Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naushin tayi taga-taga ta tsaya akan gwuwowinta, saida ta watsa mashi wani mugun kallo sannan ta juya ta soma maida martani, ta kaiwa waccen wani naushi karkarfa saida tayi baya-baya sannan tayi warwas a kasa, aka dauki ihu, yayi mata alamar congratulations da hannunsa with murmurshi akan fuskarsa, ya juya yabi ayarin mutane masu fita with smile on his face, ji yayi an rik'e hannunsa anyi gaba dashi, saida ta wuce inda mutane suke sannan ta sakar mashi habbu kafin ya samu zarafin magana ta naushi wani spot a wuyansa ya baje a sume, saida ta targad'a both kafafunsa sannan ta dauko mota tayi parking har inda yake, ta sakashi a backseat, ta wuce frontseat ta dannawa motar key tareda searching inda yake zaune, har villa dinsa tayi parking....
Kasim da ya hango motar tun daga balcony, ya k'araso da sauri saying,
"What happen to him?".
Ta fito dashi tareda reverse ta wuce ba tareda tace dashi komai ba....
Saidai farkawa Maheer yayi yaga kafafunsa nannade, yayi yunkurin d'agawa dasu yaji azaba, smile yayi da gefen baki yana mamakin yadda tayi mashi haka, yana a hayyacinsa amma boom ya rasa hayyacinsa, ta aikata abun da tace....
Kasim yace, "Har godiya saida nayi mata ta kyauta mamu domin ta rabaka da zuwa inda zaka kassara lafiyarsa da sunanka...".
Maheer ya wurga mashi harara saying,
"Wacce kake tsoron ita kayi wa godiya... I see...".
Kasim yace, "Oho...".
Maheer ya ware idanu, da sauri yace,
"Momcy...".
Kasim yace, "She didn't know and I warn them...".
Maheer ya sauke ajiyar zuciya saying,
"You save me....".
Throughout jinyar kafafunsa da yayi Kasim ne yake kula dashi, shine yake mashi komai, har ya soma takawa da abun dogarawa guda biyu, a koda yaushe tana manne a tunaninsa yana wondering akan a wanne hali take ciki, meyyy takeyi, har ya soma takawa da abun dogarawa guda daya, saida kafarsa ta warke sosai sannan ya soma fita, first place da ya fara zuwa shine inda take, saidai har aka gama fad'an baiyi tozali da ko mai KAMANNI da ita ba, haka ya koma gida jiki a sanyaye, Kasim ya lura da halin da yake ciki, ya bishi upstairs saying,
"Buddy what wrong with you?".
Maheer ya zube akan kujera yana maida lumfashi yace,
"Ban ganta ba, and I'm feeling like something is not right...".
Kasim yace, "Kadda ka damu, In shaa Allah komai lafiya lau... Watakila bata da wasa ne shiyasa bata zo ba...".
Maheer yace, "Hakane kuma...".
Throughout the day sukuku ya wuni saboda rashin ganinta da bai yi ba, ji yake kamar ya shekara, zaune ya mike tareda kallon agogon bango, it's late amma ya kasa bacci, ya mike ya wuce bathroom ya zare kayan dake a jikinsa tareda kunna shower ruwa suna dropping a kansa, ya jima a haka sannan ya fito yana daure da towel ya kwanta, ya jima sosai sannan ya samu bacci yayi awon gaba dashi.....
The following day ya koma amma still bai ganta ba, saida ya shafe kwanaki ukku yana zarya amma babu ita babu alamarta, ya damu sosai ya fita hayyacinsa, Kasim da Momcy ne suke tausarsa amma ya sakawa zuciyarsa damuwa sosai har tsoro abun yake basu....
Washegari tare Kasim sukaje amma har aka kusa gamawa babu ita babu alamarta, Maheer ya tab'o wani saurayi tareda mashi pointing hotonta dake a wayarsa tareda tambayarsa dalilin rashin zuwanta....
Kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace,
"She's not coming soon...".
Maheer ya ware idanu saying,
"Why?".
"She got an accident with broken hand...".
Da sauri Maheer yace,
"What? Where did she live?".
Saurayin ya gumtse baki tareda mashi alamar sai ya biya sannan zai fad'a mashi, Maheer ya zaro kudi wadanda shi kanshi bai san adadin yawansu ba, ya mik'a mashi saying,
"I'm hearing...".
Baki daya hankalinsa a tashe yake jin abun da ya faru da ita, Saurayin ya ware idanu yana kallon tullin kudi, baki yana rawa yace,
"No one knows where she live... You can find her at...".
Sai kuma ya juya ya wuce yana tafiya da sauri-sauri....
Maheer ya dafe kai saying,
"I have to go there...".
Kasim yace, "It is late...".
Maheer with damuwa kwance akan fuskarsa yace,
"Kasim kaji abun da yace... I have to see her...".
Kasim yace, "Ka bari sai gobe, she can't be there now...".
Maheer ya gyad'a kai ba don ransa yaso ba, juyawa sukayi suka koma mota, Kasim yayi driving dinsu, throughout the night Maheer baiyi bacci ba yadda yaga rana haka yaga dare, washegari tunda safe ya shirya ya wuce wajen, a zuba mashi coffee ya huce a dauke, ya k'ara saka order a kawo masu, ya zubawa hanya idanu yana dakon ta inda zata bullo amma babu ita babu alamarta, saida ya soma fidda rabo sannan ya hangota tana tafowa with the injury hand an saka mashi abu around her neck, har taja kujera ta zauna bata lura dashi ba, kafin tayi order ya mike tareda jan kujerar dake a opposite da ita ya zauna, saying,
"How's the hand?".
Da mamaki take kallonsa, a fusace ta mike saying,
"Why are you doing this to me? Why are you disturbing my life?".
Maheer yayi murmurshi yana mai kallonta sannan yace,
"Saboda ina sonki, ina son in aureki...".
Ta ware idanu tana kallonshi saying,
"What? Har abun ya kai haka? Wannan salon yaudaren har ina... Ka dubeni ka dubeka sannan kace kana sona zaka aureni, ai Koda makaho ya shafa yasan BAN DACE DA KAI BA... Kai babban mutum ne mai kudi sannan kana da reputation, ni kuma ka ganni kaga kalar rayuwar da nikeyi... Duk wanda yaji wannan maganar da kayi yasan tsabar salon yaudara ne...".
Maheer ya girgiza kai saying,
"Da gaske nike... I'm really serious...".
Ta kalli kanta while saying,
"Bana tunanin kyawuna har ya kai haka, da zaka rink'a bina kana wadannan karyayyakin domin kawai kana san tarayya dani, ka duba da kyau, ba wani kyau ne dani ba... Kuma na fad'a maka ni bana haka, duk salon yaudara da zaka zo dashi... I will not fell for it... Ba haka nike ba...".
Ta juya zata wuce, ya mike tareda riko hannunta, ta juyo tareda mashi wani mugun kallo, da sauri ya sakar mata hannu, ya zaro kudade masu yawa ya mik'a mata saying,
"Gashi kiyi amfani dashi...".
Tace, "Meyyy? In amshi kudinka in biyaka da meyyy, kaga please Ina cikin halin rayuwa wanda bana buk'atar a rink'a joking da rayuwata... Ka barni inji da yadda rayuwa tazo min... Please ka rink'a tausayawa a rayuwarka, wasu suna da tab'o mai ciwo a rayuwarsu kadda kace zaka k'ara masu da wani kuncin...".
Ta juya ta wuce ta barshi tsaye, yayi wa daya daga cikin bodyguard dinsa dake gefe alama, da sauri ya soma bin bayanta cike da kulawa, Maheer ya wuce mota yayi relaxing yayinda maganganunta suke mashi yawo a kwakwalwa, musamman inda take cewa,
"Please ka rink'a tausayawa a rayuwarka, wasu suna da tab'o mai ciwo a rayuwarsu kadda kace zaka k'ara masu da wani kuncin...".
That means ba abu bane mai dadi ya kawota a wannan rayuwar ba, har direba yayi parking tunaninta ne manne a cikin zuciyarsa, ya fito ya shige ciki tareda zubewa akan kujera, Kasim yace,
"Fatan ka ganta...".
Maheer ya gyad'a kai tareda sanar dashi yadda sukayi, Kasim yace,
"What? Are you out of your mind? Yanzu kai sai ka aureta...".
Maheer ya gyad'a kai saying,
"Ehhhh saboda tana a cikin halin rayuwa wanda take buk'atar taimako...".
Kasim yace, "Amma kace saboda tana KAMANNI da abokinka Mujaheed ne wanda kake nema tsayin shakaru...".
Maheer yace, "Ehhh saboda shine, sannan itama tana da buk'atar taimako, kuma zan iya aikata komai domin sanin halin da yake a ciki saidai idan ya kauce hanya ne...".
Kasim yace, "Amma...".
Maheer yace, "Kaga I don't want to talk about it again, a baya na kasa aure ne saboda tunani da yayi min yawa akan halin da abokina Mujaheed yake a ciki, yanzu kuma na hadu da mai KAMMANI dashi kuma zan aureta domin ta sadani dashi sannan kuma a lokaci daya in kub'atar da ita daga halin da take a ciki... Tana buk'atar taimako...".
Kasim yace, "Amma ka duba da kyau, bata dace da kai ba...".
Maheer yayi mashi banza ya wuce upstairs, sai bayan awanni ukku sannan wanda ya saka ya bita ya dawo kuma ya samu nasarar ganin a inda take zaune....
Maheer ya zaro kudade ya mik'awa daya daga cikin bodyguard dinsa saying,
"Bana son ta nemi komai ta rasa, ina sone kayi komai ta yadda ba zata tab'a zargin wani abu ba... Na yarda da kai shiyasa na baka wannan aikin... She is precious to me...".
Two Weeks Later,
Maheer yana zaune a balcony yana duba newspaper yayinda a lokaci guda tunaninta yake manne a cikin zuciyarsa, gobe ne zai koma gida Nigeria kuma zai jima kafin ya k'ara dawowa, rabonshi da ita tun ranar da yace mata zai aureta, kamar a mafarki ya hangota tana tafowa ciki fuskarta a murtuke, da mamaki yake kallonta yayinda ya lumshe idanu ya bude, yayi kewarta sosai, sanye take da dogon wando da riga mai hood, mikewa yayi ya sauko kasa yayinda ta durfafo inda yake, bodyguard dinsa zasu tareta yayi masu alama da hannu, naushi ta sakar mashi a kafa saida ya kusa faduwa, ya saki k'ara saying,
"Ouch... It's painting...".
A fusace tace,
"Da kaga waccen hanyar ba zata b'ulle ba shine ka biyo ta nan, ka sakani amfani da abun da bani da hanyar biya, duk da haka ba zaka samu yadda kake so, ka rubuta adadin kudadenka, idan na samu sauki zan biyaka su daki-daki...".
Maheer yace, "Ni kyauta na baki...".
Tace, "Because you want to sleep with me...".
Maheer ya rumtse idanu saying,
"Why are you doing this to me?".
Tace, "Saboda manufarka kenan... Dole kana da manufa a ranka... Bani da kyau, bani da diri amma ka manne min....".
Maheer ya girgiza kai saying,
"Babu wata manufa... Ina son aurenki ne kawai... Ban tab'a tunani mara kyau a tattare dake ba... Ban shiga rayuwarki domin inyi wannan tarayyar dake ba, babu wata mummunar manufa a tattare dani ba... Trust me...".
Tace, "Yau zan turke mai k'arya... Miye manufarka a kaina?".
Maheer yace, "Ina sonki, ina son in aureki...".
Tace, "Idan har aurena kake so kayi kuma baka da manufa a kaina ni kuma zan dingaya maka sharudda, kadda ka tambayeni komai dangane da rayuwata saidai idan har nice na sanar da kai da kaina... Sannan ba zaka bukaci tarayya dani ba har sai idan nice na bukaci hakan da kaina... Idan kazo da salon yaudara zan k'arya maka kafa da hannuwa ne domin kasan koda karfi ba zaka iya kwata ba...".
Maheer yace, "Na yarda da sharuddanki...".
Tace, "Muje a daura mamu auren...".
Maheer ya ware idanu saying,
"Gobe zan bar kasar nan saidai muje Nigeria a tare sai a daura a can...".
Ta girgiza kai saying,
"Zan bika Nigeria ne kawai idan ka yarda muna sauka zaka nemi Masjid a daura mamu auren...".
Maheer yace, "Na yarda...".


Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

*For those of you da zasuyi payment, zaku tura 600 ta wannan account....*

*9169472057*
*Aisha*
*OPAY BANK*

*Sai a turo evidence of payment via WhatsApp 09169472057...*

*Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057...*


Hafsat Hisham *(AYSHER ANGEL)* 🥰🥰🥰
💨 *BAN DACE DASHI BA* 💨
By Hafsat Hisham
*(AYSHER ANGEL)*


Page 7 and 8
Free page na biyun karshe

Wannan shine free page na biyun karshe da zanyi maku, Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057


Momcy tace, "Amma Maheer baka ganin akwai damuwa...".
Maheer yace, "Momcy babu damuwa In shaa Allah...".
Momcy tayi jim sannan tace,
"Alright, nayi magana da Malam, ku sauka sokoto, akwai daurin auren diyarshi da za'ayi sai a had'a dashi... Maheer amma ina gudun tijarar da Uncles dinka zasuyi...".
Maheer ya dafe kai saying,
"Momcy ki rabu dasu, komai zamuyi ba zamu burgesu ba, ba kaunarmu sukeyi ba, a kullum cikin neman laifinmu sukeyi...".
Momcy ta sauya maganar saying,
"Where's the girl?".
"Tana daya bangaren...".
**********
Zaune take a gefen gado tana bin bedroom din da kallo, mikewa tayi ta tsaya a gaban window tana kallon da tunane-tunane da dama a zuciyarta wadanda suka shafi abun da ya faru da ita a shekarun baya da suka wuce, knocking aka yi tace,
"Yes...".
"Your food...".
Ba tareda ta motsa daga inda take ba tace,
"Drop it there...".
Saida ta dauki lokaci sannan ta mike ta bude kofa ta dauki abincin ta maida kofar ta rufe tareda murd'a mata makulli, ta zauna a saman sofa tana tsakurar abincin, ta kora da ruwa, tunane-tunane ne barkatai a ranta....
Knocking aka yi ba tareda ta mike ba tace,
"Yes... Who's?".
Maheer dake tsaye a bakin kofar dauke da kaya yace,
"Maheer...".
Cikin ranta tace,
"Sunanshi Maheer kenan....".
Amma a zahiri tace,
"Miye?".
"Kaya ne na kawo maki...".
Ta tab'e baki saying,
"Ban san shishshigi, nace maka ina da buk'ata ne... Ko kuwa dama manufarka kenan...".
Maheer yace, "Sorry amma kinyi sallah...".
Tace, "Ina fa shi...".
Maheer ya ware idanu saying,
"Fa shi kuma....".
Saida ta harari kofa sannan tace,
"Idan kana da k'anwa mace kaje ka tambayeta, idan kuma baka da ita ka wuce ka bani waje...".
Maheer yace, "Ohhh na gane... Good Night...".
**************
Washegari da safe,
A hankali take saukowa daga stairs, ta hangoshi a parlor yana sanye da suit, da mamaki yake kallonta ganin tana sanye ne da dogon trouser da rigar sanyi mai hood, a maimakon kayan da ya ajiye mata, ta murtuke fuska ganin kallon da yake mata, har zaiyi magana sai kuma ya share ya mike yayi gaba tabi bayanshi, a Helcofter aka kaisu a inda suka bi private jet dinsa to Nigeria, da mamaki take kallon jirgin har ta zauna, ya zauna opposite da ita, suka dauki hanya, ba tareda Kasim suke ba kasancewar zai wuce ta Dubai ne, tunda suka dauki hanya take busy tana tunane-tunane har sukayi landing a sokoto, har mamakin hakan yake....
**************
SOKOTO
Flight dinsu yana landing motoci sukazo suka daukesu, Maheer yace,
"Miye sunanki?".
Ta murtuke fuska saying,
"Haka mukayi da kai... Nace ban da tambaya...".
"Ina son sanin sunanki ne domin in rink'a kiranki dashi...".
"Call me with whatever name you want, zan amsa... Okay...".
Maheer yayi jim sannan yace,
"Muna a sokoto ne kuma ni dan Kaduna ne, nayi magana da Momcynah tace inzo wajen Malam ya daura mamu auren kamar mahaifi yake a wajena... Kinga kayan da kike sanye dasu... Please I beg of you muje ki sauya wadannan kayan ayi maki gyaran gashi da kafa sai mu wuce...".
Saida tayi jim sannan tayi nodding head saying,
"Okay then kuma idan kazo da salon yaudara sai na tabbata na fitar da kudin jirgin da zan biya a jikinka sannan zan wuce, domin ba zan tsaya kafa da hannu ba...".
Maheer ya ware idanu saying,
"Babu yaudara a lamarina... Angel...".
Ta kalleshi da sauri tana maimaita...
"Angel...".
Maheer ya gyad'a mata kai saying,
"Yeah...".
Ta tab'e baki saying,
"Whatever...".
Direct ya wuce da ita wani katafaren waje, suka shiga ta zauna akan kujera yayinda ya k'arasa yana magana da daya daga cikin ma'aikatan wajen....
Maheer ya koma mota....
Suka soma mata gyaran kafa yayinda wata take kunce kitson dake a saman kanta, sunyi mamaki sosai na kasancewar duk tsayin kitson gashinta ne....
Some Hours Later,
Wata cute babe ce take fitowa daga wajen tareda daya daga cikin ma'aikatan wajen, tunda suka fito ya zuba mata idanu ba ya koda blinking, she's brown, slim, tall, gorgeous and breathtaking, he can't take his eyes off her, tana sanye ne da black arebian gown mai adon fatar damisa, tayi rolling veil, hancinta dauke da pierce readymake, kafafunta sanye da flat shoes, the more yake kallonta the more take k'ara mashi kyau sai yake ganin tana mashi KAMANNI da wata wadda ya sani, ya ware idanu ganin sun nufo inda yake, ta bud'e daya bangaren ta shiga yayinda ma'aikaciyar da suke a tare ta mik'a mashi card dinsa ya amsa, ya juya tareda zuba mata idanu yana tantamar sauya mashi Angel aka yi, kyanta, dirinta, komai nata daban ne, slinder in shape, figure 8, kafin ya ankara ta kai mashi punch a hannu, ya saki k'ara saying,
"Ouch...".
Yana mai yarfe hannun, ta murtuke fuska saying,
"Ban san kallo...".

Maheer yana tuki yana satar kallonta tayi matuk'ar mashi kyau, a bakin wani get ya danna horn aka wangame mashi get ya danna motar ciki, yana parking ya fito tareda zagayawa ya bud'e bangaren da take ta fito, saida ya saci kallonta daga sama har kasa ya hade miyau dakyar sannan ya juya ya soma taking steps yayinda tabi bayanshi, sashe shidda ne a gidan, da salaam ya shiga falon a inda wani mutane mai cikar haiba yake zaune yana bitar littafin addini, ya d'ago tareda amsa salaam da sukayi, ya nuna masu kujera, Maheer ya zauna yayinda ta zauna kujerar dake kusa dashi...
Malam yace, "Maheer kune... Ya hanya...".
Maheer yace, "Alhamdullilah... Mun sameku lafiya...".
Malam yace, "Lafiya lau...".
Tace, "Ina wuni?".
Malam yace, "Lafiya lau diyata... Kun zo lafiya...".
Tace, "Lafiya lau...".
"Masha Allah... Maheer munyi magana da mahaifiyarka tayi min bayanin komai... Diyata miye sunanki?".
Maheer ya kasa kunne eager to hear her name...
Saida ta kalli inda yake ta wurga mashi harara sannan tayi kasa da kanta saying,
"Maimoon...".
Maheer under his breath yace,
"Maimoon... Nice name...".
Malam yace, "Maimuna ashe ma Mamana ce, anyi min bayani, akwai auren diyata da za'a daura gobe idan Allah ya kaimu sai a had'a dashi... Zai barki a nan... Ki kwantar da hankalinki nan gidanku ne kema, sunan uwar mai gidan kike dashi, babu wanda zai takura maki... Ki saki jikinki...".
Maimoon ta gyad'a kai ba tareda tace komai ba, Malam yace,
"Maheer kuje ka kaita bangaren Hajiya Babba, kace masu dayar amaryar ce, kaje ka dawo in yanka maka sadakin Mamana domin Mamana tsada ne da ita, idan baka iyawa mu nemi wani...".
Maheer yayi kasa da kai yana sosa kai, ya mike yayi gaba tabi bayanshi, yana gaba tana biye dashi suka nufi wani sashe, da salaam suka shiga, en mata ne zaune a parlor, a tare suka gaidashi ya amsa da murmurshi akan fuskarsa, yayi pointing kujera wa Maimoon ta zauna, yace,
"Jasmine... Momi fa?".
Daya daga cikin en matan tace,
"Momi tana sama bara nayi mata magana...".
Maheer ya gyad'a mata kai yayinda ta mike ta wuce sama, jim kadan ta dawo saying,
"She's coming...".
Maheer yace, "Thank you...".
Wata cute Hajiya ce ta sauko tana da sanye leshe, da murmurshi akan fuskarta tace,
"Maheer, idonka kenan, baka son zumunci...".
Maheer yayi kasa da kai yana sosa kai yace,
"Momi Ina wuni?".
Momi tace, "Lafiya lau... Ai dama ka janye maganar tunda baka da gaskiya...".
Maimoon tace, "Momi Ina wuni?".
Momi tace, "Lafiya lau en mata... Kun zo lafiya...".
Maimoon tace, "Lafiya lau...".
