Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka sa mata ido babu gaira babu dalili, ko mai ya yi masu zafi da ita? Allahu A'alam.

Bayan bisiting da sati biyu, rannan Mairo ta fito domin yin fitsari da daddare a lokacin Kausar ma ta fito ta tsugunna a bakin rariyar hostel tana goge bakinta domin ta kwanta. Mairo na daga bandaki ta hangi wani mulmulallen abu mai sheki da tsayi na sanda ya nufi Kausar. Ta ware idanunta gabadaya sai ta gane katon maciji ne wanda ake rade-radin akwai a makarantar.
Ta yar da butarta ta sheko da gudu dai-dai sanda macijin ya fasa kai, ta angije Kausar tun karfinta ta wulwula ta fada kwatami da baka, abin tsautsayi, sai kulbar (macijiyar) nan ta huce fushinta a kafar Mairo, wato ta sare ta.
Kausar ta mike cike da bala'i a lokacin idanunta suka gane mata abin da ke faruwa, dai-dai lokacin kulbar ta sulale tana komawa inda ta fito, ga kuma Mairon da ta angije ta kwance a kasa ba yadda ta ke. Ta daura hannuwa aka ta rafsa ihu, wanda ya ratsa gaba dayan hostel din, student da metron suka fito. Kausar ta ce “macijiya ce ta sare ta.”
Ai jin haka captain ta suri Mairo, sauran yara suka bi ta yuuu! Har da su Kausar sai gidan principal ana buga mata kofa.
Ta fito a gigice ita ma nan take ta bugawa school doctor waya, nan da nan sai ga ta, aka wuce da Mairo asibitin makaranta, Doctor ta dukufa ga son ceto ranta.
Kausar da Nabilah suka kasa komawa hostel ko babu komai akwai tausayin rai a zukatansu, balle ita Kausar da tasan hakikanin yadda abinda ya faru. Nadamar abubuwan da ta ringa yi wa Maryam Bedi, suka shige ta. Ta ji tausayin Maryam matuka, ta kuma tambayi kanta, shin ko wace irin zuciya ce da ita? Irin su Maryam ne masu rama sharran da hairan, babu shakkah ta yi nadama.
Nabilah ta yi mamakin damuwar Kausar akan Maryam ta yi yawa, ta kasa ko magana. Ta ce "Kausar kowa ya koma hostel sai mu, ni fa tsoro nake ji".
A salube Kausar ta sa kafa cikin dan karamin asibitin ta samu benci ta zauna, ba ta da niyyar tashi. Nabilah ta biyota cikin mamaki, ta ce "Wai me ya faru ne? Ba zaki zo mu tafi ba?"
Ta ce "Je ki abinki Nabilah. Amma ni a nan zan kwana".
Nabilah ta kama baki, dai-dai lokacin da Mummy Dukku wato principal ta fito zata koma gidanta. Ta hango su Nabilah ta ce, "Ku kuma me kuke a nan ba ku koma hostel ba?"
Kausar sai ta sa kuka. Ta matso ta dafa kanta domin ta santa farin sani sabida mahaifinta, ta ce "kawarku ce ince ko?"
Nabilah ta yi saurin cewa "A'ah, dakinmu ne kawai daya".
Mummy ta lura da kukan da Kausar ta ke sosai ta ce, "Ke kuwa tausayinki ya yi yawa Kausar, alhamdu lillahi dafin bai shiga cikinta ba, kuma Doctor ta zuke shi. Insha Allah zuwa safiya za ta warware, tashi ku tafi dare ya yi sosai".
Sai da suka je daki ne Kausar ta ke gayawa Nabilah hakikanin yadda akai maciji ya sari Maryam. Ta ce "Yanzu ni tashin hankalina shi ne, idan ta mutu ban nemi gafararta ba ina zan sa kaina?"
Jikin Nabilah ma ya yi sanyi, ta ce, "Allah Sarki, irin su ne ake cewa masu halin 'yan aljannah".
Suka yi jugum-jugum har wayewar gari ba su runtsa ba, nadama ta ishe su, sai kuma kaunar Maryam farat daya ta bi zuciyoyinsu.
Washegari Uncle ya zo kiran suna kamar yadda ya saba, cike da mamakin rashin ganin Maryama a class don kullum ya shigo idanuwanshi akan wurin zamanta yake. Duk da haka bai fasa kiran sunan ba, har ya zo No. 40, shiru ba ta amsa ba.
Ya dago manyan idanunsa ya zubawa Kausar cike da zargi kamar ita ce ta boye Maryaman.
Ya ce "dakin ku daya, tana ina ban ganta ba?"
Kirjinsa har wani harbawa yake da sauri-da-sauri. Fargabarsa kada ace da shi iyayenta sun cire ta daga makarantar sabida su Kausar. Bakin-cikinsa shi ne yau ace Maryama ta bar makarantar nan. Tashin hankalinsa shine ko sunan kauyensu bai sani ba, alhalin yanzu yadda yake kaunar Ilham haka yake kaunar Maryama. Idan zai iya rabuwa da ita, to hakika zai iya rabuwa da Ilham.
Cikin in-ina Kausar ta ce "Maciji ne ya sare ta, tana kwance a maternity..."
Tun kamin ta kai karshe Uncle ya fita. Ya doshi maternity cikin matsanancin tashin hankali, ko gani ba ya yi sosai. Ya banka kofar da kafarsa babu neman izini.
A kwance ta ke, idanunta a rufe, rana daya kacal ta zabge, ta yi wani irin fari fat kamar babu jini a jikinta, sannan ta kumbura kamar an hura balam-balam.
Nurse din da ke kokarin daura mata 'drip' ta juyo a razane ta dube shi, bai kula ta ba ya karisa gaban gadon da Maryam ke kwance ya tsaya kurum yana kallonta. Kamar an ce da ita bude idonki, ko kuma alamar tsayuwar mutum ta ji a kanta oho, ta bude fararen idanunta a hankali wadanda suka kumbura suka yi mata nauyin budewa, a hankali ta ce "Uncle…….." Sai hawaye suka zubo ta gefen idonta.
Ya yi saurin kama hannun damanta, ya ce "Sannu Maryama, sannu kin ji. Allah Ya ba ki sauki".
Ya juya ga nurse din ya ce "Edcuse me madam Serah, na yi miki shisshigi cikin aikin ki. Maryam na daga cikin dalibai na masu muhimmanci a gare ni. Ki yi hakuri".
Ta yi murmushi ta ce "Ai na ga alama, wannan patient din taka akwai raki da saurin kuka. Na dauka dadi zaki ji da kika ga Uncle sai kuma ki kama kuka?"
Mairo ta maida idanunta ta rufe tana murmushi. Ta nemi ciwon da jikinta ke yi ta rasa, sabida kasancewar Uncle Junaidu tare da ita.
Suna magana a kanta shi da Madam Serah ta gaya mishi wannan macijiya ta dade tana sarar dalibai, anyi duk iya kokarin da za a yi don ganin an fitar da ita daga makarantar an rasa. Wani zubin sai a yi tsammanin ma ta mutu don sai a yi shekaru biyu ba a ji duriyarta ba. Amma yanzu kam za a daukaka zancen zuwa federal da yardar Allah za a fitar da ita.
Ya ce "Maryama ta kumbura, ta yi biyun yadda ta ke".
Ta yi murmushi ta ce "Jini ne babu isashshe a jikinta, wanda aka zuke tare da dafin amma already an tafi a sayo wanda za a sanya mata a asibitin Aminu Kano".
Hankalin Uncle ya tashi, ya ce yana son ganin Doctor Nanah, ta ce tana ofis ka karisa.
Ya samu Dr. Nanah a ofis cikin tashin hankali. Ta ce "Yaya dai Uncle Junaidu?"
Ya ce "So nike ki debi jinina idan ya yi dai-dai ki sanyawa student dina".
Ta ce "To bari in diba kadan a auna a gani".
Ta zuka kadan a sirinji ta mikawa lab asisstant ta auna, ya nuna (negatibe), ga duk wasu gwaje-gwaje da akayi, sannan dukkansu a 0+. Ya kwanta ta debi leda biyu ta ce ya ci gaba da kwanciya ya huta. Ta ba nurse ta sanyawa Mairo ta dawo tana fada mishi irin abincin da zai ringa ci har zuwa kwana bakwai.

Nan da nan labari ya watsu cikin FGGC cewa Uncle Junaid ya yi donating jini wa Maryam. A'ah, cece-kuce ya soma (round) zagaye makarantar musamman daga 'yan ajinsa da daman suna hankalce da su. Yara kanana da su amma sun iya gulma. 'Yan manyan aji kuwa masu yi masa asirtacciyar soyayyah, wadanda a da ba su san da Maryam din ba suka zo suna kallonta, duk ta takura ta rasa inda zata sa kanta, balle da ta lura har da masu yi mata mugun kallo.
Ranar da ta dawo hostel Kausar kunyarta ta ke ji, ko ido ta kasa hadawa da ita. Daga baya da ta ga Maryam din ma ba ta damu ba harkar gabanta kawai ta keyi, sai ta zo bakin gadonta ta zauna ba ta ce komai ba.
Nabilah ta shigo itama ta zauna a katifarta abin da ko da wasa ba su taba yi ba. Suka ce "Don Allah don Annabi Maryam ki yafe mana. Wallahi sharrin shaidan ne, kuma mun gode da sacrifice (sadaukar da kan) da kika yi mana. Muna rokonki daga yau mu zama daya a makarantar nan, wato mu zama mu uku cikin amana".
Mairo ta yi murmushi ta ce "Babu komi, ni dama ban taba kullatarku ba, mamaki dai kuke ba ni. Amma shi ke nan, komi ya wuce".

Daga ranar Maryam, Nabilah da Kausar ba a kara jin kansu ba.
To sai kuma ciwon ciki ya kama Kausar, kullum ba ta iya barci, sai murkususu da kuka cikin dare, haka suke kwana tsaye a kanta har asubah sannan zata samu barci.
Da suka ga abin ya fi karfinsu sai suka yi reporting ga hukumar makaranta. Aka dauki Kausar zuwa maternity inda aka gano kabar ciki ke damunta. Nan da nan aka yi hamzarin mikata gida, domin abin ya fi karfin asibitin makaranta.
Suka koma kewar Kausar tare da yi mata addu'a, kullum, har lokacin jarabawa ya matso. Kokarin Uncle shi ne Maryam ta saki ranta ta yi abin kirki a jarrabawarta, amma ina! Tunanin Kausar da halin da ta ke ciki ya hanata zama lafiya.
Ranar da suka soma jarrabawa suka dawo hostel sai suka ga babu ko allurar Kausar a dakin. Captain da Metron sun kwashe sun bai wa iyayenta.
A gigice Mairo ta fita kafarta ko takalmi babu, kanta babu kallabi. Nabilah ma ta bi ta dakin Metron suna tambayarta yaushe aka kwashe kayan Kausar?
Ta ce "Allah sarki, wannan yarinyar diyar Gwamnan Jos, ta rasu. Tun satin da ya wuce".
Suka rushe da kuka, suka zube anan suna ta yi. Tsoron Allah Ya kara shigar Maryam da Nabilah. Tun daga ranar suka koma wasu irin sukuku, ba fuss ba ass. Shi kansa Uncle ya girgiza da mutuwar Kausar, ya yi ta lallashinsu yana ba su baki. Ya ce da Nabilah abin da yake ankarar da ita ke nan kan daukan duniya da zafi. Shi Ubangiji ba ruwansa da ko kai wane ne, dan wane ne, wane ne ubanka face ayyukanka kyawawa.
Nabilah ta fi Maryam ramewa, ta fi ta gigicewa, domion dai ta fi ta shakuwa da Kausar. Sannan ta kara rungumar Maryam a matsayin 'yar uwarta don sai ta ke ganinta kamar Kausar.
Aka yi jarrabawa aka kare, sai hutu sati mai zuwa. Sai dai fa daga Maryam har Nabilah kowacce cike ta ke da zullumin sakamakonta. Uncle ya yi fushi da Maryam sosai, domin ta dauko na talatin da takwas yayin da Nabilah ta dauko na arba'in.
Ta kaskantar da kai ta dinga ba Uncle hakuri, ta tabbatar masa zango mai zuwa za ta dage ta yi abin da zai ji dadi. Mutuwar Kausar ke nukurkusarta har zuwa lokacin.
Ranar hutu malam Bedi sammako ya yi domin hedimasta ya gaya masa tun ana saura kwana uku, don haka a kwanakin nan barcin da suka yi kalilan ne sabida dokin dawowar Mairo. Barin ma Inna Hure da shiga goma, fita goma sai ta siyo abin da zata ajiyewa Maironta. Tun daga kan goriba, kurna, goba, magarya, dinya da ire-irensu wadanda tasan Mairon na so babu wanda ba ta nemo ta ajiye mata ba.
Duk sammakon Baban Mairo bai isa makarantar ba sai da aka soma dadewa.
Mairo da Nabilah na zaune karkashin dalbejiya dukkaninsu cikin damuwa suke na rashin ganin kowa nasu. Nabilah ta ce "Da na san gidanku Maryam da na zo kamin na wuce Lagos hutu wurin Auntyna".
Maryam ta jinjina kai ta ce "Ba zaki iya zuwa gidanmu ba, can ne cikin surkukin kauye, cikin Fanshekara".
Nabilah ta ce "Don ba kisan yadda nake son zuwa kauye ba ne, idan kuma kin musanta hakan ki gaya min ki gani".
Ta dauko biro da jotter tana jiran ta bakin Mairon.
Mairo ta ce "Fanshekara, motar Gurin Gawa, idan an shiga Gurin Gawa, sai a tambayi gidan Malam Bedi kowa ya sani. Idan kuwa yara ne kika ce musu 'MAIRON HURE' da gudu za su rako ki".
Duka Nabilah ta dauke cikin jotterta, wanda ke bayansu ma ba su san da tsayuwarshi ba shi ma ya dauke cikin kakkaifar kwakwalwarsa.

"Lah, ga Babana nan!". Mairo ta fada cikin matsananciyar murna, kamin ta kwasa da gudu ta rungume Malam Bedi. Nabilah ta dago daga rubutun da ta ke ta bi bayan Mairo da kallo, sai ta hango ta rungume da wani yagulallen tsoho, sanye cikin yadin algarara, kanshi duk furfura. Ta ce a ranta, "Ya za a yi ace wannan ne ya haifi Mairo? Ya fi kama da kakanta fiye da babanta".
Ba tasan cewa ba wai shekarun da ya yi a duniya ba ne suka janyo masa wannan tsufan ba, a'a, wahalar rayuwa ce kawai ta noma, girbi, da sussuka irin ta kowanne manomin kauye.
Tausayin Mairo ya kamata, ta tabbata ita 'yar talaka ce futuk, amma she is contented with what she habe (a gamshe ta ke da abin da ta ke da shi, ba ta taba kwadayin abin hannun wani ba).
Mairo ba ta taba tambayar Nabilah ita 'yar waye ko daga ina ta fito ba. Wannan ya sa Nabilah tambayar kanta, shin Maryam wace iri ce? A zahiri miskila ce, abin da tasa a gabanta shi ne kawai ya dame ta.
Ta mike ta tadda su tana gayas da Malam Bedi cikin tsananin girmamawa.
Mairo ta ce "Baba Nabilah sunanta, ajinmu daya, dakinmu daya. Da har da Kausar amma ita ta rasu".
Fuskarshi ta nuna bai ji dadi ba, ya ce, "Sannunki Nabilah, Allah Ya jikan Kausar".
Idanunta ya ciko da hawaye, ta juya tana sharewa ta ce, "Amin".
Babu irin neman da ba ta yi wa Uncle ba, don su gaisa da Babanta, amma ba ta ganshi ba. A haka cikin rashin jin dadi ta yi sallama da Nabila rike da 'yar jakar kayanta ta buhu (Ghana Must Go) suka fita. Sun sha wuya matuka irin ta motocin haya kamin Allah Ya kawo su gida.
Ganin irin wuyar da Babanta ya sha ya sa ta alkawarta wa ranta daga wannan hutun zata hutar da shi kai ta makaranta da dawo da ita, tunda ta gane hanya zata dinga tafiya da kanta.
Tunda yaro ya shigo da jakar Mairo Hure ta biyo bayansa da saurinta. A soro suka yi kacibus, da Mairon nata. Suka rungume juna kamin Hure ta soma hawaye ta ce "Ashe wannan ranar zata zo Mairo, ranar da zan kara ganinki?"
Mairo kuwa baki ya ki rufuwa a haka suka karasa cikin gidan kamar wadanda suka shekara ba su ga juna ba.
Inda duk Inna ta mika hannu sai ta zarowa Mairo abin sawa a baka, ta ci ta yi nak! Ta ci girkin Innarta da ta yi kewa, ba kadan ba. Duk da cewa abin da ta ke ci a makaranta ya fi na gidansu amfani a jikin dan Adam.
Hure ta kasa boye mamakinta, ta ce "Shin mai kike ci a makarantar nan ne Mairo? Kinga kuwa yadda kika zama buleliya, kika yi fari sai sheki kike?"
Mairo ta sa dariya, ta ce, "Ba abin da bana ci Inna. Tun daga kan kwai, dankali, agada, doya, madara, nama da kifi ba abin da ba a bamu. Har 'ya'yan itace (fruits) ba dole in zama buleliya ba?"
A ranar dai Mairo da iyayenta kwanan zaune suka yi, tana ba su labarin rayuwarta a makaranta. Sai dai fa duk rabin hirarta, "Uncle Junaidu" wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wurin sama mata farin ciki da walwala a cikin dalibai 'yan uwanta.
Malam Bedi ya ce, "To Allah Ya saka mishi da alkhairi".
Sai dai a cikin labarinta ba ta kawo labarin saran sa macijiya ta yi mata ba, don ta tabbata idan suka ji, kidimewa za su yi su ce ba zata koma ba.
Hutun Mairo gwanin ban sha'awa a gidansu, gabadaya yanayin rayuwarta ya canza, ba ta barin Innarta da aiki ko ya ya, sai ta karba ta yi. Haka ta ke bin babanta gona tana taya shi shuka da ban ruwa. Abokinta Rabe da ya ji ta zo hutu daga makarantar kwanan da aka kai ta, sai ya aiko yaro rannan da yamma wai Mairo ta zo su je su hau tsamiya. Malam na jin sanda ta maida dan aiken ya tambayo mata Rabe, shin yanzu ta yi masa kama da 'ya'yan birrai ne da zai ce ta zo ta hau bishiya?
Sai ya yi murmushi yana kara shi wa Habibu albarka a zuciyarsa.
Rannan sun dawo gona ke nan ita da Babanta, ta zuba ruwa a buta tana alwala a gindin rijiya sai ta ji rurin mota. Kamin ta kare alwallar sai jin sallamar Nabilah ta yi a tsakar gidansu. Da ta yi wurgi da butar cikin rijiya ta kwaso da gudu ta cacume Nabilah suna ta tsallen murna.
Inna ta fito da sabuwar tabarma ta shimfida mata a shararriyar rumfar hutawar su tana, "Lale da Nabilah, muna murna da zuwan Nabilah".
Shi ma malam ya fito daga turakarsa yana na shi marhabin da bakuwar Mairo domin dai labarin Nabilah kamar na Uncle ne a cikin kansu.
Nan da nan ya fita ya shigo mata da damammiyar sabuwar fura da nono kindirmo gami da gasasshen nama. Nabilah karamcin iyayen Maryam ya burge ta, rayuwarsu kuma ta ba ta sha'awa. Ta raba komai biyu ta kaiwa direbanta wanda ya kawo ta. Ta dawo tana ci suna hirar bayan saduwa har goshin magriba, sannan suka yi haramar tafiya.
Nabilah ta ba ta mamaki kwarai yadda ta iya ta sarkafo kai cikin surkukin kauyen su, ko da wasa ba ta kawo zata iya cika alkawarin da ta dauka ba. Ta yi zaton dai ta karbi adireshin ne kawai. Direbanta ya sauke musu kwandon dankalin Turawa da doya cikin (boot) wanda Nabilar ta kawo musu a matsayin tsaraba.
Hutu ya dauko karewa, Mairo ta soma shiri cikin nutsuwa. Tarkacen da ta tafi da su da farko, yanzu duk ta rage, sai wanda zai amfane ta kadai.
Ta ce da Innar ta daina tara wannan uban kanzon da ta ke tara mata, ana ba su lafiyayyen abinci sau uku a rana. Ta tsefe kanta ta wanke tas da shampoo ta je aka yarfa mata sabon kitso yiri-yiri. Ana saura kwana biyu su koma makaranta. Ta yi wankan yammanta ta sanya sabuwar atamfarta 'jaba' ta zauna a rumfar tsakar gidansu tana gyaran kumbarta. Wani yaro mai zakin muryar tsiya ya kwada sallama ya kara da cewa, "Wai ana kiran Mairo a waje",
Sai ta ji abin banbarakwai ta dago kai tana hararar yaron. Dai-dai lokacin da Inna ta fito daga bayan gida rike da buta zata yi alwala a gindin rijiya, ta ce da yaron "Wane ne mai kiran Mairo?"
Yaron ya ce "Wani mutum ne dogo, fari ne kamar Balarabe, kayanshi masu kyau ne, ban taba ganin mutum mai kyawunshi ba. Ga dukkan alamu daga birni ya ke".
Mairo ta saki kunne tana mamakin surutun Ilu dan makotansu. Ita kuwa waye wannan? Ina za ta tsaya tana yi wa mutum irin wannan kallon kowane ne shi, balle har ta iya yin sharhi a kansa?
Kanta ya daure, haka kawai ta ji tana son ganin wannan mutumin mai kiran nata. Inna ta ce "Mairo kuwa, wa ta sani a birni? Ga shi ka ce namiji ne balle ince ko diyan baffanta ne, je ka ce ba zata zo ba, haka kawai mutanen birnin nan ba abin yarda ba ne".
Ilu ya juya da gudu don isar da sako, Mairo ta mike ta jawo hijabinta a jikin kyaure tana cewa "Bari na je Inna, kika sani ko sako ne daga Yaya Habibu?"
Inna Hure ta ce, "Ai kuwa, maza je ki jiyo mana".
Ta fita tana dariyar Inna, ganin yadda ta rikice daga ambaton Habibu.
Tsaye yake jikin bishiyar maina, wadda ke gaba kadan da gidansu, sanye da kufta da wando na farin yadin boyel mai salki, kafarshi cikin rufaffen takalmi baki (cober) sumar kanshi kwance lub a kanshi, sai sheki yake. Eh, gaskiyar Ilu ne, yana yanayi da jinsin Larabawa sabida murdaddiyar suma ke gare shi irin tasu. Mamakinta da farin cikinta ya kasa boyuwa, bakinta ya kasa rufuwa. UNCLE JUNAIDU ne tsaye yau a kofar gidansu.
Ta kai hannuwanta biyu ta rufe bakinta ta kasa cewa komi. Shi kuwa murmushi ya yi, murmushin nan nasa mai aji da tsada da ba kowa yake yimawa ba. Ta bude baki a hankali ta ce "Uncle…….."
Sai kuma ta juya gida da gudu ta yayibo sabuwar tabarma ta shimfida masa a tsakar gidansu, Innar na ta tambayarta wane ne, amma ta kasa magana, ta komo ta ce "Inna debo ruwa mai sanyi, Inna Uncle Junaidu ne".
Ta fita da gudu ta shigo da shi. Lokacin Inna ta debo ruwa cikin kwanon sha mai tsafta, mai sanyi daga randarsu. Ta tsugunna daga can gefe suna gaisawa da Uncle tana ta yi masa godiyar dawainiyar da Mairo ta gaya masu yana yi da ita. Cikin girmamawa ya dukar da kai yana cewa "Babu komai Goggo. Maryam kanwa ce a gare ni".
Innar ta mike ta shige daki, ya dubi Mairo suka yi murmushi, sannan ta duka tana gayas da shi cikin ladabi. Sau tari tana jin nauyin Uncle Junaidu kasancewarsa malaminta, duk da shakuwa da amincin da ke tsakaninsu.
Ya ce "Zuwa na yi na ji shin sau nawa kika yi bita a tsawon hutunki, ko kuwa tunda kika shigo gida kika jingine jakar shi ke nan?"
Ta ce "Wallahi Uncle kullum da dare ina yin karatu, kuma ka tambayi Innata".
Ya ce "Shi ne kuma ranar hutu kikayi tahowarki ko ki neme ni in gaisa da Baba?"
Ta mike ta sa silifas tana cewa, "Jira ni in zaga gona in kira Baban, ya yi min shaida akan lokacin da na bata mishi ina nemanka".
Dariya ta ba shi sosai, yarinyar ta kan burge shi haka ta ke 'frank' komai da ke zuciyarta fade ta ke iyakar gaskiyarta. Ya ce "Dawo zauna abunki, barshi ya dawo da kansa kada ki katse masa aiki. Na yarda kin neme ni ba ki ganni ba, don ni kaina nasan na koma gida da wuri sabida ciwon Sagir, abin da ban yarda ba shi ne, ba ki yi kewata ba Maryam, don ga ki nan kin yi kiba abinki. Ni kuwa dubi yadda duk nabi na rame sabida kewarki". Yana fada yana taba kashin wuyansa wai yana nuna mata ramar.
Dariya ta yi, wadda ta fiddo jerarrun hakoranta farare kal, da siririyar wushiryarta. Ta ce "Allah Shi ne shaidana akan hakan. Babu ranar da zata fito ta fadi ban tunaka ba Uncle, ban kuma yi wa Inna da Baba tadinka ba. Idan ba ka yarda ba na kira Inna yanzu ka tambaye ta".
Ya kama baki "Ke kuma haka kike da son a yi miki shaida Maryama? Tunda kin ce Allah Shi ne shaida ai kin gama magana. Na yi kewarki Maryama yadda ba kya zato, nayi-nayi in bari kwanaki biyun nan su cika ki koma makaranta in ganki a can na kasa. Ban san mai yasa kika shiga raina har haka ba".
Kalamanshi sun yi mata tsauri, kuruciyarta ta fito a fili, cikin halin ko'in kula ta yi murmushi kawai ta ce "Ina Ilham? Wane irin ciwo ke damun Sagir?"
Ya ce "Ilham tana gaishe ki. Ga aike ma ta ce na kawo miki".
Ya zura hannu cikin aljihunshi ya fiddo wani abu kulle cikin leda. Ya mika mata ta amsa cikin jin dadi tana kuncewa, ya ce "Sagir sikila ce ke damunshi, tun yana yaro".
Ta ce, "Ayya Allah Sarki, Allah Ya ba shi lafiya".
Ga yadda ta lura Uncle na son 'yan uwansa kamar yadda ta ke son Yaya Habibu. Awarwaraye ne na silba sirara masu kyau guda shidda. Ta sanya a hannunta tana murmushi, ta ce "Ka ga Uncle sun yi min dai-dai, ka ce da Ilham na gode".
Shi dai kallonta kawai yake yi, shi kadai yasan abin da yake sakawa a zuciyarsa. Ba ta kula ba ta ke shaida mishi jibi da kanta zata dawo makaranta.
Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, kansa dauke da kullin hatsi, kafadarsa rataye da fartanya da lauje, su duka biyun suka mike suka karbe shi suna yi mishi sannu da zuwa. Ya bi bakuwar fuskar da kallo cikin mamaki, kamin ya tanka Mairo ta ce "Baba Uncle Junaidu ne".
Da sauri Malam Bedi ya mika masa hannu suka yi musabiha, sannan suka zauna a tabarmar da Mairo ta shimfidawa Junaidun suna kara gaisawa. Ya yaba kwarai da nutsuwar Uncle, haka kawai ya ji yaron ya shiga ransa. Ya yi masa godiya mai tarin

4 Comments On A BARI YA HUCE
avatar
fatimah-1

1 year ago

Reply

Pls book 2

avatar
shuraih99

1 year ago

Reply

Replying to fatimah-1

Tuntubi nambar nan 07030137870

avatar
hajara-muhammad

1 year ago

Reply

An interesting Novel

avatar
hajara-muhammad

1 year ago

Reply

An interesting Novel

Please Login or Register in order to submit comment