Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari na fice kar wani nemanmu ,Ammi batasan naxo bama ,


MIQDAD kwa yawancin kullum såi yaje schl in Su MUWADDAH nemanta ,Amma basu taba haduwa ba ,wataran MUWADDAH na ganinshi amma sai ta boye ,

*SILAR SOYAYYA*MIQDAD yaxama silent ,yamai då komai nashi thinking ,baida aiki sai tunani då yadan samu pre time to baida aiki sai tunanin MUWADDAH,




**********

After 7 month

cikin MUWADDAH ya tsufa sosai ,amma duk da haka tana xuwanta makaranta ,


MUHIBBAH ma cikinta ya isa watan haihuwa ,haihuwa ko yau ko gobe ,ana ya gobe xata haihu ta tadda MIQDAD xaune a falo ,ya kurawa hotan MUWADDAH ido yana kalla ,saida ta danji kirjinta ya buga alamun kishin ya morsa ,amma haka ta daure ta risina gabanshi ,


tana ta masa magana ,shi baima San tanaiba ,yariga ya lula duniyar tunani ,

saida ta girgixashi ,sannan ya dawo duniyar då yake ,hannuwanta biyu ta hada tana neman yafiyarsa ,bisa dukkan laifin då tai masa ,

yace ya yafe mata ,itama ta yafe masa ,tace " Allah ya yafe mana baki daya ,suka hada baki wajen cewa Ameen ,

Washe gari ta tashi då naquda ,kwananta daya tana Abu daya ,ta Kifara sosai ,ganin haka yasa likitoci sukace aiki xa'a mata ,ba bata lokaci MIQDAD ya saka hannu ,aka shiga daita dakin thearter ,tana ta cije baki ta kasa magana hawaye na kwaranya a idanunta ,a haka aka shige daita ,



Än ciro mata sankaceciyar yarinyarta budurwa ,saidaifa numfashin MUHIBBAH bai dawo ba,duk Yadda likitoci sukai ,amma numfashin MUHIBBAH yaki dahowa ,anan sukai gwaje -gwajensu ,suka gano Allah yaiwa MUHIBBAH rasuwa ,


Kullu nafsin xa'ikatul maut ,

dukkanin rai sai ta dandani mutuwa ,

duniya kamar makaranta take ,randa xakaje ,a ranar wasu xasu kareta ,wassu suna murna ,wassu na kuka ,haka duniyar take ,

Allah ubangiji kai mana kyakkyawan karshe ,kar karbi ranmu muna masu tuba Ameen ,kasa mucika då kalmar shahada😭😭😭😭😭😭Ameen ya Allah ,


MIQDAD yaji mutuwar MUHIBBAH sosai abin ya hadu ya hade masa biyu ,

Momy ce ta anshi jinjinniyar take bata madara ,kowa då ya kalli jaririyar ,sai xuciyarshi ta kara narkewa då tausayin jaririyar ,a haka har aka share makoki ,

shikenan fa duniyar 👌🏽
jama'a ya kamata mu hankalta ,musan abinda muke mu aikata dai-dai a rayuwarmu ,domin mutuwarnan ba sallama take mana ba ,då lokacinka yayi xaka tafi ,dan hka komai xamui muji tsoran Allah mufa tuna mutuwarnan Akwai ranar xuwanta ,Allah kasa mu dace Ameen,

Ranar bakwai aka sakawa yarinya sunan Momy ,xa'a dinga kiranta då mimi ,xuwa ranar suna amma muni duk tayi duhu ,kuma kunnanta dama bakine ,alamu ne dayake nuna baka ce dama ,
bakin Momy bam kake jinshi ,ba bakin magana ,


Nikwa nace ai duk dabararka baka isa kawa Allah wayo ba ,duk Yadda yaso yin halittarshi haka xaiyi ta ,


MUWADDAH da mubina ke sanar musu ,taji mutuwar MUHIBBAH sosai,

Anan duk ta tsorata da haihuwar ,itama gani take kamar mutuwa xatai ,saida Ammi tai taimata nasiha , tace bakya gudun garin tunani ki dorawa kanki wani ciwan ?kana aka samu ta saki ,





Momy ce då mami ke hira ,mami ta kalli mimi dake hannunta tace "ji ikon Allah uwa fara uba fari ,amma ji ya " tayo baki ,ko bakin wa tai ?"


Momy tace "Hmmmmm Kedai bari ,ishara ce Allah ya nuna mun ,duk Kina då bakin fata ,sai gashi än haifmun jika baka ,Wannan ishara ce ga masu irin halina ,nidai a yanxu duk halitta ta ubangiji ina Santa ,Muma ba rawa mukai Allah ya bamu ba "



Mami tace _Ai nima naga ishara ,yau duk xan gaya miki irin tuggun abinda nai a gidannan ,

Nice asalin cusa muku kiyyyar Ammi ,
Tunda abbansu yaxo mun då maganar auranta ,muka gargada gurin wani boka (tir då makomar masu aikata haka )anan yake gaya mana ai aure ba fashi ,na kadu då jin hka ,sai nace ina so yasanyawa duka ahalin *GIDAN FARARE* tsanar Ammi ,to anyi näsarar jefa kiyayyatta a xukatanku ,Amma Allah bai bashi nasarar jefawa a xuciyar mrigyi alh bukar ba ,sannan na nemi då amayar mun då Ammi böra ,

To lokacin då aka haifi MUWADDAH ne ,naga alamun abbansu yafi kaunarta ,nanma ba shiri na garxaya na fada masa dan yashiga tsakaninsu ,shiyasa kikaga abbansu ba ruwanshi då harkar Su MUWADDAH ,


To sai gashi abin ya juyo kan nabila ,kishiyar då akai mata taxo ta maidata bora ta karfi da yaji ,kwakkaran motsi batai ,in suna gurin ,
Nikwa nace "to ai dama haka rayuwar ta ga'då ka dila dan wanine kaima a dila naka"



Momy ta girgida kai tace cabf kinyi kuskure sosai mami na xuwa gun boka ,Ashe kece meyin sihirin kike ta xigani (to ai dama duk mmai daukar xiga a rayuwa baxaiga då kyau ba ".)Ai dama in mutum na aikata mummunan aiki,gani yake kowa haka yake ,ni yanxu då wani ido xan kalli Ammi ,kingama damu wlh ,


Abba dake tsaye a byansu ,ygma jin dukkan abinda suke fada ,sai ya juya hnkli tashe ,yaje ya xaiyyyanawa hjya ,


A take hjya ta kira metting ,



Kowa saida yai ta'ajjibbi då wannan lamari ,a take hjya tasaka abban MUWADDAH da yasaki Ammi saki biyu ,dan taje ta gane kuskuren då ta aikata ,




Kuka take tana cemusu ta tuba ,Su yafe mata ,amma ba wanda ya saurareta ,


Nanfa abbah yashiga neman Ammi da diyarshi afujajan,soyayyar dayakewa Ammi da diyar tashi ,tsiminta ya taso ,





MIQDAD yaxama abin tausayi ,in kika ganshi baxa kixaci wannan dan gayen bane ,meji då kyau da gayu ,











Yau MUWADDAH ta tashi då nakuda tun asuba suka tafi asibbiti ,ba ita tahaihu ba sai 04:50pm ,ta santalo santaleliyar yarta budurwa ,

då yake daga ita har Jaririyar lafiyarsu qalau sai aka basu sallama ,


Ammi da tagayawa mubina haihuwar kuka ta sakawa Ammi akan ta bata kwatancen gidan taxo ,a take Ammi ta bata adress din gidan ,Amma då sharadin ba wanda xata sanarwa ,




Ranar då mubina taxo ,sun huni cikin farin ciki ,daga ita har Ammi sai lelen MUWADDAH suke ita då jaririyarta tamkar yar larabawa ,farin jaririyar mai kyaune sosai ,ga sumar gashi sosai Allah ya bata ,kmarsu daya sak då MIQDAD in ta kalleta ,sai taji tsimin soyayyar mahaifinta na taso mata ,



Ammi duk ta gayowa yan uwanta ,ta basu adress din gidan då take a yanxu ,sbda duk sunsan lbrin mutuwar aurenta ,


Ansha bidiri sosai a wannan suna ,akasawa jaririya sunan Ammi ,xasu na kiranta då nuwaira ,

Anyiwa jaririya kalandu wanda suke dauke då hotanta ,tayi kyau ainun a jiki ,

Mai jego ma tasha kyau ,ita då diyarta duk inda suka gifta kyasa musu hotuna ake ,


MUSADDIQ dan gidan ya'yar Ammi ne ,bai taba xuwa garinba sai Wannan xuwan ,saurayine kyakkyawa mai jini a jika ,tunda yaga MUWADDAH xuciyarshi tai katakam då soyayyarta ,duk inda xata bi idonshi na kanta ,xaxxafar kauna yake mata ,Wacce ya kasa boye hakan har saida ya bayyana mata ,

Ranar MUWADDAH kuka ta huni tanai ,ita dai tasan MIQDAD kawai xuciyarta keso ,baxa taso wani ba byan shi ,Amma kuma då kunya ta kalli idon dan uwanta tace bata sanshi ,
ga Yadda yake kaunar diyarta ,komai yace nuwaira,



Mubina na dakin mai gidanta ,MIQDAD yashigo gidan ,falon tsit ba kowa ,sai wayarta dake kan kujera tana tatsiwa ,

Idanshi ne yasauka kan sicring din wayar ,byan wayar ta katse ,

då hanxari yasa hannu ya dauki wayar ,hotan kan scring in wayar ya xubawa ido yana kalla ,


MUWADDAH ce tai masifar kyau ,ita då diyarta nuwaira ,sunyi kyau sosai a jikin hotan ,

Kmar ance yadaga kanshi ,ya hango calandar nuwaira ,da sarsarfa yaje ya cirota a inda take ,källan yarinyar yake sosai ,a take soyaryar yarinyar tabi jini då tsoka na jikinshi ,a take ya gano ainihin tsananin kmar då suke då nuwaira ,ashe dama rabuwarsu yabar MUWADDAH da ciki ,shine abinda xuciyarshi take ta tambayarshi ,kuma baida amsar hakan ,

Juyawa yai yafice då calanda a hannunsa ,

Momy yaje ya nunawa ,itama xubawa yarinyar ido tai ,a take wata nadamar ta kara shigarta ,soyayyar yarinyar yabi lungu då sako na xuciyarta,

tace "dama ka barta då cikine ?"


Ammi nima abinda ban saniba kenan ,amma idan har MUWADDAH ce ta haifeta ba makawa ya'ta ce

Tom ,Allah dai yasa hakane ,wlh soyayyar yarinyar har yashigeni ,yanxu ka koma gidan mubinan ka roketa då tagayama inda suke ,


Yace tom ,kna ya juya yafita ,


då yakoma gidan nata yatadda Su a falo suna hira ,


har kasa ya tsugunawa mubina yana hawaye akan ta sanar dashi inda Su MUWADDAH suke ,

Kin gaya mishi tai ,sbda Yadda sukayi då Ammi ,amma ganin irin kukan då MIQDAD yake , idanuwanshi sunyi jajir yasa xuciyarta karyewa taji tausayinshi ,ta bashi address in gidan ,



bai wata2 ba ya nufi gidan ,


MUWADDAH suna falo suna hira ita då MUSADDIQ ,nuwaira na hannushi ,MIQDAD yashigo falon kawa än jefoshi ,

MUWADDAH jitai gabanta ya fadi ,ta dake ,
shima MIQDAD jiyai xuciuarshi na harbawa ,a haka ya karasa gun då take ya xuguno yana källan fuskarta ,hannu yasa yana shafa fuskarta hawaye nabi mishi fuska ,

doke hannunshi MUWADDAH tai ,tace "wa ya kawoka gidanmu ,ko angayama har yanxu ni matarka ce då xakaxo kana tabani ,to Wannan då kake gani ,ta nuna MUSADDIQ shine mijina jiyannan aka daura mana aure dashi ,dan haka kai gaggawar fuce mna daga gida ,


Irin kallan da MUSADDIQ yake jifanshi dashi ,na kishi kara ra a cikin idonshi ,ya tabbatar masa då maganar da MUWADDAH ta fada ,a take ya fara jin jiri na dibanshi daga xaunen då yake ,Amma a haka ya cije ya lallaba yafita yashiga möta ,yajata ,

då taimakon Allah yaisa gida ,yana fitowa daga motar yaxube a gurin hannunshi rike då saitin xuciyarshi ,idonshi na neman kakkafewa ,mai gadi ne yaje ya gayowa Momy abinda ke faruwa ,

basui wata2 ba aka daukeshi akai asibiti dashi ,










abinda MUWADDAH bata saniba ,Ammi da abbanta sun dade då shirya kansu ,Abba ne yaitai mata tinsiri tun bata sauraranshi har saida ta tsaya ta saurareshi ,ya xayyane mata dukkan abinda ya faru ,abinka då MASOYA nan då nan suka shirya kansu ,hjya bulki tai matukar farun ciki då alhj yaje mata då labarin ,a washe garin ranar aka maida musu då auransu ,


byan tafiyar MIQDAD ,MUWADDAH tashi tai tanufi daki då gudu tana kuka ,MUSADDIK ya rintse idonshi xucianshi fal kishi ,


A haka Ammi da Abba suka shigo suka taddashi ,

sunxo subawa MUWADDAH suprise ,Ammi ce ta tambayeshi MUWADDAH yace tana daki ,

dakin ta nufa ,a kwance ta tadda ita tai shiru hawaye nabi mata fuska ,då sauri ta karasa gunta tana tambayarta lpya ,tace mata ba komai ,Ammi ta ganota sai tai murmushi tace taso muje falo ,komai ya kusa xuwa karshe ,


hannunta taja xuwa falo ,
Abba yana xaune då jikarsa då kaunarta tabi ruhinta ta mamaye xuciyarsa ,

MUWADDAH kallan abban nata take ,ya bude mata hannunsa alamun ta taho ,då gudu ta karasa ta fada jikinshi ,xuciyarta ta cika da farin ciki ,


anan suka bata labarin duk abinda ya faru ,harda maida auransu ,a take MUWADDAH yashiga cikin. matukar farin ciki ,






Momy banda kuka ba abinda take har xuwa Wannan lokacin MIQDAD bai farfado ba ,

Ikon god , *SILAR SOYAYYA*yaudai ga MIQDAD a kwance a gadon asibiti ,

waya akaiwa abban MUWADDAH aka gaya masa lokacin suna xaune suna hira cikin farin ciki ,Abba yace Su taso Su rakashi unguwa ,


harda MUSADDIQ suka rankaya suka tafi hospital in ,

Momy tana ganinsu taje ta rungumo MUWADDAH ta amshi nuwaira dake hannunta ,knä tace "kimin rai MUWADDAH ki shiga dakincen MIQDAD yana ciki ki taimaka ki masa magana ko xai farfado ,dan näsan *SILAR SOYAYYA* rki yake cikin wannan hali ,

MUWADDAH kanta a sunkuye yake ,ta dago ta kalli Ammi ,Ammi tai mata nuni daka alamun taje ,da gudu ta juya ta nufi dakin då MIQDAD ke ciki ,




byan barinta gurin momy ta nemi yafiyar Ammi ,Ammi tace Allah ya yafe mna baki daya ,


A bakin kofar dakin ta tsaya tana kallanshi hawaye na xirara a idanunta ,

motsi ya fara då kafafunsa yana sambatu ,
Meyasa kikai aure kika rabu dani ,kinsan baxan taba iya rayuwa babu ke ba MUWADDAH,ina sanki ina kaunarki dan Allah ki dawo gareni MUWADDAH ,

Kalmomin då tadae tana jira taji daga bakin MIQDAD sai yau tajisu ,da gudu ta karasa inda yake ,ta kama hannunshi ta rike kam ,nima ina sanka MIQDAD baxan iya rayuwa da wani namiji ba byan kai ,

Xumbur yai yamike yna kallanta ,ganinin abin yake kmar a mafarki ,jikinshi MUWADDAH ta fada ta kamkameshi tana hawaye ,hannuwansa shima yasa ya matseta pls ko da wasa kar ki rabu dani MUWADDAH ina sanki ina kaunar ki ,kece farin cikina kece nutsuwata ,





A ranar aka sallami MIQDAD ,washe gari aka maidar musu da aurensu ,musaddq ya hkura ysan koda ya auri MUWADDAH saidai ya xauna da gangar jikinta amma xuciyarta na ga MIQDAD,


Ranar då tare ,tasha tattali gurin MIQDAD soyayya yake nuna mata xallah babu digon algus a ciki ,ga diyarsu nuwaira tana samun kauna ta kowani bangare ,




Abbah yna kulawa då MUWADDAH sosai ,wanda då baimata ba ,bya xuwa gidan ya"yanshi amma akanta ya fara ,yanai mata soyayyar da ya maye gurbin Alh bukar ,hjya tasaka ya maida mami byan ta ladabtu ta gane kuskuran da ta aikata ,



soyayya MUWADDAH suke gurxa san ransu ,soyayyace ta gaskiya då mutnta juna ,duk abin da MIQDAD yasan xaiyi ya kära masa soyayya Gun MUWADDAH shi yake ,hakama MUWADDAH ta xage damtse wajen farantawa mijinta domin takai ga samun aljannah ,

kullum xancen MIQDAD kar MUWADDAH ta rabu dashi ,domin rabuwarsu shi yasan wahalar da yasha ,iatakuma sai tace masa "SILAR SOYAYYAr då nake maka baxaisa na rabu dakaiba ina tare dakai a ko dayaushe masoyina "


*TAMMAT BI HAMDILLAH*


Kuskuren dake ciki Allah ka yafeni ,abinda ke cikii mai kyau Allah kasa mu amfana dashi Ameen ,


ina matukar godiyya gareku yan gruop ina abin alfaharina ,

HEENAH NOVELS GRUOP

Yan uwana ,abokan rayuwata ,nababa family wannan littafi sadaukarwa ce gareku ,Allah ya kara hade kawunanmu ya kara mna dankon xumunci Ameen,


Sakon gaisuwa gareku mutane na kwarai ,

My bestty na Ayshat
Huussaina
Xaharatee(Amarsu)
nafiisa musa
Ummi abuja
Fadima (uwens)
Ummu suhaima

Ina fatan sakon gaisuwata ya iso gareku,


Taki gaisuwar daban take my aunty ,Allah ya karo lafiya da nisan kwana ,halinki daban yake my aunty hudah ke dinma ta dabance luv u with all my heart😘

Kuma taku gaisuwar då ban take,

Suhana '(jinin jikina)

Ayusha(autynmu)

Classic feedoh(sis inmu)

Maryam yar mama

Jannart(yar basaja)

Ferst lady

Hussaina(momma)

Asy khalil

deejah waxiri
Eshert (tsafawa)
Aunt ummah ,dama dukkanin members in *musan junah o.h.w* dukkaninku inai muku fatan alkairi ,allah ya karo muku fasaha då basira ,
Ameen,



sai mun kuma haduwa cikin karashen littafina *masoya*

Yar gatan hudah na muku fatan alkairi


ina cigiyar kawayena

Humaira xamfara
nd
Umukhurrsum (diyana)

in sakona yaisa gareku ku tuntubeni a wannan numb 👇🏻

09037093702
Rabee'arth shu'ayb nababa





*THE*🔚







Author
: bebe'arth😘

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment