Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskarsa daidai tata, ya ce, "Ke Darzil ina sauran abokan tafiyarki kuma ina mutane hamsin ɗin da kuka saba kawo mini a kowanne mako?"
Cikin ƙarfin hali Darzil tace,
"Ya shugabana ka yi sani cewa wannan karon sabon al'amari ya faru domin wasu baƙin shaiɗanun mutane sun bayyana a birnin Azbir har sun ƙera wata ƙatuwar kibiya wadda ta hallaka abokan tafiyata da ƙyar na tsira da rayuwata."
Jin wannan batu sai Galbasa kwarara uban ihu, wanda ya sa fadar gaba ɗaya yin girgiza.
Cikin tsananin fushi ya yi wurgi da Darzil tamkar yayi jifa da 'yar tsana,sannan ya ɗauko wani zagayayyen farin dutse ya shafa shi da tafin hannun sa. Nan take hoton abinda ya faru tsakanin su Darzil da su Gulzum ya bayyana.
Galbasa ya ƙarewa su Jafar kallo tsaf ya jinjina kai sannan ya waigo ya dubi babban bafadensa Barzuzu yace,
"Yakai Barzuzu ka yi sani cewa waɗannan baƙin mutane ba ƙananan shaiɗanu ba ne. Haƙiƙa mun fi ƙarfinsu to amma sun kasance masu matuƙar hikima. Lallai ina so ka je ka yi tunani akan yadda zamu iya hallaka wannan mugun makami da suka ƙirƙira domin mu, sannan mu yi gagarumin shiri mu je mu shafe garin gaba ɗaya yadda ko a tarihi ba za'a tuna da shi ba."
Yayin da Barzuzu ya ji wannan batu sai yace, "Ya shugabanmu yanzu don wannan ɗan makamin na su guda ɗaya zamu yi gayya da shiri. Ai ina tabbatar maka da cewa ni kaɗai ma idan ka turani zan iya hallaka su, na ƙone makamin na su."
Koda jin haka sai Galbasa ya yi murmushi ya ce, "Kai ƙaramin mayaƙi ne baka san tuggun yaƙi ba. Kar ka yi tsammani za su tsaya ne jira kawai,suma sabon shiri za su yi don sun tabbatar da cewa ba zan kasa ɗaukar mataki ba. Ka yi sani cewa waɗannan mutane sun karya mana darajarmu a wannan duniya tamu, domin fiye da shekaru dubu baya ba'a taɓa cinmu da yaƙi ba, don me za mu yi sakaci wasu mitsatsan mutane kuma baƙi daga wata duniyar su shigo har tamu duniyar su cimu da yaƙi. Lallai ka hanzarta yin abin dana umarce ka."
Barzuzu ya sunkui da kai ƙasa, ya ce, "An gama."
Barzuzu ya miƙe tsaye ya fice daga cikin fadar. Galbasa ya dubi Galadimansa ya ce, "Ya kai Hutum ka je kasa a yi shela a gari cewar ban ɗaukewa kowa wannan yaƙi ba, babba da yaro,mace da namiji. Lallai kowa ya fara shiri nan da kwana bakwai za mu ɗunguma ƙwanmu da kwarkwatarmu mu tafi birnin Azbir sai mun shafe garin gaba ɗaya, mun zuƙe jinin kowa da komai, kai ko tsuntsu guda ba zamu bari ba a garin face ya zama maye kamar mu."
Hutum ya risina, ya ce, "An gama ranka ya daɗe."
Nan take fada ta watse, kowa ya kama gabansa.
Lokacin da sarki Galbasa ya shiga cikin gidansa zuciyarsa baƙin ƙirin take, kuma tana tafarfasa, kamar za ta faɗo ƙasa, sai ya iske matarsa Hatimal tare da kyakkyawar 'yarsa, Mazalish zaune sun yi jugum. Koda ganinsa sai Mazalish ta miƙe zumbur cikin yanayin damuwa ta tare shi, tana mai cewa,
"Ya kai Abbana wane irn yaƙi ne ya taso mana haka har da za ka ƙi ɗaukewa kowa da kowa yaro da babba?"
Koda jin wannan tambaya sai sarki Galbasa ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Yake 'yata mafi soyuwa a raina, kin sani cewa a duniyar nan tamu kaf babu abin da nake so sama da ke, saboda tsananin son da nake yi miki ne ya sa na raba ƙarfina da tsafina na baki rabi-rabi. Kuma saboda tsananin son da nake yi miki ne na cire miki maita ya zamana ke kaɗai kika fita dabam da kowa a garin nan. To ki ƙara sani ke ma ɗin ban ɗauke miki wannan yaƙi ba,domin da na yi asarar wannan yaƙi gwara na rasaki.
Asarar wannan yaƙi daidai take da asarar mulkina,ƙasata da al'ummata gaba ɗaya. Tabbas idan ba mu yi nasara a wannan yaki ba, shi kenan sai dai a tuno da mu a tarihi domin hatta ƙasar nan tamu shafe ta za'a yi."
Yayin da sarki Galbasa ya zo nan a zancensa sai hankalin Hatimal da na Mazalish ya ƙara dugunzuma fiye da da. Nan take idanun Mazalish ya ciko da ƙwallah, ta dafa kafaɗunsa da hannu biyu tace,
"Ya kai Abbana ka tuna cewa ni a iya sanina ban taɓa ganin jarumi mai tsananin ƙarfin damtse da iya yaƙi kamar ka ba. Haka kuma ban taɓa ganinbmashahurin matsafi irin ka ba, domin a matsayinka na bil'adama har takai cewa ka juye ka zama ruwa uku. Za'a iya kiranka aljani ko fatalwa ko maridi,domin ba ka mutuwa ko an kasheka tashi kake yi.
Ga shi shekarunka a duniya sun linka irin na bil'adaman wannan zamani, don na tabbata kafi shekara dubu biyu a duniya.
To don me wani mahaluƙi zai zo lokaci guda rana tsaka har ya firgitaka ka ce da jama'arka kowa ya fito da ki bacin ni a zatona kai kaɗai ma zaka iya tashin ƙasa guda ta bil'adama?"
Sa'adda sarki Galbasa ya ji wannan tambaya daga bakin 'yarsa Mazalish sai ya yi shiru gami da sunkuyar da kai ƙasa, cikin yanayin damuwa, sannan yace,
"Yake 'yata ki yi sani cewa kamar shekaru goma sha tara baya lokacin da ya rage saura shekara ɗaya a haifeki na yi wani dogon nazari a cikin bincikena na tsafi na gano cewa akwai wasu irin mutane da za su zo daga wata sabuwar duniya dabam su yaƙe ni har su cini da yaƙi. Tabbas ba wasu ba ne waɗannan mutane face waɗanda zamu tunkara yanzu. Ina tabbatar miki da cewa siffofinki irin na waɗannan mutane ne domin in kikai tunani duk a ƙasar nan babu mai ƙaramin jiki irin na ki.
Babu irin ƙoƙarin da banyi ba akan na gano hanyar da zan bi na hallaka waɗannan mutane idan sun zo,amma na kasa. Da naga haka sai na ci gaba da bincike akan ya za'a yi na tsira da rayuwata idan sun zo ɗin, sai na gano cewa in dai ina son tsira saidai idan na haifeki na cire miki maita kuma na raba ƙarfin jikina da tsafina na baki rabi.
Tabbas indai ina tare da ke zan kuɓuta. Haka kuma na gano cewa a sanadiyar wannan yaƙi ne zan rabu da ke rabuwa ta har abada, amma ban ga yadda zamu rabu ba."
Ko da Galbasa ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka kaɗa suka yi jawur, suka fara shirin zub da hawaye, ita kuwa Hatimal tuni ta fara kuka tun sa'adda ta ji batun ccwa za ta rabu da 'yarta. Mazalish ta rungume Galbasa tana mai rusa kuka, tace,
"Yanzu in na rasaka ina zan sami uba kamar ka?"
Koda ganin haka sai ita ma Hatimal ta ruga gare su ta rungume su gaba ɗaya tana mai taya su kuka.
A can birnin sarki Azbir kuwa sai da aka kwana ana walimar farin cikin samun nasara akan mutanen Galbasa. Har aka ƙare walimar su Mashrila ba su saki jikinsu sosai ba, domin duba ɗaya za ka yi musu ka san cewa suna cikin damuwa, kai ko murmushin arziƙi ba sa iya yi, sai dai ka ga suna yaƙe. Ana ƙare walimar ne Mashrila ta ce babu wanda zai je ya kwanta sai dai a ci gaba da ƙera kibiyoyin nan da na'urorin harba su kuma ba za'a tsaida ba,dare da rana. Hakan kuwa aka yi domin sai da aka kwana shida ana wannan aiki har aka kai gacin ƙera kibiyoyi dubu ɗari uku da sittin da na'urorin harba su guda dubu ɗari shida da arba'in, wato dai na'urorin sun fi kibiyoyin yawa. Nan take aka ware mutane da yawa adadin yawan na'urorin aka koyar da su sarrafa na'urar da iya harba kibiya. Ba'a gama wannan shiri ba, sai a daren kwana na bakwai.
Yayin da dare ya raba, mutane sun gaji saboda gajiyar wannan gagarumin aiki da suka sha fama a dalilin hakanne aka fara tafiya ana kwantawa.
Mashrila,Jafar,Yelisa,Gulzum,sarki Azbir da manyan dakarun ƙasar kuwa basuje sun kwanta ba,duk sai suka hau kan na'urar harba kibiyoyi suka yi fako suna jiran farmakin mutanen Galbasa don sunsan ako yaushe suna iya zuwa. Da yawa daga cikin suma gyangyaɗi sukeyi, amma har gefin asuba basu ji motsin komaiba kuma kusan ko yaushe
hankalinsu akan sararin samaniya yake, kai har gari ya waye rana ta buɗe sosai ba'aji komaiba ba aga komaiba, wannan tasa mutane suka fara sakin jikinsu,Karfan yazo gaban sarki Azbir ya ce "Ya shugabana ina ganin Galbasa da Jama'arsa sun tsorata damu baza su sake kawo mana hariba." Koda jin wannan batu sai sarki Azbir ya turɓune fuska yace,
"Ashe baka da hankali to dakata na gayamaka kaji har abada karka saki jiki da abokan gaba komai shirinka da ƙarfin ka. Kai a tsammanika don munyi musu ɓarna zasu ji tsoronmune su daina zuwa. Dubi canfa kagani mutanen sune guda huɗu tsire da kibiyoyi a kwance,har yanzufa da ransu motsi sukeyi inda zasu iya cire kibiyoyin jikinsu da tuni sun halakamu, ina tabbatar maka da cewa tuni labari ya isarwa Galbasa kuma tabbas zaiyi shirin ɗaukar fansa. Babu mamaki yana kan hanyarsa ta kawo mana mamaya.........." Kafin Karfan ya ƙara buɗe baki yace wani abu sai suka ga
wasu abubuwa acan ƙololuwar sama kamar tsuntsaye. Saboda yawansu sun lulluɓe saman wajen gaba ɗaya har sun dusashe hasken rana kuma sun tsaya cak su ba su sauko ƙasa ba kuma basu ƙara yin samaba,nanfa kowa ya ɗaga kansa sama hankali ya dugunzuma kowa ya fara faɗin albarkacin bakinsa,wasu suce ai tsuntsaye ne wasu kuma suce wannan dai wata sabuwar masifarce, cikin tsawa mashrila tace, "ku shashashai ku nutsu kowa ya ɗana kibiyarsa, waɗancan abubuwan da kuke hangowa ba komai bane face gungun dakarun Galbasa."

Anan zamu dakata, sai wani lokacin idan Allah ya kaimu.
Fatan alheri.Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part J

A baya, mun tsaya a inda:-
A ranar da Nazmir ya cika shekaru ashirin cif a duniya, sai Halufa ya shirya masa walima,a wannan rana Zuwaisa ta sha ɗawainiyar girke-girke.

####
In ba don ma ta sami taimakon ƙawayenta ba iyayen su Husuf da aikin yafi ƙarfin ta, gaba ɗaya 'ya'yan sarakan garin sai da suka halarci wannan walima.
Kai daga wasu ƙasashen ma haka 'ya'yan sarakai suka yi ta shigowa cikin birnin Dahamul duk da cewa kuwa da yawansu ba gayyatarsu aka yi ba.
Kawai sunzo ne don su ga jarumin da
labarin sa ya cika duniya wato Nazmir bin Halufa.
Yayin da taro yayi taro sai jarumi Nazmir tare da abokanansa suka yi ta
gaisawa da baƙi ana bashi kyaututtuka,kai har saida ya gaji da karɓar kyaututtukan ya wakilta su Huzaik suka cigaba da karɓa.
Nan take aka shigo da kayan ciye-ciye
da shaye-shaye,makaɗa da mawaƙa kuwa suka hau aikinsu.
Nazmir ya koma inda iyayensa ke zaune cikin farin ciki suma abokansa
suka koma gefe guda ana kallon masu yin rawa.
Anan cikin tsakiyar wannan shagali ne aka hangi sarkin dogarai ya shigo wajen kai tsaye riƙe da wata takarda a hannunsa.
Nan take wurin yayi tsit kowa ya ƙame
tamkar babu mai numfashi a wurin kai
kace mutuwa ce ta gifta. Sarkin dogarai ya ƙaraso gaban Halufa ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya miƙa masa takardar yace, "saƙo ne daga majalisar sarki."
Koda Halufa ya karɓi takardar sai ya miƙawa Nazmir ba tare da ya duba ta ba yace, "ya kai ɗa na buɗe takardar nan ka karanta abinda ke ciki a fili mu ji."
Cikin biyayya Nazmir ya buɗe takardar ya fara karantawa kamar haka:-
"DAGA MAJALISAR BIRNIN DUHAMUL ZUWA GA SARKIN YAƘI,JARUMI UBAN JARUMAI, SADAUKI HALUFA.
YA KAI GARKUWAR MUTANEN DUHAMUL KAYI SANI CEWA HAR KWANAN GOBE WANNAN MAJALISA NA ALFAHARI DA KAI A MATSAYIN KA NA SARKIN YAƘIN TA DON HAKA GAISUWA,YABO DA KARAMCI SU TABBATA A GARE KA, KAMAR YADDA KA SANI CEWA SHEKARUN BAYA AN SAUKE KA DAGA KAN AIKIN KA HAR TSAWON SHEKARU ASHIRIN.
TUN DAGA WANNAN LOKACI KAWO IYANZU BA'A NAƊA SABON SARKIN YAƘI BA.
MAJALISA NA SANAR DA KAI CEWA WA'ADIN DA AKA ƊIBAR MAKA YA CIKA DON HAKA ANA UMARTARKA DAKA DAWO BAKIN AIKI.
DA FATAN ZAKA KASANCE MAI BIYAYYA GA MAJALISA."
Yayin da Nazmir ya gama karanta wannan wasiƙa sai ransa ya harzuƙa,har ya yunƙura zai yayyaga takardar sai Halufa yayi masa wani irin kallo.
Nazmir ya ajiye takardar a gefe guda shi kuwa Halufa sai ya dubi sarkin dogarai yace, "kaje ka sanar da majalisa cewa saƙo ya zo mini kuma gobe da safe zan hallara a fada."
Sarkin dogarai yayi godiya ya fita cikin
farin ciki.
Shi kuwa Halufa sai ya bayar da izinin
a cigaba da walima.
Take wuri ya sake hautsinewa da hayaniyar kaɗe-kaɗe da raye-raye.
Ba'a gama walimar ba sai da duhu ya fara sannan baƙi suka fara yin sallama suna bankwana ɗaya bayan ɗaya.
A haka dai wuri ya ɗaɗe aka bar su Halufa kaɗai.
Nan take halufa ya koma kan kujera ya zauna sannan ya umarci su Nazmir da su zauna.
Dama Zuwaisa na can gefe ɗaya a zaune. Halufa ya dubi Nazmir yace, "ya kai ɗana haƙiƙa na fuskanci zuciyarka ta sosu sa'adda saƙo yazo mini daga majalisa. Lallai ina son ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi."
Yayin da Nazmir yaji wannan batu sai yace, "ya abbana ai dole ne zuciyata ta sosu domin ban ga dalilin da zai sa majalisa ta buƙace ka ba yanzu,alhalin ta wulaƙanta ka a lokacin da kake ganiyar sharafinka wace gwaninta zaka iya yi mata a halin yanzu da tsufa ya riske ka wacce ba ka yi kamarta ba abaya."
Halufa yayi ajiyar zuciya yace, "yakai ɗana haƙiƙa kayi tunani mai kyau nima kuma jikina ya bani cewa lallai akwai babbar buƙata da ta tasowa sarki wadda dole sai da taimakona zata biya shi yasa aka neme ni."
Huzaik yayi murmushi yace, "abba ni
kam ina ganin babu wata buƙata kawai ana so a yaudare ka ne a tura ka wani wurin inda zaka hallaka don a bayar da sarautar ga wani."