Momi tace, "Masha Allah...".
Sai kuma ta juya ga Maheer tace,
"Na dawo kanka ina jinka tunda nasan taka ce ta kawoka...".
Maheer ya sosa kai saying,
"Baba Malam yace in kawota, dayar amaryar ce...".
Momi ta fad'ad'a fuskata da murmurshi saying,
"Masha Allah... Allah yasa albarka... Miye sunanta?".
Maheer yayi murmurshi saying,
"Maimoon...".
Momi tayi murmurshi saying,
"Hajiya kaka ce kenan... Mariam tashi kuje ki rakata sashen Hajiya k'arama wajensu Fatima...".
Mariam tace, "Sure...".
Ta mike, Momi tace,
"Ki bita kuje...".
Maimoon ta mike suka jera suka fice, Momi tace,
"Ka wuce dinning table akwai abinci and I don't want a complain...".
Ta mike ta koma sama....
Maimoon tana biye da ita har suka shiga wani sashe, wata mata ce zaune a parlor tareda wasu mata....
Mariam tace, "Mamaah Ina kwananku?".
"Lafiya lau...".
"Dayar amaryar ce Momi tace in kawota wajensu Fatima...".
"Daya amaryar ce... Masha Allah...".
Maimoon ta d'ago saying,
"Ina kwananku?".
"Lafiya lau...".
Mariam tana gaba tana biye da ita suka haye sama to one of the bedroom dake a upstairs, ta bud'e suka shiga, en matan amarya ne zaune a parlor, tayi masu waving hand suka wuce bedroom, en mata ne guda ukku, Mariam tace,
"Aunty Fatima.... Ammi tace in kawo maki ita, dayar amaryar ce...".
Fatima ta fad'ad'a fuskata da murmurshi saying,
"Maimoon barka da zuwa... Seat...".
Maimoon ta zauna akan sofa tana bin bedroom da kallo, Fatima tace,
"Mariam ki amso mata abinci a sashen Ummy... Bara na kira Nabila, idan ta gama tayi wanka sai tayi mata henna...".
Maimoon ta soma tsakurar abincin har ta koshi ta kora da ruwa, Fatima ta mike ta wuce bathroom jim kadan ta fito saying,
"Na had'a maki ruwan ki shiga kiyi wanka, mai kunshi zata zo tayi maki, Momi ta turo wacce zata maki gyaran gashi da jiki...".
Maimoon tayi jim sannan ta mike heading to the bathroom, sai kuma ta tsaya cak tareda juyowa tace,
"Pad...".
Fatima tace, "Tana nan a cikin locker har da auduga...".
Maimoon ta jima a cikin bathroom sannan ta fito tana daure da towel yayinda jikinta yake dropping, wani kamshi mai dadi ne manne da ita, wayam ta tarar da bedroom din, kaya ta hango riga da zani akan gado, ta k'arasa gaban mirror tayi applying cream tareda goge fuskarta tana kallon sauran kayan makeup yayinda take tuna yadda aka koya mata yadda zatayi amfani dasu, ta mike ta dauki rigar ta saka, ta dauki zanen tana juyawa amma ta rasa ta yadda zata daurashi, koda a shekarun baya bata iya ba ballantana kuma a yanzu....


Wannan shine free page na biyun karshe da zanyi maku, Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

*For those of you da zasuyi payment, zaku tura 600 ta wannan account....*

*9169472057*
*Aisha*
*OPAY BANK*

*Sai a turo evidence of payment via WhatsApp 09169472057...*

*Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057...*




Hafsat Hisham *(AYSHER ANGEL)* 🥰🥰🥰
💨 *BAN DACE DASHI BA* 💨
By Hafsat Hisham
*(AYSHER ANGEL)*


Page 9 and 10
Free page na karshe

Wannan shine free page na karshe da zanyi maku, ku hanzarta kuyi payment kadda ku bari a baku labari, Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

Maimoon tayi jim tana k'ok'arin tuna sunan da taji an kira amaryar dashi, tace,
"Aunty Fatima...".
Fatima ta shigo tana mai ware idanu saying,
"Wacece Aunty Fatima kuma... Ki rufa min asiri kadda Yaa Maheer yaji labari...".
Maimoon tace, "Ban iya daura zanin ba...".
Fatima tace, "What? Are you serious, daura zanin...".
Maimoon ta gyad'a kai saying,
"Ban iya ba...".
Fatima ta amsa tareda nuna mata yadda zatayi sannan ta daura mata, Maimoon ta mik'a mata kallabin saying,
"Ki daura min shima ban iya ba, na manta...".
Fatima ta amsa ta kashe mata dauri samfurin ture kiga tsiya, she looks gorgeous and breathtaking a cikin atamfar wacce take dinkin riga da zani, Fatima tace,
"Masha Allah... Ya kamata ki koyi daurin kallabi, akwai wasu videos a wayata da ake koya samfurin daurin kallabi iri daban-daban...".
Maimoon ta ware hannuwa saying,
"Bani da waya...".
Fatima tace, "Sai inyi maki sending a wayarsa...".
Kafin wata a cikinsu ta k'ara magana, aka yi salaam, daya daga cikin en matan da ta gani a sashen da suka fara zuwa ce....
Fatima tace, "Afrah...".
Afrah ta k'arasa tareda mik'a wa Maimoon waya dake a hannunta tace,
"Inji Yaa Maheer... Aunty Fatima mai kunshi tana jira a waje...".
Fatima tace, "Alright kice ta shigo...".
Afrah ta juya ta fice wanda yayi daidai da k'arar da wayar tayi, Maimoon ta duba taga an rubuta _Hayatee_ ta tab'e baki sannan tayi picking, daya bangaren yace,
"Salaam alaiki...".
"Wa alaikissalaam...".
"Na wuce gidana dake a garin nan...".
Maimoon ta tab'e baki saying,
"Did I ask? Who's care...".
Sai kuma tayi gum da bakinta lura da Fatima tana a dakin....
Maheer yayi murmurshi saying,
"Amaryata...".
Maimoon ta tab'e baki saying,
"Uhmm...".
Maheer yace, "Da mutane a kusa kenan otherwise ba haka zaki ce ba... You will be like, ka k'ara sai na k'arya maka hannu da kafa, ki rink'a min mugunta, saukin abun kanki kikeyi mawa... Daga gobe I'm all yours... Maimoon...".
Maimoon tayi mashi banza, yace,
"Hope kina jin dadin zama a nan...".
Maimoon tayi jim kamar ba zata amsa ba sai kuma tace,
"Ehhh... Bye...".
Tayi hanging call din tareda kashe wayar baki daya....
Fatima tace, "Kawo wayar sai inyi maki sending...".
Maimoon ta kunna wayar da sauri sannan ta mik'a mata yayinda mai kunshi ta soma cancara mata henna wacce take unique irin na amare en gata, saida aka gama mata henna sannan aka soma wankin kai da gyaran jiki, sai karfe sha biyu na dare sannan aka gama ta kwanta bacci ne yayi awon gaba da ita wanda yake tattare da mafarkai akan yadda rayuwarta take a shekarun baya kafin ta bar kasar bayan da ta yanke tsammani akan daidaituwar komai....
A hankali Maimoon ta bud'e idanunta tareda kare hasken da ya dalle idanunta, ta duro daga saman gadon ta wuce bathroom ta jima sannan ta fito tana daure da towel, ta tarar da breakfast tareda gown akan gado, tayi applying cream ta zura gown din tareda rufe kanta da veil, ta soma tsakurar abincin tana gamawa, Mariam ta shigo ta mik'a mata kofi wanda yake cike da wani abu kamar magani, tace,
"Momi tace ki shanye ki bada kofin a mayar mata...".
Maimoon ta kalli abun da yake cikin kofin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment