Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce da waziri,to na ji ba zan kashe shi ba, to ya ya za mu yi da shi"

ya matsa kusa ya ce "ai kawai yanzu ka sa a kai shi kurkuku a kulle shi a rika horon sa har zuciyarsa ta mutu, ya zamo mai biyayya gareka mai taimakonka wurin yaki." Haka kuwa Sarki ya yarda da
wannan shawara ta Waziri, ya sa aka kai Sadunizzanji kurkuku aka
kulle shi.


Can kuma aljani Iluru ya dauko Malukussaifi suna tafiya a kan
hanyar su ta zuwa Yemen inda ya bar rundunarsa da Sa'adunizzanji sai
hanya ta biyo da su ta gefen birnin Sarki Afarahu. Sai suka rika jiyo
kade -kade da bushe-bushe da hayaniyar jama'a. A nan sai MalukuISsaifi
ya umarci lluru da ya ajiye shi a nan ya je ya gano abin da ke laruwa
cikin wannan gari.


lluru ya ajiye Malukussaifi kan wani dogon dutse, shi kuma ya
tafi nemo labari, jim ka dan sai ga Iluru ya dawo ya ce, Ai Sarkin
wannan birni ne yake bikin wata yarsa wai ita Shamatu zai aurar da
ita ga wani babban sarki wai shi Saifu'ar'adu, wannan shi ne dalilin
wannan hayaniya da kake ji.

Ko da Maukussaifi ya ji wannan magana
sai hankalinsa ya tashi, idanuwansa suka kada sukai ja-jawur kamar
garwashi. Shi kuma lluru da ya ga haka sai ya tambaye shi, ya ceYa
shugabana me ya faru ne na ga ranka ya baci hake"
Malukussaifi ya amsa masa, Ai ita wannan yarinyar da ake biki
ita ce wadda nake ta shan wahala wajen neman aurenta. An nemi
sadakinta na kawo, an kurma nemi dukiyar auren ta ita ma na kawo, amma
sabode cin amana shi ne yanzu ake aurar da ita ga wani.

iluru va
ce,Ya shugabana, kai min izini yanzu na je na dauko yarinyar na rusa garin gabaki daya." Malukussaifi ya ce, Aa, yanzu abin da nake
so shi ne, ka dauke ni ka kai ni dakın da Shamatu take na gani. Idan
da yardarta ake wannan biki zan ko kasheta sakamakon yaudarata da
ta yi, in kuma ba da yardarta ake yin wannan biki ba. to shike nan ka
dauko mu ni da ita bakidaya."


Iluru ya dauke shi ya kai shi dakin da Shamatu take ya ajiye shi,
Mahalussaifi ya shiga ya tarar da ita tana zaune tana kuka, har
gaban rigarta ya jike da hawaye. koda ta gan shi sai tai zumbur ta
mike tsaye ta rungume shi, tana shissshikar kuka da ajiyar zuciya. ya dube

Ya ya abar begen zuciyata, ya ya a kai har ki ka manta
alkawarin zuciyoyinmu, kika yarda za ki auri wani ba ni ba.

Shamatu ta dube shi ta ce, Ya abin kaunata, ban yi zaton za ka
zarge ni cikin wannan lamari ba, amma zauna in ba ka labarin duk abin
da ya faru. Suka zauna.
Shamatu ta dube shi fuskarta cike da hawaye ta ce, Bayar
tafiyarku yaki kasar Yemen, yayin da Ubana ya yi jiranku ba ku dawo
ba, wata rana sai Sarki Saifu'ar'adu ya aikowa mahaifina cewa, wai
Sarauniyar wannan gari ta kashe ka, kuma ta kama Sa'adunizzanji.


Saboda haka dama wannan yaki fansar laifin kashe Manadihu ne, tun da
kuma ba su yi nasara ba, to yanzu abin da zai Zama fansa shi ne aura masa ni.
To saboda tsoro bisa ga sharrin babban Sarki Saifuar'adau shine
ubana ya amsa wannan lamari, ba don son ransa ba. Ka ji yadda
wannan lamari ya kasance." Tana rufe baki sai ga ubanta Sarki
Afarahu ya shigo dakin.


Ko da ya ga Malukussaifi sai ya ce, Ya kai dana, an ce ka
mutu, kuma yanzu na ganka a nan.

