Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da idanuna,ina mai fatan zaka riƙe ƙanwata Lamiz amana kuma ina son....." Koda Husuf ya zo nan a zancensa sai jikinsa ya sandare, idanuwansa suka ƙafe suka daina motsi. Nan take jarumi Nazmir ya kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba ɗaya yayi ta amsa kuwwa har su Bardil suka jiyo ihun daga inda suke. Koda jin ihun sai Bagwan da dakaru biyar suka biyo sawu suka bar Bardil tare da gimbiya Luzaiya da sauran baraden nan a wajen.
Koda zuwan su Bagwan inda jarumi Nazmir yake sai suka iskeshi zaune a gaban gawar Husuf yana ta rusa kuka. Shima Bagwan sai ya fashe da kukan,anan dai akayi ta rarrashinsu da ƙyar suka bari aka haƙawa Husuf kabari aka binne shi. Bayan an binne shine, jarumi Nazmir ya fiddo mayafinnan na Lamiz ƙanwar Husuf daga cikin kayansa,koda ya dubi mayafin ya tuno da sa'adda Lamiz ta danƙa masa kuma ya tuno da irin kalaman da tayi musu a wannan rana sai ya sake fashewa da kuka, cikin ƙarfin hali jarumi Nazmir ya ɗaura mayafin akansa sannan ya kama dokinsa ya hau,Bagwan ne da sauran barade suka hau nasu dawakan suka nufi inda suka baro su gimbiya Luzaiya.
Tun daga nesa Bardil ya hango mayafin Lamiz akan jarumi Nazmir kawai sai ya fashe da kuka don ya tabbatar da cewa abokinsa Husuf ya mutu.
Yayin da su Nazmir suka iso sai Bardil ya dubi Bagwan ya ce "Ina kuma labarin Iklam." Cikin alamun karayar zuciya Bagwan yace, "Kafin Husuf ya rasu ya gayawa Nazmir cewar yaga gawar Iklam a filin yaƙi." Koda jin haka sai Bagwan ya kurma ihu irin wanda jarumi Nazmir yayi ɗazu sannan ya rugo gaban Nazmir da Bardil ya rungumesu,yana mai cewa shike nan saura mu uku kacal. Dukkaninsu suka cigaba da kuka,duk wanda ya dubesu a wannan lokaci dole ne tausayisu ya kamashi.
Kowa da abin da ya dameshi, kamar yadda su jarumi Nazmir ke kuka da baƙin cikin rasuwar abokansu haka gimbiya Luzaiya ta kasance cikin tsananin baƙin ciki rasuwar mahaifinta.
A duk sa'adda ta ɗaga kai ta dubi Bardil sai taji ta tsaneshi bama shi ba har su jarumi Nazmir ɗin duk ta tsanesu inda tana da iko da tuni ta hallakasu gaba ɗaya sannan ta kashe kanta ta huta da takaicin duniya.

Anan zamu dakata, sai wani lokacin idan Allah ya kaimu.
Fatan alheri
Contact 08167757245

Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part N

A baya mun tsaya a inda:-
A duk sa'adda ta ɗaga kai ta dubi Bardil sai taji ta tsaneshi bama shi ba har su jarumi Nazmir ɗin duk ta tsanesu inda tana da iko da tuni ta hallakasu gaba ɗaya sannan ta kashe kanta ta huta da takaicin duniya.

####
Haka dai suka ci gaba da tafiya,su kwana nan su tashi can. Gimbiya Luzaiya da su jarumi Nazmir basu daina kukan baƙin ciki ba har sai bayan kwana bakwai,domin duk sa'adda suka tuno da masoyan nasu sai dai kawai ai sun fashe da kuka.
Tsawon kwanakin gimbiya Luzaiya bata yi magana da kowa ba kuma bata ci komai ba face ruwa sai kuma ƙwayar dabino guda uku kullum. Nan da nan ta fita haiyacinta ta rame sosai.
A yammacin kwana na bakwaine sa'adda suka ya da zango a ƙarƙashin wani dogon tsauni.
Luzaiya ta zauna ita kaɗai a gefe guda tana rawar đari, ashe zazzaɓine ya rufeta. Koda ganin halin da ta shiga sai tausayinta ya kama jarumi Nazmir,da yake sun gasa naman wata barewa a jiya da daddare kuma akwai sauran naman acikin jakarsu sai ya fiddo dashi yaje ga Luzaiya ya miƙa mata yana mai cewa yake wannan 'yar sarki ya kamata ki rungumi ƙaddara haka ki fara cin abinci mana."
Kamar za taci kawai sai tayi wurgi dashi izuwa cikin wata ƙorama wadda ruwanta ke gudu bisa duwatsu cikin ɗacin rai da kakkausar murya ta dakawa jarumi Nazmir tsawa tace, "Ina ruwanka da lafiyata ka ƙyaleni na mutu mana,daku da mutanenka duk na tsane ku kamar yadda na tsani rayuwata a yanzu. Tsakanina daku sai gaba har abadan abidina kune kuka dakusar min da farin cikin rayuwa kun kashe mahaifina kun rabani da ƙasata da kuma mulkina kun rabani mahaifiyata da duk dangina,mene ne ya rage agareni." Ko da ta zo nan a zancenta sai ta fashe da kuka har tsawon 'yan daƙiƙu sannan ta cigaba da cewa, "Yanzu ku shi kenan buƙatarku ta biya kun rabani da kowa nawa ku kuma za ku koma ga iyayenku da 'yan uwanku ku ci gaba da rayuwar duniya cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Kun cuceni kun gama dani. Na roƙeku da ku kasheni
yanzu ku jefa gawata cikin kwazazzabon nan."
Haka dai ta ci gaba da surutai tana kuka amma ko ci kanki babu wanda ya faɗa mata.
Haƙiƙa maganganun Gimbiya Luzaiya sun ratsa jarumi Nazmir kuma ya ƙara kamuwa da tausayinta amma sai ya dake ya ƙi nuna tausayin a fili ya yi ta maza. Tun sa'adda ta fara surutan ya koma can gefe guda ya zauna yana kallonta har ta gaji ta yi shiru.
A lokacin ne tunanin iyaye ya faɗowa
jarumi Nazmir kuma ya tuno da abokanansu guda huɗu waɗanda suka mutu duk a sanadiyyar wannan mugun yaƙi wanda sarki Bashakur ya turosu. Kawai sai hawaye ya zubo masa. Sa'adda Bagwan da Bardil suka ga hawaye na zuba a idanun jarumi Nazmir sai suka taho gareshi suka zauna tare da shi. Bardil ya dubeshi yace, "Ya kai abokina yanzu saboda tausayin Gimbiya ne ka ke zubar da hawaye?"
Nazmir yayi murmushi yace, "Ba don haka ba ne. Na tuno da irin halin da muka baro iyayenmu ne kuma na tuno da abokanmu waɗanda suka rasu na tahbatar da cewa har abada ba zamu sake samun masoya kamar su ba. Kuma ba zamu samu masu đebe mana kewa irin su ba."
Bagwan ya numtasa yace, "Lallai kam ba zaku iya samun abokan shaƙuwa ba kamarsu amma babu mamaki nan gaba ku haɗu da masoya waɗanda zasu ɗebe muku kewa su cire muku baƙin cikin rashinsu kuma ku ƙarasa sauran rayuwar ku ta duniya tare dasu." Koda jin wannan batu sai Jarumi Nazmir yace, "Nifa bangane manufarku ba." Bagwan yace, "Ina nufin zaku iya haɗuwa da 'yan matan da zaku aura kuma kuyi gagarumar soyayya dasu iyakar ƙarshen rayuwarku." Koda faɗin haka sai Nazmir da Bardil suka bushe da dariya sannan Nazmir yace, "Ni tunda nake ban taɓa jin ina son wata ya mace ba a zuciyata kuma bana zaton zan iya soyayya nan gaba a rayuwata." Bagwan yayi murmushi yace, "Haba abokina ai bakasan meye so ba shi yasa ka faɗi haka kaga ni nayi soyayya kuma ina kan yinta harma naci ribarta tunda nayi aure. Tabbas yanzu ina sa ran cewa idan mu koma gida zan iske ɗana ko 'yata tunda na baro matata Muslaiya da tsohon ciki,tabbas yanzu ko mutuwa nayi,za ana tunawa dani ina so kusani cewa babu abinda yafi soyayya daɗi a duniyar nan domin idan kana da masoyi duk irin baƙin cikın daka shiga kana ganinsa sai zuciyarka tayı sanyi ka manta da komai yanzu idan muka isa gida kuka sadu da iyayenku wane irin daɗi zakuji a ranku? To ina tabbatar muku da cewa wannan daɗin da zakuji bai kai kaso ɗaya ba daga cikin đari na irin daɗin da mai masoyiya yake ji yayin da ya sadu da ita bayan doguwar rabuwa. Ni kam yanzu ji nake kamar na zama tsuntsu nakai kaina gida dan na sadu da matata Muslaiya." Sa'adda bagwan yazo nan a zancensa sai duk jikin su jarumi Nazmir yayi sanyi suka kasa cewa komai domin maganganun na sa sun ratsasu kuma sun gamsu cewar gaskiya ne.
Haka dai tafiya taci gaba da wakana suka cigaba da ratsa dazuzzuka gari da ƙasa ƙasa har tsawon wata uku,wata rana hanya tabi dasu ta saman wani dogon tsauni wanda ƙarƙashinsa na da nisan gaske kuma ruwane ke kwarara a kan tsaunin yana zuwa ƙasansa inda wasu manyan duwatsu suke da magudanar ruwa. Bìsa dole suka sauka daga kan dawakansu suka fara tafiya a hankali sai da suka zo kan tsakiyar tsaunin kawai sai gimbiya Luzaiya ta faki numfashin su ta daka tsalle ta faɗa ƙarƙashin tsaunin nan ba tare da yin wata shawara ba jarumi Nazmir ya kwaɓe rigarsa da sauri shi ma ya daka uban tsalle yabi bayanta. Al'amarin da ya firgita su Bagwan kenan, suka leƙo ƙasan tsaunin cikin ɗimauta da baƙin ciki don sun tabbatar da cewa Nazmir da gimbiya sun halaka kenan.
Kafin Luzaiya da jarumi Nazmir su faɗo ƙasan tsaunin nan sai da suka yi tafiyar daƙiƙa dubu biyu a sama, tuni a lokacin ƙarfin iska ya sa Luzaiya ta suma,shi kuwa Nazmir bai suma ba sai da ya isa ƙarshen ramin, kafaɗarsa ta fado kan wani dutse.
Cikin sa'a Luzaiya ta faɗo akan ruwa. Gaba ɗayansu su biyun ruwa ya jasu ya tafi da su izuwa gaɓar kogi ya watsar da su.
Bayan kamar rabin sa'a sai gimbiya Luzaiya ta farfaɗo. Tana buɗe idanunta ta miƙe zumbur a firgice. Ta hau kalle-kallen daji tana mamakin yadda aką, yi ta rayu. Ba zato sai ta ga jarumi Nazmir
kwance a kusa da ƙafarta. Ta dube shi cikin mamaki tace a ranta, ya akai wannan ya zo nan alhalin ni kaɗai na faɗo ƙarƙashin tsaunin nan. Na tabbata ba zai jeho kansa ba tunda yana son rayuwarsa. Koda taga wata ƙaramar wuƙa a jikin Nazmir sai ta cirota ta tsaya tana kallonta tana mai yin shawara da zuciyarta tana mai cewa, "Tun da dai na jeho kaina cikin rami ban mutu ba, ai sai na kashe kaina da wuƙar nan dan na huta da takaicin duniya."
Tana gama faɗin haka sai ta zare wuƙar daga cikin kufenta ta daga sama ta saita cikinta zata burma. Caraf ta ji an riƙe hannunta. Cikin sauri ta waiga suka yi arba da juna. Ba wani ba ne ya riƙe hannunta face jarumi Nazmir. Cikin tsananin fushi tace, "Don me ka damu da rayuwata ka ƙyaleni na mutu mana."
Nazmir yace, "rayuwarki ita ce rayuwata da ta abokaina da suka rage. Idan ban kai ki ba ga sarkinmu a raye ba muma kashe mu za'a yi."
Yana gama faɗin hakan ya sunkuceta sama ya đora a kafaɗarsa ya shiga laluben hanyar đa zai bi ya koma inda abokan tafiyarsa suke."

*************************************

Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa kawai sai aka ga wata ƙatuwar damisa ta shigo cikin fadar a guje kuma a haukace, kawai sai ta daka tsalle da nufin ta dirga kan sarki Dujalu. Cikin tsananin zafin nama tsoho Rafkanagu ya shaƙo wuyanta da hannu đaya ya fyaɗata da ƙasa. Ko shurawa ba ta yi ba,ta zama gawa.
Al'amarin da yayi matuƙar jefa sarkí cíkin tsananin mamaki kenan,domin ba su taɓa ganin tsoho mai ƙarfi irin na wannan ba. Sarki Dujalu ya tambayi kansa cikin zuciya, ''An ya kuwa wannan tsohon mutum mutum ne?"
Wani bafade ya je kan damisar ya duddubata sannan ya dubi sarki Dujalu yace, ''Ranka ya daɗe ai wannan damisar kace wacce ake kiwo anan gidan. Lallai duk yadda aka yi jiya mai bata abinci ya mance bai kulle ƙofar kejinta ba."
Koda jin haka sai sarki Dujalu ya fusata yace, maza aje a kamo mai bata abincin,a tsire shi tunda har ya yi sakaci haka ya janyo tashin hankalin sarki,kuma ya zamo sanadin katse wannan labarí mai daɗi na hikayar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya. Bazan cigaba da baku labarin ba sai bayan an ƙaddamar da mai kula da damisar nan.
Wannan shi ne abin da ya faru a fadar sarki Dujalu na birnin Misra sa'adda su Ruziyal ke aikin rubuta sabon KUNDIN TSATSUBA na biyu.
*****************************************
Al'amarin su Jafar kuwa bayan Mazalish ta gama kalle-kallenta suka faɗo duniyar su Jafar sai hankalinta ya koma kan KUNDIN TSATSUBA, wanda ke buɗe a gabansu ta ƙare masa kallo tsaf a cikin nutsuwa. Sannan ta dubi Jafar,Yelisa,Mashrila da Gulzum tace, "Yanzu a cikinku nan babu wanda zaí iya tsayar da littafin nan daga ci gaba da buɗe kansa don na tafi neman masoyina jarumi Hubairu."
Koda jin wannan batsu sai Yelisa ta yi tsaki tace, "Wannan kuma wace irin maganar banza kike yì, inda muna da wannan ikon ai da tuni muma mun yì ko dan mu huta da tsananin azabar da muke sha a cikinsa."
Jafar ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba yayata ai kawai ki rungumi ƙaddara kawai domin kin sayi wahala da kuɗinki tun da kika yi gangacin biyo mu. Da dai kin yì zamanki a can duniyarku ta mayu da ya fiye miki kwanciyar hankali."
Gama faɗin haka ke da wuya sai shafin KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha uku inda suka yi arba da hoton wani surƙuƙin daji a samansa an yi rubutu kamar haka:
"WANNAN JEJI, JEJI NE NA ABUBUWAN MASIFA IRI-IRI. AN ƘIRƘIRESHI NE KIMANIN SHEKARU DUBU BAYA."
MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO."
Wata siririyar murya ce ta karanta wannan jawabi. Muryar na đaukewa iskar cikin kundin zuƙe su Jafar suka zama 'yan mini-mini suka faɗa ciki. Kawai sai suka tsinci kansu a tsakiyar wannan jeji irin wanda ba su taɓa gani ba a rayuwarsu,domin komai na cikin sa ya kasance babba mai girman gaske. Ma'ana bishiyoyi, duwatsu da tsirai. Manya-manya ne, girmansu ya wuce ƙima domin bishiya ɗaya sai kaga girman ta ya ninka irin ta duniyar su Jafar sau arba'in. Kuma kowacce bishiya siffar fuskar mutuntaka wato tana da ido,baki da hanci har da ma kunnuwa,kuma suna motsi wato suna harkokinsu kamar yadda sauran halittu masu rai da jiki keyi, saidai ka ga bishiya na tafiya da ƙafafunta ko kuma ka ga tana aiyuka iri-iri. A cikinsu kuma akwai manya da ƙanana.
Ba zato ba tsammani sai gaba ɗayan bishiyoyin dake wajen suka yi wa su Jafar ƙawanya ya zamana babu wata hanya da za su iya bi su tsere.
Mafi girma daga cikin bishiyoyin ta buɗi baki tace, "Yaku waɗannan mutane mene ne ya kawo ku duniyarmu? Shin kun zo neman wani abu ne ko kuwa kun zo leƙen asiri ne?"
Cikin firgici su Jafar suka ƙurawa bishiyar idanu aka rasa wanda zai bada amsar tambayar har sai da bishiyar ta daka musu tsawa gami da maimaita tambayar. Jafar ya ɗaga kansa sama ya dubi wannan ƙatuwar bishiya mai kama da tsauni a gabansa yace, "Yake wannan bishiya ki yi sani cewa ba mu kawo kanmu nan ba kawo mu aka yi, kuma bamu da nufin komai a kanku kuma ba mu zo neman komai anan ba,muna neman alfarma idan har zaku iya mayar damu in da muka fito to ku taimakamana."
Koda jin wannan batu sai babbar bishiyar ta tuntsire da mahaukaciyar dariya mai kama da tsawa.
Nan take sauran 'yan uwanta bishiyoyin suma suka tayata dariyar. Al'amarin da ya hargitsa jejin gaba ɗaya kenan,ya kama girgiza kamar ƙasa zata daddare. Wata irin ƙara mara daɗin ji ta cika kunnuwansu Jafar bisa dole suka toşhe kunnuwansu suka farfaɗi ƙasa.
Lokaci guda bishiyoyin suka daina dariyar,komai ya tsaya cak. Babbar bishiya tace, "Yaku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa mun san duk irin makircinku da wayonku lallai ba ku isa ku yaudare mu ba, domin a shekarun baya ire-iren ku sun zo mana don leƙen asiri da nemạn wasu abubuwa don bunƙasa harkokin ƙere-ƙerensu na zamani wanda da sune suke yi mana ɓarna. Bisa wannan dalili yanzu zamu tafi da ku izuwa fadar sarkinmu don a bincike ku,a gane ko kuna ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane. Kafin wani daga cikin su Jąfar ya ce wani abu tuni wasu bishiyoyi guda biyar sun jeho rassansu sun kanannaɗesu kamar yadda ake naɗe tabarmå,kuma kowacce bishiya mutum đaya ta ɗauka. Kawai sai suka ga bishiyoyin sun tashi da su sama kamar ɓacewar taurari,sannan aka bayyana da su a wani jejin dabam wanda babu komai a cikinsa face jerin bishiyoyi irin waɗannan masu tsananin yawan gaske. Ko'inà ka duba sune iya hange ba adadi.
A can gefe guda bisa kan wani ƙaton tsauni wata jibgegiyar bishiya ce wadda duk ta kere sauran a girmą. Nan take gaba ɗayan bishiyoyin suka yi mata sujjada alamar gaisuwa. Jibgegiyar bishiyar ta buɗe baki tace, "An gaisheku mutanenn birnin tsirrai."
Daga nan sai aka gurfanar da su Jafar a gaban bishiyar. Ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauko su tace, "Ya sarkin sarakai ɗazu ne muka kama waɗannan bil'adaman a cikin gonarka ta bayan gari,muna zargin suma sun zo ne leƙen asiri, ko neman ma'adanai babu mamaki ma suna daga cikin al'ummar Sukardas."
Koda jin haka sai sarauniyar bishiyoyi ta dubi su Jafar ta ƙare musu kallo cikin nutsuwa,sannan ta buɗe baki cikin wata irin siririyar murya mai taushi tamkar ta ƙaramar yarinya 'yar shckara huɗu,tace, "Ammą dai fadawannan nawa kun cika shashashai. Shin makafi ne ku ba ku yi nazarin waɗannan mutanen bą sosai? Ai ko kaɗan ba su yi kama da irin waɗancan masu zuwa leƙen asiri ba,ko ncman ma'adanai haką kuma ba su yi kama da irin al'ummar Sukardas ba."
Sarauniyar ta dubi su Jafar tace, "Yakų waɗannan baƙi ina son ku saki jikinku damu lallai ba zamu cutar da ku ba, kuma ku matso nan kusa dą ni."
Nan take su Jafar suka ƙarasa gaban sarauniyar bishiyoyi suka zazzauna. Sarauniya ta sa aka-kawo musu ruwan sha da 'ya'yan itatuwa masu zaƙi da daɗin ɗanɗano,irin wanda ba su taɓa ci ba,suka kimtsa cikinsu. Bayan sun nutsu ne sarauniyar ta sake dubansu tace, "To ina son yanzu ku bani labarinku da yadda kuka zo nan."
Ba tare da wata gardama ba Jafar ya kwashe labarinsu tun daga lokacin da suka ɗauko KUNDIN TSATSUBA a rijiyar gidan Riziyal shi da Yelisa kawo i yanzu ya zaiyane shi. Koda ya gama bada labarin sai sarauniyar ta hau yi musu tafi suma sauran bishiyoyin sai suka yi koyi da ita. Daga can kuma sai suka daina tafin tace, "Yakai Jafar haƙiƙa kai da abokan tafiyarka kun cancanci yabo da jinjina domin kun yi matuƙar ƙoƙari wajen kare kan ku abisa wahalar da kuke sha a cikin KUNDIN TSATSUBA,kuma kun cika jarumai. Muma yanzu zamu sanar daku masifar da ke addabarmu a garin nan,kuma muna fatan zaku taimaka mana mu kawo ƙarshenta,domin idan ma ba ku taimaka mana ba in ta zo sai ta haɗa da ku. Mun sani cewa ku bil'adama kuna da basira da hikima fiye da kowacce irin halitta shi yasa muke son ku taimaka mana,ku yi sani cewa a bayan kowanne kwana goma akwai wasu irin mutane masu kawuna irin na batoyi da kuma fufafukai irin na jemagu suna zuwa mana su yi ta feso mana wuta daga sama suna ƙonemu.
Sai sun yi mana ɓarna mai yawa sannan suke tafiya. Babu irin hikimar da ba mu yi ba,don mu harbosu ko mu kama su amma abu ya faskara domin komai ƙarfin makami baya iya huda jikinsu.
Haka kuma jikin na su na da matuƙar santsi baya ruƙuwa."
Koda jin wannan batu sai Mashrila tace, "Ai wannan matsalar taku mai sauƙi ce ni na san hanyar da za'a bi a iya kama waɗannan halittu."

Topah,wace dabara uwar hikima Mashrila zata kawo,mu haɗu a babi na gaba don jin yadda zata kaya.
Ahmad Munir ke muku sallama.
Fatan alheri.
Contact:- 08167757245Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part O

A baya mun tsaya ne inda:-
Koda jin wannan batu sai Mashrila tace, "Ai wannan matsalar taku mai sauƙi ce ni na san hanyar da za'a bi a iya kama waɗannan halittu."

###
Cikin zumuɗi sarauniyar bishiyoyi tace, "Yarinya maza ki sanar da mu wannan hanya domin yau saura kwana uku waɗannan halittu su zo."
Mashrila tace, "Kada ku damu yanzu dai ku barmu mu huta tukunna domin mun sha wahala mai yawa a duniyar su Mazalish. Nan da wani lokaci kaɗan zan sanar da ku hikimar da ke raina."
Sai da su Jafar suka yi baccin sa'a bakwai sannan suka farka. Farkawarsu ke da wuya aka sake kawo musu nau'in ya'yan itatuwan suka ci suka ƙoshi. Sannan Mashrila tace aje a samo mata ɗanyar jijiyar bishiya mai tarin yawa. Nan take wata ƙatuwar bishiya ta bugi ƙirji tace, ita ta yarda a yanki tata jijiyar. Kawai sai ta fiddo da jijiyoyinta aka yi ta tsinka sai da aka tara mai yawa, a sannnan ne bishiyar ta faɗi ƙasa summmiya sai da aka yayyafa mata ruwa ta farfaɗo.
Mashrila tace, "Waye gwanin iya saƙa a cikinku?" Wata mitsitsiyar tace itace. Mashrila tace mata, "ina so ki ɗauki jijiyar nan ki saka mini raga mai ƙananan ƙofofi kuma mai girman gaske, kuma ki yi mata mariƙai guda huɗu a ƙarshen bakunanta. A ƙallah ina son ki
yi ragar guda dubu."
Mitsitsiyar bishiya tace, "An gama" Nan take ta zauna ta fara aiki. Ai kuwa a cikin rabin sa'a ta kammnala abin da aka umarce ta,koda ta gama sai Mashrila ta dubi sarauniyar bishiyoyi tace, "To kin ga waɗannan abubuwan da su zamu yi amfani muna lulluɓe waɗannan halittu muna ɗaure su a jikin duwatsu. Ko sun fesawa wannan raga wuta ba za ta ƙone ba,saboda danshin ruwan da ke jikinta."
Koda jin haka sai mamaki ya kama kowa a wajen. Sauraniyar bishiyoyi tace, "Haƙiƙa wannan yarinyar kin cika mai basira, tabbas wannan hikima ta ki za ta yi aiki sosai."
Kwana uku na cika sai ga waɗannan halittu masu kan batoyi da fukafukan jemagu,sun iso sai shawagi suke a sararin samaniya. Suna feso wuta tana ƙone bishiyoyi. Nan da nan jejin ya hargitse gaba ɗaya bishiyoyin sukai ta guje-guje da iface-iface. Idan mutum na wajen ya ga yadda rayukan bishiyoyin ke salwanta dole ne ya tausaya.
A wannan lokaci su Jafar tare da wasu manyan bishiyoyi sun ɓuya a cikin wani kogon dutse ɗauke da waɗannan raga-raga guda dubu. Sai da suka barí halíttun nan sun fara saukowa ƙasa-ƙasa,sannan suka yi fitar burgu suna lullube su da ragar,sannan su ɗaure su a jikin duwatsu, cikin zafin nama da sauri.
Kafin a jima an kama halittun sama da guda ɗari tara. Sauran kuwa duk saí suka tsere. Waɗanda aka kama ɗin sai suka kasa ceton kansų daga cikin ragar suka yi ta ruri suna fesa wuta,amma a banza don ba su sami damar kuɓuta ba. Koda ganin abin da ya faru sai gaba ɗayan bishiyoyin garin suka rugo suka hau tsalle-tsalle da waƙe-waƙe don murna. Sarauniyar bishiyoyi ta zo gaban Mashrila ta tsaya tace, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan halittun da muka kama?"
Mashrila ta ce, "Haka za ku bar su su yi ta zama a cikin ragar nan har yunwa da ƙishirwa su kashe su."
Nan fa bishiyoyi suka yi ta godiya ga
Mashrila da abokan tafiyarta,bayan an nutsu sai Jafar ya dubi sarąuniya yace, "Yanzu ya za'a yi mu fita daga wannan garin naku,mu shiga wani?"
Koda jin wannan tambaya sai sarauniyar bishiyoyi ta dubi wata basamudiyar bishiya tace, "yake Kalbaladu na uwarce ki da ki fitar da su daga birnina."
Tana gąmą faɗin hakan saita zuro rassanta ta suri Jafar,Yelisa,Mashrila,
Mazalish da Gulzum ta yi sama dąsu sannan ta wangame bakinta ta jefa su a ciki. Kawai sai su Jąfar suka ga an watso su cikin duniyar su ta KUNDIN TSATSUBA. Har yanzu shạfi na goma sha uku ne a buɗe. Gaba đayansų suka dubi juna kamar waɗanda suka farka daga mafarki. Jafan ya ce, "Kai amma fa wannan shafin na goma sha uku ya zo mana ɖa alheri domin ba mu sha wata wahala mai yawa a cikinsa ba."
Yelisa tace, "Ƙwarai kuwa ai sai ka buđe mana shafin gaba babu mamaki mun fita kenan daga cikin wahala."
Caraf Mashrila ta tari numfashinta, tace, "Waye ya gaya miki cewar mun fita daga wahala?
Ina tabbatar muku da cewa yanzu ne ma zamu fara shiga wahala duk wadda aka sha a baya sharar fage ce."
Gulzum yace, "Kun ga ba hira zamu tsaya yi ba aikin shekara goma sha tara da wata shida ne a gabanmu,ku yi sauri ku buđe mana shafin gaba ko mun ragewa kanmu tsawon lokaci."
Cikin yanayin mamaki Jafar ya dubi Gulzum yace, "Ya akai ka san cewa sai mun shafe wannan lokacin muna karanta KUNDIN TSATSUBA?"
Gulzum yace, "Kai dai na ga alama daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa gareka. Yanzu ashe har ka manta cewa an gaya mana shekaru ashirin za mu yi muna karanta littafin kuma duka-duka yanzu a cikin wata na huɗu muke?"
Kafin Jafar ya ƙara cewa wani abu sai Yelisa ta yunƙura ta buɗo shafi na goma sha huɗu inda suka yi arba da hoton wani kogon dutse. A samansa
an yi rubutu kamar haka.
"WANNAN KOGO,KOGO NE NA MASIFA DA BALA'I IRI IRI.
AN ƘIRƘIRESHI FIYE DA SHEKARU DUBU GOMA BAYA. MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO."
Koda Yelisa ta

2 Comments On MATSATSUBI Book 1
avatar
armiyau

1 year ago

Reply

For fun

avatar
muhammad-musa-2

11 months ago

Reply

Akwai matstsubi

Please Login or Register in order to submit comment