Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kadan aka iso birnin Misra. Ana shiga cikin turakar Gimbiya Lamirat aka kwantar da ita, jim kadan sai ga shi ta farka.
Tana bude idanunta tayi arba da dakaru masu yawa tsaye a gabanta, gashi a lokacin kwata-kwata bata jin karfin jikinta sakamakon wannan magani da aka shayar da ita nasa barci, duk da haka sai da ta yunkura da nufin ta tarwatsasu amma kuma sai suka danneta da karfin tsiya, suka sa sarkoki suka daure mata hannayenta da kafafunta.
A sannan sarkin yaki ya dubeta ya ce, ki gafarcemu ya shugabata sarki ne ya umarcemu da mu daurewa kuma mu tsareki anan cikin turakarki don baya son ki koma can birnin Misra har sai an gama gasar kambun jarumta.
Gimbiya Lamirat ta kalli sarkin yaki sannan ta ce da shi, shin tsawon kwana nawa nayi a ckin akwatin gawa ina barci?
Ko da jin wannan tambaya sai mamaki ya kama sarkin yaki ya dubeta ya ce, ya shugabata wai dama kin sani cewa an baki maganin barci kin sha ne, kuma ya akayi kika san cewa an saki a cikin akwatin gawa alhalin ba a saki a cikin akwatin ba sai bayan da kika sha maganin barci sannan aka saki?
Ko da jin wannan tarmbaya sai Gimbiya Lamirat ta bushe da dariya sannan ta ce, ai nice na shirya duk yadda za ayi a fitar da ni daga cikin birnin na Misra, saboda kowa ya yarda cewa na mutu, ina mai tabbatar maka da cewa dole ne na koma birmin Misra saboda kwararan dalilai guda biyu. Dalili na farko shine dole ne naje naga lmhal saboda na kamu da tsannain son sa a Zuciyata, idan har banje naga halin da yake ciki ba zan iya rasa lafiyata da rayuwata ma gaba daya. Dalili na biyu kuma shi ne zuciyata tana ta bugawa da karfi gadke bisa rashin sanin halin da mahaifina ke ciki a yanzu da kuma abin da zai iya faruwa nan gaba gareshi a cikin wannan gasa ta kambun jarumta.
Hakika Ina son jarumi Imhal kuma ina son mahaifina, ko kadan bana son na rasa daya daga cikinsu, kuma a yanzu ne nayi nadama tare da tsananin bakin ciki bisa yadda mahaifina ya tsananta gaba akan jarumi Imhal wacce ban san dalilinta da kuma asalinta ba.
Ko da gimbiya Lamirat ta zo nan a zancenta sai hawyaen takaici ya zubo mata, al'amarin da ya sa zuciyar sarkin yaki ta karaya kenan kuma ya kamu da tsananin tausayinta, sannan hankalinsa ya dugunzuma ainun ya sunkuyi da kansa kas a lokacin da ya ji wani irin tsananin takaici ya rufeshi kuma kwalla ta cika cikin idanunsa.
Ashe gimbiya Lamrita ta lura da cikar kwallar a idanun sa don haka sai ta kamu da mamaki gami da zargi, ta dubeshi cikin yanayi mai nuna rashin yadda ta ce ya kai sarkin yaki shin kasan wani abu ne dangane da asalin gabar da ke tsakanin jarumi Imhal da mahaifina?
Ko da jin wannan tambaya sai sarkin yaki ya sake sunki da kansa kas ya budi baki cikin rawar murya da sauri ya ce ya shugabata ban san komai ba.
Cikin tsawa Lamirat tari tsawa numfashinsa ta ce, akwai alamun rashin gaskiya a cikin muryarka, a yanzu kuma akwai alamun cewa akwai wani babban sirri da kake boye mini. To kayi sani cewa nan gaba idan na gano wannan sirri ba zan yafe maka ba, kuma sai ka zamo babban makiyi a gareni.
Ko da jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya bai san sa'adda hawaye ya zubo masa ba, kawai sai ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa ya dakawa sauran dakarun dake bayansa tsawa ya koresu daga cikin tantin. Suna gama fita gaba dayansu sai sarkin yaki ya fashe da matsanancin kuka.
Al'amarin da ya yi matukar girgiza gimbiya Lamirat kenan ta dubeshi ta ce, ya kai sarkin yaki ina dalilin wannan kuka naka?
Sarkin yaki ya dago kai ya dubi Gimbiya Lamirat a lokacin da hawaye ya ci gaba da shatata bisa kumatunsa ya ce, ranki ya dade na aikata wani babban aiki na cin amana a gidan sarautar nan wanda shi ne asalin kiyayyar mahaifinki da wannan yaro Imhal. Sarkin da ya yi sarauta kafin mahaifinki dan uwan mahaifinki ne ubansu daya kuma shi ne ainihin mahaifin jarumi Imhal.
Ko da jin wannan batu sai idanun Gimbiya Lamirat suka zazzaro ta cika da tsananin mamaki kuma jikinta ya kama tsuma.
Sarkin yaki ya ci gaba da cewa, mahaifinki ne ya kashe mahaifin Imhal da hannunsa ya caka masa wuka a ciki, ni kuma ni ne na yanka mahaifiyar Imhal, yankan rago kuma muka kashe duk iyalinsa saboda kawai mu karbe karagar mulki daga hannunsu. Mace daya ce daga cikin dangin mahaifiyar Imhal ba mu kashe ba ana kiranta da suna Muzaira, kuma itama mun bita da gudu ta fada daji muka nemeta sama da kasa muka rasa. Bayan mun kai gawar mahaifiyar Imhal daji a cikin keken doki mun yar da kimanin shekaru ashirin da biyar ne bokan mahaifinki ya gano cewa ashe ba ta mutu ba wani dattijo mai suna Imzanu ya ceci rayuwarta har ta haife shi. A wannan rana ne muka shiga cikin daji domin farautar tsoho Imzanu da Imhal amma ba mu sami nasarar kashe tsoho Imzanu ba, sai jarumi Imhal muka kama da kyar bayan ya tsere mana ya fito a cikin wani kogi dake bayan gari. Nan take muka sumar da shi muka kaishi kurkukun sarki inda aka sashi a cikin rijiya gaba dubu aka yi masa azabobin cikinta.
Rijiyar da a tarihin wanzuwar ta babu wani mahalukin da ya taba dandana azabobin cikinta ya rayu sai jarumi Imhal.
Ko da sarkin yaki ya zo nan a.zancensa sai gimbiya Lamirat ta daka masa tsawa ya yi shiru sannan ta fashe da matsanancin kuka na bakin ciki ta ce tabbas mahaifina ya cika babban azzalumi kuma maci amana. Yanzu ashe jarumi Imhal danuwana ne na jini amma ban sani ba, har aka rabani da shi tsawon shekara da shekaru, na taso ni kadai a cikin gidan sarautar nan babu dan uwa? Ai kuwa yanzu ne ma zan kafa tubalin soyayyata a gareshi kuma ta kowane hali sai na taimakeshi na sanar da shi cin amanar da mahaifina ya masa. Daga yau na tsani sarki kuma ba ni ba shi har abada.
Ko da gama fadin hakan sai Gimbiya Lamirat ta bugawa sarkin yaki goshinta da karfi akan fuskarta. Saboda karfin dukan sai da ya baje a kasa wanwar a lokacin da jini yayi tsartuwa daga cikin hancinsa ya dimauce.
Kafin ya dawo cikin haiyacinsa ta tsinka sarkar da aka daure hannayenta da karfin damtsenta saboda kasanewarta basadaukiya.
Cikin zafin nama ta sake tsinke sarkokin da aka daure kafafunta sannan ta zare takobi a jikin sarkin yaki ta ruga waje da gudu ta afkawa dakarun dake tsaron turakarta, ta hausu da sara da suka tana samarwa kanta hanya da karfin tsiya, sannan tana ci gaba da gudu.
Lokacin da Gimbiya Lamirat ta tarwatsa dakarun dake kofar turakarta da karfin tsiya ta samarwa kanta hanya tana gudu sai suka ci gaba da yi mata rubdugu suna shan gabanta domin su tsaida ita su kamata amma sai abu ya
gagara.
Kafin su ankara ta iso inda bargar dawakai take na gidan sarautar. A daidai wannan lokaci ne sarkin yaki ya iso wajen aguje rike da takobi jini na diga a kan hancinsa.
Ko da ya hango gimbiya Lamirat ta nufi bargar dawakai sai shima ya falfala da gudu domin ya shawo kanta ya hanata shiga cikin bargar dawakan saboda ya gane manufarta, kawai so take ta hau doki ta gudu.
A daidai wannan lokaci ne sauran dakaru gidan sarautar suka rinka tururuwar rugowa izuwa kan gimbiya.
Ko da taga cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma lallai idan ba ta yi dabara ba zasu iya kamu sai ta daka tsalle sama ta ci gaba da gudu tana taka kawunan dakarun, su kuma suna kaiwa kafafunta cakfa, amma saboda zafin namanta sai suka kasa dankarta, tana dira akan rufin dakin da dawakan suke sai ga sarkin yaki ma ya dira akan rufin ya sha gabanta ya na mai ritsata, kawai sai ta dubeshi tayi murmushi ta ce, ai dama na gaya maka ba za ku iya hanani ida nufina ba. Kauce ka bani wuri idan baka son lafiyarta ta tabu.
Sarkin yaki ya girgiza kai ya ce, da dai na sabawa mahaifinki gwara na rasa rayuwata ma saboda ban san irin rashin imanin da zai yi mini ba.
Kafin sarkin yaki ya gama rufe bakinsa tuni gimbiya Lamirat ta kawo masa wawan sara a kafada. Cikin zafin nama ya kare saran amma saboda karfin saran sai da takobin ta dan shafi saman kafadarsa ta yankeshi kadan.
Nan fa suka kacame da azababben yaki akan rufin ginin dakin dawakan. Su kuwa sauran dakarun sai suka daga kawunansu sama kawai suna kallonsu saboda a cikinsu babu wanda zai iya daka tsalle ya haye kan saman saboda tsawonsa yayi yawa.
Da yake shima sarkin yaki gwarzon jarumi ne sai ya ci gaba da 6atawa Gimbiya Lamirat lokaci kuma ya hanata samun damar rugawa izuwa kan wani rufin ginin.
Ko da ta fahimci cewar idan fa aka dada bata lokaci komai zai ya faruwa, ma'ana za a iya amfani da wata dabarar ta yaki a kamata. Ko da gama aiyana hakan a zuciyarta sai ta sake shammatar sarkin yaki ta daka tsalle sama ta doki kirjinsa da kafafunta biyu kuma da dukkan karfin ta. Saboda karfin dukan sai da ya yi tsale sama da baya tamkar an janyeshi da Inajajjawa ya fada can kan wani rufin gini dake nesa. Ko da gadon bayansa ya bugu da rufin ginin sai ya baje a kansa sumamnme.
Ko da ganin haka sai farin ciki ya kasa kama Gimbiya Lamirat ta ruga cikin tsakiyar dakarun tana mai nunasu da tsinin takobinta, ta bude baki ta ce duk wanda ya sake ya kusantoni to a bakacin ransa.
Ko da jin wannan batu sai gabadayan dakarun suka fara buda mata hanya ta wuce zuwa cikin bargar dawakan, tana tafiya tana waigensu gudun kada su kawo mata farmakin bazata.
A haka har ta karasa inda dokinta yake wani ingarman dokine, ta karasa wajen ta dubi mai kula da barga dawakan ta daka masa tsawa, tare da umartarshi da ya yi sauri ya daurawa dokin siddi. Cikin rawar jiki kuwa ya dauko siddi ya daurawa dokin.
Nan take Lamirat ta daka tsalle sama ta haye dokin ta zabure shi da gudu ta tsakiyar dakarun tana bangajesu. Maimakon ta bi ta kofar gidan sarautar sai ta nufi doguwar katangar gidan. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda dokin nata ya durfafi katangar kai tsaye ba tare da shakkar komai ba duk da cewa tsawon katangar ya ninka nasa sau biyar.

TopA Nima A nan zan dakata kuma sai wani lokaci insha Allah

Karku manta zaku iya Samun mu a wadannan shafukan sadarwa kamar haka

PAGE https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295

PAGE
https://www.facebook.com/AlaminGuyson

A WhatsApp group dinmu ta hanyar danna wannan rubutun dake kasa
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

Saikun Zo

Domin shiga WhatsApp group dinmu saiku wannan blue din rubutun
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

AA Misau ke Magana



RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Biyar (5)
Part C

Na Abdulaziz Sani M Gini
Labari Ya Isowa Shagala Cewa πŸ₯°
Marubucin Yaci gaba Da cewa

Nan take Lamirat ta daka tsalle sama ta haye dokin ta zabure shi da gudu ta tsakiyar dakarun tana bangajesu. Maimakon ta bi ta kofar gidan sarautar sai ta nufi doguwar katangar gidan. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda dokin nata ya durfafi katangar kai tsaye ba tare da shakkar komai ba duk da cewa tsawon katangar ya ninka nasa sau biyar.
Su kansu gaba dayan hadiman gidan sarautar da dakaru sai suka fara
kyalkyala dariyar mugunta ga Gimbiya Lamirat saboda ganin wautar da take shirin yi. Su dai sun san cewa dokinta ba zai iya fasa katangar ba ya wuce bare kuma har ya iya tsallaketa sai dai idan fuka-fukai zai yi.
A daidai wannan lokaci ne sarkin yaki ya farfado daga suman da yayi ya mike zaune zumbur akan saman wannan rufin yana mai dafe kirjinsa gami da tari. Ko da ya hango Lamirat bisa doki a sukwane ta durfafi katangar gidan sarautar sai ya kama kyalkyala dariyar murna don ya tabbatar da cewa babu yadda za a yi ta tsira.
Cikin hanzari ya duro kasa ya falfala da gudu yana mai yiwa dakarun dake kan katanga inkiyar su jefawa gimbiya Lamirat raga ta lullu6eta.
A wannan lokaci saura taku bakwai kacal tsakanin kafar dokin Lamirat da katangar gidan sarautar kuma a sannan ne dakarun suka jehowa Lamirat ragar amma sai dokin ya daka tsalle sama ya bar kan kasa gaba daya tamkar cilloshi akayi daga cikin baka, ragar ta zubo a bayansa, kawai sai gani akayi dokin ya shallake katangar gaba daya tamkar aikin sihiri.
Nan fa kowa ya kame tamkar an zare musu ruhin halitta, shi kansa sarkin yaki kuwa bai san sa'adda ya yi turjiya ba ya tsaya cak a waje daya yana mai wangame bakinsa saboda tsananin mamaki.
Dokin Lamirat na dira a wajen gidan sarautar sai ta ci gaba da yi masa kaimi yana falfalawa da azababben gudu babu sassauci.
Bata saurara ba har sai da taga tayi nisa ga barin cikin gari ta yi nisa sosai a cikin daji, a sannan ne hankalinta ya kwanta ta sami yar nutsuwa.
Kawai sai ta tuno da cewa to ai ko guzuri ma bata nema ba gashi kuma tafiya ce ta kwanaki a gabanta kafin ta isa birnin Misra, amma da ta tuna cewa ita fa jaruma ce wacce ta yarda da kanta zata iya rayuwa a ko ina. Nan take sai fuskarta ta fadΔ‘ada da murmushi ta ci gaba da tafiya cikin
nutsuwa da farin ciki. Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Kisra bayan an kawo gimbiya Lamirat a matsayin gawa cikin akwati.

********** ************ **************

A can birnin Misra kuwa bayan wadannan dakarun sumame masu bakaken kaya sun bar dajin da suka tare gawar gimbiya Lamirat sai suka rarrabu kowa ya kama gabansa, shugabansu ne kawai ya durfafi hanyar cikin gari kuma shima sai da ya yi kewaye kewaye na bagararwa sannan ya sauya tufafinsa ya yi shiga ta kamala sannan ya durfafi gidan sarauta.
Yana isa gidan sarautar aka bude masa kofa ya kunna kai ba tare da an tuhumeshi ba. Nan dai ya ci gaba da tafiya abinsa tamkar cikin gidansa yake shiga, duk kofar da yaje ya iske dakaru sai dai kaga sun risina a gareshi sun yi gaisuwa.
Haka dai ya ci gaba da tafiya babu mai yi masa shamaki har sai da ya kai cikin wani daki na musamman wanda sarki Taryan ke ganawa da amintattun hadimansa.
Yana shiga cikin dakin ya iske sarki Taryan shi kadai jal a cikin dakin tsaye yana kai kawo cikin alamu tsakanin damuwa.
Ko da suka yi arba da juna sai sarki Taryan ya taryeshi da sauri yana mai rike kafadunsa ya ce ya kai Barwal menene labari?
Cikin alamun karayar zuciya Barwal ya gyada kai kuma ya risinar da kansa kas ya ce ya shugabana na duba gawar gimbiya Lamrita da kyau amma ko kadan babu alamar rai a tare da ita.
Ko da jin haka sai sarki Taryan ya yi shiru yana tunani cikin alamu damuwa har izuwa tsawon 'yan dakiku sannan ya dubi Barwal ya ce ta wannan bangaren dai sarki Gurzalu ya sha gabanmu yanzu abin da ya rage mana kawai shi ne mu yi duk yadda za mu yi domin mu gano abin da aka sacewa sarki Gurzalu a garin nan nawa wanda ya sa hankalinsa dugunzuma ainun.
Bokayenmu da yasa su yi masa wannan aiki ba zasu iya gano ko menene ba, amma zasu iya gano barawon da ya sace abin. Yanzu abin da nake so da kai shine yau da daddare ne sarki Gurzalu zai gana da bokayen kasar nan, lallai ina son duk yadda za ka yi ka jiyo mana duk abin da zasu tattauna, hakan zai bamu damar da zamu iya gano wani abin.
Lallai ka tabbatar da cewar babu wanda ya ganka a lokacin da kake leken
asirinsu da dauko mana rahoto.
Barwal ya gyada kai ya ce, an gama ya shugabana. Yana gama fadin hakan sai ya juya ya fice daga cikin dakin.
Shima sarki Taryan sai ya bishi da sauri ya nufi wani bangaren daban na gidan sarautar. Yana cikin tafiya ne ya hango sarkin yakinsa wanda ake kira Zamaru ya durfafoshi da sauri, kai da gani kasan cewa akwai alamun damuwa a tare a shi.
Da isowar Zamaru daf da sarki Taryan sai ya zube kasa bisa guiwoyinsa yana mai sunkui da kansa kas ya ce, ya shugabana akwai matsala. Yanzun nan wadansu dakarun sumame kimanin su dari biyu suka kawo hari izuwa dakin da ake tsare jarumi Imhal da nufin su hallakashi. Kafin na isa wajen har sun kashe dakarunmu guda goma. Nayi kokarin na kama ko da mutum daya daga cikinsu a raye domin mu tuhunesu mu ji wanda ya turosu amma abu ya gagara saboda sa'adda suka ga munci karfinsu sai sauran suka kashe kansu nan take. Mun yi bincike ainun akan gawarwakinsu amma mun kasa gano ko mutanen ina ne, dukkaninsu bakin fuskoki ne kuma babu wata alama da zata nuna daga garin da suka fito.
Lokacin da sarkin yaki Zamaru ya zo nan a zancensa sai kan sarki Taryan
ya daure ya cika da mamaki, kuma ya yi shiru yana tunani da nazari har izuwa tsawon 'yan dakiku sannan ya juyo da sauri ya dubi Zamaru ya ce, to yanzu wane mataki ka dauka don tabbatar da tsaron lafiyar jarumi Imhal?
Ko da jin wannan tambaya sai sarkin yaki Zamaru ya yi murmushi ya ce, ai tuni nasa an daukeshi daga cikin wannan daki an mayar da shi can dakin nan na sirri na karkashin kasa kuma ko kadan jarumi Imhal ma bai san duk abin da ya faru ba saboda barci yake ta sharawa sakamakon maganin da likitoci suka ba shi ya sha.
Ko da jin wannan batu sai sarki Taryan ya dan samu nutsuwa da kwanciyar hankali ya yi murmushi ya ce, ka yi tunani mai kyau. To yanzu kai a ganinka tsawon kwana nawa ne jarumi Imhal zai warke har ya ci gaba da gasa?
Ko da jin wannan tambaya sai Zamaru ya yi shiru yana mai tunani, sannan ya dubi sarki Taryan ya ce ya shugabana ai ni dai kam na gama tsorata da al'amarin jarumi Imhal domin shi mutum ne na daban a cikin mutane don
haka yi masa kiyasi a cikin sha'aninsa al'amari ne wanda babu yakini a cikinsa. A iya sanina da jin labarina ban taba jin mutumin da ya warke daga karaya ba a cikin kwana daya jal, sai jarumi Imhal, kaga kenan yanzu ma jarumi Imhal zai iya warkewa daga wadannan raunika dake jikinsa koyaushe walau a cikin kankanin lokaci ko kuma kishiyar hakan.
Ko da jin wannan batu sai sarki Taryan ya yi ajiyar zuciya ya ce, hakika maganarka dutse če amma dai muna sa ran cewa jarumi Imhal zai iya warkewa a cikin kwanaki uku kacal domin ina ganin cewa hakan shi ne mafi alheri a garemu gaba daya.
Zamaru ya risina ya ce, wannan gaskiya ne ya shugaba shin kana da wani aikin da kake son nayi maka banda wanda ka umarceni da yi?
Sarki Taryan ya ce babu na sallameka kaje kayi mini leken asirin Gurzalu a yau kuma komai dare ka kawo mini sakamako.
Zamaru ya ce, an gama. Nan take ya juya da baya ya fice daga cikin dakin. Har dare ya raba ko boka guda daya jal bai zo masaukin sarki Gurzalu ba kuma wannan lokaci akwai yan leken asirin sarki Taryan a ko ina cikin gidan sarautar sun lallabe a kowanne kusurwa domin su ga zuwan bokayen, amma sai akaji shiru kamar maye ya ci shirwa.
Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan, abin da basu sani ba shi ne sarki Gurzalu ya fi su wayo gami da hangen nesa ashe tun ranar da ya sa aka tara masa manyan bokayen garin ya gaya musu bukatarsa, bayan sun tafi sai da ya aika musu da wani hadimi nasa a sirrance ya rarraba musu kudade masu yawan gaske kuma ya ce da su kada su sake dawowa fada wajensa, sai ya gaya musu wani keba66an musamman wurin da zasu hadu.
Ashe tun da tsakiyar rana sarki Gurzalu ya yi bad da kama ya yi shiga irin ta dakaru gidan sarautar sarkΔ± Gurzalu ya sulale ya fice ya nausa can bayan gari.
Wani tsohon rusasshen gida ne wanda a kalla ya fi shekara dari uku da wanzuwa a wajen. Duk da cewar gaban gidan ya rushe amma akwai dakuna da yawa a cikinsa wadanda basu rushe ba.
A tarihin wannan gida shi ne masarautar farko ta birmin na Misra. Jama' ar birnin Misra da yawa sun camfa wannan gida da cewar akwai mugayen kwankwamai a cikinsa don haka nema mutane suke matukar kin zuwa kusa da gidan ma bare batun a shiga cikinsa. Duk wanda ka ga ya zo kusa da wannan gida to lallai gawurtaccen boka ne ko kuma jarumin kwarai mai dakakkiyar zuciya da shiri.
Lokacin da sarki Gurzalu ya iso bakin wannan tsohon gida sai ya ja linzarmin dokinsa ya yi tirjiya sannan ya sauko ya daure dokin a dirkar ginin gidan ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa ya tabbatar da cewar babu wani mutum a wajen sannan ya kunna kai ciki.
Sai da sarki Gurzalu ya yi tafiya mai dan tsawo a cikin gidan yana kallon yanayin ginin gidan yana mamaki. Gini ne na ban al'ajabi kamar ba mutane ne suka yi shi ba sai dai ace aikin aljanu saboda yadda aka sarrafa duwatsu aka fikesu aka yi musu ado kala kala, sai ka rasa irin kayan aikin da aka yi amfani da su.
Tsananin shirun da ke cikin wannan gida kuwa tamkar wani abu mai rai bai taba shigarsa ba. duk inda ka duba sai dai kaga kura da yana akan kwarangwalolin bil adama da sauran kayayaki na kawa.
Kwatsam sai sarki Gurzalu ya yi arba da wadannan bokaye wadanda ya basu aiki suna zaune a sama cikin iska kuma sun yi kawanya, idanunsu a rufe amma suna jin motsin takun kafar sarki Gurzalu sai suka bude idanunsu suka dubeshi a tare suna murmushi.
Kawai sai suka ga shima sarki Gurzalu ya tashi sama tamkar tsuntus ya shigo tsakiyarsu ya zauna yana mai harde Rafafuwa.
A tare bokayen suka sunkui da kawunansu kas suka kwashi gaisuwa a gareshi sannan shugabansu ya dube shi ya ce ya shugabana mun sami nasarar gano barawonka kuma ba wani bane face wata takadiriyar ma tsafiya 'yar asalin cikin bininka wacce talke da dangantaka da gidan sarautarku. A yanzu haka tana nan a cikin wannan birni namu kuma tana taimakon jarumi Imhal.
Kafin shugaban bokayen ya gama rufe bakinsa sai kawai suka ji muryar mace a can bayansu tana mai cewa, kwarai kuwa ni ce barauniyarka. A firgice su duka suka waiga suka dubi inda muryar ta fito sai ga Muzaira ta nufosu a sama rike da wani mashi karfe fari fat na sihiri kuma tana sanye da fararen tufafi ta taho da gudu a sama shu... kai kace fukafuki ne da ita.
Ko da ya rage baifi tazarar taku biyar ba tsakaninta da su sai ta tsaya cak! a cikin iska ta kura musu ido su ma suka kura mata idanu aka kama kallon kallo.

Zamu dakata Anan saikuma wani lokaci idan Allah yakaimu

Domin shiga WhatsApp group dinmu danna blue din rubutunnan
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Biyar (5)
Part D
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana
WhatsApp Group
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

Labari Ya Isowa Shagala Cewa πŸ₯°
Marubucin Yaci gaba da cewa

Ko da ya rage baifi tazarar taku biyar ba tsakaninta da su sai ta tsaya cak! a cikin iska ta kura musu ido su ma suka kura mata idanu aka kama kallon kallo.
Sarki Gurzalu ya kurawa Muzaira idanu a lokacin da jikinsa ya kama tsuma har fuskarsa na yatsinewa. Su kuwa sauran bokayen sun tsorata ainun da ganin Muzaira rike da wannan mashin sihiri saboda mashi ne wanda babu mai iya mallakarsa face wanda ya kai makura a hallarar tsafi.
Kawai sai Muzaira ta dubi sarki Gurzalu ta bushe da dariyar mugunta, daga can kuma sai ta tur6une fuska ta.ce, ya kai wannan azzalumin sarki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

5 Comments On RIJIYA GABA DUBU 5
avatar
abdulmudallib-8

1 year ago

Reply

I already paid N1000 why don't you allow me to download the document

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I just check now i am unable to saw your payment can you send me receipt if the payment through WhatsApp 08140419490

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

Alhamdulillah now you can check and see that your subscribtion is active, and you can download any of your desire book here. feel free to contact me anytime you face any minor or big issue related to our site Thanks for using our services

Please Login or Register in order to submit comment