Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*search me on Wattpad at zainab muhammad kabir*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*
I just published "GUGUWAR ANNOBA" of my story "Guguwar annoba". https://www.wattpad.com/1172169279?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZaynerbmuhammadKabee&wp_originator=Sj1zDcraxaYZzmC9Io4rpJM4imk7lyp3vv1kuKHu3mzg2UiRAc0QKSxjxuwFfOsLsMVxF5kkeKlOYOIqwuBH418Z4dzWmV2ANoWpbUlG%2FgvG37fLNf9j31tMcduxf4z0

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*FREE PAGE 1&2*

*JOS LOCAL GOVERNMENT PLATEAU STATE*

*RING ROAD ARE'A*


Wata unguwa ce a bayan gari ,inda dɗaɗɗaikun mutane ne ke zama a cikinta....

Babu laifi anguwar nada kyau da tsaruwar gaske ........

Saidai ba kasafai ake samun mutane a Anguwar ba .....


Wani katafaren gida na hango mai matukar kyau da tsaruwar gaske....

Fentin gidan jajawur ne ,sai ratsi_ratsin dark brown kadan a jiki...

Gida ne na Alfarma, gidan sama ne mai hawa biyu....

Tsayawa tsara irin had'uwar gidan 'bata lokaci ne......

Kai tsaye na kutsa kaina cikin gidan , don shiga na gano ko su waye a ciki......

Ga mamaki sai na hango yarinya yar shekara goma sha biyu tana ta fama da tilin wankin da ke gabanta....

Jikinta sanye yake da wando da riga gashin kanta anyi Kitso guda hudu duk kitson ya tsufa, har ba'a ganin tsagun kitson.......

Da gudu wata yarinya ta nufo gurinta wacce bata fi shekaru hudu a duniya ba da d'an tsamun bakinta tace," Aunty HIBBA, kinga mufida ta dakeni ko, kuma ta zubar mun da abinci na tafad'a kamar me shirin yin kuka.......

Mi'kewa tayi tsaye kasancewar a sunkuye take wankin....

hannunta tasa tarike dan karamun kugunta tace,"wash Allah na , gwanin ban tausayi.....

Nan ta maida hankalinta zuwa ga yarinyar da takemata magana cikin sigar rarrashi tace," kiyi ha'kuri kinji ilhama na ki kiramun ita, daganan kice nihat tazo ta tayani wankinan mana nagaji wallahi , to ilham tace gamida komawa cikin d'akin da gudu....

Zazzaune suke akan kujera a lafiyaiyyan falonsu ...

A'kalla zasu kai su bakwai....

Maza uku mata uku, mata hudu.. ...

Babban mai suna Mujahid zai kai shekara bakwai a duniya ,sai na biyu mai suna Ajmal shi zai kai shekaru shida ,sai na ukun jawad zai kai shekaru biyar ......

A matan kuwa Hibba itace babbarsu sai Nihat datakeda da shekaru takwas ,sai kuma mufida da takeda shekara biyar itama ,sai kuma ita ilham da takeda shekaru hudu......

Kallon nihat ilham tayi tace," wai kizo inji Anti hibba ....

Mai da kallanta tayi zuwa ga mufida tagalla mata harara tace,"kema kije,tafad'a tanayi mata gwalo ....

Kai tsaye nihat ta fita..
Taje gurin hibba , tace," Anti hibba gani ...
Haba nihat kina gani inata wanki tuntuni bakizo kin tayani ba hibba tafad'a gwanin ban tausayi ...

Hannu nihat tasa akai tace", wallahi kaina ciwo yakemun yau tun safe ....

A jiye wankin hannuta ta tayi , ta goge hannnuta ,ta matso kusa da nihat din tace," ciwon kai kuma? shine baki fadamun ba kikayi shuru ko?....

Rike hannuta ta yi tace," sannu muje d'aki na baki magani sai kisha ki kwanta ko?....

To tace," suka nufi d'akin ta d'aukko magani ta tabata tasha tace ta kwanta .....

Kwanciya nihat tayi a 'katon gadansu itakuma hibba ta Koma ta ci gaba da wankin ta ......

Bayan ta gama wankin, ta d'ebo safinansu na school ta wanke musu ta d'aukko sandals dinsu ma ta wanke musu.......

Sauran yaran suna d'aki suna wasa....

Misalin karfe biyar ta gama wankin.....

Bayan ta gama ta fara 'ko'karin d'aura girkin dare ......

'Daki ta shiga ta same su suna zazzaune tace,"yau me kukeso kuci?

Shinkafa da wake suka fad'a lokaci d'aya...
murmishi hibba tayi da ya baiyyana kyakyawan dimples dinta tace," to shikenan barin je in d'aura yanzunan....

to sukace ,cike da murna .....

Wake ta tsince kafin daga bisani ta d'ora akan Wuta , tafara 'ko'karin had'a girkin .....

A na kiran sallar magriba hibba tace suje suyi sallah ..
ba musu suka je sukayi ....

Misalin 'karfe bakwai na dare hibba tagama abincinta ....

Zuzzuba musu tayi suka fara ci .....

Bayan sun gama ta umarcesu da suje suyi sallah isha'i .....
ba musu kuwa suka tashi sukayi sallan .....

Bayan sun iddar Hibba itama tayi sallahn ta ci abinci ...
Bayan ta gama ta debo uniform din su na school ta goge .....

Bayan ta gama ta 'Kara gyara Inda suka 'bata , ta d'aukesu ta kaisu gurin kwanciyarsu , ta gyarasu ....

Misalin 'karfe goma na dare hibba tagama komai ....
Bayan ta gama itama ta nufi d'akin ta kwanta a kan gadonta ..

Shuru tayi kamar me nazarin wani abu..

Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo mata a gefen idonta tayi saurin sharewa , da haka har barcin wahala yayi awun gaba da ita .....

Misalin 'karfe biyar na asuba hibba ta tashi tafara 'ko'karin saka ruwan wanka kamar yanda ta saba ......

Bayan ta gama ta fara 'ko'karin had'a musu breakfast ....

DanKali ta d'ebo tafara ferewa....

Ana kiran sallah tayi sallah .
Bayan ta iddar tacigaba da aikinta .......

Zuwa karfe shida ta tashesu.....

Mufida da ilham ,da jawad hibba tayi ma wanka, ta zubama sauran ruwan wankan suma sukayi , daga bisani suka fara 'ko'karin shiryawa.......

Bayan sun sa uniform hibba ta had'a musu tea , ta zuba musu chips din da ta soya musu suka faraci.. ...

Bayan sungama suka shirya tsaf_tsaf cikin uniform din school din.....

Bayan sun gama shiryawa hibba ta kulle gidan ta rakasu suka tafi ......

Bayan ta kaisu ta dawo , nan tafara kokarin gyara gidan ...

Misalin karfe tara hibba ta gama gyaran gidan tas......

Bayan ta gama tawanke kwanukan da suka karya , daga bisani itama tayi wanka ta karya ....

Zuwa karfe sha d'aya hibba tafara 'kokarin girka musu Abincin rana ......

Shinkafa dafa duka ta girka musu ...
Da Sauri_Sauri tayi ta gama gudun kar su dawo daga school suji yunwa bata gama ba , hakan yasa hankalinta ya matu'kar tashi .....

Zuwa sha biyu da rabi tagama girkin kasancewar a gas ta d'aura , hakan yasa girki da dahu nan danan ....

'Karfe d'aya da minti ishirin suka shigo gida.......

Da gudu suka rungu mota sukayi mata oyoyo cikeda da jin dadi ...

Itama oyoyo tayi musu , suka Shiga daki ......

Cikin farin cikin take fad'in," yauwa 'yan Albarka kun taimakeni wallahi , yau bakuyi datti da uniform d'inku ba , basai na wanke ba tafad'a tana 'ko'karin cirema ihlam uniform d'in jikinta......

Bayan sun cire uniform din ta d'aukko musu kayansu suka sa, daga bisani ta zuba musu abinci suka ci......

Bayan sun gama hibba ta share gurin da sukaci abincin tas ....

Tasa su sukayi sallah , bayan sun iddar ta ce su daukko home work din su suyi...
Daukkowa sukayi , suka farayi , ita kuma ta fara wankemusu safinansu na school .......

*RIKKOS ARE'A*

'Karamin gidane d'an daidai .....
Bazamu kirashi da gidan talakawa ba sai dai zamu kirashi da gidan masu karamun karfi .......

Domin gidan babu ko fenti a jiki ,sai 'yar 'karamar kofar Shiga ....

Gefen gidan akwai dan 'karamin dakali.........

Wata 'yar budurwace a 'kalla zata kai shekaru goma sha bakwai zuwa sha takwas a duniya.....

Tana da haske daidai gwargwado ba laifi ,doguwace bazamu kirata mai kiba ba kuma bazamu kirata siririya ba .....

Tana dakayu sossai ba laifi ga dogon hancinta da d'an 'karamin bakinta ....

Kwance take a d'aki tana danna wayar tana murmishi da Alama dai chartting takeyi ....

Ringing wayarta tafara ,murmushi tayi ganin sunan nurul_aini akan screen din wayar ...
mamaki fal a fuska , ta daga wayan cikin sigar shagwa'ba tace,"menene kuma ?ai nayi fushi tunda kace bazaka zo ka ganni ba yau....

Dariya ya tuntsure dashi yace," okay to in an gama shagwa'ban, an gama turo d'an karamun bakin sai a fito gani a waje ina jira ,yakarasa maganar yana dariya gamida kashe wayar ....

Firgit ta mike tana zaro ido tana me cike da mamaki .....

Da sauri ta d'auki hijabinta tafita.....

Dakin mahaifiyar ta tashiga , da Sauri tace,"Ammi ina zuwa , barinje nadawo tafad'a gamida juya ta fita da saurii....

Da kallon mamaki amma ta bita tace," hmmm Hamdiyya , Allah dai ya shiryaki ,duk yanda akayi wannan d'an ana cen ne yazo ta d'ebi jiki ta fita , ammi tafad'a tana ta'be baki ,had'e dakai loman tuwanta baki .......

Fita tayi, ga mamaki ta hangoshi zaune akan dakalin gidansu, murmushi tayi da ya baiyyana kyawawan fararan hakwaranta ta kura mishi kallo tana 'ko'karin karasawa gurinshi .....

Tsayawa tayi agabanshi tace, baby am happy to see you ,ashe da gaske kake , shagwa'be fuska tayi tace,"Allah da bakazo ba da ka zo ka sameni kwance gadon asibiti ......

Dariya yayi da ya baiyyana wushiryanshi yace,"ohhh to ke a gadon asibiti zaki kwanta nikuma da banzo na ganki ba da a mutuwary zaki sameni ......

Zaro ido tayi ta bud'e baki tasa hannunta ta rufe bakin tace,"laaa dan Allah rufamun asiri karka 'karamun irin wannan fatan ,tafada tana shirin zama kusa dashi ......

Dariya yayi yace," to shikenan na daina bazan karaba ,yakike? Lafiya kalau ta amsa ...

Mai da hankali shi yayi gare ta ya kura mata ido yace," baby! Kura mishi ido tayi ta amsa da na'am...
Baby na matsu naga na aure ki , na matsu naga kunfara exams dinan kungama komai yayi daidai , wallahi ina san ki ina kaunar ki, .. ...

Murmushi tayi tace," my love nima haka ina sonka , kamar yau ne fa , sauran watanni uku ne mu fara fa , ka kwantar da hankalinka , ni takace ta har abada inshallahu ......

Baby to ki amince na kawo sadakin ki mana kawai , kinga kafinan kin gama exams din sai asa ranar aurenmu kawai ......
Murmushi tayi tace", hmm my love kayi ha'kuri mubi komai a hankali inshallahu hamdiyya takace ta har abada so ka kwantar da hankalinka kaji mijina ...

To shikenan Allah yasa ,yafada gamida da sakar mata wani 'kayataccen murmushi.......

Da Ameen ta amsa itama ta sakarmishi 'kayataccen murmishi..

Hira sukayi sosai irin nasu na masoya sukayi , cike da farin ciki da so da 'kaunar juna.......

Bayan sungama hirarsu daga bisani sukayi sallama cike da kewar juna da kauna....

Bayan hamdiyyah ta koma gida , kai tsaye d'akin mahaifiyarta ta shiga tace," sannu Ammi ....

Harara ammi ta galla mata tace," eh kyace sannu ai , dariya hamdiyyah tayi tace," me za'a girka da daddare?

Ki siyo taliyar hausa kawai zuwa anjima sai ki dafa, to tace," gamida cire hijabin jikinta tafara 'ko'karin yin wanke_wanke dake zube a tsakar gidan.....


*KASAR INDI'A*

Wani katon daji ne a wani yanki na kasar indi'a....
bishiyoyi ne ko ta ina da kanan kududdufai .....

Shuru dajin yake , banda kukan tsuntsaye da kwad'ina babu abun dake tashi a gun, dajin nada matukar had'arin gaske......

Ba ko wane ke iya shiga ba sai wanda yasan kan dajin , saboda duk wanda ya shiga ba lallai ya fito da rai a jikinshi ba ...

Sai dai abun mamaki wani katon gidane a dajin shi kadai , anyi mishi rufi da jan kyalle , da bakin kyalle .......

Wata shu'umar dariya na jiyo mai dauke da kuwa da kuruwa , wanda matukar mutum yaji shi to fa ba lallai ya kara jin magana ba ,domin ko shakka babu sai kunnenka ya toshe ..

bugu da 'kari jin wannan dariyar kad'ai ya isa yasan mutum cikin firgici da tsananin tashin hankali da tsoro .. ...

Lokaci d'aya ihun ya d'auke difff kamar ma ba'ayi shiba....

Wata iskace ta taso kafin daga bisani ta lafa.......

Kutsa kaina nayi cikin gidan , na leka dan ganin ko suwaye a cikin gidan......

Wani d'aki ne dake tsakiyar gidan, kofar d'akin anyi mishi fenti jajawur ....

Ko da na kutsa kai na cikin d'akin ga mamaki na hango mutane a 'kalla zasu kai su shidda ...

Sanye suke da jajayen kaya doguwar rigace sai ratsin baki kad'an ta saman wuyan rigan....

Manya manyan mutane ne .....

Wata kauryace a gabansu cikeda da jini fam, bakinsu na fitar da wani hayaki , wasu irin maganganu sukeyi suna kirkiza kayikansu.....
Ta gefensu kuma kayikan mutane ne a gun ....

Babban cikinsu ne ya mike tsaye yana wani jijjika , yafara magana cikin harshen indiya , yanuna wanda yake kusa dashi ,cikin tsawa yace,"to mun dawo gareka , a wannan karon munaso kanemo mata ka aura domin kuwa a wannan karon da ita zamuyi aikin gaba............


Hmmmmm to fa!!!

*MUJE ZUWA*


*Zaku iya fara biyan kudinku dan na saku a paid group*

*Dan neman karin bayani zaku iya tuntubar ta wanan layin kamar haka 09066386347*

*DAN ALLAH KUYI SHARRING MUN PLEASE👏👏👏*

*I NEED MORE COMMENTS*


*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
*&*
*VOTE*

*STORY & WRITTEN BY MUM FU'AD*

*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

I think you'd like this story: "GUGUWAR ANNOBA" by ZaynerbmuhammadKabee on Wattpad https://www.wattpad.com/story/296429855?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=ZaynerbmuhammadKabee&wp_originator=5i30La2OXFVYeOaF0CVtsLwLiUAqaZ6WywxGHvXeBQ%2BNpMII4KOOm0m4PzNnvOskFyEgsvvhp2rRuiXbm%2BAvBMOLebVg1NSz2q94M1yyxDSmFu9GrJEDh7ro%2BV%2BDeKyV

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 3&4*

"Wata shu'umar dariya yasa yace," angama ,shugaba Naburtu ni kaina ina da bukatar aure , dan yanzu a'kalla nakai shekaru uku batare da nasake wani auren ba, yafad'a batareda wani annuri a fuskarshi ba......

'Dayan ne ya mi'ke yana karkad'a kaii ,yayi wani juyi , ya mi'ke hannunshi ya mi'ka sama, idonshi sunyi jajawur kamar garwashi.......

Wata karamar 'kauryace ta fad'o a hannunshi....

Wasu maganganu yafara yi irin nasu na matsafa yayi kafin daga bisani ya juya 'kwaryar batareda da tafad'i kasa.....

Sau'k'ko da 'kauryar 'kasa yayi....

Kafin daga bisani ya ajiye 'kauryar a kasa...

Hoton hamdiyya ne ya baiyyana a cikin kwaryar , tanata sakin murmishi .....

Cikin wata irin murya mai d'auke da amo da kururuwa yace," TANIMU GAMJI!!!!! Wanda aka kira da tanimu gamji ne ya d'ago rinanun idonshi ya sauke a cikin kwaryar ya karema kwaryar kallo...

Wata shu'umar dariya ya sa ya'kara d'ago rinanun idonshi yace," Angama na fahimta kuma na gane a ina take ? yaya sunanta? . .....

Wanda yake zaune ta gefenshi ne shima ya mi'ke ya runtse idonshi Kafin ya bude yace," kasar Nigeria ,garin jos ,rikkos Are'a yana fad'an haka yayi shuru batare da yakara cewa komai ba ya koma yazauna .....

Gaba d'ayan su suka bushe da wata matsananciyar dariya .....

Take wata 'katuwar kwarya ta sake baiyyana da taimakon sihirinsu ......

Babbansu ne yafara yin wasu irin maganganu da yaren indiya ....

Take daloli suka faa zuba cikin kwaryar ....

'Deban kud'ad'den sukayi gamida zubasu a cikin manyan mayan akwatinansu , sai da kowannensu ya cika akwatinshi fam da kud'i......

Bayan sun gama d'eban kud'ad'en suka 'kare bushewa da wata matsananciyar dariya gamida mikewa tsaye suka cigaba da tsafe_ tsafensu....

Bayan sungana 'yan tsafe_tsafensu gaba d'ayan su suka fita ,a d'akin sai babbansu Wanda yake zaune shi kad'ai....

Wani d'aki suka shiga suka canza kayan jikinsu zuwa manyan kaya kamar mutanen arziki....

Bayan sun sa kanyan sun fito , suka fara wasu irin maganganu ,gamida runtse idanunsu.....

Nan take ko wannensu yaganshi a gidanshi da suka kama na cikin kasar Indi'a.....


Hibba ce zaune da 'yanwanta suna kallo...

Kasancewar week end ne babu school......

Tsefe ma ilham kai hibba take , ita kuma Nihat na tsefema mufida bayan tagama nata........

'Karamar wayar da take kan TV Stand ce tafara ringing , da Sauri suka taso har suna rige_rige , suna fad'in laa baba ya kira waya, Allah yasa ba dawowa zaiyyi ba .......

Tunda hibba ta ji ringing d'in wayar gabanta ya fadi....

Mi'kamata wayar Ajmal yayi , jiki a sanyaye juwairriya ta 'karba ta kara a kunnenta tace,"sannu daddy ina wuni ?

Lafiya kalau hibba yaya kuke ?
Fatan duk kuna lafiya ?
Lafiya 'kalau tafad'a jiki a sanyaye ......

Kunada komai ko? kuma ba wata matsala?

Numfasawa hibba tayi tace,"ehh daddy muna da komai, okay to shikenan... ..

Amm inasa ran ma zandawo ko zuwa next week ......

Jin ya yace zai dawo yasa gaban hibba yayi mugun fad'uwa ....
muryar ta na rawa tace," to shikenan Allah ya kaimu , Allah ya dawo dakai lafiya , Ameen ya amsa, yace," ki gaida kowa da kowa , daga bisani ya kashe wayar......

Tagumi hibba tayi daga bisani ta ajiye wayar tace," Nihat, jawad ,mujahid,Ajmal,ilham, mufida, daddy yace wai yana gaisheku , kuma yace zai dawo wani satin ......

Kallonta sukeyi suka 'bata rai , anti hibba ki kirashi kawai kice mishi basai ya dawo ba Mufida ta fad'a...

Murmushi hibban tayi tace," Allah sarki mufida bazai yuyu ba , Allah dai yadawo dashi lafiya kawai......

Bayan sun gama tsifan , hibba tafara yima ilham Kitso , ba laifi tayi kokari sai dai baiyyi kyau sossai ba kasancewar koya tayi dan dole .....

Zuwa karfe shida ta gama musu , bayan tagama tafara 'ko'karin d'aura abincin dare .....

Zuwa karfe bakwai tagama kasancewar doya ta dafa musu

Please Login or Register in order to submit comment