Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce miki ko,"? ta fada da yaren buzanci, murya alhaji ce ta katse mata amsar dataso bawa abrar "ashe hajiya ta haka kike da tsoro ?yafada yana kara fashewa da dariya domin ya kasa riketa. Ajiyar zuciya ammi ta sauke ganin ba abinda take tunani bane, nan workers din suka dinga zuwa gabanta suna gaisheta cikin sakin fuska take amsa musu kana suka nufi cikin gidan mamakin irin dukiyar alhaji fal ranta...

*1 MONTH LATER*
zuwa yanzu ammi ta zama yar gida domin lafiya lou suke zaune da alhaji, abrar kuwa har yanzu bata sakewa da alhaji daga gaisuwa shikenan, a daki take wuni duk yanda alhaji yaso ya jawota jikinsa ta ki bari ammi kuwa tun tana damuwa da halin da abrar da tsiro dashi har ta hakura domin tayi fadan tayi lallashin akan ta dauki alhaji shettima amatsayin uba amma sam ta ki yarda, da ammin ta fara maganan zata sa kuka.

zaune alhaji shettima da ammi suke akan hada'ddun kujeran falon da girma falon kadai ze kai 100/100.
"hajiya?"
"na'am alhaji" ammi ta amsa.
"ki sanar da abrar cewa ran monday in sha Allah zasu fara jarabawan waec da neco domin na gama mata komai na registration ga exams card dinta da uniform" ya fada yana mika mata wani leda mai kyau.
kasa magana ammi tayi gaba daya hawaye sun ciko idanunta tama rasa bakin godiya ashe zata samu wand ze meye gurbin musu sajeed? shiyasa akullum yaumil alhaji ke kara matsayi aranta dalilin kaunar da yake nunawa tsoka daya a miyar ta wato(abrar).
n
"alhaji nago.... shhhhhh cewar alhaji shettima kana yadora ai abrar na dauketa tamkar yar dana haifa don uba ya sauke wa yarsa hakkin dake rataye awuyansa sai ya zama abun godiya har haka, murmushi ammi tayi kana ta bashi side hug bubbuga bayanta yayi kana yace ta kaiwa abrar kayanta domin ta fara shiri ba musu ta mike ...
Kwance take tayi matashi da hannayenta tayi zurfi cikin tunani tamkar wata babbar budurwa mai tarin damuwa, girgiza kai ammi dake tsaye abakin kofa tun dazu tayi kana ta karaso bakin gadon ta zauna
"abrar"
shiru ba amsa adan tsawace ta sake kiranta hadi da girgizata, dawowa hayyacinta tayi ganin ammi ce yasa ta fara kokarin tashi zaune hadi da cewa
"ammina"
"abrar mekikeso ki mayar da kanki ne eyeh? Gaba daya kin daurawa kanki damuwa kina yar karamar ki dake meye matsalarki? meye matsalarki abrar amsa min"
"ba...bu komi ammi ta fada muryanta na rawa" shikenan tunda haka kika zabawa kanki ,dakin ya dau shiru na mintuna uku kana ammi tacegashi inji alhaji ya biya miki waec da neco akwai uniform da wasu abubuwan dazaki bukata aciki, in kin ga dama kuma karki gode masa. Ammi ni banason wani abu daya fito daga hannunsa , toh zaki iya zuwa ki gaya masa haka ammi ta fada cikin fushi kana ta dafa kafadarta ta cigaba da cewa koda wasa abrar kada ki bar alhaji yasan baki kaunarsa, domin zan saba miki aranar kuma ki biyoni ki masa godiya ki kuma saki fuskarki ammi ta karasa hadi da ficewa, jiki ba kwari abrar tabi bayan ammi tana kokarin daidaita yanayinta"

"da...ddy nagode Allah ya kara arziki. Abrar ta fada kamar batason yin magana murmushi alhaji shettima yayi cikin jindadin ta kirasa da "DADDY" ameen daddy's girl ya fada yana shafa kanta ajiyar zuciya ammi tayi ganin bata kwabtsa mata ba. Abrar kuwa wani iri take ji ganin ta kira mutumin data k i jiki da daddy wanda batasan dalilin tsanar ba, saidai tayi hakan ne don farinciki ammi, kuma tayi farincikin domin ta gani afuskarta mikewa tayi domin komawa dakinta alhaji shettima yace" abrar bazaki zauna tare da mu ba har yanzu dai baki gama sakin jikin ki ba, sae da ta runtse idanunta kana ta juyo tace
"ina dan jin baccine daddy tafada ok toh it's alright yafada yana mai da hankalinsa wurin ammi suka cigaba da hirarsu...
ranar monday abrar tafara zuwa zana exams.
dinta kuma alhamdulillah bata samun matsalan komai domin makarantar masu kudi ce, bayan wasu watannin ta gama exams dinta sai jiran fitowar result...

*some month later*

"hajiyata ki sanar da abrar ta fara shiri na duba result dinta ya fito kuma alhamdulillah bata da matsala, na kuma samo mata admission a cyprus wanda acan nakeson ta hada degree dinta if possible har da masters ko ya kika gani" yakarasa yana girgiza kafaffunsa. shiru ammi tayi tama rasa bakin godiya domin kullum da kyautatawar da alhaji ke musu shiyasa yake kara samun matsayi aranta domin soyaayar dayake nunawa tsoka daya amiyarta wato abrar...
"ai alhaji abrar diyarka kana da iko da ita Allah yakara arziki, cikin jindadi yace ameen"
bayan ammi ta sanar da abrar nunawa tayi ita batason ya dinga mata komai, sai da ta ga fushin ammi kana ta hakura ta je ta masa godiya.

*******************************************
suna filin jirgi ana kiran sunan massengers har aka kira su abrar, basu wani nuna rashin sabo ko kauyanci ba tunda wanna shine karon farkon su wanda hakan dasuka yi yasa alhaji shettima jin dadi kwarai...

"CYPRUS"
bayan duk sun gama mata komai na karatun ta har alhaji shettima yace ze samo mata gida awajen school din amma abrar ta nuna tafison zaman cikin campus ko nace hostel din makarantar.
Washegari su ammi suka nufi airport domin komawa gida, abrar data rakosu sai kuka take, ita da ammi zata zauna anan kada ta tafi alhaji sai bata baki yake amma ko kallons a bata yi, cikin kuka abrar tace "ammi ki kulamin da kanki kinji ni ban yarda da mutumin nan daddy ba, ki kula kinji idan ya miki wani abu ki gayamin zan rama miki da kaina tafada cikin yarinta tana daga damtsen hannunta alamun karfi
murmushi mai tafe da hawaye hadi da ajiyar zuciya ammi tasaki at once tana mamakin maganganun da abrar keyawan yi tamkar babba, ta kuma ji dadi daba da hausa tayi magana ba domin batason ko kadan alhaji shettima yasan cewa abrar batasonshi...
haka abrar ta cigaba ta attending lectures har ta kai kwana shida, kamar yau ta fara shirin zuwa makarantar sanye take da jeans trouser sai riga ta ciki pink colour sai jacket din jeans din data dora asama pink top din snickers dinta ma pink ne sai mayafin data yi rolling dashi shima pink color,babu ko digon kwalliya afuskarta amma sosai tayi kyau duk da cewa har yanzu babu komai akirjinta 🙈 jaka ta rataya tana yamutsa fuska domin kasan cikinta taji yana mata ciwo tun safe, rufe dakinta tayi da padlock domin wadanda zasu zauna adakin har yanzu basu iso bah, bata jima da shiga aji ba lecturer ya shigo yafara gabatar da lecture saidai ba komai abrar ke fahimta ba domin ciwon cikin sai gaba yake
kwas! kwas!! suka ji takun takalmi na tukaro ajin, dakatar da bayanin lecturan yayi domin ganin mai shigowa, wata farar yarinya ce ta shigo da'a shekaru zata girmewa abrar da shekara daya haka, cikin girmamawa tace" sorry for disturbing your class sir" jinjina kai yayi kana yace "its alright but why are you attending my class by this time" yafada yana nuna wristwatch din hannunsa.
"i just resumed today, i mean right now sir"
"ok" yace kana yana mata nuni data je ta zauna sannan yacigaba da bayaninsa, gaba daya wanna yarinyar ta kalli ajin jitayi tafison zama kusa da abrar, murmushi ta sakarwa abrar lokacin data daidaita zamanta amma sam mutuniyar batasan tana yi ba domin ciwon ciki yasata agaba, ganin abrar bata kula ta ba yasa ta dan bangaji kafadarta abrar da tata hadi da cewa "hey" dagowa abrar tayi tana murmushin yake...
can da cikinta yayi wani azababen ciwo batare da tasaniba ta saki ihu tana zamewa kasan desk din sauri wanna yarinyar rikota tana cewa
"are you okay"?
" no am not my stomach!!!" abrar ta amsa da kyar.
lecture ya bada umarnin akaita clinic su bata drugs ba musu wanna yarinyar ta rikota hadi da daukan jakarta, yawanci yan ajikin suka hada baki wurin furta "sorry"
suna cikin tafiya abrar tace
"please take me to my room i will fine"
"noo you need to see a doctor" inji wanna yarinya.
"Please just take me to my room i beg you" abrar tafada wasu siraran hawaye na zubo mata. ba musu ta gyada kanta abrar na nuna mata hanya har suka zo dakin zaro ido wanna yarinyar tayi ganin dakin aka ce zata zauna shine na abrar kara kallon dan card din hannunta mai da dauke da number dakin tayi sai tayi murmushi da ita kadai tasan ma'anarsa...
wanna yarinyar ta dau mukulli a jakar abrar suka shiga dakin, zaunar da abrar tayi akan gado tana sakin ajiyar zuciya domin gaba daya nauyin abrar ajikinta yake har sukazo dakin kallon farar abayar jikinta tayi zaro ido tayi hadi da cewa" blood"
" you re mensturating" azabure abrar tamike tana kallon jikinta, kallon gadon tayi sai taga shima ya cike da jini, ihu tasa hadi da fashewa da kuka itakam tun dazu take jin kamar abu na fito mata amma bata kawo cewa jini bane. cikin tausayawa wanna yarinyar ta rungumeta tana cewa" sorry don't cry again, i guess this is your first time don't worry i will help you through okay" ajiyar zuciya abrar tasaki still hawaye na zubo mata, cire zanin gadon wanna yarinyar tayi hadi da cewa "go and take your bath am coming" tafada tana ficewa da sauri bata ko damu da jinin dake rigar ta ba...
wanna yarinyar kuwa wurin masu kula da kayan dalibai tanufa domin daman ta ajiye kayan wurinsu ne domin ta gano dakin sai tasa akai mata kayan, tayata daukan kayan sukayi tana gaba suna biye da ita...
bayan sun ajiye kayan ta janyo dan karamin akwati ta fito da sanitarypad hadi sabon pant ta saita pad din ajikin pant din kana ta mike ta nufi hanyar toilet din, kwankwasa kofar tayi batareda ta kalli abrar ba ta mika mata pant din cikin kunya ta amsa, sanyawa tayi ta fito tana jinta uncomfortable, burinta kawai ta kwanta ko zata dan samu sauki, rub da ciki tayi duk da tasan babu kyau amma tafi jin dadin hakan domin ciwon yana lafe mata babu jimawa bacci ya dauketa. wanna yarinyar kuwa kayanta tafara jerawa asite dinta bayan tagama komai ta kwashi kayan abrar har ma da zanin gado ta saka awashing machine itama toilet ta fada tasakarwa kanta ruwa bayan ta fito ta sanya simple dress ta haye gadonta tausayin abrar fall ranta domin itama bata manta wahalar data sha akaron farkonta, bayan kamar awa biyu abrar ta farka abunda ta gani yasa ta zaro idanunta....


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
✍written by noor Eemaan
wattpad@noorEemaan

sorry guys nayi mistake a page din baya maimakon nasa 3-4 sai na 2-3 yanzu zamu tashi ne a 5-6 fatan an gane.

page 5-6
ganin wanna budurwan data taimaka mata kwance kan nata katifan ga kuma kayan ta a jere a abangarenta kenan itama room mate dinta ce kenan? ta aiyana hakan aranta, jin alamun motsi yasa wanna budurwan tashi daman ba bacci take ba game take a tsadaddiyyar wayarta.
mikewa tayi ta dawo gadon abrar tana sakar mata murmushi zata yi magana kenan wayarta yafara ringing amsa kiran tayi tana murmushi
" ya Aaban dina" tafada cikin maganarta mai dan sauri -sauri daga dayan bangaran akace
"yes little hanan how are you doing?"
"am doing great my sweet yaya"
"happy to hear that" yafada cikin tsadaddiyar muryansa, kin gama settling komai little?"
"yes yaya gani a dakinmu ma tareda roommate dita"
"ok hope she's good i mean mutuniyar kirki ce?"
"i guess so yaya i just met her today"
" ok bye take care"
"i will ya Aaban, bata da lafiya zaka mata sannu ina nufin room mate dina?" kit ya kashe wayar, murmushi tayi tana mamakin halin yayanta bayason magana sam haka kuma kula mace baya cikin tsarinsa da kyar kaga dariyarsa...

abrar datake kallon wanna budurwan tun dazu cikin mamaki don bata yi tunanin tana jin hausa ba, saboda yanayin kalar fatarta yafi kama dana larabawa.
"so sorry for disturbing you, so tell me which country are you from?" murmushi abrar tayi kana tace " banyi tunanin kina jin hausa ba"
"lah kema ashe kina jin hausa"
wanna budurwan tafada, sai suka fashe dariya su duka biyun suna rungume juna.

"gaskiya nayi farinciki sosai musamman lokacin dana gane cewa room dinmu daya, ashe har yarenmu daya"
toh dai sunana hanan abdur-rauf babana dan asalin garin adamawa ne, mummyn na kuma shuwa-arab ce ina da yayye biyu ya Aaban da anty amal, muna zaune a abuja a unguwar maitama tarihi na atakaice kenan"
" kefa?"
"sunana abrar sajeed abbina dan asalin garin nijer ne ammina kuma yar cameroon ce, abbina yarasu yanzu dai ina zaune tareda ammina a gidan mijin ammina dake abuja"

"ayyah Allah ya jikan abbinki, gaskiya komai naki mai kyaune har sunan ki ma, kinsan da farko wallahi nazata ke irin black american dinan ce domin yanayin kalar fatarki mai kyau ce" hanan tafada cikin iyakar gaskiyarta

"ai nima nazata ke balarabiyar riyad ce" abrar ta fada, sai sukayi dariya atare.

"oops surutuna yasa na manta ban tambayi jikin kawata ba, so how are you feeling now?"
" feeling more better alhamdulillah nadan ji dadin jikina nagode da kulawa" abrar tafada tana murmushi
" never mind my dear" zan nuna miki yanda zaki na saita pad din, gashi da yawa aka siyo min daga gida sai mu dinga amfani dashi kafin mu siyi wani, kinsan tun ina10years nafara ganin period" zaro idanu abrar tayi cikin madaukakin mamaki tace
" are you kidding me"
abrar ta fada cikin rashin yarda.

"i swear hanan ta fada tana dariya kinga lokacin ban kaiki bako?"
"Allah mai halitta abrar tafada tana jinjina kai haka dai suka cigaba da hirarsu wanna abrar tasaki jikinta ba laifi wanda rabon data yi hira haka tun da alhaji shettima ya shigo rayuwarsu, ga hanan akwai surutu kam, can sai ga cikon ta ukunsu da kayanta yar america ce mai suna linda robbet nan suka cigaba da hirarsu gwanin burgewa...

"NIGERIA"
cikin sanda alhaji shettima ya bude dakinsa yafito gudun kada ammi dake kwance tana bacci taji abunda zae fada babban palo ya fito ya kara waya akunnensa kasa kasa yace " hello kwaro ya akayi ne kayan nan sun iso kuwa?"
daga can bangaren akace " Allah ya ja da ran alhaji ai mun sha da kyar, saura kiris daka ji an garkamemu" ajiyar zuciya alhaji shettima yasaki kana yace afili yace "toh gobe mu hadu a guest house dina"
"an gama ranka ya dade" kwaro yafada cikin muryansa mara dadin amo.

washegari kamar yadda alhaji shettima ya fada suka hadu da kwaro a guest house dinsa inda suka tattauna akan gurbataciyyar harkansa ta shigo da barasa daga waje, kuma har ila yau Allah be basu ikon kamasu ba, bayan kasuwancin sa dayake babu wanda yasan alhaji shettima na wanna harkan daga shi sai yaransa su kwaro, bayan sun raba tsadaddiyar giyan wa customers dinsu ba karamin riba aka samu ba shiyasa alhaji shettima yace baya iya hakura da harka domin yana samun kudi masu tsoka wanna kenan...

"CYPRUS"
"abrar yau shirun ki yayi yawa what's the matter?"
" hanan ina kewar ammina sosai" murmushi hanan tayi tana jinjina kaunar dake tsakaninsu domin abrar batada magana sai na ammi.
"but why not ke kirata"
"banda waya, tace kuma bazan rike waya ba har sai na gama school"
jinjina kai hanan tayi kana tace
" ga wayata ki kirata idan kina da numbern off head"
cikin sauri abrar ta amsa tana murmushi itama hanan murmushi tayi ganin tasa kawarta farinciki domin sosai take son abrar.
"ammina" tafada bayan taji alamun an daga
"abrar?"
"na'am ammina ina wuni fatan kina lafiya"
" lafiya lou, ya karatu hope dai baki wasa da karatu?"
"eh bana wasa ina kewarki sosai ammina tafada cikin muryan kuka"
"murmushi mai sauti ammi tayi cikin sahihiyar kaunar yarta tace" ina kewarki nima sosai diyata, daina kuka kinji?"
jinjina tayi tayi tamkar ammin na gabanta "amma abrar wayar waye wanna"
kallo hanan tayi kana tace "wayar kawata ce dakinmu daya" kafin ammi ta amsa hanan tace "kaji mun yarinya wai bazaki bani wayar mu gaisa da ammi ba ko taki ce kedai" tafada tana warce wayar, girgiza kai kawai abrar tayi yayinda ammi dake jinsu ta ke murmushi, nan dai suka gaisa da ammi, linda dake gefe tana murmushi domin sosai take jin dadi idan taji su abrar na hausa "hey why are starring at us like that?" abrar ta tambayi linda tana dage girarta
"i love you guys language so much, will you teach me i mean hausi(hausa)" dariya suka sanya gaba dayan su musamman hanan da kiris take jira dama...

haka dai rayuwa ta cigaba da juya musu daga ranaku zuwa satittika, daga satittika zuwa watannin daga watannin zuwa shekara, ayanzu haka su abrar suna level200 exams kawai ya rage sun kamalla wanda agida nigeria zasu yi hutun su linda kuma zata koma america domin yin nata hutun...

yan mata uku ne suka jero cikin shiga mai birgewa, ta hannnun dama ita ce tafi kowaccensu haske sanye take da black half gown mai spaghetti hand yayinda gashinta mai kalan sliver ke daure da band, ta hannun hagu itama farace sosai amma ta dama ta fita fari, sanye take da jumpsuit na jeans sai farar riga ta ciki, kafarta kuwa sanye yake da black cover shoe ta yane kanta da bakin veil ta sha makeup tayi kyau ta tsakiya kuwa mai brown skin tafi ko waccensu kyau amma ita ba fara bace, itama irin shigar ta gefenta tayi wato jumpsuit, sai yanzu dana kallesu sosai naga ashe abrar, hanan, da linda ce. sun kara girma musamman abrar da take kokarin shiga 16years yanzu komai na budurwa ya gama bayyana mata cikin shekaru biyun nan tayi girma mai ban mamaki domin kirarta mai kyau ce wato cocacola shape kallonta zaka san cewa akwai kuruciya atare da ita domin hanan da linda sun girme mata, brown skin dinta ya kara wani kyau da sheki ga teddy a hannu wacce mahaifiyar linda ce ta siya mata awani zuwa data yi duba linda ta fita dasu shopping tace kowa ya zabi abunda yake so amma abrar abunda tafara dauka shine teddy, daga nan sai kayan zaki dangin su chocolate da icecream.
"nikam abrar kina badamu, kalli fa kin wani rike teddy sai kace da, kina ajiyewa a hostel mana amma ki kalli mu sha wanna wankan zaki kwabsa mana"
"hanan wallahi kin sa wa teddy na ido ina ruwana da mutane abrar ta fada tana wani murguda baki"
girgiza kai linda tayi tana murmushi duk da batasan mesuke cewa ba amma jikinta ya bata dramman dasuka saba shi sukeyi.
hadaddiyar wurin siyarda pizza da burger suka nufa domin ya aaban ya turowa hanan kudi jiya shine tace lallai sai sun fita outting da friends dinta, hadadd'un kujerun wurin suka zauna waitress tazo ta gaishesu hadi da mika musu menu zaba musu hanan tayi, babu jimawa aka kawo musu hanan da linda asake suke cin abinsu yayinda abrar ta kasa ci sai lemo data sha duk da babu mai kallonta domin kowa harkan gabansa yake amma ta kasa sakewa...
"ya naga bakya ci ne?"
"zan ci" inji abrar
"nikam wallahi be isheni ba bari nayi musu magana su karamin wani"
"a'a hanan zo kici nawa ni nama koshi"
"Allah baki isa ba, ki cinye duka idan bason ganin fushina kika ba" hanan tafada tana shan kunu.
"toh naji masifatu" inji abrar tana dariya
itama hanan dariya tayi, wayarta ta mikawa abrar kana ta nufi wurin masu serving mutane ...

abrar ta dauki yanka daya na pizza zata sa abaki kenan wayar hanan ya fara ringing, ras! ras!! gabanta yafadi kurawa hoton daya bayyana a screen din ido tayi bata ko kiftawa, "shin mutum ne wanna ko aljani?" ta fada abayyane...
har kiran ya katse bata sani ba domin gaba daya kallon hoton yadauke mata hankali wani kiran daya sake shigowa ne yasa ta dawowa tunaninta "ya Aaban" shine sunan data gani a rubuce ana haka sai da hanan ta taho dauke da plate din pizza, " gashi ana kiranki" abrar ta fada "shine baki daga ba?" abrar bata amsa ba ta mika mata wayar...
"hello ya Aaban"
" assalama alaykum" yace mata
"rufe baki tayi da hannayenta tana zaro ido hadi da cewa " sorry ya Aaban wa'alaikumu salaam"
"sorry for yourself, next time i won't repeat my self"
"in sha Allah yaya zan kiyaye"
"good of you, so exams dinku saura nawa?"
" uhmmm saura uku yaya i think nan da two weeks time zamu dawo nigeria, yaya i know kana missing dina shiyasa kake ta tambayana ko?"
daga bangaren Aaban tsadaddan murmushin sa ya saki kana ya katse wayar yana matukar son kanwarsa hanan, domin da ita ne kadai yake zama yayi hira baya ga iyayensa...
bayan sun gama ci suka nufi wuraren shakatawa masu yawa kana suna koma hostel agajiye....

*SOME DAYS LATER*
gaba daya sunyi shirin komawa gida, domin gobe da misalin karfe 8:00am jirginsu ze dira a nigeria, domin linda ta tafi tun jiya abunta, zaune suke abrar ta dafa musu noodles suna ci, sae dai abrar ba ci take ba tsakura take, cikin damuwa hanan " tace abrar lafiya yau gaba daya kinyi looking dull"
hannun hanan ta kamo hawaye masu zafi suka zubo mata " hanan jinake kamar kada na koma gida, jiya nayi wani mafarki dana kasa fassara shi, taba kirjina kiji yanda take bugawa" ta fada tana kamo hannun hanan zuwa kirjinta.
cikin tausayawa hanan ta sake damko hannunta tana cewa" kiyi shiru abrar duk abunda kika ga ya faru da bawa toh yana cikin kaddararsa wallau mai kyau ko akasin haka, kuma in sha Allah alkhairi zaki gani ki cigaba da addu'a kinji"
"in sha Allah" tafada tana goge hawayenta...

"NIGERIA"
ahankali jirginsu ya sauka a airport din Nnamdi azikwe, nan mutane suka fara fitowa, can sai ga hanan na saukowa, ga abrar agefenta cikin shigar cairo abaya peach color babu makeup a fuskarta amma sosai tayi bala'in haduwa, nan suka yi sallama da hanan tana cewa sai tazo gidan su ta gaida ammi, murmushi kadai abrar tayi tana gyada kanta kallon mutane ta fara yi ko zata ga ammi can kuwa ta hango ta tsaye jikin mota ita da alhaji shettima, tunkarosu tafara yi tana murmushi ammi na bayar mata da martani domin duk girman da abrar ta kara da kyau amma ta gane yarta, alhaji shettima kuwa sai yanzu ya shaidata kura mata ido yayi tun daga sama zuwa kasa baya ko kiftawa take wani abu ya darzu aransa.....





SHARE ✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌


NoorEemaan✍

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
written by noor Eemaan
watttpad@noorEemaan

page7-8
sosai yake mamakin girman datayi tamkar budurwa yar shekara 18zuwa20 daidai lokacin abrar ta iso wajensu cikin sauri ta rungumi ammina tana fashewa da kukan farinciki " i so much miss you ammina" tafada tana bata sumbata a kumatu itama ammi sumba ta bata a goshi cikin kaunar tilon yarta, cikin yaren cameroon ammi tace" baki ga daddyn ki bane?" take annurin fuskarta ya dauke ta rasa dalilin daya sa taki jinin ko da ganin alhaji shettima ne, ita kanta tarasa dalilin wanna tsanar data maza amma ya zatayi yana taka matsayin uba ne agareta yanzu, murmushi ta kakaro hadi da cewa " daddy ina wuni na sameku lafiya"?
dan firgigit yayi yana cewa " abrar daddy's girl ya studys? welcome back home"
" thank you daddy ta fada kamar an mata dole kurawa jerarrun fararren hakoranta mai siririn wushirya atsakiya ido yayi lokacin datake magana har be san lokacin data kare maganar ba, ammi ce tace "alhaji kana jina kuwa?
" uhmm na'am mekika ce hajiyata?" ya fada yana wayancewa.
"cewa nayi mutafi gida ko"
" toh toh" yafada yana dan satan kallon abrar dake kallon hanan dake nesa dasu tareda wani saurayi mai kyawun kira saidai bata ga fuskarsa ba domin ya bata baya...
tana cikin motar sai Allah-Allah take ya juyo, domin haka kawai taji tanason ganin fuskarsa ba, amma inaa sai kwantaccen sumbarsa mai dan tsayi domin tsaf za'a iya masa parking...

"

Please Login or Register in order to submit comment