Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata get ta fice kamar wadda zata tashi sama sai taunar cingom dinta takeyi.

Ta mik'i hanya tareda k'ule volume na wakar dj Ab sai biyar wak'ar takeyi tana kad'a kai, duk inda ta zo wucewa sai an kalleta saboda kid'an da ke tashi , ita kam ko a jikinta domin in da sabo ma ta saba da irin wannan kallon a duk lokacin da take driving, saboda banzar shigar da takeyi sannan uwa uba kid'an da take kur'e volume ko'ina sai ansan da zuwanta, shiyasa mummy take hanata tuk'i saboda labarin abunda takeyi yazo kunnuwanta, dalilin da yasa take b'oye makullin kenan amman duk da haka idan taso fitar, tasan hanyoyin da zata bi sai ta fita da motar, domin kuwa wani zubin ma daddy take rok'a ya karb'o mata key d'in idan ta kasa gano inda Mummy ta ajiye shi, aiko da yake baya son ganin b'acin ranta sai yasa mummy dole sai ta bata makullin.

Tana tafe tana duba agogo ganin k'arfe hud'u har ta gota, yasa ta k'ara gudu a cikin minti biyar ta isa zambia Park, tana ajiye motar inda ake parking ta fito ta tsaya a jikin motar, tareda jawo wayarta ta fara kiran number'r honey'nta, yana d'agawa yace da ita ta k'araso gashi yana jiranta, tareda yimata kwatancen inda zata sameshi, a cikin takunta na k'asaita wanda tsinin takalmanta ya k'ara taimakonta wajen taya ta rangwad'a, sai taunar cingom takeyi tana kad'a key a sama sai wani shan k'amshi takeyi, tana daf da kai wurin da yayi mata kwatancen ne aka kirata a waya, tana k'ok'arin dauka taci karo da wani har sai da wayar ta fad'i a k'asa, gaba d'aya ta tarwatse a cikin masifa ta d'ago fuskarta, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar mutuminta wanda ta kira da mai fuskar shanu, a razane taja baya tareda nunashi tace, "You again?"

Shi ko sai murmushinshi yakeyi mai kama da yak'e cikin sanyin muryarshi yace, "Munara ko.?"

Munara a cikin tsantsar tashin hankali take kallonsa, sannan da bak'in cikin wayarta da yayi sanadin tarwatsewarta a daidai lokacin da tafi buk'atar ta, da kuma takaicin ko inkular da ya nuna akan b'arnar da yayi mata bale ya bata hak'uri taji sanyi, k'arin haushinta kuma sunanta da taji ya kira a bakinshi, cikin zafin nama ta d'aga hannu ta kai masa mari har biyu, sannan ta d'aga murya tace, "kai wanene da har zaka fashe man waya ka kasa bani hak'uri?, sannan kazo da wani banzan bakinka ka kira sunana."

Jikin mutumin yana rawa ya duk'a ya tarkato mata wayar, sannan ya mik'ata mata yana cewa, "Don ALLAH kiyi hak'uri ba da gangan nayi maki ba, na amince duk hukuncin da kika ga ya dace dani ki yanke man kawai, idan dai har zaki fuce ki yafe mani."

Munara tayi masa wani banzan kallo tareda buga masa tsaki, ba tareda ta karb'i wayar ba ta saka hannu ta zaro Sim card's d'inta sannan ta k'ara buga masa wata harara tace, "Me zanyi da wayar da ka rarratse kai ne matsiyaci kaje da ita ka gyara na barmaka, don bazan tab'a had'a hannuna da na kutare irinka ba, masu saka safa hannu da k'afa don salon cuta su shafawa mutane kuturta,amman tunda har neman gidan aiki kakeyi to ai kasan gidanmu ka zo gobe zan samar maka aikin yi, koda zaka sami kud'in da zaka sayi maganin sauk'in kuturtar ka daina saka safa."

Har k'asa yakai yana yimata godiya ta saka k'afa ta ture shi ya fad'i ta tafi tana warar idanuwan ta inda zata hango honey'nta, amma kash duk inda ta kurd'a lungu da sak'o bata hango ko mai kama dashi ba, a dole ta koma gida zuciyarta cike da bak'in cikin rashin had'uwarsu, sai tsinewa mai fuskar shanu ta keyi tareda k'udurta irin wulakantashin, da zatayi idan har ya kuskura yazo gidansu da sunan d'an aiki.






Akwai Gumurzu fa😹😹shin wai wanene basarake???, haka ma munara da munawwa su waye???kuci gaba da biyoni domin in warware maku zare da abawa💃🏻.



D'ari biyu kacal zata baki damar ci gaba da jin labarin BAKON YANAYI 09032685442 number ta ga mai bukata.




Akafta



Nice taku🤝🏻

*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki buk d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

Free page 4.

**********************

Tana cinno kan motar cikin gidansu taji gabanta ya fad'i, saboda tuno irin artabun da zasuyi ita da Mummy idan ta shiga gidan, cikin rawar jiki ta samu ta ajiye motar sannan ta fito ta nufi cikin gidan, sai da ta fara lek'e lek'e ta tabbatar bata hango Mummy ba, aiko afujajan ta bazama da gudu ta fad'a d'akinsu tareda murza key ta rufe, hannunta a gaba ta sauke ajiyar zuciyar cin nasara, juyawar da zatayi tayi arba da Mummy dake zaune tana kallonta fuska tamau ba alamun sassauci, aiko Munara ta gwalalo idanuwa tareda juyawa tana k'ok'arin bud'e d'akin ta fita, bulalar da taji ta sauka a bayanta ne yasa ta daina yunk'urin bud'e d'akin, ta fara kururuwar kiran sunan Daddy ya zo ya taimaketa, Mummy ko ta saki k'wanji tayi ta jibgarta da dorina, sai ga Daddy cikin tashin hankali yana kiran sunan Mummy yana mata kashedi akan kada ta kuskura ta sake dukanta har da yin ratsuwa, cak Mummy ta tsaya saboda jin rantsuwar da yayi tana huci ta bud'e d'akin ta fice, Daddy jikinshi yana rawa yaje ya ri'ko Munara suka fito falo sai gunjin kuka takeyi, Daddy ranshi a b'ace ya fara zubawa Mummy fad'a har da ik'irarin duk ta sake dukan Munara to a bakin igiyarta d'aya ta saki.

Ba Mummyn da Munawwa ba har ita kanta Munara lafazin ya girgizata, saboda tun da suke makamancin hakan bai tab'a faruwa a gabansu ba, wasu hawayen takaici suka saukowa Munawwa a fuska cikin zuciyarta tana nemarwa 'yar uwarta shiriya, saboda abunda takeyi ya shalle tunaninta duk da kasancewarsu 'yan biyun da suka fito ciki d'aya, amman halayensu sunsha bambam da juna matuk'a gaya.

Munawwara Hasana da Munara Husaina 'yan biyu ne masu kama da juna sak,wanda a duba d'aya baza iya tantance wannan itace hasana ko hussaina ba, sai dai halayyarsu ce kawai take banbance su saboda Hasana wadda ake yiwa lak'abi da suna Munawwara ALLAH ya yota mai sanyin hali da gudun zuciyar iyayensu, yayin da Hussaina Munara ita kam tijararra ce tun tana 'yar karamarta, Munawwara tasha matuk'ar wahala wurinta a zamanin k'urciyarsu, wanda har izuwa wannan lokaci bata shan inuwa d'aya da ita, duk da kasancewarsu 'yan biyu saboda Munara bata raga mata ko kad'an, duk fad'a da dukan da Mummy zata yi mata a banza sai dai idan bata yi niyyar aikatawa ba, sai ta k'are sannan ta dawo tana jin tsoron hukuncin da za'a yi mata, Munawwara komi nata mai sanyi NE kamar yanda halayenta suke sauk'ak'a, sab'anin Munara da komi girman mutum bata shayin sakin jiki ta karta masa rashin mutunci, da bakin tsiwarta tsaf zata wanke mutum da soso da sabulu sai dai in bai shigo gonarta ba.

**

Yinin ranar cur wurin lallashin Munara Daddy ya lalace, don ko abinci da Mummy ta kawo masa bar mata kayanta yayi bai ci ba, saboda kawai an tab'a masa shalelenshi Munara 'yar gaban goshin Daddy.

Koda dare yayi suka shiga bacci daga Munara har Munawwara ba wanda yace da wani k'anzil, amma Munawwara da takaicin Munara ta kwanta cikin zuciyarta, saboda taji haushi sosai wai ace sanadiyyarta Daddy yake yi wa Mummy barazana da saki, sai juye juye takeyi ta kasa bacci, sab'anin Munara da take ta baccinta hankali kwance.

Munawwara ta tashi zaune tareda kunna 'yar k'aramar fitilar dake rage duhun d'akin, tareda bubbuga MUNAra ta fara kiran sunanta a hankali tun tana baccin har ta jiyo sautin kiran sunanta da Munawwa takeyi, a hasale ta d'ago fuskarta tana yiwa Munawwa kallon tuhuma a cike da jin zafin tada ita daga baccin da tayi, Munawwa ta had'e fuska tace, "Ki tashi akwai maganar da zamuyi."

Munara ta buga mata wani tsaki sannan ta tashi zaune tana yimata wani kallon up anda Dawn tace,

"Aikin kenan gulma ba aci gaba da yi ai har safiya ta waye, tunda kin yiman munafucci an dake ni to kuma yanzu me kike so kice dani?, inyi hak'uri ko kuma wani tsegumin ne kike so ki kwaso ki sauke shi a kaina, to ni banida lokacinki hajjaju."

Ta k'are maganar tareda gyara kwanciyarta, Munawwa ranta yayi k'ololuwar b'aci shiyasa ta fara furzo kalamanta kamar haka, "Duk abunda zaki yiman ba zan fasa fad'a maki gaskiya ba, saboda abunda kike aikatawa kwata kwata bakya kyautawa kanki da iyayenm, domin naga abun naki yana so ya wuce makad'i da rawa, wai ace kina ji kina gani kin had'a hasuma tsakanin iyayenki, wai akanki Daddy yake furta datse igiyar aurenshi da Mummy, shin ribar mi kikeci idan kin saka Mummy a damuwa?meyasa kike mance cewa Mummy ce fa ta haifeki ba ke kika haifeta ba, yazama dole a gareki kiyi mata biyayya ko da bakya so, tun kafin fushin ubangiji ya sauka akanki. "

Munara daga kwancen tace, "ALLAHU AKBAR malama tashi kin faye naci."

Munawwara tace, "Kome zaki ce to ki fad'a gaskiya ce dai bazan fasa fad'a maki ba, don haka ki daina yin abunda zai kawo rikici tsakanin iyayenmu."

Shirun da Munara tayi mata ne yasa ta kwanta itama tun tana tunani har bacci ya yi awon gaba da ita.

**

Da safe musalin k'arfe goma na safe mai gadi ya zo yana sanar da Mummy wani yazo neman Munara, Mummy ta k'wallawa Munara kira dake kitchen tana dafa indomi ,bayan ta fito ne Mummy take sanar da ita tayi bak'o a waje, a haka da take da 'yar guntuwar riga mara hannu sai wando three quarter da d'an gyale saman kanta, tazo zata fita Mumm ta maka mata harara sannan taje d'akinsu tana gunguni ta d'auko hijabin sallahrta ta saka, ta fito tana ta Alla Alla a ranta idan mai fuskar shanu ne saboda tanadin rashin mutuncin da tayi masa, a dalilin sanadin da yayi na rashin had'uwarta da honey'nta wadda har a lokacin take cike da jin haushin wayarta da ya fasa.

Tana fita harabar gidan kuwa tayi arba da mutuminta, ta k'ara tamke fuska kamar wadda bata tab'a dariya ba, tazo ta tsaya k'erere a gabanshi jikinshi yana rawa ya risuna yana gaidata, ranta a had'e take amsawa kamar bata so kafin ya k'ara wata magana sai ga Daddy ya fito a cikin shirinshi na fita sai sauri yake zubawa, ya nufi motarshi zai shiga idanunshi suka sauka inda Munara da wannan mutumin suke a tsaye, cikin mamaki yace, "Ya akayi baby? meke faruwa ne?"

Munara ta fara magana cikin shagwab'a tace, "Daddy aiki yake nema shine nake so a taimaka masa."

Daddy ya washe baki yana dariya yace, "To ki d'auke shi kawai baby tunda kina so."

Munara tazo da gudu ta rungume shi tace, "Nagode Daddy i love you so much."

Ta k'are maganar tareda rik'o hannunshi ta yi masa kiss, Daddy yana murmushi yace, "Me too my daughter. take care"

Ya k'are maganar tareda dafa kanta sannan ya shige mota ya bata wuta, suna yiwa juna bye bye har ya fice amma ko kallon mutumin bai yi ba bale ya tsaya su gaisa, duk da yunk'urin gaida shi da mutumin yayi.

Munara daga inda take tayi masa nuni da hannu akan yazo, jiki ba kuzari ya fara taku ya nufi wurinta a cikin girmamaw yace, "Gani hajiya."

Munara tayi masa wani kallo mai had'e da harara tace, "Kaci nasara an d'auke ka aikin amma ka sani misbehave kad'an zai sa ka bar gidannan a wulak'ance, yanzu ka jirani inzo aikinka zai fara."
Bayan shigarta gida da minti biyar sai gata ta fito da kaya dunk'ule a hijabinta, tana zuwa ta watsa masa a fuska tace

"Gasu kaje ka wanke man yanzunnan."

Da sauri ya kai kallonshi a k'asa inda kayan suke watse, aikuwa sai ga bra ta kai goma zube k'asa yana k'are masu kallo d'aya bayan d'aya.







Na kudi ne mai buk'atar book d'in ga number ta 09032685442



Akafta






Nice taku

*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki buk d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

Free page 5.

**********************

*Shin wai wanene basarake?honey'n Munara, kuma mutuminta mai fuskar shanu😒*

*Aliyu Haidar* shine ainahin sunanshi, wanda ya kasance d'a a wurin Alhaji Dikko mai gwalagwalai, wanda mutane suke yiwa lak'abi da sunan *Dikko mai Gwal.*

Dikko mai gwal mai arzik'i ne sosai wanda duniyar masu kud'i kanta tasan da zamanshi, siyar da Gwalagwalai itace sana'ar da ya rik'a kuma ta zamo silar arzik'inshi, wanda ta k'ark'ashinshi mutane da dama suke cin abinci har suma suyi wa wasu hanyar samu, kasancewar shi mutum ne shi da baya son tauyewa na k'asa dashi hanyar hak'k'insu, baya bak'in cikin ta sanadinshi kai ma ka zamo wani abu, saboda ALLAH ya azurtashi da kyakkyawar zuciya da d'inbin arzik'i, wanda shi kanshi bai san iya adadin dukiyar da ya mallaka ba,ta sanadin wannan sana'ar da ya gada a wurin mahaifinshi.

A yanzu haka Matanshi hud'u amma babu wadda ALLAH ya baiwa haifuwa dashi sai mahaifiyar Aliyu Haidar, wanda ake yiwa lak'abi da suna *Basarake*, wadda ta kasance matarsa ta farko a yanzu, duk da ainahi cen ba itace matarshi ta farko ba, saboda bai aure ta ba har sai da Matarshi ta farkon ta rasu, wadda suka yi are irin na saurayi da budurwa amma har ta kwanta dama ALLAH bai bata haihuwa da shi ba, kuma bai yi sha'awar k'arin aure ba har sai bayan rasuwarta.

Wata rana yana tafe a kan hanya sun kawo wurin wata roundabout, inda danja ta tsayar dasu mutane suka yi cincirindo da ababen hawansu, suna jiran lokacin da za'a basu damar da za su wuce, Alhaji Dikko yana duba wata jaridar dake hannunshi sai ga wata 'yar matashiyar budurwa irin sadakar yalla d'innan, sai k'wank'wasa masa glass d'in mota takeyi wadda alamu suka nuna mabaraciya ce, saboda yanda take nuna masa hannu alamar rok'o, da fuskarta da ta zama kalar tausayi idanuwanta sunyi ja wadda a duba na farko zaka gano kukan da tasha, a lokaci d'aya Alhajin yaji ta bashi tausayi sosai duba da yanayinta da ya gani, direban har ya fara yimata fad'a yana korarta, Alhaji ya sauke glass da niyyar yaji k'orafinta aiko sai ga muryarta tar tar tana fad'in, "Don ALLAH Alhaji ka taimakeni mahaifiyata bata da lafiya, in sami abunda zan siyo mata magani."

Alhajin ya ciro kud'in da shi kanshi baisan ko nawa bane ya mik'a mata, jikinta yana rawa ta zuro hannu ta karb'e tareda barin wajen da gudu ta nufi wata 'yar hanya har ta shige lungun yana kallonta, haka kawai Alhaji yaji yana sha'awar ya sani shin da gaske mahaifiyarta ce ba lafiyar ko kuma k'arya ce takeyi irin ta mabaratan, a take yace da direban idan sun fita ya samu guri ya tsaya subi yarinyar cen, aiko ana basu hannu suka fito cincirindon ababen hawar dake wurin suka sami wani wuri suka tsaya, Alhajin ya fito tareda direban suka bi hanyar da suka ga tabi, abin mamaki suna shiga lungun suka hango taron mutane suna ta kallon wani abu, koda suka isa wurin sai suka ga ashe yarinyar ce rungume da wata mata sai magagin mutuwa take yi, wadda a duba d'aya zaka gano mahaifiyarta ce saboda kamar da suke yi da juna sosai,yarinyar sai kuka take yi tausayinsu ya kama Alhaji matuk'a saboda ganin ba wanda yayi yunk'urin taimaka masu a wurin, shiyasa ba wani b'ata lokaci yace a d'aukota suje asibiti, aiko matan da ke wurin suna kallo suka talallabo ta yarinyar tana biye dasu tana kuka aka saka ta mota tareda d'iyarta, Alhajin yace da direban yayi sauri su je asibiti saboda matar tana cikin mawuyacin hali.

Da zuwansu asibitin aka karb'e ta likitoci suka rufu a kanta, bayan d'an lokaci da shigarta ne wani likita ya fito yace da Alhaji su shiga matar tana son ganinsu shi da 'yarta, jikin Alhajin a mace ya nufi d'akin da aka shiga da matar yarinyar tana biye dashi sai sharb'ar kuka take yi.

Koda suka shiga yanayin da ya ga matar a ciki ne yasa jikinshi ya k'ara yin sanyi k'alau, matar sai kiran sunan 'yarta take mai suna Mu'azatu, da sauri yarinyar taje wurinta tana kuka gwanin ban tausayi, mahaifiyar ta fara magana kamar haka, "Alhaji duk da bansanka ba amma yanayinka ya nuna kai mutumin kirki ne, na baka amanar 'yata don ni nasan tawa ta k'are mu 'yan k'asar agadas ne idan 'yata ta nemi sanin danginmu duk suna cen gidan sarkin agadas, da kaje kace innayo ni kad'ai ce a duk familynmu, Allah ya taya ka rik'on mu'azatu na baka amanarta ko bayan raina bance ka baiwa kowa ita ba kai naba ita halas malas, mu'azatu kiyi hak'uri kiyi hak'uri ALLAH yayi maki albarka da ke da zuri'arki gaba d'aya idan kin had'u da iyayena kice su yafeman laifin da nayi masu don ALLAH su yafe ma..... ."

Daga nan kuka yaci k'arfinta numfashinta ya sark'e ta fara shak'uwa, likitoci suka yo kanka duk iya k'ok'arinsu basu hana mata amsa kiran Ubangiji ba, mu'azatu kam tana tabbatar da mahaifiyarta ta rasu sai gata a k'asa ta fad'i somammiya, hankalin Alhaji ya k'ara tashi da sauri aka bata gado bayan an samu ta farfad'o aka yi mata allurar bacci, har aka je aka rufe mahaifiyarta bata sani ba, sai bayan ta tashi ne, Alhaji yayi mata bayani tareda bata hak'uri, sannan ya kwasheta yakai gidanshi yana bata kulawa tamkar wata k'anwarshi ta wadda suka fito ciki d'aya, bayan wasu 'yan kwanaki yayi masu shirin zuwa k'asar agadas suka lula.



Manage plss


Na kud'i ne maiso ta tuntub'e ni ta wannan Number 09032685442.




Akafta





Nice taku💋

*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki buk d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

Free page 6.

**********************

Basu sha wahala ba wajen gano ahalin innayo ba, kasancewar gidan sarkin Agadas suka nema kai tsaye, ALLAH ya taimakesu suka sami ganin sarkin ba tareda sun sha wata wahala ba, saboda kamar da mu'azatu take yi da familyn gidan jalaludden jamil sarkin agadas tsoho mai ran k'arfe, wanda yaci lokacinshi kuma ya ke cin na wasu, don a lokacin shekarunshi zasu kai saba'in amman kar yake ba wani alamun mugun tsufa da ya bayyana a jikinshi.

Bayan sun kai gaisuwa a wurin sarkin ne kafin ma Alhaji yayi bayanin abunda yazo dasu ne, sarkin ya k'urawa mu'azatu idanuwa a cikin muryarshi mai cike da tak'ama yace, "Duk inda wannan yarinyar ta fito tabbas jinin jalaludden ce."

Alhaji wani farinciki ya lullub'e shi saboda ganin komi zai zo masa da sauk'i a cikin kwantar da murya ya fara bayani kamar haka, "Tabbas wannan yarinya 'ya ce a wurin 'yarka Innayo."

Ba shiri sarkin ya fara zubar hawaye cikin muryar kuka yace, "Ina kuka baro man 'yata innayo? duk girman laifin da tayi mani na yafe mata duniya da lahira, 'ya mai ladabi da biyayya amma saboda soyayya ta zab'i ta rabu da ahalinta, don ALLAH ku sanar dani ina 'yata innayo?saboda ina son in nemi yafiyar 'yata"

Mu'azatu ta fashe da kuka Alhaji ya sunkuyar da kai a cikin damuwa yace, "Sai dai ku bita da addu'a domin innayo ta rigamu gidan gaskiya."

Daga nan ya kwashe abunda ya sani ya sanar da sarki, sarki da sauran masu ruwa aji na fadar sai taya sarki kukan rasuwar 'yarshi sukeyi, sarki ya taso da kanshi ya ri'ko hannun mu'azatu suka shiga cikin gida, kai tsaye d'akin mahaifiyar innayo ya kaita, bayan yayi mata bayanin abunda yake faruwa kafin kace me gidan sarki ya runtume da koke koken kukan rasuwar innayo, saboda innayo 'yace wadda ta taso mai farinjini da tsantsar ladabi da biyayya ga kowa, innayo ta zuba lokaci a zamani k'urciyarta har zuwa lokacin aurenta, inda sarakuna da manyan attajirai suka yi ta rubibin aurenta, amman zuwan wani bak'on Nigeria gidan sarkin ya hargitsa kwakwalwar innayo, wanda akanshi ne ta zab'i ta bar mahaifarta da ahalinta, saboda nacewar da tayi akan soyayyarshi shine yayi silar rabuwarta da danginta bayan an d'aura masu aure, amman da sharad'in bata ba ahalinta kuma duk taji ta amince ta biyo angonta zuwa k'asar Nigeria.

Wanda shi kuma ya kasa rik'on amanar innayo ya dinga gasa mata aya a hannu har lokacin da ALLAH ya azurta ta da haihuwar mu'azatu, uk'uba babu wadda bata sha ba a hannunshi abinci ma sai wanda yaga ALLAH ya taimako ta dashi sannan take ci, batasan kowa ba sai ALLAH sai shi shiyasa lokacin da ya saketa tayi ta tanb'ele ita da 'yarta, rayuwa tayi masu tsanani basu wannan gida aikatau basu wancen, daga baya dai suka fad'a sana'ar bara bak'in ciki yayi mata yawa ta fara ciyo a tsaye wanda shine yayi silar kwantar da ita magashiyyan, wanda a sanadinshi ne suka had'u da ALHAJI Dikko har zuwa lokacin ajalinta.

Alhaji Dikko bai baro k'asar ba har sai da aka d'aura masa aure da mu'azatu, saboda a cikawa innayo wasiyyarta, bayan an sanar da dangin baban mu'azatun inda d'aya daga cikinsu ya wakilci aurenta, haka Alhaji ya tattaro amaryarsa tareda rakiyar dangin mahaifiyarta zuwa gidanshi.

Shekara d'aya da aurensu mu'azatu ta haifi santalelen d'anta, mai kama da ahalin gidan sarki jalaludden sak!, Alhaji da danginshi sunyi farin ciki sosai da wannan haihuwa, rana ta zagayo aka sawa yaro suna ALIYU HAIDAR, fad'in shagalin da aka yi a wannan lokaci ba b'ata baki ne, domin kuwa nera tasha kashi sosai marok'a da makad'a sun tabbatar da lalle wannan yaro d'an gata ne, Aliyu haidar ya taso a cikin kula da tattali na mutane da yawa, ta b'angaren uwa da uba kowa sai sam barka musamman mahaifinshi Alhaji Dikko da yake ji dashi tamkar tsoka d'aya a miya.

Aliyu har ya kai shekara goma amma ko b'atan wata mu'azatu bata sake yi ba, ganin haka ne Alhajin Dikko yayi sha'awar k'ara aure koda ALLAH zai sa ya sake samun wata haihuwar, sai gashi itama matar da ya auro har tayi shekara biyu shiru, aka bashi shawarar ya sake wani auren koda rabon a cen yake, aiko baiyi k'asa a gwiwa ba ya sake wani auren itama dai haka tabi sahun 'yar uwarta shiru ba wani labari, Alhaji bai yi k'asa a gwiwa ba ya k'ara murzo sabuwar amaryarshi sabuwa dal a kwali, sai gashi ita d'in dai ba wani alamun haihuwar har tsawon shekara, daga nan Alhaji yayi saranda ya garzaya asibitoci domin a binciki lafiyarshi, binciken farko aka gano matsalar daga gareshi ne, aka had'o shi da magunguna ya dinga sha amma har izuwa wannan lokaci ba canji.

Shiyasa ya d'auki son duniya ya d'ora akan Aliyu haidar wanda yanayin yanda yake tafiyar da takunshi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

1 Comments On BAKON YANAYI
avatar
mukhtar-naziratu-sani

9 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment