Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune ita kadai ta dawo da wuri dan lecture daya kawai suka yi ta gama sakwara se nishi take dan daka dan ma maigidan yace shi yake so yau da bazata yi ba bata son dakan sakwara tayi miyar agushi taji nama da kaza zako zako a ciki da busasshen kifi yaji kayan hadi da gyada a ciki ta jera tebur kawai jiran dawowarsa take tadan kishingida taji tsayuwar motoci kusan guda biyu ta ce aa yau da bako yazo min?
Ta cigaba da zama seda aka buga kararawa tukuna ta mike cike da zumudi ta duba ta dan ramin kofar taga hamma mubarak da hamma ni'imatullahi a tsayi da sauri ta bude tayi wani ihun dadi
Sannu da zuwa hamma sannu da zuwa
Kafin yace oh ke kam kin fiya ihu ba cewa mu shigo ciki?
To mu shiga hamma ya hanya?
Suna shiga wata motar ta kuma tsayawa
Yau ksm kace gidan nawa ya yi albarka su waye kuma?
Da dada,da mijinki,da hajiya,da aunty maryama,da baffa idi da baffa...bari bari fada hamma nasan housefull kuka zo min ki tsaya mana kiji da wa kuma
Aa i cant gwara na karasa na gan su da ido na dada fa kace ka barni naje na yi tsalle kanta
Yana dariya ta fita daga falon tayi waje da gudu wani tsalle ta daka kan dada tana ihu sannun ki dada kingan ki yau a gidan aisha humaira naji dadin ganin ki
Humaira ki na nutsuwa mana
Hararsa tayi cikin wasa
Ya maida mata
Baffa idi ya mata dakuwa
Tayi kasa da kai taja dada zuwa cikim gidan bakin ta yaki ruhuwa dan murnar dadin ganin dada

Aisha kina da bako fa a waje baki kula ba?
Bako kuma,waye?
Wani bawan Allah ne
To bara naje na ga
Aa zauna masdook shigo dashi
Ai tunda suka shigo tare da hamma masdook ta saki baki galala tana kallon sa cike da mamaki da al'ajabi ta kalli wannan ta kalli wancan
Ma..
Dada Abbana ne?
Uhm shi ne aisha abban kine ahmad ne yazo ganin diyarsa
Hawayen da suka taron mata a fuska suka karasa zubowa se kuma ta mike ta karasa kusa da shi tana hawaye
Ashe zan ga abbana?
Ashe zan gan shi a duniya na furta wannan kalmar ta abba?
Ya Allah !Allah nagode maka Allah nagode maka kaine abun godiya kai ne me yadda kaso a san da kaso a lokacin da ka so dada,hamma,yau ga Abban *aisha humaira*ina kallon sa yana kallona wanda zan kalla nace Abbana
Ta rike hannyensa ta dora goshin ta a kam su tana hawaye
Abba ka dade baka zo ba
Ka nisanta ni da kiran ka da suna abba
Abba ni me nawa a sabanin ka da ummina da dada ?
Da har ta shafe ni ban samu arzikin cin yarinta da ku ba bayan ina da dangin uba
Abba *ba a min adalci ba* a *rayuwa ta* da ka hane ni da sanin *waye kai a gareni*
Abba soyayyar uba nada muhimmanci a rayuwar ko wanne dan 'adam bayan ta uwa abba ni mesa baka yi tunanin ko da daga nesa ne ka kalle ni ko ka min magana ko ka gan ni?
Abba bakin jinina ya kai haka?
Yana hawaye ya girgiza mata kan sa kiyi hakuri humaira ni na kasance me laifi a gareki ban san mezan ce miki ba ban san da wane ido zan kalle ki ba ban san ta ins zan fara neman ahuwar ki ba aisha ki yafe ma mahaifinki da ya yi rashin kula da d'iya kamar ki
Abba ka daina fadin haka ni nasan komai ka gani daga Allah ne yanzu lokaci ne abu daban lokaci ne na farin ciki abba nagodewa Allah da ya kuma hadani nida kai nasan waye mahaifina
Yau duk wanda zai min tambya cewa ni din *yar waye*zan ce ni din diyarka ce abba zauna kaji
Ta cika masa gaba da kaysn ciye ciye
Yana fara'a yace duk ni kadai humaira?
Uhn abba na
Hajiya tace ba a ta kaka ko?
Ai ku kun tsufa
Aka sa dariya
abban naki se ya rigani cikawq ni ina nan tare dake
Humaira tayi dariya lallai ma hajiya sannu
Masdook yace hajiya gaya mata kin fita kwari ita sabuwar jini ku tsohon hannu
Aka yi dariya gaba daya dakin.

Nan hira ta kacame ta bayan rabuwa ana ta raha kamar kar a rabu
_dama komai yayi farko zai karshe har ya zamo labari komai na zaman duniya dan hakuri da juna ne da zaman lafiya_

Da daddare ko suna hira suna cin tuwon shinkafa da miyar kubewa danya cikin tray daya
Aisha ta kalli hamma mubarak tana dariya hamma
uhm aisha
Kulle
Kamar ya?
Kai de kulle?
Uhm cas
Tom
Youwa abbana
Uhm aishata
Abba kayi wa hamma aure shi da hamma faruk
Kema kya fada sun fara tsufa ba magaji na gaji da neman masu mata ke kila kya samo musu
Sossai ma abba ai sun yi mata fa sun rufe ka ne basu sanar da kai ba
Aisha me haka?
Me kuwa gaskiya zan fada musu ne ayi da wuri ko kuwa nasan fa kuna so kuna kaiwa kasuwa
Eh lallai ma yarinyar nan
Abba da fadimatu ta gidan mu da rabi'atu
Kee aisha sharri inji dada
Wallahi Allah dada da gaske nake miki in kuma sun karyata dada ki tamaye su kiji
Megidana wai haka ne
Shiru yayi be tanka ba dan aisha ta gama dashi wallahi shi kuma kunya ce dashi kamar me
Ka fada min faruku haka ne?
Dada ni mezan ce?ai tunda ta fada hakan ne
Kinji ko dada kawai se munzo neman aure dikko
Masdook ya mintsine ta a baya ta zabura wayyo Allah na hamma mena ma?
Ai da sauri yayi waje dan aisha zata kunyata shi cikin su baffa aka sa dariya
Dada tace meya miki?
Mintsini na fa yayi?
Kowa ya s driya wayanan yaran halin su sai su yan banxa
To ai shi kenan mu dama haka muke su a dinga *zumunci* Allah ya tabbatar da mafi alkhairi
Amin dada
Ahmadu mu kuma daginmu sun kare a dikko ta katsina
Aiko dai hajiya gashi nan dai zuri'ar tamu daga kumo zuwa dikko Allah dai ya kara tabbatar da mafi alkhairi a zamantakewar mu ina jin dadin wannsn *yanayin*Allah dai ya sada mu dukka a gidan aljanna
amin ya Allah
[6:28PM, 3/14/2017] Kairat Up: ✨✨✨✨✨✨✨
*AISHA HUMAIRA*
✨✨✨✨✨✨✨
*Na*
*Khairat up*
*76-78*
_*©*_
_*daga fadar*_
_*hikima writer's association*_

Kwanan su uku a gidan su masdook suka tarkata da kewar juna suka koma garuruwan su yan gombe suka dau hanya yan dikko ma suka dau hanya
ba karamin dadi humaira taji ba dan zuwan abban ta da yayunta maza guda biyu ita ma yanzu alfahari take da dangin ta
Har an samu anyi maganar auran hamma mubarak da hamma faruk abbsn da baba sunusi zasu je dikko neman aure.
Allah sa ayi damu.

***
Cike da kasala ta take kwana biyu tankar ba ita ba ga uban bacci da zazzabi ta take yi da ciwon kai.

Har kusan karfe tara bata farka ba wanda ba sabon ta bane masdook har ya shirya ya ja mata dan yatsa
Ta dan juya alamun baccin be isheta ba
Humaira lectures din fa?kin ga kin makara nima baki min break ba baki tayani na shirya ba kwana 2 naga wani sabon alamari kika fara mun a gidan nan kin fara wasa da komai ko?
Hmm!hamma na gaji wallahi baccin be isheni ba ka hada tea ka sha kaji?
Kallon ta yayi ya sunkuyo kusa da fuskarta meke faruwa matas?
Hankade shi tayi ni ka daina zuwa kusa dabi ban san wannsn turaren ko ta fada da tsawa tsawa
Mamaki ya ciks shi ya kufula kawai ya dungure mata kai ya dau jakar sa ya kara gaba
Ita kuma ko a jikin ta komawarta baccin tayi abunta .

Yarinyar nan bata da kunya wallahi mtsw.

***
Humaira bata farka ba se wajajjen karfe daya da rabi na rana tayi salati ta shiga bandaki tayi wanka ta zura atanpa doguwa ta koma falon nan cikin ta ya fara kugin yinwa yana zillo tsaki tayi dan wani irin 'kiwa take ji
Wayarta ta lalubo ta danna number din hamma masdook yana duba mara lafiya lokacin se be dauka ba har ta tsinke
Tayi tsaki mtsw
Shi kuma da ya gams da mara lafiya ys tafi yin sallah saida ya dawo ya kuma ganin kiran ta kusan missed call goma
Ita kuma wannan lafiya?
Kiran ta yayi da sauri ta dauka tana dauka ta fashe da kukan shagwaba ni shi kennsn tun dazu ina kiran ka bska dauka ko ?
Shi ne abun kuka
Uhn uhm ni yunwa nake ji .
Hah'ah ,kina jin yunwa humaira ki shiga kitchen mana!
Ni baxan iya ba
Ya kike so ayi yanzu?
Ni alala nake so na gwangwani ka kawo min
Humaira ban son fitina fa da tashin hankali wane irin alele ina zan samo miki ki daure ki tashi ki gyara ki dora ki ci ni kuma ki min tuwon shinkafa zan dawo da wuri ban san wani alele
Ai seta sa mishi ihun kuka wallahi ba abunda zan yi ka siyo min kawai ta kashe wayar.

Kan sa ya dafa ni in banda rigima da masifa humaira ina zan samo miki wani alala tsaki yayi ya dau mukulinsa ya shiga office din wani abokin aikin sa dr.muhammad isa zage
Yana gurnanin masifa kawai
Ya dai mijin aisha humaira?
Hmm wai alele take so ni ban san me yske damunta ba kwana 2 se rigima take ji abu kadan fada da masifa in ta gs dama kuka ga tashi a latti.
Ya dinga murmushi
Ya ina ma bayani kana min murmushi?
To ai kaine ma masdook banda abunka ai kai seka godewa Allah ka raba goron murna
A wannan tashin hankalin da nake ciki zan raba goro?anya kana jina kuwa zage?
Wai idan ka ne ya rufe ko kan ka ne ya kulle?
Kamar ya
Duk ka fado alamumin masu ciki kuma ksna neman answer da ka riga ka santa.
Alamomin masu ciki kuma...... la'ilaha illa lahu ai zama be kamani takalmin sa ya zare ya kalli gabas yasa goshin sa a kasa yana nuna godiyar sa ga Allah bakin sa har kunne zage amma naji dadi tashi mujr nemsn abuncin gargajiya dan Allah
Tsaya in kira mrs.dita ince ta aika a siyo yadda in mun karasa an karbo ko kuwa kar aje ya kare
To maxa yi sauri kirawota.

***
Wajan karfe hudu da rabi ya dawo yadda ya sameta ya basa dariya sossai
Tana zsune jigum a kasa ta ware kafafuwa tana shan iska dankwalin a kasa bakin ta a tsuke tana kuka shame shame
Duk yunwa ta gama mata kamu ta na ganin sa ta mike zumvur ta karasa kusa dashi ta fara duksn kirjin sa da karfin gaske ta dinga mintsinin sa
Yau naji mugunta aisha wannan ai cin zali ne kashe ni zaki yi?
Ba kaine ka min fada a waya ba bazaka samo min alele ba ina ta kaina nima ina zan iya maka wani tuwo
To yi hakuri zauna ys zaunar da ita ya ajie mata flask din alele a gabanta
Tana budewa kamshin ya daki hancin ta ba karamin dadi taji ba gashi yaji manja kusan guda goma taci ya tsaya yana kallon ta wai aishar sa na dauke da babyn sa a ciki kwansa kwallar dadi ta zubo masa a fuska
Ysna kallon yadda taje ta lodar abinci aishar da ba ta wani ci sossai
Aisha ai se kiyi kiba irin wannan cin abinci haka kamar an aiko ki?
Uhm bazaka gane ba hamma yunwa nake ji sossai na rasa dalilin wannan cin nawa yayyi yswa
Bara nayi wanka na duba lafiyar ki
To hamma kar kasa wNnan turaren kaji?
To ur highnesss na daina sawa
Ta washe masa baki nagode.

Wanka yayi yasa 3quter da singlet ya fito da kaysn awo ya auna ta ya ya duba plus dinta da komai da ya kamata ya koma daki ya ajiye
Ya dawo falo ya sunkuce ta sama ya dinga juyawa da ita a duniyar sama janati(lol)
Humaira mu godewa Allah sarkin sammai da kasai mu godewa Allah da ya bamu ikon na ganin wannan ranar da kunne na yaji wannan dadadan albishir din kema zan jiyar dake
Hamma ajiyeni kaina ta juya ajiye ni
Ys zsunar da ita kan kujera ya riko hannayen ta biyu ya sa kunnen sa a cikin ta yana hawaye saukar ruwa taji a jikinta
Hamma kuka?
Kukan dadi ne humaira kukan dadi ne barni na gama dan kin gama min komai kinsan ko babbsn rana gun ko wanne da namiji a duniya da abunda zai fi son ji a duniya?
Uhm me kuwa sama da matar sa tana son sa kuma ya sameta kuma gata da ladabi. Duk ba wannan ba humaira ba moment me dadi irin moment din da nake ciki yanzu moment din dana fuskanci na kusan zama *baba*ba momont me dadi irin moment din da zan ji wannan kalmar daga bakin abinda zaki haifa msna *BABA* wallahi humaira kin gama min komai
Wai ni ban gane ba me kake cewa ne?
Abunda nake cewa shi ne aisha humaira ta kusan zama *UMMA* kin kara takawa matsayi me girma daga *'ya*kika xama *kanwa* daga ksnwa kika zama *mata*daga wata zaki zamo kuma *UWA*Kinga kuwa kin kara daraja fiye data
Hamma are u serious?
Kai ya gyada mata
Ta rungumesa dan dadi ta dinga mika godiyar ta ga Allah hamma Allah ya nuna mana fitowar abun cikina _i want to also experience the moment_
Murmusa mata yayi to se ki ji sharuda na
Ban da aikin wahala
Cin abinci kan lokaci
Bwn da tsalle tsallen kin nan.
In kina son abu ki fada min.
Ban da yawo
_An gama boss_
Saboda ina son babyn nan that will be my first born
So ki kula sossai ban san abunda zai taba min shi
To hamma i ll be extra careful.
Youwa banda wasa da ruwa a toilet saboda tsantsi zsn dinga rakaki
To babban baby
Ke kuwa *_dan so_*
Hhh
Kinga huta a nan zanje in dawo
Tom ka taho min da chocolates to da grapes to ds gwanda
Naji madam kar fa ki mtsa daga nsn.
To
Rungume filon kusa da ita tayi tsna murnr dadi daga bisani ta shiga tayo alwala ta yi sallah raka'a biyu dan nuna godiyar ta ga Allah.
Daf da magariba ya dawo ya dinga shigo da kaya niki niki yana ajiyewa a falo
Ita dai kallon sa kawai take yana ajiye kaya.
Seda ya gama ya xsuna wash na gaji da yswa
Sannu da zuwa
Yauwa sannun mu.
Kinga sakon ki .
Nagode
Wayanan meye?kayan baby ne na wasa kingan su ya juye mata kayan wasan irin na yara su jirage yartsana mota mashun da sauran tarkace dai haka gasu nan
Su hamma gandoki ke ina rywanki yadda nake jin babyn nan banki ba ya fito ba yau
Dariya ta sa masa wayanan fa?
Frame ne masu kyau na jarirai ki dinga kalla zaki samu cute babies sannsn wannan radion karatun qurani ne me grma kullum kina ji dan babyn kasance me ilimi kullum kina cin dabino ki sha zam-
zam
hamma an dau course to Allah amfana amin
se ki rage kallon tv da yawa ban san babyna na kallo over da shan zaki lyk u ya lakuci hancin ta
Ta dinga dariya nan suka baza kaya suna aikin hadawa
Daga bisani ya dauko biro da takarda zo mu zabi sunayen yara
Kai hamma wallahi bada ni ba duk gasu abbi dasu baffa dan rashin kirki kai zaka zabi sunan baby din ka bari ma yazo duniyar msn shi ma yayi kwari cikin
Ke bar tsofaffin nan zasu sa masa sunaye irin nasu irin su yusha'u su .... ta toshe masa bakin sa kaje ka huta ka gaji da yawa ko kuma fara yanka min gwandar nsn in ci ai ni kuma yanzu na zama bawanki se yadda kika yi dani bara na dauko wuka da plate se kina ci kana bsni a baki dai to madam.

***
Haka rayuwar su take tafiya yadda yake kula da ita har aikinsa yake shiga dan ta fiya kwadayi shi yasa wani zubin yana gida dan zata iya bukatar wani abun kuma kar aje baya nan
Basu samu saukij laulayin ta ba seda cikin ya yi wata hudu tukuna ta samu sauki amma tayi kiba ta hau kamar ba ita ba tayi jajir da ita
***
An sa bikin su mubarak wata biyu masu zuwa
Tana ta lallaba shi ya yarda taje dikko da kumo yaki ya ta bari in ta haihu seya ksits ganin daki
Kai.hamma fadimatu fa da rabi'atu
Ko ma amira ce
Ai lokacin nayi wata shidda ai yayi kwari by then baya son gardama yace Allah ya kaimu amin.
[6:28PM, 3/14/2017] Kairat Up: ✨✨✨✨✨✨✨
*AISHA HUMAIRA*
✨✨✨✨✨✨✨
*na*
*khairat up*
*78-79*
*_©_*
*_daga fadar hikima writer's association_*

_yan uwa kuyi hakuri nayi kuskure wajan rubuta number 78 a maimakon 77 shi yasa na gyara a nan da fatan mun tashi lafiya?_

Cikin aisha humaira na da wata biyar aka fara shirye shiryen bikin su fadimatu amma masdook ya hana taje tun ana sati bikin seda ta fadawa abbi da mama tukuna ya kaita amma duk motsin ta yana jin ta yana ganin ta baya barin ta yin komai.

Lokacin cikin amira watan shi takwas saura wata daya ta haihu ita ma tayi nauyu cikin nata babba kuma se nan da ita hamma yusuf yake yi.

Ranar kamu suka sa wata atampha sharooton sukyi gown a tsakanin su aka kama amaren guda biyu

Washe gari wuni da safe aka daura auren ansha shagali da du dj su aisha ana ganin rawa ba damar aje a taka dan gam gam ya rike hannun ta yana ta zsre mata ido hamma sau daya
In kin haihu kya yi
Ta zumbura masa bakin sa yayi murmushi.

Washe garin daurin aure wato ran litinin aka dau hanyar gombe yayin da jikoki dada suka sha kuka da fada da nasiha wajen iya zama da miji da dangin miji.

Aisha humaira da amira da hamma yusuf da shi masdook da nas tare suka tafi a mota daya saura kuma a mota daban daban.

Can wajan magrib suka karasa gidan guda daya ne babba kato amma two part wato su biyu ne masu gidan da mubarak da fsruk amma a wajan gidan aka rubuta
*Aisha Humaira mansion*
Ba karamin kyau ginin yayi ba da beni kuma kowacce a bsngaren ta dakuna uku uku da toilet ko wanne a ciki kitchen din guda biyu ne daya a sama daya a kasa ba katamin kokarin hada musu kayan kitchen abbi da baffa suka yi ba falon fadima purpule komai kitchen dinta lemon green tun daga fenti har kayan da aka zuba mata a ciki.

Ita kuma rabi'atu pink ne light cikin kitchen dinta kuma purple dark da komai na cikin sa gaba daya.

Ba karamin sha'awa ya bawa mutane ba
Tun da suka zo aisha ta samu guri ta zauna ta mimike kafafun ta tana ta haki ita ksm ta gaji hamma masdook suna waje su kuma hade da angwayen suna hira

Abinci sun ci har seda suka ture da ksn su da hannun su .
Kwana abba yace su kuma yi gobe se su koma aka aminta da hakan.

Da daddare suna hira shi da humaira a bsngaren sa ta tsakanin d'a da mahaifi amma aishata ke se kin kwana biyu ko?
Aa abba gobe zamu koma
Amma da na so ki kuma kwana ko sati ne se kiyi in yaso kya bi jirgi ki koma gida

Abba sede ka fadawa hamma dan shi ke da matsala bazai barni ba in na tambaye shi kai kuma ko be so ba ze yarda dan kunyan ka
Aa baxsn masa haka ba in kin sauka lafiya daga baya kwazo mana ganin gida yawon arba'in.
Shi kennan abba.
Waysrta ke ringing abba kaga ma ysna kira ai shi baya so nayi nisa dashi ne bara naje ts mike abbsn ya taya ta tashi daga zaune
Hello hamma
Wai kina ina ne?
Ina gun abba amma gani na fito
Kin san dare yayi ya kamata a ce kina bacci ki huta babyn ma ya huta da wuri zamu wuce gobe
Ai gani nan zan shiga gun su hajiya ko
Zo tukuna zan miki seda safe
Hamma Allah da nisa tafiyar fa kasan da kyar fa...
Lokacina ne baki da shi amma kina dana kowa gud nagode
Ya kashe wayar
Ta bi wayar da kallo tana zumburar baki mutum ya gaji ace baze ce ya gaji ba.

****
Da safe aka soya dankali da kwai aka yi kunu aka kuma soys kosai masu shan tea suna sha masu son kunu kuma suka hada da kosai.

Seda suka gama aka yi wanka dan sha daya zuwa sha biyu zasu fara komawa garin su

Abba ya rarraba musu dubu biyu biyu gaba dayan su.

Tun da ta tashi bata ga hamma masdook ba ko a gun break dan tasan haushin ta yake ji to ita ya zata yi ?

Zaman ta tayi kawai.
Shi kuma se kallon wayar sa yake yi ko zata kira sa amma shiru
Lallai humaira raini .
Amma ba komai zan rama.

Banza yayi da al'amarin ta shi ma har suka zo tafiya ya wani daure mata fuska ba alamun dariya a ciki se jikin ta yayi sanyi ita kam ta kasa katabus nas ya taya ta shiga baya ta kukuta ta shiga yau sun ga miskilanci tun da suka dau hanyar kano uffan masdookbe fada ba balle yayi tari haka suka yi tafiyar lami sede hira a tsakanin hamma nas da kuma ita humaira din.

Kuma yana jin su har gida ya sauke nas sannan ya maida ta gida ya bata key din yayi reverse ya koma da bsya ya fice daga gidan ita dai bata ce komai ba to mezata ce?tasan laifin ta ne ita ta siya da kudin ta ba wani ne ya siya mata ba.
Amma idan ta ysyi rau rau da hawaye tana kokarin basarwa amma seda ya zubo mutum se bakin hali da nukufurci

Ciki ta shigs ta zauna ta huta sannan tayi wanka ta dawo ta dafa musu abincin da zasu sa a bakin su tayi lemon kwakwa da kankana ta sa a fridge sannan ta zauna tasa kararun qurani me girma kamin bacci ya dauke ta a ksn kujera tana jin karatun.

Shi kuma gidan abokin sa ya je suka sha hira a tsakanin su kamar ba za a rabu ba se da ya gama ya koma gida yaga tana bacci a gun yasan tayi kewar sa amma yana son yaga iya son da take masa ya koma koya mata hankali kar ta kuma masa haka shi sa ze horata.

Ya debi abincin ya ci sannan ya sha lemo ya shiga yayi wanka ya yi sallah ya kwanta.

Tashi tayi ita ms tayi sallah seta ga alamun an shigo kuma anci abinci wato ya dawo kennsn sallah tayi ta koma dakin sa taga yaba baccin gajiya seta koma dakin ta kawai ta kwanta kan kushin din dakin tana nazari shi yafiya daukar abu da zafi ta shafi cikin ta *babyna u miss dada ryt?*nima i miss him ya daina mana irin wannsn fushin gaskiya amma koda yake laifin moma ne ai shi yasa dada is angry amma zamu shawo kan sa insha Allah.
[6:28PM, 3/14/2017] Kairat Up: ✨✨✨✨✨✨✨
*AISHA HUMAIRA*
✨✨✨✨✨✨✨
*na*
*khairat up*
*79-80*

_tallah_

_a sanadinki yau har asibiti nazo gwaji_
_wannan wane irin iskanci ne zaki zauna a falo a haka?_
_ka manta ni yar iskar ce

Please Login or Register in order to submit comment