Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi da gefen bakunshi yace, "Me nayi wa babyna ni kam, baby sai kinyi hak'uri dani fa saboda nayi busy da yawa, lokacin da nayi maki kwatancen inda zaki same ni a zambia park, muna k'are wayar aka yiman kiran gaggawa, nayita kiranki akan ki k'araso mu gaisa ban same ki ba, shiyasa na tafi amman nima banji dad'i ba, naso naga babyna ido da ido domin in banbance fili da photo wanne tafi kyau, duk da jikina yana bani za ki fi kyau a fili."

Wani farinciki ya lullub'e zuciyar Munara, tayi wani tsallen jin dad'i tace, "To yanzu yaushe zamu koma had'uwa kuma?"

Basarake yayi murmushin mugunta yace, "Yanzu haka ina cikin garinku idan zaki iya zuwa k'ofa a bud'e take sai ki zo mu gaisa."

Munara tayi hanzarin fad'in "What??? surprise, wayyo ALLAH honey a ina kake? don Allah fad'a mani yanzu yanzunnan zan zo mu gaisa."


Yana murmushi ya yi mata kwatancen inda zata same shi, a guje ta fito ta jefa wayar kan gado, sannan ta koma toilet d'in ta darzo wanka jikinta yana rawa ta shirya a cikin shigarta ta k'ananan kaya, ta zunbula k'aton hijab d'inta na sallah wanda sallah ce kawai ke sa ta saka su, sannan ta d'auko wata jaka ta tura k'aramin gyalenta, da glass d'inta da turaruka sannan ta rufe jakar ta rataya, ta fito da gudu talkaminta a hannu tace, "Mummy bari inje in karb'o littafina wurin Nucy yanzu nan ma zan dawo minti biyu ma sunyi yawa."

Tana magana tana tafiya cikin sauri har ta fice, Mummy ta kalli Munawwa tace, "Anya yarinyarnan kanta d'aya kuwa.?"





Mummy kar kiga laifinta soyayya ce ta rufe mata idanuwa🤣🤣🤣🤣🤣



Na kud'i ne maiso ta tuntubi wannan number 09032685442





Akafta





Nice taku🤝🏻

*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki buk d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

K'arshen free page's 9.

**********************

Sai da ta zagaya ta bayan gidan ta cire hijabin da ta sako sannan ta bud'e jakar ta ciro gyalenta ta yafa, tareda k'wama k'aton glass d'inta bak'i wanda ya k'ara fito da kyawonta, bayan ta feshe jikinta da kalolin turaruka sannan ta fito da sauri ta jefa jakar a mota, ta ja motar da k'arfi ta fice gidan zuciyarta cike da d'okin ganin honey'nta, tafe take akan hanya tana ta wassafa yanda za suyi four eye's da shi ido cikin ido, zucuyarta lullub'e da farin ciki marar misaltuwa tafe take a kan titi kamar kullum ta saki kid'a sai tashi yakeye, duk da go slow d'in da ke kan titunan amma minti goma kacal suka kaita hotel d'in, saboda yanda take ta zuba gudu abinta sai kace ita kad'ai ce a saman titin.

Bayan tayi parking d'in motar ne ta k'ara jawo turaruka ta bulbulewa jikinta sannan ta fito tana gyara zaman half gawn d'in rigar kantin da ke jikinta,sai yatsine yatsine take yi tana wulla idanuwanta sama da k'asan hotel d'in, a zuciyarta tana ta tunanin ta ina ma zata fara ne?, aikuwa sai ga kiran Basaraken ya shigo wayarta, jikinta yana rawa ta d'auki wayar tareda cewa, "Honey Ga ni na shigo a ina zan same ka?"

Sadauki ya yi mata kwatance inda yake sannan ta kashe wayar ta fara taku k'wask'was da takalminta masu bala'in tsini, tafe take tana yauk'i yayin da idanuwa da yawa suka lalace wajen kallonta,a hankali take taku tana rausaya har ta kai inda Basaraken yayi mata kwatance, amman abun mamaki tun daga nesa ta hango kamar shine rungume da wata tana yi masu selfie, duk da bata tabbatar shine d'in ko ba shi ba ne ba amman ranta yayi matuk'ar b'aci sosai , a cikin sauri ta fara taku kamar wadda zata tashi sama haka take tafiya har ta isa wurin, mezata gani ashe Honey'nta ne rungume da macen ba wani dogon tunani da tayi bale jinkiri kawai ta saka hannu ta wanka mata mari, sannan ta jawota k'iiiii ta jefata cikin ruwan swimming fool d'in tana huci tareda nuna ta da d'an yatsa tace, "Babban kuskuren da zaki tafka a rayuwarki shine in k'ara ganin kin rab'i honeyna, domin akan hakan wallahi babu kalar matakin da bazan iya d'auka a, kanki ba, ke akan ma duk wata shegiyar macen da tsautsayi zai biyo kanta, idan kuma kina da ja a zancen nawa k'addara ta aike ki ki k'ara kwatanta abunda kika yi."

Tana k'are maganar tayi fuu zata bar wajen mutanen da ke zagaye da wurin suka fara sowa suna tafi tareda jinjina mata, matar da ta jefa a ruwan kuwa ba k'aramin tsoro fuskar Munara da kalamanta suka bata ba, duk da kasancewarta tsohuwar 'yar bariki saboda a zatonta Munara matarsa ce, shiyasa ta fito da kunyarta tsamo tsamo ta bar wajen.

Munara kuwa ko kallon Basarake bata YI ba ta juya ta fara tafiya zata bar wurin, aikuwa sai gashi da sauri ya biyo bayanta yana kiran sunanta, tayi banza dashi ta ci gaba da tafiyarta a cikin zafin nama ya ci gabanta tareda rik'o hannunta, ba shiri Munara ta fashe da kuka basarake ya fara magana damuwa shinfid'e akan fuskarshi kamar da gaske yace, "Haba baby cooling down plss."

Munara ta d'ora idanuwanta cikin nashi tace, "Ba wani cool dawn da zanyi ashe daman ka kira ni ne domin ka tozartani?, to na gani sai me kuma kake so in k'ara sani? Wallahi nayi danasanin zuwana wajenka, ina d'okin zan sami farin ciki a raina amman sai gashi bak'in ciki ya kawo man ziyarar bazata, ni kam wannan rana ta zame mani bak'ar rana mai cike da d'inbin takaici."

Ta k'are maganar a cikin wani sabon kuka Basarake yayi murmushi yace, "Duk wannan kishin ni kad'ai wow ashe haka nike da babban matsayi a gunki baby?Alhmdllh naji dad'i sosai babyna tana kishina kiyi hak'uri kinji wallahi nayi ne kawai don na gwadaki, amman wallahi ba halina kenan ba trust to me my sunshine baby."

Munara ta d'ago fuska tareda galla masa hararar soyayya tace, "Kaji dad'i ka sanya ni kuka a had'uwarmu ta farko."

Basarake ya rik'e kunnuwanshi duka biyu yace "Am sorry."
Tareda jifarta da wani irin masifaffen kallo har sai da taji tsikarta tayi yarr, sannan tayi murmushi tareda gyara tsayuwarta tace,

"Ai shikenan kuma tunda munga juna ni zan wuce gida."

Basarake ya yi saurin fad'in, "Ai baki isa ba har sai kinzo mun zauna mun gaisa a tsanaki, don haka zo muje mu d'an zanta in k'ara bada hak'uri."

Munara tayi murmushi wanda ya kasa b'oye farincikin da take ciki, saboda ba k'aramin dad'i taji ba da ganin Honey'nta wanda a zuciyata sai fad'in take yi, "Ashe ma Honeyna yafi kyau a fili."

Yace ta zo su koma cen wurin tace ita sam bazata koma wajen ba saboda hotonshi da na yarinyar ya kasa barin idanuwanta, shiyasa yace da ita tazo su je wani gun, ai kuwa suka jera suna firarsu ta masoya suka nufi wata 'yar rumfa inda tsirarun mutane ne a ciki, bayan sun zauna ne ya bada odar a kawo mata abun tab'a baki, minti biyu tsakani aka cika d'an table d'in dake tsakiyar kujerun, Basarake ya kalleta yayi murmushi yace,

"Ashe haka kike kishina baby.?"

Munara ta jefe shi da wani kallo tace, "Da kasan yanda sonka yake wahalar da zuciyata da baka yi wannan tambayar ba, Wallahi honey baka ji yanda naji ba lokacin da naga wannan matsiyaciyar a jikinka, ji nayi kamar an watsa mani wani ruwan dalma a jikina, don ALLAH honey ka soni ko da rabin son da ni nike yimaka ne kaji."

Ta yi maganar cikin sanyin murya tareda zubowar wasu hawaye a kan fuskarta, Basarake ya kalleta sosai tsawon minti biyu saboda ta bashi tausayi sosai, amman tuno halayenta na rashin ganin girman d'an Adam, da tsagwaron rashin mutuncinta ya yi saurin kawar da tausayin yace da ita, "Yanzu a k'addara wani abu ya gifto a tsakaninmu ace ban aure ki ba ya zaki ji kenan.?"

Munara tayi saurin runtse idanuwanta tace, "Ka daina fad'ar wannan magana plss honey wallahi zuciyata zafi take yi, kasani har abada bana fatar abunda zai gifta d'in wanda har zai yi sanadin rashin aurenmu, saboda tabbas ko wacece k'addara ta hau kanta ta aure man kai wallahi zata jefa rayuwarta a cikin gagarumin had'ari, kai bari in ma kai maka k'arshen zance ko Munawwara ce tayi k'ok'arin raba ni da kai, wallahi bazan tab'a barinta taci bulus ba saboda kai nawa ne babu wata shegiyar macen da ta isa ta mallake ka face ni babynka Munara."

Lafuzzan da ke fita a bakinta sun saka Basarake fad'uwar gaba sosai, musamman Sunan Munawwa da ta ambato ya sanya jikinshi yayi sanyi k'alau, a cikin sanyin Murya yace da ita, "Anya baby wannan zafin kishin naki bai yi yawa ba kuwa?kinsan fa yanzu ba'a son mata su kasance masu zafin kishi sosai, ki rage kinji baby don bana son ki d'aga hankalinki a banza."

Munara ta harareshi tace, "To ka kiyayi abunda zai jawo kishin shikenan sai a zauna lafiya."

Basarake yayi murmushi tareda rungume hannuwanshi a k'irji yace, "Rigima baby."

Munara tayi 'yar dariya tace, "Ai kai ka jawo komi."

Basarake yayi murmushi mai sauti yace, "Har marin da kika yiwa 'yar mutane ni na jawo mata kenan? cab amma kam ta maru gaskiya ."

Munara ta k'yalk'yale da dariya tace, "kad'an ma tagani WALLAHI don bazata iya jurar tanadin balbalin bala'in da nayiwa duk wata 'yar iska mai son raba ni da kai ba."

Basarake yayi wani murmushi da shi kad'ai yasan ma'anarshi yace "ko"

Tace "Of course"


A haka dai Basarake ya biyeta, yayi ta janta da fira har ta saki suka ci suka sha suka koma photuna har sai da aka yi magriba sannan ya rakata har bakin motarta, bayan sunyi sallama ya fad'a mata cewa gobe tun da sassafe zai wuce Abuja.

Munara ta dawo gida a cikin shauk'in son Basarake da ya mamaye lungu da sak'o na zuciyarta, ko da ta dawo gida har an fara Isha'i saboda sai da ta biya gidansu Nucyn sannan ta garzayo gida, farinciki fal ranta shiyasa lokacin da ta dawo Isah yana sallah tayi ta horn amman bai zo ya bud'e mata get ba, da kanta ta fito ta wangale get d'in sannan ta shiga da motar ta ajiye, bata bi ta kan Isah'n ba ta shige cikin gida abinta, Isah da har rafkanuwa yayi a cikin sallahr saboda jin tsoron abunda zai je ya dawo, yana ganin ta shige hankalinshi ya kwanta tareda sauke ajiyar Zuciya yace, "cab ALLAH ya soni yau."


Munara koda ta shiga Mummy tana d'akinta tana sallahr,kai tsaye ta wuce d'akinsu ta tarar da Munawaa ma sallahr takeyi, itama ta fad'a toilet ta d'oro arwallah ta ranka magriba sannan tayi isha'i, bayan tayi addu'o'inta wad'anda duk na rok'on ALLAH ya k'arawa Honey'nta sonta cikin zuciyarshi ne, sannan ta tashi tsam tareda jefar da hijabin akan gadonsu, sannan itama tayi sufa ta fad'a gadon tana murnar jin dad'in ganin honey'nta da tayi a yau ido da ido, sannan ta jawo wayarta ta fara duba pic's d'in da suka yi dashi, d'aya bayan d'aya wad'anda duka sunyi kyau masha ALLAH, Munawwa sai kallonta takeyi a cike da mamakin wannan farin cikin da take yi, ganin Munara ta raja'a da kallon wayar ne tana ta murmushi yasa ta lek'o kanta domin taga me take kallo haka, aikuwa sai ga photon Munara da Basarake ya fito b'aro b'aro a kan screen d'in wayar sai kallon juna su ke suna murmushi, ba shiri k'irjin Munawwa ya buga dam! Saboda ita ta rasa me ke saka ta fad'uwar gaba a duk lokacin da taga pic d'in Basarake, tun ranar da ta fara d'ora idanuwanta a photonshi take jin haka, wanda ta rasa gano dalilin da yake saka ta fad'uwar gaban, duk da watarana tana jingina hakan da cewa saboda tsananin kyaun da yake da shi ne.

Munawwa ta shagala da kallon pic's d'in da Munara ta ke ta bud'awa nasu ita da Basarake, jin numfashin Munawwa a kusa da ita ne yasa ta d'ago fuskarta ta dubeta, da sauri ta tashi zaune tace, "To uwar tsugudidi me ake kallo ne?"

Munawwa tayi dariya sannan tace, "Pic's dinku na gani kunyi kyau."

Munara ta galla mata harara tace, "To kije da ALLAH ya isar kallon honeyna da kika yi, don wallahi in dai kinsan kin kallar man shi to ban yafe maki ba."

Munawwa ta zaro ido a waje tace, "Munara kinsan me kike fad'a kuwa?"

Munara ta harareta tace, "Ciyon hauka ne a kaina."

Munawwa ta yi mere tace, "Naga alama kam, amman in dai haukar bata duka bace ai da sauki."

Tana k'are maganar ta fito falo ta bar mata d'akin, Munara ta buga mata wani uban tsaki tace, "Kyaji da shi Uwar tsugudidi wallahi akan honeyna zan iya sab'awa da kowa don bani da aminci da kowace mace akanshi, duk girman kusanci na da mutum kuwa wallahi zan iya yaga masa rigar mutunci ."





Akwai tarzoma😱




*Free pages sun k'are maiso ta saya d'ari biyu ce kacal ta hanyar turo katin Mtn ko aitel ta wannan number 09032685442 ko kuma Transfer ta wannan account 1230094555 Access Bank Hadiza D/Auta sai kun garzayo ⛹🏻‍♀️kada ku bari ayi babu ku, saboda akwai ruguntsumi a gaba💃🏻*




Akafta







Nice taku🤝🏻
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

1 Comments On BAKON YANAYI
avatar
mukhtar-naziratu-sani

9 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment