Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai hade da kuka ta fara da bada labarin asalinta, mutuwar Abbinta, zuwansu Nigeria, haduwar Ammi da alhaji Shettima da aurensu... Sai da tazo dai dai wurin fadin ranar da MIJIN AMMI (wato Alhaji Shettima) ya fara yi mata fyade kukanta ya karu, domin har wani sama sama numfashin ta ke yi, sai da ta kai kusan mintuna sha biyar kyawawa kana ta fara bada labarin komai, da rashin amincewar Amminta, da biyota Cyprus da alhaji Shettima yayi, bayan kammala karatun su da dawowarsu Nigeria, da shigo dakinta da yayi cikin dare, da yanda ta kubuta daga sharrinsa har ta fada hannun Aaban......
Bata boye musu komai ba ta gayamusu



kuka daya ci sunan shi kuka suke yi, har da Amal data dau karan tsana ta daurawa Abrar, Daddy ma duk girmansa kuka yake, mummy ma kuka take domin sosai sautin kukan ta ke tashi, Aaban kuwa har yanzu idanun sa a lumshe suke yayinda idon sa ke zubar da hawaye, karo na uku kenan da yake kuka domin ita kadai bayan girmansa, jikinsa har wani mugun rawa yake wanda da ace zai ga alhaji Shettima a yanzu babu abinda zai hana shi rabi shi biyu saboda wani mashahurin tsanar sa dake ratsa jijiya da jinin jikinsa.



Mikewa Abrar tayi domin gani take dukanninsu banda Hanan di'nta sun tsaneta, ta ma kasa kallon Aaban domin bata son ganin yanayi ko kallon da take tunanin zai mata, taku daya, biyu ta fadi wani jiri ya dauke ta, duhu ya gilma ta idanunta take ta fadi kasa summamiya....




Comment, vote, share please🙏

editing is not allowed❌❌

Jama'ata ku yi mun afuwa, kasancewar ana ta hidimomin bikin sallah yasa bana baku update da wuri, ga shi na ba ku ba yawa, amma in sha Allah gobe da wuri zan muku posting, ngd da kaunar da kuke nunawa books dina, son so nake muku.💞

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)


ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

Page 53-54
........salatin da su Mummy suka sanya ya sa shi saurin bude idanunsa, hankali tashe kana kuma a firgice ya nufi ta, cikin zafin nama ya manna ta da kirjinsa yayinda zuciyar sa ke wani mahaukacin bugu, hawaye ke zuba kan kyakyyawar fuskar sa, duk jarumtar sa ya kasa daurewa, saboda tsananin tausayinta, daga karshe ma fashewa yayi da kuka mai sauti, ya kara kamkame Abrar a kirjinsa, gaba daya ya rasa abinda zai yi domin kwakwalwar sa ta tushe.....



Cikin karfi hali Daddy yace "abokina me kake yi haka ne? Ka bata taimakon gaggawa mana"



Sai a lokacin yayi tunanin hakan, da mugun gudu yayi hanyar saman bene ya dauko box din treatment din sa, kwanatar da ita yayi kan kujera three seater yayin da ya shiga bata taimakon gaggawa hawayen fuskar sa ya gagara tsayuwa....




Amal kuwa matsanancin nadama ne ke cin zuciyarta, ta kasa tsayar da hawayen fuskar ta, haka zalika Mummy son Abrar, tausayinta, dama nadama, su suke yi wa zuciyar ta dabaibayi, tana ji kamar hannu agogo ya dawo baya ta goge tsanar da ta yi wa Abrar ta kuma nuna mata, dan ma bata cikin hankali ta a lokacin, da da wani ido zata kalleta? gaba daya mamakin tsantsar rashin irin imani da son zuciya irin na alhaji Shettima suke yi....



ta kai kusan awanin 4 ba ta farfado ba, kana ta fara bude idanunta, hawaye ke bin gefe da gefen fuskarta..., a cikin awanin nan sallah kadai ke ta da su Daddy daga falon, da zarar sun iddar zasu dawo su zauna domin ganin farkawar ta...




"sannu ya jikin?" gaba daya suka hada baki wurin fadin haka, yayinda suke yi kanta, jinjina musu kai tayi, still hawaye na cigaba da zuba kan kyakyyawar fuskar ta da yayi fayau tashi daya, sosai kuma kanta ke mata ciwo tamkar ana buga mata guduma...



gyaran murya daddy yace"hakika Abrar kin ga rayuwa, ta SILAN MIJIN AMMINKI, mun yi matukar tausaya miki, kuma kaddarar ki ce ta zo da haka, domin mutum baya kaucewa kaddarar sa, sai dai ina so ki sani cewa babu wanda ya kai uwa son danta ko yarta a duniya, duk da Amminki ta yi kuskuren rashin sauraren ki, wanda iyaye da dama na aikata hakan, idan yayansu sun kawo musu wata magana mai muhimmanci maimakon su tsaya su yi wa maganar duba na tsanaki, amma sai su yi watsi da maganar...(izinah garemu iyaye) da wanna nake cewa kada ki yi fushi da Amminki, nasan a yanzu tana cikin matsananci damuwa da kuma kewar ganin ki, sannan idan an kwana biyu zamu je can gidan inda Ammin taku take aure kin ji ko? ".... daga kai tayi alamun "toh" yayinda take take kokarin bude baki tayi magana, amma ta kasa, girgiza mata kai Daddy yayi alamun ba sai tayi maganan ba, wayar Amal ce ta fara ringing "sweet Adam" ta gani a rubuce, dagawa tayi ya sanar da ita cewa yana jiran ta a waje domin su tafi gida, a sanyaye ta mike ta yi salama da su Mummy tana waiwayon Abrar ta fito...





"Amma Daddyn'su bai kamata a bar dan iskan mutumin nan haka ba fa, domin irinsu a cikin al'ummah masifa ce" Mummy tace cikin tafarfasan zuciya, domin ji take kamar ta ga alhaji Shettima gabanta tayi ta kwada masa lafiyayyun maruka...




Murmushi irin nasu na manyan Daddy yayi a ransa yana fadin duk shekarun mace, toh ba shakka namiji ya fita kaifin tunani "relax mana Mummyn'su komai a nutse ya kamata mu bi shi"...

Jinjina kai tayi kawai tayi, ba dan haka ta so ba, kallonta ta kai ga Aaban da ke ta fama hargitsa sumar sa hadi da cije tattausan labbansa, cikin tausayinsu tace " son, ya kamata ku je daki ku kwanta haka, domin tara saura" ta fada tana duba tsadadden agogan dake makale a jikin bangon dakin...


Bai ce kala ba ya nufi sama cikin sassarfa ba tare da ya ko kalli inda Abrar take ba, da kallon Abrar ta bishi yayinda hawaye masu suka cigaba da gudana a fuskar ta, gani take kamar ya daina sonta ne...


cikin tausayin ta Mummy ta kamo ta hadi da mikar da ita tsaye, kana ta kaita har saman bangaren su kana ta sauko... a hankali ta dora hannunta kan handle din kofar, ta tura ta shiga a hankali, zaune ta gan shi kansa na kasa, dauke idanunta tayi ta nufi toilet, alwala ta dauro kana ta fito ta shimfuda sallaya ta shiga rama salollin da ke kanta....


bayan ta iddar ta ninke sallayan ta ajiye in da ya dace kana ta nufi in da yake a zaune kuma har yanzu kan sa na kasa, tattausan hannuwanta ta dora a kan fararen kafafun sa, cikin kuka tace "I knew it! I knew it that zaka daina sona idan ka ji labarina, domin nasan cewa babu wanda zai iya rayuwa ko auren na a haka pure heart, babu mai auren ragowan mijin Ammina...."

Cikin sauri ya toshe mata baki ya ce "shhhh" kana ya rungumota izuwa jikinsa, yayinda ya fashe da kuka tamkar mace, ita ma Abrar kukanta ne ya karu domin har wani sama sama numfashin ta ke yi...



Sun dau tsahon lokaci suna kukan kana ya yi karfin halin bubbuga bayanta, sosai fuskarsa ta yi jaa abunka da farin mutum, daidaita muryan sa ya yi yace "kada ki kara tunanin cewa zan bar ki ko zan rabu da ke, domin ke din rayuwa tace, ko a wani yanayi ko a wani hali na same ki, ina sonki a haka ko da maza dari ne suka keta miki mutunci ina sonki, it's you i love not your body, dan haka kada ki kara tunanin wanna maganar, abu daya nake son ki sani cewa ina matukar kishin ki fiye da tunanin ki".... ya kara sa fadin haka yana kara rungumeta



"Ba zan kara ba, ina sonka nima, ina matukar son ka pure heart "...


Murmushi mai tafe da hawaye ya saki, matsanancin sonta, tausayinta na ratsa shi...

"ya kamata ki kwanta ki huta haka" ya fada yana mikar da ita tsaye hadi da kwantar da ita kamar jaririya, kallonsa take, kallon so da burgewa hure mata ido yayi yace "sleep" murmushi tayi kana ta rufe idanunta ba dan tana jin bacci ba, sai dan cika umarnin sa kawai.....



Bayan kwana biyu Mummy, daddy, Aaban, Hanan, Abrar suka shirya tsaf domin zuwa gidan alhaji Shettima, mota biyu su ka yi, yayinda hawaye ya kasa barin fuskar Abrar tunda suka bar gida... Bayan sun isa gidan Alhaji Shettima dake maraba, driver ya danna horn aka wangala musu yalwataccen gate din suka shiga kasancewar yau asabar suna da tabbacin cewa masu gidan na nan, kukan Abrar ne ya karu ganin ta cikin gidan, take komai ya shiga dawo mata daki daki.....


Zaune alhaji Shettima yake kan daya daga cikin kujerun falon, ya dan yi rama kadan, baka hango komai sai tulelen tumbinsa, yayinda ya yi tagumi cikin damuwa, domin tun bayan barin Ammi gidan kwanciyar hankali ta kauran masa, yasa anyi nemansu, amma babu wani kyakyyawar labari har yanzu... Sallaman daya daga cikin ma'aikatan gidan ya ji, dago kansa da suka shige loko yayi ya zuba wa mai aikin nasa

"ranka ya dade kayi baki"

Cikin mamaki yace "baki?"

"Eh! suna waje nace su shigo, amma sun ki shigowa"

"Toh toh bari na fito" alhaji Shettima yace

"A fito lafiya Alhaji" mai aikin nasa ya ce yana fitowa...

Sanar da su Daddy yayi cewa alhajin na zuwa, kana ya koma bakin aikinsa... tun daga nesa ya hango wata uwa Abrar, murmushin farinciki ya fara saki sanda ya tabattar da cewa ita din ce "daddy's girl kece? kin tayar mana da hankali, sannu bayin Allah ku ku ka taimaki wa diyarmu ta dawo garemu, mun gode kwarai, naji dadi tunda kin dago gida Alhamdulillah!" yace cikin damuwa yayinda yake kokarin tunkarar ta...

"Dakata! ka da ka yi tunanin yaudarar kanka Malam, domin mu ba shashashun bane irin ka da zaka rainawa hankali, a gidan uwar uwa ta zama yarka? Da yar cikin ka ce da baka yi tunanin ta ba mutuncin ta ba, dalilin daya ya sa mu ka shigo cikin gidan nan, albarkacin Ammin Abrar da a kotu zamu hadu"... Mummy tace a zafaffe kamar zata kai masa bugu, Abrar kuwa rawa jikinta ya dauka domin gani take kamar abinda ya faru da ita a baya zai Sake faruwa, cikin tausayin ta Aaban ya riko ta izuwa jikinsa yayinda yake jifan alhaji Shettima mai tumbin kosai lolz😜😂 da mugun kallon tsana da matsanancin kishin sa.


kame kame ya fara yi domin ya lura cewa sun riga sun san komai, kuma kallon daya ya musu ya tabbatar cewa su din masu hannu da shuni ne, sannan sun yi masa kwarjini ainun.
Fuska ba alamun wasa daddy yayi gyaran murya kana yace


"ina mahaifiyarta take?"

"uhmm...wato... uhmm.... ta..." wani mahaukacin tsawa Aaban ya yi masa yace "kana bata mana lokaci ina Ammi take!?"... sosai Abrar ta tsorata da tsawar tasa, kamkamesa tayi, shi kan shi bai yi tunanin cewa ya iya tsawa har haka ba, kokarin rarrashen kansa yayi kana ya shiga bubuga bayan Abrar, gaba daya ji yake kamar yana cikin dajin domin daga mai gidan zuwa gidan gaba ya tsane su...



wani kishin Aaban ne ke sukar alhaji Shettima, amma ya kasa nunawa saboda wani mugun tsoran Aaban din yake ji...

"ta...ta gudu, ban san inda take ba" alhaji Shettima yace cikin rawar murya hadi da in- in -na.

Sai a lokacin Abrar ta dago kanta, ta rushe kuka mai ta ba zuciya.

"Kai kada kayi kokarin raina mana hankali, domin kana daf da shiga hannun hukuma, ka gaya mana gaskiya ina take?" Inji Daddy


"Wallahi summa billahilazi ta gudu, za ku iya tambayar ma'aikatan gidan su gaya muku, nan ya shiga basu labarin komai.... Domin sosai alhaji Shettima yake cikin tashin hankali wanda bai yi tunanin ba


Salati suka sanya duka yayin da kukan Abrar ya zarta na dazu muryan ta har dishewa ya yi " Ammi kada kiyi nesa da ni, ki dawo mu cigaba da rayuwar mu, ki dawo gareni Ammina!!!" ta zube kasa ta na cigaba da kukan...


Ganin cewa Abrar na cikin matsanancin damuwa yasa Daddy cewa su tafi, kana ya kalli alhaji Shettima yace "ka saurari sammaci daga kotu....


mu hadu a gobe dan ji yadda zata kaya masoyan littafin MIJIN AMMINA NE SILA...


SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

Written by Noor Eemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

Not edited

Page 55-56

.......haka suka shige motarsu driver ya ja suka fice daga gidan, da kallo alhaji Shettima ya bisu kamar ya rusa kuka, domin ya ga samu ya ga rashi, ga Abrar nan ta zo har gaban sa amma ba halin daukar ta domin ta fi karfinsa, saboda bambamcin a bayyane yake bazai iya ja da su Daddy ba, ga kishin Aaban din dake cin sa arai, "shi din waye da har zai rike ta a jikinsa?" Ya fada a bayyane...



Cikin mutuwar jiki ya koma cikin gida, yayinda ya tarar da wayarsa na ringing, number Kwaro ya ga ni baro baro a rubuce kan screen din wayar sa, cikin sauri ya daga hadi da karawa a kunnensa

"Oga akwai matsala fa, hukuma ta kama mu yanzu a hanyar dawowar mu, daga mu har motan barasa (giya) gamu a tsakiyan su" kwaro ya fada cikin tashin hankali ...

Kasa tiles alhaji Shettima ya zube ya shiga birgima yayinda yake ta maimaita "na shiga uku shettima" tamkar wani zautacce... Maganar kwaro ce ta sanya shi dawowa nutsuwar shi "ya haka kuma oga? Mun fi ka shiga tashin hankali fa, domin mu dari muka shiga ba uku ba, gasu sun zagaye mu da manyan manyan bindigogin su jira kawai suke mu bude motar"

"Kwaro ku bi ta kan yan iska da motar ku taho, kafi kowa sanin cewa naira na gugan naira har million dari na sa aka yi order barasan nan saboda riban da muka samu a baya, ta ya ya kake tunanin zan juri rasa wadan nan zunzurutun kudade'n?"

Kwaro kallon manu da ya hada uban gumi yayi yana daf da sa kuka yace "manu oga ya ci kai fa, ta ya ya zamu iya wucewa gaba daya suna zagaye mu? sarai alhaji Shettima yayi abinda yace amma sam bai damu ba yace; kwaro ku yi duk yadda zaku yi ku kubuta daga hannunsu, idan haka bata samu ba toh kada ku bari sunana ya fito cewa ni na aike ku, zan yi iya kokarina domin ganin an fidda ku, amma kada ku bari sunan... "

"Tau" ya ji karan bingida ta cikin wayar yayinda yaji ihu'n su kwaro ya cika kunnen sa,,, kuka mara dadin ji Alhaji Shettima ya Sa yayinda ya cigaba da birgema yana surutai, da alama ya fara fita a hayyacin sa....


Bangaren su kwaro kuwa, daya daga cikin yan sandan ne ya arbi bindinga dai dai saitin glass din gaban motar take ta tarwatse, hakan yasa su kwaro sakin ihu, cikin kwazo da sanin makamin aiki dan sanda yace "ku fito, kafin na kirga uku in ba haka ba zan tarwatsa kan ku da alburushi"...



Cikin rawan jiki su kwaro suka fito, manu kuwa fitsari ya saki saboda tsananin tsoro dama kwaro ya fishi dakakiyyar zuciya... Cikin mota suka cilla su bayan an sanya musu handcuffs, waya suka bugawa station din su, take manyan su suka basu umarnin su tafi da giyan, su tarwartsa su hadi da kona su, haka kuwa suka yi wasu sun nufi station yayinda wasu suka ja motar su kwaro.... Mutanen gari musamman wandanda suka tsani giya, murna suke sosai suna kabbara suna fatan a cigaba da kama irin wadannan mutanen masu shigo da giya kasar muslimai....


2 MONTH LATER (BAYAN WATA BIYU)

" innalillahi wa Inna ilaihi raju'un " Adam ya ambata bayan Amal ta gama bashi labarin Abrar, domin ya ganta tana yawan kuka shiyasa ya tambayeta
"tabass wanna diyar anty na ce" in ji Adam

Cikin mamaki da faduwar gaba tace "diyar anty ka kuma wace antyn taka?"


"Anty Rahilat mana, domin wanna labarin sak irin wanda ta bamu ne, kuma ita ma yarta ta bata dole yanzu in je gida mu tafi gidan ku dukanmu, domin bana ko tantama wanna Abrar din ita ce Abrar din Anty na"


Adam yace cikin tabbaci kana ya kalli Amal fuska a daure ya sake cewa "yanzu Amal diyar anty Rahilat kika nuna wanna tsanar da tsangwaman? Ya fada rai a bace...

Kuka ta fashe dashi ta durkusa gaban sa domin babu abinda ta tsana kamar bacin rai Adam saboda tsananin son da take masa, rungume kafafunsa ta yi tana bashi haku'ri janye kafarsa yayi yana kokarin barin dakin har ran shi ya ji haushin abinda tayi... Ringing wayar sa ce ya sa shi tsayawa daga barin dakin, " hello baba" ya ce maimakon yaji muryan baba Sai na mama cikin tashin hankali tace "maza kazo Adam baban ka yayi hatsari muna asibitin da muka saba zuwa"... Ai katse wayar ya yi ya fice daga dakin hankali tashe yayin da Amal ta sanya mayafi ta biyo shi, saboda duk ta ji abinda maman ta ce...


Ninke sallaya yayi bayan ya idar da sallar shafa'i da wuturin sa, domin lokacin karfe sha daya ta yi, mafi yawan lokuta a irin wadanan lokutan yake sallar, kan gadon ya hau
"Wiffffy"
ya kira sunan ta dai dai saitin kunnenta, yarrr ta ji tsigar jikinta ta tashi, bude idanunta tayi karaf suka hada idanu kasa ta yi da kanta tana mamakin tsananin haku'rin sa, domin duk wadan nan tsahon lokutan da suka yi tare bai taba gwada kusantar ta ta ba ko wani abu ba, daga ya rungumeta ko ya sumbaceta a hannu, kumatu, ko goshi shikenan ta aiyana hakan a ranta tana sakin ajiyar zuciya...

"Wifffy" ya sake kiranta a karo na biyu "uhmm" ta amsa a shagwabe, tana turo dan karamin bakinta.

Murmushi ya saki yace "tashi, nasan ba bacci kike ba" ya fada yana daga ta zaune.

Hannunta ya riko cikin nashi yana kallon dacewa da hannuwansu suka yi, domin farin fatar sa da brown skin din ta da ya hadu da juna sai hakan ya bada kala mai kyau, turo baki ta yi ganin yadda ya kurawa wa hannunta ido, a shagwabe tace
" kana kallon bakin hannu na ko?"

Murmushi mai sauti ya saki ya ce "ai ke ba baka bace, you re brown in complexion which I so much like, na fi son kalar fatar fiye da tunanin ki"...

Murmushi ta yi cikin karfin hali, domin damuwar rashin Ammin ta ya fi komai damunta a yanzu, hannunta ya shiga murza wa cikin wani salo ya ce " Decent one nasan cewa ba dadi rasa babban jigo a rayuwa kamar uwa, duk da tana raye amma bamu san in da take ba, ana kan neman ta muna kuma fatan a dace, please ki kwantar min da hankalin ki domin kada idan mun hadu da Ammi tace bana kular mata da ke " ya kara sa fada da iyakar gaskiyar sa...

Murmushi ta yi wanda har jerarrun fararen hakoranta mai dake da siririyar wushirya a tsakiya ya bayyana, domin sunan Ammin ta kadai daya ambata ya sa ta cikin farinciki...

"In sha Allah na daina" tace cikin zazzakar muryarta da ya hadu da yanayin sanyi da take ciki ya bada amo mai dadin gaske...

Haka kawai yaji yana jin son sa ta farinciki ta hanyar siya mata favorites dinta wato nama, ice cream da chocolate, duk da cikin su tafi son nama sosai.

"Za ki ci nama?" Ya fada yana kallonta
Cikin sauri ta gyada kai alamun "eh" da murmushi farinciki kan fuskar ta.

"Bari in je in siyo miki yanzu zan dawo" ya fada yana mikewa, saurin mikewa tayi itama tana kokarin daukan hijab din ta, kallon ina zaki? yake bin ta da shi.
"zan bika" tace fuska a marairaice
Ba musu ya kamo hannunta suka fice bayan ya sanya mata hijab din, haraban gidan suka fito ya nufi parking space_ wani sabon lifan din sa wanda ya siya kawai dan irin wanna fita musamman ta dare bai fiye son hawa mota ba...

Tayar da mashin din yayi yace ta hau, a tsorace ta hau domin tana tsoron mashin, kamkame shi sosai tayi hadi da kwantar da kanta kan gadon bayan sa suka fice... Mummy da Daddy dake zaune kan gadon dakin Daddy suna shan hirar soyaayyar su, suka kalli juna suna saki murmushin farinciki, domin kan idonsu su Abrar suka fice kasancewar lalube a dage yake.


Cikin kwarewa yake gudu sosai kan kwalta yayinda iska mai dadi ke kada su, kasancewar kuma babu ababen hawa a titin sosai ya bashi daman gudun son ranshi, yayinda yake murmushi jin yadda Abrar ta kamkame shi, daga karshe ma da ta gudun ya ki sauki ta fashe da kuka domin har wani laayi yake da babur din kamar zai zubar dasu... "Pure heart ka taimka ka rage gudun nan dan Allah!" tace tana kuka da iyakar gaskiyar ta

Shiru ya yi, bai kuma daina gudun ba domin sosai yake jin dadin yanayin da suke ciki "sai na gaya wa Mummy kana gudu dani" tace tana cigaba da kukan.

dariya ce take cinsa amma bai yi ba, wani tsalle ya yi dasu gaba daya daga Babur din har su suka yi sama kana suka sake dira kan kwalta wani ihu ta sa yayinda kukan sakalcin ta ya karu tace "ni ka sauke ni na fasa cin naman"....




Manage pls bana da a enough charge.

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌


Noor Eemaan✍
07082281566


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

Wanna page din sadaukarwa ne ga sisters dina much love (bloodlines)❤

Page57-58

(Not edited)

Sosai dariya ke cin sa amma bai yi ba, kasancewar dariya ba dabi'ar ba ce, bai taba tunanin cewa ita din matsoraciya bace sai yau...


Wani tsallen daya dara na baya yayi, wani mugun ihu ta saki, cikin kuka sosai tace "pure heart na fasa cin naman, ka bari kada na mutu ban hadu da Ammina ba"... Ta kai karshen maganar tana sake rungume shi da kyau.



Cak! Ya tsaya, domin kalamanta sun yi matukar ta ba zuciyar sa, domin ba hakan bane manufar sa, yayi hakan ne domin sanyata farincikin bai yi tunanin cewa hakan zai tsoratata balle har ta furta wanna kalami mai taba zuciya ba...

Cikin wani salo ya dawo da ita gabansa sai ya zamana suna fuskantar juna, da hannu daya ya shiga shafa fuskar ta ya ce" Ana aseef wifffy (kiyi haku'ri wifffy) ban yi da niyyar sa ki kuka ba, na yi hakan domin sanya ki farinciki, am so sorry ok?"


Cikin tsoron da bai gama tsakin ta ba hadi da tausayin sa tace "ni ba ka min komai ba fa, kawai ina tsoron mashin ne, kayi haku'ri ka jiiii?" Ta ja karshen maganar.

Murmushi mai taushi ya sakar mata hadi da bata Sumba a kumatun ta, bayan shi ya sake mayar da ita, kana ya tayar da mashin di'n ya shiga Jan su a hankali, duk da haka matsoraciyar sai da ta kamkame shi....

Hada'dden wurin siyar da nama irin daban daban suka nufa, kowa na harkar gabansa yayin da mutane ke cike a wajen makil tamkar ba dare baa, suna zama babu dadewa waiter ya zo da menu, pappersoup yayi mata ticking da table water, yayin da ya yi wa kansa ordering only soft drink.

Babu jimawa aka kawo musu, tun kafin Abrar ta fara ci take hadiyan yawu, duk da uban kunyan da ke dawainiyya da ita ganin jama'a hakan bai hanata fara shan romon naman ba, domin ta ga kowa harkan gaban sa yake...

Da cokali ta fara cin naman, ganin hakan bai mata ba ta ajiye spoon din hadi da sanya dogayen yatsunta ta fara gutsiro naman,... Aaban hade hannunsa yayi cikin na juna yana bin duk wani motsinta da kallo, kallo na zallan so, bai yi tsanmani ba yaji romon naman ya fallasa a kan farar rigarsa, sakamakon wani kyakyyawan ja da tayi wa naman... Cak ta tsaya da cin naman yayin da ta kwabe fuska cikin rashin jin dadi hadi da turo bakinta tace "pure heart am so..."

"Shhhh" ya ce yana kallon fuskar ta yayinda murmushi ke kan fuskar sa har yanzu, romon daya dan bata gefen bakin ta yasa hannunsa ya fara goge mata hadi da cewa "you dont have to say sorry decent one, domin ina son duk wani abu da kike yi yanzu, i enjoy looking

Please Login or Register in order to submit comment