Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi sani cewa na dade ina tanadi da shiri akan zuwan wannan lokaci na daukar fansa a kanka. Tabbas ni ce na sace gurunka na tsafi saboda nasan cewa idan
har kana tare da shi ba zan iya komai a gareka ba. Idan na ga dama a yanzu take zan iya kasheka amma na fi son kayi mutuwar wulakanci a hannun đana jarumi Imhal tunda kai ne ka kashe mahaifinsa kuma ka kashe mahaifiyarsa 'yar uwata kuma ka kashe duk zuri'armu har ya zamana cewa n kadai ce na tsira daga sharrinka.
Ko da Muzaira ta zo nan zancenta sai mamaki ya kama gaba dayan bokayen saboda sun ji babban sirrin da basu taba ji ba kuma ko a bincikensu na tsafi basu gano ba. Muzaira ta ci gaba da cewa, ina mai tabbatar maka da cewa dana ba zai wuce kwana ukuba a kwance yana jinyar wannan rashin lafiya don haka sai ka zauna a cikin shirin fafatawa da shi nan da cikar kwana ukun. Ba zan gaya maka cewa kai ne ka kashe ubansa ba sai a ranar da za ku yi wannan gasa kafin ya shiga filin gasar. Na sani cewa baka da wani abin dogaro wanda ya fi na gurinka na tsafi wanda da shi ne kadai zaka iya samun nasara a kaina. To yanzu ga gurinka daure a kuguna, da me kuma ka dogara?
Ko da Muzaina ta zo nan zancenta sai sarki Gurzalu ya takarkare
ya bushe da dariyar mugunta wacce ta cika gidan gaba daya da amsa kuwa, lokaci guda kuma ya turbune fuska ya ce, ya ke Muzaira ki yi sani cewa wanda duk ya riga ka kwana dole ne ya rigaka tashi, ki sani cewa baki isa ki tona mini asiri ba duk da cewar gurin sihirina yana hannunki kuma nayi miki alkawari kafin cikar kwanakin da zan fafata da Imhal sai guruna ya dawo hannuna.
Yana gama fadin hakan sai ya zaro wata siririyar allura ta tsafi ya sokawa daya daga cikin bokayen a kunnensa.
Take allurar ta fito ta cikin đaya kunnen ya shiga cikin kunnuwan ragowar bokayen, nan take su duka suka kame kamar gumaka.
Gurzalu ya sake bushewa da dariya ya ce, daga yau wadannan bokayen ba zasu sake ko da motsi ba sai da yarda ta kinga kenan babu wanda ya san sirrina a yanzu sai ke kadai, kuma kema yanzu ba za ki fita daga cikin gidan nan face na kasheki na kar6e gurin sihirina dake hannunki.
Ko da jin wannan batu sai Muzaira ta ta kyalkyale da dariya sannan murtuke fuskarta ta ce, to ai sai mu gani tun da dai in da babu kasa a nan ake gardamar kokawa.
Kafin Muzaira ta gama rufe bakinta tuni sarki Gurzalu ya zare takobinsa ya shillo a sama izuwa gareta, ai kuwa itama sai ta tareshi tana mai daga wannan mashi nata na tsafi suka kacame da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka.
Ana fara wannan gumurzu sai sarki Gurzalu ya raina kansa domin duk sa'adda Muzaira ta kawo masa hari ya kare sai yaji kamar wani katon tsauni aka buga masa saboda nauyin mashin nata, haka kuma sai yaga cewa zafin namata ya ninka nasa sau uku don haka kafin ya kai mata hari daya ta kai masa bakwai.
Ko da Muzaira ta sauya salon fada ta hada da naushi da bugu sai nan da nan ta rikita sarki Gurzalu kuma ta kuntatashi har ta sami nasarar kwada masa mashin nata a gadon bayansa ya fado kasa tim yana mai kwala ihu cikin ruf da ciki sai gashi yana amon jini.
Kafin ya dago kansa tuni ta bace bat, ya nemeta sama da kasa ya rasa. Cikin tsananin takaici da bakin ciki sarki Gurzaul ya yunkura da kyar ya mike tsaye ya kama waige-waige yana mai goge jini dake kan lebensa.
Ko da ya tabbatar da cewar Muzaira bata cikin gidan kuma ya san cewa yanzu fa tayi masa zarra a karfin sihiri sai kwalla ta ciko a idanunsa amma kuma da ya yi wani dan guntun tunani sai ya yi murmushin mugunta.
Nan take ya karkade kurar jikinsa sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin gidan tarihin ya bar wadannan bokaye dake zaune a sama kan iska a Kame kamar gumaka kai kace dama can a haka suke a wajen tun fil azal.
Tafiyarsa ke da wuya sai Muzaira ta sake baiyana a wajen tana kyalkyala dariyar murna.
Daga can kuma sai ta nutsu ta shiga kokarin ceto rayuwar wadannan bokaye domin ta dawo da su daidai yadda suke da ta hanyar amfani da mashin ta na sihiri amma sai abu ya gagara.
Nan take bakin ciki da takaici suka turnuketa saboda ta fahimci cewar rashin sanin yadda zata sarrafa gurin sihirin sarki Gurzalu ne ya sa ta kasa ceto rayuwar wadannan bokaye kuma in dai ba sarki Gurzaul ba ne ya je kasa babu yadda za a yi wadannan bokaye su kubuta.
Kawai sai Muzaira ta yi murmushin mugunta ta ce a cikin ranta, ai babu komai nan da cikar kwana uku taka ta kare. Tana gama aiyana hakan a ranta sai ta sake bacewa bat tamkar bata taba
baiyana ba a wajen.
Al'amarin sarki Gurzalu kuwa yana fitowa daga cikin tsohon gidan tarihin sai ya kwance dokinsa ya hau ya zabureshi da gudu.
Maimakon ya nufi gidan sarautar Sarki Taryan kai tsaye sai ya nufi wata hanyar daban wacce zata kaishi izuwa karshen gari, bai tsaya a ko ina ba sai a bakin wani kogon dutse. Da isarsa wajen sai ya tsai da dokinsa ya bude baki yayi wata inkiya ta kukan wani tsuntsu.
Nan take yaji an yi masa irin inkiyar, al'amarin da ya sanyashi farin ciki kenan ya sauko daga kan dokinsa da sauri. Kawai sai ya hango wani badakarensa ya fito daga cikin wannan kogon dutse fusksrsa cike da annuri.
Cikin hanzari sarki Gurzalu ya bi bayan wannan badakaren da sauri suka koma izuwa cikin kogun dutse.
Yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso karshen kogon dutsen inda suka tarar da wasu dakarun na sarki Gurzalu kimanin su dari uku a zazzaune, ga fitilun itace a rataye jikin dutsen kogon. In ba don darajar fitilun itatuwan ba da babu yadda za a yi mutum ya iya ganin ko da tafin hannunsa a cikin wannan kogon dutse saboda dubu.
A gefe daya kuma wani mutum ne tsoho tukuf a zaune, an daddaureshi da sarkoki a kafa, hannaye da kuma wuyansa. Kallo
daya zaka yiwa tsohon ka tausaya masa saboda ya sha bakar wuya domin an yi masa dukan tsiya an fasa masa baki da hanci jini na yoyo kuma an yayyaga masa rigar jikinsa.
Ba wani bane wannan tsoho face Imzanu, tsohon da ya ceci rayuwar mahaifiyar Imhal har ta haifi Imhal a cikin daji ta mutu, sannan ya ci gaba da renon Imhal tun daga kuruciyarsa kawo izuwa girmansa.
Lokacin da sarki Gurzalu ya iso gaban tsoho Imzanu sai ya durkusa daf da shi suka dubi juna da kyau ya kura masa idanu har izuwa tsawon 'yan dakiku, kawai sai sarki Gurzalu ya kece da dariyar mugunta. Lokaci guda kuma sai ya kama kukan bakin ciki ya fakaici tsoho Imzanu ya gabza masa naushi a fuska. Saboda
karfin naushin sai da tsoho lmzanu ya zube kasa a matukar galabaice, sa'adda jini yayı feshi ta cikin bakinsa.
Sarki Gurzalu ya cakumo kwalar rigar Imzanu suka sake kallon juna a lokacin da hawaye ya zubowa sarki Gurzalu ya ce ya kai wannan tsohon mafarauci kayi sani cewa kai ne kadai mutumin da ya taba wargaza mini shirina a rayuwata. In ba don ka ceci rayuwar mahaifiyar jarumi Imhal ba da yanzu babu wani mahaluki da ya isa ya shiga gabana.
Naso nayi maka kisan giilla a yanzu take to amma in nayi hakan ba za taba samun nasarar gamawa da makiyana ba. Mun sha bakar wahala kafin ni da yarana mu gano a inda kake. Duk da cewa ina nan birnin Misra ina gabatar da gasar kambun jarumta sai da na aika can birnin Kisra a sirrance nasa aka ci gaba da binciken inda kake boye har aka gano cewar kana nan a cikin gidan Muzaira tun daga lokacin da kuka gudo daga cikin daji kai da jarumi Imhal kuka fada gidanta.
AA Misau ke Magana
To ka sani cewa ni sarki Gurzalu har abada makiyana ba zasu sami nasara ba a kaina. Yanzu da kai zanyi amfani na sami nasarar kashe jarumi Imhal a gaban idanunka a ranar da za mu yi gasar karshe ta kambun jarumta.
Ko da sarki Gurzalu ya zo nan a Zancensa sai hankalin tsoho Imzanu ya dungunzuma ainun ya fashe da kuka yana mai cewa, ya kai wannan azzalumin sarki kayi sani cewa ni rayuwata ta kare kuma ko yanzu na mutu bani da wata asara tunda ba ni da wani buri a rayuwa am6na ka sani cewa shi zalunci baya dorewa a wannan duniya, akwai ranar karshensa domin kafin kai an yi manyan azzaluman sarakuna amma duk sun shude akan doron kasa tamkar ma ba a yi su ba. Albarkacin iyayenmu ko ka yi amfani da ni a matsayin garkuwarka don ka cutar da Imhal ba zaka yi nasara ba.
Ko da tsoho Imznau ya zo nan a zancensa sai sarki Gurzalu ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga cikin kogon dutse.
Shugaban dakarun ya bishi da sauri a baya. Suna isowa wajen kogon dutsen sai sarki Gurzalu ya dubeshi ya ce, da kyau Kamsaru aikinka yayi kyau. Abin da nake so da kai shine kada ku kuskura a san da zamanku anan cikin wannan kogon dutse kuma lallai a ranar da zan fafata da jarami lmhal ku zo da tsoho Imzanu cikin filin gasar, ku yi masa shiga irin ta bayi ku kawoshi gaban yan kallo daidai inda jarumi Imhal zai yi arba da shi kuma ku nunawa Imhal cewa za ku kasheshi idan bai bari na kashe shi ba a gasar tamu.
Ko da jin wannan batu sai Kamsaru ya jinjina kai cikin murna ya ce, an gama ya shugabana.
Cikin murna sarki Gurzaul ya juya ya nufi inda dokinsa yake. Har ya kama dokin zai hau sai ya fasa ya juyo da sauri ya dubi Kamsaru ya ce, wane labari ka zo mini da shi dangane da halin 'yata ke ciki a can birnin Kisra?
Kamsaru ya risina ya ce shugabana ni dai ban karasa can gidan sarauta ba saboda cikin gari na wuce kai tsaye tare da yarana izuwa gidan Muzaira a cikin daren da muka isa domin dauko tsoho Imzanu kuma muna daukoshi muka fice daga cikin garin muka taho nan amma dai mun iske garin tsit ana ta "yan koke-koke.
Ko da jin wannan batu sai sarki Gurzalu ya yi murmushin farin ciki ya ce, ai na san cewa sarkin yaki zai iya tsare gimbiya da kyau, ba zai barta ta dawo nan garin ba har a gama wannan gasa saboda ita ce kadai- zata iya sake wargaza mini shiri.
Sa'adda Kamsaru ya ji wannan batu sai ya jinjina kai, sannan ya ce ya shugabana to yaya batun matsafiya Muzaira fa, ta yaya zaka bullo mata?
Ko da jin wannan tambaya sai sarki Gurzalu ya yi dan guntun murmushi na mugunta sannan ya ce, ka rabu da wannan kawai, ni na san ta hanyar da zan gama da ita.
Ko da gama fadin hakan sai sarki Gurzalu ya juya da sauri ya kama dokinsa ya hau ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar cikin gari.
A can dakin sarki Taryan kuwa sarkin yaki Zamaru ne tsugune a
gaban sarki Taryan yana bayani a cikin wannan tsohon dare ya ce ya shugabana har yanzu da nake yi maka wannan bayani babu boka guda daya daga cikin bokayen kasar nan da ya zo gidan sarautar nan.
Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Taryan ya dugunzuma ainun. Idanunsa suka zazzaro ya dubi Zamaru cikin firgici ya ce, ai kuwa in dai haka ne sarki Gurzalu ya shammace mu domin duk yadda zai yi sai ya gana da wadannan bokaye a sirrance a wani wajen daban.
Shin an ga fitar sarki Gurzalu daga cikin gidan sarautar nan a yau?
Zamaru ya gyada kai ya ce, ai a yau gaba daya babu wanda ya fita daga cikin.gidan sarautar nan face wani badakarena guda daya wanda na umarceshi da yaje yayi mini leken asiri a cikin gari ko zai ga wani abu da su sarki Gurzalu ke shirin yi a sirrance?
Sarki Taryan ya ce yanzu ina shi wannan badakare na ka da ka aika? Ya dawo ne ya sanar da kai abin da ya gani?
Zamaru ya ce, ai har yanzu bai dawo ba.
Ko da jin haka sai hankalin sarki Taryan ya sake dugunzuma anun ya ce, ai kuwa sarki Gurzalu ya shammaceka. Wannan badakare da ka aika ba shi ba ne, ya fita daga cikin gidan nan, sarki Gurzau ne ya yi bad da kama ya yi shigarsa. Maza kaje ka nemi badakaren naka ka ga halin da yake ciki yanzu. Duk abin da ka gani ka dawo ka sanar da ni domin mu gani bain da ya kamata mu yi.
Kafin sarki Taryan ya gama rufe bakinsa tuni sarkin yaki Zamaru ya juya da gudu ya fice daga cikin dakin, yana mai nausawa wani bangaren daban na gidan sarautar. Bai tsaya a ko ina ba sai wanı sashi daban na dakarun dake tsaron gidan Sarautar ya kunna kai izuwa cikin dakin wannan badakare wanda ya aika ya yi masa leken asiri cikin gari.
Yana shiga cikin dakin ya iske wannan badakare kwance a kasa rub da ciki an daure hannayensa ta baya da igiya kuma an daure kafafunsa an toshe bakinsa da tsumma.
Cikin gaggawa Zamaru ya dubeshi a dimauce ya ce, me ya faru gareka?

SHIN ME YAKE SHIRIN FARUWA DA SU SARKI SARKI TARYAN?

YAUSHE NE ZA A CI GABA DA WANNAN GASA TA KAMBUN JARUMTA, KUMA WAYE ZAI SAMI NASARAR LASHE GASAR A
KARSHE?

To Anan Mukazo Karshen Littafi Na Biyar Domin Jin yadda zata kasance saimu hade a littafi na shaida

Mai MaganaA
Al Amin Ahmed Misau
AA Misau ke Magana
Nake cewa mu zama lafiya

Karku manta zaku iya Samun mu a wadannan shafukan sadarwa kamar haka
WhatsApp
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

Facebook page
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295

Facebook page
https://www.facebook.com/AlaminGuyson?mibextid=3amO3DAFELuS4Abp

Saikuma Shafin Matashin Marubuci Yusuf imam
https://www.facebook.com/profile.php?id=61553596297488

Saikun Zo
Admin AA Misau ke Magana
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

5 Comments On RIJIYA GABA DUBU 5
avatar
abdulmudallib-8

1 year ago

Reply

I already paid N1000 why don't you allow me to download the document

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I just check now i am unable to saw your payment can you send me receipt if the payment through WhatsApp 08140419490

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

Alhamdulillah now you can check and see that your subscribtion is active, and you can download any of your desire book here. feel free to contact me anytime you face any minor or big issue related to our site Thanks for using our services

Please Login or Register in order to submit comment