Halufa yayi murmushi yace, "a'a ina ganin ba haka bane koma dai mene ne nayi mku izini gobe da safe ku zo ku duka kuyi mini rakiya zuwa fadar domin ku gani kuma ku ji komai da kunnenku."
Da wannan furuci ne Nazmir da abokan sa suka yi sallama suka bar Halufa da Zuwaisa zaune su kaɗai a harabar gidan. Zuwaisa ta dubi Halufa tace, "ya kai miji na kayi sani cewa ni da kai duk tsufa ya
riskemu ga shi ɗan mu guda ɗaya ne kacal a duniya, saboda me za ka ja shi izuwa fada alhalin tun da yake bai taɓa zuwa fadar ba. Shin baka tsoron ya zama bawan azzalumin wanann sarki namu?"
Yayin da Halufa ya ji wannan batu na Zuwaisa sai hankalinsa ya dugunzuma ya yi shiru bai ce da ita komai ba, har tsawon lokaci. Daga bisani sai ya miƙe tsaye ya juya mata baya yana mai cewa. "Yake matata ki yi sani cewa ko mun so ko mun ƙi dole ne mai rabawa ta raba mu da ɗan mu domin tsufa da mutuwa aminnan juna ne. Zuwan Nazmir fada ɗaukaka ce a gareshi amma kuma wata sila ce da za ta iya zama sanadiyar rabuwarmu da shi ta har abada."
Koda Halufa ya zo nan a zancensa sai ya juya suka haɗa idanu da Zuwaisa kawai sai ya ga hawaye na zuba a idanunta. Nan da nan shi ma zuciyarsa ta karaya, idanunsa suka ciko da ƙwallah. Zuwaisa ta miƙe tsaye suka rungume juna, suna kuka tana mai cewa, "Haƙiƙa mafarkina ya zama gaske, ranar da nake tsoron ganin zuwanta ne ya yi."
Kashe gari fadar sarki Bashakur ta cika maƙil da jama'ar gari,domin tuni labari ya bazu cewa yau ne sarkin yaƙi jarumi Halufa zai dawo kan kujerarsa ta fada. Sarki Bashakur na zaune fadawa sun kewaye shi, yana mai tunƙaho da ƙarfin mulkinsa sai ga sadauki Halufa ya shigo, jarumi Nazmir tare da abokansa guda shida na take masa baya.
Koda ganinsu sai sarki Bashakur ya ƙarewa Nazmir kallo sama da ƙasa, ya ga irin halittar da Allah ya yi masa ta kyau da surar jarumta, sai ya cika da ɗumbin mamaki domin bai taɓa ganinsa ba sai yau kawai dai yana jin labarin bajintarsa ne amma bai taɓa sha'awar ya sa shi a idonsa ba saboda kishi da girman kai irin na sarakai.
Koda zuwan su Halufa sai suka risina a gaban sarki suka kwashi gaisuwa. Sarki Bashakur ya karɓi gaisuwar yana mai farin ciki da nuna walwala yace, ''An gaisheka sarkin yaƙi kuma muna murna da ka amsa kiranmu da gaggawa muna fatan ka karɓi abin da muka dawo maka da shi bayan ka rasa shi tsawon shekaru ashirin baya."
Cikin nutsuwa sadauki Halufa ya yi gyaran murya ya ce, "Ya sarkin sarakai haƙiƙa na yi farin ciki da wannan saƙo, to amma ina da uzuri guda,ina son sarki ya dube ni da kyau don ya gane cewa jiya ba yau ba ce. Haƙiƙa yanzu tsufa ya riskeni, ba zan iya yin abin da na yi ba a shekarun baya. Ina neman alfarma da a baiwa ɗana Nazmir wannan sarauta a maimakona domin ya cancanta,kuma na tabbatar da cewa zai iya yin abin da yafi wanda na yi."
Koda jin wannan batu sai sarki Bashakur ya tuntsire da dariya, sannan ya ce, "Ai shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama, domin dama akwai wani gagarumin aiki da ya taso don biyan wata muhimmiyar buƙata tawa. Ya yarda zan baiwa ɗanka sarautarka amma sai bayan ya je ya biya mini buƙata ya dawo cikin nasara. Yana dawowar zan sa a shirya bikin naɗa shi wannan matsayi na sarkin yaƙin ƙasata. Idan kuwa ya kasa samun nasara zan kashe shi tun da ban ga amfanin đan da ya kasa gadon mahaifinsa ba. "
Koda jin wannan batu sai jarumi Nazmir ya dube sarki Bashakur ido da ido ya ce, "Na amince da wannan tsari kuma ina mai rantsuwa da darajar mahaifina kowacce irin buƙata ce kake da ita zan biyata, domin na nuna cewa na cika ɗan halak, ɗan da ya sha jarumta a nonon mahaifiyarsa."
Koda jin haka sai fadar ta ruɗe da shewa ana yiwa jarumi Nazmir jinjina. Sarki Bashakur ya ɗaga hannu aka yi tsit. Sannan ya ce, "Nima na amince da hakan, shin akwai wanda zai ce wani abun?"
Huzaik ya risina ya ce, "Ya sarkin sarakai ina son na roƙi wata alfarma da yawun abokan Nazmir."
Sarki Bashakur ya yi murmushi ya ce, "Faɗi buƙatar ku na ji."
"Muna son inda za ka tura Nazmir tafiya biyan buƙatarka a yi mana izini mu yi masa rakiya."
Koda jn haka sai sarki ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "An yi muku izinin. Yanzu na sallame ku amma ku dawo nan fada gobe war haka cikin shirin barin ƙasarman don aiwatar da buƙatata."
Da wannan furuci ne aka sallami kowa fada ta watse. Kowa ya kama gabansa. Tun da su Nazmir suka dawo gida ya kasance cikin tsananin damuwa har ma ya rufe su Huzaik da faɗa yana mai cewa, "don me zai jefa kan su a cikin wannan masifa. Ya sani cewa aikin da za'a tura shi ba ƙaramin bala'i bane,duk da cewar bai san mene ne ba, duk za su iya hallaka."
Koda jin wannan batu sai Huzaik, Sharhil,Bagwan,Husuf,Iklam da Bardil suka haɗa hannyensu waje guda suka buɗe baki a lokaci guda suka ce,
"Mun kasance abokan juna tun ƙuruciya mun shaƙu da junanmu kuma bama rabuwa komai ruwa komai iska. Ya kai Nazmir gamu mu shida da kai ne cikon na bakwai shin kana tare da mu ko kuwa za ka ware daga cikin mu ne?"
Yayin da Namzir ya ji wannan jawabi daga bakin abokan sa sai zuciyarsa ta karaya idanunsu akan na su ya ce, "Ina tare da ku har abada,zumuncinmu da soyayyarmu ga juna ta ratsa jini da tsoka." Take suka rungume juna gaba ɗaya cikin kukan farin ciki.
A wannan rana su jarumi Nazmir suka gama kimtsa kayansu don yin tafiyar da ba su san inda zasu je ba.
Bayan sun tanadi dawakai da guzuri da kayan yaƙi, sai suka ɗunguma suka tafi gidan su Huzaik don yin sallama da mahaifinsa tsoho Marnush. Da shigarsu inda yake sai suka iske shi a zaune yana sharɓar kuka. Gaba ɗayansu sai hankalinsu ya tashi, suka durƙusa a gabansa, Huzaik ya kama hannayensa ya riƙe yana mai zubda hawaye ya ce, "Ya kai Abbana ina dalilin wannan kuka naka?"
Tsoho Marnush yace, "Ya kai ɗana ka yi sani cewa kai kaɗai nake da shi a duniya, ga shi har tsufa ya riskeni ban ga auren ka ba. Yau dare ɗaya labari ya zo mini cewa za ku yi tafiya mai haɗari.
Idan rayuwarka ta salwanta shi kenan, ba ni da kowa a duniya, in da za ka haƙura da wannan tafiya da hankalina yafi kwanciya."
Huzaik ya kasa jurewa zuciyarsa bai san sa'adda ya fashe da kuka ba, yana mai cewa, "Ka yi haƙuri Abbana na rigaya na yiwa abokaina alƙawarin wannan tafiya. Babu abin da zai hanani yinta face mutuwa. Ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa lallai zamu dawo gida lafiya,kuma zan zo maka da kyakkyawar sirika."
Koda jin wannan batu sai tsoho Marnush ya rungume Huzaik a ƙirjinsa ya ƙara fashewa da kuka yana mai cewa, "Ina fatan abin da ka faɗa ya kasance."
Bayan Huzaik ya gama ganawa da mahaifinsa sai kuma suka ɗunguma suka tafi, gidan su Sharhil. Da zuwa suka iske mahaifiyara Ushaiya wacce ta kasance makauniya mai kimanin shekaru sittin da shida. Suna shiga suka risketa ita ma tana kuka. Cikin hanzari Sharhil ya matsa daf da ita ba tare da sanin sun shigo ba.
Koda ya durƙusa a gabanta ya taɓa gwiwarta sai tace, "Wane ne?" Maimakon ya bata amsa sai shima ya fashe da kuka,cikin sauri ta shafa fuskarsa da tafin hannunta ta ce, "Au ɗana ne,yaushe ka shigo ban sani ba?"
Sharhil ya ɗago kai ya dubeta, idanunsa cike da hawaye ya ce, "Yake Ummina haƙiƙa na san kina kuka ne saboda samun labarin tafiyar da zan yi."
Ushaiya ta share hawayenta ta ce, "Ƙwarai kuwa ai dole ne na yi kuka, ka tuna cewa tun dana haifeka ban taɓa ganin kamanninka ba, kuma taɓa rabuwa da kai ba tsawon kwana guda ba. Kai kaɗai gare ni a garin nan ga shì na kasance makauniya, tun sa'adda ka zama mutum ka ɗauke wahalar cina da shana, kuma ka kula da lafiyata.
Yanzu idan baka nan waye zai samo mini abincin da zanci, ka sani cewa a yadda girma ya kamani ba zan iya yiwa kaina komai ba,kai ne gatana, in na rasaka na rasa komai, babu wanda zai iya taimako na in babu kai face abokanka to kuma ga shi na ji ance gaba ɗaya za ku yi wannan tafiya."
Sa'adda Ushaiya tazo nan a zancen ta sai gaba ɗaya jikin su Nazmir ya yi sanyi, suka kamu da tausayinta. Sharhil ya ce, "Yake Ummina ina mai ƙarfafa miki ƙwarin gwiwa da ki kwantar da hankalinki ki, sani cewa ni da abokaina mun kasance jaruman gaske,don haka kowacce irin masifa da zamu shiga zamu dawo gida lafiya."
Ushaiya ta rungume Sharhil sannan ta fashe da kuka tana mai cewa, "Na san kuna da jarumta amma ai ba ku san in da za ku je ba, da kuma abinda za ku tunkara." Haka dai su Sharhil suka yi ta lallashin Ushaiya har suka shawo kanta ta daina kuka,daga nan kuma suka tafi gidan su Bagwan.
A cikin waɗannan abokai guda bakwai waɗanda suka taso tare kai ɗaya Bagwan ne kaɗai ya yi aure, koda yake ya yi aure da wuri sakamakon ya taso a matsayin maraya, domin tun bai fi shekara bakwai ba iyayensa suka yi haɗarin jirgin ruwa, suka rasu. Bagwan ya sha wahalar rayuwa domin tun yana ƙarami ya ke sana'ar dako, leburanci da sauransu don kawai ya riƙe kansa. Lokacin da ƙarfi ya zo masa sai ya yanke shawarar ya yi aure da wuri don ya sami zuri'a ya huce takaicin rashin dangi.
Cikin dacewa ya gamu da wata budurwa mai suna Muslaiya wacce lokaci guda suka kamu da matuƙar
ƙaunar juna.
Muslaiya baiwa ce ta wani attajiri, wanda tsufa ya riske shi ainun amma yana da tarin iyali.
Lokacin da attaiirin ya fahimci cewar Muslaiy na soyayya da Bagwan sai ya 'yanta ta ya yarje mata ta taje tayi aurenta kuma ya taimaketa lokacin aure.
Bagwan suka zauna cikin kwanciyar hankali har tsawon shekaru biyu. A halin yanzu Muslaiya na dạ tsohon ciki wata takwas don haka kusan ko yaushe Bagwan na tare da ita, yana taimaka mata wajen aikace-aikacen gida.

2 Comments On MATSATSUBI Book 1
avatar
armiyau

1 year ago

Reply

For fun

avatar
muhammad-musa-2

11 months ago

Reply

Akwai matstsubi

Please Login or Register in order to submit comment