Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yara su ganni ina goyo a napep? Ke kina ganin hakan dai dai ne?" Sumayya tana bin ta a baya tace "to labor prefect, sai ki gaya mana yaya zamu yi? Hamsin din ce zata haifi wata hamsin ɗin ko kuma mune zamuyi aman wata hamsin ɗin" Ruqayyah ta ja hannuta suka yi sauri suka shige gaban wata taxi data tsaya a gaban makarantar da niyyar daukan dalibai. Wasu daliban duk suka shiga baya.

Sai da mai motar ya tayar ya fara tafiya sannan sumayya ta rada wa Ruqayyah "kudin mu fa ba zai kai ba, gwara mu gaya masa tun kafin muyi nisa in yaso ya karo wasu mu zauna tare, ko a cinyoyin mu mu dora su" Ruqayyah ta ture ta tana gyara zamanta tace "sai dai a dora miki a cinyarki ba dai a tawa cinyar ba. Bari kiji in gaya miki, hamsin din ma ni bani da niyyar bayarwa ajiye wa zanyi gobe in an bamu kudin motar sai mu hada da shi dan ya ishe mu" Sumayya tace "to shi wannan ta yaya zamu sallame shi?" Ruqayyah ta kalli driver din ta gefen ido sannan ta tabe baki tace da Sumayya "look at him, ba bahaushe bane ba. Dan haka duk baya jin abinda muke cewa. Muna zuwa gida sai mu nuna masa kamar mun yar da kudin a hanya bamu ganshi ba, sai mu bashi hakuri"

Sumayya ta leka ta bayan Ruqayyah ta kalli driver din. Saurayi ne daga ganin sa bai dade da gama secondary ba, that's in yayi secondary din, kana ganin sa kasan ba bahaushe bane ba amma Sumayya ba zata iya tantance wanne yaren bane ba. Kuma a fuskarsa babu alamar cewa yana jin abinda suke cewa. Fari ne tas kuma jikinsa fes yake babu alamar wahalar duniya a tattare dashi dan haka daga gani kasan asarar naira dari ba zata dame shi sosai ba amma kuma a ranta tasan naira darin nan still hakkin sa ce, ta tuna da jerin waazin da Inna Ade take yi musu kullum akan cin haram, cin zali, daukan alhakin mutane, ballantana wannan bayan cin haram din ma kuma akwai karya, gaskiya zunubin yayi mata yawa.

Ta dawo da dubanta kan Ruqayyah tace "Rukee babu kyau fa, kinsan babu kyau" ta harare ta "to shehiya malama Sumayya. Sai ki zaba, ko dai ki karyata ni ki tona min asiri ni yaruwarki kuma har abada ba zan manta ba ko kuma ki yi shiru kici zalin inyamurin da ba kara ganin sa zaki yi ba a rayuwarki. Ai ina sane muka shigo motarsa, sai dana kalle shi sosai na zabe shi sannan muka shigo" Sumayya tace "to yanzu in ma mun gaya masa haka, what if yaki yarda yace sai mun biya shi kudinsa? Idan ya fara yi mana hayaniya fa a unguwa ya zamuyi dashi?" Ruqayyah tayi murmushi tace "da zarar naga ya fara kokarin daga murya zan zunduma ihu ince ya rike ni yana tattaba ni" ta kare maganar da murmushin mugunta a fuskarta.

Sumayya ta sunkuyar da kanta kasa tana kallon hannayen su da suke cikin na juna ita da Ruqayyah. Tasan Ruqayyah kusan fiye da Inna Ade data haife su, tasan kuma zata iya aikata abinda tace ɗin, but it is not right, in ta biye mata ita ma ta zama irinta kenan kuma kamar ta kara encouraging dinta kenan. A hankali ta zare hannunta daga cikin na Ruqayyah ta juya tana kallon titi.

Luckily sai da duk aka sauke sauran passengers din sannan aka zo bakin layin su Rukee. Suka nuna masa inda zai tsaya ya tsaya sannan ya juyo sosai yana kallonsu yace "your money please, 100 for the both of you"

Ruqayyah tayi pretending as if tana nemo kudi a jikinta, sai kuma ta hau duba jakarta tana da bincike, in ka kalli fuskarta zaka iya rantsewa da Allah cewa da gaske neman kudin take yi, sannan ta dago kai tana kallonsa da budaddun idanunta da suke nuna alamar tsoro tace "I can't find it. I can't find the money." Ta sake shashshafa aljihunta sannan tace "I swear I put it inside my pocket. I must have lost it at school" ta langwabe kai "we are sorry sir. Please dash us the money".

Sai ya dauke kansa gefe yace "check again. Maybe you hid it somewhere" sumayya ta juyo tana kallonta tace "Rukee ki bashi hamsin din, sai mu roke shi yayi hakuri in yaki yin hakurin sai inje gida in karbo masa a gurin Inna Ade" Ruqayyah ta harare ta tace "chafdi, wallahi ba za'a bashi din ba, so kike Inna Ade ta saka mu a gaba da nasiha"

Sai ta juya gurin drivern da fuskar tausayi tana ta shashshafa pockets dinta "I can't find it. It must have been stolen at school" ya juyo yana kallonta sannan ya kawo hannu kamar zai taba ta yace "let me help you check. Da azama ta rike hannun daya miko, idanuwa a waje, sai ya kawo daya hannun, Sumayya tayi saurin rike shi shima. Abin duk ya faru ne in seconds. A take kuma Ruqayyah ta bude baki da niyyar zunduma ihu, sai Sumayya ta saka hannu ta rufe bakin tana girgiza mata kai sannan ta juya tana kallon driver din tace "please, please sir, we are sorry, let me go and get you the money"

Sai ya zare hannayensa daga nasu yana kallon Ruqayyah yace "ki bata hamsin din jikin ki sai ta karbo wata hamsin din ta kara akai" sai tsoron fuskarsu ya juye zuwa mamaki. Ya daga kafada yace "I might not be hausa, but ina jin hausa kamar jakin kano, dan haka you picked the wrong target" ya bude musu kofar motar yace "get out of my car. Da nayi niyyar ganin karshen drama dinki, but naji tausayin twin sister dinki dan naga kamar ita ta gari ce" a salube Sumayya ta fito daga motar, Ruqayyah kuma ta fito tana kumbura baki sannan ta juya tana kallon sa ta rike kugu tace "aikin banza aikin wofi, dan kana jin hausa kuma sai me? Dan kaji abinda muka ce sai me? Naira darinka din banza, drivern taxi kawai"

Sumayya ta sunkuyo ta window tace "dan girman Allah kayi hakuri. Ni ka tsaya ma dan Allah in karbo maka kudinka a cikin gida, ta boye hamsin din kuma nasan ba bani zata yi ba" ya juya hannun sa yace "ki barshi kawai. Na bar miki, ita ma na bar mata hamsin din tayi arziki da ita. Sannan ki fada a gida a kara muku kudin mota in ba haka ba wata rana zaku samu wanda zai daki kudinsa. Sannan ki saka ido akan twin sister dinki, bata da kirki" ta gyada kanta da sauri yayinda Ruqayyah take neman irin zagin da zata yi masa, da sauri sumayya tace "dan Allah kar ka kulata" ya kalli Ruqayyah yana tayar da motarsa yace "I will not, am not her mate" daga nan yayi tafiyar sa.

Ruqayyah ce ta fara shiga gidan su a fusace kamar zata tashi sama. Inna Ade tana gaban murhu tana zubawa yan samarinta abinci wadanda suma dawowarsu kenan daga tasu makarantar.

Duk da cewa daga Ade har Yusufa basuyi karatun boko ba hakan bai hana su saka nasu yayanba, amma sai sun tabbatar cewa sunyi sauka kuma sunyi hadda. Hatta karamin su zunnur yayi hadda, duk iskancin Ruqayyah babu ayar da zaka bude mata ba tare da ta karanta maka ba. Bayan Alqur'ani kuma sun san sauran littattafan addini.

Bata ko kalli inda suke ba ta wuce su da sauri tayi hanyar dakinsu. Suleiman yace "kububuwa! yau kuma wanne mai tsautsayin ne yayi wasa da jelar damisa?" Zunnur ya kwashe da dariya. Inna Ade tace "Allah yasa ta jiyo ku, in ta kama ku tana jibga babu wanda zan ceta" Sumayya ta shigo da sallama, ta zarce kan baranda ta ajiye jakarta da robar abincin su sannan ta dawo inda suke ta gaishe da Inna Ade, Suleiman yace "wa ya taba Rukee ne yau" Sumayya tace "ina ruwanka? Bana son tsegumi" daga nan babu wanda ya kuma tambayarta dan sun san babu wanda zai samu amsa, sai dai ita kanta bata iya bin Ruqayyah zuwa daki ba sai tayi sallar ta anan sannan ta debi ruwa ta fara wanke musu uniform dinsu wanda zunnur ta aika ya dauko na Ruqayyah, sai data gama sannan ta daukar musu abincin su ta shigar musu dashi daki, tasan dai zuwa lokacin Ruqayyah ta sauko, dama ita saurin hawa ne da ita da kuma saurin sauka.

Ta tarar da ita a kwance tana karanta littafinta na makaranta. Ta zauna ta bude shinkafa da miyar da akayi har da yankakken salak a sama. Rukayya ta mike zaune tare da karbar chokali a hannun sumayya suka fara ci babu wanda yayi magana, sai da suka kusa gamawa sannan Ruqayyah tace a hankali "duk laifin Baba ne" Sumayya ta dago kai cikin rashin fahimta tace "laifin baba kuma? Menene laifin nasa? Shinkafar ko miyar ko kuma salak din?" Ruqayyah tace "talauci. Talaucin da muke ciki. Shine ai yake da alhakin kula damu, shi yake da alhakin nema mana abinda duk muke bukata a rayuwa amma kuma ya gaza, ya gaza sauke abinda yake dole ballantana abinda yake ganin ba dole bane ba" sumayya tace "kina da hankali kuwa Ruqayyah? Kin manta Allah? Ina karatun ki ya tafi? Shin arziki da rashinsa ba duk na Allah bane ba" Ruqayyah ta ajiye spoon din hannunta tace "Allah ba zai taba taimakon wanda ba ya taimakon kansa ba. Allah ba zai taba baka abu in baka tashi ka nema ba" Sumayya tace "amma kuwa in zaki yiwa Baba adalci ke kanki kinsan yana neman ai. Kinga yadda hannun Baba yake kuwa? Kanta ce fa a hannunsa saboda tsabar leburancin da yake yi. Shine aikin labura shine gini, har dako fa baba yi yake yi, kuma duk dan mu yake yi dan muci abinci muyi suttura muje makaranta. Tunda muke bamu taba kwana da yunwa ba, shin ba zamu gode Allah ba? Shinkafa muke ci da rana, gidajen masu hali irin na Baba nawa ne suke samun shinkafa a sati? Jiya fa ina jin Inna ade taji kina complain kin gaji da cin mai da yaji shine fa ta karbo wankau tayi na tabbatar kudin da aka bata shine ta siyo kayan miya da salak din nan tayi mana. Kuma duk dan kar muga gazawar sune a matsayin su na iyayen mu. Kar ki zama butulu mana"

Duk maganar da Sumayya tayi abinda Ruqayyah taji kawai shine kalmar butulu, "nice butulun ko? Ni zaki kira da butulu ko? To ki jira, in dai nice muna nan dake zaki ga nayi kudi. Gabaki daya gidan nan sai na saka an rushe shi anyi mana sabo, an zuba mana kayan alatu irin na gidajen masu kudi. Inna Ade sai ta manta da cewa ta taba yin wani abu wai shi wankau ballantana har a goranta min a saboda shi" Sumayya tace "oh oh, Inna Aden ce zata yi miki gori? Kenan biyanta kike nufin zakiyi na hidimar da tayi dake? Duk kudin da zakiyi Ruqayyah kin isa ki biya iyayenki wahalar da suka sha a kanki? Ballantana ma baki da tabbas din zaki yi kudin"

Nan take rigima ta kuma kachamewa. Inna Ade ta shigo ta tsaya tana kallonsu. "Ya ilahi, yaran nan ko hanjin junan su suke gani ne ni ban sani ba? Ba yanzu kuka gama wani fadan ba har kun sake wani? Kuma in an tambaye ku me ya hada ku ba zaku fada ba ballantana a sulhunta ku?" Ruqayyah ta mike zata fita daga dakin tana kunkuni. Inna Ade ta jawo hannunta "ke Ruqayyah ban hanaki in ana miki magana ki fita ki bawa mutane guri ba? Wato bama zaki tsaya kiji abinda za'a gaya miki ba ballantana kiyi aiki dashi ko?" Sumayya tace "kiyi hakuri Inna" Inna tace "ke ce bakinta? Ita bata da bakin magana ne?" A hankali Ruqayyah tace "Allah ya baki hakuri" Inna Ade ta sake ta ta fita daga dakin zuciyarta babu dadi.

Sai da suka yi sallar laasar suka yi wanka suka shirya sannan suka fito tsakar gida, yau thursday dan haka masu zuwa daukan karatu basu shigo ba sai Ruqayyah ta dauki tsintsiya ita kuma Sumayya ta harhada kayan wanke wanke suka fara gyaran gidan. Suna gamawa Sumayya ta hada wuta ta dora tuwon dare Ruqayyah kuma ta dauko dutsen guga ta hada wuta ta fara goge musu kayan gugar su daya taru. A lokacin Inna Ade ta rufe Alqur'anin da yake gabanta tana karantawa tunda tayi laasar, ta shimfida tabarma kusa da inda Ruqayyah take guga ta zauna. Kamar hadin baki sai ga Sulaiman ya shigo tare da Zunnur, suka zauna suka gaishe da Inna Ade suma bata labarin shagon da suke zuwa koyon dinki.

A lokacin kuma Baba ya shigo, da sauri yan samarin suka mike suna karbar kayan hannunsa suna yi masa sannu da zuwa. Ya amsa yana zama akan tabarma kusa da Inna, Sumayya ta ajiye rariyar hannunta da take tankade da ita ta wanke hannun ta ta debo masa ruwa a randa. Ya karba yayi mata godiya, yasha ya ajiye kwanon sannan inna ta gaishe shi, yace "yauwa Sa'adatu. Ya gida?" Ta amsa da fara'arta, "ka dade yau baban biyu, har na fara tunanin in aika gidan maman Minal in aro wayarta a kira ka muji ko lafiya" Yace "wallahi na je gurin wannan neman aikin da na gaya miki ne, wannan sabon kamfanin da aka bude, *H & H* to naji sanarwa a gidan radiyo cewa sun fara daukan kanana da manyan ma'aikata shine naje ko Allah zai sa a dace su dauke ni ko aikin gadi ne inke yi musu, ko wani aikin dai daban, aikin dai da za'a ce mutum kullum in ya fita yana da aiki kuma duk wata zai samu albashinsa" Inna tace "insha Allahu muna da rabo a aikin nan. Mun gaya wa Allah kuma insha Allahu zai dube mu" yace "ameen" sannan ya jawo ledar daya shigo da ita yace "ga garin masara nan na auno mana uwar biyu, sai a lallaba ya kai mu wani satin" ta shafa ledar tana jin yawan garin tace "wannan baban biyu ai har wani satin zai kaimu in sha Allah. Mungode Allah ya kara budi, jazakallah bi khair" yace "ameen. Amma bance ake yin tuwo kadan ba dan kar gari ya kare, a yi isashshe wanda yara zasu ci su koshi da safe a dumama suci kafin su tafi Makaranta. Bana so suke zuwa makaranta da yunwa" Inna tana murmushi tace "lallai masu 'ya'ya" ya jawo wata karamar leda yace "wannan busasshen kifi ne na siyo dan ake saka wa a cikin miyar kaɗi, saboda yara suji dadin cin ta" Inna Ade tace "Lallai yara yan gatan baban su, komai dai ace dan yara, ni ba a yin komai dan ni" ta fada da sigar tsokana, Zunnur yace "ai sai dai kiyi hakuri Inna mum kwace miki power a gurin Baba" duk sukayi dariya banda Ruqayyah da take ta gugar ta kamar bata gurin.

Inna ta tashi ta dauko masa abincinsa ta kawo masa, yana bude wa yace "lala, uwar biyu miya akayi mana haka harda salak? A ina kika samu kuɗi?" Ta dan bata rai tace "saboda nasan kana so shi yasa na danyi wani aiki na samu kuɗi nayi dan in faranta maka. Ni dan kai nayi ba dan yara ba" duk akayi dariya har da baban shima, sai kuma yace "to ai ke nasan baki da matsala, tunda ke kika zabe ni kika ce kinji kin gani, su kuwa yara basu suka zabi zama yayan mu ba, bana so suke sha'awar iyayen wasu suna cewa ina ma dai sune nasu" Sulaiman yace "haba dai Baba, ni da ace za'a sake haihuwa ta ace in zabi iyaye ai da ku zan zaba sau goma, kunyi mana komai sai fatan Allah ya saka muku da alkhairi ya bamu ikon yi muku biyayya da faranta muku".

Sai a lokacin Baba ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta gugar ta kanta a kasa yace "Hassana. Baki ga na shigo ba ko gaishe ni baki yi ba?" Ta dago da murmushin yake a fuskar ta tace "na gaishe ka Baba, baka ji ni bane" ya girgiza kansa kawai ya fara cin abincin sa.

Sai da yayi nisa da cin abincin suna yar hirarsu da Inna sannan ya dago kai yana kallon Sumayya yace "Hussaina yaya jarabawar taku? Ana dai kokari sosai ko?" Ta rufe tukunyar data ke juyawa ta taho tana cewa "Baba alhamdulillah, ai mun kusa gama wa ma insha Allahu nan da sati biyu zamu kammala gabaki daya" Ruqayyah ta ajiye iron din hannunta wanda ta gama guga dashi tace "nan da sati biyu zamu gama Neco Baba, saura Waec" yayi shiru sannan yace "ita ce wadda ba'a biya muku bako?" Sumayya tayi saurin cewa "ai bata da wani muhimmanci Baba. Kaga Minal ita fa waccan shekarar ta gama amma har yanzu bata karbo waec dinta ba tunda taci duk abinda ake bukata a Neco" Ruqayyah ta zauna akan tabarmar tace "muhimmancin ta daya shine idan mutum bai ci Neco ba, ko kuma yaci rabi bai ci rabi ba, zai iya hada wa da waec sai ya samu duk abinda ake bukata a jami'a" Baba ya gyada kai kawai bai ce komai ba, amma fuskarsa ta nuna damuwa.

Inna Ade tace "maganar jami'a fa naji kuna yi, ita minal din bata gaya muku uban kudin da mamanta take bani labarin an kashe kafin a saka ta a jami'a ba? Ita kadai ma ballantana ku biyu?" Baba yace "abin ai na Allah ne, insha Allahu, indai sunci wannan jarabawar kuma suna so zasu je. Ko ba zan iya turasu su biyu a lokaci daya ba sai in saka daya wata shekarar sai a saka dayar. Abin ai na Allah ne"

Friday bayan sun tashi daga makaranta, suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa sai ga wata taxi ta tsaya a gaban su. Ruqayyah ta sunkuyo da niyyar yi wa driver magana sai taga mutumin ranar nan ne, ta ja tsaki tare da komawa baya tana hade rai. Sumayya ta leka itama ta gashi zata matsa taji yace "ku shigo in kai ku" Ruqayyah ta leko tace "ko babu motocin haya a titin nan gwara mu tafi a kafa" ta kuma komawa baya ta tsaya. Yace da sumayya "ke shigo in kaiki" ta girgiza kanta "bazan iya tafiya ba tare da sister ta ba" yace "I understand" tace "mungode bawan Allah" yace "yes, ni bawa ne na Allah but sunana Adam" Ruqayyah ta leko "babu wanda ya tambaye ka sunanka saboda babu wanda ya damu daya sani" Sumayya ta kalle shi tana murmushi tace "Sunana Sumayya, yar uwa ta kuma sunanta Ruqayyah,".


Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only👬🏻 TAGWAYE 👭🏻


By


Maman Maama


Free Episode



Episode Six : Chloroform

Hira tayi dadi tsakanin Hussain da gimbiyar sa, har lokaci ya tafi ba tare daya sani ba, tun suna kan kujera suna hira har suka sauko kan carpet suna ta magana cikin yiwa juna murmushi da dariya, kasancewar duk su biyun masu fara'a ne sosai. Suna cikin hirar ne alarm ya kada a wayar Fatima, ta dauka ta kashe tace masa "lokacin tafiyar ka yayi kar kayi missing Flight dinka" yana kallonta da mamaki yace "wai kina nufin har alarm kika saka min?" Ta juya idonta tace "nasan zamu iya mantawa, kuma tafiyar ka tana da muhimmanci, bana so inso kaina da yawa"

Ya jinjina kansa yana jin soyayyar ta tana karuwa a zuciyarsa, sosai yake son yadda take gudanar da al'amuran ta, komai nata a tsare yake, komai nata a nutse take yinsa. Har airport ta kai shi sannan sukayi sallama a ransu suna jin kamar kar su rabu, Hussain yana ji a jikinsa cewa in sukayi aure duk tafiyar da zaiyi tare da ita zai ke yi tunda dai matarsa ce kuma babu abinda zata zauna tayi a gida.

Cikin sauri yaje gida, ya tarar Hassan ya gama hada masa kayan tafiyar sa ya zuba masa a mota dan haka wanka kawai yayi ya chanza manyan kayan jikinsa zuwa ƙanana sannan ya shiga mota Hassan ya mayar dashi airport. A hanya babu wanda yayi magana har suka je, haka kawai Hussain yaji jikinsa yayi sanyi and for the first time tunda ya fara tafiye-tafiye yaji cewa baya son tafiya, yaji cewa baya son ya rabu da danuwansa.

Sai da Hassan ya karkada masa key a fuska sannan ya juyo yana kallonsa yana kirkiro murmushi. Hassan yace "what's wrong? Tsoron jirgin kuma kake yi yau ko me?" Hussain ya duba agogon sa yana noticing mintinan daya rage kafin jirgin su ya tashi, wata zuciyar tana gaya masa ya juya ya koma gida amma sai yayi sauri ya girgiza kansa yace da Hassan "take care of yourself bro. Bazan jima ba dan bana jin zan wuce sati daya. Duk abinda ya kamata ayi to ayi kawai kar ace sai an jira ni. Ka bawa Aunty hakuri kace tafiyar ta zama dole ne bana so auction din nan ya wuce ni" Hassan ya rike dariyar da take taso ma sa yace "Badan na sanka ba da sai ince kamar tsoro nake gani a fuskarka kuma nake ji a muryarka, amma na sanka kuma nasan Hussaini baya jin tsoron komai, shi jarumin jamurai ne" Hussain yayi murmushin da ya tsaya a lips dinsa yace "bana jin dadi ne kawai. Amma nasan kafin mu sauka zan ware" ya sake kallon abogon hannunsa sannan yace "take care of yourself bro" Hassan yace "you already said that bro" sai hussain yayi murmushi yana bude hannu yace "okay take care of everyone at home" sannan ya bude kofa ya fita.

Hassan ya bishi da kallo har ya shiga kofar departure hall, sai daya daina ganin sa sannan ya tayar da motar ya bar gurin yana jin part of him ya tafi tare da Hussain. Amma dama ya saba da wannan feeling din, kullum in basa tare da Hussain sai yaji kamar rabin sa ne a gurin rabi kuma yana inda Hussain din yake, tun suna yara haka yake ji, duk fadan su duk rigimar su amma duk duniya babu abinda yake so sama da Hussain, baya jin kuma akwai wani abu da zai raba shi da Hussain.

Direct gida ya koma, yana ta lissafin abubuwan da suke gabansa abubuwan da ya kamata ya yi kafin dawowar Hussain daga Beijing. Dazu dai yayi wa kananan ma'aikatan da za'a dauka aiki a sabon kamfanin interview kuma har ya riga yayi grading dinsu, sai ya zauna zai yi final zabe sannan sai a kira wadanda aka zaba din a sanar musu. Shi komai yafi so yayi a hankali, ya tuna yadda suka yi da Hussain a lokacin da suke maganar daukan ma'aikatan. "Kaga Hassan, don't stress yourself akan maganar nan. Kananan ma'aikata ake magana fa ba manyan ma'aikata ba, ba takardu zaka duba ba ba komai ba, kawai just look at their physique ka tambaye su akan past experiences dinsu shikenan. Wanda kaga ya dace ka bashi aiki kawai a take wanda bai dace ba ka sallame shi kace masa babu aiki dan kar yaje gida yayi ta saka ran zai samu"

Hassan yace "so kake mu dauki baragurbi kenan mu bar masu kyau? Ai shi lamari na daukan ma'aikata a nutse ake bi ayi interview idan da hali ma sau biyu dan aga mai juriya, ni har medical certificate nake so suje suyi saboda in tabbatar da lafiyar su, sannan sai na zauna a nutse sai in tace wanda naga sun cancanta" Hussain ya mike tsaye yana bude hannu yace "do whatever you want. Ni dai abinda na sani shine, duk wanda Allah ya tsara yana da rabon samun aiki a *H and H* ko ka bashi yau ko kuma kayi ta delaying sai nan da shekara daya still dai sai ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment