Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawa kan hidimar da Mairo ta gaya masu yana yi mata.
Ya ce "Don Allah ka kula min da karatun Mairo ko bayan raina, na baka amanar Mairo a wannan makarantar, ba ta da kowa sai Allah, Ba don alkawarin da na daukarwa Habibu ba, da bazan barta ta je ba".
Jikin Uncle ya yi sanyi matuka da kalaman Baban Mairo. Ya ce "Insha Allah Malam lafiya Maryama za ta gama karatunta ga dukkan alamu yarinya ce mai hazaka da nan gaba za a amfana da ita. Na dauki wannan amanar ta tsayawa akan karatunta iyakar karfina. Ku dinga yi mana addu'a".
Ya ce "Addu'a ga 'ya'yan musulmi duka muna yinta kullum. Sai dai daga yau JUNAIDU kana cikin addu'ata ta safe da dare, har zuwa ranar da na daina numfashi".
Uncle Junaidu bai bar kauyensu Mairo ba sai yamma lis. Ya tafi cike da tunanin Baban Mairo da tausayinsu. Bai san mai yasa yake jin tausayin Malam Bedin ba, bayan ba ya da hujja na yin haka, Tunda kuwa bai rasa ci ba, bai rasa sha ba, kai a fadin kauyen Gurin-Gawa ma yana daga cikin attajiran garin.
Manomi ne mai zuciyar neman na kansa, bai dogara da kowa ba. Baya kuma nema a hannun kowa. To ko Maryaman yake tausayi sabida iyayenta dattijai ne? Bai sani ba, abin da ya sani kawai shi ne, yana kaunar Maryam da iyayenta. Wannan amanar kuwa da ya daukarwa Malam Bedi, yana rokon Allah Ya ba shi ikon rike ta.

Litinin, Mairo ta yi shiri, tun da asubah Malam Bedi ya rakata tasha ya sata a mota sabida ta dage ita kadai zata dinga kai kanta tana dawo da kanta, don ta saukakawa Babanta. Kafin azahar tana cikin Minjibir, suka game da Nabilah suka gyare dakinsu suka durfafi karatu da kwarin gwiwar Uncle, da kulawarsa gare ta.
A karshen zangon sai ga Maryam Bedi da sakamakon (5th position), wato ta biyar a ajinsu. Ga yadda Uncle dinta ya ce da ita, wannan alama ce mai nuna wata rana zata fi hakan. Haka nan ita kadai ce ta fito da (80%) a darasin da ta fi so (Ingilishi). Sai dai a cewar 'yan ajinsu, ba wani nan, sama da fadi ne Junaid ya yi mata, kasancewarta 'yar gaban goshinsa. Amma ina za a ce wannan bakauyar ta fi su iya Turanci daga zuwanta a zangon baya? Koma dai me ye, Maryama ba sune a gabanta ba, burinta ta cimma burinta na cika alkawarin da ta kaukarwa Yayanta Habibu.
Kwanci tashi ba wuya wurin Allah Maryam da Nabilah suka zana jarrabawar wucewa babbar sakandire (SS.1), wato placement, suka fara shirin tahowa hutu. Sai dai kamin lokacin Maryama ke daukar na daya, Nabilah na biyu, ko Nabilah na daya Maryam na biyu.
Kamin kuma su zana jarrabawar nan ba haka Uncle ya barta ba, sai da ya tabbatar ya tusa mata karatu cikin kwanyar kanta ta yadda faduwa, sai wani babban ikon Allah.
Zuwa lokacin Maryama ta kara girma, matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha biyar. Zama da Nabilah ya sa Mairo tasan me ake kira 'gyara' na diya mace. Ta yi sharr ta yi 'fresh' jazur da ita. Kirjinta ya soma cika dagwas haka kirarta ta soma fitowa na alamun budurci. Gashin kanta ya mike baki sidik na Fulanin usuli sabida samun gyara. Duk wani abu da tasan zata yi amfani da shi a kantin makaranta ta ke saye ta tafi da shi gida, wasu abubuwan kuma daga Nabilah ta ke samu duk da ko yaushe cogewa ta ke da karbar abin hannun Nabilah, amma naci da mitar Nabilah ke sawa ta amsa wani zubin ko ta ki ko ta so, don ba zata barta ta zauna lafiya ba da korafi da mitar ba ta dauke ta ‘yar uwa yadda ta dauke ta ba.
Suka kare jarrabawa ta dawo gida inda ta tarar da tashin hankalin da ba ta taba haduwa da shi ba a rayuwarta. Malam Beddi ya fadi a gona rabin jikinsa ya mutu (paralysed), sai dai a kwantas a tayar.

Mairo ta yi ta kuka kamar ranta zai fita, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a rayuwarta. Daga kwancen da yake Malam Bedi, ya miko hannun shi mai lafiyar ya kamo hannunta yana dan girgizawa alamun lallashi. Mairo ta soma damuwa kwarai da rashin zuwan Habibu, tana tunanin da yana nan, da tuni ya kai Babansu asibiti, shekaru biyar curr ba aike ba sako, anya kuwa Yaya Habibu bai manta da su ba?
Daga ranar ta ajiye komi ta shiga taya Innarta jinyar Baban. Ita ce ke ba shi abinci safe, rana da kuma dare. Ita ke yi masa alwala ta fuskantar da shi alkibla, yayin da Innar ke kula da tsaftar jikinsa da dahuwar abinci. Maganar makaranta Mairo ta ajiye ta a gefe, ba ta jin tana da ranar komawa har sai Allah Ya baiwa Baba sauki. Duk da shelar da ake ta yi a rediyo na cewa, a koma.
A karshen watan Allah ya jefo Alhaji Abbas ya tarar da halin da dan uwansa ke ciki, ya yi ta yi wa Hure fada kamar ya doke ta ya ce, mai yasa ko da kanta ba zata je ta fada masa ba? Da dan uwansa ya mutu cikin wannan halin da ba zai yafe mata ba.
Ya debo su duka a motarsa suka taho asibitin Murtala a Kano, aka ba su gado. Nan aka ci gaba da bai wa Malam Bedi kulawa ta masu lalura irin tasa 'Physiothearaphy'. Har zuwa watanni biyu, babu wani canji ko hannunsa ba ya iya motsawa.
Mairo cikin asibitin ta zama 'yar gari ba inda ba ta shiga. Rannan Malam Bedi ya bude baki ya yi magana, ita da Hure suka matsa sosai cikin tsananin murna, suka kasa kunne don jin abin da zai fada. Babu abin da ya ke ambato sai, "Habibu... ku kirawo min Habibu".
Dukkansu babu abin cewa, dai-dai lokacin da Ladidi daya daga cikin 'ya'yan Alhaji Abbas ta shigo dauke da kwanukan abincinsu. Tana yatsina ta ajewa Innar kwanukan babu ina wuni, balle ya mai jiki. Ta juya zata fita, wannan al'adar 'ya'yan Alhaji Abbas ce ga su Hure, tun zuwansu asibitin don ba su ga dalilin da Alhajinsu zai damu da wadannan shirgin kauyen ba akan wannan gawa-ta-ki-ramin Bedin, shi a wahale su a wahale. Kullum dare da rana ana aikensu kawo abinci, tun daga Yakasai suke takowa a kasa har zuwa asibitin. Yanzu kam yaran har buyarwa iyayensu suke idan lokacin kwashe abincin ya yi a neme su sama da kasa a rasa, wani lokacin sai shi Alhajin ne ke kawowa da kansa.
Har ta kai bakin kofa sannan ta juyo ta ce "Ke Mairo, tare muke da wani mutum wai yana nemanki, Baba ne ya hado ni da shi na nuna masa ku".
Ta ce "Yana ina?"
Ladidi ta ce "Ga shi can a kofar shigowa ward din nan". Ta kada kai ta fita abinta.
Mairo ta sanya gyale ta fito tana dube-dube, sai ji ta yi cikin taushin murya mai cike da damuwa an ce "Sannunki Maryam, kin kyauta".
Ta daga idanunta a hankali ta dube shi cikin mamaki, Uncle Junaidu ne, rungume da hannayenshi a kirji, kafarshi ta dama jingine da bango, ya yi rama ainun cikin riga da wando na yadin siliki.
Suka zubawa juna ido na 'yan dakikai, kamin ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba, suna diga kan tafin kafarta. Uncle ya kula, ya ce "Ni ne ya kamata na yi kuka ba ke ba. Ni da kika bari cikin zullumi da yawon nemanki kusufa-kusufa. Idan har yanzu ba ki yi hankalin da za ki damu da damuwar masu kaunarki akan ki ba, sai yaushe ne Mariama? Watanni uku Baba ba lafiya ba ki neme ni kin sanar da ni ba, ba ki sanar da hukumar makaranta uzurinki ba. Na raina wayonki Mariama, kin bata min sosai, amma hakan da kika yi ya taimaka min wurin gano matsayin da kika ba ni a zuciyarki. Na gane ba ni da wani muhimmanci, ni kadai na…...."
Muryarshi ta sarke sabida takaici, ya wuceta ya shiga ciki yana raba ido a cikin ward din, har ya hango Inna Hure tana yi wa Malam firfita. Da sauri ya karasa ya rungume dattijon hawaye na fita mishi tararara! Bedi ya mika hannunshi mai lafiyar yana shafar kanshi, ya ce, "Habibu...."
Ya zube a gabanshi ya kamo hannunshi ya rike tamau cikin nasa kai ka ce mahaifinsa ne. Ya ce "Baba ba Habibu ba ne, Junaidu ne, Baba Allah Ya ba ka lafiya".
Jikinshi na mazari da karkarwa ya ce, "Junaidun-Mairo?"
Ya ce "Shi ne Baba".
Ya kama hannunshi da nashi hannun mai karkarwa ya ce "Ina Mairo?"
Mairo da ke rakube a gefe tana rasgar kuka maras dalili, ta karaso ta ce "Ga ni Baba".
Ya ce "Miko min hannunki".
Cike da fargabar abin da Baban ke shirin yi, ta daura hannunta na dama akan nashi. Ya zare nashi, nata ya sauka akan na Junaidu, ya kama su duka biyun ya dunkule ya ce "Na ba ka amanar Mairo, ka rike min ita amana kar ka bari a raba ta da mahaifiyarta. Idan Habibu ya dawo ka damka masa ita, shi kadai na yarda ya rike min Mairo sai uwarta, kai kuwa dama amanata da kai…. ita ce karatunta……."
Ya zare hannunshi ya yi shiru.
Jikinsa ya mace murus, daga shi har Mairo an rasa wanda zaiyi jarumtakar fara dauke hannunsa. Ita kuwa Hure tana gefe akan tabarma tana ta sharar hawaye, ya yi ta maza ya zare hannunsa cikin karfin hali ya ce "Baba Allah zai ba ka lafiya. Da yardar Allah kai zaka ci gaba da rikon Maironka, har ka daura mata AURE".
Haka suka kasance har dare, jikin Malam ya ki dadi.
Bayan sallar isha'i Junaidu ya tafi gida da alkawarin gobe da sassafe zai zo ya nema masu (transfer) zuwa asibitin Aminu Kano.
Da asubahin ranar Hure ta tashi ta ciko ruwa a buta ta dauko roba ta zo da niyyar yi wa Bedin alwala.
Allahu Akbar ashe Allah Ya amshi abinSa cikin dare. Ta ja mayafi ta rufe masa ido ta yi alwala tana hawaye ta tada kabbarar sallah. Mairo ta tashi daga kan tabarmar da ta ke kwance ita ma ta yo alwalarta ta tada sallah. Da ta idar ta juya tana gayas da Inna, a nan ta lura Innar lazimi ta ke tana kuka. Sai ta ja gefe ita ma ta soma kukan da ba tasan dalilinsa ba.

Gari ya yi dan shaaa! Haka, Misalin karfe shidda da rabi na safe, Junaidu ya iso biye da shi, Ilham ce rike da filas din ruwan zafi da filas din abinci. Shi kuma niki-niki da ledoji ya rusuna yana gayas da Inna, tare da tambayarta lafiyar mai jiki. Ta daure ta ce "Ka taimaka ka je gidan nan na Yakasai, inda idan aka rakoka nan, ka fadawa maigidan ya zo ya dauki gawar dan uwansa a yi masa suttura".
A firgice Junaidu da Mairo suka dago, kamin dukkansu su karasa ga gadon Malam Bedi. Mairo ta sa hannu ta yane zanin da Inna ta rufe shi da shi. Ta tabbatarwa kanta Innar ba wasa ta ke ba, sai ta sulale a kasa ita ma babu alamun numfashi a tare da ita.

*** ***

U
ncle Junaidu ya yi mata halarcin da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. Tare da shi aka yi ta zaman makoki har tsayin kwanaki bakwai, mahaifiyarshi da kannenshi duka ya kawo su sun yi wa Inna Hure gaisuwa. Ranar da aka yi sadakar bakwai ya tura aka kira masa Mairo azure, ya kara yi mata ta'aziyya, ya kara da nasihu masu sanyaya rai da karfafa gwiwa. Ya ce ta daure sati mai zuwa ta dawo makaranta har zangon ya yi nisa ba tareda ita ba.
Ta rantse masa zata dawo amma tana tausayin Innarta, yadda zata barta cikin kewa. Ya ce "Wata rana aure zaki yi Maryama, ke da Inna sai gani da yawo, ita kanta tasan hakan. Don haka ki taimake ni in rike nauyin da marigayi ya aza mani akan karatunki".
Bayan tafiyarsa Mairo da Innarta idan ka gansu gwanin ban tausayi. Tunanin Mairo shi ne, wa zai dinga nomawa Innarta abin da zata ci? Idan wanda ke cikin rumbunsu ya kare? Allah maji kan bawa, washegari sai ga Alhaji Abbas niki-niki da kayan abinci ya kawo musu. Ya kuma ce, wannan nauyin ya dauke shi insha Allahu. Sai a nan hankalin Mairo ya dan kwanta duk da Innar ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Shi ma Alhajin ya yi mata zancen makaranta ta ce, insha Allah karshen wannan satin zata koma.
Hakan kuwa aka yi, ranar litinin ta yi shiri ta koma makaranta. Nabilah ta yi mata ta'aziyyar babanta wanda ta ji a bakin Uncle Junaidu.
Rayuwar Mairo ta sauya kwarai, ta zama babu walwala, akwai shakuwa da kauna mai tsanani tsakaninta da mahaifinta, don haka ta ke jin kanta tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai ta samu kanta da son yin abin da zai debe mata kewa, don haka ta fara tunanin yin RUBUTU.
Tana yi tana gutsirewa ta ajiye, idan ta ji bai yi mata ba. Kamar da wasa, ta fara rubutun labarai cikin harshen Turanci a kalla guda biyar tana yagawa. Lokacin da ta shiga aji biyar na babbar sakandire aka ba ta kallabin 'AMIRA' sabida hidimarta ga masallaci da kungiyar dalibai musulmai da Uncle Junaid ya sa ta. Haka nan ita ce ja gaba a club din Uncle, watau English club.
Kowa yasan Uncle Junaid a Minjibir, yasan shi tare da Maryam Bedi. Mairo ce mai rubutawa club din DRAMA Uncle ya yi gyara a gabatar da ita. Wannan wata hikima ce da Allah Ya yi mata wadda ke bai wa kowa mamaki. Sai dai iyaka kwakkwafinka da sa ido, haka nan so kulla karya da sharri, ba zaka ce akwai soyayya tsakanin Junaid da Mairo ba, sai mutunta juna.

A wannan hutun na zangonsu na biyun karshe a sakandire da Mairo ta zo gida. Ta tarar da ciwon kafar Inna ya yi tsanani. Ko bayan gida ba ta iya takawa sai dai ta ajiye (foo) a kusa da ita. Don haka Mairo ta kara kadewa ta rame, ta kuma soma tunanin jingine makaranta domin Innarta, tun tana tunanin Habibu har ta watsar ta hakura da shi, shi da ya ce shekaru shidda kacal zai yi.
Ta tabbata inda duk Habibu ya ke tunda ya iya ya yi shekaru takwas bai neme su ba, to babu shakka ya manta da su, ya samu sabuwar rayuwa a gaba. Ba zata taba amincewa da cewa wani mugun al'amari ne ya faru da shi ba, tunda kuwa lafiya ita ke buya, amma ba rashinta ba.
Cikin watan January ne sanyi ya yi tsanani, hazo ya mamaye sararin samaniya, wanda duk ya yi kuskuren fita babu shakka gashin ido dana girarsa fari fat za su koma. Mairo ta dawo daga wani chemist inda ta amsowa Inna maganin mura tana tafe yafe da mayafin gyauton atamfa, ta dunkule hannuwanta wuri guda.Tana ta sauri domin ta daura dafa-dukar taliya akan wuta, wadda zata bai wa Innar, kasancewar ba komi ta ke iya ci ba, sai abu mai laushi, kuma mai dan ruwa-ruwa, duka Mairo na kokari a kai. Ta kada ta raya da Innar ta kai ta asibiti, amma Innar ta ki, ta ce, ciwon kafa ba a kanta tsoffi suka fara shi ba.
Ta doso zauren gidansu ke nan ta hange shi, tsaye a kofar gidansu. Sanye yake da farar shirt (Armani) da dogon bakin wandon jeans ya daura jibgegiyar rigar sanyi mai hade da hula bisa. Duk hazo ya ba ta tsararren gashin idonsa, girarsa da sajensa. Mairo ta ce a ranta, Allah Sarki Uncle! Cikin wannan sanyin ya taho tun daga Minjibir sabida rashin komawata makaranta.
Tun daga nesa ta ke yi masa murmushi amma shi fushi yake sosai. Ta kariso cikin nutsuwa, tana karasowa ta russuna tana gayas da shi ya ce "Ni bana son wata gaisuwarki, kawai shiga ciki ki hado kayanki ki zo mu tafi".
Ta girgiza kai kamin ta wuce cikin gidan ya bi ta a baya. Ta fara da sauke tukunyar daga kan wuta, kana suka karasa dakin Innan da sallama. Shi kansa ya girgiza da ganin ramar da Innar ta yi, tana kwance bisa katifar auduga ta amsa sallamar su. Nan ya gano amsarsa ta rashin komowar Mairo makaranta.
Jikinsa ya yi sanyi, ya daga manyan idanunsa ya dube ta suka yi wa juna kuri da ido.

Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A yanzu kam ji ta ke ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da Alhaji Abbas na iya kokarinshi akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan cikin matsananciyar damuwa, ya ce "Sannunku da jiki Inna, amma ya dace ki daure yanzun nan mu tafi asibiti".
Ta ce "Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai likitan da ya isa ya raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!"
Ya ce "Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya saukar dashi tare da maganinsa ba".
Ta ce "Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru…….."
Cikin matsananciyar damuwa ya ce "Wane abu ne kike gudu Inna?"
Ta ce
"Zaman Mairo da Iyalan Abbas". Daga haka ta yi shiru.

Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji Abbas, abin kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani boyayyen abun don yadda ba ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma.
Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar ba ta taba zuwa ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin irin maganganun da Innan ke yi a kullum suna kara tayar mata da hankali.
Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan gidan su ne. Ya dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya ba Junaidu.
Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban dakin shan magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa Innan allura.
Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata alhamis da daddare suna kwance ta ce "Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba, da na ce Junaidu YA AURE KI".

Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce "Inna ke ko mai yasa kika yi wannan tunanin?
Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani na daban ko ya ya game da shi a zuciyata.
Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin wannan, sai mutunta juna".
Inna ta yi murmushi ta ce "Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba ganin inda namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare na sunsunar takalmi, wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki gaskiya na hango miki abin da ke ba ki hango ba, cikin kwayar idon Junaidu.
Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai cikin kwayar idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan, amma kina son Junaidu. Adadin soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa. To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce ba ki ambace shi ba?
Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike ki da kauna ta gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun. Duk runtsi, duk wahala da tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki jira LOKACI ya fada miki……."
Cikin gundura da zancen ta ce "Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki ce wai ya aure ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da ita? Ni kam gare ni har gobe Uncle Junaidu Yayana ne".
Inna ta yi murmushi ta ce "Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina hango inda za a alkinta min ke".
Ta ce (kamar ta yi kuka), "Ni dai don Allah Inna ki bari……..".
Ta ce "Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki Junaidu na sonki, tun ba ki mallaki hankalin kanki ba".
Ta yi narai-narai da fuska, ta ce "Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?"
Ta ce "Na bari".

Ashe karshen hirar tasu ke nan. Inna Hure ta tako da asubahi cikin dafa bango domin yin alwala, ta zo gittawa ta gefen da rijiyarsu ta ke, santsin cabalbalin gindin rijiyar ya kwashe ta ga kafafun babu karfi, ta zame ta baya sai ji kake cindummmm….! Ta fada rijiyar ita da butar da ke hannunta.
Mairo wadda ba ta yi barci ba tun daren jiya, tana tunanin zancen Inna akan Uncle Junaidu, ta kasa yakice al'amarin a zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da fatan ina ma ace zancen Inna ya tabbata gaskiya? Uncle Junaidu ya so ta? Ita kuwa da wace irin sa'a zata yi a rayuwarta?
A farkon shekatun karatunta ba ta tantance wane ne Junaid ba, sai da girma da hankali suka fara game mata jiki.
Uncle Junaidu na daya daga cikin irin mazan da suka yi karanci a wannan zamanin. Ta fannin sura, halayya da kyawawan dabi'u.
Ta kasance ma'abociyar karance-karancen littattafan nobels' na Turanci. Littattafan Shakespear, Wole Soyinka, Zainab Alkali, Abubakar Gimba, Ama Ata Aidoo da mabiyansu babu wanda bata karanta ba. A duk lokacin da ta ke karatun, takan rasa dalilin da yasa ta ke danganta al'amarin jaruman littafin da Uncle da ita kanta. Ba tasan dalilin da yasa a duk lokacin da aka ambaci managarcin mutum mai kyawun sura ta ke cewa cikin ranta, "Kaman Uncle Junaidu".
Eh, Junaidu kyakkyawa ne, ma'abocin kwarjini, zati da kamala, wanda kwata-kwata bai dace da matsayin da yake kai ba, wato malamin makaranta. Saidai da yake ance (ra’ayi riga ne)
Mutum ne da yasan mene ne 'dressing' wanda kuma kowanne irin kaya ke karbarsa, su dace da da zubin halittarsa. Kai kace don shikadai aka kirkiresu. Junaidu idan ya shigo waje dole kasan ya shigo, sabida kwarjininsa da cikar zati. Yana da fara'a amma yana da zucciya, abu kadan sai ya bata mishi rai, haka abu kadan zaka yi ya wanke laifinka nan take daga zuciyar shi. Ba ta san me yasa ba, komai Uncle ya yi burge ta yake koda kuwa ace fada ne yake mata. Ta sha tambayar kanta, anya za a samu mutum mai kirkin Junaidu? Ta taba ce da Nabilah matar duk da Uncle ya aura ta caba.
Nabilah ta ce "Dalili?"
Sai ta dauko mata littafin da ke boye a bayanta, GENDER STUDIES (wani bangare ne na sociology mai banbance jinsin maza da mata). Shafin da aka fasalta halittar maza masu gamsar da diya mace a shimfida, kuma irin mazan da matansu ba sa iya rabuwa da su komi wulakancin da zasu yi masu. Tana jan layi-bayan-layi tana fassarawa Nabilah.
Ta kare tana murmushi, ta ce "Edactly Uncle ko?"
Nabilah ta kama baki cikin mamaki, ita karance-karancen Maryam ya fara ba ta tsoro. Yadda ta nakalci harshen Turanci ko goyon Birtaniya dole ya sara mata. Ta ce "Ke dai wallahi shegen karance-karancenki sai ya lalataki. Yanzu ina ke ina littafin 'yan jami'a? Tukunna ma ina kika samo shi?"
Ta yi dariya cikin nishadi ta ce "A wurin Uncle na dauke rannan daya aikeni in kai mishi littattafi staff-room na ganshi cikin lokarsa shi ma bai sani ba na dauke".
Nabilah ta ce "To wallahi ki bar karanta sociology za ki hauka ce".
Maryam ta ce "Da

4 Comments On A BARI YA HUCE
avatar
fatimah-1

1 year ago

Reply

Pls book 2

avatar
shuraih99

1 year ago

Reply

Replying to fatimah-1

Tuntubi nambar nan 07030137870

avatar
hajara-muhammad

1 year ago

Reply

An interesting Novel

avatar
hajara-muhammad

1 year ago

Reply

An interesting Novel

Please Login or Register in order to submit comment