Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan ya ce Wannan ku kaiwa Sarki." Sannan kuma ya
dauko wannan littafi na Halwanu ya sake mikawa mutanen nan ya ce Wannan kuma ku kula da shi sosai, idan kün je ku baiwa
dan uwana boka Sakaradisa wannan littafi."

Nan boka ya sallamesu cikin daren suka fice daga garin ba tare da kowa ya gansu ba.
Wannan abu duk ya faru ba tare da sanin Sarki -Afarahu ba.


A kwana a tashi har mutanen nan da boka Sakaradiyyuna ya aika suka isa garin Sarki Saifu'ar'adu. Da zuwansu suka wuce
zuwa fada suka iske Sarki na zaune ana fadanci.


Suka fadi suka
yi gaisuwa gaban Sarki, suka mika wannan takarda ga Sarki, suka kuma mika wannan littafin Halwanu ga boka Sakaradisa.


Nan da nan Sarki ya umarci magatakarda da ya karanta wannan
wasika.Cikin kankanin lokaci ya karanta abin da wannan takarda
ta kunsa, Sarki da wazirinsa Baharu da Boka Sakaradisa duk
suka ji irin abin da Sakaradiyyuna ya rubuta.


Ran Sarki ya baci
hankalinsa ya tashi, ya yi duba ya zuwa Sakaradisa ya ce.Ina dabara?"
Boka Sakaradisa ya ce Idan ba da gasake ka yi ba, to wannan tsinannen farin yaron sai ya karbe wanan mulkin naka
kuma ya mayar da mu bayi, kai hatta tauraruwa Zahlu ma sai va hana mu bautarta."


Bayan ya gama wannan magana sai ya mikawa Sarki littafin halwanu ya ce, Riki wannan, dan 'uwana ne ya aiko min da shi

Wanpan shine littafin tarihin Nil Sarki ya karba ya ajiye.
Can shi kuma Waziri Baharu da yake musulmi ne sai ya ce
Wai sakaradisa me ya sa kuka damu da wannan farin yaro bayan a wannan lamari bashi da laifi ai in ma kamawa ne Sarki Afarahu da Sa'adunnizzanji su Sarki zai hukunta a bisa laifinsu kashe Manadihulbigali da suka yi.


Amma shi wannan yaro Kuma da kuke cewa shi ne wanda zai karbe mulkin Sarki, ya aka yi kuka sani, kun san gaibu ne? ai babu wanda yasan gaibu in ban da tauraruwa Zahlu kamar yadda muka sani


Sarki ya ce Haka ne Wazirk, wannan magana taka haka take, babu wanda ya san gaibu in bán da Zahalu, to yanzu Weziri ina dabara bamu shawara.


Ana cikin haka sai wani daga cikin dogarawan Sarki ya
shigo ya gayawá Sarki cewa ga wani tsoho ya zo yana so ya ga
Sarki.

Sarki ya yi umarni da a shigo da shi, nan- da nan aka shigo da da tsohon nan gaban Sarki.

ya fadi ya yi gaisuwa. Sarki ya
tambaye shi, "Me ya kawo ka."
Tsoho cikin raurawar murya ya ce, Na zo ne na kawo karar shugabanmu gareka, domin ta raba mu da birninmu har ta
kashe wasu da dama daga cikinmu, kuma ta kama ya'yayenmu
da matayenmu suna yi mata bauta,
Ko da Sarki ya ji wannan magana sai ya ce,


Kai mutumin wane gari ne kuma waye wannan shugaba naku, wanda har ya yi
muku wannan ta'adda?"


Tsoho ya amsa ya ce, "Ni mutumin birnin Yemen ne, ni ada na kasance ni ne shamakin Sarki Ziyyazanun kafin ya rasu,
kuma mu duk mutanen kasarmu, mun kasance masu biyayya ga
Sarkinmu.


to yana ciwon ajali kafin mutuwarsa ya yi mana Wasici da cewa, matarsa tana da ciki, idan ya mutu ta cigaba da sarauta bisa gadonsa na mulki har ta haihu. Idan ta haihu dan ya girma ta sauka ta ba shi mulkinsa. Haka muka bi wannan umarni
nasa ba saba ba,


bayan mutuwarsa muka dora wannan mata
mai suna Kamriyya bisa gadon sarauta.

to tun wannan lokaci sai ta fara korar mutanenmu tana jawo
wadansu mutane daban tana ba su mukamai a majalisar kasarmu


Ana haka rannan sai ta haihu da namiji, bayan yaro ya kwana
bakwai ta fito mana da shi fada muka ganshi.


Amma tun daga
wannan rana har yau shi shekara ashirih kénan ba mu kuma ganin yaron ba.

Shi ne na zo na nemi taimako a gareka domin kuwa na ga kai Sarki ne mai girman lamari."


Ko da boka Sakaradisa ya ji wannan labari sai ya dubi Sarki ya ce, Ai wannen Sarauniya da ake magana ba wata ba ce illa baiwar nan taka Kamriyya, wadda ka ba ta guba ka aike wa da Sarki Ziyyazanun domin ta ba shi ya sha, shi ne ba ta aikata hakan ba ya rike ta a zaman mata, kuma ga shi har ta shekara
ashirin tana mulki amma ba ta aiko maka da haraji wai ita ma
shugaba ce tana gasa da kai ai lallai ne ka yaketa."


Da jin wannan magana Sarki ya fusata ya ce, Wato wannan tsinanniyyar dai na tura ta ta kashe Sarki Ziyyazanun shi
ne ba ta aikata hakan ba, kuma har ta kira kanta shugaba tana jayayya da ni, to na rantse da Zahlu sai na yake ta na rusa
birninta."


Waziri Bahru ya ce da Sarki, Ai ba yakar ta za ka yi ba,
domin kuwa ita ma yanzu ta tara sadaukai masu yawa
karkashinta. Ka ga yanzu idan ka tura a yake ta kuma aka je ba
ai nasara ba mutuncinka zai zube a idon sauran sarakunan duniya, a kuma rika cewa ka yaki mace kuyangarka ta gagareka.


Abin da za a yi shi ne, tun da ita Kamriyya ta ki aiko maka
da haraji har tsawon wasu shekaru, to ta saba maka, kuma ga
Sarki Afarahu ya kashe maka dan aike, shi ma ya aikata laifi a
gareka.


To yanzu ka hada su yaki da junansu, duk wanda ya
karya wani mu kuma sai mu rufar masa mu karasa shi. Ka ga
shike nan mun huta."



Boka Sakaradisa ya yi dariya ya ce, Madalla da wannan
shawara taka, ai kawai ran Sarki ya dade haka za a yi, shi ke nan
Wannan shawara ta yi sarki iya yi na'am da shawarar Waziri, nan da nan ya sa aka
rubuta takarda zuwa ga Sarki Afarahu ya shaida masa da cewa,
Mun samu labari ka kashe dan aikena Manadihu saboda haka ka aikata laifi a gareni. Amma girmanka wajenmu na gafarceka bisa ga abin da ka aikata.


Amma ina so yanzu kaje ka yaki kamriyya sárauniyar yemen, shi ne diyyar da za ka biyani a maimakon Manadihu."


Bayan da aka gama rubuta wanan takardar aka tashi wani sadauki wanda ake kira da suna Sijiinfili aka hada shi da sadaukai dari uku da dukiya dukiya aka umarce su da su kai wa Sarki
Afarhu wanan takarda da kuma wannan dukiya.


Nan da nan
suka daura surada suka hau suka tafi.

Can kuma Sarki Afarahu hankalinsa ya tashi saboda ya san
idan Sarki Saifu'ar'adu ya samu labarin an kashe Manadihulbigali
a kasarsa kuma babu zancen auren Shamatu da Sarkin ya nena
ko ya san ba makawa sai ya aiko an yaki kasarsa, saboda haka ya
dimauce ya rasa yanda Zai yi.


Bayan wasu yan kwanaki Sijijimfili da sauran jama'arsa suka iso garin Sarki Afarahu. Ko da Sarki Afarahu ya samu
labarin ai ga baraden babban Sarki sun iso kasarsa an aiko su, sai
hankalinsa ya tashi, ya tara yan majalisarsa, cikin su har da
Malulkussaifi da Sa'adunizZanji. Sarki ya ce, To kun ga babban
Sarki can ya aiko Sijijinfiili ya yake mu sakamakon kashe Manadihul bigali."


Malukussaifi ya dubi Sarki Afarahu ya ce,Kwantar da
hankalinka, mu Za mu fita mu tare shi idan da nufi yake ya zo mana, za mu yake shi mu kashe shi sannan shi ma babban Sarkin
da ya aiko shi mu je mu yake shi."


Nan da nan sadaukai sukai ta
daura surada suka hau dawaki, Malukussaifi ya shige gaba shi da
Sa'adunizzanji sauran jarumai suka bi su suka fita taryar Sijijiimfili
Ko da Sijjimfili ya hango irim shirin da su Malukussaifi
Suka yi sai ya san lallai sun zata yaki ne ya kawo shi. Sai ya turo


daya daga cikin mutenensa ya zo ya
shaida musu cewa ai ba da yaki suka zo ba kawai an aiko su ne.


Da suka ji wannan bayani sai suka ba Sijjinfili da jama'arsa damar su karaso inda suke da suka zo sai suka hadu suka
dunguma cikin birni, aka sauki Sijijinfili da jama'arsa akai tayi
musu hidima har dare ya yi duk aka kwanta barci.


Bayan da gari ya waye Sarki Afarahu ya fito fada jama'a
duk sun taru ana Jira a ji sakon da Sijijimfili ya ke tafe da shi.


can an nutsu sai Sarki ya ce da shi, Shin menene sakon dake
tafe da kai?"
Sijijimfii ya dauko takardar da Sarki Saifu'ar'adu ya ba shi
ya mikawa" Sarki Afarahu, shi kuma ya karba ya mikawa
magatakardansa domin ya karanta.


Magatakarda ya karanta kowa
ya ji abin da babban Sarki ya rubuto
Ko da Malukussaifi ya ji haka sai ya ce, To ai wannan ma zancen baza ne ya ya wata can ta yi masa laifi shi bai yake ta ba
sannan kuma ya aiko mana wai mu je mu yake ta. a nan
yana nufi kai Sarki a Karkashinsa kake kenan,

to ba za mu yi abin da ya neba ba shi ya zo ya yake ta in kuma ya ji haushi mu
ya zo ya yake mu
Sarki Afarahu ya yi shiru yana tunanin cewa lallai
Malukussaifi da Sa'adunizzanji lallai jarunmai ne na gaske, amma
kuma duk da haka sai ya tuna ai babban sarki Saifa ar'adu yana
da yawan sadaukai jarumai fiye da kima, kuma ya san lallai idan
ya yi fiushi da su duk zai halaka su.


Sai ya dubi Malukussaifi ya
ce, Ya dana, ai ya zama dole mu bi umarnin babban sarki, mu Je mu yaki Kamriyya, idan ku ba za ku ba to ni zan shirya in tafi
da mutanena na yake ta.


Da Malukussaifi ya ji wanan nmagana ta Sarki Afarahu, sai ya
yarda da hakan saboda kasancewarsa mai biyayya a wurin Sarki
domin daukarsa da ya yi Uba a wajensa.


Ya ce,To shike nan mun yarda da wannan magana , za mi bi ka mu je mu yaki
wannan sarauniya ta kasar yemen.

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 4.
.
Bayan wasu yan kwanaki kadan sukai shirin yaki, Sarki
Afarahu da Malukussaifi da Sa'adunizzanji da Sijijimfili da sauran Sadaukai suka fita suka kama hanyar zuwa garin babban
Sarki Saifu'ar'adu, domin su yi gaisuwa da nuna amsa umarni,
sannan su wuce zuwa kasar Yemen su yaki Sarauniya Kamriyya.


Da zuwansu garin babban sarki, sai ya turo aka tarye su aka
kai su fada kowa ya yi gaisuwa gabansa suka zauna ban da
Sa'adunizzanji, shi sai ya yi tsaye yana muzurai ko gaida Sarki
bai yi ba.


Ganin haka sai babban sarki ya dubi Sarki Afarahu ya
ce, Shi kuma wannan waye wanda yake tsaye?" Sarki Afarahu
ya ce, Wannan shi ne Sa'adunizzanji." Babban Sarki ya ce, To
shin shi ya fiku ne duk kun yi gaisuwa amma shi yana tsaye
Ko da Sa'adunizzanji ya ji wannan magana sai ya fusata ya
ce da babban Sarki, To don me zan gaishe ka, kana zaton ni
talakanka ne, to baka isa na gaishe ka ba."


Nan da nan sai
jayayya ta balle tsakanin babban Sarki da Sa'adunizzanji, su kai ta yi Can sai boka Sakaradisa ya matsa kusa da Sarki Saifu'aradu ya rada masa ya ce, Ran Sarki ya dade, mai ya kai ka jayayya
da wannan bakin bawan.


Ai in ka biye masa yanzu yaki ya tashi
a nan, ka rabu da shi kawai ya fi"
Sarki ya yarda da wannan shawarar ta boka ya daina jayayya da
Sa'aduniZZanji, ganin haka shi kuma Malukussaifi ya umarci Sa'aduni
da ya zauna, sannan ya zauna.


Akai ta fitowa da abinci iri-iri ana
baiwa jama'a, suka ci suka sha, kai haka dai akai ta yin hidima har
kwana biyu
Bayan wadannan kwanaki sai babban Sarki ya sallame su suka fito
domin su tafi su yaki sarauniya Kamriyya.


A wannan lokacin bayan sun fito sai Malukussaifi ya umarci Sarki Afarahu da ya koma gida shi da
Sa'adunizanji da sauran sadaukai za su tafi wurin wannan yakin.

Sarki Afarahu da rabin mutanen da suka fito suka koma gida, Malukussaifi
da Sa'adunizzanji da sauran sadaukai suka kama hanyar su ta zuwa
Yemen domkn su yaki Sarauniya Kamriyya.


A lokacin da suka je kasar babban Sarki Saifu'ar'adu kafin su fito, bash san ba sai babban Sarkin ya rubuta takarda zuwa ga Sarauniya Kamriyya ya ce,"Zuwa ga sarauniya Kamriyya, na rubuto
miki wanan takarda domin ina so ki biya ni haraji har na iya tsawon
shekarun da kika yi kina mulki.


ldan kuma ba haka Ba rundunar
mayakana suna nan tafe Zuwa gareki Da ya gama rubuta wannan
takardar sai ya aika wa wani dogari ya umarce shi da ya yi maza ya tafi
kasar Yemen ya kai wa Sarauniya Kamriyya.


Bayan yan kwanaki dogarin nan ya isa birnin Yemen da zuwansa
ya wuce zuwa fada a kai masa iso ya shiga ya yi gaisuwa ya fadi sakon Sarki.


Da Kamriya ta karanta wannan takarda sai ta ce da dogarin nan, in ce ko dai shi Sarki Saifi'ar'adu ba shi da hankali ne? Yanzu kamar ni ya ce in biya shi haraji, to ka koma ka gaya masa
ba zan biya shi ba, kuma idan yaki ne zamansa nake.


Kwana biyu da yin wanannan sai Kamriyya ta samu labarin ai ga wata rundunar mayaka nan ta nufo biminta kuma ga yadda labarin ya zo mata ta firgita da jin yadda aka gaya mata yawan su da kuma irin
shirinsu.

Wato wannan runduna ba wasu bane illa Malukussaifi da
Sa'adunizanji da Sijijimfilk da sauran jama'ar da suke tafe da su
kafin magaruba Malukussaifi da jama'arsa suka karato birnin yemen suka hangi katangar birnin an gina ta da farin dutse da manya manyan kofofi na jan karfe.

A nan sai ya umarcesu da su sauka
a nan su kwana, gari na wayewa su auka cikin garin da yaki, nan duk
aka sauka aka kafa rumfuna na tanti, duk suka saki dawakinsu domin
Su yi kiwo su kunma kowa ya shiga rumfarsa ya kwanta aka bar wasu suna
gadi
Can bayan an natsu cikin dare sai Kamriyya ta hau doki ta sulalo
ta fita daga cikin birni ta nufo inda su Malukussaifi suke.


Da Zuwa da sai ma su gadun nan suka tare ta suka tambaye ta ina za ta,
ta ce da su ai ite lallai shugabans take so ta gani nan da nan aka
je aka gaya wa Malukussaih cewar ga wani mutum ya fito daga
cikin birnin nan ya ce lallai kai yake so ya gani ya ce ku je ku ce
da shi ya koma gebe ya dawo. suka komo suka gayawa kamriyya amma sai ta ki ta dage, ta ce ta lallai sai ta gan shi, suka koma suká sake
gaya wa Malukussaifi, sai ya ce a shigo da shi, aka shigo da
Kamriyya duk
suka fita suka barsu su biyu a cikin tanti.


Malukussaifi ya ce, Me ke tafe da kai?" Kamriyya ta bude
fuskarta ta ce, "ba namiji ba ne, ni mace ce kuma ni ce Kamriyya
Sarauniyar wannan birnin da kuka kawo wa yaki. Abin da ya kawo ni shi
ne, na ga rundunarka tana da karfi kuma ni ma tawa rundunar tana da
karfi, sai na ga in mu kai yaki za a zubar da jini sosai, shi ne na
zo yanzu mu yi kokawa ni da kai duk wanda ya yi nasara a kan dayan to
shike nan ya ci shi da yaki, ba sai an gwabza a filin daga ba.


Da ya ji wannan magana tata sai ya ki ya ce sam shi ba zai yi
kokawa da ita ba, tana mace shi yana namiji. Haka dai sukai ta jayayya
har ta shawo kansa ya yarda za su yi kokawar.
Kamriyya ta cire duk kayan dake jikinta ta tsaya daga ita sai
wata riga doguwa mai shara-shara, wadda duk ana ganin halittar
jikinta.


Ita ta yi haka ne domin ta yaudari Malukussaifi ya kamu da
sha'awarta ta samu ta yi galaba da shi. Shi kuma da ya ga haka sai ya
ce bai yarda ba, ba zai yi kokawar a haka ba, sai ta sa kayanta. Ta rika kawo masa wabta yana gocewa har ta yaga masa riga ganin haka shi
kuma sai ya fusata ya cire rigarsa, yana Cirewa sai Kamriyya ta ga
sarkar nan da ubansa ya ba ta kafin ya mutu ya ce in ta haihu ta
rataya wa dan a wuyansa.


Tana ganin haka, sai jikinta ya yi sanyi ta tambaye shi inda ya
samu wannan sarkar ya gaya mata, ya ce shi dai tashi ya yi ya ganta
a wuyansa tun yana karanmi. Nan da nan ta ce, Wallahi kai dana ne,
duk inda a kai kai dana ne, domin kuwa wannan sarkar asalinta ta
ubanka ce Sarki ziyazzanun.


Kafin mutuwarsa ya bani ita ya ce idan
na haihu na rataya wa dan da na haifa a wuyansa, shi ne da na haife
ka na rataya maka i ta, kuma tana wuyanka na je far da kai a daji. Ni ce uwarka."


Malukussaif ya ce ai shi bai yarda ba, ya za ai in dai uwar tasa ce ita ta yada shi, Sukai ta jayayya can sai ya ce, To na ji.

yanzu meye kuma shaidar ki bayan wannan Ta ce.akwai shaida, zan koma cikin birni zan zo da irin yaran ubanka domin su yi maka
shaida."
Nan da nan Kamriyya ta koma cikin birni ta kirawo wasu tsofaffi
su hudu wadanda suka rage daga cikin yaran Sarki Ziyyazanun, ta taho
da su gurin Malukussaif ta ce da su, Ku raba mana wannan gardarmar,
ni na ce dana ne, shi kuma ya ce ba shi bane."Tsofaffin nan suka
dube shi suka ga yar alamar nan dake kundukukinsa (kumatunsa kenan),
sai suka ce, lallai babu shakkar cewa danta ne,"Shugabanmu ne kai,
mun rasa ka yau tsawon shekara ashirin da daya."
Nan dai har sai da Malukussaifi ya gasgata su ya san lalai
Kamriyya uwarsa ce ba aljana ba ce uwarsa.


Sai ya ce da ita, Ke
kuwa me ya sa kika yadda ni kina mahaifiyata?" Kamiyya ta fashe da
kuka, ta zare takobinta ta mika masa ta ce, dana, karbi takobin nan
ka yanka ni, domin ka rama abin da na yi maka, domin ni yanzu burina
na duniya ya cika tun da na sake saka ka a idona. Yimaza ka yanka ni
ka shiga birninka, kaci gaba da mulki.


"Malukussaifi ya rungume ta
yana hawaye yana cewa, Ki yi
shiru ba komai."


Bayan haka sai Kamriyya ta ce, Ai sai ka kwana a nan, gobe da
safe za mu fito ni da jama'ar gari baki daya.


Mu zo mu tarye ka mu
shigar da kai garinka, in baka mulkinka." Sukai sallama Kamriyya da
tsofaffin nan suka koma cikin birni.


Da komawarsu ta bai wa tsofaffin
nan abinci da guba suka ci duk suka mutu, babu wanda ya san abin da
ya faru, ta zauna tana bakin ciki tana cewa a zuciyarta, "Ka ga
shegen yaron nan da na jefar da shi don ya mutu saboda kada ya karbe
mulki na, ashe bai mutu ba ya
dawo.


Haka dai ta zauna tana ta tunanin makircin da za ta sake kullawa
danta Malukussaifi. Can sai dabara ta zo mata, ta tashi ta hau doki
cikin wannan daren ta kuma komawa bayan gari wurin Malukussaifi.

Da Zuwanta a kai mata iso ta shiga ta ce, Ya dana na dawo.
Abin da ya dawo da ni shi ne, na z0 ne domin na faiyace maka dukkan yanda lamarin ya faru a baya.

Ni na kasance na kan sami tabin hankali wani lokacin,
Wani lokacin ka ganni da hankali. Lokacin da na yadda kai ba nida
hankali, a wannan lokacin ban san abin da nake ciki ba. Na ki gaya
maka ne dazu saboda ganin wadannan mutane da na zo da su.
Abu na biyu kuma shi ne, ubanka ya bar maka dukiya mai yawan
gaske, saboda gudun kada wasu daga cikin Sarakunan duniya su kwace
maka ita sai na debi mutane muka dauki dukiyar muka tafi can dan
daji muka binine ta. Bayan mun binne wannan dukiya, mulanen da na je da su
sai na kashe su, yanzu duk duniyar nan babu wanda ya san inda wannan
dukiya take sai ni. Saboda haka yanzu tashi mu tafi in nuna maka
dukiyarka."


Bai yi musu ba ya tashi ya bita suka hau dawaki suka kama hanya
sukai ta tafiya cikin daren nan, har gari ya waye rana ta fito suna ta
tafiya subiyu cikin daji har rana ta tafi. Kai haka dai sukai ta
kutsa kai cikin daji su biyu har kwana uku.


A cikin wannan hali duk
lokacin da dare ya yi sai ta kwanta ta yi barci shi kuma ya tsaya yana
gadinta har sai ta farka, sannan su ci gaba da tafiya. To a wannan
rana ta uku sai barci ya kama Malukussaifi, mahaifiyarsa ta ce, To
yau kai ma ka yi barci ni kuma na yi gadinka."



Malukussaifi ya kwanta ya tada kai da cinyar mahaifiyarsa ya fara
barci. Cikin kankanin lokaci sai ya fara minshari, barcinsa ya yi
nisa. Ko da Kamriyya ta fahimci ya yi nisa cikin barci, sai ta zame
jikinta a hankali ta tashi ta dauko wata Gariyo (wuka) mai guba ta
dubi kan Malukussaifi ta kafta masa sara jini ya yi tsattuwa sama, ta kuma saransa a wuyansa, ta sake saransa a kirji, sannan ta yanke shi a ciki.


Ta juya ta hau dokinta ta tafi ta barshi cikin jini
kwance, tana zaton ta kashe shi. Haka ya kasance cikin wannan hali har asuba ta yi, sanyin asuba
ya buge shi ya farka daga suman da ya yi.


Malukussaifi ya ga duk
jikinsa jini ya yunkura zai tashi amma sai ya kasa saboda gubar dake
jikin gariyon nan ya shige Shi nan sai ya yi addu'a ya roki
Ubangiji da ya kawo sababin da zai kubuta daga wannan hali da yake
ciki. Yana rufe bakinsa sai ya ga wasu tsuntsaye guda biyu sun zo sun sauka akan wata bishiya da take kusa da shi.

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 5.
.
Daya da ga tsuntsayen sai ya dubi dayan ya ce, "Shaihu Jayyada,
ka ga fa wannan uwarsa ce fa mahaifiya ta aikata masa wannan aiki,
Saboda kwadayin mulki kawai " Sai daya tsuntsun ya amsa ya ce,
Haka ne Shaihu Abdussalam, amma ka ga da zai ci ganyen wannan
bishiyar ya shafa a jikinsa da sai ya warke sarai, kamar ma bai yi
Wani ciwo ba."


Bayan sun gama zantukansu sai tsuntsayen suka tashi Suka tafi
Shi kuma Malukussaifi yana daga kwance ya ji duk maganganun
tsuntsayen nan sai ya kuma yin addu'a ya roki Ubangiji ya Kawo sababin yadda zai iya samun ganyen wannan bishiyar.


Nan da nan sai iska ta taso ta girgiza bishiyar ganyenta ya zubo masa a jiki, ya
Samu ya kama guda daya da lebensa ya auna ya hadiye, da yin haka sai
ya fara jin karfin jikinsa. ya mika hannu ya sake dauko ganyen ya rinka gogawa a jikinsa. Nan da nan duk jikinsa ya warke, ya mike ras,
kai ba ka ce ma wani abu ya taba Samunsa ba.


Ya tashi ya yi godiya ga
Madaukakin Sarki, ya hangi dokinsa yana kiwo. ya bi shi ya kama ya
hau ya kama hanya ya fara tafiya, ba tare da ya san inda ya nufa ba.


idan ya ji yunwa sai ya ci daga ya yan itatuwa. yana shan ruwa daga
kwazazzabai
Bayan Malukussaifi ya samu kwana arba in yana tafiya cikin daji.


Sai ya hango wasu manyan duwatsu guda biyu masu tsayi, tsakanin
duwatsun akwai kogi mai gudu ya raba su. Daya dutsen wanda daga
bangaren hagu wato bangaren da Malukussaifi yake ja ne, dayan kuma
na dama da shi fari ne.



Da ya karaso gindin wannan jan dutsen Sai ya ga wani kogo a
jikinsa, ya ji ana magana daga cikin kogon ana cewa, Barka da zuwa
Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun, dan Tabi'ul Yamani, dan Usudul
baida'a, dan Samu dan Nuhu Alaihissalatu wassalam. Sai ya ga wani
farin mutum dogo ya fito daga wannan kogon yana yi masa barka da zuwa
cike da farin ciki
Sai ya tambayi mutumin ya ce, Kai kuwa ya ya a kai har ka san
Sunana, bayan kuma kai ba ka taba gani na ba sai yau?" Sai mutumin ya ce, Ai yau shekara ta ashirin ina zaune a nan ina jiran zuwanka, domin na nusassheka aijiyar da kakanka SAMU ya yi maka, kuma ni ma dai na gaji wannan gadin a wajen babana, shi ma wajen kakana ya gada, Shi kuma a wajen nasa uban, shi kuma a wurin kakansa.


mutumin nan ya kama hannun Malukussaifi suka shiga cikin kogon
nan. da Shigar su sai wannan mutum ya yi tafi sai ga kujeru guda oiyu
an kawo tare da abinci. Suka zauna sai mutumin ya ce da Malukussaifi
ya ci wannan abinci. Shi kuwa sai ya ce, Ya ya za'ai in ci abincin alhalin ban ga wanda ya kawo shi ba, ai ba zai yiwu ba. Shin wai kai yaya
Sunanka ne kuma mene ne addininka?


Mutumin nan ya amsa masa da
cewa, ni sunana Ihimimiddalibi, kuma ni Malami ne. ina bin Addinin
Annabi Ibrahim (AS). Saboda haka ka gasgata ni ba zan cuce ka Da.


Da ya ji wannan bayani na Malam Ihimimuddalib, sai ya saki jikinsa
Suka kama cin abinci
Bayan Sun ganma cin abincin nan. sai Ihimimuddalib ya ce da Malukussaifi. To gobe da asuba za mu fita mu hau sanman dutsen nan zan jarraba ka domin na tabbatar da cewa kai ne mai wannan ajiya ko
kuwa ba kai bane."


Nan suka kama zikirillahi har dare

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment