Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai yaga zoben Sarki. Nan da nan
ya mika wa MAALIKUS-SAIF zoben nan yace Kaga wani zobenan cikin kifin nan
koda MAALIKUS-SAIF ya gogeshi, sai Abdussamad yace duk yadda akayi wannan
zoben Sarki ne ba makawa.


Nan dai ya kwashe labarin wannan zoben yabawa
MAALIKUS-SAIF labari yakuma fada masa cewa Duk wanda ya mallaki wannan
zoben to ba makawa shine Sarki wannan gari.

Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai
yace ba komai Allah ya kaimu gobe zanje fada na tunbike wannan mushitikin Sarki
naku.


Gari na wayewa MAALIKUS-SAIF da Abdussamad suka kama hanya suka doshi
fada, da isarsu sai suka ga fada ta cika makil Sarki DUHAN yana bisa kan karagar
mulkinsa anata fadanci.


Da shigar su fada Sarki ya cika da mamaki yace "Ya kaida
nasa a kasheka kuma naga ka dawo." MAALIKUS-SAIF ya dubi Sarki yayi dariya
sannan ya daga wannan zoben ya nuna wa Sarki da Duk jama'ar dake fadar.


Koda
jama' a suka kyalla ido sukaga zoben, sai suka kama cewa "Aiko zoben sarki ne ai
shine. ai tunda ka mallaki wannan zoben ba makawa kaine Sarkin mu, dama
ka'idarmu kenan ta samun sarautar wannan gari."


Koda Sarki DUHAN yaga haka sai
ya mike yana hargagi yana karyata MAALIKUS-SAIF yana cewa wannan zoben na
karyane ba zobena bane nawa na barshi a gida.


Rufe bakinsa keda wuya sai
MAALIKUS-SAIF ya nunasa da hannunsa mai zoben nan take kansa ya gutsire ya fadi kasa matacce. Sarki DUHAN tasa ta kare makomarsa ta munana aka gaggauta
zuwa da ransa jahannama.


Bayan ya gama da Sarki DUHAN sai MAALIKUS-SAIF yace yanzu bautar wuta
ko zobe ta kare kowa ya zai koma bautawa Allah da manzon sa Annabi Ibrahim
Halilullah, in kuma kukaqi in halakaku gaba dayan ku.


Jama'a gaba daya suka yi
mubayia. MAALIKUS-SAIF ya zauna dasu har tsawon wata biyu yana sanar dasu
hanyoyin bautar Allah.


Ranar da MAALIKUS-SAIF zai bar garin sai ya dora Abdussamad bisa gadon
sarauta ya umarci Jama' ar garin da yi masa biyayya.


Daga nan Jama'a suka yi masa
rakiya har bayan gari sannan suka juya suka koma cikin gari. Shi kuma ya doshi inda
yabar AKISA tana jiransa. Da zuwansa sai ya iske AKISA tana jiransa.


Koda ta
ganshi sai tace ya Dan Uwana na ina kallon lokacin da mutanen wannan qasa sukaso
halaka ka, inaso na taimakeka amman bani da ikon shiga garin tilas haka na hakura
ina gani zasu kasheka.


MAALIKUS-SAIF yace ashe kin ganni, ai yanzu gashi Allah
ya kubutar dani, ai yanzu saiki daukeni ki kaini birni na uku. Koda jin haka sai
AKISA tace "A'a Dan Uwana bazan iya kaika ba, ina gani a cutar dakai domin kuwa
suma birane biyar din bazan iya shigarsu ba, saboda haka koda hallaka za'ayi inaji
ina gani babu yadda zanyi, kaga kuwa ya za'ayi na rika kai Dan uwana ga mahallaka
bani da ikon taimaka nmasa."


Da MAALIKUS-SAIF yaji haka sai ya fusata ranshi ya
baci yace kidai ki kaini mana ina ruwan ki. Itako AKISA da taga ran MAALIKUS-
SAIF ya baci sai tayi masa dabara tace haba ya dan Uwana kada rudin duniya ya
shagaltar dakai abinda kafito nema mana littafin tarihin NIL, koda jin abinda AKISA
ta fada sai hankalinsa ya karkata izuwa gida, ya tuno da SHAMATU abar begensa.


Sai ya umarci aljana AKISA data daukeshi ta mayar dashi birnin KAIMARA yayi
amfani da hularsa ya dauko wannan littafin tarihin.


AKISA ta daukeshi sukayi sama
bata zame ko ina ba sai bakin wannan rijiyar data fito dashi.


AKlSA ta mika masa
hularsa BADUHU wadda ya samo Sannan tayi masa adduar Allah yasa ya dauko
wannan littafin na tarihin NIL.

Sukayi sallama AKISA ta tashi sama, ta tafi shi kuma
ya tsaya yana tunanin yadda zai shiga garin KAIMARA yana cikin wannan tunanine
can kuma Bokanya AKILA ta hangosa a madubin tsafinta..

YANZU SHIN MAALIKUS-SAIF YANA SHIGA GARIN KAIMARA NE HAR
YA DAUKO LITTAFIN NAN KO KUWA HAKURA YAKEYI YA KOMA GIDA?

IDAN KUMA YANA DAUKO LITTAFIN TO YA YAKE A SHIGA GARIN
TUNDA SUNADA GUNKI MAI TONON SILILI.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1
avatar
haruna-dau

1 year ago

Reply

I really love to read this novel

avatar
abdullahi-isah-mika39i

1 year ago

Reply

Yeah

Please Login or Register in order to submit comment