mata, sannan yayi godiya .
Sauran 'yanmatan suka dubeta suka kyalkyale da dariya ,
wata cikinsu tace
.
"Yanzu ke Asma'u don wahala bata isheki ba shine zaki
bayar da kyautar ruwan da kika debo acan nesa da gari ,
aikuwa mu baza mu koma da baya ba don raka ki debo
wani"
.
Nan take suka wucu su kai gaba , ita kuma Asma'un sai ta
dora tulunta aka ta juya da baya dan komawa rafi. Koda
ganin haka sai ashwar ya sauka daga kan dokinsa yace ta
hau , shikuma ya ruke mata tulun , batare da musu ba
Asma'u ta hau kan ganjarma Ashwar ya ruke mata
linzamin , su kai gaba suna tafe suna hira kai da kagansu
sai ka dauka bawa ne da uwargijiyarsa, kasancewar
ashwar bakin fata ita kuma balarabiya.
.
Shuraih 99% nake ce daku"Kai kuna tare dani kuwa "
.
"Baiwar Allah shin anan garin kuwa akwai musulmi
mabiya Addinin musulunci?"
Ashwar ya tambaya
.
"Kwarai kuwa , fiyr da rabin mutanen garinnan duk
musulmine sai de , saidai sarakunanmu azzalumaine ,
kuma mai karfi shi ke da ikon yin abinda yaga dama ,
yanzu haka da akwai wasu azzalumai 'yan fashi da suka
addabe mu, shi yasa da zarar magariba tayi kowa sai ya
shige gidansa ya rufe kofa , komai zafi ba a isa ayi
kwanciyar waje ba , in kuwa mtum ya kwanta a waje
saidai da safe a ga gawarsa "
.
Koda ashwar yaji haka sai ya cika da mamaki yace " Ni
kuwa da yardar Allah zanyi muku maganinsu daga yau
sun dai na yin fashin"
.
"Haba dan samari wane kai , ai BABBAN GORO SAI
MAGOGIN KArFE. Mutanan da sun fi mayakan garin nan
ma karfin tsafi da sihiri , ya za kai da su"
.
"To shikenan tunda kina shakka ina so ki amince mini
kwana a kofar gidanku"
.
"Wannan mai saukine amma fa duk abin daya sameka
kada ka zargi kowa ka zargi kanka"
,
99% ke magana kuna biye dani kuwa
.
Haka dai ashwar da Asma'u suka ci gabada hira har suka
je rafi suka debo ruwa suka dawo.
Asma'u takai ashwar gidansu ta gabatar dashi a gaban
iyayenta , tare dayi musu bayanin tarar aradu daka
wadda yace zaiyi cikin mamaki mahaifin Asma'u ya dubi
ashwar da kyau yace
.
"Kai yaro shin rayuwar duniyace ta ishe ka haka ko kuwa
wani abin bakin ciki ne yasa kazabi mutuwa akan
rayuwa?"
.
Ashwar yayi murmushi yace " baba babu ko daya amma
dai ni nakasance mai son yin fada da karya da kuma
azzalumai, na tsani kafirci da zalunci , burina Addinin
musulunci ya rinjayi kafirci a doron kasa, bana dogoro
ko takama da karfi ko tsafi,face taimakon ubangijina
wanda shine masanin dukkan abinda ke fili da boye "
.
Wannan batu yasa jikin mahaifin asm'u yai sanyi yayi
shiru daga bisani yace
"To masu magana sunce ba'a kwacewa yaro garma
amma wannan garmar da kake shirin dauka tafi ka nauyi
sai dai muce Allah yaba sa'a"
.
Haka dai ashwar ya cigaba da hirarsa da Asma'u da
iyayenta har rana ta fadi.aka kawo abinci sukaci tare
gabadaya , magariba nayi suka yi sallama da shi suka
shiga cikin gida suka rufe kofa .shi kuwa gogan sai yai
alwala yai sallah a kofar gidan , har ya idar da sallar yayi
yan Addu'oinsa baiga wani yazo gare sa ba ,
Ashwar ya debi ruwa arijiya ya baiwa ganjarma sannan
yai shimfida. Agefe gida yayi kwanciyarsa tamkar yana
cikin dakin matarsa.
.
'Yan fashinnan da suka saba shigowa sai gasu sun dira
akan ashwar kimanin su arba'in ashe Asma'u a soro ta
kwanta koda taji magan ganunsu sai ta kwalla ihu take
ashwar ya farka , alokacin har daya daga cikinsu ya hau
kan ganjarma yana cewa
" Ni kam yau na fito a sa'a na samu lafiyayyen doki"
.
Ashwar ya mike zumbur ya dube su yace " ku azzaluman
bayi me ke tafe daku"
.
Gaba dayansu suka bushe da dariya , dayansu yace
"Yau kuma bakon marar kunya aka samu a garinnan ? Kai
yaro yau karar kwana ta kawo ka makasa "
.
Wannan batu ya fusata ashwar nan take ya hausu da
duka, gashi babu ko allura agareshi amma su da manyan
makamai a hannunsu ya zame musu ala kakai, duk
wanda yakai masa sara ko suka sai ya goce cikin zafin
nama ya kama hannunsa ya murde ko ya karya. Cikin
kankanin lokaci ya zubar da mutum goma kasa
sumammu da 'yan fashinnan suka ga haka sai suka fara
jarraba tsafe tsafensu da sihirce sihirce, amma duk suka
zama a banza don basuyi tasiri ba akan ashwar ,
sakamakon Addu'ar daya ke ta karantawa a zuciyarsa ,
nan fa wuri ya dada ya mutsewa , ihu da kuwwar 'yan
fashin tasa duk jama'ar garin suka bubbude gidajensu
suka fito, don ba'a taba jin irn wannan tashin hankali ba a
garin . Yayin da jama'a suka taru sai aka iske ashwar tsaye
shi kadai a kofar gidansu Asma'u .
'Yanfashinnan gaba dayansu su arba'in suna kwance cikin
jini, wasu a sume , wasu akarairaye. Nan take gari ya
dauka da shewa don farin ciki aka yi ta al'ajabin
jarumtakar ashwar.
.
Koni nan nafishi jarumta 99% ke magana
.
Ita kuwa Asma'u saita ruga da gudu ta rungume Ashwar
tana cewa ta samu mijin aure Mutanen gari sukayi ta
kawowa ashwar kyautar dukiya, amma ko daya bai karba
ba .
Anan ya sanar dasu labarinsa da dalilin fitowarsa daga
garinsu, ya bukaci o akwai wanda yasan inda birnin duma
yake .
Gaba daya akayi shiru sai daga can wani dattijo tsoho
tukuf wanda duk garin babu mai tsufansa ya dogaro da
sanda ya karaso inda ashwar ke tsaye ya dafa shi ya ce
.
"Yaro nasan inda birnin duma yake"
.
Koda jin haka sai farin ciki ya kama ashwar , ya rungume
tsohon yana mai matukar farin ciki, daga nan yabi tsohon
zuwa gidansa.
.
Daga nan zuwa birnin duma tafiyar shekaru ukune.
Birnin duma garine na aljanu zalla inda sarki kifyan ke
mulki" dattijo yafadi tare da ajiye numfashi.
.
Cikin tsananin damuwa Ashwar yayi ajiyar zuciya yace "
hakika duk abin da aka fadi haka yake , amma ni yanzu
guiwata tayi sanyi , burina ya yanke ,domin babu yadda
za'ai naje birnin duma a cikin kwanankin da aka diba
mani wa'adi"
.
Bisa mamaki tsohon ya dubi ashwar yace "ban gane
bayanin ka ba "
.
Shuraih ke cewa daku
.
Nan take ashwar yai masa cikakken bayani kan sharadin
da sarki Abul dinar ya shimfida masa , kafin ya amince ya
aura masa gimbiya mabaruka . Tsoho yayi shiru yana
tunani har izuwa wani dan dogon lokaci , sannan yace
"Ya kai wannan jarumi ina da wani dan'uwa wanda zai iya
taimakonka a bisa wannan al'amari sunansa raslanu ,
bawan Allah ne wanda ya kaura daga cikin gari ya koma
can jejin surgam yaci gaba da bautar ubangiji, don kada
wani abun duniya ya rude shi daga nan zuwa jejin
surgam tafiyar kwana goma sha biyuce, amma ka sani
akwai ababan hadari a wannan jeji, fiye da shekaru sittin
a tarihi babu wani mutum wanda ya keta ta cikin surgam
batare da ya zama gawa ba, face wannan dan'uwa nawa
wato ruslanu. Shi ma hakan ta farune sabida Allah ya
hore masa baiwa mai dumbin yawa . Idan har ka sami
nasarar ganinsa , tamkar ka sami nasarar shiga fadar
sarki kifyan ne"
.
Ashwar yayi shiru yana nazarin wannan bayani sannan
yace " ya kai wannan dattijo mai albarka , ina tabbatar
maka da cewa ko zan rasa raina sai naje jejin surgam na
sadu da wannan dan'uwa naka Ruslanu, kuma gobe
goben nan zan yi shiri na tafi
.
Ashwar na rufe baki suka jiyo tambura sun cika gari ,
cikin sauri suka fito daga cikin gidan, kawai sai su kai arba
da mutane jingim akasa , sun rako wani doki guda daya
izuwa ga ashwar , ba kowa bane akan dokin face Asma'u
ta sha kwalliya da ado irin na amare, cikin mamaki
ashwar ya tambaya
"Me ke faruwane"
.
"Ai an daura aurenka ne da Asma'u , yanzu haka
amaryarka muka kawo maka"
Mahaifin Asma'u ne da kansa tabada wannan amsar
.
.
Laifin dadi karewa
Abdulziz sani m/ gini ke ce daku
Kash! Mai karatu anan zan dakata sai mu hadu a BABBAN
GORO KaSHI NA BIYU don mu ji yadda zata wakana
.
SHIN JARUMI ASHWAR ZAI YADDA DA WANNAN AURE DA
AKA YI MASA BATARE DA NEMAN AMINCEWARSA BA?
.
ME ZAI FARU YAYIN TAFIYARSA ZUWA JEJIN SURGAM?
.
A CIKIN WANI HALI GIMBIYA MABARUKA TAKE AYANZU?
.
SHIN ALJANIN BOKA GULMANU KUTUNTUMA NA BIYE DA
JARUMI ASHWAR KUWA?
.
TA YAYA ASHWAR ZAI SHIGA BIRNIN DUMA HAR YA SHIGA
FADAR SARKI KIFYAN YA DAUKO BISHMALU?
.
Toh Alhamdulillah dama tun kafin nafara na sanar daku
cewa book 1 ne kadai akasa
.
Sai kun jini a sabon littafi
$ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
Shuraih Usman
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment