Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai yaga ita wannan yarinya wanda zai aureta farin mutum
ne, kuma shine wanda zai mulki duniya, sai ya zaci ko WAHASHINFALA ne, sai ya
fusata yace wa Sarki ya zama dole ya kashe wannan yaron WAHASHINFALA in
kuma yaki to zai aika wa Dan uwansa Boka SAKARADUSA, ya fadawa Sarki SAIF
ce wa "Sarki AFARA'U ya ajiye wani farin yaro kuma idan ya taso to duk zai
halakar damu ne, sannan kuma ya mayar da wasun mu bayi.

Boka SAKARAJUNA
ya kare da cewa kaga kuwa idan Sarki SAIF yaji wannan batu to labudda zai halaka
ka da ki da jamaaar taka baki daya."


Koda Sarki AFARA'U yaji wannan magana daga bakin Boka SAKARAJUNA, sai
hankalinsa yayi kololuwar tashi saboda yasan indai har wannan magana taje kunnen
Sarki SAIFIRRA'ADU to kashinsa ya bushe.

Koda gama wannan tunani sai yace da
boka SAKARAJUNA daya bashi nan da kwana biyar zaiyi shawara, boka ya yarda
da hakan.

Boka yayi wa Sarki sallama ya nufi masaukinsa, yayin da shikuma a
bangaren Sarki AFARA'U ya zurfufa kogin tunani na neman mafita, yana cikin
wannan haline na tunani Wazirin sa mai suna HARISU ya fado masa arai.

Waziri
HARISU ya kasance mutum ne mai hangen nesa, saboda sanin yakamata da kuma
hangen nesashi ne yasa Sarki AFARA'U ya nadashi Wazirinsa.

Wanda ada yake da
mukamin Sarkin gida.

Koda Sarki AFARA'U yazo nan a tunaninsa, sai ya kira wani barde yace yayi
maza gidan Waziri HARISU ya kirashi yanzu yanzu.

Bardennan ya amsa da angama
ya shugabana. Ya haye dokinsa ya sukwaneshi. Lokacin da barden nan ya dawo shida
Wazirin HARISU Sarki yana cikin turakarasa.

Saboda haka shima Waziri sai ya
zarce inda turakarsa Sarkin take. Bayan ya nemi izini Sarki ya bashi, ya kunna kai
cikin dakin. Koda shigar sa sai Sarki ya bashi labarin duk yadda sukayi Boka
SAKARAJUNA akan WAHASHINFALA. Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi
na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron
numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan...

Zamu cigaba

MALUKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 3
posted by Shuraih Usman
@ https://dlhausanovels.com.ng

Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi
na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron
numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan wannan lamari tunda kaidai kanason yaron nan bakason rabuwa dashi ko kadan.


Mezai hana mu jewa da wannan boka kalamai masu sanyaya rai da kwantar da
hankali, muyi masa alkawarin cewa Indai har wannan yaro ya girma mukaga
take taken shi nason rushe mana masarauta da kuma hanamu bautar zahalu to sai mu
kashehi."

Koda Sarki AFARA'U yaji wannan zance sai yace "Maraba da fasihin
Waziri, hakika hakan za'ayi".Da haka Waziri yayi wa Sarki sallama ya tafi gida.


Bayan kwana biyar Kamar yadda Waziri HARISU yayi wa Sarki AFARA'Uu
bayani, cikin sa'a kuwa suka shawo kan boka SAKARAJUNA.


Sannu a hankali soyayyaya mai karti ta kullu tsakanin WAHASHINFALA da
SHAMATU ba tare da Sarki AFARA'U ko boka SAKARAJUNA sun sani ba.


Bayan wasu yan shekaru kowa a cikin wannan garin saida ya fahimci soyayyayar
dake tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU saboda haka boka
SAKARAJUNA ya fara kokarin rabasu ta hanyar alqalaman tsafi amman abu ya
farkara.

Ganin haka ya shirya mashi makirci ta qarkashin kasa.
Sannu a hankali manema suka fara fitowa neman auren SHAMATU, cikinsu kuwa
harda WAHASHINFALA wanda shine kan gaba.

Saboda haka Sarki AFARA'U ya
nemi shawarar boka SAKARAJUNA, koda boka yaji harda WAHASHINFALA sai
yayi dariyar qeta yace "Inaso gobe a tattatara mani manemanta a kofar fada".

Daga
haka Sarki AFARA'U yasa aka rubuta takardu zuwa ga masu neman auren "Yarsa
SHAMATU. Yakira wani bafadensa ya aikesa.


Washe gari tunda sanyin safiya masu neman auren SHAMATU suka fara bayyana,
bayan wani lokaci, suka gama bayyana a bakin fada, cikin mutanen nan kuwa harda
WAHASHINFALA dashima ya shiga layin manenan SHAMATU.

Bayan wani
lokaci suka fara jin bugun tabura gami da busar algaita hakan ya tabbatar masu da
cewa Sarki yana tafe. Haka kuwa akayi Sarki AFARA'U ne sanye cikin alkebba,
daga damansa Wazirin sa ne mai suna HARISU Sannan daga hagunsa kuma boka
SAKARAJUNA.

Koda ya karaso bakin fadar, bayan yayi masu barka da zuwa saiya
umarci boka SAKARAJUNA daya fada masu abinda ake buqata ga duk wanda
yakeson SHAMATU.

Boka SAKARAJUNA ya fara magana kamar haka "inayi wa
bakinmu barka da zuwa, dalilin dayasa muka taraku anan shine, duk wanda yake son
auren SHAMATU to sadakinta shine zai kawo mana kan Shahararren dan fashin nan
wato SA'ADUNUJJANJI, koda wadannan jaruman da yayan attajirai dake neman
auren SHAMATU sukaji haka sai suka fara sulalewa, cikin kankanin lokaci wajen ya
zama fetal ba kowa sa WAHASHINFALA.


Koda ganin haka sai boka yayi
murmushin keta yace da WAHASHINFALA jarumtarka ta burgeni sai ka shirya
nanda jibi ka kama hanya.

Daga haka suka juya izuwa cikin gidan sarautar.

Bayan kwana biyu WAHASHINFALA ya shirya cikin bakin sulke, yayi wa
SHAMATU da Sarki AFARA'U sallama y kama hanya cike da kewar garinshi da
kuma masoyiyarshi SHAMATU.


Alamarin SHAMATU kuwa tunda masoyinta WAHASHINFALA ya tafi ta shiga
damuwa kasancewar bata da tabbacin cewa ko zai dawo da rai.

Ahaka ta kwana ta
wuni a rana ta biyune tana bacci tayi mafarki da annabi HALLIRU alaihissasatu, yace
mata ai ita taimakon WAHASHINFALA yana hannunta.

Cike da mamaki ta kalleshi tace taya ya? Sai yace da ita a gidan akwai wata matattala ita wannan matattalar ta
kasance idan ka taka ta farko lafiya ta biyu bazakata lafiya, yacigaba da cewa saboda
haka ya zama maki dole kije ki sanar dashi.

Koda SHAMATU ta farka cikin dare
bata zame ko ina ba, sai bargar dawakai, cikin sanda ta kanto doki ta haye cikin sa'a
kuwa ta tadda masu gadin kofar sunata sheka baccisu.

Ba tare da tsoron komai ba ta
bude kofar ta fice.


Kasancewar WAHASHINFALA be dade da lafiya ba ita ta bi bayansa koma dokin
data dauko irin na musammanne wanda ba koda wane lokaci ake fani da suba,
tadauki lokaci tana tafiya cikin kurmumun daji ba tare da tsoron komai ba.

Aiko cikin
sa'a ta fara hango WAHASHINFALA wanda yana gab da shiga cikin gidan
shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI ta kwala masa kira, koda yaji
ankwala masa kira sai yayi turus yaja ya tsaya ba tare daya waiwayo ba.

Ganin shirun
yayi yawa yasashi ya waiwayo koda ganin wadda ta kirasa sai fuskarshi ta fadada da
murmushi.

Ya tabayeta keko meya sa kika biyoni? SHAMATU tace Zan baka labari
amman ba yanzi ba.
WAHASHINFALA shida SHAMATU sukayi kokari suka shiga cikin gidan
kasurgumin dan fashin nan SA'ADUNUJJANJI can suka hango wata matattakala,

nan take WAHASHINFALA ya doshi inda matattalar nan take ya mika kafa ya taka
ta farko ya kuma taka matattala ta biyu daga takawarshi sai ya rufta ciki wasu
wukake guda biyu masu matukar kaifi, da tsini tare da suka nufoshi zasu rabashi biyu
cikin azababben sauri SHAMATU ta rugo da gudu ta rikeshi sannan tayi wuf ta
jawoshi waje.

Ai koda ya ganta sai ya cika da matukar mamaki ya tambayeta ya akayi
kikasan haka? Nan ta kwashe labari kaf ta fada masa.

Da yaji haka sai yace gashi
yanzu adduarki taci. Nan dai SHAMATU ta ci gaba da bashi labarin wannan
matattala tace Ita wannan matattalar idan ka taka ta farko lafiya to tabiyu ta Sharri ce
dan haka idan ka taka ta farko to saidai ka tsallake ta biyu ka taka ta uku. To haka
sukayi har suka isa can sama da suka isa sai suka riski wata katuwar kofa ta baki
karfe saboda haka sai MALUKUSSAIF ya leka ya hango wani mutum baki, kato,
mai manyan idanuwa gasu jajaje tamkar garwashin wuta, gashi da katon hanci kamar
gwangwani, ga katon kai Kamar mangala Sannan ga manyan labba kai kace fata aka
shinfida.

Daga gefen damansa mutane arbain ne haka ma bangaren hagunsa. Koda
WAHASHINFALA yaga haka sai ya dawo bayan wannan kofar ya labe, koda ganin
haka sai SHAMATU tace da WAHASHINFALA shi wannan mutumin na tsaki baki
mummunan shine SA"'ADUNUJJANJI.

Suna zaune can sai SA'ADUNUJJANJI yace
da mutanensa kai kutsaya nifa kamar motsi nake ji fa? Inaga daya daga cikin mutanen
da kuka kamo ya kwance, daya daga cikin ku ya tashi ya duba.

Yana gama rufe
bakinsa, daya daga cikin Sadaukan nan ya tashi domin ya dubo yana zuwa daidai
inda kofar nan WAHASHINFALA yayi wuf ya sare masa kai, ita kuma SHAMATU
ta janyeshi ta boye gawar, da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yaji shiru sai ya kuma
turo wani barden nan ma dai WAHASHINFALA ya sare masa kai kamar yadda yayi
wana farko, haka SA'ADUNUJJANJI yayi ta aiko da mutane har akazo kan na biyar
nan fa kowa tsoro ya darsu a zuciyarsu aka rasa Wanda zai tashi shikuma
WAHASHINFALA dayaga anjima babu wanda ya sake fitowa sai ya kutsa kai ya
shiga cikin dakin ya tsaya gabansu koda SA'ADUNUJJANJI yaga
WAHASHINFALA sai yace kai kuma wannan karamar halitta daga ina haka? Kuma
maiya kawoka nan harka halaka mani mutane?

WAHASHINFALA ya amsa masa da
cewa babu ruwanka daga inda najo, kuma dalilina na zuwa na wajenka shine nazo ne
na kasheka, Sannan na tafi da kanka a matsayin sadaki.

Koda SA'ADUNUJJANJI
yaji wannan magana sai ya bushe da dari sannan yace kai yanzu wannan yaro har

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 4
post by Shuraih 99%

zaka iya fada dani? Dubeka fa ka dubeni na ninka ka sau goma, yanzu kaiko wannan
saurauyin wane ne ya turoka ka aikata wannan abu gareni? WAHASHINFALA
cikin bacinrai yace ba'a sani ba idan zakayi shirin yaki kayi.


SA'ADUNUJJANJI
yace zo mu shiga cikin gidana akwai fili isasshe wanda zai ishemu ni da kai.


SA'ADUNUJJANJI ya tashi yaransa suka biyoshi a baya, WAHASHINFALA ma
ya biyo shi a baya, suka shige wasu manyan soraye guda uku suka riski wani fili, da
suka isa wannan fili sai SA'ADUNUJJANJI ya juyo wajen mutanen sa yace idan
muna yaki da wannan yaro kar wanda ya kawo mani dauki koda kuwa kunga yana
kokarin samu galaba a kaina ne, ku tsaya kawai kuyi kallo.


Koda yaran
SA' ADUNUJJANJI sukaji haka sai su dukansu suka babbake da wata mahaukaciyar
dariya, domin sun san cewa ba ta yadda za' ayi wannan karamar halittar ya iya kai
shugaban nasu kasa ko yazo da matemaka bare ya zo shi kadai.

Suka amsa da sunji
sun yarda.
Can kuma SHAMATU data ga sun shiga wannan gida, sai ta fito daga inda take
boye ta hau kan wani dutse inda zata iya ganin karawar da za'ayi tsakanin
SA'ADUNUJANJI da saurayinta.


SA'ADUNUJJANJII ya yiwo kan WAHASHINFALA yana gurnani tamkar zakin
dakejin yunwa ya hango nama, WAHASHINFALA shima ya zare tashi takobin yayi
dauki kan sa suka kaure da yaki bají-ba-gani har dare yayi rana ta take.

Can suna
cikin wannan dauki ba dadi dine sai WAHASHINFALA ya taka wani karamin dutse
ya durkushe kasa.


SA'ADUNUJJANJI ya daga takobinsa ya kawo wa
WAHASHINFALA wani wawan sara koda SHAMATU taga haka sai ta tabbatar da
cewa indai har saran nan ya dira a kan masoyinta to saidai wani bashi ba.

Sai tayi
wuf! Ta zaro wani gariyo daga cikin sulkenta ta wulwuloshi ta jefi
SA'ADUNUJJANJI dashi, sao gariyon ya sare shi a hannu wanda hakan yayi sanadin
faduwar takobin dake hannunsa.


WAHASHINFALA ya rike takobinsa a hannu yayi
niyyar sarewa SA'ADUNUJJANJI kai amman sai ya fasa yace tashi ka dauki
takobinka muci gaba da yaki, domin bazan kasheka ta hanyar yaudara ba, sai kuma
ya juya ya fuskanci dutsen da SHAMATU take tsaye yace jinjina gareki ya
ma'abociyar bege.


Koda SA'ADUNUJJANJIl yaji haka sai ya tashi ya dauki takobinsa
suka ci gaba da yaki, haka suka cigaba da wannan gwabzawar har tsawon kwana uku
a rana ta ukun ne shuka tsaya domin su huta, ko wannensu ya samu guri ya zauna
yana haki.


Su kuma yaran SA'ADUNUJJANJI sun cika da mamaki ganin irin
jarumta da kuma sadaukartaka ta WAHASHINFALA.


Can da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yace "Yaro me yasa lokacin da takobina
ta fadi ka samu damar kasheni amman kaki kace bazaka kasheni da yaudara ba?
kuma naji kamar kana magana da wani.


WAHASHINFALA yace wannan yarinyar
da zan aura itace ta cillo mani wuka, kuma da ita nake magana shiyasa nace bazan
kasheka da yaudara ba.


WAHASHINFALA ya sakko da SHAMATU daga kan dutsen nan ya shigo da ita
cikin wannan filin ta zauna kusa da shi.

SA'ADUNUJJANJI yace lallai yau zan shayar da ku gidauniyar mutuwa daga kai har ita sannan naje har kasarku na kashe
uban wannan yarinya na fatattaka garin gaba daya, na kwashe dukiyoyinsu sannan na
koro bayi.

Koda sukaji haka sai suka zabura suka cigaba da sara da suka, a takaice dai
saida WAHASHINFALA da SA'ADUNUJJAN.JI suka shafe tsawon mako duga cir
suna gwabza yaki amman babu wanda ya samu nasara a kan dan uwansa, har saida
makamansu suka lalace nan take kowa ya yada nashi suka tsaya sukayi cirko-cirko
kamar zakaru suna kallon juna suna muzurai.


Can sai SA'ADUNUJJANJI yace "Kai
yaro! Yanzu tunda makamanmu sun gaza yanzu sai mu fidda sharadi,
WAHASHINFALA yace wane sharadi? SA' ADUNUJJANJI yace sharadin shine
yanzu zamuyi kokawa nida kai duk wanda ya kada wani sau uku to shi ya cinye
wannan gasar, idan kai ka kadani sau uku to kai ka cinye wannan gasa sai kayi yanda
kakeso dani, haka zalika idan ni na kadakai sau uku to sai nayi yanda nakeso dakai.


Koda WAHASHINFALA yaji haka sai ya yarda da wannan sharadin, suka fara
kokawa kici-kici, can sai SA'ADUNUJJANJI yayi wuf! Ya suri WAHASHINFALA
ya daga sama zai fyada da kasa, kawai sai WAHASHINFALA ya Kama kunnen
SA'ADUNUJJANJI ya murda cikin ikon Allah sai ga SA'ADUNUJJANJI ya fadi
kasa tim!.


Haka dai WAHASHINFALA yayi ta kada SA'ADUNUJJANJI har sau
uku, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro kayi nasara aikata abinda
kakeso dani ya durkusa bisa gwiywoyinsa.


Da WAHASHINFALA yaga haka sai ya
dauko gariyonsa yayi niyyar sare kansa, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace
yaro amman da zaka kyaleni, da raina, ka kuma riqeni na zama bawanka domin kila
wata rana zan maka amfani.


Da WAHASHINFALA yaji haka sai ya ajiye wannan
gariyon yace gaskiya ne na yarda da maganarka.


SA'ADUNUJJANJI da kaf yaransa suka jinjina ga WAHASHINFALA sukace
"Gaisuwa gareka ya shugabanmu" anan suka kwana.

Da gari ya waye
SA'ADUNUJJANJI da yaransa suka zo gurin WAHASHINFALA suka kwashi
gaisuwa Sannan suka zauna daga gefen WAHASHINFALA.

WAHASHINFALA
yace da SA' ADUNUJJANJI da mutanen sa to ai saiku tashi mu tafi kasar DUWAR
domin kuwa nasan Sarki AFARAU yanacan yaba jirana.


Nan da nan SA'ADUNUJJANJI suka dora wa giwayensu sirdi, shi kuma
WAHASHINFALA da SHAMATU suka haye kan dawakansu suka kamo kan
hanyarsu ta dawowa kasar DUWAR.


Bayan sun samu Kamar kwanaki uku suna
tafiya sai suka fara hango katangar birnin DUWAR, anan sai shamatu ta rigasu shiga
cikin birnin dankada a gane cewar tare suke, takoma gida ba tare da wani ya ganta ba.


A wannan lokacin kuma sai akayi sa'a boka SAKARAJUNA yace da Sarki
AFARA'U cikin gatse zomu je bayan gari muga ko wannan yaron zai dawo, Sarki,
Waziri da sauran fadawa suka fito bayan gari suna diban hanya.

Can sai suka hango
WAHASHINFALA ga kuma SA'ADUNUJJAN.JI da yaran sa bisa giwaye, "kagani
ko gashinan abinda kaja mana kasa wannan yaron ya tsokano mana
SA'ADUNUJJANJI, ya matsa mashi ya sanar dashi cewa mu muka turo shi, gashinan
sun sakoshi a gaba suzo su halakamu".


Koda jin haka sai Sarki, boka da jama'ar gari
suka ruga da gudu cikin gari suka rurrufe kofofin gari, da suka karaso sai
WAHASHINFALA yasa daya daga cikin yaran nan ya bubbuga kofar amman ba'a
bude ba.

Koda WAHASHINFALA yaga haka sai yayi tsawa ya umarci
SA'ADUNUJJANJI daya karya kofar birnin.


Nan da nan SA'ADUNUJJANJI yayi
wa toron giwarsa qaimi ya bangaji kofar garin ta karye, suka kutsa kai izuwa cikin


MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
kashi na daya 5
fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Mr Hausa Ebooks


Da WAHASHINFALA yaga haka sai yace "Baba yanaji kace dani Sarki bayan ba
haka bane, kuma ka kirani da wani suna wai MAALIKUS-SAIF bayan ni sunana
WAHASHINFALA.

Tsoho ya dubeshi yayi murmushi yace "Katahone daga garin
DUWAR kuma yau kwananka sittin kana tafiya kafin kazo nan, kuma
WAHASHINFALA ba sunanka bane sunan ka wanda Allah ya nufa shine
MAALIKUS-SAIF, mahaifinka kuwa shine Sarki ZIYAZINUN mai mulkin kasar
HAMRA'U YAMEN wanda ya rasu, kuma kaine wanda adduar Annabi Nuhu zata
fada a kansa zai samu mulkin duniya baki daya, ya kuma tambayarsa ya
MAALIKUS-SAIF yanzu mai kake bautawa? Ya amsa masa da cewa "Eh nidai naga
mutanen nahiyar mu suna bautawa rana da wata ne, amman ni bana bauta masu sabo
da nasan Allah ne ya halicceni saidai ban samu Wanda zai koya mani yadda zan
bauta mashi bashiyasa ni ban bauta wa komai Tsohon yace "Ka dogara ga Allah
yanzu zan musuluntar da kai. MAALIKUS-SAIF yace na dogara ga Allah, Tsohon
yace kace na gasgata babu abin bauta sai Allah kuma na gasgata da Annabi
Muhammadu Annabi da zaizo a karshen zamani da Annabin wannan zamanin Annabi
Ibarahim alaihissasatu wassalam.


MAALIKUS-SAIF ya maimaita shahada kamar
yadda Tsohon nan ya fada masa. Bayan ya gama sai Tsoho yace masa ni sunana
Shehu ZAJJADA, yanzu tunda ka musulunta ka zama dan uwana kuma ya zama dole
na taimakeka nasan ka fito neman littafin kogin NIL zan fada maka inda yake amman
inaso kafin ka tafi ka kwana a nan domin inason sanar dakai hanyoyin bautar Allah.


Shehu ZAJJADA ya koya wa MAALIKUS-SAIF alwala da zikirin Allah suka zauna
suna ta zikiri har cikin dare sannan shehu ZAJJADA ya mike ya daga hannu ya roki
Allah ya kawo masu abinci daga arzikinsa.


Nan da nan sai ga abinci da abubuwan sha
iri-iri a gabansu, MAALIKUS-SAIF ya cika da dunbin mamakin ganin wannan
abinci saboda baiga yadda ya kawoshi ba. Shehun ya umarceshi da yaci abinci
amman kafin ya fara ci yace Bismillah.


MAALIKUS-SAIF ya fadi haka ya fara dibar
gara abinka da maijin yunwa. Haka yayita ci har saida yaji ya koshi sannan ya sha
ruwa, sannan ya kwanta ya huta.


Kwanciyarshi keda wuya bacci ya kwasheshi, shi
kuma Shehun ya ci gaba da zikirinsa.


Can da gari ya waye Shehun ya tada MAALIKUS-SAIF yayi masa wa'azi sannan
ya kuma cewa ka dogara ga Allah, zaka kubuta da duk wani yanayi da ka samu
kanka.


Sannan ya zagaya da shi bayan wannan dutsen ya nuna masa yace yanzu
kabar dokinka anan domin baya da amfanin tafiyar da zakayi dashi, ya nuna masa
yace kabi gefen kogin nan kayi dama zakayi tafiyar kwana uku zakaga wani fili,
bayan ka wuceshi zaka kuma ganin wani kogin mai matukar girma dan girmansa
babu iyaka, to saika tsaya a nan. Akwai wata dabba mai suna HATSHA.


Ita wannan
dabba tunda Allah ya halicceta idan rana ta fito daga gabas tana daga tsakiyar wannan
kogin sai tayita tsalle wai sai ta kamo rana, idan rana ta tsaya daidai a sama sai
bakinciki ya kamata, sai ta fito da kanta daga bangaren gabas tayita turmutsa kanta a
cikin yashi dan hushi, haka kuma idan rana ta koma gabas sai tayita tsalle da niyyar
ta kamota har rana ta fadi, idan ta fadi nan ma sai ta fito da kanta a bangaren yamma
ta rinka turmutsa kanta a yashi nan ma dan haushi.


To idan kaga wannan dabba tana
tumurmusa kanta a cikin wannan yashi to kar kaji tsoro ka kana gashin wuyan
wannan dabbar ka dafeta, bazataji komai ba saboda girmanta, kai koda cikin idanunta
zaka shiga bazataji komai ba. Ka zauna kana makale a kanta har ta maida kanta
yamma, bayan ka sauka zakaga wani mutum, to ta dalilin wannan mutumin zaka
samu wannan littafin.


Daya gama wannan bayanin sai MAALIKUS-SAIF yayi
godiya Sannan yabi wannan hanyar da Shehun ya nuna masa, ya shafe kwana uku
yana wannan tafiyar har ya isa wannan filin da Shehun ya fada masa....

Anan zan dakata
Zamu cigaba zuwa Gobe Ana yin comment yan uwa

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 6
post by Shuraih 99%
.
Isar sa keda wuya kuwa yaga wannan dabbar tanata tumurmusa kanta a cikin yashi
kamar dai yadda Shehun ya sanar dashi.

Nan da nan sai yayi maza ya dane kanta har
rana ta fadi,takai bakin gabar daga bangaren yamma, koda MAALIKUS-SAIF yaga
haka sai ya fado daga kanta ji kake tik!. Ya tashi ya fara tafiya.


Can yana cikin yafiya sai yaga wani mahayin doki a sukwane ya yi yo kanshi, koda
mahayin yazo gab da MAALIKUS-SAIF da niyyar bankeshi sai MAALIKUS-SAIF
yayi sauri ya banke dokin, haka suka rinka yi har sau shidda ko da mahayin dokinnan
yaga haka sai ya zare takobinsa ya kaiwa MAALIKUS-SAIF Sara da suka shi kuma
yana gocewa, hardai ya harzuqa MAALIKUS-SAIF, MAALIKUS-SAIF ya dubi
mayin sai yace kaidai Allah wadaranka ragon banza, ai ba haka ake gwanimtar yaki
ba, haka kawai mutum yana tafiya ka tasar masa dan ganin yana kasa Kai kana doki,
kuma ga makami a hannunka, bari in nuna maka yadda sadaukai suke nasu sha'anin.


MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya damki wuyan dokinnan da hannun dama, ya
kuma sake yin wif! Ya shaqo Wuyan mahayin da hannun hagu ya daga sama ya
jinjina shi sannan ya saukeshi a hankalı ya ce "Kaga yadda sadaukai suke nasu
lamarin".


Da ganin haka sai wannan mahayim dokin ya sakko daga bisa dokinsa ya tsaya
gaban MAALIKUS-SAIF ya yaye kyallen dake rufe a fuskarshi koda ya yaye sai
MAALIKUS-SAIF yaga shema mace ce ba namiji ba ne ya dubeta yaga kyakkyawa
ce, sai tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN koda yaji ta kira
sunansa sai yace kekuwa yaya akayi har kika san suna na? bani labari mana.


Yarinya ta fara da cewa "Suna na DAMATU, na samu labarin kane a wajen
mahaifiyata wacce itace Sarauniyar bokayen birni KAIMARA, sunan ta Bokanya
AKILA.


Wata rana muna zaune da ita sai nace mata ta buga mani qasa taga waye
wanda zai aureni, sai ta amsa mani da cewar Wanda zai aureki sunansa MAALIKUS-
SAIF na ainahi amman yanzu ana kiransa da suna WAHASHINFALA, kuna asalinsa
dan wani Sarki ne mai suna ZIYAZINUN Sarkin kasar hamra'u yemen amman yanzu yana
qasar wani sarki mai suna AFARA'U, bayan an kwana biyu, sai tace mani shi
wannan wanda zaki aura ya nemi auran wata yar Sarki aka nemi ya kawo kan wani
dan fashi kuma gashi can ya dawo.


To a wannan lokaci sai na rinka damunta da
yaushe zai zo garin nan? Sai ta rinka ce mani ai ya kusa Zuwa, sai yau kuma dana
sake tamayarta sai tace dani inyu maza ai gakacan ma ka iso, amman ta fada mani
cewa inyi qoqarin yaqarka, indan naga baka da niyyar cutar dani sannan ka kama
wuyan dokina sannan ya dagani daga ni har dokin, sannan ya saukemu a hankali to
Wannan shine wanda zan aura, saboda haka kaji na kira sunanka kada kayi mamaki.


Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan yarinya ta fadi wadannan batutuwa a kansa sai
ya gasgata zancenta, amman a fili sai yace da ita "Ke kuwa wannan da qaryar tsiya
kike, sannan kin iya shirya batu, domin wannan mutumin da ki ke fada to ni ba ni
bane, kedai kawai kinyi niyyar ki yaqeni kikaga babu nasara shine kika shirya
wannan zantuka".


Koda 'DAMATU taji haka sai tayi murmushi sannan tace "Daman
uwata ta fada mani cewa kona fada maka bazaka gasgata ba, kuma kazo wannan qasa
tamu domin neman littafin tarihin NIL, kuma babata itace zata taimaka maka ka
dauko wannan littafin.

Tana gama wannan bayani sai ta yaye lullubin dake a fuskarta.
MAALIKUS-SAIF ya dubeta ido cikin ido yace yanzu ina babar taki take? Tace tana
gida, yace to mu tafi izuwa gareta.


Sai DAMATU tace "A'a ai a kaidar wannan garin bako baya shiga, domin kuwa tarihi ya nuna wa mutanen wannan garin cewa wani
bako ne zai zo ya sace shi wannan littafin tarihin NIL wanda ka fito nema, su kuma
wadannan mutanen tun kaka da kakanni wannan littafin shine abin bautarsu, tun
lokacin da suka samu labarin cewa wani bako ne zai zo ya sace wannan littafin sai
suka tsafe garin, suka sana' anta wani gunki mai suna GAMMAZI wanda duk lokacin
da bako ya shigo zai dinga îhu yana Ga... Bako! Ga Bako! Daga nan sai a kama
bakon a yankashi wannan dalilin ne yasa bako baya shiga, amman duk da haka,
babata ta fada mani cewa idan kazo qofofin shiga garinmu ka lissafa qofa ta tara sai
ka duba zakaga wata bishiya a kusa da wannan qofar zakaga akwatu ka shiga ciki
sannan ka girgiza igiyar sai mu jawo dakai daga cikin kwatun mu shiga dakai cikin
garin.


Koda DAMATU ta gama bashi wannan labarin sai ta haye dokinta ta tunkari
qofar birnin nasu.


Shi kuwa MAALIKUS-SAIF sai ya dinga bin sawun dokinta har ya fara hango
katangar birnin KAIMARA.


Daga nan sai ya juya bangaren gabas ya fara qirga
qofofin shiga garin koda ya qirga ta tara, da ya hango kofa ta goma sai ya dosheta,
Kamar yadda 'DAMATU ta fada masa, to daya isa bakin qofar nan sai ya boye ajikin
wannan bishiyar da yake duhun dare ne ba wanda zai iya ganinsa, can yana tsaye
jikin bishiyar nan sai yaga ana sako akwatu daga kan katangar, koda ya sakko qasa
sai yaje ya shiga cikin wannan akwatu, sannan yaja murfin akwatin ya rufe ya girgiza
igiyar sau uku.


Su kuma can bokanyanya AKILA da DAMATU da sukaji an girgiza
wannan igiyar sau uku sai suka jawoshi suka shiga dashi cikin birnin.


Da suka isa gida, sai bokanya AKILA ta kawo masa abinci da ruwan sha, bayan ya
gama sai ya kwanta, bayan ya huta sosai bokanya AKILA tace barka da zuwa
MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN.MAALIKUS-SAIF ya amsa mata da cewa
yawwa, kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin kogin NIL, kuma nice
zan taimakeka saka makon auren yata da zakayi.


Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka
sai yace wai meye amfanin wannan littafin da har

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

2 Comments On MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1
avatar
haruna-dau

1 year ago

Reply

I really love to read this novel

avatar
abdullahi-isah-mika39i

1 year ago

Reply

Yeah

Please Login or Register in order to submit comment