Malukussaifi ya yi wuf ya zare
takobi ya yi kansa, Sarki Afarahu ya juya ya fita a guje ya nufi
dakin da babban Sarki Saifa'ar'adu yake.


Da shigarsa ya ce, Ai ga Maukussaifi can a dakin da Shamatu
take." Yayin da babban Sarki ya ji wannan labari, sai yai wa
mutanensa tsawa ya ce, Maza ku kamo shi ku zo min da shi." Nan da
nan suka gewaye dakin.
A wannan lokacin sai Iluru ya zo ya yi tsawa, sama ta yi dubu
duwatsu suka rika gangarowa da tartsatsin wuta. Iluru ya dauke
Malukussaifi da Shamatu ya fice da su daga wannan birni. Da mutanen
Sarki suka ji rugugi da hatsaniya ta lafa sai suka shiga ciki suka
iske babu kowa a ciki sai suka koma suka gayawa babban Sarki, sarki ya dubi bokayen nan nasa guda biyu Sakaradisa da
Sakaradiyyuna ya ce, "Kun ga kamriyya ta ce mana ta kashe wannan tsinannen, yanzu kuma ga shi ya zo, ga abin da ya aikata mana." Sai bokayen suka ce da Sarki Ai wannan duk aikin aljanu ne domin mun duba mun gani yanzu aljanune suka taimake shi ya yake mu ya dauke
amaryarka."


Da Sarki ya ji haka, sai ya umarci jama'ar da ya taho da su wajen
wannan biki da su, su daura surada su hau su koma gida. Nan da na
Sarki Saifuar'adu da-jama'arsa Sukai sallama da Sarki Afarahu suka
kama hanyar komawa birninsu, suna masu bakin ciki.

Can shi kuma iluru da ya dauko Malukussaifi da Shamatu sai ya kai su kan wani dogon
dutse dake kusa da garin Sarki Saifuar'adu, ya kafa musu rumfa suka
zauna
Bayan da Sarki Saifu'aradu ya koma gida ya tara bokayen nan nasa
ya tambaye su da su ba shi shawara a kan yadda zai bullowa
Malukussaifi.


Sai bokayen suka ce da shi,. "Ai tun da aljani ne ke
taimakonsa bamu da yadda za mu yi da shi, sai dai yanzu abin da za kai
shi ne. ka rubuta masa takarda ka aika masa ka ce da shi yaya zai rika
yakar mu da aljanu bayan yana jin kansa shi namaji ne. kuma sadauki
Yaya zai rika abu irin na matsorata mata, to ka ga idan ya ji haka mun
san zai yi girman kai ya bi ta magananmu, Ka ga da ya fito yakanmu ba
tare da taimakon aljanu a gare shi ba. sai mu samu damar kama shi."


Sarki Saifu'ar'adu ya yarda da wannan shawara ta su, ya ce da su,
To yanzu naji wannan shawara taku. ina so ku buga mini kasa ku gano mini inda yake.
nan da nan suka baje rairayi su ka zana alkaluma suka duba suka fitar da bayani.

jim kadan bayan sun gama nazari suka ce da Sarki," Ai
yanzu ma gashi can kan dutsen nan na gabas da garin nan. "Sarki ya
sa aka rubuta takarda kamar yadda bokayen nan suka fada masa, ya ba
Su ya ce su je wannan dutsen da Kansu su kai masa. Bokaye suka karbi
takarda suka tafi wajen Makukussaifi da zuwansu Iluru ya sanar da
Shi cewa ga su nan, Malikussaifi ya umarce shi da ya sauko da shi ya same su, yaji abun da ke tafe, iluru ya saukar da shi., da zuwansa gabansu suka gaishe shi suka mi ka masa takardar Sarki, ya
karba karanta ya ce da su " ku koma ku gayawa sarki na yarda zan fitona yake shi ni kadai a bisa sharadin zan yake ku daya bayan daya da haka duk zan iya karar daku gabadaya.

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 8.
Bokaye suka koma suka gaya wa Sarki wannan sharadi nasa, ya
kuma yarda. Aka tsayar da magana a kan gobe za a fito a buga a fagen
fama, tsakanin Malukussaifi da mayakan Sarki Saifuaradu, amma ta
hanyar fito na fito.


Gari na wayewa Sarki Saifu'ar'adu da rundunar
sadaukansa da wazirinsa da bokayen nan guda biyu suka fito filin
daga. Can kuma sai ga Malukussaifi Iluru ya kawo shi ya ajiye shi a
gefe guda.Sai ya dubi sadaukansa ya ce, Cikinku waye zai fita ya
yaki wannan yaro, ya kashe shi, ni ko in ba shi dinare dubu da tufafi
na alfarma?"


Duk gabadaya sai suka rika jayayya wannan yana ni zan
fita wannan yana ni ne. Da sarki ya ga haka sai ya ce a yi kuri'a
wanda duk ta fada kansa shi zai fita, a kai kuri'a ta kuma fada kan
wani sadauki mai suna Samsami. Samsami ya fito ya tunkaro
Malukussaifi, da zuwansa ba wata magana sai ya kai masa suka da
mashi.


Malukussaii ya goce ya yi wuf ya buga wa Samsami kulki a ka
ya fadi matacce. Wani ya kuma fitowa, nan da nan Malukussaifi ya
kashe shi, kai a haka dai sai da ya kashe mutane bakwai daya bayan
daya.


To da Sarki ya ga haka fa sai ya yi wa sadaukan tsawa ya ce
mutum goma su fita gabadaya, su ka fita, cikin kankanin lokaci
Malukussaifi ya halaka mutane goman nan. Ganin haka sai Sarki ya
umarci mutum ashirin da su fito, su ma nan da nan Malukussaifi ya
shayar da su gidauniyar mutuwa. Kai a wannan rana dai sai da ya kashe
wa Sarki sadaukai guda dari uku da sittin.


Bayan da rana ta fadi sai Sarki ya ce a dakata haka sai gobe a cigaba. Iluru ya dauki
Malukussaifi ya-mayar da shi kan dutsen nan ya iske Shamatu tana
zaune tana jiransa. Sarki da jama'ar sa suka koma cikin birni.
bayan da suka koma Sarki ya -sa aka kirawo masa bokayen nan da
Waziri, suka zauna ya ce da su, Kun ga dai yau wannan tsinannen va
yi mana barna, ya kashe mana mutane da dama. Kuma na ga alanmun idan
aka ci gaba da haka zai karar da mutanenmu, shi ne na kirawo ku do min
ku ba ni shawarar yadda za mu bullo masa."


Waziri Baharu ya ce, Ai ran Sarki ya dade, ka sani fa yanzu wannan yaro ya girma kuma duk naniyar nan na san babu sadauki
kamarsa. Saboda haka kama shi ko Cinsa da yaki gurin 'yan tsirarun, mutane zai yi wuya, ai yanzu mutum daya ne kawak wanda zai iya kama
malukussaifi shi duk fadin duniyar nan, domin kuwa shi ne sadauki kamarsa.

Koda Sarki ya ji wannan magana ta Waziri sai ya tambaye shi,
Waye wannan kuwa, wanda zai iya kama mana shi, kuma a ina yake?
Waziri ya ce, Ai ba wani bane illa Sa'adunizanji. Domin kuwa shi
ne kadai yanzu nake ganin zai iya kama shi.


Sarki ya yi shiru yana tunanin lallai Sa'aduizzanji zai iya kama
Malukussaifi, sai kuma ya tuna to ai kuma shi bawansa ne. Sai ya ce, wannan magana taka Waziri haka take, to amma kuma fa ka tuna shi
Sa'adunizzanji bawan Malukussaifi ne, kana ganin idan har muka sake
shi muka tura shi ba zai iske shi su hada kaisu yake mu ba?


Waziri ya ce aini ka bani izni na je na sami Sa'adunizzanji a kurkikui na rarrashe shi zan shawo maka kansa ta hanyar kwadaitar
da shi dukiya da mulki, da Sarki ya ji haka sai ya sake tambayar
Wazirin, To yaya kakegani, wace hanya za ka bi har ka shawo mana
kansa?


Waziri ya ce In kai mini izini yau zan same shi na gaya masa
cikin rarrashi kana so ya fito gobe za ka sa a sake shi domin
ya kama maka Malukussaifi, wanda idan har ya kama shi za ka raba
baitul malinka biyu ka ba shi rabi. Kuma za ka aura masa 'yarka, ka
kuma sanya shi wazirin ka na hannun hagu. To na tabbata idan ya ji wannan tun da na fuskanci shi mai kwadayi ne babu abin da zai hana shi yarda ya aikata duk abin da ka umarce shi."

Sarki ya yarda da
wannan shawara kuma ya umarci Waziri da ya je ya samu Sa'adunuzzanji
ya gudanar da wannan lamari.


Waziri ya je kurkuku ya iske Sa'adunizzamji yana daure cikin
sarka, ya zauna kusa da shi ya tambaye shi ya ce, Sa'adunizzanji kana da labarin shugabanka kuwa Maukussaiif?" Sa'ádunu ya ce, "Ai
shugabana tuni uwarsa ta kashe šhi, ai ina ma ina wajen lokacin da za
tà aikata wannan makirci plnata, wallahi da sái na fanshe shi da raina,
domin rayuwarsa ni ta fi wanzuwata a doron kasa."


Ko da Waziri ya ji wannen magana ta Sa'adunizzanji sai ya ce da shi to ka kwantar da hankalinka, shugabanka dai yana nan bai mutu ba yanzu ma haka yaña nan kasar"
Yayin da Sa'adunzzanji ya ji haka sai ya
ce Wallahi ban da ina daure da sai na halaka ka. Don raini har na zamo abin zolaya a wajenka'? Bayan an gaya min shugabana ya mutu sannan ka zo ka
cè wai yaná nan.


Waziriya ce, Wallahi tallali wannan zance nawa babu karya a
cikinsa Wannan rantsuwa wadda Waziri ya yi ta baiwa Sa'adunu mamaki
har ta sa jikinsa ya yi sanyi, ya dubi Waziri ya ce, Me ya faru
gareka Waziri? Ya ya ku da kuke rantsuwa da tauräruwa Zahlu, yanzu
na ji ka yi rantsuwa irin tamu Musulmi?


Waziri ya amša da cewa Ai dama can ni Musulmi ne, ina Boye
Musuluncina ne saboda tsoron wannan azzalumin Sarkin namu." Haka
dai ya kwashe labarin duk irin yakin da akai tsakanin malukussaifi
da sadaukan Sarki Saifu'aradu ya gaya wa Sa'adunizzanji.

Sannan kuma ya gaya masa irin yadda sukai da Sarki game da shawarar da ya
bayar, da yadda har Saki ya yi masa izinin ya zo ya gan shi, ya kuma
ce na shirya wannan dabara ne domin kaa samu hanyar da za ka
kubuta ka koma zuwa shugabanka"

Sa'adunizzanji ya yi farin ciki
kwarai da wannan dabara ta Waziri, ya sumbaci hannun Waziri yana yi
masa godiya.


Wazini yasa ke cewa da Sa'adunizzanji, "Abin da nake so ka yi
shi ne, gobe idan an kai ka gaban Sarki ka kasance mai biyaiya. Duk
umrnanin da ya baka ka bi, to idan ka yi haka zai sa a kwance ka ya
umarce ka da ke je ka yaki Malukussaifi, to ka tafi. ldan kun hadu
kada ka yi saurin bayyana kanka ga shugabanka, ka fara yakarsa,
har zuwa wani dan lokaci, sannan ka bayana masa kanka. Ka ce da shi
dama Idan yake shi ne domin ka jarraba karfinsa, saboda kun dade da
rabuwa. Yin hakan ni kuma zai kubutar da ni daga zargi a wajen
Sarki za a daukagani kai zai rinjaye ka da yaki ka sallama masa, ka
bi shi. Bayan Sa'adunu ya ji kuma ya yarda da dukkan dabarar da
Waziri ya shirya masa, sai sukai sallama da juna, Wazir ya fito daga kurkukun ya bar Sa'adunizzanji cikin farin ciki da begen gamuwa da
shugabansa Malukussaifi lbn Ziyyazanun.
Gari na wayewa sarki saifur'adu ya sa aka fito da Sa'dunizzaji daga kurkuku aka kawo shi gabansa. Sarki ya umarce shi
da ya fita ya yaki Malukussaifi da alkawarin cewa.idan ya kamo shi zai aura masa yarsa ta cikinsa, ya kuma ba shi dukiya mai yawan gaske
daga baitulmali Sa'adunizzanji ya amince kamar yadda Waziri ya ba shi
shawara, aka ba shi makaman yaki, ya fito filin- daga Ko da
Sa'adunizzanji ya hango Malukussaifi sai-wani farin ciki ya mamaye
Zuciyarsa, amma ya boye abun a ransa.


Shi kuwa MalukuSsaifi bai gane cewa wannan barde wanda ya fito
wajensa domin ya yake shi Sa'adunizzanji ne ba, domin ya yi rawank
ya rufe fuskarsa. Haka suka farma juna da yaki har rana tai sama ta
zi tsakiya, sannan Sa'adunizzanji ya yaye fuskarsa. Yayin da
Malukussaif ya gane shi sai ya ce, Kai kuwa Sa'adunu me ya sa ka
yake ni? Sa'aduni ya ce,"Ya shugabana, wannan na yi ne kawai don
na jarraba ka na ga yaya kake, don mun dade ba ma tare. Ya shugabana
ina ka tafi ka bar mu?" Malukussaifi ya ce, "Ai wannan ba lokacin
zance ba ne, lokacin yaki ne."


Da ganin yadda suke hira da juna
Sarki ya fahimci cewa Sa'adunu da Malukussaifi sun yi sulhu. Ya
waiwayo wajen waziri ransa a bace ya ce, Waziri ka ga shegen yaron
nan ya ga Sa'adunu zai rinjaye shi, ya nemi sulhu da shi ko.
Nan da nan Sarki Saifu'aradu ya yi wa mutanensa tsawa yana
cewa, Ku abka musu gabakı daya ku, kama min su." Nan da nan
sadaukan suka yiwo caa gabaki dayansu a kan Malukusaifi da
sa'adunzzanji, suka far masi da yaki Malukussaifi ya riki baryar dama, shi kuma Sa'adunizzanji ya riki baryar hagu, a kai ta gabzawa har rana tadi magariba ta kawo kai.


To a wannan lokaci iluru ya zo ya dau Malukussaifi da Sa'adunuzzanji ya mayar da su kan dutsen nan.

Bayan sun huta liuru ya kawo musu abunci Su ka ci su ka sha ruwa, sai
malukussaifi ya ba shi labarin duk abin da ya faru gare shi bayan
rabuwarsu ya gayawa Sa'adunu, ya kuma nuna masa takobin da ya samo
gidan kakansa Samu dan Annabi Nuhu (AS), Shi ma Sa'adunu ya kwashe
labarin duk irin abin da ya faru gare shi bayan rabuwarsu.

Da gari ya waye, lluru ya kawo musu abinci suka ci suka sha.

Bayan sun gama sai Malukussaifi ya umarci aljani iluru da ya dauke
Su ya kai su kasar Yemen, domim ya dau fansar abin da uwarsa tai
masa. Nan da nan lluru ya kwashe su, su ukun, wato Malukussaifi da
Shamatu da Sa'adunizzanji, ya kama haryar zuwa Yemen Jim kadan Suka
isa bakin birnin Yemen, ya sauke su a kan wani dutse dake bayan
birnin ya kuma je ya samo musu dawakin da za su hau su shiga cikin
birnin.

Awannan lokaci sai Sa'adunuzzanji ya tambayi lluru ya ce,
To yanzu iluru ina so ka gano mini inda mutanena suka tafi bayan an
kama ni
lluru ya ce, Ai mutanenka suna tsakanin wadancan duwatsun da
kake hange."Nan da nan suka hau dawakin nan da Ilura ya kawo musu,
suka nufi inda mutanensu suke. Su kai ta tafiya har suká isa wajen,


ko da mutanen nan saka hango su sai suka zata ko Kamariyya ce ta samu
labarin cewa suna nan, ta turo a yake su, sai duk su kai shirin yaki.
Da suka kusa zuwa inda suke sai Saadunizzanji ya yi musu tsawa
ya ce. Kai ku tsaya ni ne Sa'adunizzanji. Ko da mutanensa su ka
gane shi, sai suka rugo a guje suka tare su suka kai su inda suke
zaune a tsakanin duwatsun nan suka zauna.


Bayan sun zauna sai Saadunizzanji ya tambaye su, Yaya me ya
faru bayan tafiyata Suka amsa masa da cewa, Aa wannan lokacin mu dai mun tashi da safe muka- neme ka ba mu ganka ba, muna cikin haka
sai kawai mutanen wannan birni suka afka mana da yaki, mu kai ta
gwabza fada. To saboda yawansu kuma ga shi mu muna yaki ba wani
shugaba mai kara mana kwarinn gwuiwa, sai muka gaza muka bar yakin
muka gudo muka buya a nan.

Kullum sai dare ya yi mu tura wasu daga
cikinmu su shiga cikin gari su sato mana abinci, haka muka kasance
cikin wannan hali har zuwa yau.
Can sai Malukussaifi ya ce, Ai ku bar wannan zance, ku tashi
ku hau dawakinku mu shiga wannan birni, mu dauki fansa." nan da nan
duk suka koma bayan dawakinsu suka dunguma zuwa cikin birni kafin
su shiga tuni labari ya iske Sarauniya Kamriyya cewa ai ga wata
rundunar mayaka nan ta nufosu. Nan da nan ta tara mayakanta sukai
hawa suka fito taren su Malukussaifi

Zamu cigaba
MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 9.
Ko da haduwar su sai aka kaure da yaki, a kai ta gabzawa,
Malukissaifi duk inda ya sa gaba sai ka ga gawawwakin mutane na zuba,
ya daga takobinsa ya yi kururuwa yana yi wa kansa kirari yana cewa,
"Ni ne Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun, dan Tabi'il Yamani, dan
Usudul bai'da, dan Samu dan Nuhu (AS)
Ko da Kamriyya ta ji haka sai ta san lallai Malukussaifi ne
danta, bai mutu ba. Sai ta ce a zuciyarta,
"Wato wannan tsinannen
dan nawa da na je na sassara bai mutu ba, ga shi har ya warke ya zo
yana yakina." Sai ranta ya baci, ta yi wa mutanen ta tsawa ta ce,
Kai ku tsaya, ku daina yaki, wannan ai Sarkinku ne kuke yakarsa,
dana ne." Yayin da jama'a suka ji haka sai duk aka daina yaki aka
tsaya.
Kamriyya ta sauko daga bayan dokinta: ta zo ta sumbaci kafar
malukussaifi tana kuka tana gaya wa mutanen ta. tana cewa, Ai wannan
shi ne Sarkinku. dan Sarkinku ziyazzanun. Saboda haka yanzu shi za
ku bi, dama ni wakiliya ce Kawai. Sanan kuma ta juya wajen
malukussaifi ta ci gaba da cewa, Ya dana abun da na aikata maka na
aikata maka ne a lokocin na rasa hankalina kamar yadda na gaya maka
a baya cewa wani lokacin na kan zama mara hankali wani lokacin kuma
mahaukaciya.
Tana fadar wadannan maganganu tana kuka, tana birgima a kasa tana
buga kanta a kasa tana cewa, Ya dana, kashe ni ka dau fansar abin
da nai maka, dama babu wanda ya dace ya kashe ni a duniyar nan in
ba kai ba, kashe ni na huta dana.
Shi kuma Malukussaifi da ya ga haka, sai jikinsa ya yi sanyi.
tausayinta ya kama shi, ya dauka da gaske take. bai san makirci ta ke
shirin kulla masa ba. Sai ya sauko daga dokinsa ya rungume ta yana
cewa, Ba komai, ai wannan abu Allalh ne va kaddara haka za ta faru
Tun da ga shi a dalilin hakan har ma na samo wasu muhimman abubuwa
ya nuna mata allonsa ya gaya mata amfanin sa ya kuma nuna mata
takobinsa ya ce, "Wadannan duk a gidan Kakana Samu na samosu
Saboda haka ki kwantar da hankalinki, wannan habu komai ya wuce
Kana ya nuna mata Shamatu, ya kwashe labarin ta ya gaya mata
Kamriyya ta rugume shamatu tana mai murna da matar danta. Sai
ta ce da Malukussaifi, Ai mu je ka shiga birninka ka hau karagar
mulkin ka, shike nan na huta
Suka dunguma cikin birni, Malukussaifi ya hau karagar mulki, a
nan ya yi godiya ga Allah, Sa'adunizzanji na zaune a gefensa. Haka
dai kullum Malukussaifi ya fito fada a yi fadanci ya koma har kwana uku. A rana ta ukun da safe kafin ya fito fada sai ya ga ran Shamatu
ya baci, hankalinta ya tashi. Sai ya tambaye ta ko me yake damun ta.
Shamatu ta ce, Ni yanzu kawai ina tunanin mahaifina ne, saboda
na san sakamakon wannan abu da ya faru babban Sarki Saifur'adu zai
dora masa laifi ne, saboda haka ina tsoron sharrin da zai kulla
masa.
Malukussaifi ya ce da ita, "Ba komai, yanzu zan sa lluru ya kawo
miki shi nan ki ganshi, kuma zan sa ya rika tsare masa garinsa." Nan
da nan ya umarci lluru ya je ya dauko Sarki Afarahu.
Can kuma babban Sarki Saifu'ar'adu, ya kirawo bokayen nan nasa
guda biyu, Sakaradisa da Sakaradiyyuna, ya ce da su,Kun ga wannan
tsinannen ya dau ke Shamatu ya gudu da ita, wato ya haramta mini
auren ta kenan." Sai bokayen suka ce, Ai wannan duk makircin Sarki
Afarahu ne, domin kuwa ba yadda ba mu yi da shi ba, a kan ya kashe shi
tun yana yaro, amma ya ki, ya raine shi har ya girma, yanzu ga abin da
ya jawo mana nan.
Sarki ya ce, Lallai kuwa wannan magana taku haka take. Lallai
ku wa sai na hukunta Sarki Afarahu." Sarki ya tura cikin yaudara a
ka kirawo Sarki Afarahu, ya ce yana so su yi wani sirri ne ya taho shi
kadai
Da zuwan Sarki Afarahu, sai Sarki Saifu'ar'adu ya sa aka kama shi
aka daure shi. Ya umarci hauni da ya sare masa kai, nan da nan hauni
ya zare takobi ya yi wo kansa. Ko da Sarki Afarahu ya ga hauni ya nufo
shi sai ya rintse idanunsa ya ce, ldan abin bautawar nan na su
Malukussaifi, wanda yake gAya mana gaskiya ne, to Ka kubutar da ni
Allah." Rufe bakinsa ke da wuya. kafin hauni ya tarar da shi, sai Iluru ya zo ya dauke shi.
Sarki Afarahu na bude idonsa sai ya ga Malukussaifi da Shamatu
a zaune gabansa. Sai ya ce, "Mafarki nake ne ko gaske ne abin da
nake gani." Malukussaifi ya ce, Ya kai azzalumin Sarki, ya za ka
zalunce ni ka aurar da yarka Shamatu ga wani bayan ka nemi sadakinta
na kawo? Wallahi ba don raino na da kai ba tun ina karami, da na kashe
ka."
Sarki Afarahu ya ce, "Ya dana, wadannan abubuwa duk da ka ga sun
faru duk sharrin bokayen nan ne da sukai kulle-kullensu; ni kuma
saboda gudun kada babban Sarki ya cutar da jama'ata, tilas sai na bi
yadda suke so. Amma ni babu komai tsakanina da kai sai allheri. Ai da ni da shamatu tda mulkina duk naka ne, ai kawai bari gobe a daura
mumu aure a cigaba da biki."
Da Malukussaifi ya ji wannan magana ta Sarki Afarahu, sai ya ce,
To babu komai na yafe maka" Ya kuma kirawo uwarsa Kamriyya su ka
gaisa da Sarki Afurahu, aka shiga maganar daurin aure.
Gari na wayewa Kamriyya ta bude taska ta debo wasu riguna irin
na mata wadanda aka saka su da farin alharini, a kai musu cín baki da
dinare ta bai wa Shamatu ta ce ta sanya, ta kuma debo sarkokin wuya
guda shida da abin kunne da abin hannu na dinare ta ba ta, da kuma
wasu takalma wadanda aka yi su da fatar zaki akai musu ado da gashin
jimina da dinaare duk ta hada ta ba ta ta sa.
Can shi ma malulaussaifi ya caba ado aka fito wajen daurin aure,
inda a nan Kamriyya ya ta kawo wasu lailayayyun dinarai guda uku
wadanda kowannensu darajarsa ta kai kimar harajin kasar na shekara
biyar, ta bayar da su ta ce gasadakın bangarenta ran. Haka dai aka
daura aure a kai ta shagali har kwana bakwai.
A rana ta bakwai, wadda ita ce ranár da Malukussaifi zai shiga
dakin amaryarsa Shamatu, bayan da dare ya yi sai ya shigo wajen
mahaifiyarsa don ya yi mata sallama, ya kuma shaida mata cewar zai
shiga inda matarsa take. Sai Kamriyya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

1 Comments On MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment