Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar yadda Hassan ya fada wannan future dinsu ne basu kadai ba harda yan kananan yaranta mata. Dole zata yi tunani kafin tayi taking wannan risk din kuma dole zata yi shawara. Shawara da abokin shawarar ta sarkin tunani. Hassan.

Tace "shikenan Hussain ka bani lokaci inyi tunani, duk abinda na yanke kuma shine final babu jayayya"

Ba haka yaso ba, amma yadda take so dole hakan za'ayi.

Bayan ya fita sai ta juyo ta kalli Hassan, a take ya girgiza mata kai.
Ta sauke ajjiyar zuciya tace "bana son discouraging dinsa, ka bani shawara yaya zanyi?"
Ya gyara zama yana kallon carpet yace "dukiyar marayu ce aunty, ina ji masa tsoro, kinsan halin Hussain in ya kafa kasuwancin ma raba wa mutane zai tayi" Ta gyada kai cikin fahimta, ya cigaba da cewa "a shawarce ina ganin a raba, a fitar masa da kasonsa a bashi ya kafa kasuwancin dashi yadda ko sun rushe ba zai rusa mu gabaki daya ba, mu dashi zamu samu abinda zamu dogara dashi. Idan kuma ya zama successful sai a kara masa wata"

Aunty taji dadin wannan shawarar, amma kuma a ranta bata son rabon gadon nan saboda tana ganin kamar raba kan ƴaƴanta ne, taso a ce komai zasuyi tare zasuyi. Amma kuma shawarar abar dubawa ce.

Haka akayi, aka raba gado aka bawa Hussain nasa, sauran kuma suka ajiye suna amfani dashi gurin harkokin rayuwarsu. Hassan yayi amfani da wani kaso a cikin nasa gurin nema wa kansa makaranta.

A lokacin da shekara ta zagayo Hussain ya kira su yana nuna musu lissafin abubuwan da yayi da kudin da ya samu sai su ka ga cewa kudin da yake dashi a yanzu ya ninka wanda yake dasu a waccan shekarar sau huɗu har da doriya. Suka rike baki suna mamaki, shi kuma ya gyara zama yana murmushi yace "na gaya muku ai, Dangote zan zama"

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only

Sai na jiku....👬🏻 TAGWAYE 👭🏻


By


Maman Maama


Free episode


Episode Four: Gimbiya Fatima

Hayin Rigasa,
Kaduna state
Yammata biyu na gani suna shigowa cikin gidan su wanda katangar sa ta kasa ta zube dan haka aka zagaye shi da tsohon langa langa, sai dakuna guda biyu a tsakiyar gidan suma dakunan na kasa ne amma anyi musu plaster da siminti, a gefe akwai bandaki shima rabinsa na langa langa ne kuma babu rufi, tsakar gidan gabaki dayansa kasa ne da bishiya a gefe a kasanta akwai murhu da tukwane da sauran kayayyakin da suke nuna anan ake girki, sai kofar dakunan da akayi yar karamar baranda, wadda simintin ta duk ya mutu yayi ramuka.

A gefen barandar akwai jerin alluna da gwangwanin tauwada.

Jikin yammatan sanye yake da uniform. Kansu daya, kamannin su daya, yanayin su daya dan sai ka kalla sosai, ko kuma wanda ya riga ya sansu sannan ake iya gane banbancinsu.

Dariya suke yi suma, karar dariyar su ta hade da karar kofar gidan da suka bude, wanda ko soro babu, hannayensu sarkafe dana juna suna tafiya ƙafafuwan su suna hardewa cikin na juna.

"Ruqayyah baki da kirki wallahi, hahhaha, kinga yadda kika ruda shi kuwa ya kasa gane ina ne kofar fita daga ajin?" Wadda aka kira da Ruqayyah ta rike ciki tana dariya, sannan tace "kinga ai gobe ma ya kuma dan kaniyar sa....., Ko waye ya gaya masa ni sa'ar sa ce? Harda wani "wallahi Rukee da gaske nake sonki nake yi, ni ban taba kula ko wacce mace ba sai ke" ta karashe maganar cikin kwaikwayon muryar maza.

Suka sake kwashewa da dariya, dayar tace "baki da tausayi wallahi, kika sani ko da gasken yake?" Ruqayyah tace "to ke Sumayya, wadda aka haifo da layar tausayi a wuyanta ba sai kije ki ce kina sonsa ba? Ai ba lallai ne ya gane bani bace ba. Ni wannan me zanyi dashi? Me na sama yaci ballantana ya bawa na kasa?" Sumayya ta tura baki tace "ai ba ce miki nayi ina sonsa ba, ni cika min hannu ke da ba'a fada miki gaskiya" Ruqayyah ta warce hannunta tare da hankada Sumayya gaba "in kina son Allah da annabin sa, daga yau kar ki kara gayamin gaskiya".

A lokacin mamansu ta fito daga daki, doguwar macece kyakykyawa, baka, daga ganinta kasan anyi kyakykyawa a zamanin yarintarta. Amma a yanzu fatarta duk ta yamushe tamkar tafi shekarun ta, bakinta a bushe, hannayenta rudu rudu da jijiyoyi. Gefen rigarta a yage. Ta tsaya da labule a hannunta tana kallonsu tace "to sarakan rigima, ku dai kamar masu ganin hanjin juna ba kwa minti biyar tare sai kun yi fada. Me ya faru kuma?" Ruqayyah tazo ta wuce ta kusa da ita tana kunkuni ta shige dakin da yake kusa da inda maman nasu ta fito, Sumayya ta karaso gabanta tace "Inna Ade barka da gida. Mun dawo. Akwai abinci?"

Inna Ade tayi ajjiyar zuciya, haka suke tunda ta haife su, sunfi shiri da junansu akan kowa kuma sunfi fada da junansu akan kowa, sannan ko wanene kai baka isa kaji sirrinsu ba. Ta amsa gaisuwar Sumayya Sannan ta nuna mata kwano a gefe wanda tun daga wajensa zaka ga ya farfashe, murfinsa daban.

Sumayya ta dauka ta shiga dakin da Ruqayyah ta shiga. "Rukee ga abincin mu. Za muci yanzu ko sai munyi sallah?" Ruqayyah ta ajiye hijab din da take ninkewa a gefen yamusashshiyar katifar su, ta bude kwanon abincin sannan ta saki murfin ya fadi a kan sumuntin dakin tace "again! Yau ma shinkafa da mai da yaji? Yau ko waken babu?" Ta karashe maganar kamar zata yi kuka. Sumayya takaraso tana kallon abincin sannan ta tabe baki tace "ni yunwa nake ji, damuwata shine ba lallai abincin ya ishe mu ba"

Ruqayyah ta cigaba da cire uniform dinta tace "ki haɗa da nawa ki cinye duka, ni ba zanci wannan abincin ba, ni na gaji da cin irin wadannan abincin. Ni na gaji da talauci, ni so nake muyi kudi, na gaji da gidan nan, na gaji da kayan da muke sakawa na gaji da inda muke kwanciya. Na gaji da rayuwa" ta saka kafa tana haurin katifar tasu, sannan ta zauna dabas a gefe ta hade kai da gwuiwa.

Sumayya ta bita da kallo da sakakken baki, sannan ta zauna a gefenta ta jawo kwanon ta juya abincin ta fara ci sannan tace "kinga, kin san dai in baki ci abincin nan ba babu abinda zaki ci ko? Kinsan tabbas da daddare tuwo za'a yi kuma nasan shima cewa zaki yi ba zaki ci ba, ƙin cin fara da mai ba zai saka gasassun kaji suyi fiffike su zo gabanki ba ko?" Jin bata ce komai ba ya saka ta kara cewa "In baki ci abinci ba kuma kinsan ba zaki samu karfin zuwa makaranta kiyi exams gobe ba"

Hakan yasa Ruqayyah ta miki hannu a hankali ta saka a cikin kwanon abincin, sannan ta debi loma ta saka a baki tana taunawa kamar mai cin kashi. Babu abinda bata so irin abinda zai kawo mata cikas a cikin ssce exams din da suke yi a yanzu, dan tana ganin zuwa makaranta shine kadai hanyarta na cikar burinta, burinta na zama mai kudi.

********************************

A bangaren samarin, bayan sunje warehouse din da suka tafi, sun gama duk abubuwan da zasu yi sun dauko hanyar dawowa sai suka biya ta gurin da ake ginin sabon companyn da za'a bude musamman saboda sarrafa rake a mayar dashi zuwa sukari. Wannan shine Company na uku da Hussain zai bude a cikin shekaru biyar da bude companyn sa na farko.

Bayan sun gama sun shiga mota ne yace "bayan wannan kuma sai na fulawa ne zai biyo baya. Shine abinda zai kaini Beijing gobe saboda injinan da nake son siyowa na harkar noma da gyaran alkama har zuwa na sarrafa ta zuwa fulawa duk anyo su sabon design, munyi magana dasu sun turo min hotunan su na gani shine nake so in je ayi launching dinsu a gaba na, injinan suna zuwa *H & H Flour Mills* zai tashi. Kasan Sawun dangote nake takawa" ya karasa cikin sigar tsokana, Hassan ya dauke kansa gefe yana driving dinsa hankali a kwance, amma idanunsa sun nuna cewa tunani yake da yawa a zuciyar sa, ba tare da Hussain ya lura ba ya dauko wata magazine yana bubbudewa da sauri sauri har yazo inda yake so sannan ya nuno wa Hassan "there! Ya kaga wannan babyn?" Hassan yayi wa motar da take cikin page din magazine din kallo daya ya dauke kai gefe yace "ita ce sabuwar da za'a chanza?" Hussain ya ajiye magazine din yace "noooo, ni da akwai wadda nake jira, har yanzu basu sake ta ba, wannan Gimbiya ta nake so inyi wa kyautar ta ranar birthday dinta" Hassan yayi saurin jefa masa wani kallo yace "kyauta? Hussain me yake damunka ne? Anya kuwa ka duba kudin motar nan?" Hussain yayi dariya yace "na gani mana mr tsimilmila. Fatima fa zan bawa, wannan ba komai bane ba indai a kanta ne"

Hassan ya girgiza kansa yace "Hussain. Naga alamar yarinyar nan ta kwace min gurina tun kafin ta shigo a zuciyar ka. Ina jin in akayi auren nan in ina son ganin ka sai na sayi form a gurin ta na cike" Hussain ya sake dariya yana kara kwanciya a kan kujerar sa, ya lumshe ido sannan yace "ba a haife ta ba ba kuma za'a haife ta ba. Yarinyar da zata raba ni da kai bata zo duniya ba ba kuma zata zo ba." Hassan yace "kana raina power ta mata Hussain. Shaidan da kansa ya ce yana tsoron kaidin mata ballantana mu da bamu san ma me duniyar take ciki ba. Mace tana iya raba tsakanin uwa da danta, ko tsakanin uba da yayansa, ballantana mu da muke brothers" Hussain yana taping hannunsa a kan cinyarsa yace "yanzu so kake in rabu da ita kenan?" Hassan yace "no, ba haka nake nufi ba, just be careful, be very careful akan mata" Hussain yayi murmushi yace "mr be careful. I am being careful ai, I have always been. Yarinyar nan fa shekarun mu uku, almost hudu tare da ita, duk wani abu nata daya kamata in sani na riga na sani, wanda ban sani ba kuma in an yi bikin mun shiga daga ciki zan sani" ya karashe maganar da dariya a muryar sa, Hassan ya bata rai yace "kasan problem dinka? Babban problem dinka a rayuwa shine komai a gurin ka abin wasa ne, komai a gurin ka is not serious, ita kuma rayiwa ba haka take ba"

Hussain ya dago kai yana kallon sa yace "ka san wani abu Hassan? Ita rayuwa nan guda daya ce, shi ran nan nan guda daya ne. In ya kare babu refilling. So ko dai kayi enjoying rayuwarka kafin ta tafi ta barka ko kuma kayi spending your entire life being careful ba tare daka mori all the goodies of the life ba, sai kawai rana daya kaga time ya kare maka a lokacin da kake tsakiya da tsara abubuwan da zaka yi nan gaba. What we have is today, what we are sure of is now, ba ayi mana alkawarin gobe ba. Zata iya kasancewa ina bude kofar motar nan zan fita mota tazo tabi ta kaina in mutu and that will be the end of me, babu abinda zai rage nawa sai memories na abinda na aikata, abinda na aikata ba wai abinda na zauna ina ta tunani ina planning cewa zan aikata sati mai zuwa ko wata mai zuwa ko kuma shekara mai xuwa ba. Bani da tabbas din zan kai wannan lokacin. Kuma ba zan iya chanza komai na daga kaddarar rayuwata ba so why worry? In na tafi bayan aiyukana da zanje in tarar a can abinda zan bari a duniya bayan memory na a zuciyoyin masoyana sai kuma sunana. And that's what am working on. Ina so in kafa H &H irin kafuwar da zai jima kafin sunansa ya goge a garin nan, ina so kuma inyi aure, auren nan daga zuriya mai karfi irin zuriyar masarautar kano, in hada jini dasu in samu yaya yadda zan bar bayana. Wannan shine burina, wannan kawai shine burina"

Hassan yayi packing motar a compound din gidan su sannan ya juyo yana kallon Hussain yace "nima duk ina da wadannan burikan Hussain, musamman burin aure da samun zuri'a kafin barin duniya, amma ni ban damu da familyn da zan hada zuri'a da su ba, ni dai fatana kawai shine in samu mace ta gari, mai kyawawan halayya, mai addini, wacce duniya sam bata gabanta balle abinda yake cikinta, reserved, wacce ba zata damu da abinda nake dashi ba balle abinda zan bata. Mai zurfin tunani, mai ilimin addini dana boko, Wacce......" Hussain ya daga hannunsa yace "in short, kafi son ka samu mace mai irin halayen ka.....boring.....to bara kaji, Gimbiya ta ma tana da duk wadannan characters din daka lissafa. But wait a second...." Ya matso da fuskar sa kusa da tashi yana kare masa kallo yace "wannan dogon lissafin da kake yi gaya min? Ta samu ne?" Hassan ya dungure masa goshi yace "tukunna dai, still searching..." Hussain yayi tagumi dramatically da hannu daya yace "still thinking about it... Planning... thinking and re planning.... Malam if you want to do something, do it now" Hassan ya fito daga motar yana cewa "sai kayi tayi yanzu din ai, gobe kuma kazo kana nadama" Hussain ya fito shima yana cewa "gwara inyi yanzun tunda bani da tabbas din zan kai gobe. In ma nayi nadamar a goben sai in sake yin wani".

A palo suka tarar da Aunty da yammatan ta ana ta hira, mostly hirar jami'a da Zulaihat take shirye shiryen tafiya, Nafisa tana ta bata tsoro akan irin wahalar da ake sha ita kuma tana korafin bata son zuwa, nan suma suka shiga cikin hirar Hassan ya shiga team din tsokanar Zulaihat Hussain kuma ya jawo ta jikinsa yana lallashinta. "Kinga autar Aunty, kije kiyi semester daya, in kika ji bata yi miki ba kina dawowa ki gaya min shikenan kin daina ta, sai ki zabi duk makarantar da kike so koda kasar waje ne zan kaiki. Ita rayuwar nan mai sauki ce, babu wani takura a cikin ta".

Washegari da sassafe Hussain ya tafi kano zance gurin Gimbiya. A jirgi ya tafi, dan haka cikin yan mintina ya isa kuma ya zarce direct zuwa fada ina Gimbiya Fatima ta aiko aka tarye shi aka kai shi masaukin da ake saukar baki irinsa sannan aka cika masa gabansa da kayayyakin abincin karin kumallo tunda tasan bai karya ba kuma tasan sauri yake yi dan tasan da tafiyar da zaiyi a yau. Kusan komai na Hussain Gimbiya Fatima ta sani.

Sai dai a bangaren Hussain din shi ba wai abincin ne a gabansa ba duk kuwa da cewa kamshin abincin ya gama cika masa ciki ya kuma tayar masa da yunwar da take kwakular hanjinsa, amma shi abinda yake gabansa shine ganin fuskar gimbiyar tasa, dan haka ya dora idanuwansa a kofar da yasan tanan zata fito, a haka har sai da ta fito din, sai ya samu knsa da mikewa tsaye yana yarfar da hannayensa, fiskarsa dauke da madaukakin murmushi wanda ya samu tarya da makamancinsa daga fuskarta.

Gimbiya Fatima diya ce a gurin maimartaba Sarkin Kano na wancan lokacin, kyakkyawa ce, mai kyakkyawan jiki wanda yaji komaida ake bukata a jikin mace. Hutu, gata, ilimi, mulki sun gama ratsa duk wata gaba ta jikinta. Kallo daya zaka yi mata zaka fahimci cewa yar sarauta ce ba wai sai an gaya maka ba kamar yadda magana day azata fada maka zaka fahimci cewa mai ilimi ce ita ba sai anyi maka bayani ba. Hanklain ta da nutsuwarta ya saka babanta yayi burin had ta aure da wani sarkin ko kuma wani dan sarkin dan ya karfafa karfin masarautar sa amma Fatima already idanuwanta suna kan Hussain. Dole mahaifinta ya bawa Hussain dama, tare kuma da fatan cewa ba zai bashi kunya ba.

Sun hadu ne a airport, Hussain ya dawo daga daya daga cikin tafiye tafiyen sa ita kuma zata kaiwa yaruwarta da take aure a Egypt ziyara. Yana cikin waya da Hassan bai gani ba suka yi karo, wayarsa ta fadi ita kuma jakar hannunta ta fadi tarkace ciki suka zube kasancewar jakar ba'a rufe take ba. Da sauri ya sunkuya ya tattaro mata kayayyakin ta ya zuba mata a jakar shima ya dauki wayarsa,a ransa yana saka rn zata sunkuyo su debe tare tunda ba laifinsa bane shi kaɗai, amma bata yi haka ba. Sai da ya gama ya mike zai mika mata sannan ya kalli fuskarta kuma a lokaci daya yasan cewa she is the one. Kuma kallo daya yayi mata yasan cewa ba zata kula shi ba, ko sunan ta ba zata gaya mishi ba ballantana phone number dan haka sai yayi dabara ya dauke wayarta ita kuma ya saka mata tasaa cikin jakarta. Ya mika mata tare da cewa "am sorry" sai data jima kafin ta motsa bakinta tace "it's okay" sannan without a second look ta juya tayi tafiyar ta.

Shi kam zuciyarsa fal murna ya fito daga airport din, sai daya fito sannan ya tuna cewa bai gaya wa abokin sa da yazo kano gurinsa cewa gashi nan yazo ba kuma gashi yayi musayar wayarsa, a dolensa ya nemi taxi.

Tunda ya koma kaduna yake kiran layin wayarsa amma shiru, sai tunani yazo masa cewa maybe kasar ta bari dan haka babu network. Option daya da yake dashi shine ya jira a kira ta ko kuma ita tayi amfani da wani layin ta kira layinta, amma shima shiru. Gashi kuma wayar tata da pin ballantana ya bude shi yayi kira da number dinta.

Kwana biyu kullum yana zaune da waya a hannunsa yana kallon hoton ta dake kan screen din yawar har sai daya haddace duk wani angle da wani hill da wani valley na fuskarta. Sai da yaga yana neman zautuwa sannan ya yi dabarar cire sim card dinta daga wayar ya saka a wata wayar ya nemo contacts dinta, a ciki ya ga "kid sis" sai ya kira, a nan ya samu bayanin cewa tana sauka a Egypt ta kira waya gida ta sanar cewa tayi loosing phone dinta dan haka kar wanda ya neme ta. A gurin sister din nata, da yake mai surutu ce ya samu duk bayanan da yake bukata kuma ita tayi guiding dinsa har zuwa sanda Fatima ta dawo kasar sannan ta hada su. Shi kuma yayi amfani da duk kanin carm dinsa da duk dadin kalaman sa da kuma good looks dinsa ya sayi zuciyar Fatima Zahra.

Bai kuma taba gaya mata komai dangane da dukiyar da yake da ita ba har sai data riga ta karbi soyayyar sa, daya gaya mata kuma bata nuna cewa it matters ba, sai dai tana iyakacin kokarin ta gurin supporting dinsa da kara masa kwarin guiwa da bashi shawarwari akan business dinsa.

Matsalar ta daya shine Hassan, tun ranar farko da Hussain yazo dashi gidan ta fahimci cewa Hassan baya son ta kuma bata san dalili ba, amma abinda ta sani shine she is never going to change herself saboda shi, zata yi kokarin kyautata masa, a hankali maybe zai so ta din. Sannan kuma bata taba yi wa Hussain complain ba akan hakan. Kuma a hankali din ta fara ganin Hassan yana saukowa, har in suna waya da Hussain ya kan karba su gaisa. Sai ta fahimci cewa ba wai sonta ne baya yi ba, shi mutum ne mai studying abu first kafin ya karbe shi. Shi mutum ne wanda yake very careful before making choices dinsa.

A lokacin tana level one, a yanzu kuma ta kammala karatunta, dan haka bayan ta zabe shi a matsayin wanda zata aura sai aka bashi damar fitowa kuma ya fito din, sannan aka saka musu rana.

Kafafunsa ya samu da takawa zuwa inda take a tsaye ta ci kwalliya da lace dinkin bubu, tayi daurin dankwalin ta da ya zauna das a saman cikakkiyar sumar kanta. Wuyanta, kunnen ta da hannayen ta sanye da gold da yake haskawa tamkar yadda murmushin kan fuskarta yake haskawa. Yammata biyu ne a bayanta wadanda suka rako ta, suka durkusa suna gaishe da Hussain, ya amsa musu da murmushi amma ba tare daya dauke idonsa daga kan gimbiyar sa ba.

Sai da suka yi musu sallama suka tafi sannan cikin sassanyar muryarta tace "welcome, Mi Amour" bai amsa ba, tace "kayi kyau sosai" ya cire hularsa ya shafa gashin kansa sannan ya mayar da hular yace "kyau, in kina guri Fatima har ana iya ambatar wata kalma wai ita kyau?" Ta wuce shi tana bade shi da kamshinta ta zauna a edge din 3 sitter, ya zagayo shima ya zauna a dayan edge din sannan ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya dauke idonsa daga kanta ba. Tace "to ka gama kallon nawa in tashi in zuba maka abinci?" Ya sake shafa kai yana murmushi, ba ya gajiya da kallonta, in dai tana guri to idonsa baya ganin komai sai fuskarta, duk sauran abubuwan da suke gurin suna yi masa duhu ne.

Ta tashi ta jawo table gabansa sannan ta dauko dan madaidaicin bowl ta bude wani food warmer ta zubo masa farfesun naman ragon da tayi masa ta ajiye akan table din sannan tace "kaci wannan da duminsa zaka ji dadinsa" sai kuma ta bude wani ta zuba masa wainar shinkafa ta ajiye kusa da naman sannan ta jawo wani madaidaicin tray da akayi wrapping da foil paper ta bude wani lafiyayyen potato pritata da yaji naman kaji da vegetables ta ajiye masa shima tare da jera masa knife da fork sannan da dauko mug tace "tea ko coffee?" Ya saki baki yana kallonta yace "duk wannan wai a ciki na zan saka su?" Ta langwabe kai tace "eh mana, in dai ba so kake duk wahalar dana tashi nasha a kitchen tun assuba ta tashi a abanza ba" ya ce "wai Fatima kina nufin ke kika yi wannan girkin da kanki" tace "to wa zan bawa tayi wa mijina abinci? Tea ko coffee?" ya jawo bowl din naman ya debi romon yayi tasting sannan yace "coffee please" ta hada masa tazo ta durkusa ta mika masa sannan ta koma gurin ta ta zauna tana kallonsa yana cin naman kamar zai hada har da hannunsa, ya juyo suka hada ido sai suka yi dariya a tare, yace "lallai sai nayi wa Hassan takeaway din naman nan, kin san shi kure ne" tayi murmushi tace "kace masa ya sha kurumin sa, duk sanda na shigo gidan sai yaci nama har ya ture" ya ajiye bowl din yana kallonta a ransa yana jin tamkar ya jawo watanni hudun da suke gabansu yace "Fatima, wallahi kinyi a rayuwa"

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only

Sai na jiku....👬🏻 TAGWAYE 👭🏻


By


Maman Maama


Free Episode



Episode Five : Adam

A bakin kofar makarantar jeka ka dawo ta gwamnati ta yammata, tagwayen ne a tsaye suna jiran abin hawa.

"Kinga Sumayya, na gaya miki fa babu me napep din da zai dauke mu tun daga nan zuwa gida a naira hamsin, ai ba baban mu ne ya saya masa ba" Sumayya tace "kai Rukee, shekarar mu nawa muna tafiya gida daga nan a naira hamsin ɗin? Kullum ba goyo muke yi mu basu hamsin ɗin ba?" Ruqayyah ta fara tafiya tana barin bakin gate din tana cewa "a da kenan. Yanzu ƙatin ƙatin da mu zamu yi goyo? Ni wallahi na gaji ba zan iya da wannan abin kunyar ba, yanzu ni ina labor prefect kawai sai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment